Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ALIYU GADANGA Complete Hausa Novel Document by ALIYU GADANGA


ALIYU GADANGA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 113526



ALIYU GADANGA

Reading Time: 9 Hours

Added On: 02, Mar 2025

Author: Janafty ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Intelligent writer's asso..

Author Phone : 09060067488, 07065481260

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 635.1 kb

File Type: txt

Views: 102+

Download: 194+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldeir man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:JANAFTY*💖

*DEDICATED TO MY MOMMAH..,HAUWA .S.ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘,Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

*Bismillahir Rahmanir Rahim in the Name of Allah,The most beneficient The most mercifull praise be to Allah lord of the words*

*Assalamu Alaikum my Janafty Real Fans,am Starting my new Novel,i ask Allah Subhannahu wata'ala to guide me Throught and make it Successful till the end,and the Story is a Fiction,duk Abunda  mutum yagani ko ya cikaro dashi na Suna,ko na halayyah,kona gari,duk an sane don kawata lbri*

•WARNING: ŃO PÁŔŤ OŦ ŤĤĨŚ PÚßĹĨČÁŤĨOŃ ŚĤOÚĹĎ ßĔ ŔĔPŔOĎÚČĔĎ,ĎĨŚŤŔĨßÚŤĔĎ OŔ ŤŔÁŃŚMĨŤŤĔĎ ĨŃ ÁŃŶ ŦOŔM OŔ ßŶ ÁĹĹ MĔÁŃŚ,ĨŃČĹÚĎĨŃĞ ŔĔČOŔĎĨŃĞ OŔ ÁŃŶ OŤĤĔŔ ĔĹĔČŤŔOŃĨČ MĔŤĤOĎŚ ŴĨŤĤOÚŤ ŤĤĔ PŔĨOŔ ŴĨŔŤŤĔŃ PĔŔMĨŚŚOŃ OŦ ŤĤĔ PÚßĹĨŚĤĔŔ,ŚO ßĔ ŴÁŔŃĔĎ!!!*


         *Chapter 1*

*GOMBE*

     """Ababban masallacin dake anguwan nan ta masu hali,wato *FEDERAL LOWCOST* Motocine suka cika anguwan Tundaga farkon farata har karshenta,layin mallacin kuwa babu matsaka tsinke saboda yadda motoci suka hada uban gowslow,kana kallon wajen zaka tabbatar da tabbas wani kusane agawannati yake Aure yau,dayake ranar takama Ranar karshen sati ne,wato asabar,Abunda zai baka mamaki,sojojin kasa ne wato army birjit awajen sanye da kakinsu suna mazurai,gefe daya kuma yan sanda ne,suma kamar anyi hayansu,sai gyara parking suke.

  Tawagar ango ce tafara isowa cikin hadaddun motocinsu na alfarma Kirar venza2019,sai 306 kirar toyota,607kirar toyota,sai Benz,bayansu kuma motar sojojine,suna tafe da jiniyansu bindigogine ahannunsu da bulalai suna wani zare ido,Abun tsoro,tuni jama"a Aka dinga darewa domin kowa na tsoron ya gifta soja ya fallamai dorina wacce kila sai ya kwana goma yana jinya bai warke ba.

Motocinsu basu gama tsayawa ba,jiniyar motocin mai girma Kwamishinar jahar Gombe tafarayima mutane maraba wato *CP AHMED SIDI NA IYA* Tare da tawagarsa,suna zuwa suka faka motocinsu nan da nan yan sandan dake biye dasu suka hau bude musu motocin suna bayyana,tabbas inda ake biki chan ake,domin manyan mutane ne,suke Fitowa cikin shigata alfarma,dukkansu sanye cikin wasu dakakkun shaddodi gezner suna daukan ido,da hulunansu zannah bukar,suna fitowa basu tsaya wajen mutane ba,suka shiga cikin massllacin bayan an buda musu hanya,yan jaridu kuwa sukayi yamm dasu suna kokarin, sonjin ta bakin kwamishinan ammh masu tsaranshi basu bada damar haka ba,kakkaresa sukayi har ya danganta da cikin massllacin inda waliyan ango da sauran manyan mutane,harda babban limamin masallacin,suke jiransu domin Daura Auren

 
*JABIR* ya kallesa ganin yadda yawani kishingida kamar yana kwance adakin matarsa yace"Mallam wai bazaka fito bane,kaga fa maigirma kwamishina ya iso,yanzu za"a daura maka ka Aure ka tabbata miji ga *NI"IMATULLAHI AHMED SIDI NA IYA..* "Yafada lokacin daya yana leka kansa cikin gaban motar...

    Yafi minti  goma bai dagoba kuma baiyi mgana ba, *HAISAM* ya gyara tsayuwa yana fadin"Kaga captain zo muje rabu dashi,Kila bai da ra"ayin isa cikin masallacin ne,mu muje saboda mu muntunta abotaka da kuma zaman tare.."Yafada daidai lokacin da suka Fito daga motar dukkansu,mazaje ne dogaye majiya karfi,kallo farko in kayi musu zaka fahimci tsantsan ilimi da wayewa ya ratsatsu,Kyawawa ajin farko ne,daka kallesu sai kara kallonsu saboda yadda suka dau wanka,cikin wani Ubansu yadi,mai ruwan kasa,wanda yanayin yadda yake yarari kadai ya isa yafadamaka sai da aka tada kai akayi iya mallakarsa, kafafunsu duka sanye da wani Brown din takalmin na fatar damisa,ayayinda kansu ke sanye da hula zannah bukar,kuma dukkansu dasame dressing ne ajikinsu,in ka gansu daga nesa kamar wata daren goma sha daya saboda yadda suke haskawa.

Ganin da gaske suke,basu jira cewarsa ba,suka dumfaru cikin masallacin domin Saura Dan mintocine adaura auren,yan jarida daga nesa suke hangosu,domin sojojin sunyi musu katanga tsakaninsu,to soja babu wargi dole sukayi gefe,Cikin wani takama da aji ya sanya tattausan hannunsa mai cike da gargasa wanda ke daure da wani royal watch mai kyau da yarari, ya bude murfin motar ya zuro kafarsa wacce ta kasance farace,ammh tana da Launin ja,kafar nasa tana sanye cikin wani ubansu Rufaffan takalmim brown colour na fatar damisa,kafar nasa itama tana cike da gargasa domin gayinan yayi kwance luf dashi,ban saki da al"amarin gayen ba,sai da duka jikinsa ya bayyana awaje,bansan sadda biron dayake hannuna ba ya subuce saboda yadda girma da haiba tare da wani kwarjini suka dakeni lokaci daya.

tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan kyakyawan halitar,dogon mutum ne,karkafa mai yalwal Fadin kirji da girman jiki kamar ingarma,fari ne tas,mai Launin ja,Hancinsa har baka yake,mai zagaye da wani bakin Saje wanda ke karamai kwarjini da haiba, kwayan idonsa tamkar wanda aka digamai daimond,saboda yadda yake wani haskawa,Yana da manyan idanu,matsaikata,wanda in ya lumshe su,sai ka zata yayi kari,wa gashin idon nasa,don ko wata mace albarka..,bakinsa dan karami ne,wanda ke dauke da wasu pick din lip masu kyau da burgewa,Kansa yana nannade dawani murdadden bakin gashi kamar wanda yayi kari,Ko fuskarsa badon yana yawan askewa ba,akwai kananan gashi da sukayi mai kwamce,Shima din sanye yake da yadi mai ruwan kasa,irn na abokansa,hatta dinkinshi iri dayane sai dai Shi harda babban riga,Hulan kansa ma irin nasu ne,sai da yadda kayan ya amsheshi dabam ne,Kana kallonsa zaka fahimci mai karfi ne shi,saboda yadda mucsles suke yawo ajikinsa,har ana iya ganinsu,Kana kallon Fuskarsa zaka Fahimci yana da miskilanci da wani irin takama,yana da jan aji,ayanayi yadda yake wasu abubuwa sai ka dauka wani basarake ne,saboda komai cikin isa da iko yakeyinshi,baka iya hada ido dashi saboda yana da bala"in kwarjini babu wanda ya taba kallon tsabar idonshi na tsawon minti biyar ,saboda baiwace Allah yayimai mutane dadama basu iya kallonsa ido cikin ido Saboda yadda kwarjinshi yake tasiri azuciyar mutane.

   *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU*  kenan,kuma COMMANDER YAKI,wanda ke jagoranta bataliyoyin sojoji kashi da kashi zuwa filin daka,ko wani kwantar da tarzoma,Wanda ko afagen fama makiya tsoronsa sukeji,matashin Sojan kasa ne wanda ke aiki a barikin Kaduna wato 1division Nigerian Army kaduna,ko abokan aikinsa sun san waye Aliyu Tambari buzu saboda kwazonsa ga aikinsa ko manyansa ma,suna shakkarsa tare da jinjinamai domin kaf bacth dinsu babu na biyunsa ajajircewa da nuna jarumta...Sai da yawani jingina da kofar motar kafin ya dan Saki Fuskarsa ya fara takawa cikin takun nan nasa na isa da takama,sojojin dake karkashinsa sai kokarin karesa suke har ya samu nasaran Shiga cikin masallacin,kusa da Haisam ya zauna,wanda ke zaune kusa da jabir,gefensa kuma *MALLAM LAWAL BATURE* ne kafin kuma *KAWU BALA* dake gefensa shima cikin Shigan kayan alfarma.

An matso domin fara gudanar da Daurin Aure kani ga kwamishina ya kira kwamishinan gefe suka danyi wasu mganganu Tunda kawu bala yaga haka, sai ya sha jinin jikinsa,yana fata wannan karon kada ayi musu gagarumin wulakanci da zasu kasa mantawa dashi,suna dawowa Sai kani ga Kwamishina ya kalli kawu bala yace"Ina waliyan ango su matso kusa adaura aure.."Yafada yana kallonsa batare da wani Tunani ba kawu bala ya matsa yana fadin"Gani,ai inaga basai ka tambaya ba,tunda ko neman Auren wajenka na neman ma Aliyu.."Yafada Shima kai tsaye.

Bude bakinsa sai cewa yayi"waliyin ango nace,ma"ana Waliyi daga *DANGIN MAHAIFINSA* bakai ba.."Gabadaya kawu bala yaji miyan bakinsa ya kafe,dayake mganar bata karfi akeyinta ba,su Aliyu dake gefe basu wani ji,su azatonsu Ana gudanar da Daurin Auren ne,Kawu bala ya kalli mallam lawal kafin yace"Eh to ai mun fadamuku Dangin Mahaifinsa basu akusa,Shiyasa muka gudanar da komai.."Kwamishina ya murmusa kafin yace" *BALA SHEHU AKARAMI* Shine cikakken Sunanka,kuma  kaine kwamishinar yada lbrai NA ajahar kaduna,kuma kai yaya kake ga mahaifiyar Aliyu,Tunda kuka gudanar da neman Aure bawani daga dangin baban yaran,kenan ya tabbata da gaske bashi da uba,Balle Asali.."

  Arazane kawu bala yace"Haba Ranka yadade wani irin mgana ne,haka baya da uba daga sama ya fado,kaga mubar wannan mganar,adaura Auren Allahbarshi bayan angama sai muyi mgana.."Yafada cikin alamar roko,kani ga kwamishina yace"Sam wannan mgana bamai yuyu bane,bazamu bada Auren diyanmu ga bara gurbi ba,matukar wani daga halin mahaifinsa baizo ba,to an fasa Daura Auren kowa ya watse..'"Ai sai waje ya kaure da hayaniya tawagar Kawu bala sunata maganganu Mallam lawal ya rike kafadan bala alamar lallashi.
 

Kawu bala yakalli kwamishina yace"kar kayi haka Ranka ya dade ka duba girman jama"an daka tara,dawanda ni na tara,da wanda Shi yaron ya tara,kabari adaura auren nayimaka alqawarin koma miye daga baya sai muyi mgana,don Allah na rokeka..."Yafada harda hada hannu,ammh sai kwamishina ya girgiza kai ya mike,liman dake zaune yana fadin"Subhannallah wai mike Faruwane,kada kubari Shedan yayi Tasiri akanku,yahanaku kullah Alheri mana.."Ammh ina Tuni kwamishina da kaninsa da nasu tawagan sun Fice daga massllacin kawu bala ya bisu da kallo kamar ya zubda da kwallah,babu wanda yake Tunani sai *SUWAIBA* yazataji in tasamu wannan lbrin ta Aliyu mai sauki ne.

  Tuni Su Jabir dake zaune suka fara Fahimtar Abunda ke faruwa,tun sadda su kwamishina suka mike,arazane Haisam ke kallon Aliyu wanda yayimai kuri da ido yana kallonsa kafin yace cikin wata murya mai cike da amon tashin hankali..'Haisam meke Faruwane,fata dai ba Abunda nakeji bane ko? yafada yana kafesa da ido,bai samu
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ALIYU GADANGA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album