Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balle kofan,na shigo har cikin naci maka mutumci,tunda kan mace,gadanga zaka dinga min kyaluwa ina mgana.."Tafada tana kwafa,Ajiyar zuciya ya sauke kan ya mike jikinsa asanyaye,bude lumsassun idanunsa yayi,bansan sadda na Furta subhannallah ba,saboda yadda idanunsa,suka chanza launi,sunkoma red sosai,Jikinsa babu kwari yazo ya murza key din kofar ta bude,bai bi takan Goggo da jabir dake tsaye ba,ya juya yakoma cikin falon yazauna kan kujera,yana kauda kansa,Shigowa dakin Goggo tayi tana fadin"Gadanga..Gadanga..Gadanga.."Saunawa na kiraka.."

Ko dagowa baiyi ba,yace cikin husky voice dinsa"Wai ni Goggo don Allah menayi miki ne?kamata fa yayi ki tsausayamin na rasa,love of my life,ammh kinzo sai fada kikemin.."Yafada yana wani kyabe fuska kamar zai yi kuka,Jikin goggo ne yayi sanyi ta karisa gareshi tana fadin"Yo ai kaine gadanga wani lokacin da ban haushi,ai ni na dauka bazaka wani damu ba,duba da yadda mahaifinta ya tozartaku gaban dubban jama"a,wlh indai kana da zuciya bai kamata kaji dacin Abun ba.."tafada tana zama kusa dashi kansa ya dauka ya kwanta bisa cinyarta yana fadin"koma miye,goggo i Love her,duk da Abunda mahaifinta yayi i knowa Ni"ima tana cikin wani hali yanzu cuz she luv me goggo i swear she can do without me.."Yafada yana damke hannun goggon

Dungure masa kai tayi da dayan hannunta tana fadin"Wai ban hanaka min mgana da wannan yaren Nasaran ba,sai na fara cin kaniyarka tukunnah ko"Tafada tana yar dariya,bai tankata ba ganin haka yasa ta hausha shafa kanshi tana fadin"karka damu kanka Kaji,Allah yabaka mace tagari saliha,na tabbatarmaka Azeema zata zemamaka sanyin idaniya nan gaba,mganar mahaifinka kuwa mucigaba da addu"an gadanga inda rabon sake haduwa,Allah zai hada,ammh ina ji ajikina,Abdulnaseer bai mutu ba yana nan Araye,Ammh inda yakene,ban sani ba,Allah shiya barma kansa sani.."Tafada idonta na cikowa da hawaye,mikewa Aliyu yayi yana kallon goggo kan ya saka hannu ya shafa fuskarta yana fadin"To goggo,in bai mutu ba,yana ina,? ko yan"uwanshi ba wanda zaki tuna,ko yataba fadamiki.."Shuru goggo tayi kan ta sauke ajiyar tana fadin"Gaskiya baitaba fadamin ba,sai dai yana yawan Ambatan Agadez domin yacema mallam ko abaya daga yankin ya fito,ammh kasan Agadaz ba karamin gari bane,kuma shekaru sunja,gaskiya mawuyanci Abune,agano wanda ya sanshi sakamakon babu wata shaida da zata bayyana hakan,..,"Tafada muryanta asanyaye."

   mirmishin karfin hali yayi yana kallon jabir dake tsaye yana kallonsu cike da tsausayi,kauda kai yayi yana cije lips dinshi ganin haka goggo ta dafa kanshi tana fadin"Aahhh..Haba Aliyu gadanga kusar yaki,Soja mazan fama,ko filin daka asan takunka,makiya da Abokan gabama tsoronka suke,kaga Saurayi na mamanshi uhmm,kaga Ango Azeema ka.."Saurin mikewa yayi yana dariyan Dole jabir ya tayashi,hanyar bedroom dinsa yanufa yana fadin"Sai da safe Goggo,plz go and sleep,nasan kin gaji dayawa.."ya fada yana fadawa bedroom din ransa bace,babu Abunda yabatamai rai sai kiransa da Angon Azeema da goggo tayi,saboda bacin rai kamar ya kunduma zagi,ammh sai ya tuna goggo ce,ita baikamata azageta ba,uwace,uwa kuma tanada matukar muhimmanci,balle tashi data kasance na mussaman ne.

  Goggo batai gaddama ba,ta mike tana ma jabir sai da safe,tasan ko banza ya sauko daga muguwar bakar zuciyar da yahau,barayinta takoma tana yan wakewakenta ko ajikinta,domin ita wannan Aure yayimata daidai,sai alokacin ma ta tuna da Azeemar wanda tun da rana tace mata zata gida,tayi wanka ta dawo ammh Shuru bata dawo ba,bata damu ba sanin halin Azeema da rashin son mutane da hayaniya yanzu haka Rashin sakewan yasata kin dawowa,alwala goggo tayi tazo ta kabbarta sallar,bayan ta sallame issha"i tayi shafa"i da Wuturi,bayan nan ta dukufa rokama Aliyu fatan nasarar rayuwa kafin ta gangaro,kan Allah yayima Aurensu da Azeema albaarka tadau tsawon lokaci tana addu'o'i kafin ta kwanta,zuciyarta fess.

Aliyu yana Shiga bedroom dinshi yafada wanka,ya dade aciki bayan ya Dauro alwala ya fito,yana daure da tawul akwankwansonsa,daya kuma yana kansa,yana tsane ruwa da jabir ya cikaro wanda yayi dare dare bisa lafiyayye gadon dayasha wani ubansu bedsheet,kallo daya yayimai ya kauda kai Aransa yana fadin"Dan iska,ba don Tsohon dan Sandan nan,yayimin cikas ba,ai da yanzu nine bisa gado na ina biyan ladan kudina.."Yafada yana wani Runtse ido,kamar yana Kallon Tanadin dayayima yau din.

Gaban Derressing mirrior din dake Dakin ya isa yana kokarin bude wani lotion na kamfanin OLIVE yana shafawa kallonsa Jabir yayi kafin yace"Hy Dude wai duk wannan Shariyan namiye ne? bafa ni bane kwamishina Ahmed Sidi na iya ba,balle ka huce akaina,kuma Dude wlh Seriously Azeemar dakake kumburi don Ka aureta,yasin tafi Ni"imar taka komai,kai infact ma itace matar Rufin asirinka,don ta rufamaka lokacin da Uban Ni"ima ya tona maka,so Ni banga Abunda damuwa in kayi duba da komai MUKADDARI NE.."yafada yana yar dariya,wani kallo Aliyu ya wurgamai ta madubi baice komai ba,ganin haka Jabir yakara cewa"am wlh Dude ta hadakomai dakake bukata wajen mace,i know kaima aikana ganin yarinya,so quiet da ita,gaskiya kana da sa"a Dude.."Wani Takaichi ya kulle Aliyu baisan sadda ya waigo yana fadin"Nagode Shehi jabiru da Tunatarwa,buh juz give me 5 minutes,.."yafada yana jan Side drower din dake gefen gado,ya fiddo da wani Memo da pen,ya yagi daya ya dora zai fara rubutu Jabir ya kallesa yace"Mezakayi..."ko kallonsa baiyi ba,yace"Sakinta zanyi...!kwalalo Ido jabir yayi kan yace"what are u mad.."?ka saketa,kai Dan iska ne..? yafada yana kama baki,wani dirty look Aliyu ya sakarmai kafin yace"yap,yo ai naga kafini bukatarta,Tunda har ka iya kwatanta tana Abun bukata na more rayuwa gata She iz quit ko?sai na sakar maka ita,tun kafin kafara tunanin binta da Aurena akanta.."yafada yana wani hade rai.

Tsaki jabir yaja kan yace"Buraouban ka,banza kawai sakarta manq,wazai hanaka.."yafada yana ballamai harara,dariyan yake Aliyu yayi kan yace"Kai ne Babban Da'n iska,in ba Da'n iska ba,gaban mijin mace ka hau suffanta ta,ai kai ne banza,ajawo gara kawai.."yafada yana wurgamai takardan da pen din afuska yana fadin"Take ur eyes away from my Wife,i Swear zan iya kashe mutum in yakara suffata Iyalina..yafada cikin kakkuasan murya,yana wani buga kafa

Zabura jabir yayi ya duro daga gadon yana fadin"Me kake takama dashi?Kaki? Kai mallam kamar yadda alluran ke yawo ajikinka,haka take yawo ajikina,ko zamu gwada,billahil lazi sai na barar maka da hakoran gaba,karyan zama Shege kake.."yafada yana hararansa fuskarsa ahade,baya Aliyu yaja yana fadin"Ubanka zanji u already know me ko"?yafada yana wucewa jikin wardrope dakin, yana kokarin budewa,da harara jabir ya rakasa yana fadin"wlh an ma Cuci marainiyar Allah,An hadata da Da"n iskan Soja kawai,ai daka tsaya kaga yadda zan sauyama kammanin.."Dariya Aliyu yayi yana fadin"Sai kaje kafadamusu su kwance auren su auramaka tunda kai ba Da'n iska bane,tunda na lura u are jealous,.'ko kallonsa Jabir baiyi ba ya fada Tiolet,yana kunkuni yana fadin zai zane Aliyu da daddaren nan,shiko yana jinsa yamasa banza,sai ma jallabiyansa daya zura ya Shimfida darduma Ya Tada salla,shiko jabir koda ya fito shima Daure da alwal,shima sallar ya tada,kowa yana nashi ko wajen kwanciya sai da suka buga,harda Ture ture agado kamar wasu yara,dat how Captain Aliyu and captain jabir Art when they are together,kuma basu iya rabuwa da juna,ko cikin bariki suna tare,ammh kuma kowanne yanajin kansa awani Shege ne...


     ********

    "Ni"ima kuwa cikin mawuyacin hali aka kaita Asibiti,likitoci suka amsheta da gaggawa zuwa emargency Sun ci bakar wahala kafin su daidaita numfashinta,domin jninta yayi bala"in hawa,ga zuciyarta ta buga sakamakon wani Abu dataji wanda yayi matukar razanata,kuma zuciyarta ta Firgita da Abun,yanzu koma miye,ayi kokarin ganin An magancemata matukar ana son Rayuwarta ta Daidaita.

   Bayanin da likita yayi masa su mami kenan da kwamishina,wanda tunda likita ke mgana,zufa ke ketomai sai yanzu nadamar Abunda ya aikata yazomai,sam baiyi Duba da halin da tilon yarsa zata tsinci kanta aciki ba,kawai yana hango kada yabata rayuwar yarsa ne da zuru"arsu,kallon sa Mami tayi tana Tsiyayan hawaye tace"Kaji ko,Haba Ranka shi dade,tayama za"ayi kafara yanke wannan hukunci batare da ka shawarceni ba,ni da ka kirani dana fadama zakayi kuskure domin Ni'ima bazata iya rayuwa babu Aliyu ba,tana mugun sonshi,tariga data sallama ma kanta yau zata zama matarsa,ammh duk ka ruguza komai,na shiga uku ni Jamila,bani da kowa sai ke Ni"ima tabbas bazan zura ido,kishiga wani hali ba,ni zani gidansu Aliyun dakaina na roke mahaifiyarsa yadawo ya aureki.."Tafada tana mikewa,da sauri kwamishina ya rikota yana fadin"Mamin Ni'ima where are u going? kidawo wannan ba mafita bace,infact ma yanzu aka kirani aka shaidamin basu bar wajen ba,Sai da aka Daurama Shi Aliyun Aure,kinga kenan ko kinje bazasu saurareki ba.."Kallonsa tayi hawayenta na zuba tace"Kaji ko? innalillahi wa'inna Alaihirraju'un wake da karfin gwiwan Tunkarar Ni"ima da wannan mganar,nidai bani dashi,wlh bani dashi.."Tafada tana kuka lokaci daya tana sulalewa daga jikinsa,Rumgumeta yayi yana bubbuga bayanta yake fadin"Banyi Tunanin haka,Sulaiman ne,ya dake kan baza"a Daura ba sai Dangin ubansa sunzo,wlh koni rainq babu dadi,shine ya dage,kuma kinga shine waliyinta bai kamata na tsinkashi cikin jama"a ba.."Dago kanta tayi tana fadin"Ka tsinka shi manq,say what,bakai bane gaba dashi ba,ai gashinan ya zugaka ka aikata Abunda yazo ya damemu,an barmu da wahalan zuciya data sarari,wlh Allah sai ya sakamana kan Abunda yayimana,kuma hakkin Ni"ima bazai taba barinshi ba.."Tafada tana fizge jikinsa,ta fito daga office din tana share kwallah,likita kuwa daman Ficewa yayi ya barsu,dafe kansa kwamishina yayi,kunyar Duniya da Nadama sun kamasa,itako Mami tana fita Munari tataso tana fadin"Mami ya jikin Sweetheart? tafada cikin damuwa,Wani kallon Mami ta watsama yan sanda take kare lafiyan kwamishina,lokaci daya suka fashe,ada sun kasa kunne ne suji mai zatace,hannunta Kawai mami takama suka koma suka zauna kantace"Komai ya dagule Muneera,don likita ya gayamana cewa zuciyar Ni'ima tayi Rauni,gashi kuma jninta yayi bala"in hawa,ceto rayuwarta shine bata Abunda takeso.."Dafe kai Munari tayi kantace"To Mami mai zai hana muje gidansu Soja mu gayamusu halin datake ciki ko Allah yasa zasu Taimaka ya aureta yanzu.."Girgiza kai Mami tayi kan tace"Hmm,ai bakin alkalami yari gaya ya bushe,muneera,kuma dama ance oppourninty comes one in life,ko kinmata,wajen su sukazo nema,kuma muka tozartasu gaban dimbin jama"a,Armm amaganar damuke ma yanzu basu tashi taron ba,sai da aka Daurama Aliyu aure,tayaya kike ganin zasu kallemu in mukaje musu da wannan bukatan,ai banajin zamu samu kyakayawan kallo,saboda mu muka saki damarmu.."Sadda kai munari tayi tana sharan kwallah takasa fadin komai,kawai jinjina al"amarin take,tanq ayyana yadda Ni'ima zata karaji matukar taji Sojanta yayi Aure,Mami kuwa tagumi tazabga,tana Tunanin mafita,Shiko kwamishina bai koma gida ba,sai da aka kawo Ni'ima daki na mussaman domin hutu,Mami ta bishi suka koma gida,don ta tahomata da kayanta da kuma tasaka masu aiki suyi girke tataho dashi.

______________

  Azeema bata yi sanyi da jikinta ba,sai da tagama duka aiknta na tsakar gida,kafin takoma ta daura girki Tuwo da miyar kuka,tanayi tana shiga Tunanim yadda makomar rayuwartake,ita gani take kamar amafarki wai itace matar Aure,matar auren ma mata ga yaya Captain? Abun nabata mamaki,ammh sanin bata da wanda zata fadama damuwarta yasa ta ijiye komai gefe daya ta cigaba da aikinta,Ramatu kuwa sau daya ta leko waje,tagani ko Azeema na aikinta samunta tayi lokacin ma tana tsalge,kwafa tayi takoma dakina,tana zaginta ita da Babanta tana fadin"kwadayayyu kawai,watarana sai kwadayi ya kashesu.."itadai ko Tak batace ba saboda inda sabo yaci ace ta saba da Halin Inna Ramatun..

Azeeza kuwa kuryan Daki ta shige ta haye gado tana kuka wurjajan saboda bakin ciki da kishi kamar ya kasheta,gawani tsanar Azeema dayakara tasiri aranta,yanzu ace Tayi shekara da shekaru tana Rainan Soyayyar yaya Captain Aranta,ta wahala akan Sonshi tagama tsara yadda zasu gudanar da rayuwarsu,ammh lokaci daya mafarkinta yatashi abanza,koda Yaya captain zai aure,Ni'ima tayi kuka,ammh zuciyarta bata kusa bugawa ba sai da taji ance Adda Azeema ya aura"Bala"i batajin ko sama da kasa zasu hade zata iya barma Azeema Sojanta,domin tayi alkwarin matukar Tana raye agidan Duniya sai ta Aure yaya Captain koda hakan zaiyi sanadiyar salwartar da rayuwar Azeemar ce ita babu ruwanta,kanta kawai ta sani,Koda Inna Ramatu ta shigo ta ganta tana kuka idanunta sunyi jawur,cemata tayi kanta ke ciwo,jiki na rawa inna Ramatu ta ballo panadol ta bata ta sha takoma ta kwanta lamo tana saka yarda zata wargaza rayuwar Azeema don yanzu ita tafi tsana akan kowa..

Ana kiran sallar mangariba Azeema ta kammallah komai,ta zuzzubama kowa a muhallinshi,tayi alwala tashiga daki takabarta sallah ta idar kenan,taji sallamar Mallam lawal,da hanzari ta fito daga dakinsu tana fadin"Sannu da zuwa Baba.."kallonta yayi sanda take shinfadamai tabarma akofar Dakinsu Baiyi mgana ba,sai da ya zauna yace"Yauwa Azeematu diyar Albarka.."Yafada yana kallon Fuskarta sadda kanta tayi kafin ta mike tatafi randa ta debomai Ruwa cikin wani kofin sulba tazo ta ijiye kafin ta shiga kichen ta daukomai wasu kwanukan sulba na tuwo dana miya,tazo ta ijiye kafin takoma gefenshi ta zauna tana fadin"Baba ga ruwa kasha.."ta fada tana mikamai amsa yayi ya bude murfin ya kwafa kai yasha dayawa kafin yadago ya mikata yana fadin"Alhamdulillah,Allah yayi miki albarka Azeema.."Cikin jin dadi ta amsa da Amin,budemai tuwon tayi,ta zubamai ruwa ya wanke hannu yafaracin Tuwo,wanke hannunta tayi itama tasaka hannu sunacin Tuwon tare,wanda daman ko karfe nawa zai kai baidawo ba,Azeema bata iya cin abinci sai tare dashi,ta riga ta saba tun tana karama,Inna Ramatu tayi bala"in tayi tsiyan ammh duk bataci nasara ba itako Azeeza Abun na cinmata rai,shiyasa take fadin Baban yafison Azeema kuma ba karyabane kowani uba yanason da na gari mai hankali da Natsuwa da tarbiya.

Tsab suka cinye tuwon kafin su wanke hannuwansu,Baba nata santi yana yaba girkin Azeema yana fadin"Uhm,diyar Albarka ta iya girki fa,zan yima mijinki albishir da yagama yin dace indai ta barayin girki ne.."Dariya take,tana jin dadin yadda Babanta ke yabonta tashi tayi ta kwashe kwanunkan takai kichen,bakin rijiya ta nufa zata jawo ruwa ya kwalamata kira yana fadin"Bar zuba ruwanan Azeematu,na hanakin zuwa bakin rijiya da dare,maza ki bari ki zo ki zauna nan mgana zamu yi.."Yafada fuskarsa ba alaman wasa,ganin haka yasa ta ijiye gugan tazo tazauna kusa dashi tana fadin"Gani Baba.."kallonta yayi kafin yayi ajiyar zuciya yana fadin"Yanzu daga gidan Baba Ade nake tace na gaisheki.."Washe baki Azeema tayi tana fadin"Kawata kenan,ina amswa Baba meta baka kakawomin..? Yar dariya yayi yana fadin"Bata bada komai ba,sai gaisuwa,aike yakamata kije ki kaimata."Daganan sukayi Shuru,Dan gyara zama Mallam Lawal yayi yana Fadin"Azeema..."Ta dago ta amsa Tana fadin"Na"am Baba.."Cigaba yayi da cewa'Kiyi hakuri Azeema nayi miki katsalandan na yanke hukunci batare da shawaranki ba,duk da ina da tabbancin Na Isa dake,kuma bazaki taba watsamin kasa a ido ba.."Dagowa tayi idonta ya ciko da kwallah,tace"Baba wacece ni agareka.."Yace'Ke diyatace..."Azeema tace"To meyasa kake cewa haka,Tun tasowata bansan kowa ba sai kai,tun bayan rasuwar mahaifiyata baka barni nayi maraici ba ka wahala dani,kayi hidima dani,niko wacece ni da bazan zama baiwa gareka ba Baba.!koda fansar dani kayi zuwa wata masaurata domin bauta Bazan bijiremaka ba,ballatana,don ka bada Aurena ga yaya captain Da ga Goggo wacce ta kasance makwafin uwa gareni,ashe ko in naki bin umarninka na zama butulu,kuma ban cika y'a ba.."Tafada tana fashewa da kuka.

Gabadaya jikin Mallam lawal yayi sanyi,tsausayi tare da kaunar yarsa,da girmama Kaifin hankalinta suka taru,sukaima yawa,dafa kanta yayi wanda ta cukwikwiyeshi cikin hijabi tana kuka yana fadin"Kiyi Shuru Azeema,dama nasan bazaki bijiremin ba,Tashi ki shiga daki ki kwanta Allah ya albarci rayuwarki,dana Aurenki,Allah kuma yajikan mahaifiyar fatima da Rahama.."Da Amin Amin Azeema take amsawa tana share hawaye.

  Inna Ramatu dake tsaye kofar dakinta tanajin duk Abunda suke fadi,taja wani dogon tsaki kan tace"mtsewwwww...Diyar so,an saka miki albarka,nikuma tawa wacce baka so ka tsinemata,dayake kwadayine,kazo kana lallabanta wlh mallam kaji tsoron Allah,ko fifinko dake nunawa kan ya'yanka Allah ya kamaka bazakaji dadi ba.."Ko kallonta baiyi Ba Azeema ta dago tana kallonta ranta na kuna ta shige daki tana fadin"Sai da safe Baba..."Allah ya tashemu lafiya.."yafada yana mike kafarsa ko kallon Inna dake tsaye tana jijjiga jiki bai yi,ba don ya lura sam Ramatu bata darajasa a mtsayinshi na mijinta,ta riga Tagama Rainsa,so take kullum su dinga hayaniya makota naji,shiyasa yake banza da ita,intagaji ta wuce,tunda ita ba karya bace.


         #Commet,share, like and Vote..#
         #Janafty ce....#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA .S. ZARIA(MMN USWAN)*
 
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

           *Chapter7*
  

Koda gari yawaye har sukaje massllaci suka dawo,Aliyu bai ko kalli barayin da Jabir yake ba,shima kuma bai tankasa ba,Suna dawo daga sallar asuba Aliyu ya shiga Hada kayansa cikin wata katuwar jakar baya,mai kalan Uniform dinsu na yaki,Jabir na kallonsa,ammh kanzil bai cemai ba,don ya lura sarautar tashi ta motsa,yana ji sanda Haisam yakiraasa suna gulmansa suna dariya,ammh sakamakon yau baya cikin mood din,nunamusu yayi baima san dashi sukeyi ba,ballatana ya tankamusu.

Misalin karfe 8:00am na safe,Wayarsa tana kara tana neman Dauki,ammh Da Aliyu ya dago yagamai kiran,sai ya kife wayar yana sakin Siririn tsaki,shi kadai Jabir yana kallonsa,yana so yagano waye ke kiran Aliyun ammh ya kasa ganowa,mikewa yayi daga kan gado yana mika yace"Dude wai shirin Tafiya ina kakeyi ne?Ko kallonsa Aliyu bai yi ba,illa kokarin zuke zip din jakar dayakeyi Dariya Jabir yayi yana fadin'Haba Dude don Allah warware jaka kada muje bariki ayi damu,kai zaka tsaya shan amarci sai nan da 2weeks zaka dawo bakin aiki.."

Wani Banzan Kallo Aliyu yayimai kafin yace"Ubanka ne zai sha Amarci ko? "Yafada cike da fusata baya jabir ya matsa yana fadin"Ah..No..No maida wukar daga Taimako Allah bada sa"a.."Kada kai Aliyu yayi kafin yace"Better Tunda barikin ba gidan Uban mutum bane,sai ya hanani komawa.."rike baki Jabir yayi yana yar dariya,Shiko Aliyu Tailet yafada Fuskarsa ahade babu alamar fara"a ko kadan,jabir bai damu ba,cos inda sabo yaci ace ya saba da Kala kalan Fuskar Aliyu.

Yana Shigewa Tiolet din ya Sufa zuwa ga wayarsa kirar iphone 9 yana Dauka Daidai kiran nakara shigowa *MUNEERA* batare dawani Tunani ba yadaga kiran ajiyar zuciya Muneera ta sauke kan tace"Hello Captain..."
 
Kansa Jabir ya shafa kan yace"Ya is captain buh not Captain Aliyu am Captain Jabir how can i help u..."Da Sauri Ni"ima ta karbi wayan tana fadin"Jabir don Allah kamin rai,ka hadani da Sojana,wlh zan mutu in banji muryansa ba.."Tafada muryanta na rawa,cikin alaman jin jiki.

  Gyara tsayuwa yayi kafin yace"Am So srry Ni"ima bazan mezancen miki ba,buh u already know Aliyu in yayi inrin wannan kafewar to sai Allah saukowanshi,koda kuketa kira yana gani yaki picking yanzu ma he iz inside d toilet dat why ma na samu daman Daukan kiran,am srry to say buh Abbanki mai kyautama kanshi ba wlh.."Yafada yana cije baki kuka Ni"ima ta fashe dashi tana fadin"Oh ya Allah help me..Na shiga uku wlh zan iya mutuwa indai banji muryan Sojana ba"..Sai dai ko ki mutu..."Jabir yabata amsa Aranshi,yana yar dariya daidai lokacin da Aliyu ya fito daga tiolet daure da wani karamin Towel akugunsa,daya yana kansa yana tsane Ruwan dake diga daga kan nasa,yana ganin jabir da wayansa,ya tsaya cak yana jifansa da wani dirty look,shiko yana ganin haka,sai yayi hanzarin bude wayar a sepeaker,daidai lokacin da Muneera ta amshi wayar tana fadin

  "Don Allah jabir do ur best wlh Sweetheart she seriously Sick yanzu haka muna Hopt tun jiya dataji Abunda ya faru,ta samu heartfailure,kabashi hakuri is not her Fuilt,yazo ya ganta ya lallasheta ko tabar kuka,wlh Tun data farfado take ta kuka tana kiran Sunansa plz Jabir..."Jabir yayi kasake yana bin Aliyu da kallo wanda ke rollin din idonsa yana wani cije baki,takowa yayi sai da yakusa gabda jabir kana yace da dan karfi.."Plz Dude tell dem to stay away From me..."Yafada muryansa na rawa,kallonsa jabir yayi sai yaga idonsa yayi ja,jijiyoyin kansa sun mike,Ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Kunji ko,plz karku sake kira,sai na nemeku don Allah,kubarsa Abun ya sakesa tukunnah,Ni"ima may Allah (SWA) Shifa u Ameen..."Yana fadin haka ya datse kiran,dagachan bangaren Ni'ima tanajin muryan Aliyu sanda yake mgana,batama gama jin Abunda jabir ke fadi ba,takara tsananta kukanta,kallonta Muneera tayi kan tace"Don Allah Sweetheart kibar kukannan hakanan,kiduba halin dakike ciki,in Mami tadawo ta tarar dake cikin wannan Halin u know bazata ji dadi bako? so plz Wipe ur tear don Allah ba karshen rayuwa ba kenan,kuma da yardan Allah zaki auri Aliyu.."Idonta jawur ta dago tana kallonta kafin tace"Are U sure..."Gyadamata kai Muneera tayi kafin tace"100%Sure Sweetheart..."Share hawayenta tayi kan takoma ta kwanta ta kurama Drip din da"ake sakamata ido tana kallon yadda yake diga sannu ahankali,lokaci daya ta runtse idonta kwallah na zubomata,ta rigaya data sani tayi bankwana da dukkan wani Farinciki Tunda Aliyu ya bar Rayuwarta.

Suko Anasu barayin Jabir na yanke wayar yafada wanka,Shiko Aliyu agurguje ya Shirya cikin wasu riga da wando black and white,kafarsa ya sanya wani bakin takalmi booth,sai kansa ya sanya wata bakar p-cap,ya dau katuwar jakarsa ya rataya yana Daura agogonsa na kamfanin Rado baki ahannunsa,Jabir ya fito,ganin Aliyu atsaye yasa shima ya shirya agurguje,shima yayi shigan Riga da wando,ammh nasa Neavy blue ne,shima jakarsa ya rataya suka dumguma suka fito,makulli Aliyu ya sanya Ya rufe shashensa,suka fada barayin goggo wacce ke kichen tana kokarin hada musu Abun kari,taji sallamarsu Fitowa tayi tana amsawa fuskarta na bayyana farincikinta data ciki.

  Ganinsu tsatsaye kuma ga kaya yasa tatsaya Tsurus tana fadin"Lafiyanku naganku da wata uwayen jaka.."Dukawa Sukayi dukkansu Aliyu na fadin"Ina kwana goggo,zamu koma kaduna ne,bakin aiki.."Yafada yana sunkunyar dakai,karisowa tayi tazo tazauna kan daya daga cikin kujerun falo tana fadin'"Kai ku kalleni nan bani son iskanci,ina zaku yanzu da farar safiya,kamar ana koronku,ina fa madafi Tundazu ina kokarin hada muku Abun kari ne,wlh baku isa ba,bazaku barni dashi ba.."Tafada cikin fada,Mirmishi Jabir yayi yana mikewa yace"Kwantar da Hankalinki Goggonmu basai kin bata ranki ba,zamu ci kalacin dakike Shiryamana kafin mutafi,medame dame aka Tanadarmana.."Yafada yana zama kusa da ita.

Washe baki yayi tana fadin"Yauwa Dan Albarka Kunun Shinkafane Sai Fanke danake soya muku,akwai Ruwan Tea wanda yaji citta,sai ku hada dashi.."Tafada tana kallon Aliyu dake duke,Mikewa tayi ta isa garesa tana fadin"Taso taso Gadanga,bar damuwa hakanan,ban hanaku tafiya ba,ammh ku karya tafiya da yunwa babu kyau,tunda gida kuke ba daji ba.."Tana fadi tana rikosa,mikewa yayi yana kallo goggo kafin yace"Karki cikamin ciki goggo,nakaasa jagorantan Bataliyan yaki na gaba.."Sajensa ta shafa tana fadin"Da"n nema kaida yakamata sai sati na sama zaka koma,tunda kana cikin Hutun amarci ne",bata rai yayi yana fadin"Soja baya Daukan Hutu goggo,koda yaushe burin sojan nageria kare dubban rayuwa daya rantsuwa wajen amsan kaki,saboda duk Abunda ya shafi kare hakkin kasata da al"ummata goggo bana jin son jiki a al"amarin...",kansa ta dafa tana fadin"Nasara tana tare dakai Gadanga,insha Allahu sai kasarka tayi alfahari dakai kamar yadda take alfahari da Sardauna.."Amsamata yayi da Amin,kan sukarisa ta zaunar dashi kusa da jabir tana fadin"Bari na kawo muku kalacin."Tafada tana fadawa kichen Jabir da Aliyu suka bita da kallon kauna da tsausayi.

Tana rawan jiki ta jera musu komai,basu ci da yawa ba,ammh goggo sai da ta dura musu kunun shimkafanan cikin wani karamin Flaks,sai Fanke ta zuba musu cikin wani karamar kula ta basu,tana fadin ko ahanya sukaji yunwa su tsaya su ci,amsa sukayi jabir na dariya,shiko uban gayyar yasan hali mirmusawa kadai yayi,sallama suka mata,Aliyu yaba goggo 10k dakyar ta amsa,wai yaya yabata kudi,har waje ta rakosu Aliyu ya Shiga garejin ya fiddo musu da motarsa 4matic baka,Suna kokarim Shigane sai ga mallam lawal ya fito daga gida,da hanzari Aliyu ya dakata bayan ya saka jakarsa abayan motan ya nufi mallam lawal yana dan Sakin Fuskarshi yana zuwa kusa dashi ya rankwafa yana fadin"brka da safiya Baba."Rikosa Mallam lawal yayi bakinsa washe yana fadin"Tashi Tashi gadanga,Lafiya kalau,ya katashi,yakuma kwanan goggonka.."Mikewa yayi yana fadin"Tana lafiya baba,dama zan wuce saboda ankira bakin aiki akwai wata bataliya da zan jagora zuwa yankinnan na zamfara ne,shine nakeson mu shiga kaduna da wuri.."Gyada kai mallam lawal yayi yana fadin"Eh gaskiya to Allah ya taimaka Allah ya doraku bisa kansu,kukuma Allah yayi musu albarka.."Da Amin Amin Aliyu ke amsawa kafin yamikama mallam lawal hannu sukayi musabaha,yana fadin"Zan Tafi baba,..Arrrm *AZEEMA* tacigaba da zuwa mkrantanta both islamiya da boko,in tana bukatar wani tashiga wajen goggo,Don Allah Baba ayi hakuri da yanayin aikinmu sai na dawo sai munsan Abunyi.."Girgixa kai mallam lawal yayi yana fadin'"Ah babu komai Aliyu Fatanmu Allah yabaku nasara,sai ka dawo.."Da haka suka rabu cikin mutumci,yana tsaye har motansu Aliyu ta bace Alayin,kafin ya fara share inda zai basa kayan gwarinsa,yana yi yana girgiza kai in ya tuna tijaran da Ramatu tayi yau da safe,Abun sam babu dadin ji.

    *********

*NIGER REPUBLIC*
 
  Awani babban masarautace dake yankin *AGADEZ* Da misalin karfe 3:00pm na silasailin dare ne lokacin adaidai lokacin acikin kayatattaciyar masaraurar wacce takwafa tarihin na tsawon shekaru hamsin da doriya ta mulkan yankin na agadez.,masauratace babba wacce take kunshe da tarihai masu dimbin yawa tunkam zuwan addinin musulunci,Yanzu da ilimi ya yawaita akasamu yan boko suka

Please Login or Register in order to submit comment