Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su saki Fitsari awando ganin yadda yake kallonsu Jiyoyin kansa na mikewa saboda bacin rai,Kallonsa ya maida kan Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka Jikinta duk ya baci ga Shi hijabinta duk ya manne mata ajiki,baisan dalili ba,sai yaji wani mugun Haushi ya tokaresa kamar ya bita cikin kwatan ya ci ubanta Tunda ta zama solobiyo,Sulaiman kuwa yana ganin captain ya koma gefe yana dariyan mugunta domin yasan daga yanayin kallon dayake musu yau din nan sai sun gane basu da wayau..

Taku yafarayi zuwa garesu yana wani kame idonsa guda daya na salon mugunta,Tuni suka tsorata suka fara ja da baya,Azeema ko jikinta na rawa ta mike saboda atunaninta wajenta zaizo ya fara ta kanta sai ta ga yayi Pointing dinsu Azeeza yana fadin1,2,3,4,5,6....All af u come here...',Yafada cikin gadara,Ai da wani tsoro suka fara kallon junansu tsawa ya daka musu yana fadin"don't Force me to Mention my Statement..All of u will be in Tourble i swear..",Yafada yana wani buga kafansa akasa,wanda saida Mutanen wajen suka Razana.


_Wowow...Ran Maza fa ya baci..Su Azeeza kun Shiga Tarama ba Uku ba,do da Alamu Fushin sojan zai sauka bisa kanku,kilama Harda horan Sojoji zai baku😂Wayyo,Allah ya kwaceku maganinku kenan,Fans ya kuka gani kuna goyan bayan Captain yaci kaniyar su Azeeza?..Cike Tagging dinki da kayatattacen Sharhi ta hakan ne kadai zan gane kuna biye dani_



         *Comment,share and vote...*
         *#Janafty...#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


      *Chapter 10*

     ""Jikinsu na rawa suka fara takowa zuwa gabansa,kowacce tanaji kamar ta saki Fitsari awando saboda tsoro da Razana,Kafin su kariso ya sunkuya akasa ya sanya hannu ya dauko wata sanda baya yakoma daga chan wajen inda ya faka motarsa ya shiga jan Dogon layi,yana gama ja,cikin wani Fusata yazo ya wucesu kamar kiftawa da bismillah ya isa chan nesa da bohol din ma nan yaja wani dogon layi,Ko kallonsu bai yi ba,daga chan bangaren ya nunasu da hannu yana fadin"Ku yan iska ko? marasa mutumci,dama kune marasa tarbiyan anguwan ko? ok To iskancinku yazo karshe daga yau oya all of u ku fara frog jump daga inda layin chan yafara zuwa inda ya kare,kuma 50 zakuyi each zuwa da dawowa to be counting one ne..."Yafada cikin gadara da isa.

  Gabadayansu suka kalli juna ganin zasu batamai lokaci yasa ya fara taku zuwa garesa ai da gudu suka isa ga layin kowacce ta duka tafara,daga nesa yace"duk wacce batayi da kyau ba,ko ta gama sai ta sake so is better da ki zage kiyi yadda nace..."Yafada yana harde hannuwansa akirji Sulaiman dake gefe yana kunshe dariya yace"Yallabai zanyi musu couting.",Da kai ya amsamai yana cije lebe kafin yace"ka sa ido akansu..Duk wacce bata yi dakyau ba juz ka waremin ita yau zasu ci ubansu ne..",Yar dariya Sulaiman yayi yana fadin"Baka da mtsala yallabai,ya fada yana kallonsu yana fadin"Toh maza kuyi da jiki...one,two...three,wlh kika bari aka barki abaya zan tsayar dake.."Yafada yana dariya jin haka yasa suka zage sai yi suke kafin kace kwabo sun Fita hayyacinsu ko goma basuyi ba,ammh haka suke kuka da majina,Tuni layin ya cika da mutane anata dariya wasu kuma na murnan Abunda ke faruwa don daman kowa yasansu Azeeza alayin basu da kunya ko kadan,wasu sai fadi suke gwara hakan,kila daga yanzu sayi hankali.

  Azeema na gefe tana barin jiki Tana kallonsu Azeeza yadda suke kuka harda majina,Dasun bude baki zasu yi mgana sai captain yace +anoder 50 din,dole sukayi Shuru da bakinsu domin Wannan wahala tayi kama da wahalan gidan yari ne,Shiko yana gefe ya harde hannuwa bisa kirji yana kallonsu yana dan murmusawa,Da kallo yabi Azeema yadda tayi wani kalan Tsausayi nufota yayi sai ta hau ja da baya,tana ganin ya kariso sai ta duka ta kama kunni tana fadin"Don Allah kayi hakuri nima zanyi..Zanyi.."Take fada tana kokarin Fara tsallan kwado tsawa ya dakamata yana fadin"Stand..."mikewa tayi jikinta na bari,Tsaki yaja kafin ya juya yana fadin"Ina abubuwan dakika zo dasu diban Ruwa.."Bakinta na rawa ta nunamai botikan guda biyu,don dayan kam ya fashe,bai kara kallonta ba ya isa garesu,da hanzari ya isa ga bohol din yasa hannu ya ture layin dake kai ya aza botikinta Yasa dayan laullausan hannunsa yafara buga bohol din,Jikin Azeema na rawa take binshi da kallo yana zubamata ruwa bai dauke hannunsa ba,sai da ya cika duka botikan guda biyu,da hannu biyu ya daukesu atare,ya nufota cike da mamaki mutane ke binsa da kallo yanayin komai cikin Jarumta da takama,sai da yazo gabda da ita kafin yace"Wuce muje bush girl kawai..."Yafada yana huci jikinta na rawa ta mika hannu tana fadin"ba..Bari na dauka.."Wani dirty look ya watsamata kafin yace"Leave dis place now..."Yafada a tsawace,da hanzari tashiga gaba tana bin su Azeeza da kallo wadanda sukayi chanza kammanin saboda wahala ga Sulaiman Shiko ba mutumci da gayyah sai yace basuyi daidai ba,sunyi yafi ashirin ammh yace biyar ne,mai kyau sauran sai sun sake,Bayanta yake bi dauke da ruwa,Ransa na masa kuna banda An raina masa wayau wai wanna ce matar da"aka Aura masa,kullum gantali alayi kamar wata karya,Saboda cin mutumci harda Debo Ruwa saboda Rainin wayau,Kallonta yake tana tafiya wani takaici ya makarosa ji yake kamar ya shakota ya kifkifamata mari saboda haushi,Suna zuwa kofar gidansu taja ta tsaya tana so ta kalleshi ammh tsoro yahanata,Kanta na kasa tace'Don..Allah ka..kayi hakuri ka..."Bata gama Rufe baki taga ya wuceta ya shige gidan dauke da Ruwan baki ta rike tana bin bayansa da kallo,kafin jikinta asanyaye tabi bayansa.

  Inna Ramatu na zaune bisa kujeran Tsugunno atsakar gida tanata bala"i ita kadai ba Azeemar babu Azeezar ba wanda ya dawo,kawai sai ganin tayi Tsulum Mutum ya shigo gidan bai dire ko"ina ba sai agabanta ya ijiyemata botikan Ruwa ta dago ta kallonsa cike da mamaki,kafin ta mike tana zare,ido lokacin idonta ya sauka kan Azeema data shigo ta rabe gefe tana hawaye,Cikin wani masifa inna Ramatu ke fadin"Kai mallam lafiyanka kuwa zaka shigo gidan matan Aure babu Neman izini.."Tafada tana binsa da harara,domin ta ganeshi yaron nan ne mara kunya,don tanajin Haushin Rashin gaishetan da bayayi.

Ko kallonta baiyi ba,saima juyawa dayayi zai Fice yana kallon Azeema data rabe gefe tana zuban kwallah,kallonta yayi dakyau lokaci daya dayaji Tsausayinta ya tsirgamai saboda koda yaushe cikin kuka take kuma duk ganin da zai mata cikin wahala ne,Ransa ne yayi zafi Shiyasa ya waiga yana fadin"plz Inna kada Akara aikan Azeema zuwa dibo Ruwa infact duk wani aike adaina aikenta,Cuz yanzu ba da bane,tana da hukunci da Nauyin igiya uku akanta,in don wanda zai dinga debo miki Ruwa ne babu mtsala zan neman miki ammh plz and plz kada in kara ganin Azeema awaje matukar ba mkranta zata ba..."Yafada idonsa kyam a na inna Ramatu wacce ta Rike baki saboda mamaki.

  Inna Ramatu hannunta abaki Tana fadin"Eh lalle sannu Lawali..Toh baza"a daina aikenta ba din,amtsayinka nawane zaka zo kana bani Umarni..."dan mirmishi yayi kafin ya tako zuwa gabanta yace"Inna kin taba zuwa bariki don Allah..."Yafada yana sosa sajensa bayan ya kafamata ido,Ganin haka yasa inna ta fara ja da baya tana kifkifta ido,Daure Fuska yayi kafin yace"Toh matukar baki bi Umarni na ba,zan sa azo asace min ke,sai kin kwana kin wuni acikin Firiza mai maida jikin dan Adam kankara,kafin na hadaki da sojoji su huce Haushi akanki..Maza ki amsa min da Toh..."yafada yana Buga hannunsa bisa cinyarsa sai da tayi kara,ai inna Ramatu bakinta na Rawa take fadin"Toh..Toh angama yallabai.."Take fada tana Dafe bakinta jikinta ba inda bai Rawa saboda jin ya ambaci xai saka asaceta tasan tsab zai iya don ba mutumci ne dashi ba..

Ganin yadda take Rawan jiki yasa dariya yakusa subucema Azeema tayi Saurin dafe bakinta,Aliyu ya bita da kallo kafin yadan murmusa yana kallon Inna Ramatu"Ahankali ya Furta "Good..."Yafada yana juyawa bai ko kalli barayin da Azeema take ba ya fice daga gidan cikin Takunsa na Takama da Jarumta,Yana ficewa Inna Ramatu ta hau leka kofar waje tana fadin"Baza abi ba din.."Tafada tana zare ido,dariyan Da Azeema take boyewa sai da ta Fito,kallonta Inna tayi tana fadin"Zan ci ubanki shegiya mai Farar kafa,wlh in yasa aka sace ni daga ke har Lusarin ubanki in nadawo bazaku ji da dadi ba.."Tafada kafin buguzun buguzun takoma daki tana borin kunya,ammh jikinta tsab da tsoron Captain..

Shiko yana fitowa ya nufi wajensu Azeema yaga yadda sukayi saboda wuya,yana zuwa yace su dakata kowacce ta mike,ai fa nan fa daya gabadayansu gwiwa tayi sanyi basa iya mikewa saboda yadda sukaji Jiki,tsawa ya daka musu suka tsaya kan kafafunsu suna rawan jiki,Kallonsu yayi yana dan mirmishi kafin yace"Gud job..Kun gaji gashi kunyi zufa,so kowacce taje ta cika botiki daya kafin in Tuna wani pushiment zaku yi next.."Kallonsa sukayi suna hawaye,Itako Azeeza duk azaban data ke ciki kallonsa take cike da so da kauna,yadda ya tsaya sai taji kamar taje ta Rumgumeshi,har wani lumshe ido takeyi tana lasan baki tsawan daya kara daka musu ne ya fargar da ita,gabadayansu suka je,kowacce taje ta cika botiki daya,na mutanen dake wajen suna gamawa yace kowacce ta dauko akanta tazo nan,haka suka dauko suka zo,suna zuwa yace"Kowacce ta kalli yar"uwanta..,Bayan sun kallah yace"Kowacce ta juye Ruwan jikin nakusa da ita..."Kwalalo ido sukayi suna binsa da kallo,tsawa ya daka musu yana fadin"in na kirga uku bakuyi Abunda nace ba,zan sauya ra"ayi daga wanka Ruwa zuwa na kasa kuma wlh zanyi Abunda nace.."Yafada kai tsaye,ah bai gama Rufe baki sukayi ma kansu wanka da Ruwa,kallonsu yayi yaga kowacce tayi tsamo tsamo kamar wasu zakaru Dariya ta kamasa,ammh sai ya matse da kallo ya bisu kafin yace"Yauwa kun warware gajiya by now kowacce tasaka gwiwanta akasa ammh kuma ta juya ta kalli hanyar gidansu.."yafada yana mirmishin mugunta,Zubewa sukayi kowacce na kuka harda majina,domin ji suke tamkar gangar jikinsu bazai iya Daukansu ba.

Wucewa yayi yafara tafiya kafin yace"Kowacce tafara jan gwiwa har zuwa gidansu,wlh tallahi duk wacce tatashi na ganta ko na kamata,yau sai ta zagaye anguwan nan tana jan gwiwa,toh tun kuna son kanku da Arziki kuyi yadda nace,dis one na small one,duk Randa kuka karama matata Rashin kunya  zanyi Doubling din hukunci danayi muku yau,so be carefull.."Yafada yana wucewa kafin yace"1,2,3...Start..."Da hanzari kowacce ta fara suna jan gwiwa suna kuka wiwa,Inda Allah ya taimakesu duk yan wajajen nan,gidajensu babu nisa sosai,nan kowacce ta nufi gida da jan gwiwa tana kuka harda majina,Shiko Aliyu gida ya shige ko ajikinsa,shiko Sulaimam bai Tafi ba sai da akaci aka sude sai dariya yake Ransa fes anyi maganin marasa kunya.

  Sai ga inna Ramatu da kanta ta fito tana hada Kulin Alalan tanayi tanama Azeema Allah ya isa,sai ga Azeeza ta shigo da jan gwiwa tana kuka Fuskarta ta hade da majina da kuka,ga jikinta ajike da Ruwa da hanxari tayi Wurgi da ludayin hannunta tana fadin"Na shiga Tara ni Ramatu Azeeza gamo kikayi kokuwa karo kikayi keda mai akori kura,yayi miki wannan damejin da jiki..."Tafada tana karisawa gareta tana riko Azeeza,gocewa Azeeza tayi ta zauna dirshan Tana kuka gwiwanta duk sun sale saboda janta datayi akaasa,Kafafunta kuwa ciwo suke matw kuka take tana hadawa da ihu tana fadin"Wayyo inna wlh kafata zafi takemin kuguna,ya rike ban iya mikewa saboda azaba.."Tafada hawaye suna zubomata,Azeema dake lekensu ta window ta kece dadariya tana kama bakin ganin yadda Fuskar Azeeza ta dawo kamar wacce akayi wasan kura da ita,kallonta inna tayi tana fadin"ke wai tsaya Hatsari kikayi ne komiye..?"Azeeza na kuka tace"Wani hatsari inna,ba yaya captain bane saboda naje kiran Azeema tazo in jiki ba,sai ta dauko Ruwa tazo zata wuce shine santsi ya kwasheta tafada kwata,shine shine fa,yazo ya hadamu nida su lantana,yasakamu tsallon gwado bayan mungama yasa mukama junanmu wanka,duk hakan bai ishesa ba,sai da yasamu kowannenmu yaja gwiwansa zuwa gida..",Takarishe tana yaye zanin jikinta gwiwanta ya bayyana Duk ya sabe,baya inna Ramatu taja tana salallami take fadin""Kutmar ubanchan,yanzu Shi yayi muku hakan?gyada kai Azeeza tayi tana fyace majina,Haba Inna ta rike tana fadin"Lalle ya cika mara mutumci ai sai ki tashi ki gasa jikin ki,kiyi hakuri.."da mamaki Azeeza ke kallonta kafin tace"Inyi hakuri fa kikace inna,nazata zaki Ramamin kan Adda Azeema tunda akanta ne yayi mana haka.."baya inna taja tana fadin"Wa ni? Rufamin Asiri nima bai dade da fita daga gidan nan ba,yamin kashedi sosai kan Azeema yace duk Randa na saba umarninsa,sai ya saka ansace,na kwana afiriza mai maida jikin mutum kankara,kafin ya hadani da sojoji suyi wasan kura akaina,.."Tafada tana waigen kofa,zaro ido Azeeza tayi tana fadin"da gaske inna..."Gyada mata kai tayi tana fadin"Wlh kinga kuwa ko saceni yayi babanki bazai damu baTunda yafi son Wanchan sakaryan Akanmu.."Shuru Azeeza tayi batama inna mgana ba,Tunaninta yatafi kan Tunano Fuskar Abun kaunarta,Inna da hanzari taje ta hura wuta ta saka Ruwan zafi kafin tazo ta ciccibi Azeemar zuwa kofar dakinta inda ta Shimfida mata tabarma,Azeezar sai wash wash take saboda azaba ammh kuma ko Ranta batajin Haushin Captain ba,saima tsanar Azeema daya kara cika zuciyarta ta kudiri niyar ko ta halin kaka sai ta mallaki muradin Ranta.

Inna Ramatu ita tagasa Ma Azeza jiki tana gasata tana kukan zafi bayan tagama ta shafe mata jiki da Man zafi,hakama Sauran kawayenta,kowa yaji Captain ne,ko ya taso da zafi sai yakoma don ba"a ma Soja wargi,Ballema kowa yasan waye captain kaf,anguwan nan Ansan baya da wasa yaci kaniyarka bawani abu bane awajenka,Azeema ko cikin dakinsu tana kashin dariya domin Ranar tayau ta mata dadi,kota tafito Diban Ruwa tayi wanka daga Azeezar har Inna ba wanda ya Tankata haka ta shige bayi tana dariya,wani Farinciki na Fizganta bata san dalili ba,ammh ko Fuskar captain Tatuna sai taji wani Sanyi ya Shiga Ranta,ita kadai ta Furta. *YAYA CAPTAIN NAGODE*


_______________

Ranar da Aliyu ya taho Gombe Aranar Ni"ima ta dira akaduna,Taji matukar takaichi da Bakinciki lokacin da captain jabir ke fadamata Cewa Aliyu ya taho gida,kuma bayajin zai dawo cikin satin nan,sai sati na sama,Kuka wurjajan Ni"ima takema Jabir kan yabata nombar wayar da zata samu Aliyu,dariya jabir yayi mata yana fadin"Bayajin cewa Aliyu ya chanza layi buh Abu daya yasani cewa ya kulleki ne,da zata tafi yace"Shawara mai kyau karta kuskura taje gombe wajen Aliyu in ma zata dawo ne tabari ya dawo kaduna yayimata alqawarin fadamata,taji dadi sosai Kafin tatafi sai da sukayi exchanging din Phone number,Direbanta ne yakawota Domin karya tayima mami wai zata raka Muneera biki sai yammah zata dawo Shiyasa har ta dawo gida mami batasan ina taje ba.


   *************

  Bayan kwanaki da Faruwan Abun,Azeema tasamu sauki sosai ta bangaren inna da Azeezar ita kanta bamai Shiga harkanta,ko aiki bamai sakata,Ammh dayake Azeemar ta riga ta saba shiyasa bata iya zama,duk Abunda tasan aikinta ne tun safe zata tashi tayi Mganar aikenta kuwa ba"a kara yi ba tun Ranar da Captain yayi mgana in ka ganta waje toh Mkranta zata ko Allo,itako da Azeeza ko mgana bata mata,in tayimata ma bata karba mata shiyasa tafita harkanta,Dayake bata zuwa mkranta tana jinyan kanta saboda kugu ya rike😂,Shikanshi mallam lawal yayi mamakin ganin chanji agidan,bai dai yi mgana bane,sai yaji dadi Aransa yana fatan ya sa Ramatun ta gyara halinta ne,itako Inna Ramatu mganar saceta a kaita barikin shine ke dagamata hankali,shiyasa ko taso yin wani Abu takejin Jikinta yayi sanyi,toh tafaa sani tsab Aliyu zai iya don ba mutumci ne da shi ba.

Goggo batasan wainar da"ake toyaba ,don yanzu bata cika ganin Azeemar ba,saboda dawowar captain sai dai da safe in zata mkranta kan yatashi take shigowa su gaisa da goggon ta wuce agurguje,Shiko Captain haryanzu goggo batamai mganar data kirasa akai ba,Shikuma bai mata mgana ba,yana jiran yaji mezatacemai,Shima yana Tunanin Dauke  Azeemar  daga wanchan Rayuwa zuwa wata rayuwar mai inganci.


**************

Yanasanya mota kenan Cikin garejin yana Sauri yasamu jam"in sallar isha"i yaji maganganu daga kofar gida,koda ya fito dayake akwai wuta,kuma haske ya wadata kofar gidan,Kallonsu yayi suna tsaye Azeeza takalli Azeema tace"Gaskiya Adda Azeema kidaina sakamin ido,ina Ruwanki dani,wato ke kinyi Aure,kina bakin ciki ni kar na tsaya na nemi nawa mijin,da anyi mgana sai kice,Baba yahana,don Allah kibarni naji dadin rayuwata.."tafada tana saka hannu ta ture Azeema dake tsaye sai da ta fadi,tsautsayi yasata tafadi ta gefen hannunta sai da yayi kara,dan Ihu Azeema tayi tana dafe hannun saboda azaba,Hawaye na shatata bisa kuncinta

  Kallonsu yake cike da mamaki,kamar ya basar ya wuce,sai kuma ya tsaya yana kallon Azeezar harta kariso kusa dashi bata lura dashi ba,sai da taji ya dakamata tsawa yana fadim'"U Stupit,Come here.."Yana fada yana gyara tsayuwarsa,ba Azeeza da"aka dakama tsawa ba,hatta Azeema dake gefe saida ta razana,jikin Azeeza na rawa ta kariso tana kallonsa kafin tace"Gani.. YAYA CAPTAIN.."Ko kallonta baiyi ba,sai ya juya kan Azeema yana fadi cikin tsawa.."Au ke bazaki zo ba,jira kike na kiraki ko?i swear in kika bari nazo na sameki sai kin zagaye anguwanan kina tsallen kwado,wawiya kawai.."Yafada yana hararanta,ai Tun kafin ya rufe baki,ta kariso gabanshi jikinta na kyarma,hawaye na zubomata,Azeeza kuwa kuramai ido tayi tanajin wani dadi kamar ta rumgumeshi,hartana wani lumshe ido saboda yadda Shaukin ke Fuzgarta

Kallon Azeema yayi kafin yace"In kika bari hawayen ki ya zuba akasa,wlh sai kin duka kin lasheshi tas.."yafada ba alamar wasa atare dashi,Azeema da hanzari,ta hadiye kukan nata,tana share hawayenta,tsawa ya dakamusu yana fadin"Daga ina kuke Don ubanku yanzu dadddaren nan?.."Azeema bakinta na rawa tace",Da..daga Mkrantar Allo.."Sauke idonsa yayi kan Azeeza wacce tayi zurfin cikin Tunani,kuramata ido yayi yana ayyana girman Rashin kunyar yarinya,kara tamke fuska yayi kafin yace yana kallon Azeema"Waye ya girmi wani acikinku..? Da rinannun idanunta ta dago ta kalli Azeeza,wacce take wani mirmishi,Daka musu tsawa yayi yana fadin"Wai bada ku nake,mgana ba,ok so kuke yanzu jikinku yagayamuku inaga."Yafada yana kokarim zare belt,da hanzari Azeema tace"Nice,na girmeta..."Wani banzan kallo yayi mata kan yace"oh kece babba ammh kina zaune,yar kanwarki na miki Raini,harda tureki,kekuma dayake sakaryace mara wayau,har kina mata kuka ko"?yafada yana sakarmata ido
 

Jikinta na rawa kuka na neman kwacemata tafara ja baya,"Tsaki yaja yana fadin"bantaba ganin sokuwar yarinya irinki ba.."yafada yana maida hankalinsa kan Azeeza,Yaga yadda ta saki baki da hanci tana kallonshi nan da nan ranshi ya baci bai yi wata wata ya saka hannu ya shareta da mari lokaci daya ya sanya kafa yayi ball da ita,Azeeza dataji saukan mari abazata dakuma yadda ya hambareta tayi gefe tana fashewa da kuka"Nunata yayi da yatsa yana fadin"Shhiii..In kikayi Min kuka wlh Sai nayi miki bulala dari,don kaniyarki sa'arkice dazaki dinga dagamata murya,harkina dukanta, wato Abunda yafaru Ranar bai Tsorata ki ba ko?wlh na kara ganin kin mata rashin kunya,sai na saki cikin kankara kin kwana biyu,Try me an See.,Bacemin daga gani,tunkafin nafara kwallo,dake bush girl mai kama da monkey.."Da gudu Azeeza tamike ta shige gida tana kurukuruwan  ihu,kallonsa ya dawo kan Azeema dake gefe tana sharan hawaye,Wani kulilin takaichi ya tokareshi,yanzu wai wannan wawiyar itace matarshi,gaskiya goggo bata kyautamai ba

  Wucewa yayi yana fadin"Kema bita,kafin na chanza mind dina,inyi kasa kasa dake,kuma Nakara ganin kina mata kuka,sai na prison ya fiki jindadi,ko mganar banza ta fadamiki slap her,beat her,yadda zata kiyaye ki,kinji ko bakiji ba..

Da wani Rawan jiki dana baki tace"Na..naji...'" Better.."yace yana wucewa massllacin cikin sassarfa,da hanzari Azeema tafada gidan Goggo don tasan tana Shiga gidansu to tabbas sai Inna Ramatu Tarama ma Azeeza dukan da yaya Captain yayi mata,duk da yanzu tana shakkar yimata wani Abun saboda shi.



*Am Srry For d late update Na mantane ban hidi muku ba,Zaku dinga samu update din Ali gadanga duk bayan kwana daya ne,cuz am busy wlh Abubuwa sunman yawa Akwana dayan ma,karfin hali nakeyi..Masu comment da sharhi duk nagani kuma ngd sosai Am srry bansamu maida Reply ba,saboda wasu abubuwa dasuka shamin kai buh duk nagani kuma ina godiya Allah ya bar Zumunci Amin..*



    
      *#Comment share,and vote...#*
      *#Intelligent writer's asso...#*
      *#Janafty....#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


*NOT EDITED*💥

        *Chapter 11*

  """Goggo na cikin kichen taji Sallaman Azeema,da hanzari ta fito tana fadin"Ah Azeema,kice kamar daga sama da daddaren nan? Tafada tana kallonta,Sunkuyar dakai Azeema tayi tana kokarin dukawa ta gaida goggon saurin Rikota tayi tana fadin"A"a tashi kada muyi haka dake,bama wannan ba,miye naga kina wani zare ido,gabadaya kamar atsorace kike,gayamin badai wani lalatattace bane ya biyoki yanzu na fita naci ubanshi,kokuma na hadashi da gadanga wlh yaci uwarshi yanzu nan fadamin waye ya biyoki naga kin Shigo a Tsorace"Dan waro ido Azeema tayi kafin tace"Ba kowa bane fa inna Dama yaya captain ya daki Azeeza saboda tamin Rashin kunya,shine na shigo nan kada na koma gida inna ta huce akaina.."Galala Goggo ta kalleta kan tace"Ai yamin daidai wlh,kema dai Azeema wlh ki kamma jikinki,in dai kina wannan sokanci wlh bazaku Shirya da gadanga ba,shi mutum ne dabayason wargi balle shashanci yo in ma kinaso sace zuciyarsa ne,na baki satan amsa ki zama mace Tukunnah bayan kinkam jikin ki Atoh.."Tafada tana Riko hannunta,Baki Azeema takama tana yar dariya,Mangare mata kai goggo tayi tana fadin"Au dariya na baki ko?yo ai gaskiya ne,ammh wani lokacin in kina wani Abun sai ki dinga Tunamin da Mahaifiyarki Fatima,wlh Azeema yadda kike da hakuri da kawaichi to Fatima ta fiki.."Tafada cikin sanyi,nan da nan idon Azeema ya ciko da hawaye,dafa kanta goggo tayi tana fadin"Karki damu Azeema wlh Tamkar Aliyu haka nake kallonki da izinin lahi sai kin zama Abun alfahari,da kin Tuna da mahaifiyarki karkiyimata kuka kiyi mata addu"a da Fatan tana kyakyawan mtsayi kinji ko? dakai Azeema ta amsa tana share,kwallah hijabin jikinta goggo ta ciremata bayan ta amshi al"qur'anin tana fadin"Maza shiga shiga ciki ki dauro alwala kizo muyi sallah sai muci abinci yanzu na gamashi da zafinsa,ai ni nagodema ja"irin nan gadanga daya bugemin Mara kunyar yarinyarnan gashi sanadin haka yata tazo wajena,duk da yanzu wasan buya ake dani Tunda Megida yadawo.."Tafada tana kyabe baki,Tura baki Azeema tayi tana fadin"kai goggo ba ina zuwa ba,kuma ni yaushe nace haka.."Goggo tayi yar dariya tana fadin"Au hakane fa,to naji baki ce ba,maza shiga kiyo ki fito an kusa sallame salla daga masallaci.."Tafada tana Ficewa daga Falon,itako Azeema dan mirmishi tayi kafin tafada bedroom din na inna wanda in ka gansa ko na wata amarya albarka saboda yadda yasha wani ubansu royal bed mai kyau da tsari gashi yana malale da capet mai kyau da tsari,da makeken wardrope dinta sai madubinta dake shake da kayan shafa na mata,wanda goggo banda kwalli bata shafa komai,ammh kullum taramata Ali gadanga yake,Tunda kawu ya daukemata Nauyin komai.

Tare sukayi jam"i da goggo suna gamawa goggo ta zubomusu abinci Shinkafa da miya sai slat datayi musu goggo fa,ba baya ba,akwai iya girki sosai kamar ka tsinke hannu,nan suka zauna Dole tasa Azeema sakin jiki don goggo dai kun santa dole ma mutum ya saki jiki da ita,da farko Azeemar kin ci tayi,aiko goggo tayimata barazana da zata kira Aliyu yanzu yazo yayimata dure,kila taci jin haka yasa taba goggo hakuri ta hau cin abinci dama yunwa takeji sosai domin tun karin safe rabonta da Abinci,Ammh tanayi tana waige da sauraran waje kada Yaya captain yazo ya Ritsata.

  Itako Azeeza tana shiga gida da ihu Ta iske mallam lawal atsakar gida shida Inna Ramatu,jin ta shigo da ihu yasa Inna mikewa tana fadin"Ke lafiyanki kuwa keda wane.."gabansu Azeeza ta zube tana fadin"Inna wlh In baki dauki mataki kan Adda Azeema ba,ni zan dauka dakaina.."Tafada tana hawaye,wanda bana zafin marin da yaya captain yayimata bane,a"a takaichi yadda taga kamar yana tsausayin Azeemar ne,wanda ita ba burinta kenan ba,burinta kafin yafara son Azeemar ita ta riga ta mallake zuciyarsa Allah barshi ya dankarama Azeemar sakinta ta kara gaba.

Inna tace"Toh me tayi miki ne,nifa bangane ba? Kyabe Fuska Azeeza tayi tana fadin"Ba ba kawai mundawo daga Mkranta bane zamu bi ta kofar gidansu yaya captain Tunda Adda Azeema ta ganshi shikenan ta nufi wajensa,bansan metacemai ba,naga dai Tana ta nunoni,ban ankara ba yazo kusa dani kawai ya mareni,kuma ya saka kafa yayi Shuru dani.."Tafada tana kara barkewa da kuka kamar gaske
  

  Kutmar ubanchan.."Inna tafada Tana rike kugu kafin ta waiga tana fadin"Ammh dai kaji Abunda tsinanniyar yarka tayi ko? ammh naga kayi Shuru bakace komai ba"Ko kallonta baiyi ba yace"Nidai ban Tsinema yata ba,sai dai in ke kika Tsinema taki,mganar kuma da makaryaciyar yarki ta fada ba gaskiya bane,na tabbata Azeema bazata kulla miki sharri har Aliyu ya

Please Login or Register in order to submit comment