Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani hotel suka kama ma Umar daki,suka ijiyesa har sai su maimartba sun kariso,wanda Shine zai sanar dasu anguwan dasu Aliyu suke bayan sun sanar dashi,basu dade anan ba sukayi mishi sallama suka Shigo cikin gari.

Karfe 10 da wasu mintina motarsu tayada zango akofar gidan goggo,tana tsakar gida tana Tsingan zogalenta don yau miyar zogale take sha"awar ci, taci kwalliyarta cikin wata Atamfa Super,wanda Aliyu ya dinkamata riga da zani,tadaura dankwalinta Ram akanta ga karamin Radio ta agefe tana jin daya daga cikin Fm dake gombe Aliyu dake gaba ya rafka sallama Jabir na biye dashi,dukkansu suna sanye da Farar shadda riga da wando,dukkansu dinki muhammed,kana aikin jikin Shadda baki ne,hakama Zanna bukar din dake kansu,ga kuma wani ubansu Sawu ciki na fata,hatta da agogon hannunsu na Fata ne,wanda kamfanin Rado tayishi.

Goggo na ganin Aliyu ta mike tamusu maraba bakinta har kunne,Rumgumeta Aliyu yayi bakin har baka yana Fadin"Gimbiya goggo..."Bayansa ta dan buga tana Fadin"Oh ni Suwaiba wai kuma wani sabon suna na samu,Jabiru sannunku da zuwa kunsha hanya fa.."Tafada tana Sakin gadanga,har kasa jabir ya duka yana gaida goggo ta karba tana tambayanshi iyayansa,ya amsa da suna lafiya,daki ta nuna musu tana Fadin",Ku Shiga bakin Sassafe,koda yake shifa gadanga ko shaho nan ya barsa da sammako,in zai taho yadako sammako,in zai tafi ma haka,to fa sai dai ko shayi zaku sha don,munciye komai na Diyata kadai yarage kuma namata alkawarin Zan ijiyemata hartadawo.."Jin Abunda ta ambatane yasa Alliyu tsayawa cak kafin ya waigo yana Fadin"Goggo wai kina nufin pretty? ina taje hala? yafada yanayin Fuskarsa na chanzawa,Kallonsa goggo tayi adage kan tace"Meye kuma Furata? dariya takama jabir yanayi yace"A"a goggo ba Furata ba,pretty yake nufi,wai Azeema..."Tsaki goggo taja tana Fadin"Mtsewwww kaji iskancin banza yarinyar tanada sunanta na musulunci kamaida mata na Kafurai,wai Furata,A"a kwarota ne ba Furata.."Tafada tana Shigewa daki ta barsu nan ba jabir ba hatta Aliyu sai da ya dara,dakin suka Shiga suka zazzauna kan kujera,kichen goggo ta Shiga ta daukomusu Flaks din Ruwan zafi da kayan Tea din,sai takoma takara Soya musu kwai ta hado musu dashi,Aliyu ya riga yasani goggo bazata taba basu wanda tace ta ijiyema Azeema ba,haka akidan goggo yake tanada kafiya wani lokacn ,nan suka baje suna karyawa ita kuma goggo tana waje tana cigaba da aikinta,Shiko Aliyu kurban tea din yake ammh gabadaya Ransa da zuciyarsa suna ga Tunanin Azeema,toh ina taje,? donshi baizata sun Fara jarabawar ba,tunda ba lissafi yake ba.

karfe 11:00am Azeema ta Shigo gidan duk agajiye,hannunta cike da leda ta Siyo goribanta,Tana Shigowa da sallama su Aliyu dake daki sukajita,goggo ma dake tsakar gida ta amsa tana Fadin"Har kin dawo.."Saboda yadda tagaji,gakuma halin data ke ciki,don yauma arike ta dawo Akasa tazauna tana yamutsa Fuska goggo ta bita da kallo tana Fadin"Tsiyana dake rashin jin mgana Azeema.."Tura baki Azeema tayi tana Fadin"Me kuma nayi goggo..? kai tsaye tace"har saunawa zance kidaina zama akasa? zaki sha takaichi ne sanda sanyi ya shigeki wlh,bazan hana gadanga yo miki kishiya ba,tunda sakarcinki yajamiki.."Jin Abunda goggo Ta Ambato na sunan gadangan datayi yasa Abun yayomata shar arai,Tuni taji idanuwanta sun cika da hawaye,aranta tana Fadin tafi kowa bukatar yaya captain,adaidai wannan lokacin don Tafara gazawa,haka hawaye suka zubomata Shar,Goggo dake aikinta taji Shesshekan kukanta ta dago tana kallonta haba ta rike tana Fadin",Oh ni Suwaiba daga wasa sai kuka,toh maza share hawayenki,dake kadai gadanga zai zauna ke daya tilo kamar Fitilar Besfa.."Dariya takama su jabir dake ciki ita kanta Azeemar sai da ta dara hijabin jikinta data cire,ta mike ta daureshi a kugunta kanta ko dankwali babu taja ledar goribanta ta Shige daki tana Tura baki,tsabar rigima ko takalman dake wajen bata lura dasu ba.

Tana Shiga kamshin Turarensa na MAN yayi mata maraba,ko acikin barcin kamshin ya sabamata gizo cak ta tsaya tana lumshe ido,don bata so ta farka ta daina jiyo kamshin, Jabir da Aliyu da suka kuramata ido suna kallon Abun mamaki,Aliyu ne ya kafeta da ido ganin yadda tacika kirjinta yakara tasawa sosai ba kamar zuwan dayayi ba juyawa yayi yana kallon Jabir shima kallonta yake ganin haka yasa ya mike da hanzari ya isa gareta babu tsammani taji Wani hanu ya jawota,mai Taushi ya direta awani jiki mai kamshi da Samun Natsuwa,yadda taji kanta yafara juyawa ne,kamshin na kasheta da dadi yasa takara lafewa harda rumgumoshi lokaci daya ledar goribanta na Subbucewa ahannunta,shikuma ganin yadda take Shigemai ne yasa yayi mirmishi yana Saka kunnensa wajen wuyanta yake huramata iska,wani zir...Zir takeji abunka ga wanda ke kan gaba Kawai sai ta kara makaleshi Ganin haka yasa yajuya yana kallon Jabir,wanda ya kauda kai yana dariya.

   Kanta ya haushafawa yana Fadin"pretty...Pretty.."Yake fada ahankali,jin muryansa daf da kunnenta yasa tayi hanzari bude ido,tana kallonsa wanda yazuramata bashi idon ya kafeta da mayen kallonshi,Kuri tayimai tana lasan lebenta Farinciki ya mamaye Ranta tuni ta manta da wani Fushin datakeyi,Tayi wani luuu da ido tana Fadin"Da gas..Ke kai ne nake gani agabana?."Tafada tana rarraba ido,Gyadamata kai yayi kafin yayi mgana ta tattara takara Fadomai ta kamkameshi tana Rawan jiki,don lokacin ji take kamar zata mutu.

Goggo ce ta shigo dakin,sai taci karo dasu awajen kamkame da juna,baki ta rike tana zaro ido tace"Wai yau naga ja"iran banza,don mai garinku in Rumgume Rumgumeneku zakuyi baku kebe kanku,wai naga lalatan yaran zamani"Aliyu najin goggo,ya kalli Azeema yaga bata cikin hayyacinta kawai rikosa take tana cije baki,Baiyi Shawara da kowa ba ya ciccibeta sai dayan bedroom din goggo,jabir dake gefe sai Dariya yakeyi goggo tayi kasake tana bin Su Aliyu da kallon mamaki,kafin ta juya tana Fadin"gadanga shi ya lalatamin Azeema,ammh har yaushe wannan badalan agaban mutane.'Take fada tana Sababi,shiko jabir aransa Fadi yake dole shima yama kanshi Fada yatafi zuwa aure,abunda ya dakatar dashi Mami tace yabata lokaci.

Bai Direta ko"ina ba sai kan makeken gadon dake dakin,Yana ijiyeta yadago zai tashi da hanzari Azeema ta rikomai wuyan Riga tana kallon cikin idanuwansa,ganin yadda take kallonsa ne,yasa ya dan Fada kanta,ammh bai sakarmata Nauyinshi ba,Kallon cikin idanuwanta yake yadda suka chanza kala,mgana yayimata ahankali yana Fadin"Pretty,wht wrong..? yake tambayanta kai ta kauda idonta cikowa da kwallah,Binta yake da kallo yana mamakin meke damun Azeema.

Ganin yana neman tashi daga kanta yasa tayi Azeeman Riko kansa ammh bayan ta runtse ido,takai lebenta saman nashi tana Tsotsa,shiko kafeta yayi da ido bayan ya rikota sosai yana tayata kissing dinshi datakeyi,Gabadaya Azeema ta haukacema Aliyu don Tuni tafara kokarim Rabasa da Rigar Shadda dake jikinsa,Riko hannunta yake tana Fizgewa idanuwanta arufe suke,tana abu kamar irin Wani Abu na damunta Rikemata hannu yake tana kwacewa ganin yahanata curemai riga sai kawai ta mike tana kuka ta cire rigar mkarantan dake jikinta Farar vest din dake jikinta ta bayyana itama Fuzgeta tayi ta Cire,idanuwanta suka bude suna masu zubba ruwa, tajawo hannu gadanga ta dora bisa Fararen boobs dinta wadanda suka cika taf,gasu atsaye cur,Hannunsa take gogawa bisa kirjinta tana wani matse jikinta zuwa gareshi,zaro ido kawai yayi yana kallonta,yama lura jikinta rawa yakeyi,Rikota yayi sosai,kafin ya daidaita hannuwansa yafara murza mata ahankali,yana kallon duka motsinta,Cikin hanzari ya Shiga bad romamce da ita,shi azatonshi Abun Azeemar na wasa ne,ammh ina Azeema tayi nisa don wani karfi takeji da karfin tsiya ta rabashi da wandon jikinasa tana kuka take kara Shigema,sai alokacin Aliyu ya Fahimci Abunda Azeema ke Nufi mirmishi yayi kawai ya Hau gadon dakyau ya Tarairayota yana fadin"Kinga pretty Natsu,am here For u kinji..? Yana Fada yana kissing dinta ganin bazata Fahimcesa ba yasa kawai yayimata Rumfa,yana karanto addu"ar saduwa da iyali yazaiyi Tunda dai Haka Allah yayi dashi Kashe arna adakin goggo.
 

Kusan minti talati kafin dukkansu su samu Natsuwa,Rumgumeshi kam Azeema tayi tana ajiyar zuciya,shiko yana kallonta,hannu yasanya yana Sharemata guntayen hawayen da suka bushe mata Afuska,kasa dagowa Azeema tayi ta kalleshi,yana taso su hada ido,ammh taki bari,sai ma juyamai baya datayi tana Kokarin Rufe jikinta da blanket,baki gadanga ya rike yana Fadin"Eh lalle kya juyamin bayamana Tunda kingama cin moriya ganga mana.."yafada yana dariya,tana jinsa,sai yanzu kunyar Abunda ta aikata ke dawo mata,ammh babu komai ko ahakan ma ita keda riba😜

Yana kokarin tashi yaji wayarsa dake chan yashe gefe cikin aljihun wondonsa tana nemam dauki da azama ya diro daga gadon,ya dauko wandonsa nasa ya ciro wayar yana duba mai kiran ido ya zaro ganin kawu ne,mai kiran kuma harta yanke,wajen 12missds cll yagani jikinsa na rawa yakirasa Ringing daya kawu ya daga yana Fadin"mun sauka fa Afilin jirgi,kuna gombe ne?Aliyu na Shafa kanshi yace"Eh kawu.."Kawu yace"Alright muma gamu nan zuwa,ga motocin Kwamishinar yada lbrai na jahar gombe nam yazo daukanmu sai mun iso.."Yana Fadar haka ya yanke kiran.

  Da Azama ya ijiye wayar akan gado ya Fada tiolet dake dakin jikinsa na rawa yayo wankan tsarki kafin ya Daurayo jikinsa ya Fito,Azeema na dunkule cikin bargo,ammh tana kallonsa ta gefen idonta,Agurguje ya maida kayansa wayarsa ya dauka yana Fadin"Pretty kitashi kiyi wanka,Tunda ki taramana aiki,gasu kawu nan zuwa..",Yanagama Fadin haka ya Fice da hanzari,jabir dake zaune Falon Shida goggo sukabi Aliyu da kallo,wanda ya Fito yana kare Fuska Shaddar jikinsa duk ta yamutse alaman dai anyi Abubuwa,Jabir ne ke kunshe dariya,itako goggo kallo daya tayimai ta kauda kai tana salati Aranta,Ficewa yayi da hanzari,motarsa yaje ya dauko makullin Shashensa yazo ya bude ya Shiga ya Chanzaa kaya,yana kokarin Fitowa yaji zuwansu kawu,goggo dake daki ta Fito cike da mamaki tana Fadin"Umaimah,a"a ga madina ga mardiya ga Haisam,la yaya.."Take Fada tana dariya da murnan ganinsu,ya"yansu Madina suka isa gareta suna fadin"Oyoyo goggo..."Suke fada suna dariya goggo fa baki yaki Rufuwa duk suka shiga daki ana gaisawa Jabir da Haisam suka Rumgume juna,suna murnan ganin juna,Goggo tarasa ina zata saka da bakinta Takawo musu wannan takawo musu wanchan,suko su madina na Faman zolayanta da gimbiya goggonmu,Tsiya ta hauyi tana Fadin"Kajimin ja"irin yara meye wani gimbiya kamar wata matar sarki haka ja"irin yayanki yazo yanamim Shegantakan nan"Dariya suka sakamata dukkansu,Sai ga Aliyu ya Shigo yana Shigowa jabir ya sakamai dariya yana kallon jikinsa ganin ya canza kaya,Aliyu na ganinshi yana ma Haisam rada akunne yayi kamar bai gansu ba,ya isa yana gaida kawu da ummah,su Anty mardiya suka gaisheshi,ya'yansu suka nufeshi suka Rumgumesa suna Fadin"Uncle ina Anty Azeema.."Rikosu yayi yana karisawa kusa dasu Jabir,kafadan Haisam yadaka yana Fadin"Dude long Time ..."Dariya Haisam yayi yana Fadin"Wlh ya Amarci.."Harara Aliyu ya jefama jabir yana Fadin"Amarci Alhamdulillah,gama aikina kenan kuka iso,shiyasa nakeso kuma kiyu ku auren nan,ko kwa daina wankan Asuba ba dalili.."Yafada ahankali yadda bamai jinsa,dukkansu suka kaimai mangari,suna dariya,ba wanda yabi ta kansu saboda sanin halinsu.

Azeema ko dakyar bayan tayi wanka ta iya Shirya ta Fito,cikin wani dogon Hijabi tana ta Faman sunne kai take gaishe dasu kawu,amsawa sukayi cikin sakin Fuska,Su hibba suna ganin Azeema suka saki Aliyu suka nufeta suka Rumgume suna murnan ganinta,dariya take itama tana rikosu,Gaishe dasu Anty madina tayi kafin ta waiga tana gaida Jabir da Haisam,Haisam kadai ya amsa Shiko Jabir cewa yayi"Sai yanzu kika ganni madam"Yafada yana wani bata rai,kunya takama Azeema ta sunne kai Su Anty madina na kallonta suna Fadin"Masha Allahu Allah ya raba lafiya( Don Tuni lbrin yakai musu).


  °•°•°••°••°•°••°••°••°••°••°••°

  Karfe 12:30am na Safe Jirgin su Maimartaba yayada zango a babban birnin Tarayyah Abuja, mai girma Shugaban kasamu *GENERAL MUHAMMADU BUHARI* da kanshi yazo ya tarbi maimartaba Abdulnaseer Tambari buzu tare da iyalansa da Kuma wasu daga cikin Masu kula da masarautarsa,kamar irinsu Shamaki, da Sarkin gida sai kuma bayin da"aka zo dasu mata da maza,daganan gidan gwannati,sukawuce sai da suka huta sukaci abinci maimartaba suka kara gaisawa da Shugaban kasa kafin kuma,jirgin ya kwashe su zuwa Gombe.

Koda karfe biyu Tayi jirginsu Maimartaba Tuni ya yada zango Afilin jirgin dake gombe,inda anan ne mai girma gwannan Jahar gombe tare da maimartaba Sarkin gombawa suka zo suka tarbesa,Sai da suka fara zuwa gidan gwannati kafin su rankaya zuwa Masarautar gombe,achan ne sukaci abinci suka huta bayan an Shiga dasu Gimbiya Razeenah Shashen matan sarki bayi kuma ankaisu barayin bayi,shiko maimartaba yana tare da Sarkin gombe suna tattawa,bai boye masa komai ba yadan gutsira masa kadan daga Abunda yakawosa,Maimartaba Sarkin gombe yayi murna sosai,sun jima suna tatttaunawa sai bayan sun yi la"asar a babban masallacin Cikin Masarautar kafin Maimartaba Sarkin Agadez yayima dansa waya Wato Yarima Umar yana Fadamai gashi sun iso,wani anguwa ne Suwaiban take zaune,ba bata lokaci ya sanar dashi Sunan anguwan da Aliyu ya sanar dashi,Maimartaba ya sanar da sarkin gombe wanda ya jinjina kai yana Fadin"Anguwan marasa hali ne,anguwan tana cikin garine bari ashirya motoci yanzu sai ku tafi.."gyada kai Sarki Abdulnaseer yayi yana ma sarki godiya.

Shiko Yarima Umar suna gama waya da maimartaba yakira Aliyu ya sanar dashi wanda yana cikin falon goggo yaga kiran Umar,din da hanzari yafice jin Gasu maimartaba nan karisowa yasa yakira jabir awaya yace asameshi awaje,yana Fitowa Aliyu ya wurgamai key din mota yana Fadin"Maza kaje kataho da Umar,gasu Abba nan zuwa.."Jin haka yasa jabir chabe key din yana fadin"angama Angon Azeema.."Yafada yana dariya kan ya Fada motar yabata Wuta ya Fita daga layin da gudu,cikin gida Aliyu yakoma yana kallon goggo yadda ta ware cikin ya'yan yanuwanta anta hira,Wani Farinciki yakeji aransa,domin burinsa bai Wuce ganin goggo cikin Fara"a ba.

Ba dauki minti talatin ba, Tambari tare da busan algaita suka cika anguwan
*KAGARAWAL* Motoci ne masu rai da lafiya daga Fadar sarkin gombe guda Bakwai suka jero cikin anguwan,daya daga cikin wata doguwar Farar motace wacce maimartaba Sarkin gombe ke hawanta,itace Sarkin Agadez ke ciki Shida iyalansa,Ga kuma yan Sanda harda mobile police,Saboda yanayin cinkuson anguwan sai da Fadawa suka sassauka suna dan bin motan da dugu,Fadawan sun hada dana Sarki gombe ne,dakuma na Sarki Agadez,jin wannan busan algaita,yasa kowa yayi waje yana kallon Abun mamaki,sarki guda a anguwansu,Harda mata masu leke ta gadanga,Daidai lokacin motar Aliyu ta Shigo Layin Wanda Jabir ke ciki Shida Umar,ganin yadda wurin ya cinkushe yasa Umar Fitowa yakarisa da gudu ga motar mai martaba yana Nuna ma Direba kwanar gidan goggo,atare motocin suka dinga shan kwana,suko Su Zafira take cikin mota sunata kalle kalle Suna Fadin"La ga yaya Yarima.."Suke Fada suna nunasa murna ta cikasu,itako gimbiya Fasilatu wani kallo takebin anguwan da kallo,Aranta tana Fadin"Kaskanci ne Sarki guda ya Shigo wannan anguwan.."

Su goggo na gida suka Fara jiyo Jiniya da algaita,ba wanda yanuna mamaki,sai goggo wacce ke fadin"To kuma yau wani babba ne yazo anguwan Tamu,Allah yasa mai girma gwanna ne yazo mganar gyaramana mana Titin anguwa haba abu duk ya lalace"Dariya aka sakamata itako ko ajikinta,Motocin mai maimartaba basu ja Tunga ba sai akofar gidan goggo wanda makota dana kusa dana nesa kowa ya Fito ganin Abun mamaki ciki harda inna Ramatu wacce ta Fito ko mayafi bata dashi,duk ta rame saboda Rashin Azeeza ido ta zaro lokacin data ga Fadawa da Sauri Sun Fito dawani katon Capet dogo sun warwareshi Tundaga Kofar gidan goggo har cikin gida inda Sarki xai taka kenan,suko suna cikin gida sukaji shigowar Fadawa suna Shimfida capet,gabadayansu sukayo waje,goggo ce ta zare ido tana Fadin!Wannan daga ina? yaya kamar Kayan Gidan Sarki ne ajikinsu,munbani me mukayi kuma? tafada cikin Rudewa,Kawu ne ya riketa yana Fadin"Natsu Suwaiba babu Abunda zai Faru sai alheri.."


Awaje kuwa Umar ne ya kariso dakanshi ya budema maimartaba kofa,Mutame kuwa baki suka bude suna kallon Abun mamaki,don su Azatonsu Umar Aliyu ne fa,Shiyasa Abun ya dauremusu kai,su duk atunaninsu Sarkinsu ne yazo gidan goggon,Basu cika da mamaki ba Sai da Sarki ya bayyana awajen,Fadawa kuwa sai kareshi suke suna kirari da cewa"Allah ya taimaki Sarkin Agadez..Allah ya taimaki Adalin Sarki mai mukin Masarautar Tambari buzu takawarka lafiya sarki jikan Sarki,kuma ka haifi sarki da yardan Allah..."Hannu kawai Maimartaba Sarki gombe yake daga musu yana Sanye cikin wata alkayaba mai kyau da tsari,ga wani Farin Rawani,wanda ya Kafemai bisa kai,daga wajen bakinsa Farin Rawanin yadan Rufemai baki har zuwa hancinsa kafarsa sanye cikin wani ubansu Takalmi na Jinin Sarauta,Kana kallonsa kwarjinsa zai dakeka,koda yake cikin Rawani kana iya hango hasken Fatansa da Karan dogon hancinsa,Mutane sai Wage baki suna kallon mamaki,don dai koda kallon Farko sunsan wannam ba Sarkinsu bane,Gabadaya Su Ummah mai babban daki suka Fito kowannesu cikin Shigar kayan Sarauta,suma bayinsu da da Fadawan masarautan Agadez suka jera layi,suna zuba kirari,mutane basu kara tsorata ba,sai da su Zafira da Safaratu suka Fito,dukkansu cikin Wasu alkayabba masu ruwan Zaiba,sunyi matukar dacewa dasu,Abunda yaba mutane mamaki kamaninsu da gadanga Zahirin gayinan ya bayyana,suko sai bin mutane suke da kallo,don basu saba Fita waje ba,ko mkrantarsu acikin masarauta take.


Ana zubama maimartaba kirari,Fadawa na karesa Umar ya bashi hanya yafara taku zuwa ciikin gidan goggo hannunsa rike da wata sandar zinare,ta gidan Sarauta Jabir dake baya yana leke,baki ya rike yana fadin",Tabdijam wani Abu sai gidan Sarauta.."mutane kowa harda masu zubar da yawu saboda kallo,ciki harda su inna Ramatu,wacce saboda kallo,harda Faduwa tayi, idonta take murzawa don ita gani take kamar mafarki take,ammh sai me agaban idonta Sarkin Agadez ya Shigo gidan goggo bayanshi kuma su Ummah mai babban daki,dasu gimbiya Razeenah sai gimbiya Fasilatu sai su Zafira dasu Jabir kana bayi da kuma su Sarkin gida daga baya.


Goggo ba inda jikinta baya Rawa,kirarin Fadawa yafaramasu goggo maraba,Kafin sarki ya bayyana acikin dan Filin Tsakar gidan,Goggo wace ke Rumgume da kawu tabi Su da kallon mamaki,daidai lokacin da Su Gimbiya Razeenah suka gama Shigowa sai gasu Zafira,sai yarima umar ya bayyana yana mirmishi,Aliyu dake chan baya ya dagama hannu alamar jinjina,Goggo data tsaida idonta kan Umar tayi wani shock ya shigeta A gauggauce ta Fizge jikinta daga na kawu tana nuna Umar,kafin tama samu Zarafin mgana gadanga ya bayyana agabanta,Yana mirmishi Azeema ma dake gefe,Ma ware ido take tana kallon mai kama da mijinta ballema Su Madina da suka daskare,hannu goggo ta sanya tana riko Gadanga,Umar take nunamai da hannu tana so tayi mgana takasa,idontane ya sauka kan Zafira cak goggo ta tsaya tana wani Nuna hannu kamar tafita daga hayyacinta,shiko Sarki Abdulnaseer Tsaye yake cak yana bin goggo da kallo,ko Shekara Dari Suwaiba zata yi bazai taba mantawa da Fuskarta,Tuni yaji hawaye sun tahomai,Baisan sadda ya Furta "SU...WAI...Baaa....."Yafada hawaye suna zubomai,Wata murya goggo keji wanda ko mutuwa tayi tadawo bazata manta mamallakin muryan ba.


Ido take warewa taga daga ina muryan take,Maimartaba dayaga haka sai ya sanya hannu,ya yaye Rawanin dake kansa duka Fuskarsa ta bayyana Tuni fadawa suka Zube suna Fadin"Allah karama Sarki hakuri,Allah ya Huci Ran maimartaba Ayimana Afuwa munga Abunda baidace mugani ba kai tsaye wato Farar Fusjarka mai cike da haiba da zati,Tuba muke Ranka ya dade.."Goggo data kafe idonta kan Maimartaba Taja baya da Sauri Tana Nuna hannu,Maimartaba take Nunawa tana so tayi mgana takasa dakyar ta iya Furta"Ya..Yaa...Kassn wa...Na..Ke ...Ganii...."Tafada idonta na Kafewa lokaci daya bakinta ya Subuce ya Furta... *AB...DUL....NA....SEEEEERRRRRRR......."Kafin kawai ta Sulale zata zube kasa kafin Aliyu ya isa gareta maimartaba yayi Sufa zuwa gareta ta Sulale bisa jikinsa.





*Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

     *Chapter..32...*

  ""Gabadayansu sukayi kan goggo wacce ta sulale bisa jikin maimartaba,dagota yayi yana jijjigata yana kiran Sunanta"Suwaiba..Suwaiba.."Ammh ina ko motsi batayi,gadanga ne ya Runtuma daki aguje ya dauko ruwa yana zuwa ya duka,maimartaba ya mikasa Tafin hannunsa yana kallonsa kai Tsaye ya tsiyayamai Ruwan ahannunsa yayarfe kafin ya Shiga Shafe fuskar goggo dashi,lokaci daya ta saki ajiyar zuciya kafin tafara kokarin bude ido,tana budewa taci karo da Gadanga,sai kawu sai Umaimah da Haisam,sai Jabir dake gefe,chan ga Mardiya da madina,sai Umar dake durkushe gefe,jin ta ahannun wani ne,yasa ta dago ido Fes ta saukesu kan Maimartaba wanda ke kallonta yana kara godema Allah...

Zabura goggo tayi daga jikin maimartaba tana Raba ido don ita azatonta mafarki take,Nunashi Tahauyi tana Fadin"Yaya kaga Abunda nake gani kuwa.."Da hanzari kawu bala ya karisa gareta ya rikota yana Fadin"Nagani Suwaiba ki Natsu kikuma godema Allah dayasan zaku kara ganin juna dukkanku kuna raye.."Fashewa da kuka goggo tayi tana lafewa jikin kawu,tamaki kara dagowa ta kalli maimartaba.

Aliyu ne ya Shiga daki ya Fito da wani kafet,babba da wasu manyan Tabarmu yazo su Haisam suka kamamasa ya Shimfida atsakar gidan,saman kafet din nan maimartaba yazauna da iyalansa sai Tabarmu su Kawu bala suka zazzauna wanda ke rike da goggo yana lallashinta,Da hannu Maimartaba ya yafito Aliyu,Jikinsa na rawa ya mike ya isa ga mahaifinsa Yana kokarin zama,Maimartaba ya rikosa yana Fadin"Aliyu..."Yafada yana shafa sumar kanshi,Ummah mai babban daki ta riko hannu Aliyu tana Fadin",Sannu sabon megida.."Mirmishi ya saki yana binta da kallo,Kusa da maimartaba ya zauna yana kallon Su Zafira,wadanda ke dagamai hannu suna dariya,shima dagamusun yayi yana mirmishi gimbiya Razeenah ta Dafa kan Aliyu tana mirmishi tace"Sannu magajin Sarki.."Tafada tana kallon gefen gimbiya Fasilatu wacce ta cika ta batse kamar ta fashe

Goggo ce ta dago tana kallon Aliyu,wani harara ta zabgamai kafin tace"Yana raye,ammh Shine yabarmu baitaba waiwayanmu ba tsawon wannan lokacin? Tafada tana Tsiyayan hawaye sai wajen ya dauki Shuru kukan goggo kadai akeji,Ana cikin hakane sai ga mallam lawal Shida inna Ramatu Sun fado gidan,domin inna ramatu na ganin Abunda ke Faruwa takoma gida ta sako mayafi tatafi kasuwa ta fesama mallam lawal,tatasoshi kuma agaba saboda in ba dashi ba,bazata samu damar Shiga gidan goggo ba balle hartaji mai ke Faruwa,kawu na ganinshi yatashi ya rikosa yana Fadin"Alhamdulillah barka da zuwa mallam lawal kazo akan gaba don kaima kana da jibi da wannan Ahalin..",Yafada yana kariso dashi gaban maimartaba yana Fadin"Ranka yadade,wannan mallam lawal kenan uba yake ga matar da Aliyu yake aure,kuma uwa uba shi na damkama amanar Suwaiba tun bayan dana kawota garin nan,su sukayi hidima da ita har zuwa haihuwar Aliyu,mallam lawal kai kuma wannan dake gabanka Mahaifin Aliyu ne,kuma Sarki ne na Kasar Niger"Ba mallam lawal da"ake ma bayani ba inna Ramatu ce,wacce ke tsaye ta zabura tana dafe kirji da karfi ta Furta"Mahaifinsa? kuma sarkin Niger to ya akayi haka? Tafada cikin Rudewa..

Kowa kallonta yake,yana mamakin kalamata,su Maimartaba ma sun zata mahaukaciyane,ganin yadda ake kallonta ne,yasa Tayi Saurin dukar dakai tana Raba ido,Fadawa ne suka dakamata tsawa suna Fadin"Hattara dai Diyar talakawa ba"a mgana indai sarki bai bada izini ba hattara Dai..."Inna Ramatu da jikinta ke rawa ta duke ta kyarma ganinsu da bulalai,kawu ne yasa baki yace"Ku kyaleta maidakin mallam lawal ce"Shiko yana gaban Sarki durkushe kamar ya kwantamai,idanunsa sun cika da kwallah,Mikasa hannu maimartaba yayi yana Fadin"Mu gaisa Tukunnah..."Kasa mikamai hannu Mallam lawal nokewa yakeyi yana Fadin",A"a Ranka ya dade,Talaka kamata baidace na yi hannun dakai ba,Allah yakarama yawan Rai.."Mirmishi kadai sarki yayi yana Fadin"Ina Surukata take.."Yafada yana kallon goggo,wacce kanta ke duke tana Sharan kwallah.

Azeema dake Gefe tana Raba ido,Kowa yasama ido ganin yadda suke kallonta ne yasa duk taji kunya,sai tahau Sunne kai,Hannu maimartaba yadaga yana Fadin"Taho diyata taho nan ki zauna.."Jikin Azeema amace tamike ta isa gaban maimartaba ta durkushe kanta ya Dafa yana sakamata albarka,nan Ummah mai babbar daki tajawota tana Fadin"Taho nan kishiyata,dani zaki zaman kishi don kinganni nan,inba Aliyu ba sai Rijiya mai gaba dubu..",Dariya aka saka,itama Azeemar yar dariya tayi Kusa da gimbiya Razeenah ta zauna ta Sunne kai,itako gimbiya Razeenah ko ajikinta ta Rumgume Azeema tana mata rada akunne,tsam naga tatashi takoma kusa dasu Zafira wadanda ke gefe sun kame,Su jabir dake Facing dinsu su suka kurama ido suna yaba tsari da kyan yan matan,Washe baki sukahau yi Suna Fadin" Our princess daya tilo A masarautar Tambari buzu.."Dan ware ido tayi tana kallonsu kafin ta Shiga tambayan sunayensu suna Fadamata tana gyada kai...
 

Kawu Bala ne yayi gyaran murya yana Fadin"Ranka ya dade zamu so muji meyafaru ne,Tun bayan aiken da mallam yayi maka baka dawo ba,munyi nemanka har ba Adadi har muka cire da cewa baka da rai ne.."Maimartaba yayi Shuru kafin ya gyara zama yana Fadin"Ko baka Fadamin ba, Nasan cewa Allah ya karbi Ran mallam da inna..",Gyada kai Kawu yayi yana fadin"Dalilin Shiga damuwar Batanka da bullowar ciki ajikin Suwaiba Shiyayi sanadiyar Jininsa har ya hau,bai dade yana jinya ba,Allah ya karbi Abunsa itama inna bata dade ba tabishi Tsakaninsu kwana 52 ne.."Yafada yana Share kwallah,don ji yake kamar yanzu Abun ke Faruwa..

Goggo ma kuka take sosai,domin mutuwar iyayan nata sun dawo mata sabuwa,Maimartaba daya dukar dakai ya dade bai dagoba yana dagowa Sai ga hawaye shar suna zuba Fadawa keta kirari suna Fadin",Allah huci Zuciyar maimartaba,Allah ya sanyaya zuciyar Adalin Sarkinmu.."Hannu

Please Login or Register in order to submit comment