Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldeir man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:JANAFTY*💖

*DEDICATED TO MY MOMMAH..,HAUWA .S.ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘,Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

*Bismillahir Rahmanir Rahim in the Name of Allah,The most beneficient The most mercifull praise be to Allah lord of the words*

*Assalamu Alaikum my Janafty Real Fans,am Starting my new Novel,i ask Allah Subhannahu wata'ala to guide me Throught and make it Successful till the end,and the Story is a Fiction,duk Abunda  mutum yagani ko ya cikaro dashi na Suna,ko na halayyah,kona gari,duk an sane don kawata lbri*

•WARNING: ŃO PÁŔŤ OŦ ŤĤĨŚ PÚßĹĨČÁŤĨOŃ ŚĤOÚĹĎ ßĔ ŔĔPŔOĎÚČĔĎ,ĎĨŚŤŔĨßÚŤĔĎ OŔ ŤŔÁŃŚMĨŤŤĔĎ ĨŃ ÁŃŶ ŦOŔM OŔ ßŶ ÁĹĹ MĔÁŃŚ,ĨŃČĹÚĎĨŃĞ ŔĔČOŔĎĨŃĞ OŔ ÁŃŶ OŤĤĔŔ ĔĹĔČŤŔOŃĨČ MĔŤĤOĎŚ ŴĨŤĤOÚŤ ŤĤĔ PŔĨOŔ ŴĨŔŤŤĔŃ PĔŔMĨŚŚOŃ OŦ ŤĤĔ PÚßĹĨŚĤĔŔ,ŚO ßĔ ŴÁŔŃĔĎ!!!*


         *Chapter 1*

*GOMBE*

     """Ababban masallacin dake anguwan nan ta masu hali,wato *FEDERAL LOWCOST* Motocine suka cika anguwan Tundaga farkon farata har karshenta,layin mallacin kuwa babu matsaka tsinke saboda yadda motoci suka hada uban gowslow,kana kallon wajen zaka tabbatar da tabbas wani kusane agawannati yake Aure yau,dayake ranar takama Ranar karshen sati ne,wato asabar,Abunda zai baka mamaki,sojojin kasa ne wato army birjit awajen sanye da kakinsu suna mazurai,gefe daya kuma yan sanda ne,suma kamar anyi hayansu,sai gyara parking suke.

  Tawagar ango ce tafara isowa cikin hadaddun motocinsu na alfarma Kirar venza2019,sai 306 kirar toyota,607kirar toyota,sai Benz,bayansu kuma motar sojojine,suna tafe da jiniyansu bindigogine ahannunsu da bulalai suna wani zare ido,Abun tsoro,tuni jama"a Aka dinga darewa domin kowa na tsoron ya gifta soja ya fallamai dorina wacce kila sai ya kwana goma yana jinya bai warke ba.

Motocinsu basu gama tsayawa ba,jiniyar motocin mai girma Kwamishinar jahar Gombe tafarayima mutane maraba wato *CP AHMED SIDI NA IYA* Tare da tawagarsa,suna zuwa suka faka motocinsu nan da nan yan sandan dake biye dasu suka hau bude musu motocin suna bayyana,tabbas inda ake biki chan ake,domin manyan mutane ne,suke Fitowa cikin shigata alfarma,dukkansu sanye cikin wasu dakakkun shaddodi gezner suna daukan ido,da hulunansu zannah bukar,suna fitowa basu tsaya wajen mutane ba,suka shiga cikin massllacin bayan an buda musu hanya,yan jaridu kuwa sukayi yamm dasu suna kokarin, sonjin ta bakin kwamishinan ammh masu tsaranshi basu bada damar haka ba,kakkaresa sukayi har ya danganta da cikin massllacin inda waliyan ango da sauran manyan mutane,harda babban limamin masallacin,suke jiransu domin Daura Auren

 
*JABIR* ya kallesa ganin yadda yawani kishingida kamar yana kwance adakin matarsa yace"Mallam wai bazaka fito bane,kaga fa maigirma kwamishina ya iso,yanzu za"a daura maka ka Aure ka tabbata miji ga *NI"IMATULLAHI AHMED SIDI NA IYA..* "Yafada lokacin daya yana leka kansa cikin gaban motar...

    Yafi minti  goma bai dagoba kuma baiyi mgana ba, *HAISAM* ya gyara tsayuwa yana fadin"Kaga captain zo muje rabu dashi,Kila bai da ra"ayin isa cikin masallacin ne,mu muje saboda mu muntunta abotaka da kuma zaman tare.."Yafada daidai lokacin da suka Fito daga motar dukkansu,mazaje ne dogaye majiya karfi,kallo farko in kayi musu zaka fahimci tsantsan ilimi da wayewa ya ratsatsu,Kyawawa ajin farko ne,daka kallesu sai kara kallonsu saboda yadda suka dau wanka,cikin wani Ubansu yadi,mai ruwan kasa,wanda yanayin yadda yake yarari kadai ya isa yafadamaka sai da aka tada kai akayi iya mallakarsa, kafafunsu duka sanye da wani Brown din takalmin na fatar damisa,ayayinda kansu ke sanye da hula zannah bukar,kuma dukkansu dasame dressing ne ajikinsu,in ka gansu daga nesa kamar wata daren goma sha daya saboda yadda suke haskawa.

Ganin da gaske suke,basu jira cewarsa ba,suka dumfaru cikin masallacin domin Saura Dan mintocine adaura auren,yan jarida daga nesa suke hangosu,domin sojojin sunyi musu katanga tsakaninsu,to soja babu wargi dole sukayi gefe,Cikin wani takama da aji ya sanya tattausan hannunsa mai cike da gargasa wanda ke daure da wani royal watch mai kyau da yarari, ya bude murfin motar ya zuro kafarsa wacce ta kasance farace,ammh tana da Launin ja,kafar nasa tana sanye cikin wani ubansu Rufaffan takalmim brown colour na fatar damisa,kafar nasa itama tana cike da gargasa domin gayinan yayi kwance luf dashi,ban saki da al"amarin gayen ba,sai da duka jikinsa ya bayyana awaje,bansan sadda biron dayake hannuna ba ya subuce saboda yadda girma da haiba tare da wani kwarjini suka dakeni lokaci daya.

tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan kyakyawan halitar,dogon mutum ne,karkafa mai yalwal Fadin kirji da girman jiki kamar ingarma,fari ne tas,mai Launin ja,Hancinsa har baka yake,mai zagaye da wani bakin Saje wanda ke karamai kwarjini da haiba, kwayan idonsa tamkar wanda aka digamai daimond,saboda yadda yake wani haskawa,Yana da manyan idanu,matsaikata,wanda in ya lumshe su,sai ka zata yayi kari,wa gashin idon nasa,don ko wata mace albarka..,bakinsa dan karami ne,wanda ke dauke da wasu pick din lip masu kyau da burgewa,Kansa yana nannade dawani murdadden bakin gashi kamar wanda yayi kari,Ko fuskarsa badon yana yawan askewa ba,akwai kananan gashi da sukayi mai kwamce,Shima din sanye yake da yadi mai ruwan kasa,irn na abokansa,hatta dinkinshi iri dayane sai dai Shi harda babban riga,Hulan kansa ma irin nasu ne,sai da yadda kayan ya amsheshi dabam ne,Kana kallonsa zaka fahimci mai karfi ne shi,saboda yadda mucsles suke yawo ajikinsa,har ana iya ganinsu,Kana kallon Fuskarsa zaka Fahimci yana da miskilanci da wani irin takama,yana da jan aji,ayanayi yadda yake wasu abubuwa sai ka dauka wani basarake ne,saboda komai cikin isa da iko yakeyinshi,baka iya hada ido dashi saboda yana da bala"in kwarjini babu wanda ya taba kallon tsabar idonshi na tsawon minti biyar ,saboda baiwace Allah yayimai mutane dadama basu iya kallonsa ido cikin ido Saboda yadda kwarjinshi yake tasiri azuciyar mutane.

   *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU*  kenan,kuma COMMANDER YAKI,wanda ke jagoranta bataliyoyin sojoji kashi da kashi zuwa filin daka,ko wani kwantar da tarzoma,Wanda ko afagen fama makiya tsoronsa sukeji,matashin Sojan kasa ne wanda ke aiki a barikin Kaduna wato 1division Nigerian Army kaduna,ko abokan aikinsa sun san waye Aliyu Tambari buzu saboda kwazonsa ga aikinsa ko manyansa ma,suna shakkarsa tare da jinjinamai domin kaf bacth dinsu babu na biyunsa ajajircewa da nuna jarumta...Sai da yawani jingina da kofar motar kafin ya dan Saki Fuskarsa ya fara takawa cikin takun nan nasa na isa da takama,sojojin dake karkashinsa sai kokarin karesa suke har ya samu nasaran Shiga cikin masallacin,kusa da Haisam ya zauna,wanda ke zaune kusa da jabir,gefensa kuma *MALLAM LAWAL BATURE* ne kafin kuma *KAWU BALA* dake gefensa shima cikin Shigan kayan alfarma.

An matso domin fara gudanar da Daurin Aure kani ga kwamishina ya kira kwamishinan gefe suka danyi wasu mganganu Tunda kawu bala yaga haka, sai ya sha jinin jikinsa,yana fata wannan karon kada ayi musu gagarumin wulakanci da zasu kasa mantawa dashi,suna dawowa Sai kani ga Kwamishina ya kalli kawu bala yace"Ina waliyan ango su matso kusa adaura aure.."Yafada yana kallonsa batare da wani Tunani ba kawu bala ya matsa yana fadin"Gani,ai inaga basai ka tambaya ba,tunda ko neman Auren wajenka na neman ma Aliyu.."Yafada Shima kai tsaye.

Bude bakinsa sai cewa yayi"waliyin ango nace,ma"ana Waliyi daga *DANGIN MAHAIFINSA* bakai ba.."Gabadaya kawu bala yaji miyan bakinsa ya kafe,dayake mganar bata karfi akeyinta ba,su Aliyu dake gefe basu wani ji,su azatonsu Ana gudanar da Daurin Auren ne,Kawu bala ya kalli mallam lawal kafin yace"Eh to ai mun fadamuku Dangin Mahaifinsa basu akusa,Shiyasa muka gudanar da komai.."Kwamishina ya murmusa kafin yace" *BALA SHEHU AKARAMI* Shine cikakken Sunanka,kuma  kaine kwamishinar yada lbrai NA ajahar kaduna,kuma kai yaya kake ga mahaifiyar Aliyu,Tunda kuka gudanar da neman Aure bawani daga dangin baban yaran,kenan ya tabbata da gaske bashi da uba,Balle Asali.."

  Arazane kawu bala yace"Haba Ranka yadade wani irin mgana ne,haka baya da uba daga sama ya fado,kaga mubar wannan mganar,adaura Auren Allahbarshi bayan angama sai muyi mgana.."Yafada cikin alamar roko,kani ga kwamishina yace"Sam wannan mgana bamai yuyu bane,bazamu bada Auren diyanmu ga bara gurbi ba,matukar wani daga halin mahaifinsa baizo ba,to an fasa Daura Auren kowa ya watse..'"Ai sai waje ya kaure da hayaniya tawagar Kawu bala sunata maganganu Mallam lawal ya rike kafadan bala alamar lallashi.
 

Kawu bala yakalli kwamishina yace"kar kayi haka Ranka ya dade ka duba girman jama"an daka tara,dawanda ni na tara,da wanda Shi yaron ya tara,kabari adaura auren nayimaka alqawarin koma miye daga baya sai muyi mgana,don Allah na rokeka..."Yafada harda hada hannu,ammh sai kwamishina ya girgiza kai ya mike,liman dake zaune yana fadin"Subhannallah wai mike Faruwane,kada kubari Shedan yayi Tasiri akanku,yahanaku kullah Alheri mana.."Ammh ina Tuni kwamishina da kaninsa da nasu tawagan sun Fice daga massllacin kawu bala ya bisu da kallo kamar ya zubda da kwallah,babu wanda yake Tunani sai *SUWAIBA* yazataji in tasamu wannan lbrin ta Aliyu mai sauki ne.

  Tuni Su Jabir dake zaune suka fara Fahimtar Abunda ke faruwa,tun sadda su kwamishina suka mike,arazane Haisam ke kallon Aliyu wanda yayimai kuri da ido yana kallonsa kafin yace cikin wata murya mai cike da amon tashin hankali..'Haisam meke Faruwane,fata dai ba Abunda nakeji bane ko? yafada yana kafesa da ido,bai samu zarafin bashi amsa ba kawu bala ya kalli jabir yace"Ku sanar da jama"a anfasa Daurin Aure,kowa yakama gabansa..."

  DAM!zuciyar Aliyu ta buga Kuri yayima kawu da ido kafin yayi mgana Mallam lawal bature yace"A"a bala,baza'a yi Saurin sanar da haka ba,Duk wanda yake kokarin tonama wani asiri Allah bazai barshi ba,yanzu za"a Daurama Aliyu Aure anan wajen Insha Allahu.."Dukkansu ido suka samai kafin Kawu bala yace"To dawa,lawal?kana ganin fa wulakancin dasukayi mana..?"

  Mallam lawal yace yana kallon Aliyu kai tsaye yace" Da..,Da.. *AZEEMA* za"a Daura in ka yarda,saboda babu dadi atara wanan jama"ar kuma ace musu anfasa Daurin Aure,hakan bai dace ba,shiya...'.Zuruf Kawu bala ya mike kafin ya damko hannun lawal yana fadin'Ku zauna mu dawo.."Yafada yana kallon jabir,ficewa sukayi zuwa kofar mallacin,nan suka ga yadda rabin mutanen suka watse,ammh wasu sun tsaya sai sunga kwal uwar daka,gefe kawu bala yajasa kafin ya ciro wayarsa yana fadin"bari na kira Suwaiba..'yafada daidai lokacin dayake kiran ta.

*************

Biki yayi biki,gida babu masaka tsinke,tana zaune *MADINA* ta shigo da waya ahannunta tana fadin" *GOGGO* gashi Daddy ne ke kiranki.."amsa goggo tayi tana fadin"Kila An Daura auren ne,kai Allah na godemaka gadanga yazama magidanci yau.."Tafada tana dariya lokaci daya tana daukan kiran da fadin"Assalamu Alaikum yaya..."dagachan bangaren ya amsa mata da fadin",Suwaiba..."Yadda yakira sunan natane,sai da gabanta ya fadi ta amsa bakinta na rawa kafin tace"Lafiya kuwa yaya? kowani Abun ne ya samu gadanga...? ajiyar zuciya ya sauke kan ya cigaba da zayyanamata Abunda ya faru cikin sauri yace"Za"a Daura mai Aure da AZEEMA diyar mallam lawal yan...."KU DAURA YAYA YANZU NAN DON ALLAH...."Ta fada cikin kuka kafin tacigaba da cewa cikin Fushi.."Ni dana ba Shege bane, yana da tarbiyar da diyarsu bata dashi,ku gudanar da komai haka Allah ya rubutu..."Tana gama fadin haka ta katse wayan tana share kwallah.

Basu tsaya bata lokaci ba,suka koma cikin massllacin sukayi mgana da liman cikin minti kadan Kawu bala ya fito da sadaki ya mika ma liman yana fadin'"Kayima Azeema walicci.."Babu bata lokaci akace amatso za"a Daura Aure,kafin kace me Tuni an Daura Auren *CAPTAIN ALIYU ABDULNASSER TAMBARI BUZU DA AZEEMA LAWAL BATURE* Akan sadaki mafi daraja,nan da nan maroka suka fara Shedan suna fadin"Allah kenan baya tsallake Abun da ya rubuta,Daurin Aure dai ya chanza,maimakon Ni"imatullahi yanzu Azeema ce mai sa"a Domin itace ta kasance mata ga Dan matashin Sojan,Allah kenan komai ya faru da saninka,kuma da izininka.."Suke fada suna shela,tuni waje ya hautsine kowa tambaya fal cikinsa,tun lokacin da tawagar kwamishina suka wuce batare da Dan Daura aure ba.

Captain Aliyu dayayi mutuwar zaune kansa aduke har akagama Daurin Aure bai dago ba,sai jabir ne,ya riko kafadansa yana fadin"Captain kayi ha..."Bai karisa ba yadago kansa idanunsa sun chanza kala jijiyoyin kansa sun Fito radau yace" Sunce baza su bani ba ko? bani da uba ,kamar yadda suke fadi..."Yafada kamar zai kifa saboda yadda kirjinsa ke tasawa,bai kara mgana ba,ya mike da sassarfa ya fice daga masallacin Da hanzari Haisam da jabir suka rufamai baya,yana Fitowa yan jarida sukayi cha suna watsamai tambayoyi wanda suke kara tunzurashi ai yana daga dago kansa ya daka musu tsawa yana fadin"Get Way from my Side..."Yafada afusace yana buga kafa kamar afilin daga,kamar mazari haka sukayi baya suna rawan jiki sojojin dake wajen da hanzari suka kame,ko kallonsu baiyi ba,ya nufi motarsu da suka zo acikinta Ya fada,ko kafin su Haisam su kariso yajata ya fice da wajen dawani mahaukacin gudu,dafe kai Jabir yayi yana fadin"Innalillahi..kada fa Aliyu ya kashe kansa,in yayi irin wannan Fushin fa sai Allah.."Haisam ya damke hannuwansa duka akirji yana fadin"Allah kawai ya kiyaye,ammh ina tsoron Fushin Aliyu kam.."Juyawa sukayi suka koma cikin wajen suna gaisawa da bakin da suka tara,haka suma su kawu bala cikin Farinciki da mura suke gaisawa da mutane suna musu godiya kamar babu Abunda yafaru,yan jaridu ko Haisam ya sallame su dole suka tafi,tunda bazasu samu Abunda sukaso suji ba.

Cikin wani Fushi yake Driving din Allah ne yakaisa *KAGARAWAL* lafiya Da wani banzan taka burki yafaka motar akofar gidansu dake cike da jama"a yan biki cikin Fushi da Wani karfi ya ture murfin motar ya fito yafara taku zuwa cikin gidan jama"an dake waje suka bisa da kallo,Azeema dake kokarin Fitowa zata koma gida,batama kalli gabanta ba,sai ji tayi anyi baya da ita an maidata zauren gidan,Cikin Tsoro Ta bude baki zata yanka ihu ya dakamata tsawa"Ke Shout up..."yafada yana zare mata ido,jin muryansa yasa jikinta yafara zikiri Bude ido tayi tana binsa da kallo yadda naman kirjinsa ke dagawa,ai sai Azeema taji wani Fitsari na neman kubcemata saboda tsoro cikin Tsawa yace"Ina Goggo take...? Dakyar bakinta na rawa tace"Ta..Tana..dakinta..."Tafada wasu hawaye sun zubomata sakinta yayi bayan ya tureta gefe ya wuce fuu kamar kububuwa.,Saura kadan tafadi sai ta ta dafa bango kafin ta tsaya da kafarta,tana ganin ya wuce ta rumtuma da gudu ta fice daga gidan,tana sauke ajiyar zuciya domin daman Duk duniya babu wanda take tsoro irin *YAYA CAPTAIN*

Shiko yana Shiga gidan akayimai chaa ana fadin'Ga angon Ni'imatullahi nan,gadanga kusar yaki,Ba gaba da gaba ba,ko ta bayan sai gwarzo..."Wani haushi ya tokaresa bai bi takansu ba yafada dakin yana fadin"Goggo..Goggo.."Goggo dake cikin daki tayo falo tana fadin"Gani Gadanga lafiyanka kakemin wannan kiran? tafada idanunta sun kada alaman tasha kuka,baiyi wata wata ba,kawai ya zube gabanta yana fadin"Don Allah goggo kifadamin wayeni?,da gaske nidin Shege ne bani da uba,goggo don Allah ki fadamin kota haramtattaciyar hanya kika same...."KAYI MIN SHURU ALI..."Goggo ta katseshi rai bace tana huci kallonta yake yaga yadda ruwan hawaye ke zubomata tace"Ka tashi kafice kabani waje.."Tafada tana nunamai kofa,Tsam yayi yana kallon goggo kan yace"ammh gogggo...'Ka ficemin daa gani nace ko Ali.."Tafada cikin wani Fushin,Baiyi gaddama ba,ya mike tsam yana wani mazari kafin ya kalli goggo kamar zaiyi mgana sai kuma ya fasa kawai sai ya kada kai yafice daga dakin,ya fada nasa dakin bayan ya rufo kofan yanaji kamar ya dauki gidanan akansa ya dinga yawo dashi saboda yadda wani zuciya tare da karfi ke zuwarmai lokaci daya.

Mutane sukayi Tsuru suna kallon kallo,share hawayenta Goggo tayi kan tace"Acigaba da shagalin biki,babu komai..'Tafada kafin ta koma cikin daki,madina da Mardiyya suka kalli juna,suna fatan Allah sa lafiya,  *RAMATU* kuwa da diyarta Shalelenta *AZEEZA* Suka kalli juna cikin sonyi gulma ammh babu dama,Ramatu ce keta kunshe dariyarta tanama diyar tata sigina da ido,suna kallon dakin da goggo ta shiga suna Dariya kasa kasa...

_*Topha,kunji fa yadda Abun yake,kanku ya daure,kun samu rashin Fahimta ko? Hhhhhhh haka janafty tace kowani book dinta tafe yake dawani salo na dabam,kuna so,kuna bukata,to cike Tagging dinki da HOT COMMENTS .."Nikuma zan himmatu da kokari wajen baku update..Oneluvs Janaf fans*_

          #Comment,share and vote#
          #Janafty.....#
*ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘,Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

_Dis NOVEL is not for sale,plz masu bina pc suna tambaya na siyarwane,nawa zasu biya suyi Rigister,So Cool ur mine Aliyu Gadanga is a special gift to my Real Dota RAHMA😘and my mommah shiyasa yazama Free,what are  u  eating na baka is zubowa kasa,😂Na kudinfa na nan tafe,tunda naga da gaske kuke u what me to become HAJIYA JAMI😂Tanque very much my Real Fans,and a big Tanque to does prople for dere hot comments,Love u Tin Tin😍😘_

*NOT EDITED*💥

*Chapter2*

    """Gidan bikin sai yakoma gidan gulma da tsegumi,sai cecekuce akeyi kunsan mutananmu,sufa basu raina Abun gulma balle wannan dasuke jiran kiris,itako goggo tana daki tana kuka duk lokacin Data tuna kalaman Aliyu saitaji kuka na kawomata,madina ne ta shigo dakin taga halin datake ciki,ita takira mardiya suka zo suna ta bata baki,nan nema take fadamusu Abunda ya faru,dafe kai madina tayi kan tace"Oh mardiya,mutane ba kyau,to ai Shikenan Allah ma ya sakamai da wacce tafi figaggiyar ni"imar ma,don Azeema tafita komai,uwa uba ga hankali da tarbiya"

mardiya tace"Kwarai ma ko goggo,kibar damun kanki,donta Captain ne,lokaci kadan ne,zai warware.."Suka fada suna kokarin kwantar mata da hankali,dakyar tayi shuru kafin ta wanko idonta ta fito kamar ba ita ba,Ramatu ko da Aziza sunyi iya yinsu su Fahimci meke faruwa ammh Basu samu dama ba,shiyasa suka kara gyara zama har sauran tawagan Daurin Auren su dawo kila sasamu wani lbrin daga barayinsu,duk da tasan mallam ko zata mutu bazai fadamata ba,tunda yace tana da rariyan baki..

*****************

  Ni'imatullahi tana zaune cikin kaawayenta acikin Shiga ta alfarma sanye take dawani ubansu material mai tsada da yarari black and red an mata wani Fitinanne Dinki ajikinsa kanta kuma an dauremata shi da head baki,fuskarta cikin makeup mai kyau da tsari,Ni"ima gajera ce,bata da tswao ammh tana da kyau sosai domin Farace sosai mai dauke da faffadan Fuska tare da dogon hancinta,tana da jikin mata babu laifi kam ko"ina ya cika,kallo daya zakamata kasan ta fito daga gidan hutu,saboda yadda fatar jikinta ya tsumu ajin dadi,kallon idonta kawai zakayi kafahimci tana da mugun wayewa da budewar idon yan matan zamani sakamakon kaf bayan Primary bata hallarci wata mkranta a Nigeria ba,kasar waje tayi rabi da kwatan Rayuwarta.

Cikakkun kawayenta yan Duniya ya"yan masu dashi,harda diyat gwaannar jahar gwambe mai ci alokacin Falon dai cike da yan gayu na bugawa ajarida,sai shewa ake ana zolayan Ni'ima da fadin Anrigaya da an Dauramata aure Da Captain din nata,kamar yadda take kiranshi,itako sai wani Smiling take,tana wani washe hakoran jin dadi,duk sanda suka ambaci an Daura mata aure da captain dinta,suna cikin wannan Halin ne,wayarta kirar Samsumg gallezy tadauki kara cikin wakan nan U ARE MY LIFE.."Da hanzari ta sanya hannu ta jawota dama tana kusa da itane, LOVELY MUNARI..."Tagani dan tsaki taja don azatonta angon natane Kawartace babbar aminiyarta ma kuwa,wacce fitanta kenan daga falon ta sauka kasa zatayi mgana Da MAMINTA.

Dagawa tayi tana fadin"Ya how far...? Cikin wata murya Munari tace"Swhrt ki sauko kasa yanzu don Allah.."Sororo Ni"ima tayi kan tace"In sauko kasa kuma?uban me zanyi miki in na sauko,kinfa san yanzu matar Aurece ni,so taku daya in zanyi sai da izini in ba haka ba,in Shiga cikin Fushin Allah.."Tafada cikin nuna iya gaskiyarta kenan,Kai munari takama tana kallon yadda falon ya hargitse tun Shigowar Abbah falon da lbrin da suka zo dashi tace"Oh my God..Swhrt kibar mganar nan,ki sauko kiji.."

  Tsaki Ni'ima taja kan tace"mtsewww...Bazan sauko ba,in bazaki fadi Abunda ke bakinki ba to rike kayanki,sai kin hauro.."Tafada tana kokarin yanke kiran"Ajiyar zuciya munari tayi kan tace"Yanzu su Abbah suka dawo..,"Da hanzari Ni"ima ta daga tsalle tace"Da gaske,shikenan na zama matar Aliyuna,plz Friend kutayani murna na zama matar my Captain.."Tafada tana dariya gabadaya falon suka saka mata ihu da tafi,Munari ta dafe kai kan tace"Ke baki da hankali wlh,baki iya tsayawa kiji zence,ba to Abunda nakeso na fadamiki su Abbah sun dawo kuma ba"a Daura Auren ba.."

  Wani Abu mai Nauyi Ni"ima taji ya tsaya bisa kirjinta cikin wani yanayi tace"ban...ga..ne...ba..?"Tafada cikin rawan murya Munari tace"Haka Abbah yace,an fadamiki an dakatar da Daurin Auren sakamakon haryanzu ba"a ga wani daga dangin mahaifin Aliyu ba,shiyasa Abbah yace bazaya bada Aurenki ga wanda ya tashi gaban mace ba,wanda haryanzu ba"a san asalinsa ba."Ihu kawai Ni"ima ta yanka ko kafin ayi wani Abu ta zube kasa Warwas bata numfashi da gudu kawayenta suka rufu kanta suna Kiran sunanta da hanzari wasu sukayi kasa suka kira mami,wanda tanajin Abunda ya faru ta dora hannu akai,tana fadin"Na Shiga uku ni Hadiza,dama sai da nafada kwamishina wlh Ni"ima bazata iya rayuwa babu Aliyu ba,kada yayi haka,kada ya aikata haka,to gashinan dai Ga Abunda nake gudun  nan ya faru.."

  Take ta fada tana,kuka,kwamishana na gidan da hanzari aka tarairayeta aka wuce da ita asibiti ba yarda take,ai sai gidan biki yakoma gidan kuka,da gulmagulmace,tuni kawayen Ni"ima suka kama gabansu Munera ce kadai wacce da ita aka tafi asibitin, *FEDERAL TEACHING HOSPITAL GOMBE*kowa yaji ba"a Daura aure ba,sai ya Shiga mamaki yana neman jin dalili,Kafin kaceme gida ya watse sai mutanen daba"a rasa ba,wanda dama sun kasance Shakikai ne,ga kwamishina din da kuma Mami Hajiya hadiza.

Wannan kenan

________________

Sai da Su Kawu suka gama sallaman bakinsu kafin su yi ayari Shida tawagarsa da tawagar angon suka nufi gidansu Aliyun,don kawu yace Sauri yakeyi yau din yakeso yakoma Kaduna,har cikin suka shiga suna gaisawa da mutane Hajiya Umaima mata ga kawu Bala wacce suka kira Da Umma ita ta fito tana fadin"Abban Haisam wai meke faruwa ne? Tundazu goggon yara ke kuka,ga Captain chan ya dawo yana wasu maganganu don Allah wai meke faruwa ne?

Dan mirmishi kawu yayi kafin yace"Bakomai Umaima mushiga daga ciki,mallam Shigo kaima don Allah.."jin haka sai gabadayansu suka dumguma zuwa cikin dakin,Ramatu da Aziza jikinsu haryana kyarma suka rufamusu baya,saboda suna so suji kwakwam,Suna Shiga kawu yasa baki ya kira Gaggo ta fito tana musu sannu da zuwa,Kallonta yayi kan yace"Suwaiba meyasa haka? don Allah kiyi kokarin danne damuwarki,domin kibawa Aliyu kwarin gwiwa,bafa

Please Login or Register in order to submit comment