Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suyi asiri su saka Mata gubar duk yak'i tasiri akanta Amma idan suka samu Dan dabba lokaci guda zai d'auke kanta da bindiga.

Ahaka Safiyya ta Samo Garba da ake wa lakabi da No mercy ta kawo shi har gidan da su Naeema basa Nan suka Gama magana ta Masa bayanin ayiwa Naeema fyad'e a Kuma kasheta.

Safiyya ce har dacewa idan suka tashi Mata fyad'e su Mata yanda bazata moru ba Naseer zai tsaneta ya saketa

Anan No mercy ya cajesu kudi take Umma ta d'auko kudin ta bashi Dan sosai Naseer ke Bata kudi tunda Suka zo gidan

Yana karbar kudin ya tambayesu yaushe zai aiwatar da aikin Suka ce Masa ya Bari sai Naseer yayi tafiya yanda ma babu Wanda zai ceci Naeemar.

Shine da Naseer yace musu zai yi tafiya Suka hau murna suna fita Safiyya taje ta samu No mercy Akan yazo yau Naseer baya Nan


Ihu Umma take sosai tana Kiran sunan Naseer daya zo ya ceceta Dan daga tukunyar Tsafin nata har komai na karfinta sun baro shi a Calabar daga ita har Saffiya dan Shugabarsu ce ta kwace Sabida tana ganin kashe Naeema sai da dabara ba Tsafi ba Kuma ita Hajara akwai bakin zuciya kurkusa bazata iya ba sai tace sai tayi amfani da k'arfi Inda take Naseer da Naeema zasu harbo jirginsu Susan ba tuban tayi ba shiyasa shugabarsu ta kwace Akan su kashe Naeema ta wata hanyar tinda tsafin yak'i ci sai gashi sun biyo ta wanan hanyar da ba'aje koina ba asirinsu ya tonu.

"Naseer bazaka zo ka ceceni ba sai sun kasheni"


Umma tace bakinta cike da jini idonta yayi luhum luhum

Naseer kuwa hankalinsa gabadaya Yana Kan Naeema da Mazan suka cikata Wanda suna cikata yayi kanta sabida yanda numfashinta ke barazanar d'auke wa sabida firgita da tayi kwantar da ita kawai yayi a jikinsa Yana jijigata tare da tofa mata adduoi

Shi kuwa no mercy cewa.umma yake "Ke Kika aiko mu kasheta ko ba ke bace wlh sai kin amsa da bakinki Zan cika ki shegiya tsohuwar Banza"


Umma kuwa dataji azaba da Sauri tace "wlh ni na biyaku nace ku kasheta Amma kuyi hakuri sharrin shaidan ne"

Naseer kuwa cikin wani irin shock da mamaki ya zubawa Umma Ido hawaye na zubo Masa.

Ni kuwa har lokacin a firgice nake Amma duk abinda sukeyi Ina jinsu

Kuka kawai nake na Kara kamkame Naseer Dan gani nake har lokacin zasu iya harbina

Hambarar da Umma yayi Yana "Duk zalunci na kinfini wlh Ina daraja mace Mai ciki a rayuwata duk aikin da aka bani idan Naga mace nada ciki Ina daga Mata kafa Amma ke dayake azzalluma ce ahaka kikace mu kasheta bayan mun Mata fyade badan kin min tsufa ba da wlh ke zanyi wa fyaden kiji ya akeji Amma duk da Haka lokaci Bai Kure ba.

Barin gaban Hajaran yayi ya kaiwa Safiiyya data k'ifar da kanta kasa duka a duwawu da kafarsa Yana "kece kike cewa ayi Mata fyade yanda bazata moru ba ko to ke zaa muyiwa fyaden ku shigar min da ita daki.

Wani irin ihu Umma ta saki Safiyya itama ta hau ihu.

Kafin kace me tuni yaransa uku suka kinkimi Saffiya dake wantsal wantsal da kafa suka shige daki da ita sai ihu take Tana Kiran sunan Umma Akan tazo ta taimaketa Shugaba ta cucesu data rabasu da mudubin tsafinsu

Naseer kuwa har lokacin Bai dawo daga shock din daya tafi ba

Bazai iya fasalta halin daya tsinci kansa a ciki ba har Mahaifiyarsa tayi nisa Haka har yanzu ya kasa gasgata abinda yake ganin na faruwa a gabansa.

Umma kuwa bayan no mercy ta bi aguje daya nufi d'akin da aka shiga da Saffiya dake ta kurma ihu tana rantsuwar indai suka Mata wani Abu sai ta kashe su daya bayan daya.

Bayan No Mercy Umma ke k'ok'arin jawowa tana Jin inama da tukunyar tsafinta a wajenta da yau gunduwa gunduwa zatayi dashi.
Wani irin wurgi yayi da Ita ya rufo k'ofar.

Safiyya kuwa ta hau zunduma ihu

Umma kuwa aguje tayi wajen Naseer dake rungume da Naeema jikinsa na wani irin rawa sosai yake Jin kirjinsa na Masa suya sabida abinda Umma tayi.

Jijjiga shi ta hau yi tana Naseer ka tashi kaje ka Hana su tab'a min Safiyya kaje ka hanasu Naseer karka Bari wani Abu ya Sameta yau na shiga uku Ni Hajara Dan uwarki daga shi yaje kika kwanta a jikinsa wlh wani Abu ya Sameta kin shiga uku a hannuna Naeema kin zame min masifa a rayuwa ki daga shi nace"

Umma tace a fusace tana k'ok'arin janye Ni daga jikin Naseer da ya kankameni jikinsa na wani irin rawa ganin k'arfi da yaji take Jana yasa ya d'ago cikin rinannun idonsa Yana "Ki cikata Umma babu Inda zani domin ban San su ba
ke da kanki Kika kirasu gidanan abinda Kika so ayiwa Naeema Allah ya mayar Kan Safiyya Dan Haka babu abinda ya shafeni Umma ko kasheta zasuyi babu ruwana Dan ke Kika jawo Umma yanzu tsanar da Kika yiwa Naeema ya Kai har Haka ki hayi Yan d'abba kisa su zo su kashemin Mata su Mata fyad'e innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Mai na Miki Haka a rayuwa Mai baiwar Allah Nan ta Miki kike San kasheta k'arfi da yaji"

"Naseer kanwarka ce fa Saffiya kake cewa babu abinda ya shafeka yanzu kafi San Abu ya Samu Safiyya akan matarka Naseer Anya yarinya Nan ta barka Haka kuwa Naseer kana Jin ihun Safiyya fa"



ihun Safiyya data juyo da k'arfi tana kwalla Mata Kira yasa ta nufi bakin kofa ta ringa bugawa tana jijjigawa tana rokon a cika Mata 'ya sai da suka Dade a d'akin suka ringa fitowa daya bayan daya suna gyara Riga

No mercy ne karshen fitowa.

Yana fitowa Umma ta fada d'akin tana ihun an kashe Mata 'ya

Shi kuwa no mercy a gabanmu ya tsaya sai daya Gama gyara rigarsa

Cikin tsawa yace ke "tashi tsaye"

Da Sauri na mik'e tsaye kamar ba mai.ciki ba jikina sai rawa yake sabida tsoro


"Mai Kika Mata take san kasheki"?

Wlh ban Mata komai ba"

"Kai Wai dagaske Bata mata komai ba?

No mercy yace Yana kallon Naseer dake tsaye a gefena ya Dan dafani sabida Kar na Fadi

Cije lebb'e Naseer yayi Yana "dagaske ne babu abinda ta Mata Haka kawai ta tsaneta"

"Toh ke Dan ubanki Dole ne zama dashi ki rabu dashi mana ki tsira da rayuwarki tunda ta nuna Bata sanki har tana neman d'aukar ranki wanan tsohuwar muguwa ce azzalluma inkika dage sai kin zauna da danta wlh watarana sai tayi nassarar kasheki yau idan Allah ya taimake ki ni ban kasheki ba idan ta hayo wani bai zama lailai yaji tausayinki ba kasheki zaiyi wlh"

Kai Kuma tunda kasan uwarka azzalluma ce ka Bata takardarta tunda ba ita kadai ce mace ba ka Saketa ta samu wani ta aura Kai Kuma ka zauna da uwar taka tunda inaga Haka take so ko?
kaji ko baka ji ba"?


Da Sauri Naseer ya gyada kansa sabida yanda yake ta nuna mu da bindiga shi kuwa no mercy yace yauwa tana haihuwa ka saketa idan ba Haka ba Zan ringa biyowa ta Nan inama zuwa"

Yace ya juya Yana nufar d'akin da Umma take

Yana shiga ya fito da Umma gabanmu Yana "yarki dai ai ta Gaya miki yanda aka sani ko toh wlh Bari kiji na Gaya miki Zan ringa zagayowa Ina tambayar mutane yanda zamanku yake da yarinya Nan duk ranar da Kika Kara tab'ata ko kikayi yunk'urin kasheta wlh sai na fasa miki Kai da bindiga ko ban zagayo ba nasan na bar miki abinda Zaki ringa tuna Ni Dan kila nan da wata Tara Zaki samu jika Killer"


Wani irin dariya ya kyalkyale dashi ya Kara kallo nida Naseer Yana kundai ji abinda nace ko idona yana kanku"


Daga Haka yayi waje tare da yin pito sauran Suka bi bayansa da Sauri suka fice daga gidan

Suna fita na zub'e a kasa na Dora hannu aka na fara zunduma ihun kuka

Umma kuwa tamin wani irin kallo ta tashi da Sauri ta nufi d'akin da Safiyya ke Sume.

Naseer kuwa ganin irin ihun kukan da nake yasa ya fara k'ok'arin janyoni jikinsa Dan ya rarrasheni Ni kuwa na saka musu ihu Tare da janye jikina Ina "Naseer na gaji Dan Allah Dan annabi ka sakeni indai kana kaunata zaka so ka gani a rayye ko dansu Zahira su girma su San Ni Umma Bata Sona Umma Bata da burin daya wuce ta kasheni har guba Umma ta zubamin a kunnu ta biyoni da wuka ta binne Abu duk Dan na mutu ban mutu ba yanzu ta hayo Yan d'abba Dan su kasheni Naseer iya wandanan Abubuwan Dana lissafa maka ya Isa yasa kagane Umma Bata kaunata Kuma babu abinda baza tayi Dan ta kasheni ba Dan Haka Naseer na gaji wlh duk San da muke wa juna Dole mu hakura da juna duk da banida kowa ka Sakeni bazan rasa Wanda zai taimaka min ba Naseer duk da cikina Haka Umma ta biya azo a kasheni ayi min fyad'e haba Naseer abin yayi yawa Dan Allah ka sakeni.

Kuka nake sosai Naseer da idonsa ya kad'a yayi jawur ya sunkuyar da kansa Yana Jin duk ihun kukan danake ahaka mukayi kwanan zaune dagani har Naseer Ni Ina kukan fili shi Yana na zuci har aka Kira sallah asuba dagani har shi babu Wanda ya mik'e daga irin ajiyar zuciyar da Naseer ke yi nasan shima ba karamin kukan zucci yayi ba Ni jikina dake rawa har lokacin yasa na kasa mik'ewa nayi Sallah shi Kuma Naseer zurfi da yayi a tunani yasa Bai ma ji Kiran Sallahr ba.

Shidda saura Yan mintina na safe muka ga an bud'e k'ofar d'akin dasu Umma suke.

Umma ce ta fito daga d'akin hannunta d'auke da jakar kayansu har akai ta Dora wani kayan kamar Mai talla.


Ko kallon Inda muke batayi ba idonta yayi luhun luhum abinka da farar mace ta bud'e kofa tayi waje

Daga Ni har Naseer kallonta muke har ta fita ta sake dawowa babu Kayan a hannunta ta shiga d'akin shigarta da 'yan mintina sai Gata ta fito hannunta rik'e Dana Safiyya data tattale kafa tana tafiya dak'yar.

Basu kalli Inda muke ba suka fita Waje

Ganin Naseer babu alamar zai tashi yabi bayansu yaji dalilin tafiyarsu yasa na Kira sunansa cikin dashashen murya Ina "Naseer bazan so ku ringa samun Sab'ani da Umma ba
bazan so na zama silar da zatayi fushi dakai ba zaka iya sake Mata sau Dubu baka Isa ka sake Umma ba ka tashi kabi bayanta ka ce mata zaka sakeni ta Bari na haihu tunda na kusa haihuwa daga Nan sai mu dage da Addu'a idan da rabon mu cigaba da zama dakai zaka ga ta sauko idan babu rabo sai mu rabu Naseer ka tashi kabi bayanta Naseer daga abinda ya faru Dani a yau Allah ya kareni na yarda duk Wanda ya dogara da Allah
Allah zai isar Masa Yana sane Dani Kuma zai cigaba da kareni insha Allahu Amma dai mafita shine mu rabu muga ko Umma zata sauko ka tashi kaje Naseer"


Mik'ewa yayi batare da yacemin komai ba ya fita wajen

Yana fita yaga suna ta tafiya a kafa Sabida masu Abun Hawa duk basu fito ba Safiyya tana tafiya tana hutawa.


Binsu ya ringa yi a baya har sai da ya ci musu Yana ta yiwa Hajara magana ta share shi hakane yasa ya rik'e jakar hannunta sabida ta juyo aikuwa tana juyowa ta d'auke shi da wani irin Mari tana hucci

Naseer kuwa ya dafe kuncinsa cikin mamakin Marin data Masa alhalin shi tayiwa laifi Amma takeso tayi borin kunya

"A gaban idona ka fifita matarka a kaina Agaban idonka aka ringa dukana Ana kwallo Dani Naseer kana kallo amadadin ka kawomin d'auki sai ka jawo matarka ka rungumeta.

Agaban idonka aka shige da kanwarka daki maza sukayi layi akanta Suka Mata fyad'e baka Kai Mata d'auki ba ka rungume matarka Naseer karka manta fa Ni na raini cikinka har tsawon wata Tara nayi Nakuda na Haifeka kamar bazanyi Rai ba shayar dakai ne kawai banyi ba amma Naseer Agaban idona kake fifita matarka a kaina daka kawo min d'auki nida kanwarka gwara.ka rungume matarka Naseer Anya kana San kayi albarka kuwa Naseer Anya yarinya Nan Haka ta barka kuwa? Naseer ta ya bazan tsaneta ba ?
tayaya Zan sota ?Ba dai ka zabi Naeema a kaina ba toh kaje na yafe maka ita karka Kara nuna wa ka sani karka Kara kirana da Sunan Mahaifiyarka Naeema ta zama uwarka"

Naseer ji yayi kalmomin sun Masa tsauri ya tsugunna akan gwiwarsa Bai damu da awaje suke ba ya rungume.kafafun Hajara Yana "Umma ya kikeso nayi a rayuwata Umma mutanen nan ke Kika biyasu da kudinki akan suzo su kashe Naeema su mata fyad'e bansan Mai yasa Suka maida abin kanki da Safiyya ba Umma tayaya Zan kawo Miki dauki alhalin ke Kika Sansu tayaya Zan kawo Miki dauki alhalin da bindiga a hannunsu Umma Kinga keyata yanda suka fasamin da gindin bindiga Umma so kike kiga na mutu da Raina Umma Naeema Amana ce agareni nayiwa Iyayenta alkawarin riketa da Amana Bata da kowa sai Ni Bata San danginta ba ta Haifa min Yaya uku ga na hudu a cikinta Umma idan na rabu da ita Ina zata je umma idan na rabu da ita wa zai Kular min da yayan data haifamin Umma Mai yasa bakya tausayin Naeema"?


"Sabida bana santa Naseer sabida ka nuna itace rayuwarka sabida ka nuna tafiye maka kowa rayuwarka Naseer bana San Naeema Kuma bazan tab'a santa ba wlh idan kana San albarka ta ka saketa bansan a baya ba tsanar ta nayi ba sai yanzu danaga ta silarta an min duka kana kallo ta silarta maza bakwai sunyi wa yata Fyad'e kaje Naseer ka tafi kawai na yafeka"


Daga Haka Umma ta hankada Naseer ta d'auki Jakarta tare da Jan hannun Safiyya suka cigaba da tafiya Naseer kasa motsi yayi ya zuba musu Ido har Suka tare taxi Suka shige suka tafi.

Naseer dak'yar ya dawo gida sabida jirin dake dib'arsa

Ahaka ya dawo gida ya sameni Akan sallaya Bai cemin komai ba ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa da kayan jikinsa sai daya gaji ya d'aura alwala ya fito ya tada sallahr asuba Yana iddarwa ya kwanta akan Sallaya ya rike kansa da hannu biyu sabida Sara masa da kansa keyi.

A ranar Sabida tashin hankali ko makaranta su Zahira basu je ba Abu kamar Wasa sai gashi zazzabi ya kwantar da Naseer har tsawon sati daya tuni na hau jinyarsa Naseer yayi wani irin Rama sosai na hau tausayinsa inaso ya samu lafiya muyi magana Dan bana so ya cutu ta silata.

Ranar da aka samu kwana takwas da tafiyarsu Umma ya Dan ji kwarin jikinsa Ina tararsa da maganr ya sukayi da Umma yacemin na ajiye maganar Nan a gefe sai na haihu kamar yanda nace din Dan Allah Kar na sake tayar Masa da maganar.


Haka kuwa akayi ban Kara yiwa Naseer maganar ba duk da Ina cikin Zullumi da tashin hankali nafi tsoron Umma yanzu akan da fatana Kar ta min wani Abu har na samu na haihu lafiya.

Naseer kuwa sosai Naga ya dage da Addu'a kamar yanda ya Saba Zan iya cewa baccin awa biyu kawai yakeyi.

Nima ban saki jiki ba duk da tsohon cikina Haka na dage da Addu'a Nima.

Haka Naseer ya cigaba da kula Dani Yana min rubutu Ina Sha ahaka har Allah ya saukeni lafiya na Kara haihuwar mace.


Naseer kuwa a fuskarsa sai Dana ga baiyi wani doki ba addua kawai ya mata ya saka Mata Aisha zaa na kiranta Humaira.

Bamuyi taron suna ba raguna biyu kawai ya siyamin ya siya Mana komai na bukata.

Naseer Bai fito ya fadamin ba Amma Ni nasan Yana cikin damuwa Dan tunda Umma ta tafi yayi wani irin Rama Kuma Ni nasan tunani ne ya haddasa masa ramar tunda Naga Umma Bata biyoshi ta dawo ba nasan kila fushi tayi sosai.

Kwanana talatin da haihuwa yacemin zaije Calaba wajen Mallam Musbahu daga Nan zaije wajen Umma suyi magana"

Haka kawai naji jikina yayi sanyi adduar dawowa lafiya nayi Masa ya shirya ya tafi bayan ya cikani da kudi......
[6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Naeema ta bani sako na Baku tana karanta labarin haka ma yaranta comment din ma mutane duk tana Gani tace ace muku ta gode da Kaunar da kuke nuna Mata har da masu San ganinta duk ta gode ahaka ma da baa tsunduma cikin labarin ba inaga an fara labarin ta roki arzikin a daina yawan tsinewa Hajara ko Dan Naseer uban yayanta duk da shi baima San Ana rubuta labarin ba ita dai fatanta a nema Mata adduar Shiriya tagane Kar abin ya Mata yawa akwai dalilin daya sa take so asan labarinta ta na mik'a sakon gaisuwa ga duk masu bibiyar labarin ita Kuma Mai rubutawan Allah ya bata ikon rubuta duk labarin.


Naga dayawa wasu na tambayar Inda Mahaifin Naseer yake ya baa sake Sako shi a labarin ba duk Wanda ya karanta daga page one zuwa 5 a karshen page 5 nace muku mahaifinsa ya mutu wayanda basu karanta wajrn ba su duba page 5

*Page 15*


Yana Isa Calabar Bai zarce ko'ina ba sai wajen Mallam Musbahu dan ko wancan zuwan da yayi Bai samu zuwa wajensa ba


Sai dayaci abinci ya huta mutane Suka ragu daga wajen Mallam Musbahu kafin Naseer ya Isa wajensa.

Gaisawa sukayi kafin Naseer ya fara fada Masa duk halin da yake ciki da yanda suka rabu da Hajara da Kuma shawarar da Naeeema ta bashi shi kam Yana cikin tsaka Mai wuya Dan Allah Mallam Musbahu ya taimaka masa da shawara shi kam Bai San ya zaiyi ba


Murmushi Mallam Musbahu yayi Yana "Naseer a gaskiya na Dade Banga Mai irin Halin mahaifiyarka ba nidai a ganina kayi istahara Nima Zan maka insha Allahu idan har rabuwarku da Naeema shi yafi alheri gwara ku rabu Dan a gaskiya Mahaifiyarka Bata San Naeema Kuma zata iya komai Dan ta ta cima burinta tunda Naga halin da suka fara jefa ta a ciki nake balain tausayinta shiyasa tunda kuka tafi tana cikin Addu'oi na dani nasan Mahaifiyarka bazata tab'a barinta ba Amma tunda abin ya Kai ga ta hayo mutane Dan kawai a kasheta toh a ganina gwara ku hakura da juna kawai"


"Mallam Inasan Naeema banasan rabuwa da ita yanzu idan na rabu da ita waye zai kularmin da yarana sanan ita Naeema wajen wa zataje ita da Bata da kowa wlh Mallam Ina balain Tausayinta Bata da kowa sai Allah sai Ni"

Toh ya zakayi Naseer ai bance lailai ku rabu ba ce maka nayi kayi istahara Nima Zan tayaka zuwa gobe insha Allah idan zama Bai Kare a tsakaninku ba sai mu San yanda zamu b'ullowa mahaifiyar taka"


Sosai Naseer Yaji ya rasa Mai ke Masa dadi tunda ya auri Naeema Bai tab'a hararo wa kansa rabuwa da ita ba zancen ma rabuwa da ita Bai taso ba zai dai dage da Addu'a Akan Allah ya kawo masa d'auki ya sa mahaifiyarsa ta sauko.

Naseer tsabar fargaba kasa ma istaharan yayi sai Mallam Musbahu ne yayi istaharan na kwana uku

Inda washegari ya Kira musbahun Yana "Mallam Naseer nayi istahara sosai Akan Kai da Naeema Zama Bai Kare a tsakaninku ba akwai ma sauran rabo a tsakaninku insha Allahu

Amma matsalar bansan ta yanda zaka b'ullowa mahaifiyar ka ba Amma Ina ganin zaka rakani wajenta Zan rok'eta na kuma Mata nasiha akan ta barka da matarka karta rabaku Amma idan Taki Naseer Kayi Mata biyayya ka hakura da Naeema inyaso sai ka dage da Addu'a idan da akwai rabon ku cigaba da zama sai kaga ta dawo maka"


Naseer Sam baiji zai iya rabuwa da Naeema ba ya dai yarda Zai Kai Mallam Musbahu ya roki Mahaifiyar tasa kila ya samu ta ji maganarsa.

Da Yamma Mallam Musbahu ya shirya shi da Naseer suka nufi gidan Naseer da ya zama na Hajara.

Suna Isa k'ofar Gidan Gaban Naseer ya hau fad'uwa haka kawai yaji Yana tsoron had'uwa da ita

Kwankwasa wa sukayi sai da suka Dade kafin suji takun tahowa Ana bud'e k'ofar suka ga Hajara ce da kanta tana sanye da bak'ar doguwar Riga.

Tana had'a Ido da Mallam Musbahu ta juya da Sauri tana k'ok'arin rufe k'ofar

Mallam Musbahu kuwa tura k'ofar da karfinsa Dan yasan za'ayi Haka yasan Dole idan ta ganshi ta tsorata

Ja baya tayi da Sauri ta kalli Naseer dake bayansa tana "Mai yasa ka kawomin wanan gidana"?

Murmushi Mallam Musbahu yayi Yana "Ni na saka ya kawoni Kuma ba abinda kike tunani bane ya kawoni Ni banida wani had'i dake Dan Haka ki kwantar da hankalinki muyi magana"



Hajara kwarjinin da yayi Mata yasa ta kasa musa Masa ta samu waje daga tsakar gidan ta zauna tana jifan Naseer da harara.

Mallam Musbahu babbar rigarsa ya nade ya zauna Akan dakalin daya gani.

Naseer kuwa ya shiga ciki ya d'auko tabarma ya shimfida ya zauna Mallam Musbahu kuwa yace ya barshi daga Inda yake zaune


Naseer kuwa sai gaishe da Hajara yake ta had'e Rai taki kallonsa


Mallam Musbahu gyaran murya yayi Yana "Mmn Naseer wajenki Nazo Dan muyi wata magana da Kuma rokon arziki da Kuma wata Yar Nasiha da Zan miki


Mmn Naseer Duk halin da kike ciki keda Naseer nasani duk wani Hali da kike ciki nasani Abu daya nakeso kisani Allah ya hallicemu ne Dan mu bauta Masa Bai hallicemu Dan muzo mu ringa zalintar juna ba nadai San kin fahimci maganata Naseer da kike gani yarone Mai hankali da ladabi kema kinsani Naseer zai iya amfani da ilimin da Allah ya bashi ya kawo karshen zaluncin da kikeyi Amma Sabida darajar ke mahaifiyarsa ce ya kyalleki bansan dadin da kikeji a halin da Kika jefa kanki ba bansan dadn da kikeji a sab'awa Allah da kikeyi ba Abu daya kawai Zan Gaya miki wlh kiji tsoron Allah kiji tsoron ranar da Zaki mutu ki tsaya a gaban Allah da littafinki a hannunki duniya ba gidan Zama bane gwara tun lokaci Bai Kure Miki ba ki tuba ki koma ga Allah ki nemi wayanda Kika zalunta ki nemi yafiyarsu idan ba Haka ba wlh ki rubuta ki ajiye zakiyi nadama a lokacin da bashida amfani Kar biyan bukata ta duniya ta saka ki ki yanki ticket din da Zaki dawwama a wutar jahanama karki dauka mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi duk tastuniya ce wlh ba tatsuniya bace gaskiya ce nasan dai kinsan wayanda suka mutu toh basu bambanta damu ba ba kuma.wasu hallittar bane su mutane ne irinmu gwara ki shiga hankalinki ki nutsu tun kafin lokaci ya kure Miki na sauke nauyin dake kaina na Gaya miki gaskiya ruwanki ne ki dauka ko akasan Haka


Sanan magana ta biyu inaso na Dan Allah ki bar Naseer ya zauna lafiya da matarsa idan yaso duk wani Abu da kikeso sai ya Miki uwa fa an Santa da Kaunar Dan data Haifa da Kuma San farincikin danta sabida me kike San ki raba Naseer da Naeema,Mai yarinya ta Miki Kika tsaneta Haka"?



Hajara sosai take Jin shakar iska na neman Yi Mata wahala sabida waje daya da suka zauna da Mallam Musbahu har wani zafi zafi takeji a jikinta gashi ji take kamar ya daudaureta yau badan shi bane bata Jin akwai Wanda ya Isa ta tareta da wandanan maganganun

"Ni kawai bana santa ne sabida Naseer ya Fifita ta akaina bana santa bana kaunarta sanadinta ba irin masifar da ban gani ba Dan Haka Ina Kan bakana ko Naseer ya rabu da ita ko ya canja wata uwar"?

Tace tana jijiga kafa

Naseer durk'usawa yayi akan gwiwarsa ya hau Bata hakuri akan ta barshi da Naeema Wanda Naseer Bai San hakan balain kona Mata Rai yake


"Ki dai Yi hakuri mmn Naseer ki barshi ya zauna da matarsa idan yaso ki gindaya Masa duk sharadin da kikeso"?


Shiru Hajara tayi Tana tunanin duk shawarwarin da Yan kungiyarsu Suka Bata da hanyar da zasu bi cikin sauki su raba Naseer da Naeema


"Naji Zan yarda ya cigaba

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment