Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakeki ba,sai dai in rashin kunya kikamai ya hukuntaki.."Yana gama fadar haka ya mike yana kakkabe rigarsa yake dakama Azeexa tsawa yana fadin"Tashi kiba mutane waje,matukar baki zama mutum ba,har abada ni dake bazamu Shirya ba.."Yafada yana Shigewa daki.

Da kallo inna ta bishi kan takoma ta zauna tana fadin"Eh na yarda tabbas Watarana Azeema zata kashemun aure,toh kan ta kashemun ni zan mata dukan mutuwa dasai ta gwammace kida da karatu,wlh tallahi sai dai duk Abunda zai Faru ya faru..",Tafada tana huci,ganin haka yaasa Azeeza tashiga zigata na taci uban Azeemar in tadawo itako inna huci kawai take kamar wata macen zakanya.

Shiko gadanga yana idar sallah yadawo gidan,yana shigowa yaji muryan goggo tana hira cikin hiran natane yaji ta ambaci Azeema jin haka yasa yayi burki zuwa dakinsa cuz bayasan ya mtsama yarinya Tunda ya lura tsoransa takeyi,bai cika cin abinci mai nauyi ba da daddare,shiyasa goggo bata damu da nemansa ba,balle ta kaimai Abinci,har wajen goma Azeema na gidan sai lokacin tace zata koma gida goggo tayi tayi ta tsaya ta kwana ammh taki dole ta kyaleta ammh aranta tana addu"ar Allah ya hadata da gadanga ya warfatota tadawo akwai illai tana Fitowa tsakar gida cikin sanda Ya hangota dama yaji karan bude kofa,Fitowa yayi yana kallonta tana tafiya ahankali Gyara tsayuwa yayi sai da takusa isa ga kofar gidan daya kulle Tun dazu kan yace"Ke...",yafada cikin sanyi,Cak ta tsaya jikinta na rawa jin muryansa kafin ta waigo Arazane kallonta yayi kafin yace"Ina zaki.."?Bakinta na rawa tace,"Gi...gida...Za..zani.."harara ya zabgamata kafin yace"dallah wuce kibama mutane wajen gidan wa zaki Da daddrenan.."Yafada yana kokarin komawa daki,kin tafiya tayi ganin haka yasa ya dakamata tsaawa yana fadin"Au zaki wuce ko sai nazo na tattaka ki anan wajen ne.."Jin haka yaasa tayi dakin goggo da gudu tana rawan jiki,gyada kai kawai yayi ya rufe kofa ya koma ciki,tana shigowa daki taga goggo na mata dariya tana fadin"Allah yamaka albarka gadanga..."Take fada tana ma Azeema dariya,Azeema tayi nakwa nakwa da Fuskar kamar zatayi kuka da sauri goggo ta rikota tana fadin"Yi hakuri kema Allah miki albarka Azeemata muje mu kwanta kinji.."Tajata zuwa kan makeken gadon nata ta kwantar da ita,tana shafa kanta tace"Toh kwanta kiji gobe da safen zan rakaki har gidan kinji ko? gyada mata kai Azeema tayi tana dan mirmishi Aranta tanajin son goggo na ratsata saboda yadda take kula da ita.

  Shiko mallam lawal koda dare ya tsala Azeema bata dawo ba,haka inna ramatu tazo kansa tanata jaraba wai Azeema bata dawo ba,tatafi gantali kuma wai nan matar aurece,hartana cewa bataga amfanin wannan Auren ba,shisshigi ba kwarjini,sai Tusa kai suke ana gwasalesu,shidai yana jinta kanzil baicemata ba,saboda yana da tabbacin Azeema na gidan goggo kuma yasan darene yayi Suwaibar tahanata dawowa,juyamata baya yayi dole datagaji ta hakura tayi Shuru Tunda bai Tankata ba.

     **************

Da Asuba bayan Aliyu yadawo daga sallar Asuba ya shiga wajen goggo yana fadamata yasamu kiran gaggawa daga bariki General ne ke nemansa da kansa,sabods haka zai zo yakoma ammh yafadamata bazai dadeba wannan karan zai dawo,fatan alheri tayimai kafin Surabu agurguje yagama Shirin saboda sauri ko karyawa baiyi ba,ya dauki hanyar kaduna,har yatafi Azeema bata sani ba,don bayan ta idar da sallar asuba takoma ta kwanta Shikenan sai barci ya kwasheta bata farkaba sai wajen Takwas saura,nan ta farka tana salati ta mike ta fito falo nan ta tarar da goggo na sharan capet din dake falon,saurin karisawa tayi ta karba tana Fadin"Haba goggo gani cikin gida saiki hau shara da kanki.."Sakarmata tsintsiyan tayi tana fadin"Na kyaleki kiyi barcinki ne,nima Fitan gadanga ne yasa nafara sharan.."Da kallo Azeema tabi goggo dashi sai ta samu kanta ta tambayan "Ina yaje Goggo..? Goggo tace"Eh ya koma kaduna wai yaasamu kiran gaggawa,yanzu bai dade da tafiya ba.."Shuru Azeema tayi taciga ba da sharanta bayan ta gama tayi mooping din dakunan duka,tana gamawa goggo tasa ta shiga wanka bayan Ta fito suka karya,lokacin har goma ta wuce,tarasa mkranta yau sai dai gobe in Allah yakaimu,Bayan sungama komai Goggo tasa hijabi ta rufo gidan suka nufi gidansu Azeema.

  Inna na madafi taji sallamar goggo Fitowa tayi tana binsu da wani kallo daga ita har azeemar"Karkace kai goggo tayi tana fadin"Mun tashi lafiya Ramatu.."Dakyar Inna ta amsa da cewa!Lafiya..'daga haka tajuya takoma ciki goggo bata damu ba tace"Ga Azeema jiya wajena ta kwana dare yayi na hanata dawowa,ina mallam din yana ciKi.."? Mallam lawal daya fito daga bayi yace"Ina nan Suwaiba ina makewayi ne,naji shigowarki sannu da zuwa.."Goggo ta amsa "Da yauwa mallam,dama Azeema na rako jiya tayi dare sai ta kwana wajena.."Dan dariya Mallam yayi kafin yace"Toh inbanda Abinki suwaiba ai Azeema takuce gabadaya koma komawata tayi wajenki gabadaya ai babu matsala.."Gyada kai goggo tayi kafin tace"Hakane..."Azeema ce ta duka tana gaida Mallam lawal ya karba yana tambayanta yatakwana,ta amsa da lafiya kalau,tashi tayi ta shiga dakinsu nan ta iske Azeeza tatafi mkranta tayi mamaki sosai saboda sam Azeeza bata son mkranta,goggo ko daganan tayima mallam lawal sallama takoma gida,inna ko ko tak batace ba,kamar mai ciwon baki har mallam lawal ya Shirya ya fice batacema Azeema komai ba,kawai tana kallonta ne tana Tunanin yadda zata chanzamata kammani cikin hanya mafi sauki,sai kawai ta yanke shawaran tayi bakan sai ankwana biyu sai ta dauki matakin da zata dauka.




________________

  *Masauratar Garin  Agadez*

  ""Wai babana meke damunka ne,kaki bari Asaka malamai cikin wannan laluran taka,suzo kayi musu bayanin yadda kake gani amafarki kila in andace su gane me hakan ke nufi ammh sam kaki kuma GIMBIYA RAZEENAH Tafadamin baka bar mafarkan ba yanzu ma kamar yafi nada.."Takarishe cikin nuna Abun ya dameta.

Jin Abunda Ummah mai babban daki tafadane da sunan data ambata yasa dagowa yana zabgama gimbiya Razeenah harara,itako ta kauda kai ko ajikinta,yana zaune kusa da kafafunta itakuma tana zaune kan wata kujera mai kyau da tsari irin na gidan Saurata su duka biyun suna sanyene da alkaybbu masu kyau da tsari,Kasan kuma wani capet ne daya malale dakin kowani lungu kuma dauke da Tuntu irin na gidan Sarauta,agabansu kuma shake da wani kayatattacen Faranti dauke da kayan Ruwa ma"ana Fruit.

  Kallonta yayi yana Fadin"Kibamu waje zanyi mgana wa Ummata.."Yafada kai tsaye mikewa tayi kafin tace",Afito lafiya Ranka ya dade..",Ta fada tana gyara zaman alkyabban jikinta kafin ta fice,yana binta da harara lokaci daya ya dawo da kallonsa kan Ummah kafin yace"Don Allah Ummah kedaina daukan mganganun yaran chan akaina,ni basan ciwon kaina bane? kokuwa Sinfini sanin mezanyi ne,kuma mganar mafarki ko na malamai don Allah Ummah kibar mganar nan,bafa Abunda yagagari Allah koma miye insha Allahu inaji ajikina yakusa bayyana.."Yafada yana jinjinamata kai,Rausayar dakai tayi xatayi mgana yayi Saurin cewa"Don Allah kibar mganar nan Ummah,kuma kidaina basu Fuska in suka kawo miki ita,duk wacce acikinsu nake takuramawa in tana barci to ki fadamusu kada wacce takara bina Sashena don ba gayyatarsu nayi ba,bankuma ce Dole azo ba Atoh.."Yafada da alamar ya fara hasala

Jinjina kai Ummah mai babban Daki tayi kafin tace"To ai Shikenan duk basai takai ga haka ba,Allah ya bayyanamana koma miye.."Da Amin ya amsa kafin ya mike yana fadin"Zani Fada Ummah yau sarkin garin Dossso zai kawomin ziyara zamu tattauna wata mgana ne nidashi.."gyada kai Ummah tayi kafin tace"Toh Allah ya taimake ka Allah tsone idon makiya akanka babana.."Da Amin yayi ta karbawa Kafin ya fice daga makeken falo,yana Fitowa dogarai na kofar Shigowa suka yimasa rumfa suna masa barka da Fitowa,basu barshi kowa ya gansa ba, suka Rufesa da riganansu har ya shige fada ya zauna,kafin afara gabatar da Abubuwan mulki kamar yadda aka saba akowacce safiya.



    ....................................

_Gombe_

  Bayan Sati  daya da Faruwan Abunda ya faru,Yau din takama Asabar ne,Tun safe Azeema tatashi da wanki danata dana babanta sai na inna Ramatu,wannan karon kam bata dauko na Azeeza ba,domin har aranta ta gane Raini ne kawai ke karuwa matukar tana cigaba da bautama Azeeza,Sai da tagama wankin Tas tana shanya Azeeza da tashinta kenan daga barci ta fito tana mutsika ido ko sallah batayi ba,taga Azeema tacika igiyoyi da shanya ammh kaf babu kayanta daki takoma taduba ma"adanar kayanta taga ko kala daya Azeemar bata dauka ba,Afusace ta fito daga dakin tana fadin"Wai ke Adda Azeema kwanan nan mekike Nufi dani ne.."?tafada bayan ta tsayamata agaba kerere,kuma duka hannuwanta takama kugu dasu,ko kallonta Azeema batayi ba,saima tacigaba da shanyarta,Ganin haka yasa Azeeza ta fusata Tanufi kayan da Azeemar ke shanyawa duk ta rikito dasu kasa kuma tasa kafa tataka tana fadin"Kinajina ina miki mgana kina min banza,yanzu ai ina fatan kin jini ko,sai na kara fatali da sauran ne.."Tafda tana wani mata banzan kallo,Azeema dake bin kafan Azeeza da kallo daga sama har kasa taga yadda tayimata da kaya,Ranta in yayi Dubu ya baci ashe haka Azeeza ta rainata bata sani ba,bata gama mamaki ba Azeeza ta sanya kafa tayi Fatali da sauran kayan dake botiki daya rage bata shanya ba,Tana fadin"An kara zubarwa sai ki..."Ji kake Tas!Tas!Azeema tadake tsaye ta zabgama Azeema marika masu lafiya dama da Hauni,wanda saida Azeezan Ta wuntsila bakinta ya fashe da hanci Dago kanta tayi bakinta bude tana kallon yadda Azeema ke huci saboda bacin rai cikin kakkusan murya tace"Ni sa"arki ce Azeeza,ashekarun haihuwa nawa na baki? kodon kinga ina kyaleki bana tanka miki to ba tsoro bane wlh gudun mgana ne,ammh Tunda nagane baki da mutumci ballatana kunya yanzu mukafara dani dake acikin gidan nan.."Tafada kafin taDuka tana kwashe kayanta Ranta bace kamar tayi kwallah.

Mallam lawal dake kofar daki Tun dazu yace"Kinyi min Daidai diyar albaarka,Hukuncin yayimata kadan dakin hadamata harda dukane kila tashiga hankalinta mara Tunani kawai.."Yafada Ransa na kuna,inna Ramatu dake bayi tana Allah Allah ta fito itako Azeeza jin zafin mari yasa ta shiga kurma ihu kamar wacce ake yankawa,Ai da gudun bala"i inna Ta fito daga bayi tana tambayan lafiya,daga Azeema har mallam lawal ko kallonta ba wanda yayi sai ta isa ga Azeeza tana fadin"Ke dallah bar kuka gayamin me sukayi miki don naasan daga Uban har yar bamai kaunarki acikinsu.."Wage baki Azeeza tayi tana fadin"Inna Adda Azeema ce ta kifkifamin mari,wai don nazo ina mata mgana kan naga bata hada da kayana ta wanke ba,shine baba yace wai tayi daidai ta takaramin da duka.."Dafe kirji inna Ramatu tayi Tana fadin'Kutumar ubanchan lalle tayi kuskure,ko ni dana haifeki bantaba saka hannu na mareki ba,balle ita,in ita bata hada miki da duka ba,ni yanzu zan hadamata shegiyar yarinya dama ina da cikinta yau zan Famsheshi.."Tafada tana Nufar Azeema wacce ke tsaye tana kallon innar,mallam Lawal yana fadim"A"a Ramatu karma ki fara,kada ki soma,Allah kika tabata zan bata miki Rai.."ina ko jinshi batayi tana zuwa ta kifama Azeema mari tana fadin"Don ubanki jakarkice ita,da zaki mareta zaki ci uwarki yanzu nan don wlh sai nayi miki dukan mutuwa gaba ko sunan Azeeza kika ji kya kiyayeta.."Bata tsaya Sauraran Azeema dake fadin"Inna ki tsaya kiji metamin wlh Azeeza ce bata da gaskiya kada ki dakeni.."Take fada kuka na tahomata,ammh inna bata saurareta ba,ta jawo wani tsohon igiyan Gugansu ta shiga laftama Azeema wacce ta durkushe tana kuka,Mallam lawal yayi Saurin isa kusa da Ramatu yana kokarin amsan igiyan ammh taki bashi da gayyah ma,take zabgamai azuwan bata sani bane,Azeeza na gefe ta share hawayenta ta mike tsaye hannuwanta sarke bisa kirjinta tana kallo tana mirmishin jin dadi.

Goggo dake tsakar gida tana Taran Ruwa afamfo daidai gatangar gidansu Azeema takejin kuka da maganganu harda Muryan mallam lawal yana fadin"Kibari nace Ramatu,kibari ko.."Yake fada,da hanzari goggo ta ture botikin hannunta ta shige daki da Sauri ta dauko hijabinta da wayarta ko Rufe gidan batayi ba,ta fito da Sauri ta fada gidansu Azeema daidai lokacin da Inna Ramatu tawani bangaje mallam lawal yayi taga zai fadi Allah ya taimakeshi ya dafe duka hannuwansa akaasa,Itako inna harda hannu take hadama Azeema,Goggo data Shigo ta ruga da gudu tana fadin"innalillahi..Ramatu mezan gani haka?me Azeemar tayi miki kike mata wannan dukan.."?Tafada tana Ture Ramatun Ta Rumgume Azeema wacce Fuskarta tayi jajir,jikinta duk ya fashe saboda duka,baya inna Ramatu taja tana Huci da sauke gajiya tace"Malama babu Ruwanki,kifice ki bani waje,wlh in ban bar Azeema kwance ba bancika Sunana Ramatu ba.."Goggo ta dago kanta idonta yayi ja tace"Aikuwa bazaki cika sunanki Ramatu ba..."Tafada cikin Fushi kafin ta Fito da wayarta ta shiga latsawa A speaker Ta bude wayar saboda tana son Suji ansam kuwarshi.

Captain Aliyu yana bakin aiki lokacin da kiran goggo ya shigomai wasu bataliyane agabansa yana koya musu Training da dubarin yaki,kiran nata ya katseshi lokacin yana sanye ne da kakinsa,Ya fito a Captain dinsa sak,dakatawa yayu yakoma da baya ya Dauki kiran yana fadin"Goggo.."Muryan ta narawa tace"Gadanga ga matarka Azeema nan Ramatu takamata da duka,na mata mgana tabari tace bazata bari ba,Tace indai batama Azeema dukan mutuwa ba bata cika sunanta Ramatu,inason ka nuna mata ikonka,kanuna mata bata isa ba,indai ni Suwaiba ni na haifeka.."Tafada cikin daga murya.

Aliyu da Tunda goggo ta fara mgana jijiyoyin kansa suka mike Tuni idanunsa suka chanza launi,dunkule hannunsa yayi yanajin yadda muryan Goggo ke rawa batare da wani Tunani ba yace"Don Allah goggo ki bani dama..", goggo ta karba da cewa"Na baka dama gadanga..Nabaka kowacce dama Tunda dai batasan mutumci ba.."Cije lebe yayi kafin yace'Ngd goggo..Yanzu Ki dauki Azeema ki Tafi da ita in Baba na nan ki fadamai *AZEEMA TA TARE ADAKIN MIJINTA..* yafada cikin tattausawa,Dariya goggo tayi kafin tace"Angama gadanga Allah yayi maka albarka..."Daga haka suka yanke kiran,Goggo ta dago tana kallon inna Ramatu da jikinta ke rawa sai yanzu ta Tuna da kashedin Captain.

Kallonta goggo tayi kafin tace"Kinga ikon namu ko,Uhmm wannan somin Tabi ne,kijira hukunci gadanga.."Daga haka Ta riko Azeeza,mallam lawal daya mike yana haki yace"Jeki da ita Suwaiba..Azeematu Allah ya albarkacin Aurenki Duniya da lahira..',yafada wasu hawaye na ziraromai saboda takaichi,Azeema na kallon babanta na kuka,sai itama takara fashewa da kuka,ammh cikin Ranta tana amsawa Da Amin,inna Ramatu baki ta rike tana fadin"ikon Allah sai kallo,Abun rabo ne budurwa da jika,wannan wani irin Aure ne,..."Tafada tana bin bayansu goggo da kallo har suka fice daga gidan.

  Azeeza dake gefe tazama mutum mutum har su goggo suka fice,kenan yanzu Azeema zata tare adakin captain a mtsayin mata,duk tana zaune batayi wani Abu ba,ina?bazai taba yuyu ba,wlh Captain nata ne ita kadai indai bata sameshi ba,sai dai kowa ya raasa,zata iya yin kisa akansa koda kisan takama na yar"uwantane Azeema,Idonta gabadaya ya soye hawaye sun kafe saboda bakinciki,juyawa kawai tayi takoma daki ko inna dake kiranta banza ta mata don alokacin ma innar haushi take bata kamar ta makureta ta mutu kowa ya huta,in da bata daki Azeema ba babu yarda za"ayi goggo tazo har takira yaya captain yace Azeema tatare adakinta ba,Duk inna taja,Ran Azeeza tafasa kawai yake saboda kishi da hassada,Shedan sai huramata wuta yake azuciya Tare da kara tusamata tsanar Azeema Aranta,kanta ta buga agaru tana fadin" *BAZAN KYALEKI BA...WLH TALLAHI SAI NA AMSHI ABUNDA YAKE MALLAKI NA NE,KODA ZA"A ZUBDA JINI NE...*"Tafada jini na biyi goshinta kafin tafada bisa gado tana fashewa da kuka.



*Tabdijam...Hmmm...Salon yanzu ya fara zuciyar Azeeza fa ta bushe babu imani ko kadan,ga Azeema zata tare agidan mijinta ga Goggo tabama Gadanga damar daukan kowani mataki..Akwai wasa sosai agaba juz keep following zan warwaremuku zare da abawa*


       *Comment,share,and vote..*
        *Janafty...*
        *Intelligent writers asso....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*Srry 4d late update...Bohot bohot love Habibaties...*

*Chapter 12*

_Kaduna_


"""Yau din Takama weeked ne,Lahadin karshen mako ne,kowani soja dake barikin manya da kanana suna gidajensu domin Hutawa hakane ta faru da Captain Aliyu,Shima din Tunda ya dawo sallar asuba yakoma bai iya tashi ba saboda gajiya da barci.


Cikin barci yakejin kiran waya da karan Door bell atare,Wayar nasa tana kan Side Drower din gadon nasa ne,hannu kawai ya mika ya dauko wayar da niyyar kasheta sunan Jabir daya gani ne,yasashi ya daga kiran yana fadin",Hey Dude wht wrong kakemin irin wannan kiran..? ya fada Muryansa da alamun barci daga chan bangaren Jabir ya amsa da fadin"Dallah mallah ka watsake daga wannan barcin Gani akofar Apartment dinka.."Aliyu najin haka ya datse kiran yana tsaki yasan halin Jabir kamar maye da takura,mirginawa yayi gefe ya cigaba da barcinsa ammh sai me karan Door bell din fa bai tsaya ba,har filo yasa ya Toshe kansa ammh duk abanza,Mikewa yayi ya duro daga kan gadon,sanye yake da wani 3quater din wando babu ko Riga ajikinsa ya fito daga bedroom din yana bata rai isa yayi isa ga kofar ya bude jabir dake Tsaye hannu harde akirji Ya bayyana Kare kofar Aliyu yayi yana rollin din idonsa kafin yace"Ya? lafiya mallam kazo kahanani barci sai famam bugamin kofa kake sai kace naci bashinka ban biya ba.."?ya fada yana ballamasa harara.

Yar dariya Jabir yayi kafin yace"Ba laifina bane Captain,banbin ka bashi ammh akwai mai binka.."Yafada yana shafa sajen Fuskarsa,Shekeke Aliyu ya kallesa kafin yace"Toh waye..? Jabir yayi Saurin matsawa baya sai ga Ni"ima ta bayyana tana sanye da Doguwar riga Baka kirar Armani,tayane kanta da bakin mayafi,kafarta sanye da wani black halfcover,mai kyau da tsari,sai wata karamar jaka,da wayarta dake hannunta,Sake baki Aliyu yayi yana bin Ni"ima da kallo daga sama har kasa,itako Tunda ya fito take kallonsa gabadaya wani soyayyarshi data binne lungu da sako Ya tasomata lokaci daya hawaye suka cikamata ido saboda tsausayin kanta.

Rausayar dakai Jabir yayi kafin yace"Toh na fita ko? Kai mallam ka bata hanya Ta shiga ciki takanas daga gombe take saboda kai,ko bakomai ka girmama bakonka.."Jabir na fadin haka ya wuce ya barsu nan,Ni'ima dake tsaye batayi gaba batayi baya ba,kallonsa kawai take hawaye suka gangaromata baki na Rawa ta Furta.."Soja..Nah...",Tafada cikin muryan kuka kafin tatafi da gudu ta fada jikinsa sai kuma ta saki kukan lokaci daya,Ajiyar zuciya Captain ya sauke kafin yayi baya bayan ya sanya kafa ya Rufe kofar takoma Tarufe kanta,hannu ya sanya yana buga bayan Ni"ima lallashi itako Fadi take"Why my Captain? why..? .meyasa zaka barni alokacin danake tsananin bukatarka da burin na sameka? wlh koda da darana daya bantaba samun kwanciyar hankali da barci mai dadi ba Tunda na Rasaka don Allah Sojana kada ka sake gujemin wlh bazan iya Rayuwa baka ba,nasha wahala kafin na sameka...",Tafada tana kara kamkameshi,tanasakin wani marayan kuka.


Bambareta yayi daga jikinsa ya isa da ita kan daya daga cikin kujerun Falon ya zaunar da ita,Kichen Ya nufa yaje ya daukomata Ruwa da wani karaminn kofi ya Tsiyayamata mikamata yayi yana kallon kwanyan Idonta,Amsa tayi kafin ta sanya hannu ta share hawayenta,dan kurba tayi kadan kafin ta mikamai,kan Center table din dake Falon ya ijiye kofin kafin ya koma kujeran dake kallon nata ya zauna bayan Ya Dora kafa daya kan Daya yana Fuskarta dago da kanta tayi Tana kallonsa Shiko Remot ya dauka yana sarrafa talabijin din dake Falon.


"Soja...Nah...."Tafada cikin Rawan murya Dagowa yayi zata kara mgana yayi Saurin dagamata hannu yana fadin",Kinga nifa bani zakizo kina ma kuka ba,babanki zaki tasa kikatayima Kuka domin shi yasaka alkamashi ya datse halakan dake tsakani na dake..."Ya fada idonsa akanta Raurau tayi da ido kafin tace", i know buh..."Dagamata hannu yayi kafin ya mike yana fadin",Ki Adana kalamanki Ni"ima domin basu da muhalli awajena,Ba shakka ada na soki,na kuma so muyi,zama na har abada dake,sai dai kash Tun Ranar da mahaifinki ya watsamin kasa a ido naji kin Fita Raina,ko koda ace banyi Aure ba bazan Taba iya Aurenki ba,..."Yafada kai tsaye

Azabure ta mike hannunta dafe bisa kirji tace",Kana nufin kayi Aure ne my Captain..? Takowa yayi zuwa gabanta kafin ya sanya duka hanuwansa cikin aljihun wandonsa yana fadin"Kwarai ma kuwa ai wajen da mahaifinki yace bazai bani Aurenki ba saboda Bani da uba awajen wani Uban ya wanke yarsa ya bani,kinga ko iya karamci da hallacin yayimin,kuma koda ma ba"ayi haka ba,ni Aliyu bani da burin zama da mace Fiye da daya..So Abunda nakeson fadamiki gwara Tun Wuri kiyi Facing Realiaty Ki cireni Aranki don bazaki taba samuna ba,shawara ta karshe don Allah kada ki kara zuwa gida,ina da mutumci a idon jama"a bana Fatan ki Fusatani har na zubda wannan mutumci...',Daga haka ya juya zai Shige bedroom dinsa har ya kusa shiga ya waigo yana fadin"Armmm..In kin Fita plz close d door...",Yana fadin haka ya Shige bedroom ya banko kofa Ransa bace,kawai daurewa yake shiyasa bai Mazgeta ba,ammh azahirin gaskiya haushinta yake daga ita har Dan sandan Ubanta.

Ni"ima ko Durkushewa tayi ta fashe da kuka,kamar zata Shide,Rike kanta tayi tana girgizawa tadade tana durkushe kafin tatashi ta fice daga gidan,Direba ya kawota Jabir na gaban gidansa yana jugging ya hangi Fitowar Ni",ima Tana kuka Dan mirmshi yayi kafin yace"i know haka zai Faru dama gaskiyan nake so ki sani asauka lafiya..,"Yafada yana dan Dariya,mota ta Shige ta Umarci Direba ya taka mota suje don yadda take jin zuciyarta kamar zata Fashe saboda kunci.




_________________

_Gombe_


Yau kimanin Sati daya kenan da komawar Azeema gidan goggo,Duk wani jin dadi da Kulawa goggo na bata,domin koda ta daukota daga gidansu Kai tsaye shashen Aliyu ta budemata tace mata nan ne dakinki Azeema,ki zauna kijira mijinki har ya dawo..Toh ya Azeema zatayi bata da yadda zatayi sai bin Umarni,Goggo da kanta ta zage suka gyara shashen suka tsabtaceshi,Washegari kuwa Goggo da kanta tadauki Azeema sukaitai kasuwa tayimata siyayyah kaya da Atamfofi da Dogayen Riguna harda masu sikat,sai kayan kwalliya da takamla duk wani Abun gayu dai na mata ta siyamata domin goggo kudi har bata sanin ina zata kaisu,in kawu yazo ya bata,hakama Aliyu,kullum Tarasu take saboda babu Abunda take siya komai na more Rayuwa sun siyamata shi ta mallakeshi,harta ta wajen gyaran kai Sai da goggo takai Azeema aka gyaramata kai aka wankeshi sosai,Ita kanta Azeema tayi Farinciki da Shigarta sabuwar rayuwa,haka Baba Ade tazo tayitama Goggo godiya harda kwallah saboda murnan chanjin Rayuwa da Azeema ta samu kamar yadda Mallam lawal Shima dauke Azeema daga gidan Yafi komai yimai Dadi.

Goggo batai kasa agwiwa ba,harta girki tazage tana koyama Azeema dawasu kissa,da dubarun yadda zaka jawo hankalin Namiji gareta,kullum bata lbrai take,tare da kawomata kissa kala kala na yadda kishi mai tsafta ya gudana agidan Annabin Rahama Muhammed Sallallahu alaihi wasallam,Tare da kissosin matan sahabbai,ba shakka Azeema na dauka shawarwarin goggo sosai don tana jin dadin xama da ita,Cikin Sati daya Azeema ta chanza kamar ba ita ba, Tuni wa"innan kuraje suka kama kansu dama wahalace ta kawosu,Tayi dan yi kiba taciko uwa uba ga chanjin abinci dana Sutura,Kullum a Sashen gadanga take kwana,ammh adayan bedroom din dake kusa danashi,wanda yake akulle Tana Tunanin makullin dakin yana hannun mai Shi ne,Watarana adakin zasu wuni da goggo watarana kuma A shashen goggo,Tunda Abun ya faru Azeema bata taka gidansu ba,kai ko Fita in ba kasuwar da sukaje da goggo ba,bata taka ko"ina ba,Babanta Kadai suke haduwa dashi in ya fito da safe zai Tafi kasuwa don yanzu yakoma cikin kasuwa da sana"arsa Ssnadin gadanga don shi ya siyamai shago ya koma chan,yanzu hankali mallam lawal akwance yake,Domin Ramatu dai bata da wanda zatayi Fitina dashi Azeema ce kuma ta barmata gidan,daga ita sai yarta suci wainarsu babu babbaka.


Azeeza kuwa Duk iya tsawon kwanakin bata taba Sarara ma kanta da Tunanin mafita ba,tabuga ta buga ammh tagagara samun wata hanyar da zata cima nasara Adaren lahadi zuciyarta tagama yanke shawaran data ke ganin tabbas ita tafi dacewa kafin tafara zartar da komai,so take ta Fara lalata Auren Azeema Tukunnah ta yadda babu wanda zai zargeta da aikata hakan.


*Monday*

Monday Tushen Aiki ko bature na tsoron zuwanki,Yau Su goggo su dan makara tashi,kuma yau din ne Azeema zata koma mkranta,koda ta Shirya har 7:30am ta wuce Shiyasa kawai ta dauki jakarta tana cema goggo ta wuce,fada goggo tafara yi tana fadin ya zata tafi bata karya ba,maza ta tsaya ko Ruwan Shayi ta sha,Tura baki Azeema keyi tana fadin"Allah goggo na makara.."Fifitamata shayin goggo keyi Tanafadin"To sai me,yanzu zaki isa ni zan Rakaki har mkrantan in Tsoron duka kikeyi bamai tabaki kina matar soja..'Yar dariya Azeema tayi kafin tayi mgana Sukaji sallama suka karba atare,Daga labulen dakin akayi Azeeza

Please Login or Register in order to submit comment