Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Masarauta kuwa murna sosai akayi tayi da shagulgula na Dawowar Yarima umar,ammh duka fa zuciyoyo suna cikin Fargaba na Rashin samun wani bayani game dasu Aliyu,ammh an dage da addu"an Allah ya dawo dasu lafiya,Abun da ke Faruwa shine tun watansu daya da tafiya aka daina jin lbrin su kwata kwata awaya balle aji lbrin hadin da suke ciki,an kuma sake Tura wasu sojoji suma dinma dai haryanzu Shuru kake ji Topha Abun fa yafara Zama Abun mgana saboda dai Abun yaci ace in lafiya lafiya Toh sun isa suma su dawo alokacin


Lokacin da Azeema taji lbrin Dawowarsu Umar ammh babu Mijinta aciki sai fa hankali ya tashi rai ya dumguzuma,bata da aiki sai kuka ga cikinta lokacin yashiga watansa na bakwai takara girma da Cika gashi cikin yana da girma sosai,tuni ya Turo gaba kamar cikin wata Tara,sukansu maimartaba karfin hali ne ke tafe dasu ammh fa sun Fara sarewa,Su Umar suna Nageria haryanzu domin ana kokarin Shirya wata tawagan ne zuwa chan maidugurin aje adubo ko lafiya don Shurun yayi yawa.


Kwatsam sai ga wasu daga cikin Tawagansu Aliyun sun dawo ammh babu Aliyu aciki da wasu daga cikin tawagan sojojin su Tara kaf,Sojojinn nageria su hudu,hudun na Cameron ne,kuma kowannensu shugabannunsu suna alfahari dasu sakamakon dukkansu zarata ne kuma jarumai ne,koda suka dawo aka tambayesu ina Sauran yan Tawagansu nan suka bada lbrin cewa wata daya daya wuce yan boko haram sun Farmakesu a sansaninsu dake Sambisa,inda sukayi bata gashi dasu,toh Lokacin an samu rabuwar kan Sojojin,akwai wadanda aka kashe ckin dajin kuma su basuga gawarsu ba,bayan komai ya lafane suka nemi wadandan Sojojin suka rasa ciki kuma harda shugaban Tawagan Nasu Captain Aliyu Tambari buzu,to kuma tun lokacin suka rasa wayoyinsu na mgana zuwa headquater kai tsaye,lokacin da wasu tawagan suka sake zuwa ,sai suka sake sabon Shiri,shine dalilin yin nasaran Cafke yan boko haram har su goma sha bakwai,Sungama duba ko",ina ammh babu gawarwasunsu toh suna kyautata zaton cewa kila sun kamasu ne,sun tafi dasu chan wani waje dabam kuma inda babu wanda ya sani sai su.


Wannan labrin yatadama gwannatin Nageria hankali ba karami ba,Su Umar da sukaji lbrin kuka reras sukayitayi Shida Jabir,basu da karfin gwiwan zuwa da wannan lbrin gida saboda zuciyoyo sun Raunta Ainun,sukansu Karfin Addu"ane ke Tafe dasu,nan da nan Cheif of Staff,yabada sanarwan Shirya jiragen yaki masu dauke da Na"urori zuwa Dajin na Sambisa Domin Ceto Wadanan Sojojin don Kasa bazata barsu su salwanta ba,duk da suna kyautata zaton samun Araye.






*Janafty
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *Chapter 36*

  "Washegari Sojojin suka yima Dajin Sambisa tsinke,wannan karon harda manyansu atare, dasu bayan su Umar da Jabir da Sauran wasu jajiratattun Sojojin,Ta jirage ne wadanda ke da Na"irorin Daukan Hoto ta kasa,ma"aikatan dake cikin Helecopter din suna ganin duk wasu kananan Abubuwan dake cikin dajin,ta Na"urorinsu,cikin ikon Allah suka tarar da wani sansani na yan boko haram din acikin chan kuryan Daji,Umarnin yin kasa akabama Jiragen bayan kowani Soja ya saka rigar iska,sun Fara sulalo wa kasa,Mamaya suka yi musu ba Shiri kawai sai dai sukaji tashin harbi kokafin su Fito da Makamansu sunyi musu kwanya harbi kota ko"ina domin Sojojin suna dayawa Suma,nan Fa akaita bata kashi har na tsawon Mintina Talatim kafin sojojin su samu Nasarar kashe wasu ammh duk da haka akwai wadanda suka kara Nausawa dajin,suma acikin Sojojin an samu Wadanda suka Raunata,ammh ba!a samu rasuwar rai ba,nan da nan suka kafa sansani bayan an Fitar da masu Rauninka likitocin cikinsu na basu Taimakon gaggawa.

Cikin katon sansaninsu da Sojoji sukayi watsawatsa dashi aka gano Sauran Sojoji 8 daga cikin wadanda suka bace,suna daure dukkansu da kacha,duk sun rame sun lalace,dukkansu babu riga ajikinsu,ko"ina tabon bulalane da sara alamar dai Suna cikin wata rayuwa,cikin azama aka kwance su aka daukesu zuwa sansanin sojojin domin basu Taimakon gaggawa Major Sadeeq Amfani ne ke Fadin!where iz Captain Aliyu Naseer..'?yake Fada Ahankalinshi take,sai alokacin Sauran Sojojin suka Fahimci babu Aliyu aciki,nan fa hankalu suka Tashi nan da nan akace su Jabir su sake bazama cikin dajin domin sake dubawa kila a dace su ganshi.

Aikuwa hakane ta Faru basuyi nisa ba,suka iske wani sansanin ammh babu kowa aciki,koda suka Farma wajen sai suka tarar da wani mutum Daure daga saman hannayensa da kasa ma an Dauremai kafafu,Shibai kai tsakiya ba,shikuma bai sauko kasa ba,kansa na sunkuye ne jina na zuba ta hanci ta baki,bayan Kafarsa ta dama daure da wani kyalle,ammh haka jini ke zuba awajen,gashi ta kumbura,Tsaye sukayi cak suna bin Mutumin da kallo,Abu daya yasa su ka gane wannan nasu ne,wandon Sojan Nagerian dake jikinsa,wanda yachanza kala saboda jini,Jabir daje tsaye yayi kukan kura yana Fadin"Dude...."Yafada da duka muryansa bude,wanda harsaida Dajin ya amsa,hatta sauran Sojojin dake baya da suka ji suka Biyosu aguje dauke da makamai.

Umar najin haka ya karisa garesa suka rikosa baya Numfashi alamar ma Asume yake,wasu daga cikin Sojojin suka fara Zagaya wajen suna dube dube,wasu kuma suka isa wajen suna kokarin kwance Aliyu,awurin kwancensa ne suka Fahimci yana da karaya biyu Akafadansa ta
dama,bayan kafarsa ta dama ta Dauke da harbin bindiga,ammh an cire harsashinsa,sai kafarsa ta hagu itama tana Dauke da karaya,sai wasu kananun gocewar kashi,kuka reras Su Umar keyi na tsausayin Halin da Aliyu ke ciki,haka suka Daukosa ko"ina na jikinsa ya saki kamar gawa,suna Fito dashi manya sojojin suka karisa garesu da hanzari Jabir ne yake sanar dasu irin Rauninka dake jikinshi,nan da nan Major Sadeeq  Amfani yasa su Jabir da Sauran Sojojin su cikon 8 din da kuma wadanda suka jiggata su shiga jirgi tare da Likitocin cikinsu su koma chan Asbitin Federal Ta Abuja,domin basu Taimakon gaggawa,su in sungama tararra komai zasu zo daga baya.

Cikin kankani lokaci aka sakasu cikin jirgin suka lula sararin samaniya,tun acikin jirgin Likitocin sojojin ke bama Aliyu taimakom gaggawa,ammh har zuwa lokacin bai farfado ba,sun dai samu daman warware kafar data keda harbi sukayimata dressing kafin su isa Abuja,shiko Chaif Amry of Staff tun suna chan lbrin ya sameshi cewa an ganosu,nan da nan suka sanar da kafafen yada labarai na Gano wadandan Sojojin dasuka bata ayayin kwantar da tarzoma agarin na maisuguri.

Suna isa Abuja direct asibiti aka wuce dasu,wanda yafi jin jiki Aliyu ne domin Shine baya cikin hayyacinsa,suko Sauran Tun acikin jirgi suka dawo hayyacinsu,Emagency aka shiga dashi domin bashi taimakon gaggawa da kuma daure karayan dake tare dashi,ga kuma harbin bindiga wanda ya dade ajikinsa don ma dai Allah yasa Tun lokacin da Abun Yafaru an cire harsashin.

Lokacin da lbrin kuboto da Sojojin dasuka bata ya zaga Duniya gabadaya Mutane nata murna,ciki harda Ni"ima wanda Tun sadda taji harda captain dinta awanda ake nema,ta Shiga tashin hankali,sai kuka ta addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya,jin dawowarsu har saida tayi sujjudan godiya ga Allah,duk da ba"a Fadi Ahalin da suke ciki ba,an dai ce Sun samu Raunika ammh ba na tada hankali ba,suna babban Asibiti dake Abuja suna amsan Taimakon gaggawa.

  Kawu Shine kan gaba wajen samun lbrin wayar Umar yakira Shiyake labartamai halin da Aliyu ke ciki hankalinsa ya tashi nan take ya biyo jirgi zuwa Abuja,Shiko Umar suna gama waya da kawu ya kira Maimartaba ya Fadamai Halin da"ake cki..Wai Fadar irin tashin hankalin da Maimartaba ya Shiga Fade bata baki ne,salati kawai yake yana kiran Sunan Allah,lokacin dayake sanar da goggo zaman ya bori tayi hannu bisa kai tana kuka,maimartaba na bata baki,gimbiya Razeenah da Ummah mai babban daki da Baba Ade sai gimbiya Fasilatu kadai sukaji lbrin Abunda ke Faruwa,sai waziri da shamaki wanda maimartaba yabada Umanin ashirya musu Tafiya zuwa Nageria.

Goggo tayi kuka tana Fadin in Aliyu ya mutu ne asanar da ita,ammh maimartaba ya dagemata bai mutu ba da Ranshi,Azeema kuwa babu wanda yake da karfin halin Sanar da ita,saboda yaya lafiyarma kura balle tayi zawo,bata da aiki kullum sai kuka tana Fadin Yaya captain ya mutu ne ba"a san gayamata ne,ga cikinta daya shiga wata na Takwas,yayi girma sosai ta kumbura tako"ina gashi yana neman Rinjiyarta in ka ganta sai ka tsausayamata Saboda yadda ta rame ta lalace kamar ba Azeeman Kaduna ba,Su Zafira na iya bakin kokarinsu na kada Azeema ta damu ammh ina Ita bata su take,kewa tare da zafin ciwon mijinta kadai ya isheta,tayi kuka kamar zata mutu ammh kullum hakuri ake bata,akwai likitar datake duba matan maimartaba ita ke kula da Azeema,duk sati sai tazo ta dubata tare dayi mata Fadan,ta rage saka damuwa aranta don hatsari ne mai tsohon ciki tana da hawan jini,kuma baya kasa kullum saima karuwa dayake,Azeema kallonta kawai take aranta tana Fadin"kaji mata,wato na zauna nayita kwanciyar Hankali mijina ya tafi yaki bai dawo ba,lalle ma wannan kwakwalwarta tatabu toh jinin yayi ta hawa ai badai Ranar sauka sai Muradin Ranta yadawo,Ko Zafira da Jabir ya kira ya sanar da ita Gargadi yayimata na koda wasa karta gayama Azeema,saboda ba"a ce asanar da ita ba.



Washegari Maimartaba da Waziri sai Goggo da Gimbiya Fasilatu Suka nufo kasar Nageria cike da alhini tare da tararradin Halin da zasu iskeshi ciiki,gimbiya Razeenah anbarta ta zauna Da Azeema ita da Baba Ade da Ummah mai babban daki,wanda sukama Azeema karya Da cewa zasu wani bikin masarautar yanki dake gabas dasu ne,kwana biyu zasu suyi dawo,bata damu ba don yanzu Abubuwa dadama basa burge Azeema,ita burinta Allah ya bayyana mata mijinta tare da Fatan Allah ya sauketa lafiya.

Koda kawu Bala ya isa Abuja dakyar aka barsa yaga Aliyu bayan Anfito dashi daga Emegency,wlh sau daya ya kalleshi bai kara ba,saboda yadda yaji kwallah sun tahomai,yanzu Gadangan goggon ne ya dawo haka gabadaya kafafunsa sagale cikin wani karafa,duka kuma nannade da bandeji,bayan Kafadansa shima daure a wuyansa,shima nannade da bandeji domin Shima karaye ne awajen,sai goshinsa wanda shima Wani katon Rauni ne awajen,gabadaya dai Abun Tsausayi,har kuma zuwa lokacin bai Farka ba,tun bayan Farfadowan da yayi lokacin ana Gyaramai Dauri,Kawu waje ya Fita yana Share kwallah,bai dade da zuwa ba,sai ga Haisam,ai Shi yana Shiga ya kame atsaye hannuwansa dafe da kai yana salati su Umar ne suka rikosa ganin yana neman Faduwa fadi yake su Fadamai gaskiya anya Gadanga na raye kuwa,?Sun tabbatar mai dayana raye,kawai dai ya jiki ne.

Sauran Sojojin dasuka dawo hayyacinsu suke bada lbrin Abunda Yafaru Ashe lokacin da yan boko haram din suka kawo masu Farmaki,suka yi ta bata kashi,toh lokacin da aka samu Rabuwa Sojojin acikin daji,harda su Aliyu aciki wanda sakamakon haka suka harbeshi akafarsa ta dama,Faduwa yayi akasa,ammh sai yayi kokarin mikewa,ganin ya kasane yasa ya Fito da karamar wukar dake kugunsa ya yaga daidai inda Harsashin ya Shiga ya saka wuka ya tsaka ya cillo shi waje yana ihu yana komai,saboda azaba,haka ya saka wani kyalle ya Daure wajen,ya mike yana dingishi ya cigaba da gudu yana rike da bindigarsa,ganin bai da wani karfi ne yasa suka mamayesa suka kamasa,suka kuma saka Sauran Sojoji 8 dake tare dashi su Mika kansu ko kuma su kasheshi,toh wannan Shine dalilin dayasa suka Ajiye makamansu suka mika kansu,shine fa suka ijiyesu anan sunata musu Azaba,dama sunce lokaci kawai suke jira dukkansu zasu kashesu,lura da sukayi kamar Aliyu ne Shugabansu yasa suka ware shi dabam suna mai Azaba kala kala,shine fa har yasamu wadanan Karayan da kuma Sauran Rauninka,suna kokarin cinye wa!adinsu na kwana biyun da suka diban musu na zasu nunasu Afaifan Vidiyo,su bada sanarwa cewa ko gwannatin Nageria su sakarmusu mutanesu suma su sakin musu Sojojinsu,in kuma sunki yarda toh suma zasu kashesu Dukkansu,toh Ana cikin hakane Sojojin sukazo suka Farmusu kuma Allah yabasu Nasara.


*****************

Maimartaba basu samu isowa ba sai Washegari,lokacin da suka Shigo cikin asibitin sun tarar da Kawu Bala da Haisam,sai Umar da Jabir,sai wasu Security dake tsaronsu,Yanayin yadda goggo taga kawu tun anan jikinta yayi sanyi kafafuwanta sukayi Nauyi,lura da Halin datake ciki ne,yasa maimarta riko hannunta ya matse alamar Karfin gwiwa kallonsa tayi wasu hawaye na gangaromata,likitocin sunyi complain Majinyacin baya bukatar hayaniya,saboda Baida de da Farkawa ba,ganin kimar Maimartane yasa aka barsu suka Shiga inda Aliyun yake,kai kodaga ganin yanayin dakin,gabadaya glass ne,zaka Fahimci saima Mutum yaji kamshin mutuwa ake kawosa irin wannan Dakin😅,lokacin da suka Shiga Dakin goggo na rabe bayan maimartaba Gimbiya Fasilatu ce kan gaba sai Waziri sai kawu bala dasu Umar,su goggo suna bayansu,Waziri keta salati yana kiran Sunan Allah lokacin dayayi Tozali da Aliyu,itakanta gimbiya Fasilatu da damuwar Abun baiwani dameta ba,sai da tayi baya tana dafe kirji idonta ya kawo kwallah,wani imani yakara Shiganta lokaci daya,yanzu Aliyu ne yakoma haka? ganin haka yasa maimartaba karisawa bakin gadon na Aliyu yana kallonsa da duka idanuwansa waje,Goggo dake bayansa tayi Saurin Rufe bakinta wanda kuka kenan Kwacemata hannu maimartaba ya sanya ya cire gilashinsa mai karamasa karfin ganin,hawaye suka taru acikin idanunsa,har sai da suka kwaranyo bisa hannun Aliyu wanda yake da lafiya,jin sanyin hawayen maimartabane yasa ya motsa hannunsa,lokaci daya da bude kumburarrun idanunsa,dishi dishi yake gani,ammh duk da haka sai da ya gane goggo da maimartaba dake gabansa,bakinsa ne yafara motsi,shiyasa da hanzari goggo ta duke gaban gadon tana Riko hanunnsa take Fadin"gadanga...."Tafada tana kuka kallonta yake,shima hawaye suna zubomai ta gefen ido,dakyar ya Furta"Na"am goggota..."Yafada murya shake,goggo Runtse ido tayi tana Rumgume hannunsa take Fadin"Allah ya Tada kafadunka Gadanga,Allah yabaka lafiya.."Take Fada tana wani kuka,wanda duk wanda ke wajen sai ya tsausayamata,Umar da jabir dake gefe banda Share kwallah babu Abunda sukeyi,Haisam ko waje yakoma don yadda kuka yaci karfinsa,Maimartabane yayi Saurin Ficewa da hanzari,Waziri ya maramai baya Shida Kawu Bala.


Gimbiya Fasilatu da Tsausayin goggo ya cikata ta Durkusa tadafa kafadanta tana Fadin"Ki bar kukan Suwaiba,kuka bazaimana mgani ba,addu"a zamu tayimai Allah ya bashi lafiya.."Goggo na jin haka tamike da hanzari,itama gimbiya Fasilatu ta mike,saboda yadda goggo take jikintama babu karfi saboda kuka,shiyasa kawai Tafada jikin gimbiya Fasilatu takara Fashewa da kuka mai cin rai,itakuma ta riketa tana lallashinta,Aliyu na kwance yana jinsu shima kukan yake,yana so ya tambayi,goggo ina Azeema ta haihu ne?ko haryanzu da Saura ammh kuma bakinsa yayimai Nauyi bazai iya mgana ba

Ashe Fitar su maimartaba sukayi Office din likitan yaje,yace ya Rubuta musu takarda yanzu zasuyi Transfer din Aliyu zuwa wani babban Asibitin kashi dake kasar india New Delhi,nan fa sukace basu san dawannan mganar ba,saboda gwannatin Nageria karkashin Sojojin kasa,ita keda alhakin kula da Aliyu Ahalin yanzu,kuma yana karkashinta babu yarda za"ayi su basu shi su tafi dashi,batare da gwannatin Nageria tasaka hannu ba jin haka yasa nan da nan Akayi waya zuwa ga *BRIG.GEN.S.U KUKA SHEKA* Shiya sanar da maigirma Chief Amry of Staff *LT.GEN.Y.T BURATAI* Abunda ke Faruwa babu Bata lokaci sai ga tawagarsa zuwa Asibitin da Aliyu ke kwance,nan suka hade dasu maimartaba bayan gaisuwa dawani dogon Turanci dole dai gwannatin Nageria ta rarrataba hannu tabasu Yaronsu,ammh sunyi kokarin nuna duk wani taimako da"ake nema suna Shirye suke dasu badashi,domin haryanzu Captain Aliyun yana mtsayin Sojan Nageria,Fatan Alheri ne ya biyo baya tare Da Fatan Allah ya bashi lafiya.


Kawu Bala shiya ta kokari har suka samu Visa zuwa gobe da Safe,shiyasa basu daukeshi daga Asibitin ba,sai Awashegari,bayan sunje hotel sun kwana,karfe 9:30 Jirgin nasu zai tashi ababban Filin jirgin *Nnamadi Azikiwe International Airport Abuja* Motar Asibitin da taimakon wasu likitocin suka daukosa daga Asibitin zuwa Airport din,Abunda zai baka sha"awa dukka masu Fada aji agwannati suna wannan wajen,harda wasu Sojoji wanda suke ta Farate,tare Sarama Shi Aliyun lokacin da"aka Fito da gadon marasa lafiya daga cikin jirgin za"a Daukesa zuwa ciki,yana kwance kamar baya Numfashi sakamakon sunyimai Allurar barci ne wacce zata daukesa har na tsawon awa biyu,bai Farfado ba,har aka Shiga dashi cikin jirgin baisani ba,su Maimartaba Sukabi bayansa,shiga da goggo da gimbiya Fasilatu sai Waziri da kawu Bala,sai Umar da Jabir da Haisam suma ba"a barsu abaya cikin lokaci jirgin da zai yada zango a babban birnin india ya lula sararin samaniya.



_________________


*INDIA*
_NEW DELHI_


""Tun Suna Nageria dama Kawu already yagama mgana da Asibitin ta yanar gizo,sun san da zuwansu,suna sauka sai ga Motar babban Asibitin na *FORTIS HOSPITAL NEW DELHI* Sunzo tare da Manyan likitocinsu sun daukesu,zuwa Asibitin inda nan take babban Likitan kashi wanda Duniya ke Ji dashi *DR KABIR KHAN* Wanda ya kasance musulmi ne gaba da baya,kuma Ba indiye ne ta uwa ta uba,yasa aka Shiga dashi Thearter Room,Tunkafin zuwansu dama Tuni kawu yagama Turamusu dukkan Bayanai game da ciwon nan Aliyu,kuma hatta da kudaden aiki sai da ya Tura musu ta bankinsu dake yanar gizo,Tunda suka shiga dashi basu Fito ba har Tsawon awa biyu shine dalilin Daya su Umar suka bar Asbitin sukaje suka kama musu masauki wanda ke kusa da Asibitin wani kayatattacen hotel suka kama musu, mai Suna _JW MARRIOTT HOTEL NEW DELHI_ Suka kuma kira su kawu awaya suka sanar dasu,sanin ba yanzu za"a Fito da Aliyu ba yasanya dukkansu suka nufi masaukin kowa yayi wanka suka ci abinci kafin sukara dumguma sukoma cikin asibitin,kuma Abun Sha"awa,harda motoar da zata dinga zirga zirga dasu mallakin Asibitin ne,komai nasu cikin tsari.


Suna komawa ba Dadewa sai ga Aliyu an gunguroshi kamar gawa zuwa dakin Hutu,indiyan likitocin kuwa sai bama junasu hannu suke suna ma juna barka da alamun dai aikin da sukayi ansamu Nasara ganin haka yasa,su maimartaba sakin ajiyar zuciya suna mai Hamdala acikin zukatansu.






*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_I dash to whole page 4r My one and only *YAYA*😘 D person of *IBRAHIM* Yaya I.B..Tanque so very much Yaya for ur luv,support and care,Allah ubangiji yabaka Mata tagari wacce zata kula dakai kamar yadda kake kula da *KANWARKA* Ameen_🙏😘

*Chapter..37*


""Dr Kabirkhan Shiya nemi ganawar Sirri da maimartaba dasu Kawu,inda yake sanar dasu cewa aiki yayi kyau masha Allahu,ya sanar dasu lalle gadanga ya Auna arziki domin da"ace an kara daukan wani lokaci da kafarsa inda wacce ke dauke da harbin bindiga sai dai ayanketa,kuma taimako ma na biyu shine sanda harsashin ya Shiga Tunkan yagama huda nama jikinsa,akayi Saurin Fidda dashi shima yabada Taimako sosai wajen Rashin lalacewar kafarsa tasa, kana daga karshe Dr kabirkhan yayaba da Jarumta tare da Dauriya irinta ta Da"nsu Aliyu gadanga,domin ya iya tsawon kwanakin daya dauka da wannan Rauninka ajikinsa tabbas ko acikin Sojojin shi na dabam ne,ammh yanzu haka yana dakin hutu kuma babu wanda zai Shiga inda yake sai nan da kwana biyu lokacin ya Farfado,kuma duka aikin nasa baza"a warwareshi ba,sai nan da wata biyu,lokacin suna saka Ran Insha Allahu komai yazama Tarihi Aliyu zai taka da kafarsa ya Fito daga cikin Asibitin nan yakoma kasarsa da kafarsa


Hakika su Maimartaba Sunji dadin bayanan Dr kabirkhan wanda yayi musu Shi cikin harshen Turanci,godiya sukayita yimishi,shima yana gode musu,kafin su Fito daga office din nasa maikama da aljannah Duniya,Koda suka Fito Abunda ya karanta musu,shi suka karanta ma su goggo dake waje hamdala kowa ya Shigayi Tare da Fatan Allah yasa anyi aikin cikin Nasara,basu koma masauki ba sai chan dare bayan sun leka Aliyu ta cikin glass,din inda gadon dayake kwance yake,gabada kafafunsa suna sagale ne jikin wani karfe,mai aiki da wasu Na"ura,haka hannunsa,shima an sagala shi,jikin wani Abu mai kama da roba,dai dai inda hannun yake anyi wani Filo,yadda hannun yayi bisa,kodaga chan suna hango Fuskarsa yadda tayi Haske,ammh yayi Rama sosai,dukkansu sunji dadin ganinshi domin yafi yadda suka taho dashi,addu"an samun lafiya sukayimai kafin su rankaya zuwa masaukinsu.


Kamar yadda Dr kabirkhan Yafada kwanan Aliyu biyu ya Farfado,kuma Alhamdulillah jikinsa yayi kyau sosai,domin koda likitoci suka gama bincikensu akanshi,suka Fito bayan sun bama su kawu damar Shiga wajensa,ammh banda doguwar mgana,koda suka Shiga sun Tarar da wata Nurse ta tadashi zaune ya jingina bayansa da wani Filo mai kyau da taushi,Yana ganinsu yafara mirmishi alamar Sauki ya samu,Tea mai zafi Nurse din ta hadamai ta mikamai,ya karba da hannunsa mai lafiya,Umar ne ya karisa da hanzari zai karbi Kofin Nurse din ta dakatar dashi kafin tace abarsa yasha da hannunsa saboda inyana motsa wannan hannun nasa,shi zai taimaka wajen Motsa wanchan hannun mai Ciwo,kai ya gyadamata alaman gamsuwa kafin ta Fice ta barsu,nan fa suka zagayesa suna hamdala,goggo ko Kallonsa take hawaye suna taruwa a idonta,girgizamata kai ya hauyi kafin yace"karki kuka goggo,kin manta kece ke man kirari da gadanga kusar yaki,ba gaba da gaba ba ko ta bayan ma karya sukeyi? yafada cikin sanyin murya dariya goggo tayi lokaci daya da mirmishi,Kofin tea din ya mika Umar yana Riko hannun goggo yace,"Toh kuma Shine kike kuka,kinsan baza su iya ba,baza su iya ja da gadanga ba,gadangan goggonsa. ba."Yafada yana Sharemata kwallah,dariya ta kubcema kowa ganin goggo na kuka tana dariya hannunsa ta kamkame tana Fadin!"Tabbas bazasu iya ba,Nasani baza su iya jada gadanga na ba,Allah ya baka lafiya"Da Ameen ya amsa kafin yace"Kawu wai muna wani gari ne,sai naga kamar nan ba Nageria bane,duba ga likitocin da suka zo suka dubani yanzu..?


Maimartaba ne yayi mirmishi yace!"Alhamdulillah Tunda yanzu kadawo hayyacinka,yanzu haka muna babbar birnin india,New Delhi,acikin wani Asibitin kashi.."Gyada kai yayi yana mamakin duk yaushe sukazo nan,kawu ne ya karbe da cewa"kuma kwananmu biyu yau da zuwa,kuma sai yau ka Farfado bayan aikin da"akayi maka Tun bayan zuwanmu.."gyada kai yayi yana bin Su Jabir da Haisam da kallo,wadanda sukayi wani kalan Tsausayi,dariya ta kamashi ya daga hannu yana Fadin"hey ya'n kannena,ban mutu bafa naga kunyi wani kalan Tsausayi ne..",Hararansa Haisam yayi kafin yace!Suwaye kanneka...? kai tsaye yace"Kumana.."Jabir ya yi Saurin Dunkule hannu zai sakamar bisa ciwo,da hanzari Aliyu yace"Kai Dude Don Allah bari wlh kuna gaba dani.."Yafada yana Zaro ido,sauke hannunsa Jabir yayi yana dariya gabadaya su goggo dariyan suke,na ganin diramar su Aliyu,mai hali dai baya chanza halinsa.


Suna Shirin tafiya masauki ne,Aliyu yakira goggo wacce ke Shirin Ficewa dawowa tayi tana Fadin"gani gadanga ko kana bukatar wani Abune? girgiza kai yayi yana Fadin"A'a goggo.."Kallonsa tayi kafin tace'"Toh mene ne? lumshe ido yayi kafin yace",Ammr,nace ba goggo banga Azeema bace ko ba"a zo da ita bane..."?Yar dariya goggo tayi kafin tace"Allah sarki ai nasan zaka tambaya,wlh Azeema na gida,bamu Taho da ita ba,kai batamasan Abunda ke Faruwa dakai ba gaskiya don ni na hana a sanar da ita,tunda aka nemeka aka Rasa,Azeema ta shiga kunci,gashi kuma cikinta ya Tsufa,kaga kuma sanar da ita kamar kara mata damuwa ne.."Dan Ware ido Gadanga yayi kafin yace"Cikin yayi kato ne goggo..? kansa ta dungure kan tace "Ban sani ba in tazo sai ka ganninma idonka..."Washe baki yayi yana Fadin"Da gaske pretty zata zo wajena.."Gyada masa kai tayi kafin tace"Haka nake so,da zarar mun koma zasu zo ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,Allah barshi sai ta zauna anan har ta haihu,lokacin kuma nasan kai Alhamdulillah kasamu lafiya sai ku tattaro ku dawo gida,ko baiyi ba.."da hanzari Aliyu yace"Hakan ma yayi goggo Allah ya kara girma.."kansa ta Shafa kafin tace"Sai da Safe Allah ya kara Sauki..."Tafada tana fita daga dakin,dayake Asibitin basu da bukatar wani mai jinya,sai dai in daga nesa kukazo,ku kama masauki kuna zuwa kuna ganin majinyacin har ya samu lafiya,ammh ba'a yarda da kwanan Asibiti ba.



Haka ko akayi Sati daya Su maimartaba Sukayi Akasar india kafin su tarrara su koma Niger,Tunda jikin Aliyu Alhamdulillah,kullum yau yakan Fi jiya,Abun mamaki harta hannunsa mai karaya yana iya motashi,hakama kafafunsa,yana iya motsasu,ammh ahankali cikin dabara,Jabir ,da umar kadai aka bari,ammh dukkansu suka koma,daga Niger kawu ya hayo jirgi shida Haisam suka koma Nageria,inda suka kaima su Ummah lbri mai dadi na cigaban da'aka samu game da Ciwon na Aliyu,wanda sai lokacin hankula suka kwanta.


Mganar da goggo ta yanke na zuwan Azeema wajen Mijinta,ta Sanar da maimartaba baiyi gaddama ba ya amince da shawaran goggo,don ko bakomai taga mijinta shima yaga matarsa,ko Allah yasa ta kwantar da Hankalinta ta haihu lafiya,koda goggo ta sanar da ita mganar Tafiya india ammh bata sanar da ita wajen Aliyu zata ba tadai sanar da ita cewa zata tafi ta haihu achan ne,Tura baki Azeema ta hauyi,daganan sai kuka wai ita ba inda zata,ana so tatafi ne,azo da gawan yaya captain abinne Shine asoke ayimata wayau,Fafur fa Azeema tace babu inda zata,dakyar da sa bakin maimartaba

Please Login or Register in order to submit comment