Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Captain,in don kyanshi ne akwai alot mazan da suke da kyau kuma suke hauka akanta buh ammh ita ta nacema Namiji kwara daya sai wahalar da ita yakeyi.

 

Goggo na cikin Daki ta hakimce Afalonta tana kallon Arewa Aminu shariff Momo,na gabatar da Shirin Sharhim Fina Finan mu,gurguru ne cikin wani dan Roba tana afawa abaki rabin hankalinta na wajen kallo,Taji ana ta sallama Daga dakin ta amsa tana mikewa,zanin leshin dake jikinta ta gyara kafin ta Daga labulen dakin tana Fadin"Wa"alaikas salam..."Tafada suna hada ido hudu da Ni"ima.

   Kallon Sama da kasa Goggo ke jifan Ni"ima dashi kafin tace"Daga ina bayin Allah...? Muneera dake bayan Ni"ima ta bayyana Fuskarta dauke da wannan Gilashin tace"Muna neman mahaifiyar captain Aliyu ne..? karkace kai goggo tayi tana fadin"Ayyah Gani,Ina Fatan lafiya ko? ta Fada tana kallon Ni'ima wacce kanta ke kasa,Mirmishi Muneera tayi kafin tace"Eh toh lafiya ba lafiya kawata ce tazo Rokonki wata alfarma.."Sakin labulen Goggo tayi tana fadin"Ku Shigo ku zauna,Allah yasa zan iyamata alfarma datazo roko.."Haka kurum goggo Ranta yabata Ni"ima ce,Duk da bata taba ko ganinta ba.

Suko ganin Farko Da sukayima goggo suka ga kamarta da captain duk da A fizgene yake kama da ita,Falon suka Shigo Kai tsaye Ni"ima tanemi waje ta zauna,itako Muneera tana ta karema falon kallo tana yatsina baki,Kafin ta nemi waje ta zauna,Kichen goggo ta Shiga Ta dauko musu Ruwa kafin tazo ta zauna tana fadin"ga Ruwa kusha.."Dan mirmishi Ni"ima tayi tana fadin"mungode goggo,munsha Ruwa.."Tafada tana sadda kanta kasa.

   Da ido Ni"ima tayi ta ma Muneera alamar tayi mgana,gyara zama tayi kafin tace"Sunana Muneera,ga Ni"ima nan Munzo rokonki alfarma ne Akan Don Allah kibama Captain hakuri yadawo ya Aureta wlh ba laifinta bane laifin Mahaifinta ne,kuma Shi yayi Nadama wannan karon bazai kara gaddama ba,Don Allah ki taimaketa Tunda Abun nan yafaru bata kara lafiya.."Tafada tana kallon kwayan idon goggo.


      Gyara zama goggo tayi tana fadin"Allah Sarki to ai ni bani da keda ikon zaban ma Gadanga Abunda yadace dashi ba,Da farko Shiya zaboki da kankishi don yana ganin kin dace da Ra"ayinshi,daga karshen mahaifinki ya hanasa ke,saboda wani dalili nasaa  mara tushe,toh barikiji na gayamiki koda gadanga bai yi Aure ba, ni mahaifiyarsa bazan taba bashi goyon bayan ya Aure ki ba,Saboda na nuna muku babu wanda aka haifa baida Uba,yanzu ku tashi kikoma wajen mahaifinki domin ni babu Abunda zanyi iya miki,Tunda haryanzu gadangar bai Kawo Asalin Uban nashi ba,ba Shi mahaifinki yace sai yakawo zai bashi ke ba.?.,"Tafada hankalinta kwance.

Tunda goggo Tafara mgana Idanuwan Ni"ima suka tara kwallah,tana gama mganar hawaye suka zubomata Mikewa goggo tayi tana fadin"Ngd ku gaida gida..."Daga haka tashige bedroom ranta bace,Muneera dake zaune ta mike ta isa ga Ni"ima tana rikota lokaci daya tana fadin"Kinji kingani ko? dama narigaya dana Fadamiki zamu wahalar da kanmu oya tashi mutafi..."Mikewa Ni'ima tayi tana kuka kamar ta Shide Hannunta muneera ta rike suka Fito daga dakin tana Fadin"Kinga ki cire Captain Aranki don ni banga alamun Nasara ba,Yadda yake baida Mutumci haka uwarsa take,gado yayi.."Tafada suna Ficewa daga gidan,Suna zuwa kofar gidan sukaci karo Da Azeeza jingine jikin motarsu tana kallonsu tana mirmishi,Cak suka  tsaya suna binta da kallon mamaki kusa dasu ta karisa tana fadin

  "Dama nasan bazakuyi Nasara ba,Don goggo bazata taba Sauraranku ba..."Kallon mamaki suka bita dashi kafin Ni"ima tace"Wacece ke? Mirmishin kasaita Azeeza tayi kafin tace"Sanin wacece ni bazai miki amfani ba,Abun da zaifi miki amfani Shine yadda zaki mallaki Abun Kaunarki Captain.."Zaro ido suka atare suna mata wani kallo ganin haka yasa ta juya tana fadin"Au naga baki Shirya ba,in kin Shirya kya nemeni,Sunana Azeeza..."Tana fadin Haka tafara Tafiya da hanzari Ni"ima tataka ta rikota tana fadin"Konawa kike bukata zan biyaki matukar zan mallaki Captain,.."Waigowa Azeeza tayi tana dariya kafin ta harde hannunuwanta akirji tana Fadin"Bada kudi nake so ki biyani ba,Zamu Taru ne mu Taimaki juna..."Da Hanzari Muneera tace"Kinga Baiwar go to d point,meke tafe dake."Mele baki Azeeza tayi kafin Tace" _KI RABASHI DA MATARSHI AZEEMA NI KUMA NAYI MIKI ALQAWARIN MALLAKANSHI AMATSAYIN MIJINKI.._"

   
Wani banzan kallo Muneera tayimata kafin tace"Toh mukuma meye hdinmu da matarsa,kinga Sweethrt muje inaga wannan yarinyar Mahaukaciyace.."kin tafiya Ni"ima tayi ta tsaya tana kallon Azeeza kur da ido kafin tace" Indai kin tabbata zaki Rike alqawari nikuma nayi miki alqawarin Farraqu tsakaninsa da matarsa.."Mirmishi Azeeza tayi ganin taci Nasara kawai sai ta juya tana fadin" Da Zarar hakan ya tabbata ina miki albishir da Kin gama mallakan Captain..."Tana gama Fadin haka tafara tafiya zuciyarta cike da Farinciki cin Nasara Allah ne yakawomata Ni'ima wacce zatayi Amfani da ita wajen cinma burinta daga karshe in tayi Nasaran Raba Aliyu da Azeema,ita kuma sai taji da Sauran Aikin domin na Ni"ima mai Sauki ne,wani lungu Azeema tabi kamar irin zata gidansu din,don bataso su gane gidansu.

Har Suka Shiga mota suka bar anguwan,Muneera nayima Ni"ima Fadar Sauraran Azeeza da tayi ko kallonta Ni"ima batayi ba ta Zurfafa Tunani lokaci daya takalli Muneera tana Fadin" *Aikin  CONOLE SULAIMAN ya tashi Sweetheart...'Wani kallon Muneera ta mata tana fadin"Bangane aikin Sulaiman ya tashi ba,me kike shirin aikatawa.."Bata kalleta ba tace" Shine zai Raba Tsakanin Captain dina da matarsa,kinsan yana gaba da Captain awajen aiki,so Shiga bariki bazai ma wanda zamu bama aikinmu wahala ba.."Kuri Muneera tamata ido,itama tana kallonta kafin su kwashe da dariya Atare Muneera tace"Indai ko hakane Rabuwa zasuyi har Abada balle kinsan Captain dinki da zuciya may be ma kila ya gangara da ita lahira.."Ni'ima ta amshe da Fadin"Ko kuma ta yanki Tikitin zama na Din din A asibitin kashi na kano ba.."Dariya Suka kara sakawa harda Tafawaa kafin su cigaba da tattaunawa yadda Abun zai kammallah cikin lokaci.


    Am Srry For d Typing Errors.

 
*Intelligent writers Asso.*
*Janafty....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

         *Chapter...23*

*BAYAN WATA DAYA*

   ""Acikin wata daya da Tarewar Azeema Fadar irin cigaba tare da zaman lafiya,dakuma wata soyayyah dasuke nuna ma juna bata baki ne,Tsayawa Lura da yadda suke kaffa kaffa da juna sai ka dauka sun Shekara goma ne,suna Soyayyar,uwa uba ga wata shakuwa daya Shiga tsakaninsu,Azeema ta yarda takamu da Son yaya captain kamar yadda Shima yakamu da Sonta duk da bai Furtaba tana gani a aikace.

  Taje gidajensu Anty madina da Anty mardiya sau daya,sai gidan Kawu dasukaje Sau biyu,dukkansu sun samu kwanciyar Hankali sunyi kiba sunyi kyau kamar basu ba,Kowannensu Kokariin Farantama dan"uwansa rai yakeyi kowa bayason ganin bacin ran Dan"uwansa baza"ace basu taba samun sabani ba,A'a Suna samu buh baya wani Tasiri suke bama juna hakuri domin dukkansu babu wanda zai iya Rashin dan"uwansa,Tuni Azeema ta Manta  da wata Aba Azeeza da inna Ramatu mahaifinta dai take kira taji yaya lafiyarsa sai goggo wanda bata iya kwana bata kirata ba,Tarigaya tazama wata ginshiki agareta.

Lokacin Jarabawansu ya kusa Aliyu sukayi mgana da goggo yace in lokacin yayi zaizo da kanshi yayimata Rigistration Allah barshi in lokacin Yin jarabawan yayi sai ya maidota ta Ta rubuta ahaka suka rabu,wanda ko Azeemar batasan kwanan zencen ba.

_________________

  Conole Sulaiman yana zaune cikin kayatattacen Falonshi na cikin Barikin,yana hutawa gefe daya kuma Sigarice Ahannunsa yana ta zuka yana Fidda hayaki,daga ganin yadda yake sarrafa zakasan ya kware, wayarsa dake gefensa tadau Tsuwa yana dagota ya zaro ido yana mamakin mai kiran da rawan jiki ya daga kiran yana fadin

  "Allah Taimaki Hajiya Muneera yar Mutan gombawa,yau kuma an Tuna dani ne, bayan tsawon lokaci An samu akwandon shara.."Wata dariyar kissa muneera tayi kafin tace"Har na isa?ka manta hausawa na cewa Da tsohuwar zuma ake mgaani,"Dariya ya saka yana Fadin"Hakane kuma ta wajena,Allah yasa wannan kiran an min ne,domin kashemin kishirruwan ki ko? Dariya ta sheke dashi kafin tace"Sha kuruminka Gani A main gate dinku an hanani Shigowa.."Yana jin haka ya mike yana washe baki yace"Karki wani damu bari nayi musu waya.."Yafada yana katse wayan,Chan main gate din ya kira yace Su barta ta Shigo bakuwarsa ne nan da nan ko suka wangale mata get,ta sulala ciki,haka sauran get din suma Tuni Umarni ya ishesu,Tana Shiga ciki dama Tuni tasan Apartment din na Conole Sulaiman,suna chan gaba Sai ansha tafiya akwai dan tazara tsakanin nasu dana su Captain Aliyu,Kuma kowanni gida yana da nombarsa da sunan Sojan dake zaune agidan,sai da tayi gaba kadan da Apartment din Aliyu kafin naga ta tsaya baya ta juya inda naji ta Furta.."Come out..."Tafada kai tsaye.

  Bayan motan naga Wani Saurayi ya Fito yana kara gyara wani bakin kyallen  dake Fuskarsa wanda yake sanye da Riga da wando black and white,Kallonsa tayi kafin tayi pointing din gidan Aliyu tana fadin"Ga gidan chan,Kayi maza kuma kayi komai da lura,and don't forget kada kabari akamaka ko aga Fuskarka saboda nan bariki ne,yana da tsaro sasai so u better Carefully kaji ko"gyada mata kai yayi yana fadin"Karki wani damu aikina ne fa,Glass din Fuskarta ta gyara kafin tace"Ok lokacinka yafara daga yanzu.."Tana fadar haka ya bude murfin mota ya Fito yana kalle kalle,lekowa tayi tana fadin"Daka tabbatar da ya ganka,kayi hanzarin Fitowa kabi nan hanyar Da zanbi zaka ga nayi parking din motata,zan barmaka abude sai ka bude ka shiga kana Fitowa kayi min text yadda zan Fito da hanzari, kayi kamar yadda muka Shigo kagane..? kai ya gyada mata kafin ta kada kai ta Figi motar da gudu,shiko sai da yadan tsaya yana kallon gefe ganin wasu sojoji zasu Wuce sai da suka wuce ya juya yaga Babu mai kallanshi kana ya Tunkari gidan Aliyu,Yana zuwa yaga Sunanshi Manne jikin kofar Wajen,ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Fito da key daga aljihunsa wanda aka kera da karfe,ya saka yana juyashi sai ga kofa ya bude hamdala yayi kafin ya waiga yaga bamai kallonsa salaf salaf,ya Shigo falon ya maida kofar yadan Tura yadda bazata Rufe ba.

Falon babu kowa yana leke baiji motsin kowa ba,dayan bedroom din ya fara lekawa,sai yaji ga babu kowa,dayan yakoma ya bude ahankali ya leka sai yaga kaya akan gadon dakin,Shigowa yayi yana waige kamar barawo,Motsin Ruwa yaji a Tiolet,sai yakara kunnenshi yaji karan Saukan Ruwa,Tsalle yayi yana murnan jin dadi Rigarsa ya cire ya rage dagashi sai vest da dogon wondo,direct yayi Sufa ya haye gadon,harda Daukan rigar dake kan gadon yana Shinshina.

  Itako Muneera direct kofar gidan Conole Sulaiman ta faka motarta tana Fitowa daga motan sai gashi ya Fito dakanshi ya tarbeta zuwa cikin gidanshi,suna zuwa falon ya Rumgumeta yana Shinshinar wuyanta lokaci daya yana Fadin" Kai gaskiya nayi kewar wannan Lallausan jikin naki.."Yake tayi tana Rikoshi take fadin"Nima haka Sojan Fama"Tafada tana jansa kan kujera suka fada,yana Rumgume da ita,kamar wani zai kwaceta,itako gabadaya hankalinta na kan wayarta tana Jiran sakon ya Shigo mata.

Captain Aliyu shida Jabir suka jero suna tattaunawa kan Sojojin hadin gwiwan da Aka gayyato wanda akace za"a saukesu cikin wannan barikin,Toh alhakin Kula da komai yana Hannunsa,suna tattauna yadda Abubuwan zasu kasance,Suka karisa gidajensu,Nan suka rabu Jabir ya nufi gidanshi shima ya nufi nashi,yana zuwa kokarin ciro key yake ya bude kofar,ammh yana Tabata ta bude,cike da mamaki ya Shiga falon,yana mamakin samun kofar abude,jin Shuru Falon babu kowa yasa ya nufi bedroom yana fadin" pretty kina ina ne,? am back..?

jin Shuru yasa ya Nufi bedroom kai tsaye yana kiran Sunanta,Itama kuma Azeema tana kokarin Fitowa daga Tiolet din taji yaya captain na kiranta,tana gyara zaman karamin Towel din dake jikinta ta fada da karfi"Am here Yaya captain.."Tafada tana Rufe baki Tuna abayi take tana bude kofar Tiolet din yayi dai dai da bude kofar bedroom din da Aliyu yayi,ita Fuskarta na Kallon kofar Shigowa ne,tana sakarma Gadanga mirmishi shiko yana Shigowa yayi 4eyes da wani gardi kwance kan gadonsu na Sunnah ba riga,ga rigar da yafita yabar Azeema dashi ajikinsa yana shinshinawa,gabadaya Aliyu jinin jikinsa ne yaji ya daskare,saboda tsoro da dimautuwa,Hannu yadaga yana nuna wajen,bakinsa na rawa Jijiyoyinsa kansa Sun mike saboda bacin rai.

Ganin haka yasa Azeema maida kallonta inda yake Nunawa Abunda tagani ne yakusa sawa towel dake jikinta ya subuce ya fadi,baya taja tadafe hannu akirji Tana zaro ido lokaci daya take fadin"innalillahi wa'inna Alaihirraju'un..."Take Fada jikinta narawa,shiko ganin yadda sukayi yasa ya kalli Azeema yana fadin"Bbby har kin Fito wanka,Toh wlh kizo na karayi don kinsan bai isheni ba.."Yafada yana Rumgume Filo cike da makirci ganin yadda tayi ne tana Rawan jiki,yasa yakalli barayin inda Aliyu yake,da hanzari ya mike yana raruman rigansa yana bayyana tashin hankalinsa,Ammh sai ya kalli Azeema yace"Baby ya haka?Kafin na yarda zanzo sai fa dakikacemin mijin ki bayanan,ammh yanzu ya na ganshi.."Haurowa gadon yayi zai Fita yana bin bango,sai da yazo gab kana Aliyu yayi kukan kura ya damkoshi ya durkusheshi akasa baiyi wata wata ba yafara bashi kulli Afuska,Jikinsa na rawa saboda tashin hankali,kokarin Cire masks din Fuskarsa yake,ammh yaki bari,ammh saboda yafisa karfi,sai da yasamu nasaran ciremai Fuskarsa ya bayyana shakesa Aliyu yayi yana fadin"I will kill u..." yake fada yana zaro ido,ganin yana neman kasheshine,yasanya kafarshi ya tokaraimai gaba da karfi,wanda ya saka dole Aliyu ya sakeshi ya rike gabanshi yana Runtse ido,shi yabashi damar tashi ya Fita da gudu,koda Aliyu yayi yunkurin binsa sai yakasa da hanzari ya Fito da waya yakira Jabir,jabir na dauka muryansa A haukace ya furta.."Jabir ka bada Umarnin Arufe kofofin barikin nan Right now.."gaban Jabir ya fadi da hanzari yace"Aliyu lafiya naji muryanka haka.?."Tsawa ya dakamai yana fadin"Kayi Abunda nace mallam.."yana gama Fadar haka ya kashe yana kokarin mikewa.

Itako Azeema wajen ta durkushe tana gunjin kuka hannunta bisa kanta,tana kiran sunan Allah,Kukantane yasa Aliyu ya dago yana kallonta da jajayen idanunsa,Yana jin kamar ya tashi yayimata dukan mutuwa ammh bazai iya ba,komawa yayi ya zauna yana cije baki kafin yace" Azeeeemmmmma...."Da karfi sai da ta Razana baya taja tana Rufe baki saboda kuka" kai ya sadda yana fadin"Dame na rageki da har zaki kawomin kato..?Girgizamai kai takeyi tana so tayi mgana ammh kuka yaci karfinta,Rarrafowa tafarayi zuwa gabanshi tana wani irin kuka tana girgiza kai,ganin haka yasa ya yunkura ya mike ya fice da hanzari yana dafe maransa,Bajewa anan Azeema tayi tana fadin" Hasbunallahu wani'imal wakil..."

  Koda Jabir ya Fito Tuni har gayen ya mike inda Muneera tabi Gudu kadan yayi sai gashi wajen motarta da hanzari ya bude ya Shiga,yana Shiga ya Fito da wayarsa ya turama Muneera Text da cewa" _Ki yi hanzari ki Fito aiki ya kammallah sai dai an kusa samun mtsala.._ Muneera dake Ta ribanta Sulaiman tana ganin Shigowar sako ta mike da hanzari tana kara wayan Akunne take fadin"hello mommy...Innalillahi ganin nan zuwa.."Tafada kafin ta kalli Sulaiman wanda ke kwance kan kujera yana kallonta tace"Zan Tafi yanzu Sistern mamata ta kirani wai Anyi Addmitting din mijinta a asibiti,kuma in banzo ba yanzu zata zargi wani Abu,Ammh dont worry zan dawo ko kazo mu hadu.."Tana gama fadar haka bata jira cewarsa ba ta fice da hanzari da gudu ta karisa wajen motar ta shiga tana kokarin bata Wuta ne take fadin"Garin yaya aka samu mtsala..? yana daga baya yace"karki damu mtsalan Fuskatace daya gani,kuma inaga don wannan ba wani damu.."zagi Muneera ta yanko tana fadin"are u mad,kasan waye Aliyu kuwa,he is very smart wlh,fuskarska kadai ta isheshi Shaida.."Take fada tana Figan Motar Jabir daya Fito daga gidansa dahanzari yana kokarin kiran waya motar tazo ta wucesa da gudu har sai da ya bita da kallo,kokafin yayi waya zuwa masu kula da Shige da Fice na barikin Tuni Muneera ta fice daga Barrak din Hankalinta atashe tana ta zazzagamai Masifa acikin mota Ammh hankalinta ya kwanta Tunda dai Aliyu ya ganshi dama su bukatansu kenan.


*Am Srry For d late update,wlh Jiya nayi busy ne*


*,Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_*Daukaka wata abace,Ta dan lokaci in ta Aureka Duniya zata sanka sosai kayi more porpular,and One Time u bcome Cele by Force ohoo😹buh duk lokacin data sakeka kashima yafika Daraja,fans ma zasu daina zencen buk dinka balle akai ga zencenka kazama mar amfani garesu,Shiyasa ka/ki yi Fatan daukaka ko Shahara ita din kamar misalin Duniyace Rigar aroce,in tashiga wanchan gobe zata barkane ta shiga wata,...Shiyasa kazama mai aiki da Hankalinka,kayi komai don Allah sai gaka yama ka sakayyah da kyakyawan sakamako wanda bakayi Tsammani ba✌🤘🙏,...Assalamu Alaikum Janafy Fans*_


          *Chapter 24*

    ""Adaddafe Aliyu ya Fito yana Tafe yana rike maransa,Da Jabir ya cikaro akofar apartment dinshi,yana ganinshi ya isa gareshi yana fadin"Wai captain meyake Faruwa ne? lafiya kake dukewa ko baka da lafiya ne? ina ita Azeemar? yafada yana leka kofar Shiga Falon.

  Ture hannunsa,Aliyu yana fadin"Kasa Ayi bincike acikin barikin nan,Kada abari wani ya Shigo kuma kada wani yafita,da anga wata bakuwar Fuska Juz ku sanar dani.."Yafada yana cije baki saboda azaba Hannunsa Jabir ya riko yana fadin"Look Aliyu nifa ba iya abokinka bane don Allah kafadamin meke Faruwa? Wani Mutum ne ya Shigo,dan Fashi ne,ko ko dai aikoshi akayi ne? Aliyu ya dago kansa idanunsa sunyi jawur,baya Jabir yaja ganin yanayin Aliyun baicemai komai ba ya koma cikin gida,ya Rufo kofar,nan ya sulale yana Rike kansa da hannu daya,Saboda yadda yake saramai,So yake yayi kuka,ammh yakasa zuwa Tunda yazo duniya bayan Abunda ya Faru Ranar Daurin Aurenshi da Ni"ima,bai taba Shiga tashin hankali irin na yau ba,dame ya rage Azeema?wata zuciyar tacemai ammh taya zaka yarda Azeema zata gayyato wani kato,karka manta kai kasameta a burduwa fa? toh ammh in ba hakabane babu wanda keda alhakin Shigo da wani cikin bariki nan sai da wanda yasan wajen? Toh ammh ai ita Azeema batasan ko"ina a barikin nan ba,Toh waye ya Shigo dashi yanunamai gidana? wata zuciyartace waye kuwa banda Azeema babu wanda zai gayyatoshi sama da ita.

Kansa ya Dora bisa Tafin hannunsa yana Kiran Sunan Allah,Yana zaune wajen yasamu kiran Jabir kan yazo Security offoce yanzu,da hanzari ya mike Fuskarsa tayi ja,saboda Bacin rai,koda yaje chan Nan jabir ke mai bayanin bakin Fuskar da"aka samu duk ziyara suka kawoma danginsu nan ya Shiga nunamai mutanen da suka Shigo barikin aranar,ammh baiga Fuskar wanda yake nema ba,da hannu yayima Jabir alamu da a sallamesu kuma abude get kowa ya fita,Jabir ya Shiga damuwa ganin Halin da Aliyu ke ciki,ammh bai bashi Fuskar sanin meke Faruwa ba,don Aliyu yace bazai iya kallon idon Jabir yacemai Azeema yakama da wani acikin gidansa ba,Shiyasa yakasa mai mgana sai dai kawai ya kalleshi yana kada kai.

  Azeema kuwa tunda tabaje akasa take kuka kamar Ranta zai Fita data Runtse ido Mutumin take gani da maganganun dayayimata,da sanda Aliyu ya dakamata tsawa,dataTuna haka sai ta toshe kunni tana sakin kuka,Tana nan kwance tana kuka har sai da muryanta ta Shide dakyar ta Tatashi ta Koma tiolet tayi alwala tazo tayi sallar la"asar tanayi tana kuka,Tana idarwa taji Shigowar yaya captain da hanzari ta mike ta Fito,tsakiyar Falon ta ganshi zaune ya dafe kai,Tunda daga kofar bedroom dinta ta durkushe tana kuka,Matsowa take idanuwanta na tsiyayar hawaye yana jin gunjin kukanta ammh yakasa dagowa ya kalleta saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa,Zumbur ya mike yana juyamata baya da wani irin karfi da Tsawa yace,"Kada ki kuskura kizo kusa dani..Azeema kin cuceni kin ha"inceni,kin kuma cucu aurenki da Yardan da mahaifinki da mahaifiyata sukayimiki,Dame na rage?,meye bana miki,?na baki abinci na baki lokacina nabaki kulawata kai hatta da soyayyata na baki Azeema why"!Why Azeema meyasa kika zabi ki cutar da zuciyata da Abunda zai kasheni har lahira.ehe..Why..? yafada muryansa Tafara rawa.

Juyowa yayi yana kallonta,Yake fadin"Sai dai, kuma bani kadai kika cuta ba Azeema harda kanki domin bazan cigaba da zama dake ba,domin zamanki tare dani watarana zan iya shakeki ki mutu saboda bakinciki gwara na tattaraki na maidama mahaifinki ke,ngda da sakayyah Azeema ngd da yardan dana baki kika cutar da zuciyata Allah nagani bantaba zina ba,kuma...Kuma Ni banta sha'awarta ba,Sai dai in shegentakan da"ake kirana dashi,shine yake bibiyar Rayuwata.."Yafada yana Runtse ido,Dakyar da sodin goshi sililin hawaye ya zubomai guda daya,Azeema da gabadaya hijabinta ya jike da hawaye ta rarrafa da gudu zuwa kafan yaya Captain takama da hannun bibbiyu tana fadin"A"a..A"a kada kayi haka..Wlh tallahi banda masaniya Akan komai,wlh ban..Ban san komai ba don Allah ka tsaya ka bincika don Darajan ma'aiki.."Take fada tana wani Gunjin kuka.

Tsaye yayi yana jin yadda zuciyarsa na Tafasa,Kafa yasa ya shureta tatafi ta bugu da kujera,center table din dake gabansa ya Saka kafa ya buga sai da ya rabe gida biyu,kallonta yayi yana fadin"Saboda haka ki tashi yanzu ki hada duka kayanki,duka nace banison ganin ko Silin gashinki agidan nan,Gobe zan maidake gombe domin Zuciyata bata da karfin gwiwan Sake zama dake.."Daga haka ya shuru kafa yafada daya bedroom din yana huci.

Hannu Azeema ta dora akai tana kuka tana fadin"Innlillahi...Na shiga uku,waye yayimin wannan kazafin,wlh kowaye bazan taba yafemai ba Har Duniya ta nade.."Take Fada tana kuka,kafin tatashi da gudu tashige daki,tafada bisa gado tana ihu tana buga kanta jikin katifa babu mai lallashinta,Shiko Aliyu tunda ya Shiga bedroom din yafada Tiolet ya sakarma kanshi Shower yana sakin ajiyar zuciya.

________________

   Dai dai wajen anguwan Rimi bus stop ta saukeshi Ta damkamai wani Abu abakar leda tana Fadin"Mungode,in wani aikin yataso zamu nemeka,and don't forget ka lura Sosai inajin tsoron ganin Fuskarka dayayi.."Mirmishi yayi yana rike ledan dakyau yace"Bafa ki da mtsala Hajiya aikina ne nasaba.."Kada kai kawai tayi kafin taja motarta tayi cikin Anguwan Rimi.

  Wani Mamaken gida naga tazuba hon megadi yazo ya budemata get ta Sulala ciki,aparking space ta faka motar kafin ta Fito ta nufi cikin gidan,tana Tafe tana cilla key din motar sama cike da Nishadi,ababban Falom gidan ta cikaro da Kanwar mom din nata ita da yaranta,da gudu suka tashi suna mata oyoyo,itama ta rumgumesu tana dariya,dakyar sula barta ta kariso Falon,tana fadin"Mommy kinga Ya"yana zasu kada ni ko? wacce aka kira da mommy na kallah yar matashiyace,wacce bazata wuce Shekara 40 ba,Kallonta tayi kafin tace"Wai ina kika je ne muneera..? Juya idonta tayi kafin tace"Anguwan Sarki naje,gidan wata Friend dina Seeyama,wacce mukayi Sch tare da ita.."Gyada kai kawai matar tayi kafin ta juya ta Nufi hanyar kichen tana fadin"Allah yasa da gaske ne..."Rantsuwar karya Muneera tafara jeromata da hanzari ta dakatar da ita tana fadin"Nifa ba Rantsuwa na tambayeki ba,kawai cewa nayi Allah sa da gaske ne.."Da kallo muneera ta bita tana Tura baki,kafin taja jakarta ta haura sama,tana kunkuni.

Tana Shiga dakin,wayarta ta dauki kara,sai da tazauna bakin gadon ne,ta cirota cikin jaka ta duba ganin mai kiran ne yasa tayi mirmishi ta daga tana Fadin"Sweetheart komai ya tafi kan Tsari harma na sallame gayen.."Dariyan jin dadi Ni"ima tayi kafin tace"Job weldon Sweetheart..Yanzu yaushe zaki dawo mukoma wajen yarinyar...? ajiyar zuciya Muneera ta sauke tana fadin"Gobe insha Allahu,buh wani hanzari ba gudu ba,ita yarinya bafa musan inda zamu sameta ba,kuma bazamu yi Saurin zuwa mujira ko nan da Sati dayane,muga shin aikinmu yayi duk da ina da tabbacin ko ta kwana Akaduna yau,toh ina tabbatar miki gobe a gidan Ubanta zata kwana..."Dariya Ni"ima tayi kafin tace"Kema mganarki Abar dubawa ce,Shikenan sai kin dawon,mganar yarinyar kuma ai bamu da mtsala tafadamama Sunanta,na tabbata in anan area take zamu sameta.."Muneera tace"Ok sai munyi waya.."Daga haka suka yanke kiran zuciyarsu cike da samun Nasara.


   *******************

   ""Koda garin Allah ya waye yadda Aliyu yaga Rana haka yaga dare,Ballatana Azeema data kwana kuka durkushe bisa sujjadarta tana kaima Allah kukanta,ada bata taba Tsorata da al"amarin Azeeza ba koda Abunda yafaru abaya,bata tsorata da Abun ba,sai da Abunda yafaru jiya ya Faru,nan ta yarda duk wanda yayi mata wannan sharhi ta tabbata baya kaunarta,kuma bazai taba Sonta,ba ta yarda ta amince bata da wata mafita domin Anrigaya da ansha Shiryamata Ta yarda bata da yadda zata Fidda kanta.

Kokafin Gare ya waye Fuskarta ta kumbura saboda kuka,idanuwanta kuwa sunchanza kala saboda kuka da Tashin hankali,Shiko Aliyu Tunda ya Shiga dayan bedroom din nan ko motsinshi bataji ba,ta nan zaune bisa darduma bayan ta idar da sallar Asuba,tana addu"a tana kuka,karfe bakwai na safe taji bude kofar bedroom din da Aliyu ke ciki,bata fargaba taji Shigowarshi dakin bai ko kalli inda take ba,ya Furta cikin kakkausan murya.."Ki Fito mu tafi malama.."Yafada kafin ya juya zai Fita,jin ta Fashe da kuka ne,yasa ya dakata yana jin wani Abu na mai daci aransa,Kallonta yayi ta gefen ido kafin yace"Bake ya kamata kiyi kuka ba,nine yakamata na

Please Login or Register in order to submit comment