Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita Naga wani Dan taxi nace ya taimakamin ya kaini asibiti 'yata zata mutu.

Tun Bai gama tsayawa ba na bud'e k'ofar na afka ciki Nadeeya rungume Dani Ina ta kuka jinin dake zuba Akan ta ba karamin girgiza ni yayi ba.

Asibitin da muke zuwa na Kai Nadeeya Mai taxi kuwa ganin halin da nake ciki yasa Bai tsaya amsar kudinsa ba yayi tafiyarsa.


Da yake nurses da likitocin sun sani sosai Sabida haihuwar Nadeeya Dana Zahira duk a asibitin nayi Kuma Naseer na musu alheri sosai Sabida bashida rowa har gida suna zuwa dubamu idan Wani bashida lafiya.

Da Sauri suka karbi Nadeeya suna tambayata Mai ya sameta.

Ko magana ban iya Yi ba in Banda ku taimaka.min danake ta cewa.

Wani daki aka Kai Nadeeya suka hanani shiga.

Minti talatin din danayi Ina jiran fitowarsu sai Dana ga kamar awa talatin ne duk na matsu su fito Naga lafiyar 'yata.

Fitowar Likitan yasa nufeshi da Sauri Ina tambayarsa jikin 'yata

Sai Dana ga yana ta k'ok'arin fusge hannunsa daga ruk'on danayi Masa nasan Ashe ma hannunsa na ruk'o sabida tashin hankali.

K'ofar d'akin ya bud'e min ya Nuno min Nadeeya da sukayi wa dinki akai da ke ta sharar bacci ya bani hakuri akan Kar nashiga sabida Kar na tasheta.

Sai sannu yakemin sabida cikina dayayi turtsetse a gaba yace na samu waje na huta.

Ban iya zama ba Haka nake ta Kai kawo ko nauyin cikina banaji har sai Dana tuna Ashe banyi Sallah Laasar ba kafin na nemi buta na daura alwala Allah daya taimakeni da hijabi a jikina Dama ban cire ba.


Kebabben waje na samu nayi Sallah duk ba nutse ba sai Dana iddar da sallahn na fashe da wani irin kuka danake taso nayi tun dazu yak'i zuwa Sosai na jika gaban hijab Dina da hawaye Ina tunanin halin Danake ciki Sabida kawai abinci kannen mijina suka rufeni da duka Haka har abin ya shafi 'yata su fasa mata Kai.

Sosai nake kudirtawa Raina guduwa daga asibitin Amma Zahira Dana tuno yasa na Kara fashewa da Kukan Dan bazan iya guduwa na barta ba da da ita na fito da wlh babu abinda zai maidani gidan.

Gani nake babu Wanda ya Kai Su Umma rashin Imani gani nake babu Wanda ya Kai Su mugunta da rashin tausayi.

Bansan Magriba tayi ba sai da naji wata nurse ta tsugunna a gabana Tana bani hakuri akan na bar kukan Haka komai yayi tsanani maganinsa Allah.

Bansan ya akayi na kwanta a Jikinta na riketa Gam Ina cigaba da kuka ba so nake na fada Mata halin da nake ciki ko Yaya ne Amma tsabar kukan danayi maganar tawa taki fitowa sai sheshek'a nake.

Dak'yar ta kwace jikinta daga nawa idonta itama da hawaye tacemin nayi hakuri ga mijinta can yazo daukarta ta Gama duty dinta.

Ji nake kamar na bita aguje Dana hango tausayina a idonta kamar na riketa Gam na hanata tafiya sabida kawai ta taimaka min.

Nadeeya data fad'omin yasa na mik'e da Sauri nayi wajen d'akin da aka kwantar da ita.

Ina bud'e k'ofar tana bud'e idonta.

Da Sauri na ka rasa gadon na jawota jikina na rungume Ina fashewa da wani sabon kukan

Sosai nake tausayin kaina Dana yayana.

Ummata kawai nake kira da Abbana.

Wata nurse ce ta shigo ta bani hakuri tace zamu iya tafiya Dan Naseer ke biyan kudin asibitin ta bani ledar magani.

Kalmar xamu iya tafiya data ce ne yasa na Kara fashewa da kuka na tsani gidan Nan inama da Zahira na fito wlh Tallahi babu abinda zai maidani gidanan na gwammace na gudu da yayana.

Nurse din kuwa Tsaki tayimin tayi tafiyar ta Tana Jin Haushin yanda nake ta kuka akan 'yata taji ciwo ita Kam batasan kukan da nake ba.

Duk da nauyin cikina ahaka na kunce dankwalina na goya Nadeeya muka d'au hanya a lokacin dare yayi.

Ba fita nake ba ballantana nasan ko ina a yanzu ma bansan hanyar komawa gida ba.

Tafiya kawai nakeyi Ina tunanin inama mota tazo ta bi ta Kaina da Nadeeya mu mutu itama Zahiran ta mutu mu huta.

Sai danayi ta zagaye kafin na gane hanyar gidan da sai Dana balain gajiya.

Ina zuwa kofar gidan na kunto Nadeeya dake bacci na kwantar da ita a kasa Ina fargabar kwankwasa k'ofar Gidan

Ciki kuwa Umma ta cika tayi fam tana jiran dawowata Dan Bata Nan mukayi fada da su Saffiya tana dawowa suka Gaya Mata Kan lami data gani a kumbure ne kawai ke tafasa zuciyarta sosai takeji lokaci yayi da zata saka Yaya matanta a kungiya ko Dan irin abinda ya faru Allah Allah kawai take taga ta Inda zan shigo Dama idan ranta ya b'ace yake shigar bak'akken Kaya takeyi.

Naseer kansa daya dawo gidan sai daya San yau Mahaifiyarsa ba daidai take ba hakane yasa daya shiga dakinsa ya kulle Dan Haka kawai yau bayajin dadin Jikinsa Yana so ya tambayi Zahira da Nadeeya Yana Jin tsoron tambaya Kar yayi laifi.


K'ofar kawai Hajara ta zubawa Ido tana kallon Naeema datayi zaman dirshen a k'ofar Gidan tana tsoron kwankwasa wa.

Hajara kallonta kawai take Tana tunanin matakin daya Dace ta d'auka akanta Wata biyu ya rage wa Naeema Dan sun Gama tsara abinsu kamar idan tazo haihuwane ta mutu Amma mutuwar tata sune sila a da batayi niyyar kashe Naeema ba taso su rabu Salin Alin data haifi Zahira Amma sabida taurin Kan Naeema shine tayi mata gardama, taki tafiye tana ta Mata haife haife ita Nan Mai wayo baa ja da ita Amma Naeema ta ja da ita gani take Dole Naeema akwai abinda ta dogara dashi shiyasa take tsallake duk abinda tayi Mata.

A yau Naeema ta Mata abinda takejin kamar tun a daren yau ta rabata da ranta.


Ahaka ta zubawa kofar ido Bata motsa ba.

Naeema itama Bata kwankwansa ba sabida tsoro har karfe dayan dare Naeema na waje ta kasa kwankwasawa Sabida masifar tsoro.

Haushin karnuka ne yasa na jawo Nadeeya jikina na fara kwankwasa k'ofar a hankali tun inayi a hankali da Sauri na fara bubugawa Sabida tsananin tsoro ga wani irin Kara da nakeji.

Da iya karfina na fara buga gidan Ina waige waige ai kuwa waigawar da zanyi Naga wani irin bakin mage ya zuromin ido.

Wani irin razanann Kara na saki na fara kwalawa Umma Kira Dasu Safiyya tsabar tsoro har da Naseer na hau Kira.

Ina jijjiga k'ofar.

Karar buga k'ofar ne yasa Naseer da bacci ya fara dauka akan Sallaya mikewa da Sauri tare da yin waje.

Wani irin fad'uwa gabansa yayi a lokacin dayaji muryar da yaso tuna na waye Amma ya kasa tuna Mai muryar sai kiransa take Tana yazo ya taimaka Mata.

Gadan gadan ya nufi kofa.

Hajara ta Dago manyan idonta ta watsa Masa shi kuwa Naseer ya tsaya cak Yana Dan addua a Ransa a idonsa sai yaga kamar ba Hajaran ba wata hallita ce zaune Mai ban tsoro.

Da hannu ta nuna Masa d'akin shi kuwa ya juya da Sauri ya koma d'akinsa.

Hajara kuwa ta mik'e ta nufi kofar tana bud'ewa Naeema ta fado jikinta sabida tsananin tsoron Magen daya nufota Yana Dab da Isa wajenta taji an bud'e k'ofar.

Wani irin kallo Hajara ta hau Mata Naeema kuwa ta sunkuyar dakai ta na bata hakuri idonta a rufe Gam Sabida tsoron Hajaran


Ji nayi kawai ta finciki hannuna tayi dakina Dani.

Muna shiga ta watsar Dani tana hucci ni kuwa na rungume Nadiya gam jikina na rawa addua kawai nake a raina.

Umma ta Dade tana kallona kafin naji ta juya ta fita tare da bankomin k'ofar.

Dan yanda ranta ya b'aci ba a iya duka zata tsaya ba sai ta raba Naeema da ranta sai dai lokacin yin hakan baiyi ba.

Ni kuwa Tana fita na shige bandakina da Sauri na daura alwala Nazo na tada sallah Dan nasan bazan iya bacci ba har yanzu Ina hango katon bakin magen Nan a idona.

Ina Kan Sallaya bacci ya daukeni bansani ba.


Naseer kuwa Yana shiga d'akin ya rik'e kansa Gam Sabida mugun ciwon da yake masa muryar Naeema kawai yake ji a kansa tana kwalla Masa Kira sosai yake so ya tuno Mai muryar matsawa.kansa da yayi da San tunawa ya haddasa Masa mugun ciwon kai.

Shi kansa yasan ba daidai yake ba ya rasa Mai ke damunsa ya Dade a Haka kafin bacci ya d'auke shi batare da.yasani ba



*Mafarki*

Naseer akwai aiki a gabanka idan baka dage da Addu'a ba
bacci Bai ganka ba Naseer ka tashi ka gana da mahallicinka ka ware murya ka fara karatun Qurani a gidanan matarka na bukatar taimakon ka.

Murya kawai Naseer Yaji Bai San Wanda ke Masa magana ba da sallati ya tashi mafarkin na sake dawo Masa kamar a gaske.

Da Sauri ya mik'e ya shiga bandaki ya d'aura alwala yazo yayi kyakyawan Sallah raka'a biyu Yana iddarwa ya jawo Qurani ya Ware muryarsa ya fara karanta Ali Imran dayake dare ne take muryar sa ta karade ko'ina.

Hajara dake zaune a d'akinta tana ayyana mugayen abubuwa kuwa ta mik'e zumbur tayi waje da saurin ta jikinta na d'aukar zafi..........[6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 7*



Salon da Naseer ya b'ullo dashi na karatun dare ba karamin dagawa Hajara hankali yayi ba Dan Naseer tunda yayi wanan mafarkin ya zage damtse wajen kusantar Allah.

Sosai ya fara Dan jin canji a jikinsa duk da har lokacin ya kasa tuna Naeema Sabida ba karamin aiki sukayi a kansa ba.

Koda aikin da sukayi Masa ya dauko hanyar warwarewa daya ci abincin da Hajara ke tilasta Masa yaci daya Sha barbaden magani sai aikin ya cigaba da tasiri akansa

Hajara da Yan kungiyanta sosai hankalinsu ya tashi da yanda Naseer ke neman zame musu barazana Dan Ta Kai Hajara Bata iya kwanan gidan Sabida kwana da yake Yana karatu Wanda idan tsautsayi yasa ta kwana a gidan komai na iya faruwa babann tashin hankalinta Bai wuce Kar aikin data Masa na manta Naeema ya wargaje ba.

Bata da burin daya wuce har ta Gama da Naeema Kar Naseer ya dawo hankalinsa.

Sanin idan Hajara ta b'ata Rai Naseer Kan shiga tashin hankali Dan sosai yake Mata biyayya Kuma bai San b'acin ranta.

Magani Shugabarsu ta Bata Wanda zata na zubawa Naseer abinci a ciki da indai ya Kai abincin bakinsa toh duk jikinsa zai mutu bazai iya aiwatar da komai ba Daga Nan ma bacci Mai nauyine zaiyi awon gaba dashi.

Da Wanan salon suka samu Naseer ya daina karatun daren Dan Da farko da Hajara ta bashi abincin dage mata yayi da ya koshi duk da yana tunanin Hajara bazata iya cutar dashi ba Amma abincin da take bashi zuciyarsa Bai kwanta da abincin ba shi ba yaro bane Dan abinda yake gani a abincin da taste din abincin na nunawa Abu aka saka a abincin.


Har a lokacin ya kasa tuna Naeema Amma idan zai kalli Zahira da ba Inda ta baro Mahaifiyarta sai yaji Yana San tuno Naeema Inda Yana matsawa kansa da tunanin kansa zai hau ciwo.


Naeema


Tun da mukayi rigama dasu Safiyya babu Wanda ya Kara kallon Inda nake da Umma Wanda hakan ya balain bani mamaki Dan na d'auka washegari Umma zata sakosu a gaba su nada min duka ga mamakina babu Wanda ya kalli ma d'akin da nake da farko a tsorace nake Ina tunanin bazasu shareni a banza ba kila akwai wani mugun abinda suke San kulla min.

Hakane yasa na dage da Addu'a Ina gayawa Allah Dan zuwa yanzu da cikina yake neman shiga wata goma Sha daya na balain fara tsorata da haihuwar da banyi ba har yanzu gashi cikin nawa ya Kara tsini ya koma kasan marrata.

Abinda ya Kara bani mamaki Bai wuce yanda Aka bar Zahira da Nadeeya suke zuwa wajena har suke kwana ba.

Kwana biyar da rigimata dasu na fito daga d'akina Sabida yunwar daya koroni dama bredin Dana d'auko daga kitchen nake ta cancanawa Ina ci da ruwa dazu na cinye ragowar yanzu kuma naji Ina Jin yunwa da biyu na fito sabida na ga ko su Umma zasumin masifa kamar yanda suka Saba Dan Ni tun sanina dasu tsawa da hantara ne a tsakaninmu sai rankwashi da duka.

Hannuna rike Dana Nadeeya data mak'alemin tunda Lami ta fasa.mata Kai muka fito Ina Dan Jin fad'uwar gaba.

Duk suna zaune a Palo suna kallon Indian film Nagi

Fitowa ta yasa Umma ta juyo ta zubamin Ido Ni kuwa jikina ya hau rawa Dan tun lokacin Dana dawo ta saka wanan bakar doguwar rigar bamu kara haduwa ba sai yanzu.

Tsintar kaina nayi da nufar wajenta.

Ina zuwa na zub'e a gabanta Akan gwiwata na hau hawaye.

Bata cemin kalla ba in Banda wani irin kallo da take Bina dashi tana jifana da wani irin murmushi daya saukarmin da wani irin tsoro da fad'uwar gaba


Hajara kuwa kallon gawa kawai take wa Naeema Dan a yanda suka tsara Naeema saura Mata sattika biyu ko.uku ta bar duniya abinda basu sani ba shine ran Naeema ba ahannunsu yake ba a hannun Allah yake.

Cikin kukan da bansan d'annewa nake ba na rik'e kafar Umma na fara magana Ina "Umma Dan girman Allah ki Yi hakuri ki yafemin idan laifi na miki Umma banida kowa sai ku ke nake wa kallon iyayena da suka ragemin Umma Mahaifina da Mahaifiyata sun tafi sun barni yayana shima ya tafi ya barni banida kowa sai ke sai Naseer da yarana Umma idan Wani Abu nake yi da bakiso Dan Allah ki gayamin wlh xan daina wlh bazan sake ba Umma duk abinda Kika Sakani zan Miki Umma Dan Allah ki rik'eni tamkar su aunty Safiyya insha Allahu zan bauta Miki na miki biyaya kamar yanda nake yiwa iyayena Umma ki taimakamin Dan girman Allah wlh banida kowa sai Allah sai ku"


Kasa cigaba nayi da Magana sabida kukan dayaci karfina na rik'e kafar Umma Gam Ina cigaba da kuka abinda bansani ba Umma ita Bata San wani Abu tausayi ba ballantana tasan yanda yake tsugunnawan da nayi agabanta Ina rokonta ita hararo gawata take a kwance Sabida tsananin Tsanar da tamin.

Irin ruk'on dana yiwa kafarta Yasa ta janye kafarta ta Dago hab'ata ta zuramin Ido cikin wani irin murmushi da idan tamin gabana ke tsinkewa banga alamar alheri a Fuskarta ba sai Sharri.

"Bakimin komai ba Naeema bana sanki ne kawai Sabida San danaga d'ana na miki da har ya kasa b'oyuwa Naeema tun Kafin ki haifo wanan er Taki Mai zubin Aljannu na baki shawara da idan kin haihu ki saka Naseer ya sakeki wata itama tazo taci rabonta Kika k'i Naeema Kika min taurin Kai Kika ja Dani
ba abinda ban miki ba Dan ki rabu dashi Kika k'i Kika sake haihuwa alamar akwai abinda kika tak'a Dan Haka nayi abinda zanyi ke gaki D'ana tare aka haifoku duniya bazaki iya rayuwa idan babu shi ba nayi abinda zanyi to nayi abinda zanyi Naeema ki haihu nagani ki tashi ki bani guri yanzu Zaki iya duk abinda ranki keso bazan hanaki ba Dan na d'an lokaci ne"


Umma tace tana Kara min wani irin murmushin daya sa na Dora hannu a aka na fara kuka.

Tuni na nemi yunwar da nakeji na rasa yau kalaman Umma sun tsoratani sun saka min balain fargaba da na hau nadamar Mai ya hanani tafiya lokacin da na haifi Zahira a Palo duk suka watse suka barni.

Ni kuwa Jin zazzabi na neman rufeni sabida tashin hankali yasa na rarrafa na shiga d'akina.

Ina kwanciya wani irin Mugun zazzabi ya rufeni.

Nadeeya da Zahira kuwa na gefena suna ta min Sannu.

Bansan ya akayi bacci ya d'aukeni ba

A cikin baccin da nake Naga kamar mahaifiyata ta shigo d'akina ta tsaya daga bakin kofa tana kallona tana ta hawaye Ni kuwa sai mik'a Mata hannu nake Akan ta tafi Dani ita kuwa ta ringa girgiza min Kai sosai nake ta kokarin mik'ewa Dan naje gurinta naji jikina yayi balain nauyi na kasa tashi a Haka na zuba Mata Ido Ina kuka tana kuka sai gani nayi ta nufi dakalin dake tsakar gida ta d'au buta ta hau alwala tana gamawa na ga ta shimfida Abu ta tada Sallah tana iddarwa ta daga hannunta sama tana ta maganar da ba jinta nake ba tana ta hawaye sai jijjga hannunta take alamar rok'on Allah take.

Idona na bud'e a hankali sai Dana kwashi Sakani nasan Ashe mafarki nake ba da gaske bane mafarkin Nan da nayi kamar ba mafarki ba.

Yanda naji jikina yamin nauyi a mafarki yasa na fara k'ok'arin mik'ewa sai dai me Ina duba jikina Naga duk na kumbura kamar wacce aka hura k'afafuna ma sunyi wani irin nauyi da kumburi jikina yayi wani irin Haske Kamar wacce Bata da jini.

Take maganganun da Umma tamin dazu suka fad'omin mafarkin danayi da Mahaifiyata tana hawaye tana rokon Allah a mafarki shima ya fad'omin.

Girgiza Kai kawai nake hawaye na zubomin Ni nasan tawa ta zo karshe mutuwa zanyi haihuwa da Umma take ta cemin nayi tagani Ashe mutuwa zanyi bazan haihun ba mutuwar da zanyi Ashe shiyasa Naga Mahaifiyata a mafarki tana kuka tana rokon Allah.

Kuka na fara sosai Ina tausayawa kaina ganin ban shirya ba mutuwa tazo min tausayin yarana da zan tafi na barsu a hannun Umma kawai ya balain Sakani kuka banso a yanzu zan mutu ba naso Na haihu Naga abinda ke cikina inkare yarana daga sharrin Umma da yayanta naso nasake ganin Naseer muyi magana kafin na mutu naso Na samu ilimi da zan San Mahallicina Sabida na bauta Masa na samu guzurin da zan tafi kabarina.

Kuka nake sosai Ina Kara kallon jikina dake ta kumbura kamar Ana hura min iska.

Hannuna kawai nauyi yayi min Kamar dutse ballantana na iya daga jikina na tashi nayi alwala nayi Sallah idan akwai abinda nake San Yi yanzu bai wuce nayi Sallah ba inama inada ilimin addini inama yanda Naseer ya iya Karatun Qurani dake balain Sakani nutsuwa idan Yana karntawa da yanzu na karanta naji nutsuwar da zanyi addua na roki Mahallicina ya kularmin da yayana dan shi kadai gareni yanzu.

Ni nasan mutuwa kawai zanyi daga yanda nake ta kumburan Nan Ashe Umma tasan kasheni zatayi shiyasa kwana biyu ta shareni ko Mai nayi Mata haka da take ganin kasheni shine mafita a gareta.


Bansan tsawon lokacin Dana d'auka a kwance a Haka ba ko kaina bana iya dagawa ballantana na kalli window naga ko dare yayi.

Sallatin da iya shi na iya da fatiha da iklas kawai nake yi a zuciyata Dan nasan kowane lokaci zan iya tafiya yayana dake ta bacci a gefena nake wa kallon tausayi Ina hawaye.

Yanayin danaji garin ya dau shiru sosai sai Haushin karnuka sama sama yasa nasan dare yayi sosai ko karfe dayan dare ko biyu.

K'ofata da aka bud'o yasa na kalli bakin kofar.


Umma ce ta shigo cikin jajjayen Kayanta hannunta d'auke da wani bak'in tunkunya an rufeshi da farin kyalle Fuskarta kuwa d'auke da murmushi.

Kallonta kawai nake hawaye na gudu a fuskata na rasa Mai nayi Mata rayuwa ta tsaneni Haka.

Ajiye tunkuyar tayi bakin kofa ta karaso kan gadon cikin murmushin daya bayyana hakoranta.

Tace "Kai da wuri Haka aiki ya fara ci lailai Shugaba aikinta yayi kyau Nan da wani satin Ana Nan ana zaman makoki Naeema Kinga illlar taurin kai ko toh Allah ya jikanki.


Daga Haka ta koma wajen data ajiye tukunyar ta tsugunna a bakin kofar Naga ta Ciro wani Abu kamar Sand'a ta fara taune kasar bakin kofar.

Nidai Ido kawai na zuba Mata Ina kallonta

Tana Gama hak'a kasar ta d'auko wani Abu Mai siffar mutum mace da ciki ta zura hannu ta d'auko farin kyalle ta nanade abin dashi ta zura a Ramin ta saka kasa ta rufe tana gamawa ta juyo ta kalleni ta sakarmin murmushi ta d'auki tukunyarta tayi waje tare da rufemin kofa

Tana fita Naga na cigaba da kumburi jikina na wani irin rawa

Rufe idona nayi na tuno iyayena na tuno fuskar Naseer da rabon Dana saka shi a idona da ganin danayi Masa na karshe ta gefen idona hawaye ya ringa zubomin inajin idona namin nauyi shima sabida kumburin danayi Sallati kawai nake Ina jiran mutuwa tazo ta d'aukeni.


Naseer


A ranar shima wuni yayi da zazzabi a jikinsa gabansa na balain fad'uwa hakan da ya gani ne yasa ya nufi wajen wani Sheik Musbahu daya zama babban mallamin da Mallamai ma suna zuwa wajensa daukar karatu.

Da Magriba Naseer ya Isa Massallacin sa da mutane ke cike suna sauraran tafseer daga wajen Mallam Musbahun

Waje Naseer shima ya samu ya zauna ahaka har sukayi Sallar Ishai

Wajen takwas da rabbi aka Dan watse daga Massallacin ya rage daga Mallam Musbahu sai wasu guda biyu da Naseer.


Naseer shi dai shiru kawai yayi kamar mara lafiya aka kawo abinci daga gidan Mallam Musbahu suka had'u suka ci.

Anan Musbahu ke fad'a musu zasu iya tafiya shi a Massallaci zai kwana sabida akwai wani addua da yake so yayi.

Naseer da bayajin zuwa gidan shima da Sauri yace shima bazai je gida ba zai kwana a Massallacin haka ma sauran biyun

Ahaka suka fara adduoi da karatun Qurani Naseer kuwa ya balain dagewa ko kad'an bacci Bai zo Masa ba.

Wajen karfe biyu bacci ya dauki Mallam Musbahu da ke rike da Qurani.

A hannunsa.

Ko minti goma baiyi da fara baccin ba ya farka da sallati ya Ajiye Qurani a gefensa ya kwanta a hannun Dama bacci ya Kara daukarsa.

Kwanciyarsa da minti goma ya sake farkawa

Ya Kara juya kwanciyarsa ya sake farkawa da sallati a bakinsa.



A hankali ya Kai kallonsa Kan Naseer dake ta karatun Qurani ya zuba masa Ido Yana kallonsa tare da tuno mafarkin da yayi .


Bai ce komai ba ya mik'e ya fita waje ya daura alwala ya dawo ya tada sallah sai daya jima Yana sallahn yaja manyan adduoi.

Tare da yin istihara.

Wajen karfe ukun ya Gama ya kalli Naseer da ya Ajiye Quraninsa a gefe ya mik'e Yana Shirin tada sallah.

Gyaran murya yayi ya kirashi

Naseer kuwa ya nufi wajensa ya zauna ya tankwashe kafarsa Yana kallon Mallam Musbahu.

"Ina iyalinka take Mallam Naseer"?

Wani dum Naseer Yaji a kansa kalmar iyali na Masa wani iri a kunne.

"Iyali"?
Naseer yace shima cikin tambaya.


"Ee Ina nufin Ina matarka take"?

Wani irin dum yaji kansa ya Kara Masa ya rik'e kansa da hannu biyu kalmar matarsa na amsa kuwwa a kunnensa.

"Baka San Inda matar taka take bane"?

Naseer shiru yayi yana so yayi tunani take fuskar Naeema ta hau gilma Masa a Ido.

"Matarka na da ciki ne"?

Kalmar da Musbahu ya sake jefawa Naseer kenan.

Inda kalmar ta tarwatsa duk wani shiri da akayiwa Naseer.


Naseer ya mik'e zumbur Yana kwala Kiran sunan Naeema tare da tuna karshen ganin da yayi Mata a dakinsa tana Masa zancen cikin dake jikinta da take fatan ya kasance namiji Mai Kama dashi.

Murmushi kawai yayi Mata ya rungumeta yayi waje da Sauri sabida Latin da yayi karshen ganinsa da ita kenan sai yanzu daya dawo hayyacinsa.

Naseer hankali a tashe ya fara k'ok'arin yin waje still Yana Kiran sunan Naeema.

Mallam Musbahu kuwa ya jawo hannunsa ya zaunar dashi.


Yana "Alhamdulillah daka dawo hayyacinka dazu Allah ya nuna min a mafarki a ciki dalibai na matar wani a cikinsu ta rasu da ciki munje mun binneta da zamu dawo sai na juya na hangoka a Kan kabarin kana ta kuka sau Uku nayi mafarkin a jejjere hakane yasa nace Bari dai nayi istahara sai Allah ya nuna min matarka tana d'auke da tsohon ciki shaidanun mutane zasu kasheta Amma mutane zasu dauka da tazo haihuwa ta mutu yanzu Haka kwana bakwai ya rage su cimma burinsu Dan Haka zan baka adduar da zakayi na kwana bakwai a ranar da zaka cika kwana bakwai kana adduar a ranar ka siyi tunkiya Mai tsohon ciki da ta Isa haihuwa itama sai ka yanka ta ka binne insha Allahu a ranar matarka zata haihu lafiya batare da ko ciwon Kai ba Amma fa daga yau karka sake sake irin wanan Dan kana dab da rasa matarka kaje idan matarka ta haihu ka dawo zan baka wasu adduoi Allah ya Dora ka akan makiyanka Dana matarka.

Naseer dak'yar ya tsaya Mallam Musbahu ya nuna Masa adduoin cikin Quraninsa tsabar matsuwa da yayi yaga Naeema.


A cikin Daren kafa ba takalmi hankali a balain tashe da gudun balai

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment