Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dadi da Naseer bai nemeni ballantana ya gayamin bansani ba ko fushi yake Dani sabida Dan tirjewar dana Masa Akan bazan koma gidan Umma ba.


Sosai naji dadin sati dayan danayi a gidan Mama tunanin halin da Naseer yake ciki ne kawai ya ragemin Jin dadi.

Har wani Dan kib'ar kwanciyar hankali nayi yayana Suma sun samu gida sai watayarsu suke suna Wasa

sosai nake adduar Allah yasa mu dawwama a wanan gidan Dan babu yanda Zan sake komawa gidan Umma na Sha yunk'urin Sanar da Mama halin da nake ciki Koda shawara ne ta bani sai naji na k'asa Mata maganar sai Naga kamar ban kyautawa Naseer ba idan na fadawa wani halin mahaifiyarsa.

Da magriba Ina zaune a daki Ina shayar da Minal naji sallamar Naseer a bakin kofa da Sauri na dago na zuba Masa Ido.

Su Zahira kuwa suka tafi da gudu Suka rungumeshi.

Sosai Naga ya rame yayi baki sai tausayinsa ya rufeni.

Sai daya Gama dad'agasu

Ya nufo wajen da muke ya sunkuya ya d'auki Minal ya Dan saci kallona sai naji duk ba dadi kamar kunyata yake ji yabi ya canza kamar bashi ba.

Gaishe shi nayi ya amsa ya zauna Akan side drawer jikin gadon

Ni kuwa na mik'e na fita Waje Dan na d'auko Masa ruwa Ina fita naci Karo da Mama da farantin ruwa har da lemon kwalba da kofi.


Godiya na mata na koma ciki na zuba Masa ruwan ya karba ya Sha Ni kuwa nace Masa ya hanya yace Alhamdulillah.


Daga Nan yacemin "Gobe ku shirya da wuri zamu dauki hanyar kano.


Kamar na tashi na dakka tsalle Haka naji sabida tsananin murna Amma tuna ko da Umma zamu koma Kano yasa nace "Kano zamu koma da zama su Umma fa"?


Ambatar su Umma da nayi yasa ya mik'e da Sauri

Yana "anan zasu zauna iya mu zamu tafi gwara mu nisanceta kafin Allah ya warware Mana komai"


"Allah yasa Hakan shi yafi alheri"


Ameen kawai yace ya Ajiye Minal Yana "Bari naje wajen Mallam bamu gaisa bama nashigo.

Sosai naji kamar anmin albishir da gidan Aljanna barin garin Calaba da zamuyi mu nisanci Umma Wanda hakan na nufin Zan samu kwanciyar hankali babu Mai kawo min farmaki.

Wajen karfe Tara na dare Mallam ya aika a kirani Ina zuwa Naga Naseer a gefensa hadamu yayi ya Mana nasiha tare da bawa Musbahu Adduoi Mai yawa Inda Nima ya bani gajeru da yasan Zan iya haddacewa idan na nace ya bamu shawara da duk da zamu bar garin Nan Kar muyi sake da addua mu zage damtse mu cigaba Dan ko shi daya taimakemu sai da suka so kawo mishi Hari Inda basu San shi ya Riga da yafi karfinsu ba daya shiga bayi aka zo Masa a siffar mage shi kuwa sai daya tabbatar da ya makawa Magen Abu a gadon Baya ga mamakinsa Yana ihu yaji muryar mace.


Shi ma yasan da zamanmu a gidan za a Kai ga Haka shiyasa d'akin da aka saukeni ya zagaye shi da Addu'oi da tuni an tab'ani ko an tab'a yayana.


Sosai naji Kuma hankalina ya tashi da maganar Mallam Musbahu Inda na fara kuka shi kuwa ya hau kwantar min da hankali.

A ranar a tsorace na kwana

Washegari da asuba muka d'au hanya......
[6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 11*


A gajiye muka iso garin Kano da tunda muka iso naji wani sakayau Dani iskar ma garin ya bambanta Dana garin da muka baro.

Sosai nayi mamaki ganin katon gidan da Naseer ya siya mana Dan gidan bene ne kasan Kuma shaguna ne da alama sabone fil duk da jikina ba kwari Haka na zage muka gyara gidan washegari nida Naseer.

Gidan sosai yayi kyau Dan d'akinsu Zahira ma yafi k'awatuwa duk da ba abinda muka d'auko a wancan gidan Nan ma komai akwai Dan har yafi na gidanmu dake Calabar

da yamma mak'ota sukayi ta shigo mana naji dadin shigowarsu sosai Dan da alama suna da mutunci Dan har Dan Tayani sauran aikace aikacen gidan sukayi.

Naseer Sam bai wani zauna ba tunda muka dawo ya Kuma canjamin bansan dalili ba Haka kawai naji ba dadin canzamin daya yi hakane yasa na shirya Masa magana idan ya dawo.

Wajen karfe Takwas ya dawo Yana dawowa na bashi abincinsa yaci.

Yana gama ci naga ya koma tsakiyar palon da wani dogon takarda Yana ta rubutu.

Su Zahira sun Dade da bacci Minal kuwa Tana goye a bayana.

Nima tsakiyar palon naje na zauna Ina kallon rubutun da yakeyi da nakeso ya Gama muyi magana

D'agowa yayi yace min "Lafiya kuwa ko akwai wani matsala ne"?


"Aaa Babu wani matsala nadai ga ka canjamin ne tun ranar da abinan ya faru shine nace ko Dan na d'an tirje ranan ne shiyasa kake fushi Dani idan ma shi din ne Dan Allah kayi hakuri.

Ajiye biron yayi akan takarda ya murza yatsun hannunsa sai daya d'auki tsawon lokaci ya fara magana "Ba daga ke bane Naeema abinda ke damuna daban tun ranar da muka Samu sab'ani da Umma nakejin ba dadi Umma Mahaifiyata ce ban Isa na canza ta ba nasan daraja mahaifiya shiyasa nake ganin Kamar ban kyauta Mata ba a matsayinta na wacce ta raini cikina har ta haifeni na fada Mata maganganun da basu Kamata ba duk da na baro garin sai nake jin ba dadi sai nake jina kamar a d'ad'aure Kamar Idan na Bata hakuri ta hakura sai nafi samun sukuni bansan mai kika Mata ta tsaneki ba bansan Mai yasa Umma ta Dora Miki Karan tsana ba abinda ke damuna kenan ba wani Abu ba.

Da Zan samu Umma ta kaunaceki ta rungume ki tamkar 'yarta Naeema da na fi kowa Jin dadi duk Inda na Kai ga na nusar da Umma ta kasa ganewa yau da ace nasan wani dangin Umma Wanda nasan suna gaba da ita da na Kai kararta wajensu sun mata naseeha k'ila taji maganarsu.


Sosai nake ganin ciwon da Naseer yake ji a zuciyarsa da koma waye Dole ya shiga cikin damuwa.

Cikin kwantar da murya na fara kwantar Masa da hankali Ina "Addua zamu cigaba da yi Naseer insha Allahu Umma zata Soni za kuma ta kaunaceni duk da munyi nisa ka cigaba da kyautata Mata kana Mata aike idan an kwana biyu sai kaje da kanka"


"Hmm abin da Kamar wuya Naeema Amma tunda Kika ce Allah ba abinda baya yuwa ga form nan na karbo Miki na islamiyya Dana Boko kina yin arbain Zaki fara zuwa insha Allah"


Kamar na tashi nayita rawa Haka naji da Naseer yace min Zan fara zuwa makarantar godiya nayita Masa shi kuwa ya jawo takarda ya cigaba da rubutu a ciki.


Bansan Haka zaman aure yake da dadi ba sai da muka dawo kano da zama bansan Haka ma'auratan da basu had'u da jarrabawa irin tawa suke cikin kwanciyar hankali ba sai da muka dawo kano bansan Haka mu'ammalla da mak'otan arziki yake da dadi ba sai da muka dawo kano Wai nice yanzu Zan kwanta batare da fargabar komai ba Wai nice yanzu Zan shiga kitchen na dafa Mana abinda ranmu keso muci mu koshi batare da fargabar komai ba.

Babu abinda Naseer Bai wadata mu dashi ba dan Zan iya cewa a wanan lokacin za'a iya saka Naseer a sahun masu kudin unguwar.


Tsabar matsuwar da nayi da na fara zuwa makaranta ko arbain din banyi ba na fara zuwa Dan ba zanyi gangancin Wasa da Wanan damar da Allah ya bani ba inaso na nemi ilimi da Zan kusanci mahallacina sosai na cigaba da Kai Masa kukana.

Cikin ikon Allah kuwa da fara zuwana makaranta na ringa ganewa da wuri sabida na saka San koya Raina.

Su Zahira ma tuni Naseer ya nema musu makaranta suka fara zuwa zan iya cewa banida matsalar komai sai karatuna Dana saka a gaba da rainon Minal danake.

Tsakanina da Naseer kuwa soyayya ce Mai tsafta da girmama juna duk da munyi nesa da Umma Hakan Bai saka mun saki jiki ba addua muka cigaba dayi Dan nima na koyi tashin dare kamar yanda Naseer Naga ya zame Masa jiki.

Sosai dawowar mu Kano ya zame Mana alheri Dan bayan sanin kaina Dana farayi ta hanyar cud'anya da mutane na fara Dan samun wayewa da bud'ewar ido ta hanyar muamalla da mutane Dan daga zuwa na makaranta na had'u da wata Aisha da ake cewa mmn Mannir yanda banida ilimin komai hakane ya kasance gareta hakane yasa tamu tazo d'aya da ita abin mamaki har na Kan Dan nuna Mata abinda bata gane ba nacewar da nayi da San koyon ilimin addini yasa nake ganewa Nan da Nan daga kasa aka fara Mana wato fatiha aka ringa had'a Mana da huruf Wanda ya taimakamin sosai wajen gane bak'i.


Mmn Mannir gida hud'u ne a tsakaninmu tana da mutunci sosai duk da ta girme min nesa ba kusa ba Amma Haka muke Dan kawancenmu da ita takan Dan fadamin abinda ya shafi rayuwar Aurenta Ni kuwa sai dai naji ta kawai bana iya fadan abinda ya shafeni Dan Ni Dama can Ina da zurfin ciki balle rayuwar gidan Aurena a ganina ba abinda Zan fito na ringa labari akansa bane.

Naseer kuwa shagunan dake kasan gidanmu duk sai daya cika su da kayan siyarwa Wanda ya samu wasu suka rik'e Masa shagon a cikin shagunan akwai Inda Nama da kifi kawai ake siyarwa layin namu dayake ba masu siyar da nama da kifi sosai Ake cinikin Nama da kifi inda cikin kankanin lokaci Nan da Nan zai Kare tun Naseer na yanka raguna biyu ya koma Yana yanka Dan Sa

Daya shagon nasa Kuma lemuna yake siyarwa akan sari masu kananan shaguna gurinsa suke zuwa siya.

Daya shagon Kuma kayan awo ne Kama daga su shinkafa gero dawa wake shima buhu buhu yake siyarwa dawowarmu Kano da wata shidda Naseer yayi wani irin kudi Dan Motocin hawansa sai da suka Kai uku.

Har ya Kara siyan wani katon fili a layinmu .

Sosai ya daina samun lokacin kansa tafiye tafiyen da yake Yi Bai fasa ba yakan yi kwana uku Haka ko biyar kafin ya dawo.


Ni kuwa ba wani damuwa nayi ba sabida karatuna Dana saka a gaba.

Har Lokacin ban saki jikina ba Ina Kan addua Naseer da Bai fiye zama ne bansani ba ko ya rik'e addua kamar yanda Mallam Musbahu ya bashi shawara.

Sosai nake addua Allah yasa na samu hutu kafin na Kara samun wani cikin Dan a lokacin ba wani sanin tsarin iyali nayi ba.

Hutu da Jin dadi sosai ya nuna a jikin Ni da yayana Dan har mota Naseer ya Ajiye da sunana akan duk Inda zani wani yaro matuki dake kasan layinmu ya ringa Kai mu Yana dawo damu duk wata zai na biyansa kudaden cinikin shagon sa kuwa Ni ake kawowa duk ranar Jumma'a wani yaronsa ke had'a lissafin kudin ya Kai banki.

Naseer kuwa bud'in dayake samu sosai yasa yake wa Hajara Aiken kudi masu kauri har wasika yake rubuta mata duk da yasan ba ilimi ne da ita ba yasan zata samu Mai karanta Mata wasika ne na neman yafiya da ban hakuri gareta akan tafiyar da yayi batare da saninta ba zai dawo idan ta huce Yana rokonta ta cigaba da saka Masa albarka a rayuwarsa.


B'angaren su Hajara kuwa a ranar da Naseer da Naeema Suka bar gidan ta nufi Kungiya dasu Safiyya da sai data zauna ta gasa musu jikinsu da ruwan zafi sosai zuciyarta ke tafasa da irin dukan da Naseer ya musu Inda take Jin da yau wani ne yayiwa su Safiyya Haka ko duk karfinta zai Kare sai ta aika shi barzahu.

Da isarsu kuwa ta korawa shugabarsu komai.

Take duk suka hau ce Mata Kar ta yarda ta d'au mummunan mataki akan Naseer da Naeema taya zaayi Naseer yayiwa su Safiyya Haka kawai Sabida sun daki Naeema ya zama Dole ko Yaya ne a koyawa Naseer hankali a Kuma dau mummunan mataki akan Naeema tunda a lokacin Bata da tsarki duk abinda aikin da zasuyi akanta zai Kamata Nan da Nan.

Take shugabarsu ta d'auko kwaryar tsafinta dake d'auke da wani irin ruwa tayi surutai tana shafawa Naseer da Naeema Suka bayyana lokacin Naseer na gaban Mallam Musbahu Naeema Kuma tana d'akin matar Mallam Musbahu.

Cikin wani irin murya Shugabarsu tace ta zama Dole su hukunta Naseer tunda ya tab'a musu Yan kungiya har ya fitar musu da jini wato Safiyya da lami


Hajara na Shirin magana Dan tace da a hukunta Naseer gwara a hukunta Naeema

Wani irin kallo Shugabarsu ta Mata ta ja bakinta tayi shiru ita kuwa shugabarsu ta daga wani irin bulala dake d'auke da allurai tana Shirin makawa Kwaryar da hoton Naseer ke bayyane har lokacin.

Taga Naseer ya bace daga ruwan mamaki ne ya Kamata ta Kara surutan tsafi Amma me hoton Naseer ko na Naeema Bai Kara bayyana ba Dan a lokacin Naseer ya shiga Massallaci Naeema kuwa Tana d'akin Mama dake d'auke da manyan adduoi na tsari a kowane kasurwar d'akin.

Duk yanda sukayi Dan su Kara bayyana abin gagara yayi a karshe akan Dole Suka bawa Hajara wani irin tsafi Akan idan taje gida ta zuba a bakin kofa Naeema zata haukace Naseer Kuma sai yanda tayi dashi.

Suna komawa gida ta saka bakaken Kayanta


Ta zauna jiran dawowar Naseer da Naeema sai dai shiru basu dawo ba Wasa Wasa har akayi kwana uku babu su babu labarinsu ahaka suka Kara komawa kungiya Inda sai da suka buga sosai suka gano Inda Naeema take Da Naseer har tafiyar da Naseer yayi ta mudubi Suka gani.

Anan Suka yi Shirin zuwa gidan Mallam Musbahu Dan su Dan tab'a shi sanin Kuma babu Inda zasu same shi batare da su sun fuskanci wani matsala ba sai a bandaki hakane yasa Suka aiki Lami akan taje gidan idan ta samu Nassara akan Mallam Musbahu ta tab'a shi idan Kuma Naeema ce ta kasheta da wuk'ar Tsafi.

Lami kuwa jiki na rawa ta zama katon bakin mage ta shiga ta rufin gidan Mallam Musbahu ta tsaya daga wajen window bandaki.

Wajen Karfe dayan dare Mallam Musbahu yaga komai a mafarki Dan Allah ya Masa wanan baiwar idan Abu zai same shi zai gani a mafarki.


Wajen daya da rabi ya farka Sakamakon fitsarin daya matse shi har zai shiga band'akin ya tuna mafarkin da yayi hakane yasa ya dawo Baya ya d'auki wani katon Sandan daya gani Yana shiga band'akin da Addu'a shiga bandaki yayi Ido biyu da Bakin Mage Yi yayi kamar Bai ga Magen ba ya juya bayansa aikuwa take mage ta fara shirin dirar Masa ta baya ya juya cikin zafin Nama ya maka Masa sand'a kafin magen ya dira ta waje ya Kara mak'a Masa a gadon Baya take yaji ihun mace.

Ya fito daga band'akin da Sauri bakinsa d'auke da Addu'a ya zagaya ta bayan gidan Amma Bai ga komai ba baccin da bai koma ba kenan.

Ya turare gidan da hayakin daya San basu Isa su Kara dawowa ba

Ko kusa da Gidan bazasu iya zuwa ba.

Lami kuwa sosai Mallam Musbahu ya sameta a baya a lokacin da ta koma siffar ta ta koma kungiya Inda Sam Bata iya mik'ewa tsaye.

Sosai hankalinsu ya tashi Yan kungiya duk dabarun da sukayi Dan suga Lami ta warke Amma abin yaci tura abinda ya d'auke hankalin Hajara kenan daga Kan Naseer da Naeema har tsawon wata hud'u tana jinyar gadon bayan lami da take Shan alwashin in ta warke babu abinda zai Hana ta kashe Mallam Musbahu.


Wata biyar da barinsu Naeema Calabar taje kungiya aka bincika Mata Inda su Naseer suke da irin kudin da yayi da irin hutun da Naeema ta samu.

Anan ma sukayi ta k'ok'arin wajen kashe Naeema ta hanyar tsafi Amma abin ya gaggara Dan yanzu Naeema ta Dan samu ilimi Kuma tana adduoi Dan saken da Naseer yayi da adduoi sabida neman kudin da yake ba dare ba Rana yasa Suka Dan karkato da zuciyar Naseer wajen Hajaran ya hau Mata aike Yana Mata wasika.

Anan shugabarsu ta Bata shawarwarin hanyoyin da zata bi wajen mallake danta ta Kuma kau da Naeema ta bar duniya na har abada sosai take ganin sabon salon da suka d'auko zai bille dasu su kau da Naeema cikin sauki wanan kenan.

A cikin kwanakin Nan Haka kawai na tsiri mafarki da Umma a mumunan yanayi tana ta Bina zata kasheni.


Ganin inata mafarkin a jejjere yasa na sake dagewa da Addu'a dayake Ina da kudi kuma muna cikin wadata sai na tsiri Sadakan dafaffen abinci duk ranar jumaa tunda Sadaka maganin masifa ce.

Kamar zanyiwa Naseer zancen mafarkin da nake yawan yi da Umma sai Kuma na fasa Sabida nasan zaiji ba dadi zai ga ma kamar zargin mahaifiyarsa nake.

Zuwa yanzu Naga ya danyi sake da Addu'oi ba kamar da ba Dan yanzu Inya dawo ya Dan Yi nafilfili takardarsa yake daukowa ya hau lissafi da rubuce rubuce.


Ahaka wani zubin bacci ke daukarsa ni Kuma sai na dauke takarda da biron na ajiye idan na Gama adduoi na sai na tofa Masa adduar kwanciyar bacci da yarana.

Dan wata shidda danayi Ina zuwa makaranta na San adduoi sosai na Kuma San daga fatiha zuwa izu uku.

Watan Minal Tara na samu wani cikin a ranar Dana San ciki ne Dani a ranar sukuku na wuni Dan banji dadin samun cikin yanzu ba naso ko shekara biyu tayi kafin na samu wani cikin.

Zuwa lokacin nasan nayi nisa a makaranta.

Sai dai ya zanyi kana naka Allah na nashi.

A Daren ranar na shirya gayawa Naseer cikin danake d'auke dashi

A dakinsa na same shi ya janyo akwati Yana ta had'a Kaya.

Na dauka wani tafiyar ne ya Kara taso Masa kamar yanda ya Saba shiyasa ban Masa magana na na je kusa dashi Ina Taya shi had'a kayan.

Shi kuwa ya dago yacemin.

"Gobe idan Allah ya kaimu zanje Calabar dazu an turomin wasika Umma Bata Jin dadi an kwantar da ita a asibiti Dan Haka gobe asubanci zanyi na tafi.

Bansan rigarsa ta sub'uce daga hannuna ba gabana ya yanke ya Fadi take jikina ya hau rawa.

Hakane yasa yace min Lafiya.

Ni kuwa cikin dauriya nace Masa ba komai Allah ya sauwake ya Bata lafiya.

Bai Kara cemin komai ba ya gama karasa hada kayan ya shige bandaki

Ni kuwa na fice daga d'akin da Sauri na koma dakina hankalina a balain tashe Allah yasa ba wani Abun ke Shirin samuna ba sabida yawan mafarkin danake da Umma bansan Mai yasa hankalina ya tashi da Naseer yace zaije Calabar ba Ina tsoron Umma Ina tsoron abinda zuwan Naseer zai haifar.

A ranar ko runtsawa banyi ba Sabida yanda na dage da Addu'a.

Washegari da assusuba Naseer ya d'au hanyar Calabar ni kuwa ya barni cikin Zullumi da tashin hankali ya zanyi toh mahaifiyarsa ce ban Isa na rabasu ba Allah ya dubeni da idon rahama ya kareni da karewarsa nidai da da yanzu ba daya bane bazan Kara yarda Umma ta bani wahala kamar yanda ta bani a baya ba.

A ranar da Naseer ya cika kwana uku da tafiyarsa Calabar da yamma na dawo daga islamiyya Ina girki a kitchen su Zahira Kuma suna Palo naji Ana kwankwasa kofa.

Da Sauri na fito daga kitchen ganin yanda ake kwankwasawa da k'arfi hannunsu Zahira Bai Kai handle din ba ballantana su bud'e.

Ina bud'ewa nayi tozali da Umma da Safiyya ga manyan jakankuna a gaba bayansu Kuma Naseer ne ya d'auko musu sauran kayansu daga cikin taxi.

Murmushi Nan da Umma kemin dake tsinkemin zuciya shi ta sakar min Ni kuwa jikina ya hau b'ari na Kuma kasa basu hanya su shiga sabida mutuwar tsayen da nayi Ni nasan da zaa auna jinina ba karamin Hawa yayi ba bugun zuciyata kuwa tun daga nesa zaka iya jiyowa.

Maganar Naseer ne ya dawo Dani hankalina.

"Ki bawa su Umma hanya su wuce Mana bakida hankali ne Zaki tare musu hanya"

Naseer yacemin a tsawace Ni kuwa na matsa da Sauri na zub'e a kasa Ina musu Sannu da zuwa Naseer kuwa hannunsu Jaye da akwati ya shige Safiyya ta bi bayansa tana kalle kalle

Umma kuwa muka tsaya kallon kallo har lokacin Fuskarta d'auke da Wanan murmushin sai data zo dab Dani tace "kin Kara d'aukar wani cikin kenan"..........
[6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 12*


Cikin tsoro da mamaki na kalli cikina da baifi wata biyu ba cikina a kwance babu alamar ma cikina ya taso ballantana ince tsinin cikina ta gani.

Da Sauri na Kara d'agowa na kalleta ta sakarmin murmushi tana "ke Kuma aikinki kenan ko Naeema kin samu Naseer Zaki cika Masa gida da 'ya'ya toh yayi kyau"


Daga Haka ta wuceni tana karewa palon kallo.

Jikina Banda rawa bbu abinda yakeyi ahaka na rufe k'ofar na juya na nufi palon Ina zufa.

A daidai lokacin da Umma ta zauna a kujera ta kalli su Zahira da shigowarsu yasa Suka mik'e tsaye suna zazzare Ido.

Hannu ta mik'a musu tana "Kuna ganina bazaku zo wajena ba ko har Kun manta Dani ne?

Tace tana kallon Naseer


Zahira da Nadeeya da Sauri suka yo wajena suka fara k'ok'arin b'uya a bayana.

Naseer kuwa ya daka musu tsawa Yana "bazaku je ku gaida Umma ba"?

Da Sauri suka nufi tsakiyar palon Suka tsaya nesa da ita Suka hau gaisheta


Ita kuwa ta amsa tana murmushi nima na karasa tsakiyar palon na zub'e a kasa Ina gaisheta cikin rawar murya.

Wani irin kallo tamin ta amsa da murmushi nan nata da babu alheri.

Kafin na mik'e Naseer har ya kawo musu ruwan Sanyi da lemo jikinsa sai rawa yake Yana ajiyewa ya koma ya juyo kazar da nake soyawa gabadaya a faranti yazo ya Ajiye musu.

Nima mik'ewa nayi nabi bayansa Dan na zubo musu abincin tunda na Riga da na Gama dama kwashewa nakeso nayi.

Kafin ma na isa kitchen din har ya Kara fitowa da wani farantin Mai dauke da soyayayyen kifi da nama dan Dama Haka nake soyawa da yawa na zuba a fridge kawai idan zanyi girki sai na dib'a da yawa ake kawo Mana daga shagonsa.

Mamakine ya Dan kamani ganin bama d'ebowa yayi ba juyowa yayi gabad'aya.

Bance masa komai ba na shiga kitchen.

Na jawo kula na zuba musu shinkafa da miyar.


Na koma palon na ajiye a tsakiyar palon.

Naseer kuwa na zaune daga gefensu a kasa ya tankwashe kafa sai murmushi yake Yana su fara cin abincin Mana.


Umma kuwa farantin da ya jere Mata a gabanta kawai take kallo tana gyada Kai Safiyya kuwa tuni ta sauko ta fara yagar kaza.


Ina Shirin juyawa na zubowa su Zahira abinci naji Umma ta fara Jan majina kamar Mai kuka tana "Naseer yanzu Haka kuke Jin dadi kuka gudu kuka barmu a can abinda zamu sakawa cikinmu ma na neman gaggararmu kasan kuwa mun Sha kwana da yunwa akan karamin kuskure Naseer ka d'auki matarka ka gudu ka barni bayan kasan Kaine babban Dana babu Mai iya d'aukar dawainiyarmu idan ba Kai ba.

A garin nemawa Lami kudin magani na gurd'e a k'afata Haba Naseer abinda Kayi baka kyauta ba karka manta Ni Mahaifiyarka ce Bai Kamata ka fifita matarka a kaina ba a baya nasan bana San Naeema Sabida shaidan daya sakoni a gaba Amma yanzu na gane Dan Haka kuyi hakuri da Kai da Naeema bazan sake ba"


"Haba Umma Mai yasa kike bamu hakuri ke ya Kamata mu bawa hakuri mun Miki ba daidai ba Dan Allah kiyi hakuri da matakin da muka dauka bazamu sake ba insha Allahu fatana kawai ki cigaba da saka Mana albarka Naeema Kuma zata kasance Mai biyayya a gareki insha Allahu"


Naseer yace Ni Kuma na koma na zauna hankalina a balain tashe shekara biyar ba Wasa bane zuwa yanzu na gama sanin wacece Umma ciki da Bai gwara Umma ta fito ta nuna min kiyayyarta data fito min da Wanan fuskar tata daya fi kowane hatsari Ni nasan Umma ba karamin shiri tayi ba kafin tazo Ni nasan idan ban dage ba wanan Karin sai taci Nassara akaina bansan Mai yasa Naseer

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment