Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani Abu dama Allah ya kaddara Ni"ima ba matar Aliyu bace Azeema ce matarsa.."

  Da hanzari Hajiya Umaima tace"Bangane ba,da wata Azeema aka Daura aure..'?Kai tsaye yace mata"Diyar mallam lawal,shi ya taimakemu ya fitar damu kunya,da bamusan ya zamuyi da tarin jama"ar damuka tara ba.."Ramatu dake gefe ta zaburo tana fadin"Da wata diyar mallam lawal din aka Daura Aure? badai Diyata bako? na Shiga uku ni Ramatu kowa na raba kanshi da hada zuru"a da mugun iri wanda ba"a son Asalinshi ba,ammh kai..."Ke Ramatu.."Mallam lawal ya katseta cikin Fushi yace"Dake ake mgana,wlh zan mugun sabamiki matukar nakarajin bakin ki cikin wannan mganar,Ba da yarki dakike kirarin itace taki na Aurama Aliyu ba,da Diyar kwarai wacce batagaji tsiya ba na basa AZEEMA.."Da hanzari Aziza ta dago tana kallon mahaifinta lokaci daya taji wani Abu ua tsaya mata bisa kokon rai tun lokacin dataji anfara mganar an Daurama Aliyu Aure kamar kunninta sai yajiyemata kamar Sunanta ake ambata da an Daura mata aure da Aliyu,alokacin wani farinciki ya mamayeta domin tunda tataso anguwa daya Da Yaya captain amtsayinsu na makota takamu da matsanancin sonsa,duk duniya kowani Namiji abanza take kallonsa,babu wanda takeso da buri yazama mallakinta irin Yaya captain koda take wani Abun,saboda Ramatu ne,karta fahimci inda ta dosa,ammh sai kuma gashi Mahaifinta yakira Sunan Azeema amtsayin wacce aka Daurama Aure da Yaya Captain dinta,lokaci daya taji jiri na neman kwasheta,sai da tarike hannun Ramatu kamkam tana rintse ido.

Ramatu ta mike tana fadin"Oho yanzu naji mgana Ai wlh da da yatace yanzu nan zaku warware aure nan domin bazan hada irin da Da"n mace ba mara asali .."Fita kibama mutane waje sakarya mara tunani.."mallam lawal ya katseta yana nunamata kofa Hannun yarta taja wacce ke wani hali tace"Ko bakace ba, zamu tafi,ammh dai an Fadi ba Nauyi kuma duk  wanda yahau motar kwadayi karshensa Tashar Wulakanci.."Tafada suna Ficewa.

Ajiyar Zuciya mallam lawal ya Sauke yanajin wani kunya tare da bakin ciki suna dirar mai lokaci daya dakyar ya iya cewa"Don Allah kuyi hakuri da maganganunta haka take sam bata da Tunani wani lokaci.."Mirmishin yake Goggo tayi kan tace"Bakomai mallam lawal Ai ba yau nake tare da Ramatu ba,ai yakamata nasan hallayanta babu komai kadaina biyemata don Allah,mungode sosai Allah ya saka da alheri bazan manta karamcinka garemu ba,ni da gadanga tun zuwana garin nan kake dawainiya dani,tare da gadanga saboda haka Allah ne,kadai zai biyaka Alherinka garemu.."Takarishe kamar zatayi kuka gabadaya suka shiga bata hakuri,nan kawu bala yace su tattaro suzo su koma gida tunda dai biki ya tashi nan akayi mganar tarewar ita Azeema ammh sai kawu yace abari nan da wani lokaci saboda Samun natsuwar Shi Aliyun,shima mallam lawal din yayi na"am da hakan saboda itama Azeeman yanzu take SS1 a babbar sakandiri,Goggo dai bataso ba,taso kawai Azeemar tatare a shashin da Aliyun ya gyarama Ni"ima,tunda nan zata fara zama,kafin yakoma wajen aiki chan kaduna su tafi tare,ammh babu yarda ta iya,domin bata iya tsallake Umarnin yayanta.

Haisam ne zai bi Su Ummah yakoma gida,domin sunyi sunyi Aliyun ya bude kofa yaki,Ran maza fa ya baci Dole yayi sallama da Jabir yabi su Ummh suka damki hanyar kaduna,dashi dasu madina da mardiya,Jabir kadai aka bari,Sai gobe Sunday zai koma Tunda monday akwai aiki,Dakin Goggo yakoma sukacigaba da tattaunawa akan Batun goggo tana nunamai ita tafi jin dadin wannan Auren,domin dama AZEEMAR yar dakinta ne,nan take komai nata ko kafin ma ayi hakan,shi kanshi Jabir sai yaji zuciyarshi tafi Natsuwa da Azeema domin ya santa sosai yarinyace mai hankali da natsuwa gata da ladabi da biyayyah bata da hayaniya ko kadan,Aliyu dai yana daki kwance,so yake yayi kuka ammh yakasa idanunsa ne,suka kada sukayi jajir,jijiyoyinsa kansa suka fito radau,Lokaci bayan lokaci sai ya naushi hannunsa da bango,goggo ko batabi ta kansa, ba saboda tasan halin dan kayanta,Aliyu gadanga zuciyarsa kamar kuturu in yatashi tsiyarsa sai tafita yammah da hankalinsa kafin suke komawa su daidaita.

**************

Azeema Atsorace takoma gida,tayi zaune cikin dakinsu tana sauke ajiyar zuciya data rufe ido tsawar da Yaya Captain yadakamata ke dawomata,sai tawani zabura kamar yanzu Abun ke faruwa,Ganin bata da mafitane yasata tamike tadauki tsintsiya ta share dan tsakar gidan nasu,domin tasani inda inna ta dawo ta tarar da ita batayi ba,sai na lahira yafita jin dadi,ta gama sharan kenan ta kwaso duka kwanukan wanke wanken duka gidan,amadafi tazo wajen wanken wanken nasu ta zube takarisa gindin rijiya ta zura guga ta dinga jawo ruwa sai da tacika botikai hudu,biyu takai Madafi,biyu kuma ta dauki kujera ta kada klin,tafara wanke wanke,tafara kenan taji shigowar inna Da Aziza,ta dago ido tana kallonsu lokaci daya tana fadin"Sannunku da zuwa..."

Inna Ramatu ta kalleta tana hararanta tace"Ke keda sannu,Tunda ubanki ya kashe miki rayuwa ya aura miki wanda ba"asan asalinsa ba,uwa uba gashi mara tarbiya,..."Da hanzari Azeema ta dago tana kallonta gabanta yana faduwa ta bude baki zatayi mgana kenan Aziza tazo ta wuce ta gabanta fuu ta bangajeta harsaida ta Fado daga kan kujeran datake kai,da kallo tabita harta shige daki,kwallah ta tarun mata a ido ta dago tana kallon Inna Ramatu tana fadin"Inna kinga Aziza ko? Tsaki Inna Ramatu taja kan tace"yo in na ganta mezan mata,dakika ga zata wuce meyahana ki kauce ki bata hanya,ai ke da mahaifinki Kwadayi zai kasheku don nasan kwadayin Abun Duniyane yasa ya bada Aurenki ga Dan mace nan..."Da hanzari Azeema ta mike tana fadin"Ni..Ni..Kuma ba.. ba..."Eh dake fa,saboda kwadayin Abun Duniya iyayan wanchan yarinyar sunce bazasu bashi yarsu ba,saboda ba"a san asalin dangin mahaifinsa ba,ammh dayake shashashan uba gareki wanda zuciyarsa tarigaya ta mutu ya daukeki yabada ke,ban damu ba,tunda kece Tunda kema zuciyarki irin ta ubanki ne,da dai yayi karambanin Auramasa Aziza wlh da anyi yakin Duniya na uku.."Tafada lokaci daya tana Shigewa daki,da wani kallo Azeema tabita kafin ta dafe kanta tana hada maganganun Innar in kunnenta yajiyemata Daidai kamar da ita taji inna na fadin A Dauran mata Aure da Yaya Captain,Saurin Dafe kirji tayi tana karanto Duk addu"ar datazo daga bakinta lokaci daya idanunta na zubo da kwallah,runtse ido tayi tana tuna yadda basu shiri sam da yaya captain saboda halinsa na rashin sakin Fuska da walwala uwa uba mugunta yaya captain baya da wasa kwatakwata ko asojojin shi na dabam, ne,nan da nan ta tuna karonsu na dazu,sai jikinta yahau rawa kasa karisa wanke wanke tayi,sai ta wuf ta wanke hannuwanta tafada dan karamin dakinsu gefen katifa ta zauna ta zabga tagumi tanajin kewar mahaifiyarta,domin da"a ce yau mahafiyarta na raye,da kila ta samu kafadan dazatayi kuka,ta lallasheta,ammh yanzu bata da kowa sai Mahaifinta,wanda kuma komai daga barayinsa ya fito,Har abada bazata taba bata kanta ba,bakuma zata watsama Mahaifinta kasa a idoba,duk duniya bata da wanda ya fishi,Share hawayenta tayi kafin tafice takoma ta cigaba da wanke wankenta lokaci bayan lokaci tana kallon dakin inna Ramatu tana share kwallah...

           #Comment,share and vote#
            #Janafty#
  *ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH..,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

*Chapter3*

        *ASALIN TUSHE*

*MALLAM SHEHU AKARAMI* Sharahararren malamin Addini ne wanda yayi suna abangaren koyar da addinin Allah,Shidin ya kasance Basakawwace ne dan Asalin garin Birnin kebbi,akaramar hukumar kangiwa awani gari da"a kekira Arewa local Goverment,karatu da neman ilimi ya barosa daga garinsu,sakamakon duka mahaifanasa Allah ya amshi kayansa,yayi yawon garuruwa inda yayi karatun Allo har zuwa sauka ya karanta littafai babu adadi kafin Allah ya jehosa garin Zaria.

  Agarin na zaria ya samu masaka wajen wani malaminsa wanda ya karisa saura karatun littafai awajensa,sunyi zaman amana tare dashi,Shima malamin ba"arene wato Shima bassakwaceni ,kuma har dangin Shehun yaje,wannan dalilin ne ya saa ya auramasa diyarsa daya tilo Aisha ido,Bayan Aurensu anan zaria suka cigaba da zama,basu dade da Aure ba Allah yayima mahaifin indo rasuwa,baiyi Shekara ba matarsa ta bisa,koda aka raba gado gabadaya dukiyan da gonaki da aka mutu aka barmata duk ta mallakama mijinta Mallam Shehu wanda yagaji mahaifinta ya cigaba da koyar da almajirai karatu daga garuruwa dadama,yakasance mazaunin cikin zaria cityne Akwarbai.

  Gonakin sai yadinga Noma dasu,yana hadawa da kiwon Dabbobi domin dogaro dakai,..Bayan Aurensu sai mtsalan wabi ta biyo baya duk ya"yan da indo ta haifa da anyi suna sai sukoma ga mahallicinsu,sai da tayi takwas basu tsaya wa,har sun Fidda rai sai gashi Sun Haifi Bala,wanda basu ma sakaran zai Rayu ba sai gashi ya rayu,Shekaranshi Bakwai Aduniya Indo ta sake haihuwan Suwaiba,wanda tun daganan bata kara haihuwa ba,sai suka godema Allah bayan sun tattara ya"yansu guda biyu da Allah ya basu suka rikesu..

Koda aka haifi Suwaiba bala ya haddace alqur"ani,itama tana tasowa itama Mallam baiyi wasa da karatunta ba,Bala yayi karatun primary sch dinsa awata makaranta mai Suna Zaria acadmy,anan kuma yayi secondary sch dinsa,yana kammallawa ya fada ABU ZARIA inda yake karantar Political Science,Ayayinda Lokacin Suwaiba take SS1 anan Zaria acadmy din,itama kafin asakata mkrantar boko sai da ta haddace Qur"ani tana biya sauran littafi.

ABDULNASEER TAMBARI BUZU.."Wani Buzu ne wanda ya fado garin zaria akuma gidan Mallam Shehu akarami,Domin neman ilimi,Mallam Shehu ya amasheshi hannu bibbiyu Tunda dama yana amsan baki daga wasu kasashen kusa da Nigaria kamar su cameron da Chadi da Niger din,Babu Abunda mallam ya sani nashi sai Shi din mutamin Niger ne,ayanki agadez Sai kuma Sunanshi da suka sani,wajen shakaransa tara tare da mallam Tuni ya Sauke qur"ani yayi haddansa yakoma yanabin sauran litttafai,Shakuwa tare da sabo Tuni yayi da mallam da iyalansa bala da Suwaiba suna kallonsa ne,amatsayin dan'uwa ba almajirin mallam ba,Shiko mallam Shehu akarami yayi Shaku da Abdulnaseer sosai yakuma jarabasa ta hanyoyi dadama inda ya fahimci yana da amana da hankali bashi da mtsala ko kadan,shiyasa yasaki jiki dashi harda harkan Dukiyansa data iyalansa yana da masaniya,sai yazama shalelen malam Domin ma,sauran almajiran da Dan mallam sukemai lakabi,kwatsam batare da shawara da kowa ba Mallam Shehu Akarami ya Daurama Abdulnasser Tambari buzu Da Diyarsa Suwaiba aure Ranar datayi candy dinta Daurin Aure daya hada mutane biyar cur,daga mallam Shehu sai Abdulnaseer din,sai wani Abokin mallam din sai wasu manya daga cikin almajiran mallam din guda biyu,azauren gidan nasa,wanda mallam din da kanshi ya biya sadakin Auren nasu,Abdulnaseer shikanshi baida masaniyar Auren sai da aka kullashi kana kowa yaji,da farko bala ne dayazo Hutun Semister yaso yayi gaddama game da Aure,duba da Aure ba mganar wasa bace,taya ya za"a bama mutum aure batare da sanin asalinshi ba ko sanin wasu daga ciikin danginsa ba,ammh sai Mallam ya tausheshi da cewa lokaci kadan yake jira zasu dumguma dukkansu zuwa chan Niger din domin ganin ahalin Abdulnaseer din,Duk da bala bai wani gamsu ba,ammh sai ya share,saboda yana daraja mahaifinsa bazai iya sa"insa dashi ba,itako indo bata wani Damu ba,domin mijinta yayimata bayani,ita kuma Duk duniya babu wanda take gani da kima da daraja irin uban ya'yanta Shiyasa tabashi goyon baya dari bisa dari..
   
Abagaren Suwaiba kuwa bata wani ji wani irin ba,lokacin da Mallam yatarasu yake fadamusu,sai ma sunne kai datake tana satan kallon Abdulnaseer din,wanda kwata kwata baya da muni,Fari ne mai kalan ja,dogo ne karkarfan Namiji gashin kansa a nannade kallo daya zakamai kasan buzu ne gaba da baya,yana da kyau na daukan hankali,domin ko a anguwa yana fama da yanmata kai harda zawarawa,ciki harda manya mata wa"inda suka kusa haihuwansa,in suka gansa,kyansa yana Rudansu sukai ma tayi,ammh sai ya taka musu birki,Shima abarayinsa baiji yana kin Suwaibarba Domin bata da muni ko kadan itama doguwa ce,ammh kuma baka ce ita,tana kyanta babu laifi wanda kyan nata mai dauke dawani Sirri ne,sai da wanda yakaremata kallo yake fahimtar haka,Mallam Shi yayi alqawarin gina musu gida su tare nan Filin dake gaban nasu yasa aka tada gini,Ganin haka yasa in akayi abinci sai indo ta umarci Suwaiba data dinga dauka tana kaiwa mijinta adakinsa na zaure,to kusan sha"anin miji da mata,kuma gashi suna son juna,daya nemeta batayi yunkurin hanashi ba tabashi kanta,Ranar da Abun ya faru duk Nuku nukun Suwaiba sai indo ta gane saboda budurci ba wasa bane,ta rude ita da kanta tagasa yarta ammh kuma Abunda ya faru bai mata dadi ba batason mai zatacema Mallam ba,don yana mata fadan barinsu suna kebewa yace yafison koma miyene,in aka kammalla ginin Zasu je chan Niger sukaga dangin Abdulnaseer din in sundawo sai su bashi matarshi koma miye zai faru alokacin babu damuwa..,Indo boyewa mallam tayi bata bari yaji komai ba,balle Ya Fahimci wani Abu,sai dai tayima Suwaibar jan ido,tare da tsoratar da ita,akan tana sake bashi kanta zatayi ciki,kuma in mallam yagani sai ya bata mata Rai,jin haka yasa Suwaiba ta tsorata koda mijin nata yakara nemanta sai tayi gaddama,ammh kusan sha"anin rayuwa,dakuma karfin soyayyar miji da mata,da kanta takai kanta komai ya afku,ammh wannan karan bata bari indo ta fahimta ba,watansu biyu da aure Mallam ya kammallah Shirin tafiya Niger wajen Dangin Abdulnaseer din,sai me Ranar kwatsam Daga mallam ya aiki Abdulnaseer kasuwa da kudade kimanin Dubu dari biyu,yakaima wani abokin kasuwancinsa,zai tafi saro awakai ne,kuma shi ga wannan Tafiyan sai sukayi mgana kan yabashi sakon shi zai je ya siyomai,daman Abdulnaseer ke zuwa,jin haka yasa yabawa Abdulnaseer kudin ya tafi kaima mutumin,Ammh Abun mamaki Tun safe yafita har dare babu lbrinsa,Mallam hankalinsa yatashi yakira Abokin nasa ya tambayesa ko Abdulnaseer yazo,Abunda yabama kowa mamaki cewan dayayi tun safe dayace zai aikosa yake jiransa ammh shuru,hankula fa suka tashi har aka kwana babu lbrin Abdulnaseer Tuni ,Suwaiba ta rasa sukuninta sai kuka takeyi,Abu tun anaganin wasa sai gashi an shafe sati babu lbrin Abdulnaseer duk inda mallam zai saka abincikamai an bincika ammh babu amo babu lbri.

Fadin irin tashin hankalin da wannan Ahali suka shiga bata baki ne,domin Suwaiba bataci bata sha sai kuka,bala ko dayaji,kallan mallam yayi yace"Kagani ko Baba wlh Abun na gudar mana kenan Tun farko nayi Tutsu a al"amarin.."Mallam ya gyada kai yana fadin"Har yanzu jikina yaki yardan Abdulnaseer zai iya aikatamin haka,zuciyata tafi karkarta akan WANI AL"AMARI NE..,Dabam yafaru dashi,ammh babu komai Koma miye Mucigaba da gayama Allah.."

Wata daya kenan Babu lbrinsa tun ana cigiya har akagaji aka zubama sarautar Allah ido,an samu saukin damuwar ta suwaiba,sai da kuma yanzu ciwo ne ya tasota gaba,kullum da zazzabi take kwana,ga shi komai taci sai ta amayar dashi ta rame ta lashe..ganin Babu yaki ci yaki cinyewane yasa Bala daukanta zuwa ABU CHIKA binciken farko aka gano dan karamin ciki na tswaon wata biyu da kwanaki,iya razana bala ya Razana,haka mallam yaji sanda lbrin yazomai,indo batayi mamaki ba sai dai Fargaban Abunda zatafadama mallam takare kanta,haka mallam ya tasa suwaiba agaba yana tambayabta waye yayimata ciki,don shi bai kawo Abdunaseer bane,Suwaiba na kuka tace Abdulnaseer ne,da mamaki Mallam ke kallonta kafin yace mata waye Shaidanta Daga ido tayi ta saukesu kan indo,Mallam dayaga haka sai yamaida kallansa kanta yana tambayanta meta sani game da hakan,cikin kaskastan dakai indo tamai bayanin Abunda yafaru takara da cewa yayi hakuri boyemai datayi,Mallam yayi Shuru yana jinjina al"amarin,Domin basu dawani Tsumi ballatana dabara sai na barma Allah..

  Mallam ya kwantarma Da Suwaiba hankali inda yace tayi kokarin kula da kanta da Abunda ke cikinta,Hankalu sunfara kwanciya har cikin suwaiba yakai wata biyar tafara zuwa awo,akuma lokacin Bala ya kamallah degree dinsa harya daura masters dinsa,sai kuma wani karin jarabbawan data bullo musu,domin mutane anguwa suka cha da maganganu na cewa Suwaiba diyar mallam tayi cikin shege,da mallam yaji batun sai da ya kwanta ciwo saboda damuwa,domin baya da ikon kare kansa da yarsa tunda kuskuren nashi ne,shaidun daya daura auren agabansu almajiransa guda biyun tuni suka koma garinsu abokinsa kuwa auren ba dadewa Allah yayimai rasuwa,baya da bakin da zaiyi mgana,karshe sai da fita ta garari indo domin duk inda taje ana tafe zundenta ana yada mata habaicin Yarta tayi cikin shege,Shiko mallam daina ma karatun yayi domin ko almajiran dayake ma karatun sun gudu,Tunda mganar ta fita,bala kuwa Shima lbri har cikin mkranta ana tafe yadawa kanwarsa tayi cikin shege,damuwa tare da tsananin ciwo ya rafke mallam kwance,dama Shine kwarin gwiwansu to shima ya kasa,Alokacin ne,kuma bala ya samu aiki a gidan Radion Nageria kaduna ashashen lbru,lokacin kuma Cikin suwaiba yakai wata na bakwai,Kwanan Mallam bakwai yana jinya jikinsa ya rikice suka daukesa suka kaisa asibitin al madina,sai dai kash kwana daya yayi mallam Shehu Akarami ya amsa kiran mallacinsa,ammh ko da ya rasu yafadama iyalansa kada su kullaci Abdulnaseer domin haryanzu zuciyarsa tana fadamai bada gangan bane ya aikata musu haka,akwai wani boyayye Al"amari,Mutuwar mallam ta girgixa mutane dadama ciki harda indo da bala da Suwaiba,wanda sukayi kuka,kamar zasu mutu saboda rashin bango agaresu,Ranar da mallam yayi bakwai kuma sai ga wata mgana wai Suwaiba ta kashe mahaifinta da bakin ciki,abu goma da ashrin gata da ciki,ga mutuwar mahaifi ga bacewar miji,ga Zunde mutane dawanne zataji,indo ko dama tuni tayi rauni dare daya Hawan jini ya fadeta ta mutu,tsakaninta da mallam kwana 70 ne,topha ta faru ta kare,maraici ya lullube Suwaiba da bala,lokacin yana gabda kammallah master dinshi,shiyasa yazama uba ga Suwaiba,shike lallashinta batare da shawara da kowa ya saida duka kaddarorinsu ya biyama mahaifansu bashi,ganin zaman zaria bazai yuyu dasu ba yasa ya saida harta komai nasu gidan dasuke ciki kadai yabari,dakanshi yahau mota ya tafi garin gombe,inda basu da kowa ya siyama Suwaiba wani dan matsikacin gida da taimakon dilallai,Koda ya dawo yafadama Suwaiba hukuncin daya yanke bata damu ba,saima dadi dataji domin garin zaria ya fitarmata akai kwata kwata,ko fita tayi yara sun dinga binta kenan wasu harda jifa,.

  Bala da kansa yadauki kanwarsa yakaita garin na Gombe da kansa,ya damkata hannun makocinta wanda garun gidansu yake ahade wato Mallam lawal bature,wanda ya kasance yana da matar aure daya Fatima,ammh basu taba haihuwa,asa"a Lawal din zaiyi sa"an Bala haka itama matar nasa bata fi sa"an Suwaiban ba,Ganin yadda suka anshi amanar daya basu hannu bibbiyu ne yasa ya zaunar dasu ya karanta musu komai na tarihin rayuwarsu daga karshe yabar amanar kula da Suwaiba da Abun zata haifa awajensu Tunda shi zaikoma ne,Saboda aikinsa da kuma hada kan karatunsa,sunmai alqawarin kula da Suwaiba tare da riketa tamkar nasu,yaji dadi sosai anan ya kwana washegari yayi sallama dasu yakoma kaduna bayan ya jibgemata kayan abinci da kudi harda siyayyar haihuwa suka rabu tana kuka yana kuka,wayyo rayuwa kenan..

Yana komawa yamaida kai ga hada kwalin master dinshi,yana kuma cigaba da aiki a gidan Redio Nageria kaduna,gefe daya kuma yana harka da yan Siyasa tunda yana hira dasu,kuma yana musu tallace tallacen siyasa nan da nan Sunan Bala shehu Akarami yayi Fice kowa ya Sansa,duk bayan sati biyu yake zuwa gombe ganin Suwaiba,ana wannan halin ne ya siyamata waya saboda wata mtsala in tataso basai ansha wata walaha ba,yafadama su mallam lawal da tafara nakuda suyi kokarin kaita asibiti.

Haka akayi Watan biyu da komawa gombe wata ranar jumma"a da yammah tafara Nakuda Allah yasa Fatima na kusa da ita,tabazama waje ta kira mallam,dayake dan sana"ar saida kayan gwari yake,anan kofar gidan,da hanzari ya nemo mota suka kaita asibiti,Suwaiba tasha walaha don sai da ta kwana ta wuni kana ta haifo santalelenta danta mai kama da Ubansa sak,kato dashi wanda yana fitowa Duniya Bala yana karisowa asibitin,lokacin da aka miko masa Yaron kura masa ido yayi,yana ganin tsabar kama dayayi da mahaifinsa Abdulnaseer,yaron ko yana harba kafa,alamar karfi,nan da nan Bala ya rumgumesa yana fadin"Sannu da zuwa Duniyarmu *ALIYU GADANGA...*

       #Comment,share and vote..#
      #Janafty#....
*ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘 Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

_*Special Thanks to Hussain80k😝 and HassanATK...Sakallahu Filjannah Dudes😘*_

*NOT EDITED*💥

*Chapter4*

   ""Kwanan Suwaiba biyu a Asibitin kafin asallamota tadawo gida,Bala yayi Namijin kokari akan Suwaiba domin Duk Abunda uba ke ma da,da Abunda miji zai ma matarsa sai da yayimata shi,mallam lawal da matarsa Fati suma sunyi namijin kokari kan Suwaiba,Fatima nan take wuni sai dare take komawa gida,ita zata sanyama Suwaiba ruwan wanka ta juyemata,kafin tazo tayima Aliyu wanka wanda Sunan da bala ya sanyamai kenan,Suwaiba bata nemi komai tarasa ba na bangaren rayuwa,bangaren yar"uwa kuwa Fatima ta koremata dukkan kishirruwan su.

Kwanan Bala uku agarin Gombe yakoma Kaduna bakin aikinsa,Ranar suna tana zagayowa aka Yankama Aliyu raguna guda biyu,makota da yan"uwan Fatima dana mallam lawal sunzo tayasu murna,dayake suma din yan Asalin Yan gombe ne,Anyi Abun cikin Mutumci da jin dadi,Suwaiba tacigaba da kula da kanta tare da Danta,duk da mutanen anguwa sunata zunde cewa tazo anguwan da ciki ta haifeshi batare da nuna alamun tana da Aure ba,domin ada sun zata Bala ne mijinta,ammh sai daga baya suka Fahimci cewa yayantane ba mijinta ba,duk da haka Suwaiba ta toshe kunnanta bataji bata gani,ta dauki nasihan dan"uwanta daya cemata ta maida hankalinta wajen kula da kanta da Abunda ta haifa.

  Aliyu nada Shekara uku aduniya babu inda baya zuwa yayi wayau haryafara Tafiya,alokacin ne kuma Bala yayi Aure da matarsa Umaima yar kadunane Haifaffiyar Kabala ce,mahaifinta shima tsohon dan siyasa ne,tunda shine tsohon mataimakin gwamna a gwannatin data sauka,Akwai girmamawa tsakaninsa da Bala,tun mahaifisu na raye yasan mallam,tunda yace sunyi karatu wajensa,to shigowar Bala harkan Siyasa ne,yasa suka sanjuna,kuma shida kanshi yayimai tayin Auren diyarsa tasa Umaimah,anyi biki lafiya amarya tatare agidanshi dake Anguwan Dosa,gidan yana da girma wanda Bala yadau tsawon lokaci yana ginashi,bayan Aurensu da wata biyu ya dauketa yakaita gombe don ta gana da Kanwarsa Suwaiba,hakika Umaima ta tsausayama Suwaiba ganin inda takoma da rayuwa daga ita sai Da"nta Aliyu wanda yana girma wayonsa da kwazonsa da Karfinsa tare da kamaninsa da mahaifinsa suna kara bayyana,awannan zuwan ne Bala ya sanya Aliyu awata mkranta da"a ke kira MATRIC INTERNATIONAL SCHOOL GOMBE..,Mkrantace mai tsada domin sai ya'yan wane da wane,kowani kusa agwannati ko yan siyasa,Cikin nasara da hazaka Aliyu yafara karatunsa Koda akayimai interview Malaman mkarantan sunyi mamakin kaifin basiran yaron,duk da ance baitaba hallartan mkranta,ammh dayake Suwaiba bata wasa zama take dashi takoyamai Dak da iya Abunda tasani na boko dana Arabi,Nursery 2 aka sanyasa saboda yadda sukaga yaron da kaifin kwakwakwa,kafin Aliyu ya rufe shekara sunansa yayi Tambari a mkranatar nan saboda yadda Allah yayima yaron baiwan karatu Shiganshi Shashen primary yasa sunanshi yakara fitowa domin koda yakeda kankantar shekaru ana zuwa dashi gasan mkranta.

   Watan Umaima tara ta haifo santalelen Danta mai kama da ubansa sak,Ranar suna yaro yaci sunan HAISAM,wanda tsakaninsa da Aliyu shekaru hudu ne,bayan shi tazo tayi yan biyu, MARDIYA DA MADINA,Daganan bata kara haihuwa ba, haihuwar Haisam dai Suwaiba bata samu zuwa Kaduna ba saboda mkranatar Aliyu,sai haihuwar yan biyu ne taje kaduna saboda lokacin su Aliyu sun samu hutun mkaranta,sati daya sukayi akaduna kafin Su dawo gombe,Suwaiba tasan yarda take da Aliyu,tun yana yaro,yana da kiriniya da kuma son wasa,ammh bata bari yana Fita,sai dai in zai fita wajene ya zauna wajen mallam lawal,kokuma Fatima tatafi dashi gida,ammh kuma baya zama,da fari ta sanyashi a islamiya anan anguwan ammh sai yaran mkranta suka fara kyamatarsa da kokarim kiransa da wanda bai da uba,Kullum da kuka yake dawowa,yana fadama Suwaiba Abun na damunta,tana tsoron kada su sanyama yaronta wani banzan Tunani,sai kawai ta cireshi ita takoma malamarsa tunda daidai gwargwardo tana da ilimin Addinin harda na boko,sai takoma tana koyar dashi agida,tun yana yaronsa Suwaiba ta fahimci Danta yana da bala"in zuciya gashi tun yana karaminsa yake da bala"in karfi kamar doki,shiyasa take binsa ahankali,Abu dayane yake cimata tuwo a kwayar irin sunan da yan anguwa suka sanyama Danta wai DA'N MACE,tun Abun bai damunta harYafara damunta,shiko Aliyu tun yana dukan yara in sun kirashi da sunan haryakura yafara amsawa,saboda ya yarda shi din Da'n mace ne,ammh kuma macen ta bambamta da sauran mata saboda jajircewanta akan Rayuwar Dan"ta.

Aliyu nada shekara Tara Aduniya Fatima ta samu ciki,wanda ya kasance yana bata wahala,farinciki wajen mallam lawal d Fatima ba"a mgana,ita kanta Suwaibar tana murna da hakan,don ita da Fatima tamkar yaya da kanwace,Saboda laulayin data fama dashi mai zafi ne,yasa mahaifiyar Fatima BABA ADE Tadawo nan gidan tana zaune da ita,tana bata kukawa,duk da itama Suwaiban data gama aikin ta zata rufo gidan tashiga gidan mallam lawal tana taimakama baba Ade dawani Abunda ba"a rasa ba,Cikinta yayi girma sosai kuma yabata wahala,wata tara nayi ta haifo yarta mace santalele da ita,bayan bakar azaban dataci asibiti,wanda Bala shi yayi wannan dawainiyar saboda alherin Mallam lawal da matarsa Fatima garesa dashi da kanwarsa,harta

Please Login or Register in order to submit comment