Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawaye Naseer ya fara magana Yana Kara damke hannunsa cikin nata

"Naeema Ina kaunarki Ina Kuma San na rayyu dake har karshen rayuwata ba'a San Raina Mahaifiyata ta kasance a Haka ba wanan Ni Kuma shine jarrabawata Kamar yanda Abba Hassan yace daidai gwargwado Ina iya kokarina Dan Naga na Mata biyayya Ina nema mata shiriya a wajen Allah ban tsorata da Umma ba sai Yau Dana ganta da wuka a hannu bansan Umma tayi nisa a tsanarki ba sai Yau Naeema na Kuma rasa Mai Kika mata.

Naeema na tsinci kaina a tsaka Mai wuya gefe gaki da kika kasance Rabin rayuwata gefe ga Mahaifiyata da ta kawo Ni duniya Naeema ba rabuwar mu ne alheri ko mafita ba kamata yayi mu hada hannu ki Tayani na samu na cinye wanan jarrabawar karki gujeni a daidai lokacin danake bukatar kafadarki Sabida ki rarrasheni insha Allahu zamu Yi magana ta fahimtar juna da Umma zan Bata duk abinda takeso idan ya Kama ne na mallaka Mata duk dukiyata sabida ta barni na Rayu dake"


Tsakanin Mata da miji sai Allah cikin kankanin lokaci Naseer ya shawo Kan Naeema duk da Naeema tasan indai Hajaran data sani ne da Kamar wuya iya magana yasa ta rissina har ta ajiye makamanta.


A ranar a asibitin Suka kwana sabida Jinin da aka karawa Naeema da sauran treatment din da akewa Mai jego


Ba karamin bacci Mai dadi Naeema tayi cikin kwanciyar hankali Wanda taji inama su dawwama a asibitin Kar su koma gida.


Wajen karfe goma Sha daya na safe aka sallamesu bayan ya biya duka bills din Dan daidai da paint dasu always da zani a asibitin suka siya sabida basuje da komai na haihuwa ba.

A hanyar komawarsu gida Naseer ya sisiiyi kayan jaririrai da komai da suke bukata.

Suna Isa gidan Gaban Naseer da Naeema ya fara balain fad'uwa har Mai taxi ya sauke musu kayansu ya tafi sun kasa shiga gidan


Naseer sai da suka iso gidan ya tuna ma da ya ture Hajara data Sha gabansa Wanda hakan ko kad'an Bai Masa dadi ba dak'yar ya tattara courage ya kwashi kayan Ya bud'e gidan ya shiga Naeema na biye dashi a baya rungume da jaririyar a balain tsorace.

A hankali Naseer yayi Sallama a palon Yana kallon Hajara dake zaune ita kadai a palon sanye da doguwar rigar atamfa idonta a rufe tana karkad'a k'afa.


Kamar Mai neman gafara Haka Naseer ya zauna agaban Hajara Naeema itama ta durk'usa daga bayansa.

Naseer cikin muryar da yake tunanin idan yayi magana Hajaran zata iya yafe Masa.

"Umma Dan Allah Dan Annabi kiyi hakuri da duk abinda nayi Miki Umma ke Mahaifiyata ce inasan na Miki biyayya da har zai zama silar shigata Aljanna Umma uwa da tausayi aka santa Umma ki tausayamin na samu kwanciyar hankali da iyalina idan wani Abu Naeema tayi Miki Dan Allah Dan annabi ki yafe mata marainiyya ce Bata da kowa sai mu Umma duk abinda kikeso wlh zan Miki Dan Allah ki taimakamin na rik'e amanar Dana d'auka Umma ya zakiji yau idan su Saffiya sukayi aure uwar mijinsu na musu Haka ya zakiji Umma"?

"Kul Naseer ka gyara lafazinka ba'ayi matar da zata tab'a min yayana ba babu Wanda ya Isa ya tak'a Safiyya ko Lami idan dai Ina rayye ko da bana rayye zasu tsaya su tsaya da kafafunsu ka daina ma had'asu da Wanan mayyar Naseer bana Santa so nake ka Saketa tun kafin ka rufeni da duka akanta Naseer jiya bangajeni kayi har sai Dana Bugu da bango duk sabida ita"


Hmmm Hajara tace tana cigaba da girgiza kafarta

Naseer hakuri yayi ta Bata Yana janyo mata ayoyi Yana mata naseeha cikin siga Naeema itama cikin kukan ta ringa Bata hakuri Suka hadu sukayi tayi.


Hajara tuna yanda duk yan kungiya suka tsara Mata a jiya yasa ta daure ta saki Fuskarta ta boye fushinta

Ta bud'e idonta tana "Naji na hakura


Washe baki Naseer yayi cikin farinciki ya fara Mata godiya kamar zai Mata Sujadda.

Naeema kuwa fargaba ne ya cikata ko kad'an Bata yarda da hakura da Umma tace tayi ba indai Umma ta Ari irin wanan fuskar ta ba komai to tafi hatsari hakane yasa hankalinta ya kasa kwanciya

Naseer kuwa sai washe baki yake Yana murna ya karbi jaririyar daga hannun Naeema ya mikawa Hajara.

Shi kansa Naseer sai daya karbe Jaririyar daga hannuna da dan k'arfi Sabida yanda na kamkameta a hannuna kamar na zunduma ihu Haka naji Kamar nace Masa wlh akwai wani mugunta da Umma take had'awa Dan Allah Kar ya Bata yata Amma ba damar nayi hakan.

Addua kawai nake a zuciyata akan Allah ya Kare min yata daga sharrin Umma Naseer Bai San waccece Umma ba shiyasa yayi saurin yarda da ita.

Karba jaririyar tayi ta zura Mata Ido tana ayyana abubuwa da Dama a ranta kamar ta saka hannu ta shake jaririyar take ji kamar ta zaro wuk'arta daga kugunta ta cakawa Naeema har lahira ahaka ta rik'e jaririyar badan ranta naso ba.

Nidai kwanakin da suka biyo Baya duk a tsorace nake da Umma Dan ban ganewa shirun Nan nata ba kwana hudu kenan da haihuwar Ameena da Naseer ya Mata huduba da Sunan Mahaifiyata Wanda hakan ya faranta min sosai sosai nake Jin Ameena a Raina da Naseer yace zamu na kiranta Minal.

Naseer tun Yana dari dari da Umma ganin babu abinda ya faru ya saka ya saki jikinsa Yana Godewa Allah da kila Allah ya amsa masa adduarsa Hajara ta hakura.

Sosai ya saki bakin Aljihu aka fara shirye shiryen suna har dasu Safiyya da Lami a cikin masu tsare tsaren Sunan.

Naeema dai har lokacin hankalinta Sam bai kwanta ba Dan tana ji a jikinta akwai abinda suke San Yi Mata gashi Naseer ya Mata wahalar gani daya doso d'akin Hajara zata ce Mai yakeso Dan jarraba bazai iya kyalleta ba duk da ta haihu.

Naseer Bai tab'a kawo komai ba Dan ko kad'an baiyi sake da addua ba.




Ana gobe suna da yamma Safiyya ta shigo d'akina da kofi a hannunta

Cikin murmushi ta mik'o min tana "ga kunnu Nan Umma tace ki Sha sabida ki Kara samun ruwan no-no".

Da Sauri na karba Ina mata godiya a madadin ta fita sai ta samu waje ta zauna.

Ni Kuma ko.kadan banji zuciyata ta kwanta da Shan kunnun ba Ni nasan dole akwai wani abu a cikin kunnun Nan babu yanda makiyanka zai tashi dare daya ya dawo masoyinka.

"Ki Sha Mana"

Safiyya tace Tana Kara murmushi


Nima na mata murmushin Ina cigaba da juya kofin a hannuna bazan soma gangancin Nan ba ni nasan Umma Bata Sona ba ynda zatayi ta bani Abu na Sha.


"Ko baki yarda da umman bane shiyasa bazaki Sha ba"?


Safiyya ta Dan ce a tsawace .

Wayyo Allah na Naseer ka kawomin agaji nayita cewa a Raina.
Ganin Safiyya ta mik'e na saki kofin kunnun da gangan ya zub'e a kasa.
Ga mamakina Yana zubewa ya canja kala.

Safiyya kuwa tace Umma ta zubar wlh.

Hajara da lami dake bakin kofar da tundazu suke lekansu suka fad'o d'akin


Hajara kuwa tsananin bacin rai da bakinciiki yasa ta kasa cigaba da pretending din ta shiga d'akin ta nufi wajen Naeema dake d'auke da Minal ta hau jibgarta su Saffiya na tayata

Rik'e Minal kawai nayi Ina ihu

Umma kuwa tayi ta zagina tana tsinemin Akan babu abinda bata min ba Amma Dan taurin Kai irin nawa Ina ta ja da ita.

Kare Minal kawai nake sabida Kar dukan ya sameta.

Umma kuwa ta zage da iya karfinta tana dukana Dan gani take shine kawai hanyar da zai rage Mata abinda takeji a zuciyarta.


Basu San Naseer ya shigo d'akin ba sai ji nayi ya Kira Umma cikin wani irin murya Amma Ina Umma idonta ya rufe sai dukana take.

Ido rufe ya karasa wajen da muke ya jawo Umma da k'arfi ya wancakalar da ita ya zare belt din jeans dinsa ya hade Saffiya da Lami ya fara dukansu....
[6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 10*



Ihu Umma kawai takeyi tana Kai wa Naseer duka akan ya cika Mata yayanta Dan duka Naseer ya zage iya karfinsa yake musu ba na Wasa ba.

Ni kuwa jikina babu Inda bayamin Zugi kamar fatata zata zagwanye Dan Umma tana da fartuna hakane yasa ta ringa Jan fatata tana mitsini na Minal kuwa sai kuka take Dan ta matsu a jikina Sabida gudun Kar dukan ya sameta.

Hajara kuwa ganin idan batayi da gaske ba sai ya lahanta su Safiyya yasa tayi waje da gudu ta d'auko wuk'ar Tsafinta ta fada d'akin tare da nufar wajen Naeema da balain saurinta Dan kashe Naeema ne kawai zai saka Taji sanyi a ran ta tunda sabida ita ake dukan Mata Yaya da ta San baa Tab'a musu irin dukan da Naseer ke musu ba.

Ni kuwa Ina ganin Umma ta yo kaina da gudu nayi wani irin tambul na haye tsakiyar gadon tare da kwalawa Naseer kira.

Naseer kuwa da Sauri ya Yar da bulalan cikin zafin Nama ya ruk'o kafar Hajara da k'arfi Dan har ta hau kan gadon ita a Dole sai ta cakawa Naeema wuka.

Ni kuwa Ina ganin Naseer ya rik'e kafarta na rungume Minal a kirjina nayi waje da Sauri Dan gwara na bar gidanan na shiga duniya dana cigaba da zama da Umma dake farautar Raina jikina sai rawa yake sabida tashin hankali.

Naseer kuwa tsananin bacin rai da bangon da Hajara ta Kai shi Yana jawo kafar Hajaran ya Yar ya ya daga hannunsa Sama kamar zai Mareta.

Hajara kuwa cikin tsananin mamaki tace "Ni Mahaifiyarka Zaka mara Naseer akan matarka Ni zaka daga hannu kamar zaka Mareni bayan dukan da kayiwa yarana a gaban idona duk akan matarka"


Cikin wani irin B'acin Rai da rufewar Ido Naseer ya damko Kafadun Hajara ya fara girgizata Yana "Ki kasheni ki Huta Umma Nagaji da abinda kike min na gaji Mai nayi miki a rayuwata da Kika sakoni agaba Kika hanani sukuni da zaman lafiya da Iyalina Ni kadai ne danki kije ki samu Tijjani ki Masa Haka Mana Mai Naeema ta tare Miki Mai kikeso da ita da kike neman d'aukar ranta Mai marainiyya yarinya Nan ta Miki bakya Jin tsoron Allah ne Umma ki had'u ke da yaranki kuyita dukanta kamar Kun samu jaka karki manta fa itama Yar wani ce Inda Iyayenta sukaje Umma sai kinje kinsan hakkin mutum kuwa Umma? Umma uwa da tausayi aka santa Umma uwa Bata cutar da danta a cikin yayanki Ni kadai kike ware kike takawa yanda ranki keso Ina iya kokarina Dan Naga na Miki biyayya Ina gudun b'acin ranki Umma Mai kikeso Dani so kike sai na mutu yau bakya tunanin Makomar Wadanan Yan iskan yaran naki marasa tarbiyya Kika San hannu wa zasu fada ayi musu irin abinda kikayiwa Naeema Umma mutuwa fa Bata Sallama idan mutuwa tazo Miki akan wanan turb'ar fa"?duk abinda kikeyi fa Allah na kallonki Umma kinyi tsafin kinyi asirin babu abinda bakiyi ba Dan ki kashe Naeema Umma Allah Bai baki Nassara ba duk wanan abin bai Isa yasa ki gane Allah ne ya tsaya mata ba Umma bayan wuyan da kika Bata da cikin jikinta ta haihu da d'anyen jego a jikinta ya kwana shidda da haihuwa Umma sai ku had'u da tsinannu yaran Nan kuyi ta dukanta da jariri a hannunta Umma wane irin Zuciya ne a kirjinki Umma nagaji Umma Nagaji ki kyalleni nayi rayuwa da iyalina cikin kwanciyar hankali Umma Ina daga Miki kafa ne sabida ke Mahaifiyata ce ban Isa na canja ki ba Amma Ina nema miki Shiriya a wajen Allah"


Daga Haka Naseer ya juya a fusace ya bar Hajara Da ta daskare a tsaye sabida tsananin mamaki

Yana fita Safiyya ta mik'e cikin kuka tana "wallahi sai na Rama dukan da yamin wlh sai na Rama"


Tayi d'akinsu da gudu ta d'auko mudubin da aka basu da zasu na d'aukar fansar abinda aka musu wuk'ar Tsafin da itama take dashi ta d'auko ta nuna mudubin dashi take Naseer dake wani irin hucci hannunsa janye da Zahira da Nadeeya ya bayyana.

Ta daga Wuk'ar Sama Dan ta caka a kirjin Naseer Hajara ta shigo a guje tare da hangad'ata.

Tana "Kina da hankali kuwa yayan naki Zaki kashe"


"Ki bani wukana wlh sai na Rama dukan da yamin"

Take Hajara ta tuno Sulaiman yayanta data dage akan sai ta Rama Wanda ramawar da tayi sai data Kai shi ga rasa Ransa.

Hajara waje ta samu ta zauna tana Shirin magana taga Lami itama ta d'auko nata mudubin ta daga wuka zata caka.

Da saurin balai ta wafce mudubin Tana "ku Wai bakuda hankali ne Dan kawai ya dakeku zaku kashe shi bama zanewa ba kamar yanda ya zaneku ga abin kashewa can Baku kasheta ba sai Yayanku.


An gaya muku karamin Abu ake d'auko mudubin tsafi ko kun manta dokar ne daga yau Kar wacce ta sake irin wanan gangancin Naseer Kuma ku barni dashi Ni nasan matakin da zan dauka a kansa har Ni ya rik'ewa kafadu yake jijigani kamar 'yarsa har Ni ya d'aga hannu kamar zai Mareni har Ni zai saka agaba ya ringa fadawa maganganu matsayina na mahaifiyarsa duk sabida wanan tsinananiyar yarinya hmmm Naseer Bai San ya tsokanowa kansa tsulliyar Dodo ba Naseer Bai San ya taka wuta ba har Agaban idona ya Fifita matarsa akaina da kanensa har Naseer ya jijigani Ina mahaifiyarsa.

Taya ma zan bari ku kashe Naseer yanzu da yake ma cikin Jin dadi Taya ma zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai ga gawan Naeema a kwance a gabansa ba? Tayaya zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai fara dandanar gudansa Yana min irin biyyayar dana keso?tayaya zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai Auri Yar Shugaba ta haifo Mana Sarauniya ba wani irin dariya Hajara tayi ta mik'e da mudubin Lami a hannunta ta karasa gaban Safiyya da Fuskarta ya kumbure sabida duka ta sunkuya ta dauki mudubinta itama ta juya musu baya tana

"Naseer zai dawo da kafarsa ya sameni zan girgiza shi tamkar yanda ya girgizani yanzu zan watsa masa farinciki kamar yanda ya watsa Nawa tun lokacin Dana saka ya saki Naeema yak'i Zan kashe Naeema da hannuna ya Kuma ga gawanta a gabansa Naga yanda zaiyi bana San kuyimin hauka shiyasa na karbe mudubin ku Zan dawo muku dashi Amma ba yanzu ba ku tashi ku Dora ruwa ku gasa jikinku Anjima zamu Rama dukan a jikin Naeema Yar gwal da bayaso a tab'a"

Daga Haka ta fice daga d'akin.

Naseer kuwa Yana barin d'akin Hannun Zahira Dana Nadeeya ya rik'e ya bud'e motarsa ya saka su a ciki ya San Naeema guduwa tayi Amma sanin halin tsoron ta yasan bazata tayi nisa ba.

Ransa a balain b'ace yake Yana sake sake a Ransa da irin mahaifiyar da Allah ya bashi ya zama Dole yayi wa tufkar hanci ya gaji Haka nan.

Dayake hanya daya ce daga layinsu har titi hakane yasa ya ringa tuk'a motar a Hankali Yana Dan adduoi ko zai Samu nutsuwa har ya bar layin Bai ga Naeema ba a Haka ya cigaba da tafiya Yana ta waige waigen ko zai ganta Amma ga mamakinsa Bai ganta ba anan hankalinsa ya tashi ya fara k'ok'arin juyawa ya koma kafin ya hango ta ta yanki wani lungu tana ta zabga Sauri Minal sab'e a kafadarta.

Ko kadan mota bazai iya shiga lungun ba hakane yasa ya sauka daga motar ya rufe yabi bayanta da sauri.

Tun Kan ya ci Mata ya ringa kwalla Mata Kira amma taki juyowa sai zabga Sauri take Tana kuka.


Gudu ya saka ya Sha gabanta Yana "Wai Ina Zaki ne kike zabga Sauri"?


"Naseer wlh Tallahi bazan koma gidanan ba Dana koma gidanan gwara na samu bola na Mana shimfida nida Minal Naseer bazan koma Umma ta kasheni ba nagaji Naseer wlh Nagaji har tsawon wane lokaci Zan ringa tsallaka rijiya da baya wlh watarana zata samu nassarar kasheni kayi hakuri bazan koma ba kaje ka Kular min da Zahira da Nadeeya wlh bazan koma ba"

Kuka take sosai Kamar zata shidde ga rigarta data b'aci sabida Mararta dake murd'a Mata.

Naseer hannu ya Kai zai kamo hannunta idonsa jawur sabida b'acin Rai shi kadai yasan Mai yake ji da bashida dauriya wlh ba abinda zai saka ya yanke jiki ya Fadi

Naeema baya taja da Sauri data ga zai rik'e Mata hannu cikin ihun kuka tace ya kyalleta ita bazata koma ba.

Naseer zuwa Lokacin Ransa ya Kara b'aci.

Da Karfin tsiya ya rik'e hannunta ita kuwa ta saki ihu tana "Wlh bazan koma ba Naseer wlh bazan koma ba ka cikamin hannu na shiga duniya wlh bazan koma ba Ina koma Umma sai ta kasheni kaga fuskata kaga yanda ta yayakusheni a jikina Dan Allah ka kyalleni karka kaini gidanan ta kasheni"?

Sosai hankalin Naeema ya tashi tana kuka tana tirjewa

Naseer kuwa ya daka Mata wani irin tsawa daya saka ta nutsu lokaci guda taji tsoronsa ya shigeta lokaci guda Dan tunda take Bata tab'a ganin b'acin Ransa Haka ba

"Da wane zanji Naeema da zafin da Umma ta hadamin ko da Wanda kike shirin hadamin yanzu
ranki a hannun Allah yake Bata isa ta kasheki ba sai dai idan lokacinki yayi ki wuce mu tafi na bar su Zahira a mota.

Da Sauri nayi gaba jikina na rawa dan sosai naji tsoron irin tsawan da Naseer ya daka min.
Ahaka nayi gaba muka fita daga lungun har muka Isa mota ya budemin na shiga.

Tsoron sa yasa ban Kara iya magana ba sai kuka danake kasa kasa Zahira da Nadeeya ganin Ina kuka yasa suma Suka hau kukan.

Naseer Bai ce komai ba ya tada motar muka fara tafiya idonsa ya kad'a yayi ja jijjiyoyin kansa duk yayi rudu rudu

ji nake kamar na bud'e murfin motar na fita daga cikin motar na gudu.

Nidai nasan yau sunana gawa matsawar na taka k'afata a gidanan.

Ban dago kaina ba sai danaji ya tsayar da motar cikin fad'uwar gaba na Dago.

Bansan rik'e numfashina nayi ba sai dana ga ba gida muka koma ba a Wani katon gida muka tsaya gaban gidan na dauke da katon Massallaci.

Naseer baice min komai ba ya bud'e motar ya fita sai daya Dan kwashi mintina ya dawo ya bud'emin kofa na fito Ina kalle kallen wajen.

Ya bud'e bayan motar ya sauko dasu Zahira.

Yana rufe motar yayi gaba dasu Zahira na ringa binsa a baya Ina tunanin Ina ne Nan ya kawo mu.

A harabar Massallacin Naga ya tsaya a wajen wani daya Sha fararen Kaya gemunsa yayi kasa sosai hannunsa d'auke da carbi fuskarsa nata fitar da annuri.

Agabansa Naga ya tsugunna Nima nayi saurin tsuggunawa da Minal a jikina na fara gaishe shi.

Cikin fara'a Mallam Musbahu ya amsa Mata gaisuwar tausayin Naeema ya balain rufeshi ganin kankantar shekarunta Amma su Hajara Suka sakota a gaba.

Daga zuwan Naseer ya karanta Masa komai in brief Inda yace Masa kansa ne ya kulle shiyasa.yayi.nan dasu.

Hakane yasa Mallam Musbahu yace yayi tunani Mai kyau da basu koma gidan ba


Nidai sunkuyar da kaina nayi ban Kara dagowa ba Sabida yanda na ga kwarjinin mutumin ya cika wajen.


Sunana daya Kira yasa na Dago ya mikomin hannu na mik'a Masa Minal banma San hawaye nake ba sai dayace "Ki goge fuskarki kinji insha Allahu watarana sai Labari babu abinda baya wucewa Allah ya Kara kareki da Karewarsa Allah yana sane dake ki cigaba da Gaya masa rayuwa sai da jarrabawa ke Kuma Taki jarrabtar kenan idan kikayi hakuri insha Allahu watarana sai Labari kinji ko Allah ya Miki albarka ya rayya Miki zuriarki"


"Ameen nace hawaye nata zubomin inajin kalmar Allah ya Miki albarka dayace min daya Sanyaya min zuciya Dan rabon danaji kalmar tun iyayena na rayye sosai naji dadin adduoi dayamin.

Sallamar wata danaji a kaina yasa na Dago da kaina.

Babbar macece zatayi Sa'ar Umma ko ta girmeta sanye da Hijabi har kasa ta rusuna tana "Gani Mallam"

Shi kuwa ya nuna mu Yana ta shiga damu ciki
Ya Mik'a Mata Minal ta amsheta tana Bismillahi na mik'e na rik'e hannun su Zahira na Dan saci kallon Naseer da ya sunkuyar da kansa ya kurawa waje daya Ido wani irin tausayinsa ne ya rufeni ahaka nayita kallonsa ko zan samu ya Dago Amma har muka bar harabar Massallacin Bai Dago ba.


A wani katon daki ta kaimu Ni kuwa nafara k'ok'arin tsugunnawa na gaisheta tayi saurin taroni ta zaunar Dani akan gadon d'akin.

Ta kwantar da Minal a gefena ta zaunar dasu Zahira a tsakiyar carpet Naga ta jawo Kular abincin ta zuba musu.

Ni kuwa sai godiya nake Mata Ina Jin wani irin niima dake ratsani iskar ma danake shak'a daban yake Dana gidana.

Take na fara Jin wani bacci bacci.

Fita tayi daga d'akin bayan 'yan mintina ta dawo da ruwan zafi a bokiti ta shige bandaki ta dawo ta d'auko min zani tace na daura na shiga wanka.

Kamar kuwa ta San Ina bukatar wankan Dan ban samu nayi ba sabida tsoron barin Minal ita kadai a daki.

Da Sauri na mik'e Ina Mata godiya na karbi zanin na shiga band'akin Dan Ina Jin kunyar cire Kaya a gabanta ko Ina Naseer ya samo mutane masu karamci Haka oho yasan duk tsawon lokacin Nan akwai.mutane irin Haka shine Bai kawoni ba ko wanke wanke na ringa musu indai zasu rik'eni a wajensu.


Sosai na gasa kaina da ruwan zafi inajin dadin jikina yaushe rabon dana jini a sake haka har na manta inama Naseer ya barni a gidanan da yayana inama mutanen Nan su zama iyayena su rik'eni a wajensu da naji dadi.


Duk Inda Umma ta yakusheni na gaggasa Dan kamar ba yakushi ba sabida zafin danake ji gashi jikina yayi rudu rudu abinka da fara ahaka na fito da Daurin kirji.

Ina fitowa tana Gama yiwa Minal wanka

Su Zahira ma har an musu wanka an canza musu kayan jikinsu an kwantar dasu sosai naji dadin yanda matar tayi Mana da alama itace matar Mallamin.


A Gefen gadon ma an ajiyemin kayan da Zan saka da auduga.

Godiya na ringa Mata sosai har sai data nuna b'acin ranta.

Ina Gama saka Kaya ta turomin flask din tuwon Massara da miyar yauki yaji namomi yaushe rabon Dana samu irin wanan abincin gefe Kuma ga shayi Mai zafi Tana Gama shirya Minal ta ajiyeta a gefena ta fita sabida na sake naci abinci.

Banyi falako ba naci na koshi Maganin data bani na ciwon jiki na Sha Ina kwanciya bacci Mai nauyin gaske yayi awon gaba dani


Naseer kuwa Yana ganin Su Naeema sun shige gida ya fara kukan bakin ciki Dan sosai yaji kirjinsa ya cushe idan ba kukan yayi ba bazai ji saukin abinda yake ji ba.

Mallam Musbahu kuwa Bai Hana shi ba sai daya Gama Dan kansa ya fara bashi baki Yana Masa nasiha da yarda da kaddara da hakuri.

Naseer dagowa yayi Yana "Mallam Nagaji inaso na gudu da iyalina ko zan samu kwanciyar hankali hakane yasa Nazo wajenka ka bani shawara wani gari Zan koma"


Mallam Musbahu murmushi yayi Yana "ko da baka zo da maganar ba shawarar da nake taso na baka kenan ka koma Garin Kano da zama batare Mahaifiyarka ta sani ba Kar wani Abu ya Kara maidaka gidanan Sabida kaima kasan bazasu barka Haka ba Haka ma matarka.

Akwai kanina a garin Kano Yana zaune a goron dutse Zan baka address dinsa kaje ka same shi ya nema maka gidan haya ka fara Kama muku kafin komai ya lafa"


"Mallam idan ma na samu gidan siyarwa Zan siya sabida Ina da kudin siyan akwai gidana a Jos Dana siyar wanan Kuma Zan barwa mahaifiyata ta zauna da yayanta Zan Kuma aika Mata sakon kudi idan ta hucce an kwana biyu Zan dawo"


Haka kuwa akayi Washegari da sassafe Naseer ya d'au hanyar Kano cikin Sati d'aya ya samu kato gida ya siya ya zuba komai dazasu bukata a gidan a unguwarsu Kanin Mallam Musbahu ya samu gidan shima kanin Mallam Musbahu mallami ne Mai mutunci da dattako Mallam Haruna.

Sai da Naseer ya Gama komai ya koma Calaba Dan ya d'auko su Naeema.


Naeema

A bakin Matar Mallam da nake cewa mama naji Ashe Naseer tafiya yayi Haka kawai naji babu

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment