Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya ya share kwallar yana Fadin"Hakika munyi Rashi,Allah yajikan mallam da Inna Allah ya sanya sun Huta.."Da Ameen aka amsa,wajen yayi Shuru kafin Maimartaba yayi gyaran murya yana Fadin"

  "Kamar yadda kuka sani Nazo garin nan bani da kowa,nazauna a hannun mahaifinku har na tsawon wasu Shekaru,kafin yarda da aminci yasa ya dauki Auren yarsa yabani.." yadanyi Shuru kafin ya Numfasa yacigaba da Fadin"Tabbas koda nazo garinnan bani a hayyacina sakamakon kurciya da"akayi min,kuma aka hadamin da Sammu,wanda zan manta Asali na ,banda sunana ba"a barni na Tuna komai ba..",Gabadaya suka zubamai ido suna kallonsa,bai wani damu da kallonsa da sukeyi ba,har goggo wacce ta maida hankalinta kanshi,tayi tagumi da hannu bibbiyu,Ya cigaba da Fadin.


   *SHEKARUN BAYA*

_LABARIN MASARAUTAR TAMBARI BUZU_

 
   _Ashekarun baya Anyi wata Masaurata Akasar Niger a yanki Agadez,awannan yanki anyi wata masarauta mai Dimbin Tarihi,Tun Ada Masauratane datafito daga tsatso mai Asali,tsatsoce ta jinin sarakai,tunkan zuwan Addinin musulunci,Mutane dadama sun mulki Garin,Adalai masu kaunar talakawa da kawoma Masarauta cigaba,Wannan Masarautan Sunanta MASARAUTAN TAMBARI BUZU,Sunanta ta samo Asali ne,daga sudin buzaye ne gaba da baya,kuma sunkasance dukkansu Farare ne,dogaye masu zati da haiba,suna da jarumta uwa uba kuma Masarautane mai Dimbin Tarihi na Kudi da Arziki ko ada chan,suna da hadin kai da Sanin mutumcin juna,ba"ta samun Sabani ko Rabuwan kai ba,sai da Manya suka Fara tafiya Mulkin yafara komawa hannun kananan_


  _Masarautar ta samo Asali ne Daga mulkin Sarki ABDULGANIYU D'AN HASHIM,wanda ya mulkin Garin na Tsawon Shekaru arba"in da wani Abu kafin Allah ya dauki Ransa,bayan mutuwarsa aka Nada babban D'ansa Wato BADAMASI D'AN ABDULGANIYU,amtsayinsa na babban Dansa,kuma ya chanchanta da zama Sarki bisa la"akari da duk Abunda ake bukata ya mallakesu,Kuma yakasance Shikadai ne Namiji Awajen Sarki Abdulganiyu,Sauran Duk matane_

  _Shekaransa goma ne akan karagar mulki Ya rasu,Bayan Mutuwarsa Anyita Rigima kafin Anada Wani sarki Wato YAKUBA D"AN BADAMASI ,Jika ga ABDULGANIYU D"AN HASHIM,Wand Shibashi daga cikin wadanda suka nemi Sarauta alokacins saboda baya Ra"ayinta kwata kwata,kuma Shine na hudun ajerin mazan,kuma duka yayyin nasa su uku ba wanda bai Nemi Sarauta ba,ammh basu samu ba sakamakon basu chanchanta ba,kwatsam sukaji an nada YAKUBA bisa chanchantarsa shi yakasance yana da ilimin boko har matakin masters,duk da bai yawaita ba awanchan lokacin,sabaninsu na Arabi"an kadai garesu,sannan yafisu sanyi Hali,duk dayake karami acikinsu Adai komai ya chanchanta Toh wannan al"amari Shine tushen komai don Shima yasama Sauran yan"uwansa hassada da kyashi Aransu,acikin yayyin nashi akwai IDRISA, sai KAMALLUDEEN Sai NASAR Sune manya kuma sune suka nemi Sarautan aka hanasu,kuma gabadayansu ba ya"yan mutum daya bane,Tunda alokacin matan Sarki hudu,Mahaifiyar yakuba ne karama_

  _Su aganinsu yaya za"ayi Adauko Yakuba abashi mulki,Alhalin gasu,an nuna musu yan ubanchi,daga wannan lokacin Zaman lafiya ya kare awannan masarautan inda su Idirisa sukasha alwashin ganin bayan wannan mulki na Yakuba,bayan an Nada Yakuba,Talakawa na jin dadin mulkinsa,sakamakon yayi gadon mahaifinsa akyawawan dabi"u,ba yadda baiyi ba don ya sansanta da Yan"uwansa ammh ina Abu yaci Tura,Har Sarauta yaso ya ijiye, yatarama manya masu ruwa da tsaki a masarautar,su suka nunamai Ahir dinshi,saboda shima bayason Abunda zai kawo Rabuwan kai shida yan"uwansa,mahaifiyarsa akullum Addu"arta Allah ya tsaremata da'nta toh Ana wannan Hali Allah yayi mata Rasuwa mutuwar data girgiza sarki Yakuba yazama maraya gida da waje,toh daman yana da matansa ,uwargidansa UMMUKHAIRI yar wani tsohon Wazirin Sarki Badamasi ne,sai GIMBIYA KILISHI yar wani Sarki dake gaba da yankinsu,bayan An danashi Sauratane Yacike da MASHASHATU itama yar sarki ce sai takarshensu yar wazirinsa ne ya Auramasa ZULAIKA_

  _Allah da ikonsa Da"n sa Namiji kwara dayane tak Duka haihuwan da Matansa keyi wabi suke Uwargidansa UMMUKHAIRI ita ta Haifasa masa Shi Wato ABDULNASEER,sarki yakuba ya dauki Son duniya ya dorama Abdulnaseer,kuma hakan ya samo Asali ne daga soyayyar dayakema mahaifiyar Abdulnaseer din,girman Yaron ne aka gane babu inda Hallayar mahaifinsa Yakuba Natsuwarsa da son Talakawa Shine dalilin dayasa mutane suke kiransa da MAGAJIN SARKI,toh wannan shiya taso da Wutar kiyayyar Dake tsakanin Yakuba da yan"uwansa,akan bazasu yarda Wani dan yakuba yazo ya mulkesu ba,suka dora daramar Kwatar mulkin kota halin kaka,awannan yanayin Masarautar Tambari buzu tatashi da wani Firgici na Mutuwar Sarki Yakuba,an kwanta dashi lafiya kalau Akatashi akaga gawarsa Bisa binciken likitoci sun gano cewa ta hanyar Filo aka kasheshi tunda gayinan akokarin kasheshi da Filon har sun jimai ciwo awuya alamar sai da sukayi kokuwa da makashin_

   _Topha wannan al"amarin yasa Jama"a Dadama acikin Rudani,Ummah tayi kuka sosai,ita da tilon da'nta kai ba ita kadai ba kaf Masarautar Tambari buzu sai da ta girgiza,balle talakawan dake Yanki na Agadez,Harga Allah Ummah ta zargi wani Abu ammh sai ta boye,wanda Tun sarki yakuba na da Rai akecemata Ummah mai babban daki,sakamakon itace uwargidan sarki kuma mahaifiyar Yarima Abdulnaseer,Bayan mutuwar Sarki Yakuba aka Fara mganar Nadin sabon Sarki Alokacin Nagama Digree na akan political Science,karatun Addini kuwa Tuni nayi nisa_

   _Azama na Farko An tabbatar dacewa anine mutum na farko da"aka  kawo wanda ya chanchanta abani Sarautar masauratar Tambari buzu,domin na gaji mahaifina,wannan Shiya kara harzuka su Idirisa,wanda sun kara neman mulkin akaro na biyu,Manazarta da magabatan Zauren wakilai na zaban Sarakai basu tsaya bata lokaci ba suka Fitar da sunana amtsayin Sarkin Garin Agadez,harga Allah bani so,kuma mahaifiyatama bata so,Saboda tana zargin mutuwar Mahaifina yana da nasaba da Sarautar garin,Abisa wannan dalilin aka Fitar da Ranar daza"ayi min Nadin Sarauta amtsayin Sarki,sai Aranar Nadin Sarautar aka wayi gari da magajin Sarki an nemi ko sama ko kasa ba"a ganni ba,har angaji anfidda rai,dalilin an kwashe wajen wata biyar bani ba lbrina yasa aka Nada IDIRISA Masaurata tazo hannunsu sai yadda sukaga dama da ita_

    _Bacewata ta girgiza Zuciyar mahaifiyata wanda na kasancemata Da daya tilo Aduniyan nan rashi biyu alokaci daya,mahaifiyata tadauki dangana tare da maida kukanta ga Allah,tana Fatan in ina raye Allah ya karematani,ya kaddara saduwarmu,wannan Shine dalilin barin gidana,zuwana Nageria da Fadowata hannun Mallam duk banda masaniya akansa,Nasan dai na zauna daku,kun rikeni tamkar dan"uwanku har zuwa bani Auren Suwaiba da Mallam yayi_

   Gabadaya wajen aka sauke ajiyar Zuciya,Kawu ne yayi Saurin cewa "Ranka ya dade ka yanke wani Abu daga cikin lbrin,yaya akayi sammun da kurciyan suka sake ka har ka iya komawa gida,har tsawon wannan lokacin..? Daman tambayan dake zukatan mutane kenan.

Maimartaba yayi mirmishi yaciga da cewa………"

   _Daman Na fadamuku kurciya sukayimin  na barin gida,tare da sammu bazan Tuna asali na ba balle har wadanda zasu tsinceni suyi Tunanin maidoni gida,Bayan mallam ya aikeni da kudi nakai sako,nidai nasan na hau mota har nasauka,sai dai kafin na karisa cikin kasuwar wani al"amari yafaru dani,naji kamar Amciremin wani Abu atsakar ka,na zabura ina bin ko"ina da kallo,lokaci daya ina kallo kaina,kaina ya Daure,meyakawo nan,nan dai ba garinmu bane,nan ba Masarautarmu bane,kuma sannan wadanan mutane ban garinmu bane,kuma suma din ba Ahalina bane to ina ne nan?Tambayan dana dinga yima kaina kenan,ammh bansamu wanda zai bani amsa ba,inda Abun ya sakeni,daganan bankara daga kafata ba,tsaye nayi ina ta zare ido,kana ganina zaka Fahimci bana cikin hayyacina ga damuwa data bayyana zahiran acikin idanuna,wani bawan Allah ne yazo wucewa sai yaganni kamar cikin damuwa,koda ya tambayeni meke damuna ina zani? ban iya mai mgana ba illah FasheWa da kuka danayi,hankalinsa ya tashi ya Shiga tambaya Abunda ya faru,bazan iya maida komai illah na sanar dashi ina Tunanin Sato ni akayi,domin ni dan Niger ne,ayanki Agadez,jin wannan lbrin nawa yasa yatafi dani gidanshi da alqawarin Taimakamin nakoma gida,kwana biyu nayi agidanshi,kuma har nagama kwanakina banta tambayansa wani gari bane,kudin da mallam yabani na aike dashi mutumin yayimin kudin mota zuwa niger bayan na tabbatarmai da zangane gida,Sauran kudin kuma na dankamai,Tunda ni duk Atunani daga Masarautarmu aka satoni da wannan dukiya,Allah bai basu sa"ar cinma burinsu akaina ba,cikin dare na isa garin kai tsaye masarauta na dosa,ina kuma Shiga sashen mahaifiyata nafara isa,wacce na isketa tana tsayuwar dare,ganina datayi bata razana ba,takamani ta Rumgume tana kuka tana godiya ga Allah,tace tasan cewa zan dawo ko bajima ko badade,bawanda yasan lbrin dawowata gida sai washegari da safe,kuma adaren Ummah na Tafadamun duk irin mulkin kama karyan da IDIRISA Yake aikatawa Tare ta taimakon yan"uwansa,da irin yadda suka lalata komai na Masarautarmu,koda ummah tatambayeni ina naje,kuma awani gari na zauna,Abu daya na iya gayamata Cewa mutumin daya tsinceni ya sanar dani ina Nageria ne,ammh bayan nan bazan iya dora komai ba game da barina gida ba_

_Bata Fadama kowaba sai Awashegarin An zauna zaman Fada kwatsam sai gani na Shigo,gabadaya Aka mike ananeman guduwa,don kowa ya cire rai da ina raye,nan take kuma Sarki ADIRISA yamike jikinsa na rawa daga kan karagar mulki,yana nunani da hannu,yana so yayi mgana ammh yakasa,nan da nan sai bakinshi ya karkace yafadi yana makyarkyata anan take yasamu ciwon Shanyewar barin jiki,wanda hakkina ne ke bibbiyarsa da kuma asirin da sukamin na barin gida,Domin da bakinsa yafadi Abunda suka aikata agareni dasa hannu yan"uwanshi da iyayensu mata,da Hadin bakin Jakadiya suka kashe mahaifina Sarki YAKUBA,Tare da yimin kurciya na bar kasar gabadaya bayan sun hadamin da mugun sammu,wanda banda sunana da kasata bani da ikon Tuna komai,kuma ko bayan kurciyan ta sakeni sammun dake jikina bazai barni na Tuna wani Abu bayana ba,sai wanda zai Faru agaba,Sun sanar damu cewa sammun yana dadewa jikin mutum kafin ya sakeshi,shine dalilin daya samu damar hayewa karagar mulkin MASARAUTAR TAMBARI BUZU,jin jaka yasa al"ummah yankin Agadez da Masarautar Tambari buzu tayi tir dasu,Sarki IDIRISA Kuwa sati daya yayi Allah yayimai Rasuwa,saura yan"uwansa kuma hukumar gidan Sarauta ta hukuntasu,harda jakadiya wadanda ta yanke musu hukunci kisa ta hanyar sare musu kai,suko iyayansu mata masarauta ta koresu daga yankinta gabadaya Fadawa suka rakasu har wajen gari suna jifansu da Allah tir dasu,bayan an gargadesu da har abada kada sukara tako kafarsu zuwa masarauta_



_Bayan lafawar komai,akama bama mai wuri wurinsa ma"ana akayi min Nadin Sarkin Yanki Agadez Amsarautar Tambari buzu wanda aka kwana ana shagali,wanda al'ummah suka nuna Farincikinsu,Talakawan Agadez sun nuna murnansu sosai wanda aka dau tsawon sati daya ana Shagalin Nadin Sarautata,zuwa wannan lokacin da"a ka nadani amtsayin Sarki nakasa gane meke damuna,inaji ajikina akwai wani babban al"amari dake damuna ammh nakasa gane komiye shi,dama kuma ba"a Nadani Sarki ba sai da Na auri GIMBIYA FASILATU wacce ta kasance diyace ga sarki yankin Yamai,dake kusa damu,Bayan Nadin Sarauta ta kuma na Auri GIMBIYA RAZEENAH,wacce ta kasance jikar sarki Dosso ce,Bayansu bankara jin ina sha"awar kara aure ba,duk da sarakai suna ta kawomin Tallar Auren ya"yansu ammh na Fadama ummah cewa subarni haka bana bukatar kowa ayanzu,bayan hawa mulkina nayi canje canje sosai kama daga jakadiya dakuma masu zaman Fada duk munafukan dake tare dasu Sarki IDIRISA saida na saukesu nayi sabon Nadi tare da sabbin mukkarabai_


_Akullum matana da mahaifiyata sun san ina da damuwa Araina Ni kaina ko sun tambayeni bani da amsan da zan iya basu,nikaina cikin wani sarkakiyane nakasa gane meke Faruwa,shekara ta daya Da komawa gida nafara wani mafarki wanda ke tsayamin arai,amafarkin ina ganin wata mata da danta suna kuka suna mikomin hannu,nikuma ko ina da niyyar Zuwa wajensu domin taimakamusu sai wani hayaki ya lullubesu koda hayakin zai washe,sai na nemesu na rasa,Tundaga ranar inda zan kwanta barci sai nayi wannan mafarki,kuma Allah baita nunamin Fuskar matar ba,kullum cikin mafarkin nan nake,tun Abun baya damuna haryazo yana damuna,balle matana wadanda ke tare dani,mahaifiyata tashiga damuwa sosai,tayi tasakawa ana kawo mata malamai wai suyi mata duba su gani meke damuna,ammh ko sun zaunar dani sun Tambayeni bana iya cemusu komai,Nidai Abu daya na sani babu maiyi sai Allah toh gareshi na maida al"amarina Shi zai yayemin duhu zuwa haske,na dau tsawon Shekara talatin ina wannan mafarkin Allah baita warwareminshi ba,sai acikin wannan Sati Allah ya bayyanamin Fuskarki amafarkina Suwaiba ina ganinki na Tuna,bayan na Farka ina kiran sunanki,Sai matana da mahaifa suke ganin kmar nayi gamone,kwana biyu akwance ko Fada bana zuwa,ina zurfafama kaina Tunanin kozan iya Tuna awani gari muka zauna dake,ammh tabbasa na tuna kedin matatace,toh ina cikin wannan halin sai na samu kiran Da'na Yarima umar ya sanar dani Ragowar Abunda ya Shigemin Duhu,na ganin yaron da kika haifamin,bayan Tsananin kamaninsu kuma suna amfani da sunan mahaifi daya tare da sunan Masarauta,Aranar hadda Bala munyi mgana bayan ya tabbatarmin da kina raye,ni na hana agayamiki komai nafison nazo dakaina ki ganni na ganki bayan na baki lbrin duk Abunda yafaru Shekarun baya,Wannan itace mahaifiyata yafada yana nuna Ummah mai babban daki sai Matata ta fari Gimbiya Fasilatu ita ta haifarmin yaro namiji mai suna Umar gashinan,sai gimbiya Razeenah mahaifiyar su Zafira da Safaratu kenan,Bayansu bankara haihuwa ba,bani da wasu ya"ya bayansu,ina Fata da wannan bayanin zaki dubeni da idon Rahama Suwaiba ki yafemin barinki danayi na tsawon lokaci batare dana waiwayeki ba.._



Gabadaya wajen yayi tsit harda masu kwallah irinsu madina da mardiya da Ummah,Goggo kuwa kanta na bisa kafadan Kawu tana Fitar da kwallah,hatta Azeema sai ta koka,Maimartaba ma kukan yake ammh yana saka gefen Rawaninsa yana Sharewa ammh idonsa kur akan Suwaiba,Ummah mai babban daki ta mike ta isa ga Suwaiba ta dafa kadanta tana Fadin"Dago kanki Diyata...",Jiki asanyaye ta dago tana kallon Ummah mai babban daki wacce idonta ya cika da hawaye tana Fadin",wlh tallahi duk tsawon wannan Shekarun Abdulnaseer baiyishi cikin kwanciyar hankali ba,muma namu hankali ba"a kwance yake ba,kullum rokom Allah nake ya bayyana mai koma miye shi,gashi yau Allah ya amsa rokonmu kiyi hakuri kiyafamai nayi miki alkawarin bazai kara barin ki ba.."Tafada hawaye suna zuraromata Goggo da jikinta yayi sanyi ta dago tana kallon maimartaba wanda yake kallonta da tsausayawa kafin ta maida hankalinta kan Gadanga wanda ya hada hannayensa yana nuna mata alamar roko,Komawa da kallonta tayi kan su Madina taga suna gyada mata kai,balle kawu dayake ta murza kafadanta alamr lallashi,Kanta ta mayar kasa kafin ta share hawayenta tace"Shikenan...Na yafemai Duniya da lahira.."Ummah ta rumgumeta tana dariya Gabadaya wajen kowa ya sauke ajiyar zuciya harda maimartaba wanda yaketa maimaimata Alhamdulillah Aransa ashe afili yakeyi,gadanga ke kallonsa yana kunshe dariya.

Ummah mai babban daki ta dago Fuskar goggo tana fadin"Sai wata alfarma daya danike rokonki Suwaiba.?."Akunyace goggo tace"Mene ita..? Ummah na kallon Fuskar maimartaba tana Fadin"Ki Amince amaida aurenku da Abdulnaseer,In zamu koma Masarauta kibi mijinki ki koma tare dashi..."Gabadaya wajen aka Tsurama goggo ido,wacce kunya ta kamata kamar ta nutse,gimbiya Fasilatu kuwa kamar ta mutu saboda bakin ciki da kishi,Gimbiya Razeenah kuwa mikewa tayi ta isa ga goggo tana zauna tana riko hannunta take fadin"Kiyi hakuri karki ce A"a domin Maimartaba hankalinsa bazai taba kwanciya ba,balle har ya iya zaman Fada ba balle har ya gudanar da sha"anin mulki ba sai dake,don Allah ki amince amaida aurenku in zamu koma mutafi dake masarauta muzauna mu Rumgumi mijinmu don Allah..."Tafada tana kallon kwayan idon goggo,wacce saboda kunya kamar ta nutse,in tace bata son mijinta tayi karya,Shiko maimartaba idonsa na kan goggo gabansa na Faduwa kada Suwaiba tace"A'a..."


goggo ta dago kanta ta bude baki zata yi mgana kenan su gadanga dasu madina suka hada baki suka ce",Karki ce A"a goggo..."Suka Fada kamar zasu kuka,kawu yace"Toh kinji suma ya'yanki suna miki sha"awar komawa Rayuwar aure wacce zaki rabauta da ita har gobe kiyama.."Yafada cikin siyasa Ummah dake gefe ta dinga Kyaftama goggo ido😂wai ta yarda goggo na jin kunya ta dago tana kallon maimartaba wanda ya Langwabe kai,alamar ki yarda dani,Saurin kauda kai tayi tana Fadin"Na Amince..."Ai gabadaya wajen ya dau ihu,Ummah ko ta ware ta dafa hanci ta saki guda,suko Fadawa nan suka fara busa algaita suna Fadin"Angaisheki giwar sarki,Angaisheki Gimbiyar Sarki...Sarkinmu na godiya ga Amincewarki Allah yabar soyayyah..."Dariya akasa gabadaya Goggo ko kunya kamar ta nuste,shiko mai martaba dariya yake har hakoransa suka bayyana waje yana kara godema Allah,addu"a Gadanga yayi aka Rufe taro da addu"a kafin abude shashenshi su Maimartaba aka Saukesu anan,itako Ummah mai babban daki tana dakin goggo ita da jikokinta ana shan hira da dariya,Ita dasu jabir da Haisam suna Fadin suma fa dole su garzayo masarauta sunga iri😜😿Ummah mai babban daki tana Fadin ba wanda zata bamawa,Suko su Zafira suna makale da Azeema wanda suke tare dasu Anty madina,Ummah ko natare da goggo wacce gimbiya Razeenah ta Shige cikinsu ana hira,Shiko maimartaba yana shashen gadanga,suna hira shida Kawu da Mallam lawal wanda kawu yake bama maimartaba lbrin Abunda ya Faru bayan tafiyan shi da dalilin barowarsu zaria yazo ya saima goggo gida anan,Maimartaba ya jinjina al"amarin kuma nan take yace zasu zaria har anguwan da suka zauna,dagachan sai ya wuce Fadar maimartaba Sarkin Zazzau,Gimbiya Fasilatu kuwa tana dayan bedroom din Gadanga tana Fama da bakinciki,Bayi kuma mata,dakin dake tsaKar gida aka Saukesu Maza kuma akwai wani daki a shashen gadanga ammh yana da kofa ta waje shi aka bude musu,inna ramatu tanajin sadda goggo tace ta amince da Auren sarki ta sulale ta fita tana zufa kafin kace kwabo tabi anguwa ta yada lbrin mahaifin gadanga Ashe sarki ne,goggo kuma matar sarki zama amaida aurensu tabishi chan masarauta.

Shiko kawu ta waya yayi mgana da kwamishinar yada lbrai na jahar gombe yayi Narrating komai ya sanar dashi yace yana so,abuga lbrin akowacce jarida bayan afitar da sanarwa akowani kafafan yada lbrai,harta kaduna sai da yayi waya ya sanar kuma yace kafin gobe yake so lbrin ya karade duniya gabadaya Maimartaba yaji dadin haka sosai,saboda masu son Shegenta masa da,yau sun sani cewa Captain Aliyu ba Shege bane yanada cikakken Asali,kuma Asalin ma daya fi na kowa.


Anty madina da Anty mardiya da Azeema da su Zafira suka Fada kichen domin yin girki saboda yau dai Ahalin yayi albarka sai wanda ya gani.




_*Ina bukatar Addu"anku daga bakunanku masu albarka,ina cikin damuwa,tare da Fuskarta wata jarabawan Rayuwa,kumin Fatan Allah ya bani ikon cinye jarabawata,in kuma Alherina ne Allah ya Tabbatarmin dashi ya kauda duk wata Fitinar dazai Tunkari al"amarin*_🙏


    
*JANAFTY*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

        *Chapter 33..*

"Abinci mai Rai da lafiya suka girka,suka zuzzuba amanyan kololi,suka kai kowani Shashe,bayan sun Hada da lemuka da Ruwan gora,Su maimarta suna dai barayin gadanda suna cin nasu,ayayinda su gadanga suka hade Shida manyan Aminan nashi,Azeema ko dasu Zafira,sai su Anty mardiya da ita da Anty madina,goggo kuwa kunya takeji takasa ci,ummah mai babban daki ita kadai takecin nata,Ummah kuma ita da gimbiya Razeenah,Fasilatu kuwa babu wanda yabi ta kanta don Tunda ta Shiga ciki bata Fito ba,bayi da Fadawa ma ankai musu nasu barayinsu.

Ko kafin yammah tayi lbri ya Mamaye gari tako"ina mutane sai Shigowa suke suna ma goggo barka tare da Murna lokaci daya,wasu gulma ke kawosu,na ganin sarki da ake fadi,don wasu gani suke duk zence ne,aikuwa Maimartaba bai hana kowa ganinshi ba, yace abarsu suyi ta Shigowa yama Fi son hakan,da dare yayi maimartaba Sarkin gombe yaso Sarki Abdulnaseer yakoma masarauta,ammh yanunamai yafiso zamanshi anan,ko banza inda Suwaiba tayi rayuwa ne,ita da gudan jininsa,Shiko Aliyu yaso kebewa da Azeema ammh babu dama,yadda gidan yacika ne yasa sukayi musu sallama suka koma hotel din da suka kama ma Umar daki da safe suka kwana da Safe koda sukadawo suna cikin Shirinsu ne,don Maimartaba yace ayau din zasu kaduna sukuma biya zaria duk atare.

Inna Ramatu kunya da Nadama duk sun kamata,yau dai ga goggo data ke zagi tazama matar sarki,yau ga Aliyu datake yawon Fadin baida Asali Ashe dane,ga Sarki,da mallam lawal yadawo ya isketa tana kuka,ko kallo bata iaheshi ba,saima gyara kwanciya dayayi,yanaji tana kuka tana rokonsa wai ya roki Aliyu don Allah yasa baki Asaki Azeema wlh tayimai alqawarin bazata kara barinta ta aikata wani Abu makamancin Abunda ta aikata ba yana jinta yayi mata banza,saima Juyamata baya dayayi,Aransa yana Fadin bai yarda da Nadamar Ramatu ba haryanzu.

Koda su Aliyu suka dawo sun iske kowa ya Shirya, Nan suka iske Baba Ade tazo, yima goggo barka da kuma taya Aliyu Farincikin Saduwa da mahaifinsa,Hatta da goggo ba"a barta abaya ba ta Shirya tsab da ita,akwatun kayansu aka saka amota ita Azeema tunda zasu dan kwana biyu inji kawu,Su Aliyu ne zasu yi Tafiyar mota zuwa kaduna,su kuma sauran Jirgin maimartaba zasu bi,Gabadaya gidan aka Fito domin Tafiya su Aliyu tuni sun mika hanya Su maimartaba ne tsaye suna bankawana da su mallam lawal,sai ga inna Ramatu ta Fito daga gida da gudu ta zube gaban maimartaba tana kuka,mallam lawal kuwa yana ganinta yafara hararaart maimartaba ne ke tambayanta Meyake Faruwa tana kuka tana Fadamai kamun da Aliyu ya sanya akama Azeeza,Jinjina kai maimarta yayi kafin yace"Ash Abu baiyi kyau ba tashi tashi insha Allahu zan shashi yasa asake yau din nan.."Yake Fada yana kallon Kawu kafin yace"Bala don Allah kiramin Aliyu.."Kawu baiyi gaddama ba ya ciro waya ya kira Aliyu wanda ke gefen Jabir yana driving,Umar da Haisam suna bayan mota,da Azama ya daga kiran kawu yana Fadin"Hello kawu.."Bai yi mgana ba ya mikama Maimartaba wanda yace"Aliyu..."Yafada cikin dattako da mulki,saurin gyara zama yayi yana Fadin"Na"am Abbah,kun taho ne..? Bai bashi amsa ba yace"Yarinyar nan daka sa akama kanwar matarka kakira waya yanzu ka saka asaketa Umarni na baka ba Shawara.."gyada kai Aliyu yayi kafin yace"Angama Ranka ya dade.."Yana fada yana katse kiran,nan take yakira DSP MALEEK KABIR KUMO,sukayi mgana kafin ya bada Umarnin sakin Azeeza,nan sukayi mganar cewa bayan ya dawo yazo nan headquater su,akwai File din da zai cike nan sukayi sallama,jabir ne kawai yasan Abunda Ke Faruwa baiyi mgana ba,ko banza ai Ta horu Shegiyan.

Daganan Fadar maimartaba Sarkin gombe Suka wuce sai da sukayi sallama kafin su isa Airport,dama jirginsu na nan,Suka Shiga suka Lula sararin samaniya,Akaduna suka yada zango Tunkafin su iso mai girma gwanna Jahar kaduna * MALLAM NASIRU AHMED YAR RUFA'I yazo da kanshi ya ya tarbeshi Shida tawaganshi,Sai da sukaje gidan gwannati kafin su wuce gidan kawu,wanda ya kasance Aljannar Duniya nan kowa ya baje,don mamaken gida ne,mai Shashe har guda uku,kowanne ya gaji da haduwa,sai lokacin su Aliyu suka kariso suma,kafin isowasu Aliyu ya amsa waya tafi dari na yan"uwa da abokan Arzuka suna tambayanshi Shin Abunda suka gani gaskiya ne,da eh kadai yake amsawa,sai Barka mutane kemai da tayashi murna,daya gajima kashe wayaryi,Ko!ina na garin gombe jaridu suna ta yawo banda gidajen talabijin din da"akayita watsawa ana nuna Hoton Aliyun dana Maimartaba Sarki Abdulnaseer,Wanda jama"a dadama sunyi matukar mamaki,ciki harda da Ni"ima da iyayanta,mami tana hawaye tana kallon Cp Ahmed Sidi na Iya,wanda yayi Tsuru duk kunya ta kamasa,itako Ni"ima daki tayi dagudu Sauri tana kokarin kiran Muneera dataga ta kirata.

Kunya duk takama Kwamishana,sai zare ido yake,Mirmishi Mami tayi tana Fadin"Ka gani ko? wannan Ranar nake jiyemaka yallabai,kabiyema Sharrin shedan da hudubar dan"uwanka gashi yau kaine,akunya yanzu duk amtsayin kaje kayi gaba da gaba da Sarki,wlh ko haka Allah yabarmu munga sakayyah,Tunda diyar tamu nan harynzu agabanmu kuma tace inba Aliyu bata ba Aure har Abada.."Tana gama Fadin haka tatashi Tafice ta barshi nan yana zufa,lalle al"amarin Allah Kenan,ashe yaron ma yawuce duk Tunaninsu ashe shi din Da ne ga Sarki yanzu haka Shidin yarima ne,Lalle ya tafka kuskure babba ma kuwa.
  

***************

Azeema ce Tunda yammah tayi take kwance Zuciyarta da gangar jikinta babu wanda suke bukata sai Mijinta gashi kuma gidan yana cike da jama"a,ita yanzu ya zatayi kwance take tarasa mafita,Duk wanda yazo ya ganta kwance sai tace batajin dadi ne,Rasa mafita tayi shiyasa ta aika hibba data aro mata wayar Anty madina,tunda ita tata ta barta Akaduna Tun Sanda Abun nan ya faru,ana kawo mata wayar ta Shige tiolet ta kulle ta lalubo lambar Captain takira wanda suke chan Wani Shashe shida su Jabir yanaganin kiran ya daga ammh kuma sai yaji Shuru anki mgana,sake duba mai kiran yayi kai Tsaye ya Furta.."Pretty..."Yafada yana Tashi saboda su Jabir da suka Tsuramai ido,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shagwabe Fuska tace"Bawani pretty,Bayan Tun ranar baka kara nemana ba.."Kanshi yashafa,jin yadda ta kashemai jiki,yace"Ba haka bane pretty kema kinsan dalili aie,ammh koda yaushe kina Raina abar Farincikina.."Mirmishi ta saki tana Fadin"Da gaske..."Tafada tana dariya basar da tambayan yayi yana Fadin"Meke damunki ne,? kowani Abu kike bukatane pretty..? yafada yana Danne dariyansa,Hararan wayan tayi kafin tace"Ni bana bukatar komai..Kai..Kai ne nake son gani.."Tafada tana Rufe fuska,yar dariya yayi yana fadin"Yanzu kuwa zanzo Tunda Service yatashi yanzu an neme ni aie..."Yafada yana rike dariyansa jin ya ganota yasa tayi

Please Login or Register in order to submit comment