Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba.


Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad'an ya Kara siyan fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari.

Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa.

A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema.

A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji.

Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu'a duk da Bata tab'a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar.

Hajara kuwa dak'yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi.

Satinsu uku a Calabar suka dawo.

Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo.

Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba.

Ahaka ya b'oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa.

Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali.

Yana tashi ta kalli Safiyya tana "Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki"

Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba
Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada.

A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan.

Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa.

Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad'uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har Naseer ya tafi.


Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba


Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran.

Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira

Zumbur ta mik'e tsaye

Tace "Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema"


Yaraf Hajara ta zub'e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik'ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me"?


Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d'auko ta zata hada Masa kudinsa.


Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada.

Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema.

Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu.

Ina zaune naji Ana buga gate da balain k'arfi mik'ewa nayi cikin fad'uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina.

Inna zuwaira ce ta bud'e gidan tana bud'e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya.

Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi.......
[6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 21*

Kirjina bugawa yake bakina d'auke da sallati ganin Umma tamkar ganin malaikan da zai zaremin Raine bamu tab'a had'a inuwa da Umma Bata nemi cutar Dani ba har ya Kai indai zanyi Ido biyu da ita tsigar jikina sai ya tashi.

Abinda ya bani mamaki irin tsoron danake ji idan naganta banji irin Wanan tsoron ba duk da dai a tsoracn nake.

Kallona kawai take daga bakin kofa jikinta na wani irin rawa Zan iya cewa ban taba ganin ta a cikin wanan yanayin ba wani irin Mugun tsanata nake hangowa a idonta da ace zanje hannunta Ni nasan sai ta rabani da numfashina.

Hakane yasa na tsaya akan kafafuna sosai Ina adduoi a Zuciyata

Saffiya ce ta shigo palon tana ta duramin zagi tana tsinemin sai zagin iyayena take

Inna zuwaira kuwa sai cewa take daga Ina kuke wa kuke nema"?

"Shegiya Mayya nataciya tsinaniya Banda maita ana dolene? munce bama sanki Umma tace Bata sanki ki rabar Mata da D'a Mana shegiya akuya Mai gindin haihuwa kinsamu waje sai haihuwa kike kamar akuya ko akuya ma na Dan bada tazara Banda ke duduu yaushe Kika haifi wancan bak'ar yar taki"


"Kema ki zuciya ki haifi naki Safiyya"

Na tsinci kaina da fad'a Nima cikin mamakin kaina
"Nace ki zuciya kema ki zama akuya ki haifi naki ba ki sakoni agaba ba Saffiya Ni ba Mayya bace Yayanki ne Mayya ya Kuma nace min kije ki nemi miji kiyi aure ki samu ki haihu Safiyya bibiyata da sharri ba naki bane Dan Allah shi ya halliceni rayuwa da Kika ga inayi shi ya tsaramin yayan da kike magana shi ya bani Kuma iya yayan da ya hukunta Zan samu shi Zan Haifa Safiyya babu yanda zakiyi Dani"


Daga Saffiya har Umma wani irin kallon mamaki suke min Safiyya kuwa tuni idonta ya kad'a yayi Ja ta nuna kanta tana "Ni kike fadawa maganganun nan Naeema"?


Maganar mmn Mannir na tuna "duk ranar da Kika kwatar wa kanki yanci zakiyi mamaki wlh sai sun fara shakarki suna tunanin kila akwai abinda Kika tak'a

"Eee ke nake fadawa maganganun nan ko Haka zai saka ki zuciya ki kyalleni Kun takura min Kun sakoni agaba ku kyalleni Dan Allah"

Cikin wani irin zafin Nama Safiyya ta daga hannunta zata kawomin Mari.

Nima cikin zafin nama na tare Marin tare da yarfar da hannunta duk wani Abu da suka Dade suna min na dawomin cikin zuciyata da zata lura da kyau zata ga yanda jikina ke rawa sabida tsoro Amma abinda sukemin ya isheni rayuwata a hannun Allah take iya rayuwar da Allah ya yarjemin shi zanyi na tafi na Kai matakin da na gaji da d'aukar abinda sukemin.

"Karki sake ki Kara yunk'urin kawo hannunki jikina wlh bazan dauka ba abaya na biku na rokeku na shanye duk abinda kuka min Amma yanzu Kun kaini bango Nagaji ku sakarmin Mara nayi fitsari Safiyya kuje ku nemi miji kuyi aure ya zakiji idan kikayi aure kanwar mijinki da mahaifiyarsa na musguna Miki Haka ya Zaki ji Dan Allah ku kyalleni Allah yayi Naseer mijina ne duk Inda kuka Kai da kuga Kun rabamu idan Allah Bai nufa ba wlh babu yanda zakuyi"

Hannu ta Kara kawowa jikina na kauce da Sauri Kafin na ankara ta kawomin shak'a wuyana

"Har Ni kike gayawa maganganu har wuyanki ya Isa yanka Naeema Mai kike takama dashi?

Inna zuwaira ce ta bambare hannunta daga wuyana dayake tana da tsayi ta wancakalar da hannun Safiyya tare da kwasheta da Mari

"Sai na tsine Miki Safiyya idan har baki Gama da yarinya Nan ba Kika bari na karaso da kaina"

Umma tace tana wani irin hucci

Inna zuwaira ce ta tare wawuran da Safiyya taso kawomin ta Kara kwasheta da Mari tana "ke Wai wacce irin Mara tarbiyya yarinya ce ke ya zaku shigowa mutane gida kice Zaki Kama matar gida da k'ok'awa"

"Kina Wasa da wuta idan baki cire kanki a maganarmu ba Marin da kikamin Kuma wlh sai kinji a jikinki ki matsa min tsohuwa babu ruwanki a maganarmu"

"Ta Allah ba Taki ba yarinya Nafu karfin sharrinki ba abinda zanji a jikina Naga alamar baki da tarbiyya ku juya ki koma daga inda kuka fito Dan bazan Bari hannunki ya tab'a jikin hajiya ba Dan Haka"


Safiyya Bata Bari ta karasa ba ta d'auke Inna zuwaira da Mari kafin kace me sun fara wani irin k'ok'awa mamakin karfin halin Safiyya data iya kaiwa Inna zuwaira duka yasa jikina ya fara rawa kafin kace me ta hau ruwan cikin Inna zuwaira ta hau Kai Mata duka ko ta Ina

Hankalina a tashe nayi kansu na fara k'ok'arin daga Safiyya daga jikin inna zuwaira Ina sallati

Dan duka take kai Mata kamar wata saarta

Sai a lokacin Umma ta shigo palon tana idan Kika barta da ranta Safiyya bani na Haifeki ba gwara tasan rijiya ba wajen wasan makaho bane.

Jinin Dana ga Yana fita daga hancin Inna zuwaira yasa na saki sallati na fara ture Safiyya da iya karfina Ina ihu Dan nasan iya karfin Safiyya bazai saka ta iya dukan inna zuwaira ba sai dai idan da tsafi take dukanta


Nima duka na fara kaiwa Safiiyya Dana ga alamar so take ta kashe Inna zuwaira dake ta sallati.

Da Hannu daya ta tureni sai gashi na Fadi kasa nayi zaman dirshan Kara mik'ewa nayi cikin tashin hankali ba dai kashe inna zuwaira zatayi ba kamar yanda Umma tace.

Kansu na Kara yi kafin na isa wajensu Naga ta mik'e daga Kan Inna zuwaira tayo kaina taku uku nayi na shige d'akina na kullo k'ofar Ina ihu

Dan sosai na ji tsoron Safiyya ya rufeni idan har zata iya dukan inna zuwaira Ina tsaya Kam kasheni zatayi.

Ina Jin Safiyya ta ringa jijjiga kofata da k'arfi tana na fito Kar na Bari ta balla k'ofar ta shigo ai ta d'auka wani Abu na taka nake zaginta Ashe karyar iskanci nake.

Ina ji Inna zuwaira nata sallati Umma na gobe ma ki Kara Shiga abinda Bai shafeki ba

Har k'ofar dakina naji Umma tazo suna ta tura k'ofar Dan ta karfi suke so su shigo Kuma yanda sukeji wlh sai sun rabani da Raina sai dai duk abinda zai faru ya faru.

Sosai na ringa Kiran sunan Allah Ina neman ya kawomin d'auki


Umma kuwa cewa take wlh a yau zata nuna Mana bamuda wayo har nida Naseer mun Isa mu Raina Mata hankali wlh a yau ko Naseer ya sakeni ko ya zab'a ko ita ko Ni sosai Naga alamar ranta ya b'aci take kirjina yayi ta bugawa wani irin balain tsoro na rufeni


A haka sukayi ta zagina suna tsinemin suna ta k'ok'arin shigowa d'akina

Bansan tsawon lokacin Dana d'auka daki ba gabana ne ya tsinke a lokacin Dana ji sallamarsu Zahira da maganar daya fito daga bakin Safiyya.

Ai Zaki bud'e ki fito idan Kika ji Ana dukan yaranki ko

Kafin kace me sai ji nayi Ana dukan Zahira da Nadeeya har da karamar Minal ihunsu kawai nakeji Ana dirmarsu.

Cikin tashin hankali na bud'e kofa Umma Zahira kawai take dagawa tana nunawa Allah Tana makata da kasa.dan a yayana tafi tsanarta sabida kawai tana Kama Dani

Safiyya kuwa had'e Nadeeya da Minal tayi tana ta duka tana ganin na fito ta cikasu tayo kaina Ni kuwa bansan wane irin Zuciya ne yazomun ba tana a haukace na daga ta na nuna wa Allah na makata da kasa


Nayi Kan Umma da take ta buga zahira da kasa.

Wani irin wawuro nayiwa Umma na Kai hannunta bakina na kafa Mata hakorina Ina ihu sai a lokacin ta cika Zahira.

Tana "wlh yau sai na kasheki Haka wuyanki ya Isa yanka

Wani irin shak'a ta kawomin da.hannu biyu

Safiyya ta hau kaimin kafa ko ta Ina suna yi suna zagina.

Umma kuwa da iya karfinta ta shakemun wuya Bata da burin daya wuce ta rabani da Numfashina Safiyya kuwa hambara ta kawai take da kafa yarana suna ihu.

Ni kuwa ihun ma kasawa nayi sabida shakar da tamin "Badai kince ke Mayya bace bazaki rabu da Naseer ba wlh yau sai na kasheki.

Tuni numfashina ya fara daukewa Ina juyo kamshin lahira muryar yayana kawai nakeji suna ihun kuka.

Sallati kawai nake a raina muryar Naseer naji da k'arfi ya gwada sallati.

Take naji Safiyya ta daina kawomin kafa

Sosai jikinsa ke rawa da yaga yanda Umma ta shakemun wuya tana San kasheni Kuma shigowar sa Bai sa ta cikani ba illa ma Kara shakeni da tayi


Wani irin finciika yayi wa Umma Kafin na dawo daidai sai karar Mari naji Tau

Duk da ba a hayyacina nake ba sai da na saka ihu danaga Naseer ne ya Mari Umma

Shi kuwa Naseer yabi hannunsa da ya Mari Umma da kallo jikinsa na wani irin rawa da alama bai San sanda yayi Marin ba.

Da alama bada niyya yaso marin Umma ba Amma sabida rufewar da idonsa yayi ya Mareta


Safiyya kuwa da hannu biyu ta rufe bakinta cikin mamakin abinda Naseer yayi.

Umma kuwa ta dafe kumatunta tana kallon Naseer cikin wani irin rawar jiki
Ni kuwa kuka na fashe dashi Ina sallati

Bazan tab'a manta ranar Nan ba Naga tashin hankali da ko makiyana bana fata ya gani ranar da wani sabon Shafin kaddarar tashin hankali ya bud'e mana Wanda da nasani da ko kukan jini Naseer keyi da ban dawo gidansa ba

Cikin wani irin murya Umma ta nuna kanta tana "Naseeru Ni ka mara? Ni Mahaifiyarka ka Mara akan matarka Naseer Ni na Haifeka fa Naseer bayan karyar da kamin akan Naeema ta gudu bayan munafurtata da kayi Akan Naeema ta gudu baka ganta ba shine wanan duk Bai isheka ba sai ka daga hannu ka Mareni Ni Mahaifiyarka Dana dau cikinka tsawon wata Tara ka Mara akan wacce zaka iya canjata sau Dubu Ni baka Isa ka canjani ba" ?


Naseer durk'usawa yayi Akan gwiwarsa jikinsa na wani irin rawa har ga Allah Bai San ya akayi ya Mari Umma ba bada niyya ya Mareta ba tayaya ma zai mari mahaifiyarsa


"Umma ba da niyya na mareki ba Umma idona ne ya rufe danaga Zaki kashe Naeema Umma ya zanyi kin hargitsamin rayuwa kin hanani zaman sakat Umma na Miki biyayyar na buyan na rasa ya Zan Miki Umma tayaya Zaki zo gidana ki nemi kashe Naeema Umma kisan Kai fa kikeso kiyi baki ga cikin dake jikin Naeema ba Mai Naeema ta Miki Haka a rayuwa Mai na Miki Haka a rayuwa umma kodan rabon dake tsakaninmu ai ya Kamata ki kyallemu Umma Kinga fa Naeema wani cikin ne a jikinta da ba matata bace wlh bazata haifi wanan yaran ba Umma ya kikeso nayi kiyi hakuri Umma inasan matata bazan iya rabuwa da ita ba ki yafemin Marin Dana Miki umma.ki taimakamin"


"Naseer Zan yafe maka Marin da kamin idan dai ka saki Naeema wlh a yau sai ka zaba ko Ni ko Naeema idan dai Ni na tsugunna na Haifeka sai ka saketa idan dai ni na raini cikinka har tsawon wata Tara wlh sai ka saki Naeema bana San Naeema bana kaunarta akanta ka Mareni Naseer sabida ita zaka iya kasheni Naseer bazan tab'a san Naeema Ina umartarka daka saketa yanzu Nan Naseer."

"Umma bazan iya sakin Naeema ba kiyi hakuri idan na saketa wa zai rikemin yarana"

Ka bani su Zan rikesu nidai kawai ka saketa

"Umma Naeema Bata Da kowa gurin wa kikeso ta tafi idan na saketa"

"Ta Shiga Duniya Naseer babu abinda ya shafeni ka Saketa nace Naseer.

Umma kiyi hakuri bazan iya sakin Naeema ba

"Dan ubanka tare kukazo duniya da bazaka iya sakinta Naseer wlh Tallahi na baka zabi na karshe ka saki Naeema ko na Sallama maka ita Kuma sallamawar na har abada Dan na rantse da Allah sai na tsine maka Naseer idan dai har Akan Naeema ka Mareni ka ki bin umarni na to bakada amfani wlh tsine ma zanyi ka saketa nace"


Naseer kuka kawai yake jikinsa na wani irin rawa.

Ni kuwa mik'ewa nayi naje gaban Naseer Ina Dan Allah ka sakeni Naseer kabi Umarninta Dan Allah Naseer karka Bari ta tsine maka Dan Allah ka sakeni

Nima nace Ina jijjiga Naseer Ina kuka

"Ina umartarka Naseer ka saketa yanzu nan idan ba Haka ba wlh Zan Sallama ka ta zama uwarka Kuma Zan baka mamaki wlh tsine maka zanyi tsinuwar da bazaka yarda Zan iya maka shi ba Idan dai har zaka iya marina Akan Naeema Nima babu abinda zai Hana na tsine maka ka saketa nace Naseer"

Umma tace a tsawace cikin mugun b'acin Rai da ban taba ganinta a ciki ba

Nikuwa jijjiga Naseer kawai nake Akan ya sakeni shi kuwa ya dafe Kai da hannu biyu Yana

"Kiyi hakuri Umma bazan iya sakinta ba ki yafemin Dan Allah Umma Zan Miki duk abinda kike so auren da kikeso nayi wlh Zan Yi Dan Allah karki tilasta min na saki Naeema"


"Haka kace ko bazaka iya sakin Naeema ba ko Akan Naeema ka daga hannu ka Mareni Naseer akan Naeema kak'i bin umarnina toh yanda kaki bin umarnina Nima sai na tsine maka"


Da Sauri umma tayi wurgi da zanin jikinta har da skirt kafin kace me har paint dinta ta cire cikin Sauri gaban Naseer tsaya a Haka nikuwa tashin hankali yasa jikina ya hau rawa Ina sallati.

Naseer kuwa har lokacin kansa na kasa.

Cikin Wai irin murya Umma ta fara magana tana kaiwa gabanta duka.

"Naseer idan dai Ni na tsugguna na Haifeka sai ka tagayyara Naseer sai ka ga tashin hankali da ifitilai rayuwa

Bansan ya akayi na tsinci kaina Agaban Umma na rufe Mata baki da k'arfi cikin ihu Ina "Dan Allah Umma karki tsine Masa wlh Zan tafi Umma wlh Tallahi Zan bar rayuwarsa har abada Dan Allah karki Masa baki Naseer bakada hankaline kanajin kalmomin dake fitowa daga bakin umma fa kasan bakin uwa kuwa Dan Allah ka sakeni Naseer"


Nace da k'arfi Umma kuwa ta tureni. ta fara dukan gaban ta tana cigaba da Magana "Naseer idan dai Ni na Haifeka sai kayi bara abinda zaka saka a cikinka sai ya gaggareka
Indai ta Nan ka fito

Ta Kara kaiwa gabanta duka "Naseer kudi sai sun.maka wahalar samu sai dai ka gani a hannun mutane"

Sallati kawai Naseer keyi Ni kuwa na ringa ihu Ina rokon Umma ta daina tsine Masa wlh Zan kwashe kayana wani irin finciko kafadata.tayi ta dagani sama Dan rike Mata kafa nayi cikin wani irinn murya tace "rokon me kikemin Badai abinda kikeso kenan ba Badai burinki ki zauna dashi ba toh gaki gashi tunda ya zabeki akaina zai Gane tasirin bakin uwa kizauna ki cigaba da cin arziki Naeema ki cika Masa gida da Yaya ki maye Masa gurbina na barku har abada"

Daga Haka Umma ta wancakalar Dani ta dauko zaninta ta daura ko kallonmu Bata Kara Yi ba ta fice.

Safiyya tabi bayanta Jikinta asanyaye.

*True life haka Hajara ta tsinewa Dan cikinta wajen Nan ya girgiza ni a lokacin data bani labari*



*AL-BISHIRIN KU MATA !!!*
INA KUKE MATA
INA AMARE
INA MANYAN MATA

CHEF DEEJARH BERVER

SISIN MAMA

MAMAN FAREEDA(MAI TSUMIN 'YANGAYU)

ANEESA_DIDI

SALWISE'S KITCHEN

SUNZO MUKU DA YADDA ZAKU KARA ILIMI AKAN GIRKUNA DA GYARAN JIKINKI DA SIRRIN SACE ZUCIYAR MIJI DA YADDA ZAKUSAN MAGUNGUNAN DA YADDA ZAKI HADA CIKIN SAUKI....
GYARA SHINE MACE...
YADDA ZAKI GYARA JIKINKI YADDA ZAKI HADA MAGUNGUNAN DA KANKI..TSAFTA KWALLIYA DA GYARAN JIKI..
GIRKI MAKAMIN DIYA MACE INA MACCEN DAKE DA MATSALA DA GIRKI INA MACCEN DAKESON KARA ILIMI AGIRKI DA LEMOKU INA MASU SON KOYAN BIRTHDAY CAKE ??
KINA FAMA DA MATSALAR MATA KO INFECTION KINASO KISAN YADDA ZAKI SAMU MAGANIN GYARAN JIKINKI???
KISSA DA KISISINA IYA KWALLIYA JAN HANKALIN MAIGIDA NUNAWA KAUNA GA MEGIDA SOYAYYA KAUNA HAKURI DA IYA ZAMA....
ZAMU GABATAR DA KOYARWAR NAN DUK AKAN NAIRA DARI BIYAR (500)NAIRA ONLY
ZAMU KOYAR NE A WHATSAPP GROUP..
ZAMU FARA RANAR 20 JUNE 2021
KOWACCE MACE ISHASHIYACE...
KOWACCE MACE TANADA KYAU ....
KOWACCE MACE SARAUNIYA CE ....
KOWACCE MACE TAGABAN GOSHIN MAI GIDA CE.....
KOWACCE MACE TANADA BAIWA BABU BALLAGAZAR MACE SAI WACCE TASO TA MAIDA KANTA HAKAN...💃🏼💃🏼
KINA SON SANIN SIRRIKAN HAKA???
TO KI GARZAYO CIKIN GROUP DIN MU KIKARA ILIMI DUK ALAN
500 NAIR ONLY
*SA'ANNAN AKWAI BONUS NA BIRTHDAY CAKE GUDA2 DA CHEF DEEJAH BABA ZATA KOYAR*
GA ACCOUNT NUMBER NAN
GA MASU BIYA
0003434251
Sadiya Garba khalil
Jaiz bank
DOMIN NEMAN KARIN BAYANI TUNTUBI WADANNAN LAMBOBI KAMAR HAKA:-
CHEF DEEJAR BERVER
08108696754
SISIN MAMA
08107499249
MAMAN FAREEDA
07033742833
SALWISES KITCHEN
08066914136
ANEESA_DIDI
08036660796
*KIYI SECREEN SHOT KITURA SHAIDAR BIYANKI TA WANNAN NUMBER 08107499249*
[6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Kuyi hakuri na rubuta labarin Nan yanda aka bani some comment are really annoying ba wacce na tilastawa karantawa Wai an tab'a Zama a rayuwa ba jarrabawa Ni na fahimci wasu readers din suna San rayuwar soyayya Jin dadi daga farko har karshen labari Amma in reality Kuma kunsan ba Haka bane wlh Ana fuskantar kalubale da jarrabawa na wani yafi wani ne kawai and shi wanan labarin badan aji dadi ko ayi nishadi nake rubutawa ba darasin ciki nake so duk mu karu dashi idan a da kafin ka karanta kana ganin wuyan rayuwa kake Sha idan ka Karanta wanan zaka ga Ashe Kai a rahamar Allah make Ashe Kai baka ga komai bama Wanan kawai zai saka ka kusanci Allah ka Kara gode Masa da naka kaddarar yazo da matuk'ar sauki ahaka ma Naeema idan taga na wani zata ga Ashe itama a rahamar Allah take karku manta fa wani na iya Gama Shan wuyan Nan ya mutu Kuma Amma ita taga rayuwa ko nace sugani Amma Allah ya basu tsawon rayuwa dagani har ku bamu San tanadin da Allah ya musu ba namu yin Dana Allah ba daya bane na Allah shine daidai Abu daya fa danake so ku Gane Hajara a duhu take rayuwa ma a duhu take yin shi duk wani Abu da takeyi a jahilce take yinsa babu Wanda yasan Dan wuta da Dan Aljanna zaka Dade kana aikin Lada saura kiris ka Shiga Aljanna sai kayi aikin Yan wuta Haka zalika zaka iya Kare rayuwarka kana yin abun Yan wuta idan Allah yaso ka da rahama wlh sai kayi Abun Yan Aljanna sai ka tafi straight karku manta karuwa fa sabida ta saka dankwalinta ta d'ebowa Kare ruwa a rijiya aka yafe Mata zunubanta our thinking is different from that of Allah Kai dai da kake Raye kayi addua Allah ya rabaka da mumunan kaddara alot da suke kashe mazajen su Kila basu tab'a sanin Yana cikin kaddararsu ba a case din Nan mu kiyaye kalmomin da zai na fitowa daga bakinmu Kar Allah ya jarrabcemu Allah ya tsare mana imaninmu Ameen*


*Page 22*


Mik'ewa na Kara yi da Sauri nabi bayan Umma a guje Sauri take ta zubawa tana surutai Safiyya kuwa har da Dan gudunta Dan ta tadota.

Banji nauyin cikin jikina ba Haka na saka gudu na tadota na zub'e a kasa tare da rike Mata kafa Ina "Umma Dan girman Allah ki janye bakin da kika yiwa Naseer Kar tsanar da kikamin ya rufe Miki Ido kiyi Masa baki Umma nice bakya so tare dashi wlh zan debbo kayana yanzu a gabanki na tafi Tasha kiyiwa girman Allah ji janye kalamanki ki saka Masa albarka Umma ki yafe Masa Dan girman Allah wlh Zan bar rayuwar sa"


Kuka nake sosai Ina Kara kankame kafar Umma dake min wani irin kallo da nasan da ace da Hali kwaf daya zata min ta rabani da Numfashina sabida tsabar kiyayya har lokacin jikinta wani irin rawa yake tunda nake a rayuwata ban tab'a ganinta a cikin wanan halin ba

Damkar kafada ta akayi da k'arfi na daga kaina Safiyya ce da itama idonta ya kad'a yayi wani irin ja ta fara magana cikin b'acin rai "Magiyar uban me kikeyi Naeema ai murna ya Kamata kiyi kinyi Nassara wajen raba uwa da danta ba abinda bayi dake ku rabu ba Kika makale Kika nace

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment