Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zama da ita Amma da sharadin wlh bazai bar garin Nan ba sai ya auri yar kawata Hindatu idan kuwa ya dage bazai Aureta ba wlh nima sai ya rabu da Naeema"


Naseer jin bazata raba shi da Naeema ba yasa yayi saurin cewa ya amince duk da har a Ransa baya San Karin auren


A takaice Mallam Musbahu sai daya Kara yiwa Hajara wa'azi Wanda Hajaran kuwa take Allah Allah ya tafi ganin yak'i tafiya yasa ta tashi tayi shigewarta ciki.


Mallam Musbahu kuwa fitowa yayi Naseer ya biyoshi a baya Mallam Musbahu ya kalleshi Yana "Naseer badan nasan addua na iya canja komai ba da nace maka ka hakura da Naeema ka samu sukuni a rayuwarka itama ta samu kwanciyar hankali akwai wani babban Al amari danake hangowa a gaba daga Kai har Naeema bazai muku dadi ba wani Kuma babin ne zai bud'e muku Amma fa bansan ko menene ba Amma ka dage da Addu'a Dan babu Abinda addua baya canzawa Zama Kuma Bai ganka ba addua ka dage akai fiye da na d'a mahaifiyarka tayi nisa da Bata Jin Kira iya kalmomi nasan bazai saka tayi laushi ba tunda har tace ta yarda ka cigaba da zama da Naeeema Amma ka sake aure akwai wani Abu a ranta Allah shi ya barwa kansa sani.


Naseer Naeema Amana ce a gareka idan kaga zata cutu zamanka da ita akwai cutarwa bi maana mahaifiyarka zata cutar da ita gwara ka Sawwake Mata Dan duk Inda ka Kai ga Santa watarana mutuwa sai ta rabaku ko ka rigata tafiya ko ta Riga ka Kuna cikin addua ta insha Allahu Allah ya shiryi mahaifiyarka yasa ta Gane daidai ka daina damuwa da Naeema Bata dangi idan dai kaga Abubuwa sun ci tura ka Sawwake Mata Ni Zan zame mata uba insha Allahu"

"Yaushe zaka koma"?

D'agowa Naseer yayi jikinsa a sanyaye da maganar da Mallam Musbahu ya masa yace

"Nima bansan ranar da xan koma ba kafin na koma Zan zo Dan naji tana sai na auri wacce zata hadani da ita Zan bar garin Nan"


Yauwa kazo akwai sakon da Zan baka ka kaiwa Naeema insha Allahu ba Tsafi ba koma me zasu Mata insha Allahu bazai yi tasiri akanta ba

Godiya Naseer ya hau mishi.
Sai daya rakashi har bakin titi ya juyo ya dawo gida.

Inda yana dawowa Hajara ta hau Masa masifa akan me zai d'auko mata Mallam Musbahu ta Inda take shiga Bata Nan take fita ba Bai ce Mata komai ba Dan shi dai lallab'ata yake.


D'akinsa na da ya shiga Inda ya tarar da komai nasa na Nan Kamar ma baa shiga d'akin sabida lodin littattafan addini dake cikin d'akin.

Da kansa ya samo tsintsiya ya share d'akin ya gyara yayi wanka ya fito Dan ya tafi massallaci da zai Samu da ya juya gobe Amma yasan Bai Isa ba yanzu Hajara zata Masa fassara.

Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi Sallar ishai ya take cikinsa a waje ya shigo gidan wajen karfe Tara na dare.

A Palo ya tarar da Hajara da Safiyya da Lami da bayanta yayi kamar Mai Kusumbi

Sai wata da kallo daya ya Mata ya dauke idonsa Dan Haka kawai yaji jininsa Bai d'auketa ba Sanye take da Bakin Riga Mai ratsin fari.

Su Safiyya kawai ya amsa gaisuwar su yayi wa Hajara barka da hutawa ya sa.kansa xai shiga d'akinsa Hajara kuwa ta dawo dashi tana ya zo ya zauna


A kujerar da babu kowa ya zauna ya had'e Rai sabida yanda bakuwar ta zuro Masa Ido kamar Mayya

"Wannan itace matar ka Hindatu sai ka fara Zama da ita anan kafin ka koma can garin wurin wancan mayyar matar taka Dan Dole sai naga Kun fahimci juna kafin ku bar garin Nan kasan Kai yanzu idonka a rufe yake babu wacce kake gani da gashi idan ba wanan Aljanar ba"


Wani fari Hindatu ta hau Yi Masa da Ido


Naseer kuwa ya d'auke kansa yana "Umma bana San na haura jibi Dan inada ayyuka Dana baro da yawa acan da zan samu da gobe an daura auren jibi sai mu wuce da ita



"Wanan ne Kuma baka Isa ba Nasiru wlh a baka Dade ba sai kayi sati a daura dai auren goben Dan baka Isa ka maida Hindatu bora ba gwara na fara ganin yanayin Zaman naku agabana.

Naseer Bai iya Kara ce komai ba ya mik'e Yana Allah ya kaimu

Ya shige dakinsa ya zauna a Gefen gadon tare da dafe kansa ba abinda yake tunani Sama da ya Naeema zata karbi zancen Karin aurensa gashi hindatun ma ko kad'an Bata Masa ba.

Bai San da shigowar mutum ba sai ji yayi an zauna a gefensa

Da Sauri ya dago da kansa Suka had'a Ido da ita ya mik'e zumbur Yana ke Mai Haka kika shigo min daki?


Murmushi ta Masa da shi a idonsa yake tona asirin muninta tace "Umma ce ta turo Ni tace muyi Hira"

"Toh sai ki Bari sai an daura ko Kafin ki fara shigo min daki Dan Allah tashi ki fita

Wani irin kallo ta Masa kafin ta mik'e ta fita a fusace.

Naseer kuwa yaja dogon Tsaki ya d'auko Quraninsa ya hau Kan sallaya

Ita kuwa Hindatu tana fitowa ta kalli Hajara data zuba mata Ido tana "wlh wanan Dan naki yaci sa'a ina Sansa da wlh yau na hukuntashi Bai San wacece ni ba ko"

"Karki damu zamu yi maganinsa Dani yake magana anjima ki zuba maganin Nan a bakin kofarsa indai ya tsallaka angama sai yanda kikayi dashi"

Murmushi hindatun tayi ta samu waje ta zauna Sha biyun dare Hajara sukayi shigar jajayen kayansu suka fita

Hindatu Kuma ta Ciro garin maganinta daga rigar no-no taje k'ofar d'akin Naseer ta Barbada daga bakin kofa Tana murmushi

Naseer kuwa duk abinda tayi akan idonsa ne.hakane yasa tana barbadawa ya girgiza Kai ya cigaba da Addu'oinsa sai daya Gama tas

Ya d'auko tsintsiyar bandaki ya share garin maganin da Addu'a a bakinsa.


A takaice washegari Hajara ta Sako Naseer a gaba aka daura auren Naseer da Hindatu ta Kuma tilastawa Hindatu tarewa a d'akin Naseer a ranar.

Naseer kuwa ko kallonta baiyi ba ya d'auko Quraninsa ya hau kan dadumarsa ya ware muryarsa ya hau karatun Qurani.

Hindatu kuwa aguje ta baro d'akin

Ta fito ta zauna a Palo Dan gidan ba kowa suna can suna shagali Yar shugabarsu ta auri Naseer.

Naseer kuwa anan ya Gane itama Yar kungiyar mahaifiyarsa ce shi kuwa ya dage ya cigaba da karatu.

Wasa Wasa Haka sukayi sati Inda Naseer ya fara had'a kayansa akan zai tafi Hajara kuwa kamar ta fashe Dan bakin cikin Dan babu irin aikin da basuyi akansa ba Amma fir tak'i kamashi abin har mamaki yake bata har a abinci sun saka Kuma yaci duk a banza.

Akan dole suka shirya raka Hindatu Kano da sunan zasu kaita wanan Karin Hajara ce da wata Yar kungiyarsu sai Hindatu.

Naseer kuwa babu abinda baiyi ba akan su zauna Hajara kuwa ta dage su zasu Kai Hindatun.

Bai Kuma manta da zuwa wajen Mallam Musbahu ba Inda ya karbo mata Sakon da zai Kai Mata ya Kuma gayya Mata yanda za'a amfani dashi.

Sosai yayi kewar Naeema da yayansa.

Ahaka suka dau hanyar Kano Yana ji Kamar ya shake Hindatun dake ta Karo jikinta a jikinsa

Yasan hanyar da zai rabu da ita cikin sauki wuyanta Hajara su dawo su barota da ayar Allah zai Gama da ita a Dan zaman da yayi ya Gane su Saffiya ma sun xama Yan kungiya Har tambayar lami yayi Mai ya sameta a bayanta tace Masa fad'uwa tayi.


Naeema

Tunda Naseer ya tafi nake cikin Zullumi da tashin hankali bansan Mai yasa hankalina ya kasa kwanciya da tafiyar ba ga wani irin hargitsatsen mafarkin da nake fama dashi hakane yasa na zage da Addu'a ko makaranta bana zuwa sabida rashin kwanciyar hankali a Dan tafiyar da yayi mmn Mannir ta ringa shigomin anan take wuni ta debb'emin kewa ahaka ta sakoni gaba da tambayar Mai ke damuna badan Raina naso Na na bud'e Mata cikina na Gaya Mata halin da muke ciki da uwar mijina mik'ewa tayi sabida girgiza da tayi da labarina Ni kuwa nayi murmushi ta koma ta zauna ta hau bani shawarar indai Umma ta Kara matsamin na saka Naseer ya sakeni kawai Kar na zauna idan ba Haka ba wlh watarana Umma zata ci Nassarar kasheni dayake ta girmeni sosai ta bani shawarwari na Kuma ji dadin gayawa wani damuwar danake ciki.

Na Kuma zauna Akan shawararta na idan Abu yak'i ci yak'i cinyewa nasa Naseer ya sakeni.

Amma kasan zuciyata bana Jin Zan iya rabuwa da Naseer din Kuma bawai sonsa ne yasa nakejin Haka ba illa rabuwa da yayana Dan Ni nasan Naseer bazai Taba bari na tafi dasu ba uwa uba Umma ko Dan ta kuntatamin ta hanani daukarsu tunda ta lura farinciki na shine Naga yayana a kusa Dani.


Gashi cikin ikon Allah yaran nawa duk da karancin shekarunsu Allah ya musu baiwa ta hankali da k'ok'ari gashi kansu a had'e yake duk kuncin da nake jina aciki da na kalli baiwar Yaya matan da Allah yamin sai naji wani irin Sansu Ina Addua Akan Allah ya raya min su yasa Naga girman su humaira.

Kullum aka kwankwasa kofar gidana sai na saka Rai da ganin ko Naseer ne ya dawo.

Yau ma Ina zaune a palon na Gama duka aikin gidana na kwantar da Humaira a tsakiyar palon su Zahira sun tafi makaranta Minal kuwa Tana wajen mmn Mannir.

Tv na kunna Ina kallo Amma hankalina baya Kan kallon Yana can Calabar.

Kwankwasa kofar danaji anayi ne yasa na mik'e a Raina Ina tunanin kila mmn Mannir ce ta Gama ayyukanta ta dawo banma tsaya tambayar waye ba na bud'e k'ofar Inda kuwa nayi tozali da Umma da wata da bansanta ba bayansu Kuma wata ce zatayi Sa'ar Umma

Idona Sam bai hangomin Naseer dake sauko da Kaya daga bayan mota ba.

Cikin wani irin fad'uwar gaba naja da baya banma.san na zub'e a kasa ba na hau gaishe su.

Wani mugun harara.umma da yarinyar suka zabgamin sai Saar Umma ce ta amsa da wani shu'umin murmushi.

Umma kuwa shigowa sukayi suka barni a durk'ushe tana " babu yanda kika iya Dani Dan gidan Dana ne sai dai ki hadiyi zuciya ki mutu Aurene dai Naseer yayi Dan badan ke kadai na haifo.shi ba tunda kin k'i Tafiya na saka shi yayi aure idan kin Isa kisa ya saketa anan Zan nuna Miki karfin ikona"

Tunda naji kalmar aure naji jina na neman daukewa ko maganganun da Umma keyi sama sama nake jinta.

Banma San lokacin da Naseer ya shigo ba sai ji nayi ya dagoni daga tsugunnen danake Yana "Naeema lafiya Kika zauna anan"?

"Ya bazaka ganta a zaune ba tana bakin ciikin ganina tana bakin cikin ganin kayi aure dalla Ni ku taso ku nuna Mana d'akin da zaa Kai kayan Hindatu"


Da Sauri na mik'e cikin San danne abinda nakeji duk da jirin dake neman kayar Dani na nufi palon Ina Kara musu sannu da zuwa tare da nufar kitchen Dan na dauko musu ruwa.

Ina Jin muryar Umma tana cewa asirce Naseer nayi ita tasan duk abinda Naseer keyi ba a hayyacinsa yake ba.

Inaji ta Kira sunan Hindatu tana ta lek'a dakunan ta zabi Wanda takeso su shigar Mata da kayanta

Ni kuwa kasa fitowa nayi sabida rawar da jikina yake sai lek'a Hindatu nake da ta kusa biyuna a tsayi Gata da girman jiki idonta kawai ya Isa ya tsorata Ni ba auren ne ya d'aga min hankali ba yanda zan zauna gida daya da ita shi yafi dagamin hankali.

Hannuna na rawa na dauko musu ruwa Mai sanyi

Ina zuwa na ajiye musu agabansu

Adaidai lokacin da Hindatu ta fito daga d'akina tana cewa Umma d'akina ne ya Mata a fitomin da kayana.......
[6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 16*

Ta zauna Gefen Umma tana kad'a kafa.

Naseer wani irin Mugun kallo ya Mata Yana "ga dakuna can guda biyu ki duba Wanda ya Miki ki saka kayanki a ciki idan Kuma Bai Miki ba sai kisan nayi babu yanda za'ayi sama taka ki zo ki wani ce a tasar Miki daga d'aki.

Daga Haka Naseer ya mik'e fuskarsa a balain had'e ya ko kallon B'arin da Hajara take Bai kalla ba ya shige dakin Naeema ya banko k'ofar

Ni kuwa Yana shigewa na mik'e da Sauri cikin fad'uwar gaba da rawar jiki na fara k'ok'arin juyawa na koma kitchen Umma kuwa ta daka min tsawa tana na koma na zauna.

Da Sauri na zauna a gabansu Kamar Mai neman gafara kafin kace me har hawaye ya fara wanke min fuska

Umma na k'ok'arin Magana naji muryar Hindatun tana "Hajara zamu daidaita da Wanan Dan naki kuwa Kinga yanda yake min fa ita Kuma nasan badan komai yasa yake Haka ba sai Dan wanan kod'add'iyar Koda uban me ta fini oho"


Da Sauri Hajara ta karbe tana "ki kwantar da hankalinki Ni zanyi maganinta idan Bata bar gidanan ba zata bar gidanan idan wuya ya kusa kasheta ko Kuma a fita da gawarta bantaba ganin nataciya irin yarinya Nan ba ni farkon ganina da ita naji batamin ba Dan Ni idan mace ta fiye kyau Tsanar ta nake Ni nasan Bata bar Dana Haka ba wlh akwai abinda tayi Masa ta juyar Masa da Kai Amma da sannu Zan dawo da hankalin Dana kanki Hindatu ke dago ki kalli cikin idona.

Da Sauri na Dago har a lokacin hawaye kawai ke zuba a fuskata "Ga Auntynki Nan Hindatu matar Naseer Kuma zabina duk abinda take so shi za'ayi a gidanan duk aikin data sakaki ki tabbata kinyi Mata idan ba Haka ba wlh ranki ne zai b'aci kindai San halina sai dai ki bawa wani labari Dan Haka Maza tashi kije ki zab'a a cikin Dakunan can Wanda yafi girma ki gyara ki zo ki kwashe Kayanta ki Kai Mata ki saka Mata kuma.ruwan wanka idan kin fito ki daka Mana Sakwara muci kinji ko bakiji ba"?

Da sauri na gyad'a mata Kai na mike na nufi d'akin karshe Dan yafi na tsakiyar girma da Umma ta zauna ita da Saffiya.


Ina gyara d'akin Ina kuka wai ni Haka rayuwata zata Kare daga wanan sai wanan Mai Nayiwa Umma Haka ta tsaneni.

Ina Gama gyara d'akin na wanke band'akin dayake da ruwa a band'akin na tari ruwa a bokiti Yana cika na fito.

Na koma palon na fara kwaso kayan Hindatun Ina kaiwa daki Umma sai zagina take Tana zagin iyayena ita kuwa kawarta kur tamin Ido kamar zata cinyeni Ni kuwa na hau addua a Zuciyata Dan kallon da takemin yayi yawa ita kuwa Hindatu sai wani girgije girgije take Tana yatsina fuska.

Ina fitowa daga d'akin na shiga kitchen na fito da doya manya guda biyu na fara feraye wa Ina cikin ferayan naji Sallamar su Zahira.

Babu Wanda ya amsa musu bansan ya akayi ba sai ji nayi Zahira ta kwalla wani uban ihu sai dum dum nakeji kamar irin an samu babba Ana duka.

Jikina ne ya hau rawa na runtse Ido hawaye na zubomin ko ban lek'a ba nasan Umma ce ke dukan Zahira na Dade da sanin Umma ta balain tsanar zahira Ni nasan tsanar data min ne ya shafi Zahira shiyasa ma a cikin Yarana Zahira ko muryar Umma taji sai ta nutsu kaga alamar tsoro ya bayyana fuskar ta sosai dukan da takewa zahira na ringa jinsa a jikina ta Sha dukan Zahira ba tare da ta Mata komai ba na Kuma rasa Mai Yar yarinya da Bata fi shekara bakwai ba ta Mata.


Zagin Zahira kawai take Tana durma Mata duka tana "shegiyar yarinya tun kina karamarki an koya Miki bakin Hali baki iya Gaisuwa ba wane irin tarbiya Naeema ta muku wato ita ta kitsa muku idan Kun gani karku gaisheni ayi yara basuda tarbiyya balle wanan Yar iskar yarinya Ni nasan yarinya Nan idan ta girma Yar iska zata Zama shegiya Mai halin uwarta"


Naseer dake Sallah a a guje ya fito daya Sallame Sallar sabida yanda Zahira ke ihu Dan ba karamin Jibga take mata ba.

Nadeeya kuwa Tana gefe tana kuka

Fusge Zahira yayi cikin wani irin B'acin Rai ya kalli Hajara Yana "Haba umma Mai karamar yarinya Nan ta miki kike dukanta Haka kamar kin samu babba haba Umma "

"Zaka iya Rama Mata tunda na daki Yar gwal Naseeru Kai baka ganin irin tarbiyya da shegiyar matarka ta musu kwanaki Dana zo suna kallona Suka k'i gaisheni yanzu Kuma sun shigo wanan Yar iskar yarinya ta zo zata wuce ta gabana har da taka min kafa duk idonka Bai bud'e kaga irin tarbiyyar da Naeema ta musu ba sanan Dan na daketa kazo ka tsaya kana min tambayoyi Na daketa Naseer zaka iya Rama Mata nidai sukayi ba daidai ba Dole na hukunta su daga Kai har Naeema San Yaya ya rufe muku Ido Kun kasa musu tarbiyya ko baki akayi ai Dole aji kunya ai tunda yarinya Nan ta kwaso uwarta nasan inta girma ba lailai tayi albarka ba"


"Allah ya Miki albarka Zahira zakiyi Albarka insha Allahu nace Ina kankame wuk'ar hannuna da har ya yankeni jini na zuba bansani ba sosai kalmomin da Umma ke jifan Zahira dashi ya ringa min ciwo har tsanar ba iya Ni ya tsaya ba har Kan zahira da bani kadai na haifeta ba Jinin Naseer daya kasance danta na yawo a jikinta har Umma tace Zahira Yar iska zata zama baza tayi albarka ba wanan wane irin kiyayya ne kuka nake kasa kasa Ina jiyo muryar Naseer na "Umma wane irin kalamai kike Yi Haka karki manta fa yarinya Nan jikar ki ce akan me Zaki na cewa baza tayi albarka ba insha Allahu yayana zasuyi albarka Umma Dan Allah Umma kiringa kiyaye kalmomin da zasu fito bakinki Zahira fa yarinya ce ballantana kice ta mallaki hankalinta Umma Kinga yanda Kika kumbura Mata jiki fisabillilahi idan Haushin Mahaifiyarta kike ji ai Bai Kamata laifinta ya shafeta ba nawa Zahira take tsakani da Allah Naeema na iya kokari Akan yaran nan ba Kuma Ina fada Dan na kareta ba"


"Ai duka nake jira kamin Naseer ya ka tsaya iya surutai"

Naseer da idonsa ya kad'a yayi ja Bai ce komai ba ya daga Zahira da numfashin kirki ma Bata iyayi ya Kai ta d'aki dawo ya rik'e hannun Nadeeya ya d'auki Humaira da ihun zahira ya tasheta take ta kuka itama"


Nima kukan Humaira ne yasa naso fitowa daga kitchen din na d'auketa na goya ta sai Naga Naseer ya d'auketa


Hakane yasa na koma kitchen na daure hannuna da jini ke ta zuba na cigaba da aikina Ina kuka Ina tunanin abin Yi Taya ya ma Zan iya barin yayana tayaya Zan iya tafiya na bar yarana a hannun Umma da Raina Agaban idona tana azabtar min da Yaya inaga bana Nan.

Ina cikin had'a Miya naji Sallamar Mmn Mannir nasan Minal ta kawomin tunda Magriba ta kawo Kai

Gaida su Umma take naji Umma na tambayarta daga Ina take

Mmn Mannir kuwa Tana Mata wanan tambayar tasan wacece ita kuwa ta had'e Rai tana Ina matar gidan take"?

Take Hindatu ta watsa Mata harara tana "Gani Nan nice matar gidan ya akayi"?

Wani kallon Tara saura kwata Mmn Mannir ta mata ta ja Tsaki tayo hanyar kitchen da take Jin motsina ciki.

Ni kuwa Ina kitchen Ina Jin maganr da suke jikina ya hau rawa.

Har kitchen mmn Mannir ta shigo ta ajiye abincin hannunta ta kunto Minal da Saura wata biyu tayi shekara biyu da bacci ya d'auketa tana "Gata Nan tayi bacci Naga alamar yau gidan naki a cike yake toh nidai shawarar da Zan baki shine wlh ki kwatarwa kanki 'yanci ki rage tsoron Nan idan babba Bai ji kunyar hawa jaki ba toh jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba.

Ihu kawai mukaji Umma nayi ta hau kururuwa

Sosai hankalina ya tashi na rude da ganinta a bakin kitchen abinda ya ban tsoro yanda take zunduma ihu

"Yanzu Ni kike cewa jaka Yar nan Mai na Miki"?

Naseer a guje ya fad'o kitchen din mmn Mannir kuwa ta saki baki cikin mamakin sharrin da Umma ke neman Yi Mata

Kuka umma ta saka ta kalli Naseer dake ta tambayar Mai ya faru

Ta hau cewa "wanan yarinya Nan ce tayi Sallama muka amsa tana ganinmu taja Tsaki ta wuce mu ta shiga kitchen dinan shine Ni Kuma nayi mamakin tsakin da ta Mana shine na biyota naji dalilin dayasa ta Mana Tsaki Ina zuwa naji tana cewa Naeema wacce jakar ce wancan Yanzu Naseer har maganata Naeema keyi da wasu har a shigo Inda nake ace min jaka toh wlh daga yau Kar na Kara ganin kafar matar Nan a gidanan wlh daga yau Kar na Kara ganinta da Naeema idan ba Haka ba daga Kai har Naeema sai na dau mummunan mataki akanku da ganin matar Nan ba matuniyar arzki bace"


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu mama da girmanki kike karya da girmanki Zaki min sharri Ni nace Miki jaka kiji tsoron Allah"

Naseer kana kallo tana cemin Ina karya bazaka dau mataki ba"

Mmn Mannir Bata Bari ma Naseer yayi magana ba ta mik'a min Minal tana "ba sai kin biyo ta Haka Zaki rabani da Naeema ba ki kwantar da hankalinki bazan Kara zuwa ba kamar yanda kikeso sabida na lura bakyaso kowa ya rab'i Naeema Sabida ki yi ta azabtar da ita Kar tayi hulda da kowa ballantana a kawo mata d'auki toh Bari kiji na fada miki kiji tsoron Allah domin shi sharri Dan aikene watarana zai dawo Miki tun a gidan Duniya Allah ke hisabi kuma Zaki ga karshenki Naeema Zan tafi xan Kuma baki shawara idan Kinga akwai cutarwa a zamanku ki hakura da Naseer tunda Zama da danta ba Dole bane daga Haka ta bangaje Hajara tayi wucewarta.

Umma kuwa hannu ta hau tafawa ta kalli Naseer tana "Ashe gulmana Naeema keyi Ashe Haka Naeema take bin mutane tana musu gulma ta abin har ya Kai har da ta tamin sharri
Dama Haka kike Naeema toh wlh daga yau makarantar ma kin daina zuwa tunda acan kike haduwa da mutane kiyi gulmana har ki zageni Naeema Ina uwar mijinki toh wlh duk zagin datamin ba Ni ta zaga ba uwarki ta zaga Kai Naseeru wlh Tallahi na soke zuwa makarantar ta ko k'ofar gida bana so Naga kafarta a da sati daya zanyi Amma na ma fasa tafiya sai na kwana biyu shegiya Mayya"

Daga Haka ta juya ta barni a durk'ushe Ina ta kuka ko kad'an ban kawo sirrin Dana gayawa mmn Mannir zata zo ta tona a gaban Umma ba Dama gudun Haka yasa tun farko naki Gaya Mata ko Naseer ma ai bazai ji dadi na fadawa wani maganar ba duk ba wanan yafi bak'anta min Rai ba sai makaranta data ce bazan koma ba Allah yasan idan akwai abinda ke faranta min a rayuwa yanzu Bai wuce makarantar da nake zuwa nake samun ilimi ba sosai nake Kara sanin rayuwa sai gashi lokaci guda Umma ta katsemin Mai yasa mmn Mannir zata min haka"

Dafani da akayi yasa na Dago Naga Naseer ne da idonsa ya kad'a yyi ja idan ba karya idona yamin ba har hawaye ne ya Dan kwanta a idonsa


"Kiyi hakuri Naeema ki cigaba da hakuri watarana sai Labari nafiki Jin ciwon abinda ke Miki Amma ba komai Zan sadaukar da farincikina na faranta Miki idan Naga Umma ta cigaba da matsa Miki Zan sawwaake miki sabida ki samu yancin Mahaifiyata ce bansan ya zanyi da ita ba Dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da gayawa Allah Yana sane damu ko auren Nan data k'ak'a bamin ba so nake ba tilasta min tayi idan kin Gama kizo akwai sakon da Mallam Musbahu ya bani na baki"

Daga Haka Naga ya mik'e da Sauri ya nufi dakina da Minal a hannunsa.

Ahaka na daka Sakwaran Ina kuka Sosai naji komai ya ficemin a Rai na ringa Jin inama inada damar da Zan gudu da yayana ko bara ne

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment