Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kasa Gane wacece mahaifiyarsa ba gani nake duk abinda zaayi babu abinda zai saka tayi laushi Haka a Karan kanta sai dai idan Allah yaso ta da rahama ya ganar da ita gaskiya.



Daga yanda Naga Naseer na rawar jiki nasan shima ba'a barshi Haka ba.
Sosai nayi k'ok'arin b'oye tashin hankalina na Dan saki fuskata cikin yak'e Ina Kara bawa Umma hakuri wanda naga Naseer ya ji dadin hakan sosai


Mik'ewa nayi Sabida cikina danaji Yana juyamin Dan idan na tsorata Haka ko na shiga tashin hankali sai na shiga bandaki.

Kafin na Kai ga shiga dakin naji muryar Naseer Yana in gyarawa su Umma d'aki suzo su huta.


Sai Dana fito daga band'akin na fito na nufi d'akin dayace na gyara musu Dan dakuna biyune bama amfani dashi shima babu abinda babu a ciki.

Kafin na shiga d'akin inajin tana Masa tambayoyin Inda ya samu kudi Haka shi kuwa cikin rawar jiki ya hau Bata labarin yanda ya samu da kudaden dake shigo Masa.

Sai Dana gyara na fito na nufi dakina Dan nayi Sallahr Magriba.

Ban Kara fitowa ba sai da nayi sallar isha shima sai Dana d'auki Qurani na Mai izu goma na karanta surorin Dana iya kafin na fito wajen Taran dare.


Ban ga kowa a palon ba sai su Zahira da bacci ya d'auke su a tsakiyar palon.

Daukarsu nayi na kai su dakina Dan Dama a d'akina suke kwana idan Naseer na gari Kuma sai na kwana a d'akinsa.

Sai Dana kwanatar dasu na tofe su da Addu'oi na kunna wani karamin radio mai daukar cassette daya Dan biyu ne damu ko uku ma akwai Mai d'aukar cassete biyu akwai Mai d'aukar daya (Kila ku gane radio danake magana ba plate ba cassete Mai zare a ciki)



Taro shi nayi sai daya faro daga Suratul Baqarah na ajiye musu
A gefen gadon.


Na fito daga d'akin na nufi kitchen Dan na d'ebo abinci Ina Jin muryar Naseer a d'akin Dana gyarawa Umma suna ta Hira.

Abincina na zubo inata mamakin yaushe Kuma Naseer ya fara sakewa da Umma suyi Hira Haka ko duk cikin Salon da Umma tazo dashi ne Haka na zubo abincin ba nama Dan duk Naman Naseer ya kaiwa su Umma Kuma a palon ma Banga farantin ba Nan kuwa su Umma Ashe da farantan Suka shiga d'aki.

Dayake Haka ma ake jibge Mana lemo a store Kuma bama rabuwa dasu a fridge lokacin lemon kwalba ne coke Haka Pepsi na d'auko daya Mai sanyi

Na koma d'akina sai Danaci na koshi na Kara fitowa wajen goma na dare har lokacin Naseer na d'akin Umma ta rik'e shi da labarai babu yanda zaiyi Nan kuwa ya gaji Kuma Yana Jin yunwa Amma bayaso ya tashi Umma taji ba dadi.

Ni kuwa kwanciyata nayi Ina jiran daya da rabi yyi na dare na tashi Dan yanzu Banga ta bacci ba sai na dage da Addu'a Ina Kuma fatan Naseer ya lek'o dakina na Dan Masa maganar dagewa da Addu'a.

Gani nake irin azabar da Umma ta gana min lokacin cikin Minal Haka zata ganamin da Wanan cikin tunanin Haka kawai da nayi sai daya Saukar min da fargaba Wanda tuni bacci yayi nashi gurin na tashi na daura alwala na hau kan Sallaya.


Naseer kuwa Bai samu barin d'akin Umma ba sai Sha biyu Dan ahaka sai daya ce Mata Sallah zaiyi .


Ita dai ba Haka taso ba sosai take so ta jawo Naseer jiki yanda zai na shagala sosai da ibada

Ba karamin kokari tayi wajen Kai zuciyarta nesa ba Dan ta lura sai ta biyo wa Naseer da Naeema ta bayan gida zata ci Galaba a kansu Kamar ta Kama da wuta data ga Naeema tayi wani irin kib'a ta samu kwanciyar hankali Karin bakin cikinta tana zuwa ta Gane Naeema na dauke da ciki Mai Naeema take nufi da ita ne wato bazata rabu da Naseer ba sai dai tayi ta haife haife ta haifi cikin jikinta tagani.



Sosai taji bakin cikin daular data ga Naeema a ciki hakane yasa ta ringa Dan bugar cikin Naseer game da dukiyarsa aikuwa ta samu yanda takeso Dan Naseer ya Gaya Mata komaii game da dukiyarsa a duk hirar da sukayi Bata ji ya mallakawa Naeeema wani ba Amma duk dahaka kaji da namomin da take ci ma ai Jin dadi ne

Ina zaune akan Sallaya Naseer ya shigo d'akina hannunsa d'auke da abinci da lemo.



A kasa ya zauna ya fara cin abincin Yana "Ai na dauka kinyi bacci"

Girgiza Masa Kai nayi Ina "Baka shigo ba tayaya zanyi bacci"


"Ai Umma ce take ta Jana da Hira tundazu dak'yar na fito"


"Kayi Sallah kuwa"?


Zaro Ido yayi Yana "Subhanallahi wlh Banyi Sallah ba Naeema banyi Magriba da Isha ba innalillahi yau Mai ya sameni Haka"?

Yace ya mik'e da Sauri ya shiga band'akin d'akina ya d'aura alwala ya shimfida Daduma ya tadda Sallah.

Lailai Umma ba k'aramin Kama Naseer tayi ba sosai naji jikina ya Kara sanyi Dan Naseer mutum ne shi jajirtace Mai ibada Zan iya cewa Yana bacci Yana mafarkin Sallah Amma sai gashi Wai shine ya shagala Haka Bai Yi Magriba da Isha ba.

A haka na cigaba da Jan Hasbunallahu wa neemal wakil Yana iddarwa Naga ya fara Hamma idonsa ya kankance Sabida bacci daya cika Masa ido.

Ganin Yana k'ok'arin mik'ewa yasa na saka hannu na dafe cinyarsa ya koma ya zauna Ni kuwa cikin murmushi nace "Wai har kayi me"?

"Nayi Sallah Mana wlh yau bacci ne a idona Naeema bazan iya adduoi Mai tsayi ba"

Rik'e Masa hannu nayi cikin Dan fargaba yanda zai dau maganata nace "A gaskiya Naseer Bai Kamata ka shagala da.hira har Sallah Magriba da Isha ya kwace Maka ba Haba Naseer yaushe Kuma Abu ya fara Sha maka Kai da zaka na mantawa bakayi Sallah ba ka manta Shawarwarin Da Mallam Musbahu ya bamu ka manta da addu'ar da yace mu dage dashi Sabida mu samu kariya daga wajen Allah ko ba Dan kariya ba ko iya Niimar da Allah ya maka kake Samun bud'i ko ta ina ya Kamata ka Kara kusantarsa ka cigaba da gode Masa Kar bud'in daya maka yasa Kuma ka manta dashi.


Daga yanda Naga ya nutsu Ya bani hankalinsa sosai yasa nasan maganata ta shige shi

A Haka na cigaba da shigar Masa maganata cikin siga wajen dage Mana da Addu'a na Kara da "kasan kafini zurfin Ilimi Dan Allah ka dage Mana da Addu'a Kar mu koma gidan Jiya Naseer ka mantani da sai Dana kusa mutuwa ka dawo hayyacinka yanzu Haka Ina d'auke da k'aramin ciki na wata uku bansani ba sai a satin Nan ranar da nake Shirin Sanar maka a ranar kayi tafiya kaga kuwa Ina bukatar addua Akan Allah ya saukeni lafiya"

Hannuna ya ruk'o da k'arfi cikin farinciki Yana "Dan Allah dagaske kike cikine dake"?

Gyad'a Masa Kai nayi ya daga hannu Yana "Alhamdulillah naji dadi Alhamdulillah Naeema banida burin daya wuce yanzu ki Samu ciki ki haifomin namiji Ina yawan mafarki naje Massallaci da Dana Yana kiran Sallah Allah yasa Rabon da namiji ne a jikinki Na gode da tunatar Dani da kikayi da Shagalar da nayi insha Allahu Zan gyara Dan Allah kiyi hakuri ki Kai zuciyarki nesa akan Umma kinsan wani zubin Tana iya rikicewa duk da Ina kyautata zaton insha Allahu ta Gane gaskiya kamar yanda ta fada Dan da naje bakiga kukan da ta ringayi tana neman yafiyar mu ba Akan tayi nadamar Abubuwan da ta miki"


Murmushi kawai nayi ban Kara ce komai ba Dan Naseer bazai Gane ba kila sai Umma ta Kara gwada halinta da zai balain bashi mamaki zai San wacece ita.

Sosai Naga Naseer na farincikin da cikin Dana samu Inda ya balain kwallafa Rai da insha Allahu namiji ne ahaka ya Kara mik'ewa ya kawo nafiloli ya karanta Qurani Inda lokacin Ni Kuma naji bacci na neman daukata hakane yasa na mik'e da hijabin jikina na d'auki plate din da Naseer ya shigo dashi Dan in mayar kitchen Ina bud'e kofa Naga na buge Umma dake bakin kofa ta sunkuya Haka ta Kara kunnenta a jikin k'ofar da alama dai lebb'e take Mana

Cikin borin kunya ta ja da baya tana "dama k'afata ce ta matsamin nace bari nazo ko zan samu magani a wajenku"

"Wlh babu maganin ciwon kafa sai dai paracetamol"

Nace Mata jikina na Dan rawa Dan indai Zan tsaya kusa da Umma sai naji Kamar zata zaro wanan kaifafen wuk'ar ta cakamin


Wani irin kallo tamin ta juya tana toh shikenan

Dawowa nayi d'akin Dan Haka kawai naji tsoron ma zuwa kitchen din na ajiye plate din na kwanta Ina mamakin Halin Umma yanzu har ta Kai Umma lab'e take Mana da Naseer da yanzu kwanciyar Aure mukayi da Haka zata na Mana lab'e ko Kuma ta lek'o mu kenan.


Zan iya cewa tunda muka dawo kano sai da Umma tazo gidan na kasa bacci cikin nutsuwa sai wasu irin mafarkai nake.

Akan Sallaya bacci ya d'auki Naseer Ni kuwa sai Kiran Sallah ne ya tasheni.

Inda na tashi Naseer ni Kuma na nufi band'aki na dauro alwala

Ina fitowa Naseer shima ya fada band'akin.


Ya d'aura alwala ya nufi Massallaci Nima na tada nawa sallar a gida
[6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 13*


Ina iddarwa na nufi kitchen na Dora Mana abin karyawa Ina cikin soya Dankalin Inata Sauri sabida na Gama na shirya su Zahira Nima na shirya na tafi.

Kamar ance na waiga Naga Umma ta hard'e hannayenta a kirjinta ta Sha jajjayen Kaya har kasa da wani irin Hula idon nan nata ya Sha kwalli.

Kau da kaina nayi da Sauri cikin Dan fad'uwar gaba Naja A'uziya na nace Mata Umma Ina kwana

Bata amsa min ba sai gani nayi tana shigowa kitchen din matar data so kasheni kota halin Kaka tuni jikina ya dau mugun rawa na kashe gas din na juyo Ina kallonta.


Wani irin kallo ta Gama min tunda ga sama har kasa a karshe ta zubawa cikina Ido kamar ta cinye Ni Ni kuwa nayita adduoi neman tsari a Raina

Da kyar ta dauke idonta daga cikina ta fara wuwurga idonta cikin kitchen din tana dage dage store din dake jibge da kayan abinci ta zubawa Ido Ni kuwa har lokacin rasa nutsuwa ta nayi Ina ta addua a Raina.

A bakin store din ta tsaya ta juyo ta kalleni tana "Lailai Dole ki k'i Tafiya Naeema Dole ki k'i rabuwa da Naseer wanan daula da Jin dadi haka ko nice ke bazan rabu dashi ba Amma fa inaso ki saka a ranki Bana kaunarki ba wacce na tsana sama dake yak'i ne tsakanina dake Dole zaa samu Wanda zai ci mu zuba mugani Naeema"

Tuni hawaye ya hau wanke min fuska Sabida irin kalmomin dake fitowa daga bakinta banma ankara ba sai ganinta nayi a gefena tayi saurin d'aukar cokali tana juya Dankalin Ashe Naseer ta hango ya dawo daga Massallaci ya nufo kitchen din.

Ni Kuma tsalle na daka na koma gefe Dan na d'auka ko man zata watsamin

Shigowar Naseer yasa nagane wayon da tayi.


Naseer kuwa ganin Umma a kitchen tana Taya Naeema girki ba karamin faranta masa yayi ba hakane yasa yana shiga ya tsugunna har kasa ya hau gaisheta.

Ita kuwa Hajara ta washe baki tana amsawa tare da cigaba da juya Dankalin da Naeema ta Dade da kashe wuta Wanda duk Naseer Bai lura ba


"Umma ai da kin Yi zamanki ba sai kin fito tayata ba zata iya ita kadai ai"

Murmushi Hajara tayi tana Ai Naga ta fito sassafe ne shiyasa nace Bari Nazo na tayata.

"Aaa ki barshi Dan Allah Umma ki barta tayi ita kadai idan ma tayin ne.ai gwara Safiyya ta fito ta tayata.

Naseer yace yana washe baki shi a lailai Umma Tayani take idonsa ya rufe da Bai hango hawayen danake zubarwa ba.

Toh shikenan Umma tace ta ajiye cokalin ta fita waje tana jifana da mugun murmushi.

Naseer kuwa sai murna yake Umma ta canza

Tsabar haushi ban kula shi ba na juya na kunna gas na cigaba da soya Dankalin

Ina gamawa na hada na Umma da Safiyya na Kai musu d'aki.

Ko kallona basuyi ba na had'awa su Zahira nasu muka karya gabadaya Nima na shirya cikin uniform Dina Dan sai an sauke su Zahira ake wucewa Dani a yanzu da Naseer yake Nan nasan shi zai kaimu.


Sai Dana kulle d'akina na fito hannuna cikin nasu Zahira muka shiga d'akin su Umma a zaune suke suna ta auna Dankali bakinsu suna had'awa da naman jiya da Naseer ya juye musu sakin baki sukayi suna kallon nida su Zahira Ina shirin ce Mata Zanje makarnata Naseer ya shigo d'akin shima cikin Shirin.kaimu da mukullin mota a hannunsa


Naseer ne ya fanshe Ni da "Umma Bari na mik'a su Makaranta na dawo"

"Makaranta Kuma har da Naeema"?

"Eee Umma har da ita muna dawowa na samo mata islamiyya da Boko take Dan zuwa sabida Karatun Yana da amfani a gareta ko Dan yaran Nan idan an basu gwaji ko karatu zata iya duba musu har ta koya musu"


Sosai Naga b'acin Rai a fuskar Umma Amma sabida makirci ta hadiye tana "Naseer Anya Naeema Bata girma da karatu ba Ya Kuma zatayi da kula da yaran har Kai Ni sai nake ganin kamar karatun zai saka ta kasa samun lokacinka har dana su zahiran"

"Ai Kuma tana dawowa da wuri Umma Kuma su Zahira ma sai wajen Shidda ake tashinsu.

A lokacin kuwa har ta dawo ta Dora Mana abinci

"Toh naji idan yaranka suna dawowa shidda mu Kuma fa Mai zamuci kafin ta dawo"

Murmushi Naseer yayi Yana "Haba Umma ga Safiyya Nan ai zata iya sama muku abinda zakuci kafin Naeema ta dawo ai gidan ba bakonta bane akwai komai da ake bukata yanzu ma zaa kawo kaji da nama sai ta silala ta soya Mana"

Hajara yak'e kawai take ba Kuma tasan Naseer ya gano ta da wuri badan ranta naso ba ta barmu muka tafi.

Naseer kuwa yaje ya saukemu a makaranta.

Sosai nake takatsantsan da su Umma da nake musu kallon dodo zuwa yanzu na balain iya takuna Dan idan na fita makaranta sai na ci abinci a gidan mmn Mannir nida yayana muke dawowa gidan Sam ban yarda dasu ba Dan tunda Naseer yace Safiyya ta ringa musu girki ta tsiri dafa na duk gidan gabadaya a haukanta ita da Umma da Naseer kawai take dafawa sai ta bar Mana kanzo nida Yara

Ni kuwa idan na dawo sai na juye kanzo na shiga d'aki dashi na juye Leda nasa a karkashin gado.

Abincin Naseer ma fakar Ido nake na juye na zuba irin abinda suka girka a ciki Dan Ina tsoron a Kara juyar Masa da hankali.

Ko shi Naseer Bai San na dauki kayan abinci a shagonsa ba na Kai gidan mmn Mannir duk wani Abu da nake bukata dauka nake a shagon har nama da kifin.


Mmn Mannir kuwa ba tambayar da batamin ba Akan meyesa nake zuwa dafa abinci a gidanta nace Mata ba komai idan lokacin tasan dalilin dafa abinci a gidanta idan yayi Zan Gaya Mata Kuma cikin ikon Allah Mmn Mannir da mijinta basuda matsala ba Kuma su nuna min komai ba Dan ban Dora musu nauyin komai ba har risho da kalanzir jarka guda na ajiye a gidan sabon tukunya da komai nawa ba abinda nake tab'a musu.

Karfe uku ake tasomu daga makaranta idan mun dawo a gidan mmn Mannir nake Gama komai nawa idan naci na koshi yayana ma aka d'auko minsu sai na basu suci na zuba sauran a Leda na jefa a jakata idan na faki idonsu sai na juye a Kular Naseer.

D'akina kuwa kullum kullewa nake Kuma Haka nake kunna karatu a d'akin har na dawo sai dai idan an d'auke wuta.

Har su Umma sukayi wata uku a gidan Ina mamaki da Banga ta aiwatar da komai ba Kuma ganin hakan Bai saka na saki jiki ba addua nake haikan idan Naga Naseer na neman yayi bacci cikin siga Zan Masa magana akan ya Kara min karatu ahaka muke rayya daren shima Naseer ba laifi tunda na Masa magana ban Kara ganin yayi sakaci da Addu'a ba Kuma ikon Allah tunda su Umma suka zo garin bai Kara tafiya zuwa wani wajen ba.


Sosai nake mamakin idon da Umma ta zubamin duk da wani zubin takan manta ta zageni ta tsinemin ta Sha mugayen alwashin akan sai ta Kau Dani nidai rabbi samawati na dogara dashi Kuma shi nake neman kariya wajensa.

Ban taba kwanciya banyi tunanin Umma na iya kawo min Hari ba a Haka har cikina ya shiga wata na shidda.

Ba zama nake a gida ba ballantana nasan ko akwai wani mugun Abu da su Umma suke hada Mana ahaka watarana
Mun shirya zamuje makaranta Naseer ya cewa Umma zaiyi tafiya sai an kwana biyu zai dawo.

Sosai Naga wani irin farinciki ya bayyana fuskar Umma ita da Safiyya har a idona Naga sun Yi magana da juna ta Ido.

Sosai ta Masa addua dawowa lafiya.

Shi kuwa yayi waje muka bishi a baya hankalina balain tashe Dan Ni nasan akwai wani Abu da Umma ke kullamin Amma bansan menene ba Anya kuwa Zan kwana gidanan idan Naseer baya Nan?

Ahaka Naseer ya saukeni yamin Sallama Yana ta Sauri kamar na Hana shi tafiya Amma Haka na barshi ya tafi.

Ahaka aka tashi bangane komai ba mmn Mannir sai tambaya ta take Mai yake damuna na kasa Gaya Mata cike nake da fargaba.

Muna isowa gidan mmn Mannir na hango wasu irin Kati biyu suna ta kallon gidan mu ban dai kawo komai ba muka shiga gidan a ranar ma ko yunwa banji ba inata so na yiwa mmn Mannir magana Ina ganin Kamar Bai dace na fallasa sirrina ba Abun mamaki a ranar Nan da Nan naga lokaci yaja har su Zahira sun taso.


Sai da suka dawo da. Wajen awa daya kafin na iya mik'ewa na yiwa mmn Mannir Sallama Dan Naga mijinta na Nan Kamar Kuma Yana so su kebb'e da ba Haka ba da mun kwana.

Cikin fargaba da Addu'oi na karasa gidan yanda nake Jin jikina nasan akwai Abunda zai faru Dani Amma me na dogara da Allah shi zai kareni insha Allahu ( duk Wanda ya dogara ga Allah Allah zai isar Masa insha Allahu)



Muna Sallama Naga Umma ta taremu da faraa ita da Safiyya sunci kwalliya suna ta murmushi anan nasan Ina cikin danger irin wanan tarbar Umma tamin na hau kumbura da na kusa mutuwa.

Tashin hankali ne ya saukarmun da zazzabi tamkar wancan lokacin

A madadin na kwanta alwala na daura na hau kan darduma nayi sallah Ina iddarwa na hau yiwa Allah kirari Ina hawaye Ina rokonsa kariyarsa a gareni.


Ban iya motsawa daga Kan sallaya ba ballantana in kwantar dasu Zahira da sukayi bacci

Ina ta juyo hirar Umma da Safiyya suna ta shewa a Palo sai yaga kaza suke.

Wajen karfe goma Sha biyu naji Ana kwankwasa kofar gida gabana ya yanke yayi wani irin fad'uwa na mike da Sauri na lek'a ta k'ofar dakina Naga Naseer ne ya shigo da suka bud'e kofa.

Wani irin Sanyi ne ya tsirgamin zuciyata bansan lokacin Dana koma Kan sallaya nayi Sujadda Ina Godewa Allah daya dawomin da Naseer ba.

Umma kuwa da Safiyya sosai hankalinsu ya tashi da dawowar Naseer suka hau tambayarsa Mai ya dawo dashi yace musu Dama Kaya zai Kai Yobe toh kayan ma basu samu ba shiyasa ya fasa tafiyar.

Matsuwar da yayi daya ganmu yasa ya kasa Gane tashin hankali da suke ciki.


Ahaka ya wuce su ya nufo d'akina.

Yana shigowa na mike da Sauri naje na rungume shi Dan sosai naji duk wani fargaba da tsoron danake ciki ya tafi.

Murmushi yayi min ya janye Ni gefe Yana na bar Masa Yaya a kasa ya d'auke su Zahira ya kwantar dasu ya nufi bandaki ya watsa ruwa ya dawo Yana ya gaji nazo na Masa tausa.

Da hijabina na hau gadon na hau daddana Masa kafarsa bansan lokacin da bacci ya d'auke shi ba.

Nima Haka kawai naji baccin nake San Yi sai na kwanta a gefensa cikin kwanciyar hankali Yana gefena.

Karfe biyun dare Naga an banko k'ofar dakinmu da k'arfi daga Ni har Naseer muka Mike a firgice da sallati.
Kattin Maza ne akalla zasuyi su bakwai uku d'auke da bindiga kanananu sauran hudun Kuma d'auke da wukake dogaye masu kaifi.

Daga Ni har Naseer sallati muka hau Yi Ni kuwa naji cikina ya wani irin murd'amin take naji wani irin gudawa kamar Zan saki sallati kawai nake Ina kankame da Naseer.

Fusgoni sukayi daga jikin Naseer Suka ja hannuna suka wurgani palo Naseer na San magana suka buga Masa gindin bindiga.

A tsakiyar palon aka jeramu har da Umma da Safiyya da suka kwanta a kasa suna ta magiya suna bada hakuri tunda nake bantaba ganin bindiga da idona ba sai ranar.


Daga Ni har Naseer sallati kawai muke Ina Jin kamar Dan cikina zai fito.


A hankali na daga kaina su bakwai ne Fuskarsu duk a rufe

Naseer kuwa sai ce musu yake akwai kudi a daki suyi hakuri ya dauko musu.

Ni kawai suke kallo suna magana kasa kasa .

Inda naji daya daga cikinsu Yana cewa "Ai ba sai munyi amfani da ita ba cikine fa a jikinta muyi abinda ya kawo mu kawai mu ware.

Ana fadar Haka Naga uku sun zo kaina sun dagani wani Kuma daga cikinsu ya saitoni da bindiga.
Aguje Naseer yaje ya zub'e Agaban Wanda ya nuna Ni da bindiga yana ya Masa Rai Kar ya kasheni zai basu duk abinda suke so idan ma shine su kashe shi Dan Allah.


Wani irin Ball sukayi da Naseer ni kuwa tuni na fara juyo kamshin lahira na kalli ringa karanta la illaha illa anta subhanaka inni kuntum Minal zalimin innalillahi wa Inna ilaihi rajiun abinda nayita fada.kenan.kafin nace Naseer Dan Allah ka kularmin da Zahira da Nadeeya Umma na yafe Miki duk abinda Kika min dafatan zakimin addua idan na mutu.

Ina Gama fadar kalmar nan Naga Wanda ya saitoni da bindiga bindigar ta silmiye daga hannunsa ya cire abinda ya rufe fuskarsa ya kalleni Yana kikace kin yafe Mata abinda ta Miki"

Ban kulashi ba na cigaba da sallati shi kuwa ya maida kallonsa Kan Umma data sunkuyar da Kai tana Jin asiirinta na neman tonuwa

"Ke tsohuwa Mai yarinya Nan ta tare Miki da.kike San kasheta.

Wanda ya saitani da bindiga yace Yana zuwa Kan Umma ya tsaya.

Umma mik'ewa tayi tana fiki Fiki da Ido tace kamar ya bangane ba wa zan kashe.

Wani irin Mari ya d'auke Umma dashi da har sai da Gefen bakin umma ya fashe

Yace "Ni zakiyiwa bariki Zaki gayamin ko sai na b'allaki Mai matar danki ta Miki da kikesan kasheta sabida rashin Imani Kika biyamu mu Mata fyade mu kasheta Mai ta Miki Haka Yar yarinya Nan dake d'auke da ciki.

Umma da Naseer. Ke jifanta da wani irin kallon mamaki cikin borin kunya da rashin kunya tace Kai yaro ka shiga hankalinka idan ma shaye shaye kayi ka dawo hankalinka a Ina na Sanka da zakamin sharri Dan ubanka wlh Zan saka Dana ya kamaku bakada hankaline

Bata Gama magana ba ya Kara d'auke ta da Mari

Yasa yaransa suka rik'e masa Umma ya hau naushin Umma Yana ball da ita......[6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 14*


Bugun Umma yake sosai kamar ya samu kato Dan uwanshi Dan Raina masa hankali da tayi duk yafi Bata Masa Rai kisan Kai aikinsa ne rashin Imanin aikinsa ne kawai Maganar da Naeema tayi akan ta yafe Mata ta Mata addua ne ya tab'a shi Bai kawo Yana Ido biyu da Naeema bazai d'auke ta da bindiga ba Dan Dubu goma su Umma suka biyashi da a lokacin kudine Mai balain yawa tunda Suka ga Naeema Bata Zama Safiyya ta bazama Nemo Inda zasu samu Yan d'abba da zasu zo gidan su kashe musu Naeema cikin sauki Dan sunga alamar duk Inda suka kai

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment