Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alwala nayi Sallah La'asar duk da jikina ba kwari Haka na fito na dau hanyar titi kafin na isa titin na hangota tana ta zabga Sauri daga yanda yake cila Kular nasan ta siyar.

Tana hangoni ta nufoni da Sauri Ni Kuma na tsaya jiranta.

Tana karasowa ta mikomin ledar hannunta d'auke da biyar biyar Lodi guda har da goma goma

"Umma Kinga na siyar da duka har yanzu nema ake"

Damke ledar nayi cikin murna Ina "Shikenan Zahira mun samu Sanaa Amma daga yau bazaki Kara fita da kanki ba da kaina Zan ringa fita"


Muna karasawa gida.na zazzage kudin na kirga Naira dari uku har da Sha biyar.

Kamar waccce akayiwa kyautar dubunai Haka naji.

Naira dari na Bata ta siyo Mana gari da suga har da gyada Wanda zamu Sha daddare .

Tana dawowa tacemin na Bata dari ta siyo min kayan hadin zobo mutane suna so Dan har tambayarta ake tayi.

Kamar Wasa na Bata ta siyo komai har da suga da yake komai lokacin da sauki ba kamar yanzu ba suga ashirin ma zaiyi Kofi uku a lokacin.

A ranar ban kwanta da fargaba ba Dan Ina kyautata zaton mun samu hanyar da kudi zai ringa shigo Mana Dan har kudi na bawa Zahira ta kaiwa Mai kankara akan gobe zamu karba har farin Leda na Karo.

Washegari na bada kudi Suka siyo Mana koko da kosai.

Da Rana ma garin muka Kara Sha.

Biyu da rabi na Gama hada Zobon dayaji kayan kamshi da suga na kukula na zuba a babban kula dayafi Wanda Zahira ta fita dashi jiya

Wanda Zahira ta tafi dashi kuma.na kukula ruwa muka zuba kankara

Ana iddar da sallah La'asar na dau babban Zahira ta d'au karamin muka Mika bakin titi.

Muna isa Kamar irin mu ake jira ko mu kadai ne masu siyar da ruwan Sanyi da zobon.

Nan da Nan aka hau siya ko awa daya bamuyi ba ya Kare.

Hamdala kawai nake a raina.

Dan na rubanya kudin Dana kashe sosai.

Daga Ni har Zahira sai murna muke.

Kayan abinci na Dan tsitinta na siya Mana mukaje gida.

Zahira ta Dora Mana abinci.

Farinciki danake ciki kamar Naseer ne ya dawo.

A takaice tundaga lokacin nida Zahira muke fita siyar da ruwa da zobo.

Allah kuma.ya saka Mana albarka Dan har sawu biyu Mukeyi.

Cikin wata guda sai gashi na Tara kudin da banyi tunani ba.

Dama rashin kudi yasa ban saka yarana a makaranta ba.

Wani karamin private school dake kusa damu.na Kai yarana gabadaya


Sai dai kudin dake hannuna iya mutane uku zai Isa a saka babu kudin biyu Raheema da Humaira kuma.ya Zama Dole na saka su

Tsugunna wa nayi nacewa Mai makaranta ta karbi dukansu Zan ringa mata.aikin nanny har na Gama biyanta.

Cikina daya fara fitowa.ta kalla tace zan iya kuwa

Nace Mata Zan iya kamar Wasa kuwa washegari yarana suka tashi tun asuba suna ta murna zasu fara zuwa makaranta Nima sai murna nake.

Abincin Dana dafa musu Basu wani ci sosai ba Haka na kulle gidan muka tafi.

Naci saa Mai makarantar nada mutunci duk da arniya ce

Sannan Zan na musu aiki yasa ta bawa yarana uniform har da littattafai duk akan bashi.

Ni kuwa na wanke band'akin makarantar na share koina sai Dana Gama naji bayana namin ciwo.

Karfe daya ake tashi gabadaya yarana sai su kirani idan na Kara gyara makaranta sai mu dawo gabadaya

Ina dawowa Nadeeya zata Tayani Dora musu abinci Ni Kuma a lokacin Zan huta na awa daya Ina Kara tashi sai na dau Kular zobo da ruwa Dan na sama musu makarantar Allo da biyar kawai suke kaiwa duk sati sai Dana Yi dagaske Zahira ta yarda ta fara zuwa Dan dagewa tayi sai ta ringa Tayani neman kudi.

Tuni na Saba da wahalar aikin duk da cikin jikina Mai tausayi daya Saba ganina yasan Ina cikin wahalar rayuwa cikina daya fito sosai da a lokacin zaiyi wata shidda yasa wani bawan Allah ya bani shawarar danaje siyar da ruwa da zobo Akan na nemi almajiri Mai Amana na ringa Dora Masa tallan Ina bashi Lada ko abinci Dan Yana tausayamin idan yaga yanda nake Dora Abu Mai nauyi a kaina.

Godiya na Masa dan tunanin hakan Bai tab'a zuwarmin ba.


Ya d'auko hamsin hamsin guda goma ya bani.

Kamar hadin baki Haka aka taramin kudi wanda sai Dana hau zubar da kwallar farinciki.

Na koma gida cikin murna akan hanya na tsaya na Mana cefanen da zai Mana kwana biyu har da Naman Miya


Yarana kuwa sai murna suke da suka ga abincin Dana dafa da.nama sai da suka koshi na fara gayawa Zahira shawarar da wani bawan Allah ya bani.

Cikin farinciki tace min akwai wani isuhu a makarantarsu zata Gaya masa gobe.

Ita kadai ce take da wayon sanin mutum ne a cikina Amma kannenta duk sun dauka ciwon ciki nake idan suga ga cikin Haka zasuyi tamin sannu

Sosai na Dan fara samun kwanciyar hankali daga ranar da isihu ya fara d'aukar min ruwa da zobon Yana kaimin dayake yaron nada kwazo har sahu biyun yake Yi Kuma Yana da amana.

Haka Zan bashi kyautar kudi na bashi abincin dare.

Abinda ke fita Dani kawai shine aikin makarantarsu Zahira itama matar a Karan kanta tace na daina zuwa na bari sai na haihu.

Sosai naji dadin mutuncin data min

Kamar a mafarki Naga Ina wayar gari Ina cin karfin bukatun gidana ta silar siyar da ruwa da zobo na hada da siyar da kananan abubuwa a gida Yarana kuma suna zuwa makaranta islamiyya Dana boko ba abinda Zan cewa Allah sai dai godiya abinda ya ragemin a rayuwata shine ganin Naseer Yana Raina kullum dak'yar nake samun bacci Mai nutsuwa sabida tunaninsa idan kewarsa tamin yawa Haka Zan hau shafa cikina Ina tuna ranar karshen da muka rabu da shine yasa na samu wanan rabon Kaunar abinda ke cikina nake sosai inajin yana ragemin kewar Naseer idan na kalli cikina.


Murja

Hatsabibiya ce ta karshe kuma makira Mai fuska biyu.

Wani irin wahaltacen zama Hajara da Safiyya sukeyi a gidan
Dan duk Inda suke tunanin sun Kai da mugunta ko makirci ta zarce su Dan sosai take musu biyayya Agaban Tijjani Amma idan ya bada baya Haka take musu rashin mutunci San ranta.

Hajara kuwa Bata tab'a tunanin bazata iya cin uban Murjan cikin sauki ba

Har wani horan yunwa Murja ke musu Dan ko Tijjani ya samo abinci ya kawo ta dafa Haka zata juye a kula ta Kai d'akinta ta kankaro kanzo ta basu .

Hajara kanyi zuciya Taki ci Safiyya kuwa Haka zata ci Tana zagin Murja

Hajara kuwa Tana Kiran Tijjani Dan ta Gaya masa Zai daga hannu ya hau cewa baya San tashin hankali Kar tazo ta daga Masa Hankali shi bazai jure ba idan taga bazata iya zaman gidansa ba Dan Allah ta tafi sosai yake Jin Haushin Hajara sabida yasan duk masifar da suka tsinci kansu a ciki itace sila .

Hajara har da kukanta Dan Tijjani ko kad'an yak'i binta sau da kafa balle yabi umarninta ya saki Murja da ta balain tsana Kamar ta jefata a wuta.

Idan taso yiwa Tijjani hargagi akan zata tsine Masa idan Bai bi umarninta ya saki Murja da ba Yar arzki bace murmushi takaici yake Yana "Tsinuwa Kuma na nawa Umma Kinga fa halin da Kika jefamu akwai masifar da yafi wanan Umma ba abinda matata ta Miki bazan saketa ba.

Daga Haka zai kad'a kansa ya fice


Safiyya kuwa data ga alamar yunwa zai kasheta kudin mota ta nema ta tafi Calabar.

Inda ta nemi Lami da itama taje wajen dangin babanta suka daura Mata aure da wani gurgu tuni ta dawo daga rakiyr Hajara ta tuba.

Kwana uku kawia tayi a gidan lami Suka fara samun Sab'ani Dan Safiyya Bata rik'e girmanta na Yaya ba tuni ta Kara ficewa daga gidan.

Ta koma gidan kanin mahaifinta Dan mahaifinta tuni ya bar garin tunda ya dawo hayyacinsa shi kuwa kanin mahaifinsu ya Riga yaci Dubu sai ceto ba abinda Hajara zata iya Masa hakane yasa bai k'i karbar su ba Dan shima tamkar mahaifinsu ne.

Sai dai itama zuwa gidan datayi sai da sukayita fada da matar kanin babansu a karshe shima yaga bazai iya ba ya Bata kudi akan ta koma Inda ta fito ko ta zuciya ta Nemo mijin aure.

Ahaka ta Kara dawowa gidan Tijjani tare da cin alwashin neman mijin aure.

Sai dai dawowarta yasa Murja ta daura damarar cin ubansu Dan ta balain tsanar Safiyya sabida Bata da mutunci itama.

Kwana biyu da dawowar Safiyya da safe Tijjani ya fita da wuri.

Daren jiya Hajara kwana tayi da yunwa Dan Dan kanzon da Murja ta basu Nan da Nan Safiyya ta cinye hakane yasa yau ta fito da wuri ganin murja bata palon yasa ta nufi kitchen da Sauri jikinta na rawar yunwa.

Ido biyu tayi da katon bredi ta Kai hannu ta d'auka cikin murna ta rufo kitchen tana juyawa suka yi Ido biyu da Murja dake mata wani irin kallo .

Hajara gabanta sai daya Fadi Amma ta maze ta matse bredin a hammatar ta tana hararar Murjan tana "Na dauka nida gidan Dana k'arfi da yaji ki ringa Mana Horan yunwa Dan uwarki wlh kyalleki nakeyi bakisan wacce ce Ni bane Ni nasan baki bar Dana Haka ba asirce shi kikayi Amma wlh zanyi maganinki Bari na samu kudi nayi tafiya na dawo"


Wani irin Dariya Murja ta kece dashi tana "Naji barauniyar bredi kafin kiyi magani na ki bani bredina"


Ta Kai hannu ta fusgo bredin Hajara ta kwace cikin zafin nama kafin kace me sun kaure da kokawa.

Murja Bata duba Wai uwar mijinta bace ta haye ruwan cikinta ta hau Kai Mata naushi ihun Hajara ne ya tashi Safiyya ta fito a guje ta hau kaiwa Murja duka.

Murja kuwa ta tashi daga Kan Hajaran ta jawo safiya ta matse a hammatar ta ta hau dirkarta.........
[6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 30*

"Lailai Ashe su Naeema haka aka samu duniya mu kuwa muna can muna garari Umma Kinga katon gidan da suke fa har tsinaniyar matar Yaya Tijjani ta ringa gasamu a wancan tsinannen gidan nata"


Cewar Safiyya tana zagaye tsakar gidan tare da lek'a ko'ina

Umma kuwa itama karewa koina kallo take

Ni kuwa ganin engine nata yi cikin Dan fad'uwar gaba na fito bansan Inda na aro jarumtaka ba na saki murmushi Ina "Umma Kune Ashe sannunku da zuwa"

Na karasa wajen da aka jona engine na kashe.

Daga Umma har Safiyya ba Wanda ya amsa gaisuwar da na musu illa ma cikina da suka bi da kallo wanan kallon tsanar kamar su jefani a wuta suka ringa Bina dashi nikuwa a Zuciyata na hau adduar tsari daga duk wani sharri.

Bana San na wuce ciki suga Kamar rashin kunya na musu hakan ne yasa nace "Umma ku Shiga daga ciki Mana kuka tsaya a tsakar gida"

"Ai ko baki fada ba zamu Shiga ciki tunda ba gidanki bane gidan Dana ne Koda kudinki Kika Gina"?

"Aaa"

"Ke Dan uwarki bakida wani aiki ne sai haihuwa yau Naga masifar jarrraba a gurin yarinya Nan ke kenan Ana tab'a ki sai ciki ko ya aka Dan kwana biyu ba a ganki ba indai aka tashi ganinki sai dai a ganki da ciki"

"Umma Ni bakin cikina ma duk Mata take ta Tarawa Yaya Naseer Bata tausaya Masa da talaucin da yake ciki ba gashi ta Kara k'unsar wani cikin"

Cewar Safiyya tana harara ta.

"Haka kawai da lodin yaran Nan zaiji da Kika tarasu duk Mata zaiji ko da me kikeso yaji na ce bana San ki ki rabu da Naseer Kika k'i ke a lailai sai kin zauna shine yanzu ma halin da Naseer yake ciki Baki duba ba Kika Kara kwasar wani cikin ko to shikenan ki haifeta nagani shegiya tsinaniya Mayya"

Fuuu Suka wuceni ni kuwa naji wani Abu ya tsayamin a mak'oshi sosai Raina ya b'aci da abinda Suka min Naga Yara matan Nan Allah ne ya bani Kuma cikin Nan ma shi ya bani insha Allahu lafiya Lau Zan haifi cikina sosai na ringa mamakin abinda yasa banji azabar tsoro da rawar jiki Dana Saba ji ba Dana tsaya dasu waje daya gabana ba tsinke ba Dana had'a Ido da Umma duk da na Riga da na Saba da Jin tsoronta ko Yaya ma naji muryarta Zan Dan ji fad'uwar gaba.

Cikin palon na Shiga ga mamakina basa cikin palon sai muryarsu naji Yana tashi a d'akina yarana Kuma suna rak'ube a waje daya Zahira kuwa jikinta sai rawa yake Nadeeya ma kina ganinta kinsan a tsorace take daidai da Raheema da take karamarsu sai data nutsu.

Idan a da ne ban Isa na Shiga d'akin ba Amma sai na tsinci kaina da shiga d'akin a tsakiyar d'akin umma ke tsaye Safiyya ita Kuma ta zauna akan gadon tana "dakuna biyu ne fa kawai Mai katifa da fanka mu dau wanan din kawai ita Kuma taje ta karata da yaran"


"Aaa Aunty Safiyya Wanan d'akina ne sai dai ku zabi na d'aya b'angaren tunda a na gyara"


Wani irin kallo Umma ta juyo ta min tana "iyyeee lailai wuyanki ya Isa yanka wato wanan dakinki ne sai dai mu zab'a a daya bangaren gidanki ne ko gidan Dana ke har kina da iko da gidanan har kina da Bakin zab'a Mana inda zamu Zauna iyye"?

"Kiyi hakuri Umma ba Wai zab'a Muku nake ba Naga can din ma yafi Nan girma lokacin da muka dawo gidanan iya dakuna biyun Nan Naseer ya iya gyara Mana da Palo sai Dana samu kudi na gyara can din"


"Ahap Umma kinji ko sai data samu kudi Ni Dama nasan Yaya Naseer da baya nan bin maza take Haba umma.kiga ga yanda gidanan aka gyara ko Ina na kyalli wlh Ni nasan a Rina karki yi mamaki ma cikin jikinta bana Naseer bane"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aunty Safiyya wane irin magana ne wanan ya Zaki min kazafi da Kuka shigo injina nawa Kika gani ban bi maza ba Ina gidanmu bana Jin yanzu da yarana da Aurena Zan bi maza Koda Naseer zaiyi shekara hamsin Bai dawo ba Zan rik'e amanar aurensa har sai ya dawo gareni"


Na karashe da Bakin ciki sharrin da Safiyya ke neman Yi min

"Allah ya Miki Albarka Safiyya badan kin ganota ba da Haka zata linkemu ta cuci Dana da baiji Bai gani ba ta lika Masa cikin da ba nasa ba maza tashi kije ki shigo Mana da kayan mu"


"Umma kiyi hakuri ku koma can d'akin wanan d'akina ne"


Mamaki ne ya rufe Safiyya da Umma Ni kuwa bansan Mai yasa naji ko kad'an banji tsoronsu ba Taya ma sama ta ka zasu zo su rasa Inda zasu zabi su zauna sai dakina Inama laifin wani d'akin inyaso sai na Kai musu katifar su Zahira yarana su dawo d'akina mu ringa kwana gabadaya duk da tun ranar da Naseer ya bar gidanan waje daya muke kwana dasu katifarsu suke daukowa su kawo d'akin su saka a kasa su uku su kwanta akai Ni kuma da Raheema da Humaira mu kwana a Kan gadon

"Kikace Nan dakinki ne Naeema da kudin ubanki aka Gina da har kike zab'a Mana inda zamu Zauna"?


Safiyya tace a fusace tana doso Inda nake a tsaye "Mahaifina Allah ya Masa rasuwa aunty Safiyya Dan Allah ki daina zaginsa bada kudina aka Gina ba Amma Nima akwai kudina a cikin gyaran gidan"

"Uwarki Kike jira Safiyya da Bazaki zubar Mata da hakora ba ki naushe min tsinane Nan cikin Nan Naga da wane baki zatayi magana"


Kamar Mai jiran umarni tayo kaina nayi Baya da Sauri ina San juyawa Amma na rasa Mai yasa na tsaya akan kafafuna Tana isowa ta daga hannunta kafin ta sauke shi a jikina na rik'e hannunta jikina na Dan rawa "Ina Wai Mai na muku a rayuwata ne Mai na muku kuke San kuka ga bayana kiji tsoron Allah aunty Safiyya karki manta kema mace ce bakisan ya rayuwa zata kasance Miki a gaba. Ba abinda na muku Kuna ta cutar Dani Yayanki ya gudu ya barni da yayansa cikin azabar talauci ban karaya ba na zame wa yayana uwa da uba nake neman kudin da Zan kula dasu wlh gidanan dakuna biyu ne kawai gyare sai Palo da kudina na gyara gidan Rana da ruwa Haka nake neman kudi duk Dan na gyara Masa abinda ya rage Masa iya wanan Bai Isa sarara min ba sai an biyoni Nan ma an takani karku manta fa Nima haifa ta akayi"


"Baki haifu ba Safiyya idan Kika Bari na karaso Baki bajeta a kasa ba"

Kara kwace hannunta ta fara k'ok'arin yi kafin kace me k'ok'awa ya kaure Mana tana ta k'ok'arin harbina a cikina a ranar Zan iya cewa yin Allah ne ba yina ba kuka nake a zuciye muna k'ok'awa da Safiyya bansan ya akai na kayar da ita ba duk da sai da bayana ya amsa na hau Kai Mata duka.

Umma a guje tazo kanmu da balain k'arfi ta damke kafadata ta Jani daga Kan Safiyya ta wurgar Dani ta cillo kafarta da zumar harbina a ciki sai gashi zaninta ya tad'e ta tayi zaman yan bori a kasa tana washhh bayana Dan ba karamin buguwa tayi a da kasa ba


Washh wash kawai take Tana "Itama ta Shiga kungiya Safiyya yanda Murja ta zanemu itama take San zanemu"

Safiyya Kara mik'ewa tayi tayo kaina Nima na mike da Sauri muka cigaba da k'ok'awan na Kara bajeta a kasa Ina kuka Ina "Kasheni zakuyi Mai na muku haka"

Umma sosai ta ringa k'ok'arin mik'ewa ta kasa yarana kuwa suka shigo d'akina aguje suka hau kuka suna Jana daga Kan Safiyya da ta samu Saar kaimin naushi a cikina sau biyu a karshe dataji azabar nauyina abinka da Mai ciki Nishi ma dak'yar takeyi


Hannuna ta Kama ta hau ciza hakane yasa na fusge tare da dagata Ina cigaba da kuka.

Ita kuwa ta mik'e ta zauna idonta ya kad'a yayi ja sai numfarfashi take.

"Zoki dagani ni nasan ba ita take da Karfin yi Miki dukan Nan ba kungiya ta Shiga Dani take maganar wlh ta janyowa kanta sai na gana Mata azaba da sai ta nemi mutuwa da kanta tashi ki dagani"


Umma tace tana cije lebb'e

Safiyya mik'ewa tayi tana "ba dai ni Kika daka ba wlh Zaki ci ubanki mu zuba nidake Kuma wlh d'akin nan zamu Zauna Zo ki fita damu nagani"


Ta karasa tana nufar wajen Umma tare da dagata tana wash wash suka nufi bakin gado ta zauna.

Ni kuwa tunda naji suna Zan ci ubana jikina ya hau rawa tsoro ya rufeni ban manta cikin Minal wuyan Dana Sha ba ban.manta kumburin da nayi a cikinta ba Ina tono wahalar Dana Sha gabana har fad'uwa yake zama nayi a d'akin Nima a kasa.
Yarana suka zagayeni Umma da Safiyya kuwa sukayita zagina suna tsinemin yarana kam ta musu baki yafi cikin kwando duk Kuma a cikinsu sunfi zagin Zahira da ta d'auko komai nawa har da tsoro sosai.nake hango kiyayyar da suke Mata na daban ne ita kuwa jikinta sai rawa yake kamar ta tsaga jikina ta shige Nadeeya ita ma sai kuka take kasa kasa.

"Ki tashi ki dauko Mana abinci Dan uwarki ko sai mun roka"?

Umma tace tana jifana da harara

Ni kuwa ko gezau banyi ba Dan gani nake idan na bar d'akin Yar tsana Mai ciki zasu binne a bakin k'ofata na hau kumbura kamar lokacin cikin Minal zuwa yanzu da zasu lura zasu ga azabar rawar da jikina yake sabida tsoro.

Haka suka yi tamin magana na sharesu Suka cigaba da zagina a karshe sai Umma cewa Safiyya tayi ta fita ta samo musu abincin

Banyi magana ba Safiyya ta fice ta zubo tuwon Massara Dana tuka da miyar kubewa da har dumame nayi Dan yarana suna so Kuma basu ci abinci ba.


Haka suka zauna Akan gadona suna cin abinci

Mu kuwa muna rab'e a gefe Raheema ce ta hau zungurina Tana Jin yunwa sai kallonsu take.
Safiyya ta hau zaginsu tana basuda tarbiyya karuwai.

Sai anan nayi.magana Ina "yarana ba zasu tab'a karuwanci ba insha Allahu"

Kamar wacce aka tsikara na mike na nufi wajen da akwatin kayanmu yake dayake ba wardrobe a d'akin.

Na hau Kai akwatuna na waje sai Dana kwashe komai tsaf ya rage daga su sai.gadon da suke.kai.

Na fito da yarana cikin.kuka na cewa yarana su hau kai Mana kayanmu daya b'angaren.

Dake d'auke.da karamin Palo da dakuna manya guda biyu Dan ginin gidan Kamar na mai Mata biyu Naseer yayi sai da shi lokacin wanan da muka koma shine b'angarensa Wanda na barowa Umma shine b'angarena Dana yarana.

Dan gyaran danayi ma so nake na zuba Yan haya na fitar musu da kofa ta tsakar gidan ganin gidan ya Mana girma idan Ina Jin motsin mutane ma zanfi Jin dadi inyaso idan Naseer ya dawo sai na sallamesu sai gasu Umma sun duro.

Har tarkacen d'akin su Zahira sai da muka kwaso daga b'angaren


Na dawo dashi b'angaren Naseer na saka katifar d'akinsu a daki daya Zahira ta.musu shimfida.

Ni kuwa na Shiga kitchen na juyo musu tuwon a faranti da Miya har da ruwa na kullo kitchen din

Abinka da Yara Basu ma.wani San Mai ke faruwa ba sai zahira Nan da Nan suka hau ci.

Zahira.kuwa sai Daka Mata tsawa ta yarda ta fara ci Dan sosai ta Shiga damuwa da hawayen dake zubomin Ina daukewa haka na zauna Ina tunanin masifar dake neman kunno min tashin hankalina Bai wuce karsu cutar Dani ba Kar bacci ya d'aukeni su biyo dare su caka min wuka gashi Naseer baya Nan.


A Haka nayi zurfi a tunani har bacci yayi awon gaba da yarana Zahira ta gyara musu kwanciyarsu.

Tare da.kunna musu maganin sauro.

Sai data tab'ani na dawo daga duniyar tunanin Dana tafi.

Abincin da suka ci Suka rage ta kawo gabana cikin karyayar murya da tayi kasa.dashi sosai ta hau magana tana "Umma kiyi hakuri kici abinci insha Allahu ba Abunda zasu Miki"


Maganarta kuwa kamar tunzurani yayi na hau rera kuka Ina Mata surutai Kamar wata babba na hau Bata labarin irin abinda su Umma suke min Dana rasa Mai na musu suke San kasheni"


Bansani ba ko kwakwalwarta zata d'auki maganganuna kuka kawai take itama Ni kuwa na mike na fito karamin Palo Naga ko sun fito daga d'akina sai dai Ina lek'awan Naga har sun turo k'ofar sun rufe Kamar d'akinsu.

Ina mamakin Halin Umma da Safiyya k'arfi da yaji sun kwace min d'akina.

Haka na koma dakina Ina Jin inama inada halin da Zan samu kudi Mai yawa a daren Nan na kwashe yarana na bar musu gidan.

Tunda na samu ciki Ina da Jin bacci ina Kuma bacci Mai nauyi ban fiye tashin dare ba idan bacci ya d'aukeni Amma zuwansu Umma yasa na nemi baccin na rasa Zahira itama haka ta zauna wajen karfe daya na dauro alwala Ina kallon Zahira ta biyoni itama tayi alawalar tazo gefena ta tsaya muka hau nafilfili.


Ban iya yin raka'oi Mai yawa ba na zauna na dau carbi nayita sallati da istigifari har lokacin hawaye Bai d'auke daga idona ba sosai na saka a Raina a wanan lokacin da wasu ke bacci Ni Kuma na zo gaban Mahallicina ina kuka zai magance min damuwata A da Inada Allah Ina da Naseer Amma yanzu banida kowa sai sarkin sarakai da baya zalunci da idan ka Kai kukanka wajensa zai magance maka damuwar ka Ni nasan badan baya sona nake rayuwar azaba a gidan Naseer ba yanda ya halliceni Haka ya hallici Umma dake neman rayuwata shi Zan kaiwa kararta yamin maganinta yau ko Umma tayi nassarar kasheni nasan a rubuce yake a ita zata zama silar mutuwata Dan kowa da hanyar tafiyar sa.

Tsabar Jan carbi da adduar zuci sai da yatsuna Suka hau ciwo.

Inajin Zahira na adduar "Allah kasa Kar suyi wa Umma komai Allah ka dawo da Abban mu lafiya Allah kasa Kar su cutar damu su cutar da Ummana"

Ahaka ta Gama hada Addu'ointa bacci ya d'auketa Nima bansan lokacin da bacci yayi awon gaba dani kaina jingine da bango ba




*2am*

Hajara ce zaune da Safiyya a tsakar d'akin da wani bak'in tukunya suka dibi abinda shugaba ta basu Suka watsa take

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment