Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar Nan Albarka k'arfi da yaji ta hanaki zaman lafiya da miji ta Kuma rabaki da yaranki Allah ubangiji ya saka miki"


Kuka nake sosai har ta mik'e ta fita bud'e kofa da ake kwankwasawa sai Gata ta shigo ita da aunty da Niki Niki kayana Isihu shima da wasu kayan jikinsa a sanyaye shima Kamar zaiyi kukan

Aunty palon ta shigo ta zauna tana "Ya Naga kuma kina kuka kinsan Allah Kika biyewa tausayin yaran bazaki iya tafiya ba gwara ki tafi tsinaniyar ta Gane ke kike rik'e da gidan ko ba ke bace kina da amfani a gidan ko bakida shi.


Yanzu Nan na biya na karbi kudin engine nacewa wacce ta siya anjima ta je ta dauki injina Naga ta tsiya ba dai kin bar Wa Naseer kudi ba"


Gyad'a Mata Kai kawai na iya Yi

Ita kuwa ta cigaba da bambami "Maza share hawayenki ki tashi muje Tasha Dan inaso na dawo a yau d'inan karbi kudin injin"

Tace tana mik'o min kudin hannunta

Kasa karbar kudin nayi inajin kamar bazan iya tafiya ba nadamar ma siyar da engine din markade na nake yanzu dame su Naseer zasu ringa samun na abinci Ni sai na ringa nadamar ma daukar shawarar ta duk da nasan duk tayi hakane Wai Dan Umma ta Sha wahala Amma Ni Naseer da yarana nake tausayi.

Tana k'ok'arin Magana mmn Abdul ta fara magana tana "Aunty sai nake ganin kamar tafiya ta bar yaran Nan bashine mafita ba ki dai sake tunani duk tsawon lokacin Nan wuyan data Sha sabida yaran Nan ne Bata gudu tun lokacin ba sai yanzu Kuma Naseer ya Mata hallaci da Bai cancanci Haka daga wajenta ba taurin Kai daya gwada.yaki bin umarnin Mahaifiyarsa ya jefa shi a halin da yake ciki Amma kwatsam yanzu yaga ta gudu ta barshi da Yara wlh zaiji ba dadi a ransa Ni nasan Mai yasa Baya iya yin komai mahaifiyarsa ce Bai San ya zai Mata ba Yana k'ok'arin biyayya ma tace Yana fifita Naeema akanta inaga Kuma ya fito ya nuna bayaso abinda ake yiwa Naeema kinsan abinda zatayi sai yafi Haka a gaskiya aunty ki duba maganar nan"


"kimin shiru larai kinsan Mai matar Nan take yiwa Naeema kuwa?kinsan Abubuwan da duk take mata kuwa kasheta takeso tayi fa akan me zata cigaba da zama a gidan?

Ke idan kece Zaki iya jure duk abubuwa da ake wa Naeema.?Naseer da kike magana akansa Naga guduwa yayi ya barta da yaran Naeema ita ta tsaya tsayin.daka ta nemi kudi duk da cikin jikinta ta tsayawa yaranta itace cinsu da shansu makarantar su abinda Naseer ya guje wa itace ta ringayi kwatsam wanan tsinaniyar matar Nan ta danno ita da kanwarsa suka hau gallaza Mata duk abinda zatayi idonsu.na Kai Naseer din ma ya dawo ba abinda ya canja sai ma gaba da yayi Dan me zata cigaba da zama wlh cigaba da zama a gidan kamar tana Wasa da rayuwarta ne Yara nawa ne suke rayuwwa ba iyaye ballantana yaran Nan da ubansu Dan nasan tafiyar.Naeema bashi zai saka shima ya tafi ba Dan Haka ya zama Dole ya kula dasu Kuma Nima duk abinda zasuyi idona na kansu tunda Isihu zai cigaba da zuwa gidan Kuma yaran na zuwa islamiyya Mallam idan dai ta musu wani Abu wlh Tallahi sai na Kai kararta na tsani matar Nan wlh Tallahi yau da nice Naeema da tuni nayi maganin matar nan"

"Duk da haka Aunty Tafiyar Naeema bashine mafita ba dann kamar ka kashe miciji baka sari kansa ba Naeema zata tafi ne Amma tunanin ta na Nan Dan Haka Aunty Mai zai Hana tayi Zamanta a garin Nan Amma a wani unguwar hankalinta sai ya Dan fi kwanciya inyaso duk lokacin data so ganin yaranta zata iya zuwa gidanki a boye idan sun zo islamiyya sai ta gansu batare da Shi Naseer yasan Inda take a garin Nan ba ta Kama haya ta had'a Kan kudinta ta ringa sana'a

Bansan lokacin Dana mik'e na rungume Mmn Abdul ba na kalli Aunty Ina "Aunty Dan Allah muyi hakan nima sai nafi samun kwanciya hankali a Haka ma wataran na kwashe yarana gabadaya batare da sun sani ba ki taimaka min Dan Allah banida kowa sai Allah sai ku danake ji Kamar Yan uwana"


Aunty ajiyar zuciya ta sauke tana toh shikenan.

Ni kuwa take naji sanyi a Raina Aunty ta koma ta zauna Suka fara shawarar Inda ya dace a samo min karamin gida na haya na zauna ahaka suka yanke nemo min gida a dorayi Dan suna da Yan uwa acan Amma kafin a samo gidan na dai tafi Bauchin na duba gidanmu na siyar sabida na samu ishahsen kudi a hannuna da zan ja jari.

Haka kuwa akayi wajen karfe goma na nufi Tasha bayan Aunty tace min ita Kuma zata wuce dorayi ta cigitamin gidan Haya idan an samu kafin na dawo zata biya kudin hayan.


NASEER

Haka kawai yaji ya kasa nutsuwa yayi sallah hankalinsa yayo gida gabadaya hakane yasa Ana iddarwa ya fito da saurinsa a bakin kofa yayi kicibis da zahira dake k'ok'arin yin waje cikin tashin hankali

Gabansa yanke wa yayi ya fadi Yana "Ke lafiya Ina Zaki"?

"Abba Umma nake nema yanzu tace na Shiga bandaki nayi alwala na tashi su Nadeeya shine Dana fito banganta ba na duba koina banganta ba"

Ta karashe da rawar murya idonta na cika da hawaye

Naseer jikinsa ne ya hau rawa cikin tashin hankali ya Shiga gidan ya duba koina ya fito Yana sallati
Tare da yin waje kafa ba takalmi duk nisan titi Haka ya je kafa ba takalmi Zahira na biye dashi tana kuka.

Ba ta Inda Bai duba ba Bai ga Mai Kama da Naeema ba.


Kamar Wanda ake sassarewa kafa Haka ya dawo gidan Yana Jan kafa Zahira nata kuka Dan tasan Naeema ta tafi ta barsu tunda kwana biyu kenan tana cewa ta kula da kanenta idan tace Umma tafiya zakiyi sai tace aa

Naseer d'akin Naeema kawai ya nufa Yana Jin jiri na dib'arsa.

Bayan ya d'au takardar da Naeema ta ajiye Mishi a bakin kofa.

Ya kwanta rigingine hawayen da yake San maidawa ta karfi Suka hau zubo masa.

Zahira kuwa Kamar wacce akayiwa duka tabi bayansa tana cigaba da kuka

Ahaka Hajara da Safiyya suka fito sabida yanda kukan zahiran ke tashi

Har d'akin Naeema Suka Shiga suna dube dube har Hajara na fatan Allah yasa Naeema ce ta mutu

Zahira na ganin sun shigo ta hadiye kukanta da Sauri jikinta ya hau rawa Naseer kuwa ya bud'e idonsa yana kallon Hajara dake kalle kalle a d'akin ta dawo da kallonta Kan zahira tana "Ke Dan uwarki kukan me kike Mana da asubar nan"?


Zahira bata iya magana ba ta matsa kusa da Naseer daya tashi zaune ya jingina da bango Yana kallon Mahaifiyarsa har lokacin hawaye na gudu a fuskar sa hawayen da ke Kara saka Zahira damke bakinta Dan Kar kuka ya kwace Mata a gabansu Hajara da take ganin tamkar malaikan da zai zare Mata Rai.

"Dan uwarki bazaki gayamin ba kukan me kikeyi ke da ubanki ko uwarki ce ta mutu"?

Wani irin murmushi daya fi kuka ciwo Naseer yayi ya d'auke hawayen fuskarsa ya kalli Hajara Yana " Ba mutuwa tayi ba ta dai tafi ta bar miki gidan Kamar yanda kikeso ta tafi da Waleed ta bar sauran yaran"

Hajara Kara dudduba d'akin tayi Wai Dan ta gaskata maganar da kunnenta ke jiyo mata

Naseer kuwa yanda Safiyya ta washe baki murnarta na fitowa fili yasa ya fara jifanta da wani irin kallo tayi waje da Sauri

Hajara kuwa ta fito ta lek'a koina taga dagaske dai Naeema Bata Nan ta koma d'akin taja Tsaki Tana "Ni zaku rainawa Hankali yau ta Saba guduwan ta Kuma dawowa Naga Haka kuka rainamin hankali na gano kuna taren yanzu ta Inda kuka Kara b'ullo wa kenan ta tafi idan an kwana biyu sai ka bita Kai da yaran ko"?



"Umma Naeema ta tafi idan da hada Baki mukayi da ita wlh bazaki gani a d'akin Nan Ina kuka ba da ace hada Baki mukayi bazata bar min yaran Nan ba barin yaran Nan da tayi ya Isa yasa kigane gajiya tayi da abinda kike Mata Umma sanin kanki ne banida komai Naeema ita ke rike da gidanan daidai da abincin da zamu ci ita take bamu yanzu data tafi daga Ina Zan fara Umma Ni Kam bansan Mai na Miki a rayuwata ba bansan Mai yasa kike San ganina a kuncin rayuwa ba"

"Ba abinda kamin Dan albarka Naeema ce kawai na tsana karka wani damu da tafiyar da tayi dama so take kawai ta gudu Dan taga ka talauce iya tafiyar da tayi yaci Yasa kagane ba Dan Allah take zaune da Kai ba karka wani damu da ita take komai a gidanan Nima Zan cigaba daga Inda ta tsaya markade ne na iya zobo da ruwa nima na iya k'ulawa ai Dan Haka Kar ka wani damu Dan albarka idan Allah ya yarda da kaina Zan Nemo maka matar da zata zauna da Kai Dan Allah Mai ake da Naeema"

Ta karashe tana yin waje cikin tsananin farinciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna.

Naseer Bai iya ce Mata komai ba har ta fice Zahira kuwa ta matsa daga kusa dashi ta fita d'akinsu ta cigaba da kukanta Su Nadeeya na k'ok'arin fitowa daga d'akin Dan su shiga d'akin Naeema Suka hadu da Naseer a bakin kofa hakane yasa Suka koma ciki Naseer ya shiga d'akin ya zauna a tsakiyarsu Yana Jin zuciyarsa na Masa wani irin Nauyi Raheema da ke da shekara hudu ya kala ya d'auketa ya dorata a cinya Yana maida hawayen dake neman zubo Masa ya hau magana a fili Yana "Baki kyauta min ba Naeema baki min adalci ba da Kika gudu Kika barni da yaran Nan Mai yasa Kika gudu a lokacin da muka fi bukatarki?Mai na Miki da zafi Haka zakimin Haka"? Kinsan banida kowa sai Allah sai ke sai yarana ku nake gani naji dadi Amma Naeema Kika Shure Kika tafi sabida Mahaifiyata Tana Miki ba daidai ba duk hakurin Dana ringa Baki akan kiyi hakuri da halinta Nima addua nake Akan Allah ya shiryeta Naeema baki zabi guduwa ba sai a irin wanan lokacin ? akanki Mahaifiyata tamin Baki har yau bana ganin daidai duk kudin Dana rik'e basa albarka na zabi Zama dake a kowane Hali na zabi nayi rayuwar talauci Dan kawai na zauna dake Bayan irin kudaden Dana Kama a baya duk ban damu da rasa sun danayi ba sabida ke Amma yau sabida tsangwamar da Mahaifiyata ta Miki Kika gudu Kika barni da Yara Mai yasa Naeema Mai kikeso nacewa yaranmu"?


Naseer ya karashe muryarsa na rawa magana yake shi kadai kamar da Naeema yake magana

Nadeeya da Minal kuwa cewa suke Ina ummansu taje.haka Suka lek'a d'akin Suka dawo Suma Suka hau kukan.

Hakane yasa Naseer ya share hawayensa Yana Zahira ta tashi ta Dora musu abinci su tafi makaranta.

Zahira hka tayi waje tana share hawayenta.

Naseer kuwa ya warware takardar da Naeema ta ajiye Mishi ya fara karantawa *NASEER KAYI HAKURI DA MATAKIN DANA D'AUKA NA RABUWA DA KAI NAGAJI DA ABINDA UMMA DA AUNTY SAFIYYA KEMIN NAGAJI NASEER UMMA TACE NI MAYYA CE TACE NI KARUWA CE BA IRIN ABINDA UMMA BATAMIN INA SHANYEWA AMMA YANZU NAGAJI DAN NAGA KIYAYAR DA TAKEMIN KARUWA YAKE BA RAGUWA BA KIYAYYAR DA TAKEMIN YA SHAFI YARANA GABADAYA DAN HAKA KAFIN NA HAIHU NA MATA ALKAWARIN RABUWA DA KAI INDAI ALLAH YA SAUKENI LAFIYA HAKANE YASA NA CIKA MATA WANAN ALKWARIN DANA D'AUKA NA TAFIYA NA BAR RAYUWARKU NA HAR ABADA ZAN RINGA ZUWA GANIN YARANA INSHA ALLAHU KASA KANKA A MATSAYINA KO KAINE MATAKIN DA ZAKA DAUKA KENAN A KARSHE NASEER NA HADAKA DA GIRMAN ALLAH KA KULARMIN DA YARANA KARKA BARI A CUTARMIN DASU NASEER BAZAN YAFE MAKA BA IDAN WANI ABU YA SAMESU NASERR UMMA TA TSANI ZAHIRA ITA DA AUNTY SAFIYYA NA BAKA LABARIN YANDA SUKE CIN ZALINTA A GABAN IDONA NASAN ZASU IYA KOMAI YANZU A BAYAN IDONA NASEER YARAN NAN AMANA NE A WAJEN MU KARKA BARI MAHAIFIYARKA TA CUTARMIN DASU NASEER KASAN YANDA NAKE KAUNAR YARANA BA ASAN RAINA NA TAFI NA BARSU BA DAN ALLAH KA KULARMIN DA SU NA BAKA AMANARSU AN FI TSANAR ZAHIRA KA SA IDO AKAN SU NA AJIYE MAKA KUDI A KARKASHIN KATIFA MAI YAWA ZAI ISA KAJA JARI KA KULARMIN DA YARANA NA SIYAR DA INJINA NA GUDA BIYU SABIDA NA HADA DA KUDIN WAJENA NA JA JARI NIMA KAYI HAKURI HAKA ALLAH YA KADDARA MANA RABUWAR MU SHI YAFMIN ALHERI DAN UMMA KARFI DA YAJI TAKE SAN KASHENI KAYI HAKURI BA A SAN RAINA NA GUDU BA NGD DA KAUNARKA A GARENI DUK.LOKACIN DANA TASHI ZUWA GANIN YARANA ZAN TAHO DA WALEED KA GANSHI*


cukwikuye takarda Naseer yayi batare da ya karasa karanta Takadar ba sabida yanda jikinsa ke rawa zuciyarsa tayi balain nauyi a fili yace "Ni kuma tawa kaddarar kenan Allah ka bani ikon cinye wanan jarrabawa ka bani ikon sauke nauyin daka doramin na yarana.

Waje ya fita yaga Safiyya na shara tana wake wake su Nadeeya sunyi cirko.kamar marayu


Zahira kuwa Tana Kitchen ta kurawa waje daya Ido


Kitchen din ya Shiga ya cigaba da girkin yacewa zahira ta shirya kannenta kafin ya Gama

Yana gamawa a faranti ya juye musu ya Kai abincin har Palo ya zaunar da Raheema a cinyarsa ya hau Bata a baki Nadeeya da Zahira kuwa kasa cin abincin sukayi duk yanda yayi dasu kuwa Akan suci abincin.

Ahaka suka fito Bayan ya d'auki naira Hamsin ya rakasu har bakin makaranta sai daya ga shigarsu ya koma gida.

Sai dai tundaga nesa ya hango Hajara taci uwar damara ta Hana a fita da engine da wasu maza Suka zo dauka sai balai take tana tsalle tana hango shi ta nufo wajensa da Sauri tana "Kajimin shegu tsinannu Haka kawai suka zo d'aukar engine Wai wacce ta siya ce tace su zo su dauka Naga engine Naeema ne wacce matar Kuma suke magana kaji barayi"


"Naeema ta siyar da engine yanzu ba nata bane masu shine suka zo d'aukar kayansu"

Naseer yace tare da cewa.mazan su dauka su tafi

Ya shige gidan ya bar Hajara na balai bazata yarda a fita da engine ba Samarin kuwa ganin er tijara ce da k'arfi Suka fita da engine Hajara data tare hanya suka hankadata gefe ta zub'e a kasa

Safiyya itama ta hau rantsuwar bazaa fita da engine ba Dan sosai suka.gama lissafa yanda zasu samu kudi da engine Umma har da lissafin zata siyi fili Dan sunga yanda Naeema ke samun kudi da engine markaden sosai suka tiki rawa a dakin Dan murnar tafiyar naeema.sai gashi Ashe ma ta siyar da engine


Suna ji suna gani aka tafi da engine Hajara Kamar tababbiya ta nufi d'akin da Naseer ke kwance.........




*Comment*

Nikuwa aganina batayi kuskure ba
Ayadda Dan Adam,musamman ma mace take da rauni ai baza'ace ma naeema komi ba Dan kuwa tayi balain kokari...
Awajena bunda ya dace tayi kenan adaidai wannan gabar. Ki duba fa
Da can sunce arxikin shi yasa ta makale masa Amma yanzu itace mai rufin asirin Amma kuma sunce kudin karuwanci ne Kuma dan naseer na taimakonta da aikin gida sunce tayi kudi ta mai dashi boyi boyi.
Haba jamaa abun Sam babu dadi gaskiya ko mai tsananin Imani ne saiya raunana..

Tunda har ba ita da bakinta ta nemi saki kotayi fitar fushi wallhy harga Allah batada wani lpya
Her decision was based on nazarin data rinka yi ba acikin son zuciya da gaggawa ta yanke shi..
Inhar da ace nice naseer wallhy zan kyaleta hakanan itama taje ta huta Amma bazann taba in saketa ba,ai zataje din Kuma itama zataji abunda yaji aransa lokacin dayayi tunanin guduwa ya barsu acikin ukubu shine mafita.
Hanklinta na kwanciya zakiga ta dawo ,but ni banga lefinta ba kokadan
Every body derserve a break and refilled.
In dauriya yayi yawa sheidan yakan saurin batar da mutum ta hanyar rusa masa aikinsa da mugayen tunani har akaiga kayi asarar tulin hakuri da jajircewan da kayi,Is best dat she leave queitly gaskiya.👍🏻

*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page 35*

"Kana kallo Suka fita da engine baka hanasu ba yanzu ta Ina zamu ringa samun kudin da zamu kashe"?


"Toh Mai engine ta siyar da kayanta Mai shi yazo ya d'auka ta Ina Zan Hana Umma abinda ba nawa ba"


"Kai Amma yarinya nan Allah sai ya tsine Mata muguwa idan ba mugunta ba ai ko Dan yaranta ta bar engine dinan sabida a samu na kula dasu Amma dayake bata da mutunci shine ta siyar da engine duka biyu idan ma tayi hakane Dan mugunta ai har da yayanta ta cuta wlh dadin abin ba iya markade akeyi a gidan ba Ana kulla zobo da ruwa Kuma a siyar Nima dai ba kuturwa bace inada hannun da Zan kula ruwa da zobon na samu na kaina wlh ko kallon yaranta bazan yi ba Kai Kuma zaman gida ai Bai kamaka ba tashi zaka Yi ka fita ka nemo kudi ba kazo ka shige daka ka kwanta Kai ga uwarka ta rabu da Kai ai Zama Bai kamaka ba ya zama dole kaje ka Nemo duk inda kudi yake ka nuna Mata Kai Dan halak ne insha Allahu sai kafi da arziki tashi Maza idan wanan shegen isihun yazo Zan aikeshi yamin cafenen zobon na hada ya kaimun"

"Ko na fita Umma bazan samu ko sisi ba ko na samu ma bazai Yi albarka ba Dan kin riga da kin tsinewa samuna Umma ko mantawa kikayi kin Kona duk dukiyata ta bakin naki kudi sai yamin wahalar samu yanzu gashi ai kingani kudi Yana min wahalar samu Umma kusan wata Takwas nayi a Abuja Ina neman kudi cikin tsananin wahala Umma Wanda ma na Dan samo sai da Yan fashi suka kwace a hanya ba abinda na taba yanzu dayake albarka"



"Duk ba Kai ka jawo ba sabida tsinanen taurin.kanka zuciya ya debeni nayi abinda nayi da Nima yazo ya shafeni Dan Haka batun ma Ni na jawo duk laifinka ne na saka albarka yanzu idan Allah ya yarda zaka samu kudi ka shirya kaje ka nemi kudi"

Daga Haka ta fito tana tsinewa Naeema akan ta siyar musu da engine.

Rai a bace Haka Suka zauna a tsakar gidan suna ta kwashewa Naeema albarka Dan canjin daya musu saura tasa Safiyya ta d'auko Suka lissafa abinda zasu kashe na hadin zobon suka zauna zaman jiran Isihu sai dai har karfe Sha biyu Basu ganshi ba ahaka Hajara ta lek'a da kanta Wai ko zata hango shi Nan ma Bata gan shi ba haka ta dawo ta Kara komawa d'akin Naeema ta tarar da Naseer a zaune a Kan Sallaya Dan tunda ya iddar da walha Bai bar Kan sallaya ba carbi kawai yake ja.

"Kaga shegen almajirin Nan Bai zo ba inata jiransa tundazu ko dashi ta tafi ne"?

Alama ya Mata da hannu alamar Bai Sani ba

Hajara kuwa ranta ya b'aci tana "Kai bana San iskanci Naga duk abinda ma shegiyar matar Nan tayi ba abinda ya dameka sai Abu kake Kamar wani maraya toh tunda Bai zo ba Kai Kuma ka k'i fita ka Nemo Mana kudi sai ka tashi kaje kayo min cafenan zobo idan zuciyarka ta mutu Ni tawa ba ta mutu ba idan tafiyar Naeema ne ma yasa kake wani nonok'ewa zaka ware me dalla tashi ka siyomin zobo da suga da farin Leda"


Ta karashe tana jefa mishi kudin hannunta.

Naseer ya d'ago da rinannun idonsa Yana "Ina Safiyya Umma da Ni zanje na siyo Umma Dan banida kudi Bai Kamata na zama kamar yaro da sai yanda akayi dashi wanan ma na iya janyo min raini a wajen Safiyya Ina gaba da ita ki wuceta kizo ki aikeni haba Umma"


"Kace kawai ban Isa dakai ba Naseer ai kafita sanin unguwar Nan sai ka fita sanin Inda ake siyar da kayan zobon shiyasa na kawo maka"

"Ki Bata idan ta fita tayi tambaya zaa nuna Mata"

"Nifa bazaka zauna a gida ni Kuma na ringa fafutukar neman kudi ba Dan Haka ko bazaka siyo ba ka zura rigarka ko dakone kaje kayi Dan Idan ma takamarka Kayan abinci da ake dashi a gidanan ne kwanan Nan zai Kare wlh Nima yanzu sama na da kasana iya kudin Nan ne Dani Dan Haka nemo kudi ya kamaka"


Daga Haka ta fice daga d'akin ta bawa Safiyya kudin ta lissafa mata abinda zata siyo Mata ta karbi kudin tayi waje tana zagin isihun da Bai zo ba

Naseer kuwa Yana fitowa

Kitchen ya Shiga ya fara k'ok'arin dorawa su Zahira abincin Rana Hajara kuwa tace ya fita idan Safiyya ta dawo zata Dora musu abincin.

Naseer Bai. Ce Mata komai ba ya cigaba da abinda yake Dan wasikar da Naeema ta bashi na ya rik'e amanar yayansa ya rik'e gam akansa bazai soma barin Safiyya ko mahaifiyarsa su dafawa yaransa abinci ba.

Haka Hajara tayi ta bambamin fad'a har Safiyya ta dawo.

Dayake taliya Naseer ya Dora musu Nan da Nan ya Gama Dan akwai Miya Mai yawa a freezer din dake d'akin Naeema Dan har freezer ta siya da ta samu kudi ta daina siyan kankara.

Haka take Miya Mai yawa sai dai su dafa shinkafa ko taliya Miya tuwo ma Haka take yinshi da yawa.

Yana gamawa ya zuba wa su Hajara a kularsu ya d'auki sauran ya Kai daki Kamar yanda yaga Naeema nayi

Ya daura alwala ya fice daga gidan Hajara da Safiyya dake kula zobo da ruwa suka bishi da kallo har ya fice.

A Kular da Naeema take zuba zobo da ruwan Suka zuba

Hajara ta nufi d'akin Naeema Dan ta dauko kankara sai dai tana zuwa taga k'ofar a kulle.

Masifa ta ringa surfawa akan me Naseer zai kulle k'ofar d'akin Mai ya mayar dasune.

Haka ta koma ganin Bata San lokacin da Naseer zai dawo ba yasa ta bawa Safiyya sauran kudin hannunta ta siyo musu kankara Suka zuba Suka zauna zaman jiran Isihu da sai daya Sha tsinuwa yafi cikin kwando Hajara har da Shan alwashin wanka Masa Mari idan yazo.

Naseer kuwa Yana fita a Massallacin dake kallon gidansa yayi zamansa bayan ya iddar da sallah Yana tunanin yanda zai fara fuskantar rayuwa batare da Naeema ba Bai San Mai yasa Bai tab'a koyawa kansa rayuwa batare da ita ba a yanzu da ta tafi a lokacin da Bai tab'a tunani ba sai yaji Kamar rayuwarsa ce ta tsaya Amma ba yanda zaiyi Haka zai rungume sabon Shafin kaddarar daya bud'e Masa.

Ganin biyu tayi yasa ya fito daga Massallacin a daidai lokacin daya hango su Zahira suna Shiga gidan.

Hakane yasa yabi bayansu.

Suka Shiga gidan kusan a tare.

Daga Safiyya har Hajaran ba Wanda ya amsa Sallamar da sukayi.

"Ka ajiye Mana abinci ba Miya ka Kama kanya ka fice tare da kullo k'ofar d'akin da bansani ba ko Gwal aka saka da zaa ringa rufewa sanan name idan an gama girki zaa wani shige dashi d'aki to daga Yau wlh idan anyi abinci Kar akara Shiga dashi d'aki idan uwarsu na Shiga dashi d'aki sabida Bata yarda Dani ba Kai ma yarda ne bakayi Dani ba shiyasa kake kaiwa daki kenan toh wlh Kar a sake idan ba Haka ba sai ranka ya b'aci"


"Ke maza ajiye jakar hannunki ki je Makarantar islamiyyarku ki kiramin wanan shegen almajirin tundazu na zauna Ina jiranshi yazo.ya kaimin zobo da ruwa har yanzu Bai zo ba narasa Mai ya Hana shi zuwa ko Uwarku ce ma ta zuga shi tace.kar yazo Dan ta tafi"

Hajara tace tana hararar Zahira data yi saurin ajiye Jakarta cikin rawar jiki zata yi waje

Naseer yayi saurin rike Mata hannu Yana "Bari ta fara cire uniform din jikinta taci abinci tayi Sallah kafin ta tafi yanzu Nan ta shigo gidan fa Bari ta Dan huta"


"Iyyeee Naseer Ni nake Aiken Yarka kake hanata akan sai ta huta kafin taje kana cikin hayyacinka kuwa ko Tafiyar Naeema yasa ka fara shaye shaye toh wlh sai taje Naga idan ma aka siyar da ruwa

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment