Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balain fad'uwa.

Ina ta addua a Zuciyata.


Su Zahira sun Gama Shirin makaranta na Shiga d'aki Dan na gayawa Naseer sun Gama a bakin kofa muka hadu ya shirya shima

Suna shirin fita waje Naseer ya juyo Yana min fadan na ringa kiyaye kunna su heater tunda kamar wutar Mai k'arfi suke kawowa.

Bance Masa komai ba Dan bazai Gane tunanin da nake ba.

Sallama mukaji ana kwadawa da k'arfi


Kafin ma Naseer ya amsa an fado palon a hargitse Lukman ne da danladi jkinsu na ta rawa

Tuni.naji gabana ya tsinke kfin ma suyi.magana na fara Jan innalillahi wa Inna ilaihi

Lukman kuwa cikin tashin hankali ya hau magana Yana "Yallabai gidanka da shagonka duk sun Kama da wuta an Shiga sallar asuba kafin a fito daga Massallaci gidan ya Kama da wuta har shagunan babu yanda mak'ota basuyi ba Dan a kashe wlh Yallabai an kasa kashewa har yanzu gidan ci yake abinda ya daga Mana hankali wlh bai wuce yanda aka rasa sanin Mai ya haddasa gobaran"?

Dagani har Naseer sallati muke cikin tashin hankali Naseer kuwa cewa yake "gida da shaguna na uku duk sun kone kake nufi Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun".

Ni kuwa zubewa kawai nayi a kasa Ina Dora hannu a ka tare da fashewa da kuka.


Naseer kuwa sallatin kawai yake Yama kasa motsi.

Sai Lukman ne yace ya Kamata suje ya gani.

Haka kuwa akayi Naseer ya bi bayansu duk a hargitse cikin tashin hankali suna Isa unguwar aka yo kansa Ana Masa jaje kowa na labarin yanda wuta ta Kama gidan da yanda aka so kashewa Taki mutuwa the more ma aka so kashewa da the more ya Kama da wuta kamar Ana zuba petur.

Maganar Umma ne ya Fado Masa a Rai " Naseer idan dai Ni na tsugunna na Haifeka Sai ka tagayyara Naseer sai ga tashin hankali da ifitilai rayuwa"

Hawaye ne suka zubo Masa Bai ma kalli wayanda ke ta Masa magana ba ya shige motarsa ya koma gida wanda ikon Allah ne kawai ya maidashi gida sabida bama ganin gabansa yake sosai ba.

Tunda nake a rayuwata bantaba ganin Naseer a cikin irin tashin hankali Dana ganshi a ciki ba tunda suka fita nake kuka

Shigowarsa yasani mik'ewa Bai kalleni ba ya Shiga d'aki nabisa a guje

A tsakiyar d'akin ya tsaya hawaye na cigaba da zubo Masa Ni kuwa na hau tambayarsa komai na gidan da shagon ya kone dagaske.

Idonsa a rufe yace "Naeema na fara ganin tashin hankali da ifitilai rayuwa Naeema maganar Umma na neman tabbata a kaina Naeema kinsan yawan dukiyar dake shaguna ukun nan kuwa Naeema kinsan dukiyar Dana rasa kuwa ?Naeema jiya motata ta Kama da wuta yau Kuma gidana da shaguna uku shima ya Kama da wuta jiya gidanan ma Allah ne ya rufa Mana asiri sai da labulen palo ya Kama Naeema na Shiga uku Naeema a Ina zanga Umma Naeema wayasan Mai zai faru a gaba idan ban ga Umma ba nashiga uku Naeema Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha"

Kuka Naseer keyi sosai Nima Ina kukan gabadaya ma Ni tsoron gidan nake Ina ganin kamar gidan na iya kamawa da wuta

Sallamar da ake tayi ne yasa na lek'a palon Naga Tijjani ne kanin Naseer da Sauri na dawo d'akin na fadawa Naseer.

Ya kuwa fito da Sauri

Tijjani kuwa jajen abinda ya faru ya hau mishi Inda yake ce Masa baya Nan ne yau ma ya dawo daga Lagos Saro Kaya yace Bari ya lek'o sa shine yaga abinda ya faru

Dayake shima tijjanin tunda Naseer ya bashi jari Allah ya dafa Masa daga shagon provision ya sake bud'e wani Yana siyar da atamfofi da shadodi yanzu Haka ma har ya samu matar da zai aura saura sati biyu bikinsa.


Naseer hannayensa ya ruk'o Yana "Tijjani ka taimaka min ka gayamin a Ina Zan ga Umma nemanta nake Tijjani inata zuwa bana ganinta"?

Cikin mamaki Tijjani yace Masa "Umma Kuma ai Umma Naga tana garin Nan Mai ke faruwa ne kana nufin baka San Inda ta koma ba"

Damke Masa hannu Naseer yayi Yana kaini wajenta Tijjani ka taimaka min na Mata laifi na nemi yafiyarta.

Tijjani tambayoyi kawai yake Masa akan Mai ke faruwa ne Naseer kuwa hannunsa kawai yake.ja

Suka Shiga cikin motar sai Tijjani ne ya karbi tukun motar suka dau hanyar gwammaja.

A wani karamin gida Tijjani yayi parking Suka fito suka Shiga ciki

Naseer burinsa kawai yaga Umma.

A karamin Palo da Tijjani ya Shiga suka ga Umma a zaune tana jijiga kafa


Ido kawai ta zubawa Nas eer daya zub'e tun daga bakin kofa ya fara kuka........

"*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page 24*

Wani irin murmushi kawai Umma keyi tana cigaba da jijjiga kafarta


Naseer kuwa ya Shiga palon da rarrafe Yana "Umma kiyiwa girman Allah ki yafemin Umma nabi Allah nabiki ki taimaka min ki sakamin albarka a rayuwata Umma nayi nadamr k'in bin umarninki Umma Dan Allah ki yafemin"


",Waccece ummanka? Ina ka baro Naeema Ni asuwa dazan saka maka albarka Naseer Ni ai ba komai bace a wajenka ai Naeema Uwarka ce Kuma matarka Kuma rayuwarka da idan kuka rabu mutuwa zakayi Naseer ai ba abinda kayimin Banga dalilin da zai saka kazo kana neman yafiyata ba kaga Dana nan"

Tace tana nuna Tijjani Shi na sani sai su Safiyya Kai na Dade da Sallama ka na dade da barwa Naeema Kai banida wani had'i da Kai Naseer ka daina batawa kanka lokaci ka tashi ka tafi"


"Wai me ke faruwane Umma"?

Tijjani yace cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa Sam bai San abinda ke faruwa ba ya dai San Umma Bata San Naeema haka ma kannensa shi dai ba ruwansa da tsanar da suka Mata shi irin mutanen Nan ne da Bai fiye Shiga abinda Bai shafeshi ba"

"Mai ka Mata ne Yaya Naseer"?


"Ba abinda ya Shafeka Babu Kuma ruwanka idan ba kana San b'acin Raina ba uban waye yace ma ka kawo min shi gida"?

"Umma Mai yayi zafi Haka Yaya Naseer ne fa'?

Tsaki Hajara tayi ta d'auke kanta tana cigaba da jijjiga kafarta.

Naseer kuwa ya cigaba da magiya Yana "wlh Umma yanzu Zan bi umarninki a gabanki Zan rubuta takarda ki aiki Tijjani ya Kai Mata Amma Dan Allah ki yafemin ki janye kalamanki Umma na fara ganin masifa tun ba'aje koina ba Umma ki tausayamin"

Wani irin kallo Hajara tayiwa Naseer ta mik'e cikin wani irin B'acin Rai ta Isa wajen da Naseer ke zub'e akan gwiwarsa

"Sai a yanzu Dana rufe babinka na sallamaka zaka cemin zaka bi umarnina sai da ka fara ganin masifa zaka bi umarnina toh ka makara Naseer ko ka rubuta ko baka rubuta ba babu abinda ya shafeni kudin da kake dashi yasa kake Jin Kai wani ne bazaka iya bin umarnina ba ka fifita mace Naseer a kaina Sabida matarka ka daga hannu ka Mareni"


Wani irin jijjiga Kai Umma tayi cikin fushi ta cigaba da Magana tana "kaci Sa'a Kai Dana ne Ni na Haifeka Naseer da ace wani ne ya mareni da yanzu sai dai ayi labarinsa Bazan janye kalmata ba Naseer da sai da kaga alamar masifa na tunkaroka ka taho wajena wlh baka ga komai ba Naseer"


"Haba umma wane irin magana ne wanan haba Umma Naseer Bai cancanci Haka daga wajenki ba karki manta fa duk abinda kike takama dashi daga ke har mu shine fa ko gidanan da Kika siya Umma da kudinsa ne yau idan kina jifansa da irin kalaman Nan ya Shiga cikin masifa ai muma sai ya shafemu"


"Kayimin Shiru Tijjani wlh Kai ma Zan maka baki Dan ubanka kayimin Shiru idan Kai ma Marin nawa zakayi kamar yanda ya mareni zaka iya matsowa ka Mareni da kake cewa shine rufin asirinmu Dan ubanka yanzu a gidansa nake zaune ko shi yake bamu abinda muke ci yaje can ya rik'e arzikinsa ya zauna da matarsa ban rokesa ya Kara min komai ba bana bukatar komai nasa yaje can ya karata"


"Umma Dan Allah Dan Annabi kiyi hakuri ki yafemin Tijjani Dan Allah Tayani Bata hakuri wlh Zan saki Naeema yanzu indai haka zai saka ta yafemin ta janye kalamnta akaina"

Wani irin kallo Umma ta jefashi dashi taja Tsaki ta shige d'akinta.


Naseer kuwa ya cigaba da kuka Yana Tijjani ya taimakeshi Tijjani kuwa cikin b'acin Rai yace "Mai kayi Mata da Zan Bata hakuri sabida me Zan Bata hakuri Dan Allah Yaya ka tashi kayi tafiyarka Umma Haka halinta yake duk da bansan Mai asalin abinda ya faru ba Ni nasan laifinta ne Kai Kuma kuskuren da kayi da ka Mareta Amma ka tashi kayi tafiyarka insha Allahu babu abinda zai sameka karka sake ka danganta abinda ya sameka da ko bakinta ne arzikin Nan waye ya baka"?


"Allah"

Naseer yace Yana Jan majina

Toh kasa a ranka zai iya karba Dan ya jarrabceka yaga ya zakayi Dan shagonka da gidanka.ya kone bashi yake nufin Wai Dan Umma na fushi dakai Dan ko dan ta maka kalamai ne marasa dadi ko mu Nan Bata barmu ba idan muka Bata Mata Rai kamar ta Mana baki har tanayi din ma ka daina wahalar da kanka ka tashi kaje kawai"

Tijjani "naji duk Mai kace burina kawai tace ta yafemin ko Zan samu nutsuwa a Raina"


Haka Naseer yaje bakin kofa d'akin Hajara Yana ta kuka da magiya Inda b'acin Rai ma yasa Tijjani ya ficewarsa ya bar sa a wajen

Ahaka Safiyya da ta fita yawon gantali ta dawo ta tarar dashi

Tana ganin Naseer ta Shiga da Sauri Dan har ga Allah Naseer na ranta daga canjin rayuwar ma kawai da suka samu da basa komai waja waja tunda Umma ta dawo gwammaja ta siyi karamin gida yasa takeso taga Naseer ko ta San halin da yake ciki.

Ummansu Bata tab'a kudurta mugayen Abubuwa data Sha alwashin samun cikar burinta ba sai Akan Naseer har rokonta tayi akan ta yafewa Naseer ta kashe Naeema tak'i sosai ta fusata da ko maganar Naseer din Bata so ayi Mata

Ita dai tasan sun Cutu Kuma suna Kan cutuwa dan badan Tijjani shima Yana musu abubuwa ba da abinda xasu saka a bakinsu sai ya gaggaresu

Lami kuwa Tana Calabar abinta tak'i ma zuwa kanon a satin Nan ma take cewa ta samu wani zai Aureta zasu zo wajen Umma ta Kai su wajen dangin babansu Dan ba saninsu sukayi ba


Da Sauri ta Shiga palon tana Yaya lafiya naganka Haka"?


"Dan Allah ki Tayani bawa Umma hakuri nayi nadamar abinda nayi Mata Kuma wlh yanzu a shirye nake Dana bi umarninta Safiyya jiya motana ya konne yau Kuma gidana na goron dutse da shaguna ukun.ya kone kurmus kinsan kuwa yawan dukiyar danayi asararsa kuwa Safiyya ki taimaka ki bawa Umma hakuri Ina tsoron bakin umma ya kamani"


Tunda yace gidansa na goron dutse ya kone Safiyya ta zaro Ido waje tana Kara tuno girman gidan da shagunan Naseer uku dake cike da.kaya.

Sosai hankalinta ya tashi itama ta hau bubuga kofar d'akin tunda ta nunawa Umma tana tausayin Naseer Bata San wani Abu ya sameshi Umma ta fara Mata boye boye ba komai ta sani ba yanzu game da.umma Umma yanzu ta kara canjawa tundaga lokacin da suka baro gidan Naseer Amma daga abinda Naseer yace yanzu yasa ta fara zargin tabbas da saka hannun Umma a konewar gidan Naseer da motarsa

"Umma Dan Allah ki bud'e k'ofar nan haba Umma ke yanzu Sabida Wata Naeema Zaki juyawa Yaya Naseer baya yanzu bakisan Haka Naeema keso ba Dan Allah kifito ki saurari Yaya"


"Safiyya"

Naam

Saffiya

Naam

"Wlh ranki zaiyi mumunnan b'aci inkika Kara Shiga maganar Nan babu ruwanki ku kyalleni Naseer ya fice ya barmin gida Dan wlh idan Bai fita ba Zan Kara Masa wani bakin na barwa Naeema shi ya dauka karya nake ko? ya d'auka duk rantsuwar da nayi akansa zai tashi a banza ne ko? Ya tun Bai fara ma.ganin komai ba zai zo neman yafiyata ai Bai ga komai ba ba dai Naeema ya zaba a kaina ba"


"Umma kiyiwa Allah ki yafemin Umma Allah ma muna Masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe mana Umma nasan nayi kuskure Dan Allah ki yafemin"


"Tashi ka fitar min daga gida Naseer idan na fito daga d'akin Nan kalmar da Zan maka sai yafi wancan Muni"

Naseer da Sauri ya mik'e yayi waje

Safiyya cikin Sanyi jiki tabi bayansa tana bashi hakuri.

Har wani jiri Naseer keji Tijjani kuwa a halin daya ganshi yasa ya taso ya karbi mukullin motar yaja suka nufi sharada.

Tijjani sai bashi baki yake Yana rantsuwar Bazai dau abinda umma ke Masa ba shi idan ma Umma zata takura masa.wlh bar Mata garin zaiyi ya siyar da komai nasa ya koma wani garin ya daina wani damun kansa ya shareta.

Naseer Bai iya magana ba har Suka iso gidan Tijjani ya sauka ya Masa Sallama akan zai Kara lekoshi idan ya samu lokaci Dan ya kwantarwa da Naseer hankali yace Masa idan Umma ta sauko zai Bata baki.

Godiya Naseer ya Masa bayan tafiyar tijjani sai daya Dade a mota tunanin Asarar dayayi ya balain tsaya Masa a Rai.


Yama rasa tunanin da zaiyi.

Jiki ba kwari ya fito daga motar ya nufi cikin gidan.

A bakin kofar palon ya tsaya Yana kallon Naeema data zauna a 3 seater da uban akwatuna taci hijab ga su Zahira suma a Gefen ta Suma ta shiryasu


Kallonta kawai yake Yana Jin wani iri a zuciyarsa da alama Naeema bama ta San da shigowar shi ba sabida zurfin da tayi a tunani lokaci lokaci takan share hawayen da ya zubo Mata da hijabin jikinta.

Tunda Naseer Suka fita da Tijjani nake Jin fad'uwar gaba zuciyata a balain cunkushe fargabar yanda Umma zata yiwa Naseer ya cike min zuciya ni dai nasan idan Naseer Yana San yafiyar Umma sai ya sakeni Dan nasan indai ya sakeni taga shaida zata iya yafe Masa

Hakane yasa ban tsaya yaudarar kaina ko sai Naseer ya dawo naji yanda sukayi ba Dan nasan Idan dai Yana da hankali dole yabi umarnin Umma ya sakeni.

Kayanmu na hada Mana tsaf nida Yarana Dan bazan tab'a iya barin yarana da Naseer ba Dan nasan Umma ko Dan ta galazamin zata so na bar yaran sabida taci zalinsu.

Zan tsugunna na roki Naseer ya barni na tafi dasu garinmu na tashi Yan hayan da nake tunanin kila.mai unguwa ya zuba a gidanmu nayi zamana acan na fara neman kudin da Zan kula da yarana duk da nasan Naseer bazai barmu Haka ba zai bamu wani Abu Abu dayane yake San karyamin komai tausayin Naseer ko ya zaiyi idan ya waiga yaga bana Nan yaransa ma.haka Naseer.mutum.ne shi Mai balain San Yara Dan wani zubin idan abin ya motsa Masa d'akinsa yake tafiya da su su kwanta a gadonsa dayafi nawa girma

Shi Kuma ya kwanta a doguwar kujera Ni kuwa idan Naga Haka Akan Dole Zan bisu haka na shimfida bargo na kwanta a kasa yayi ta tsokanata Yana cemin matsoraciya idan na Isa na kwana Ni kadai Mana ba sai na biyo su ba

Idan Kuma Yan tsokanar na kansa idan yaran basuyi bacci ba zaice duk su tashi zaune dashi Dani wane Suka fiso


Hade Rai nakeyi Dan nasan Zahira kadai ce take cewa ni tafiso su kuwa sauran duk shi suke cewa sabida yakan yaudaresu da alewa ko yayi ta musu signa da ido akan zai siyo musu kayan Wasa sabida yarinta da gudu suke cewa shi suke so Zahira kuwa komai zai Bata sai tace ita tafi San Umma hararta zaiyi tayi idan tace.haka Wanda a karshe sai ya koreta daga Kan gadon akan tazo wajena tunda tafiso na Ni kuwa sai nayita Masa gwalo Ina harararsu Nadeeya zaman mu gwanin shaawa da bamuda matsala da Umma Naseer mutum ne shi da nake fatan ya zama miji a gareni har a Aljanna sai dai k'arfi da yaji Umma kesan rabamu.

Tunanin Nan danayi na irin Rayuwar Dana shimfida da mijina da yayana cikin so da Kaunar juna yasa kukan danake dannewa ya k'wacemin na Shigar da fuskata cikin hijabi na naci kukana na gode Allah kukan Zahira Dana fara ji kasa kasa yasa na Dago

Na share hawayena anan idona ya fada Kan Naseer daya zubamin Ido cikin jajjayen idonsa Yana min wani irin kallo da na kasa ganewa.

Mik'ewa nayi na dauki Raheema dake gefena na sab'ata a kafadata daga yanda Naga idon Naseer ya kad'a yayi ja Ni nasan ya sakeni ya kasa shigowa ne sabida Ni.

Umarni na bawa su Zahira akan su tashi mu tafi

Dan so nake idan naje waje na samo Mai mota yazo har k'ofar Gida na kwashi akwatunan kayanmu


Kukan dake San k'wacemin nake ta dannewa

Na nufi wajen da Naseer da har lokacin yakemin wani irin kallo.
Cikin muryar kuka na mik'a Masa hannu Ina ya bani takarda Zan tafi banasan nayi Rana


Murmushiin dayafi kuka ciwo yamin ya matsa daga bakin kofa cikin wani irin murya ya hau magana Yana "Zaki iya tafiya ke kadai ba sai kin tafarmin da yarana ba Naeema baki zabi ki gujeni ba sai da masifa ta tunkaroni Naeema baki nemi rabuwa Dani ba sai a yanzu danake cikin tsaka Mai wuya ?baki nemi na baki takarda ba sai a yanzu da nake neman Wanda Zan Dora kaina a kafadarsa ya rarrasheni shine a yau da Kika ga nayi asarar dukiyata a yau Zaki hada kayanki ki tafi Naeema"


Bansan lokacin da na fashe da wani irin kukan bakin cikin fassarar da Naseer yamin ba na hau magana numfashina Kamar ya d'auke

"Haba Naseer Mai yasa zaka min wanann mummunan Fassarar wlh badan Haka na had'a kayana ba Umma tace indai kana so ta yafe maka sai ka sakeni Kuma fitar da kayi Dan kaje ka nemi yafiyarta ne hakane yasa na hada kayana Naseer wlh ba dan komai haba Naseer bazan tab'a guje maka Dan ka tsinci kanka a cikin wani Hali ba"

Bai cemin komai ba da ga kallon dayake min ya nuna ko kad'an maganata Bata shigeshi ba girgiza kansa kawai yayi ya nufi d'akinsa ya shige Ni kuwa na zub'e a kasa na fashe da kuka Mai ciwo.

Sai danaga yarana suma suna ta kukan na daure na share hawayena na koma Kan kujera na zauna.

Abincin Rana ma banyi ba Sabida tashin hankali Cabin biscuit kawai na rabawa yaran Haka nayita Zama a palon Ina tunanin Naseer zai fito ya tafi massallaci yyi sallah Magriba Amma shiru Bai fito ba.


Nadeeya da Bata da juriyar yunwa ita ta fara min kukan yunwa hakane yasa na tashi na Shiga kitchen na dafa musu shinkafa tunda Ina da Miya na sati nakeyi.

Gabadaya na rasa Mai kemin dadi ga wani irin tsoron gidan da nakeyi sai Naga kamar gidan zai iya kamawa da wuta na rasa Mai ke sakamin wanan tunanin

Har karfe goma na dare Naseer Bai fito ba na buga Masa ko gezau baiyi ba har kuka na Masa Ina Masa rantsuwar ba Dan ya Shiga wani Hali zan tafi ba Amma duk da Haka Bai bud'e k'ofar ba.


Da farko na dauka ko wani abune ya same shi sai danaji muryarsa Yana karatun Qurani hankalina ya kwanta nayiwa yarana shimfida a d'akina naje na kwantar dasu.

Na buga tagumi Ina tunanin halin da muka tsinci kanmu a ciki dayake fashin sallah nake hakane yasa banyi sallah ba surorin Dana haddace a kaina kawai na ringa karantawa ko zanji sanyi a Raina.

Bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba.

A cikin baccina na fara mafarkin Wai shagunan Naseer na Sabon gari Wai Yana ta konewa Ana rik'e Naseer Wai zai Shiga ciki shagon daya ragewa Naseer kenan Umma Wai ita Kuma tana daga nesa tana ta Mana dariya tana kad'an muka gani bamu ga komai ba"



A firgice na tashi da sallati jikina na balain rawa duk na hada zufa sai waige waige nake ganin ba wuta dake ci a d'akin yasa na fita da Sauri na duba Palo da kitchen Naga ba komai har store da d'akinsu Zahira.


Muryar Naseer dake ta karatun Qurani dayake dare yayi muryarsa sosai yake fita daga muryarsa kawai zaka San Yana cikin damuwa.

Bakin kofar naje.na tsaya nayita Kiran sunansa Amma babu alamar zai saurareni a Haka na hakura na koma d'akina Ina tunanin mafarkin da.nayi hankalina na Kara tashi bansan lokacin Dana daga hannu na fara rokon Allah Ina "Ya Allah ka Mana maganin masifar daya tunkaromu ya Allah ka dubemu da idon rahama ka tsayar Mana da Wanan masifa ya Allah Kaine masanin Sirrin sake bayyane da b'oye bamu San komai ba ya Allah mun yarda Kaine Mai bayarwa Mai Kuma karba a duk lokacin daya so ya rabbi ka bamu ikon cinye wanann jarrabawa ka bawa mijina ikon cinye wanan jarrabawa ka Kare Mana shagunan da suke rage mana ya hayyu ya qayyum"

Bansan Mai yake sani tsoro da fargaba ba Ina tsoron wani Abu ya Samu shaguna ukun daya ragewa Naseer.

Ina Nan zaune bacci ya Kara kwasheni cike da.mafarkai marasa.dadi.

Bani na farka na sai da gari ya waye.

Kukan Raheema ne ma ya tasheni.

Zumbur na mike nayi waje Dan na makara k'ofar Naseer danagani a bud'e ne yasa na shiga ciki Amma baya ciki alamar ya fita banji dadin yanda Naseer yamin ba ya kamata ace yafi kowa sanin abinda zanyi da Wanda bazanyi ba.

Ahaka na Shiga kitchen na samawa yarana abinda zasu ci da abinda zasu tafi dashi.

Zahira kuwa har ta Tayani shirya Minal da Humaira Nadeeya itama ta iya shirya kanta.

Ganin babu Mai Kai su makarantar yasa na saka hijabina na dauki naira Ashirin na rufe gidan na tare Mana taxi ya Kai mu har makarantar sai Dana ga shigarsu makarantar na Kara hawa taxi na dawo.
Na sauke Raheema Dana goyata na fara aikina gyara gidan zuciyata kuwa na wajen Naseer.

Naseer kuwa daga Massallaci sabon gari ya nufa jikinsa duk a mace jiya kwana yayi Yana addua Akan Allah ya Kare Masa shaguna ukun da suka rage Masa zuciyarsa kuwa sosai tayi nauyi sabida halin daya ke ciki Haka kawai yake Jin Naeema so take ta rabu dashi Sabida ifitilai data fada Masa alhalin duk ma halin da ya tsinci kansa a ciki Sabida kin sakinta da yayi ne badan Allah ya bashi dangana ba da zuciyarsa na iya bugawa ya rasa yanda zaiyi Umma ta sauko ta yafe mishi.


Sabida Kar ma wani tsautsayi ya gifta duk sauke layin NEPA yayi daga shagunansa ya Kuma gayawa yaran shagonsa su ringa kula da shagon nasa sosai.

Yau ma Bai hau motar tasa ba taxi ya hau Haka.kawai.ma.yake tsoron Hawa motar tasa.


Wajen karfe daya na Shiga kitchen Dan na Dora Mana abincin Rana Dan karfe biyu yarana ke dawowa daga makaranta .

Da yake na gama komai Zama nayi a palon Raheema na d'aga gefena tana bacci Nima sai na Dan kishigida bansan lokacin da bacci Mai nauyi ya d'aukeni ba.

A cikin baccin nawa na fara mafarkin kitchen Dina ya Kama da wuta har ya fara cin ceiling din Palo.

Sai ihu nake inaso na tashi na dau Raheema mu gudu Amma na kasa.

A Haka Wai Naga Mahaifiyata ta shigo palon ta tsaya a bakin kofa Tana "Tashi Naeema so ake wuta ta Kama gidan kina ciki ki tashi nace ki tashi Naeema"


A firgice na tashi idona cike da bacci wutan dake ci a kitchen Dina ne yasa na wartsake na rarumi raheema Ina ihu tare da yin waje da gudu Ina ihun neman taimako.

Cikin Ikon Allah akwai Samarin dake gini a Gefen gidanmu da Sauri suka Shiga gidana da bokitan ruwa suka Yi ta watsawa ni kuwa sai ihu nake jikina na rawa.

Suna watsa ruwan dayake suna da yawa cikin Ikon Allah wutar ta mutu duk da sun kashe wutan kasa Shiga nayi gidan nayita tsoro sai a gidan mak'ota na zauna har yarana Suka taso suka sameni a gaskiya ya zama Dole mu bar gidanan sau.uku kenan gidanan na neman yin gobara.


Ahaka muka zauna har sai da Naseer ya dawo.

Tun Kan ma ya Shiga cikin gidan aka hau Masa jaje Mai gidan mak'otan da muka shiga ne yacemin Naseer ya dawo.

Da saurina muka fito daga gidan muka Shiga gidan mu Inda na tada Naseer a tsaye a tsakiyar palon Yana kallon yanda kitchen din yayi bakikirin har k'ofar kitchen din sabida konewar da yayi Ni kuwa cikin kuka na fara magana

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment