Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hidiman suna da Kayan babby dana maijego Duk bala yayi su,ranar suna kuma ya yankamata katon ragonta yarinya taci suna AZEEMA..,Sai da tayi arba"in kana Baba Ade takoma gida tabar Fatima nakara kula da yarta,Tare da taimakon suwaiba,wacce tadauki son Duniya ta dorama diyar Fatima,sabida suwaiba na son Diya mace arayuwarta,ammh Allah bai bata ba,sai yabata namiji,Saboda Amintakar dake tsakanin Fatima da Suwaiba ne,yasa Fatima tayima suwaiba tayin Auren mallam lawal,mganar data kawo rudani sosai,suwaiba taki yarda.hartayi ikirarin barin garin gombe,Bala ya shiga mganar yace Fatima tayi hakuri suka cigaba da zumuncinsu,tunda Suwaiba taki,dole Fatima tabar mganar ammh harga Allah tana kaunar suwaiba aranta.

Shekaran Azeema biyu Aduniya Fatima tafara wani ciwo,daga ciwon nono,shikenan sai cancer ciwon Daji,Tun ana ganin abun dawasa har babbar magana tazama babba,mganin gargajiya aka fara ammh Abu yacitura nono sai zagayewa yake,harya harbama dayan ma,Suwaiba da kanta takira bala ta fadamai kan yazo ya taimaki,Fatima koda yazo yaga halin datake ciki sai da ya zubarmata da kwallah,nan da nan aka dauketa zuwa babban asibitin jaha,sai koda sukaje likitoci kin amsanta sukayi,suna ta fada suna fadin sai da ciwo yagama cinyetane za"a kawo musu,bazasu amsa ba,ran Bala yabaci yace adawo da ita gida washegari sai sutafi da ita kaduna,Allahu Akbar Allah yaga Abunda yagani ne,ya takaitama musu wahala Karfe 3:00am na dare Fatima ta karbi kalmar shahada tarasu agaban mahaifiyarta da mijinta mallam lawal bayan ta bayyana amanar diyarta ahannun Suwaiba,wanda Aranar sai wajen sha biyu takoma gidanta,itada Aliyu da Azeema wacce keta kuka,shiyasa ta dauketa suka tafi gidanta takwana awajenta,alokacin mallam lawal ya bugama Suwaiba kofa dayake Bala na nan shi ya fito,nan yake shaidamai rasuwar Fatima,sanda Suwaiba taji sai da ta suma gau,saboda jimami da sabo,Tayi kuka kamar ranta zai fita,babu Abunda take tunawa sai irin sabon dasukayi da Fatima da zaman amanan da sukayi,tunda take da ita bata taba batamata da gangan ba,macece mai hakuri da sanin yakamata,balle mallam lawal dayayi kuka rasa nagartattaciyar mata irin Fatima,ita kanta Azeemar ta fahimci rasuwar mahaifiyarta nata,haka ta wuni kuka,Suwaiba na lallashinta Aluyu ma yasan lokacin da"akayi rasuwar,saboda yana da shekara 12 alokacin Domin har yakammallah karamar primary dinsa sai wucewa gaba,Baba Ade ma takoka domin itakadai ne yarta gashi Allah ya amshi Abunsa,Anayin bakwai Baba ade tatafi da Azeema wajenta,dayake basu da nisa saman anguwansu,shiyasa kullum sai Azeemar tazo wajen Suwaiba,wanda ko Azeema batajeba Suwaiba take wanke kafa taje ganinta Haka kurum Allah ya doramata son yarinyar da tsausayinta,shiyasa komai zatama Aliyu tare take hadawa da Azeema.

  Fatima tayi Arba"in da Rasuwa Bala yazo yatafi da Aliyu zuwa kaduna domin hallartar mkarantan daya neman masa Wato COMMAND SECONDARY SCHOOL KADUNA..,Makarantar sojoji dake kaduna,Babu yarda Suwaiba zatayi Tunda Aliyun yanuna yana son mkranatar na Sojojin,dole tanaji tana gani ya hada kayansa yabi kawunsa zuwa kaduna,wanda awannan karon yayan nata yaso tabiyoshi sukoma kaduna ammh suwaiba taki,tace tafi sabawa da Gombe bazata iya barin garinba,shikuma bayason takuramata sai ya rabu da ita,ammh duk Abunda zata bukata sai da ya barmata kafin su tafi,Da shi da Haisam aka sakasu amkranatar dayake anyima HAISAM din jamping din aji shiyasa sukayi Daidai akaratu.

Shekaran Fatima daya da Rasuwa yan"uwan Mallam lawal suka matsamai sai ya kara aure zama hakan bai yuyuwa,Dole tasa ya sake aure da wata yar saman layin dasuke RAMATU,Ramatu Mai awara ne Sunanta saboda awara take soyawa akofar gidansu tana yawan zuwa wajen mallam lawal siyan kayan miya shiyasa suka saba,Ramatu bazawarace tayi aure Allah yayima mijinta rasuwa,ammh bata haihu ba,Ramatu bata da uwa bata d uba,ahannun kakarta take,gabadaya rayuwarta tataso babu kwaba ne,ballatana tsawawartawa,Komai taga dama shi takeyi babu ruwanta,tunkan Auren ta na farko idonta yake abude,irin matanan ne marasa mutumci,da kamun kai,gata bata da kunya sam,ko mallam lawal din ita fara nunamai alamun so,don haka zata dinga aikamai da awara ko yabata kudi bata amsa,da taganshi zata hau sunne kai kamar munafuka,Ko lokacin dayazo da izinin neman amincewarta batayi gaddama ba Ta amince ko wata ba"ayi ba aka Daura aure tatare agidan mijinta,adakin dake gefen na fatima,dayake gidan,gidan laka ne,dan karami mai dakuna biyu da kichen sai dan filin tsakar gida,sai rijiya dake gefe,gidan babu siminti sai dai tarin kasa,ammh dayake lokacin Fatima nada kokarin tsabtaceshi shiyasa sai kasan ta kwanta kamar an daddadeta,.Satinsu biyu suna cin amarci kamar Abun arziki ammh daga Ranar da mallam Lawal ya fadamata zai dauko Azeema ya kawomata ranar basuyi barci ba,don Ramatu cewa tayi bazata rike diyar da bana nata ba wlh,shikuma yace bata isa ba,gata kuwa bazai barma Baba Ade wahala ba,dole tanaji tana gani ya tattarro Azeema ya dawo da ita gidan da zama,Suwaiba bataso haka ba,domin tuni taji lbrin Ramatu bata da mutumci sam,kuma tasani cewa Azeema bazataji dadin zama da ita ba.

Illai kuwa Domin Tunda Azeema tadawo hannu Ramatu take gana mata azaba,duk da karancin shekarunta domin lokacin tana da shekara biyar ne aduniya tayi girma dayake tana da tsawo,gabadaya aikin gidan nan ita keyinshi,da gari ya waye zata jawo ruwa tacika duka botikan gidan,kafin tazo tayi shara,tare gidan gabadaya takoma dakin mahaifiyarta inda yazama wajen kwananta ayanzu,bayan nan takoma kichen ta hura wuta ta sanya ruwan koko ta dama,ta zubama Babanta da inna Ramatu,kuma bata da ikon sha sai Ramatu taga dama,da kananan shekarunta tasaba da wanki na Ramatu da Babanta duk ita ke wankesu,Mallam lawal baya da yadda zaiyi domin kamar Ramatu tafi karfinsa ne,domin yana mgana zata tasomai kamar zata dakeshi,baya da yadda zaiyi sai ya dinga bama Azeema Hakuri,itako ko afuska bata nuna,bataso mahaifinta ya shiga damuwa saboda ita.

  wajen datake samun sauki guda biyu,daga gidan Baba Ade sai wajen Suwaiba,wanda tazama tamkar mahaifiyarta,Ramatu tunda ta lura Azeema najin dadi in taje gidan Suwaiba sai ta hanata zuwa,inko taje asace Ranar sai ta kusa kasheta,ko wani Abun amfani Suwaiba tabata to Ramatu zata kwace ta saida,da Suwaiba ta fahimci haka sai ta daina bata sai dai in zatayi amfani dashi taje gidan Suwaiban da Dauka,Suwaiba da hannunta ta sanya Azeema amkaranta awata mkrana dake nan garin gombe G.D.S.S.S GOVERMENT DAY SCIENCES SECONDARY SCHOOL GOMBE,mkrantace mai kyan gaske,saboda tana hade da private ce,sakamakon mkrantar ta masu dashi ne,Tana nan a Federal Lowcost layin ministery of Agric,wanda Ramatu bataso Azeema tashiga mkranta ba,taso tayi ta zama tana mata bauta,ammh sai wannan karan,Mallam lawal ya nunamata bata isa ba,harda islamiya Suwaiba ta sakata,karfe hudu zuwa Shida na yammah asabar da lahadi kuma ta sanyata hadda,wanda in tadawo take zuwa Suwaiban na kara biyamata karatun,wannan dalilin shi yadan samama Azeema salama da takuran Ramatu,duk da haryanzu bata daukemata kowani aiki ba,sai tayi shi kafin tatafi mkranta.

Ramatu nada wata uku da zuwa gidan tasamu ciki,shikenan sai Tsurfa da iyayi ya shigo ciki,Allah ne ma yasa za"a haifi jikin lafiya ta haifi yarta mace mai kama da ita,kuwa Ranar suna lawal ya sakama yarinya suna AZIZA tunda Ramatu ta haihu Azeema ke wahala da ita da yarta,Ko duba kankatarta batayi kamar jaka,itace cin kashin Aziza da cin Fitsarinta,kullum zaka ganta goye da Aziza ko itace uwarta sai haka,Haka Rayuwa tacigaba da tafiya da dadi babu dadi,Azeema na girma kullum wahalarta na karu,bata da wajen jin dadi sai wajen suwaiba,wanda haryanzu Aliyu bai dawo ba,yana chan kaduna wajen Kawu bala,sai dai yana Zuwa lokaci bayan lokaci.

  Aziza tafi Azeema jikin girma domin tana shekara goma kamar yar sha biyar,saboda tana da girman gabba,shekaru Biyar ne kwarara tsakaninta da Azeema ammh in kuka ga yadda takema Azeema zakuyi zaton kanwartace takusan ukuma,saboda yadda ta rainata ko agaban waye haka zata dakamata tsawa kamar tsaranta,itako Azeema bata da hayaniya ga hakuri da kawaichi,shiyasa kotayimata wani Abu bata daukan mataki sai dai tafadama Ramatu wacce suke kira da Inna,ammh daga karshe in ma batayi wasa ba ita zataci duka,Gabadaya Ramatu ta lalata Aziza domin ta danneta ta damata arashin kunya da Rashin mutumci,kullum cikin yima yan anguwa take,Azeema bata iya yima Aziza komai saboda tarigaya data raina ta,ko wankinta ita kemata har kuma yanzu ita ke aikin komai agidan,Aziza bata kauda kara suna zaune ita da mahaifiyarta sai dai ta dafa ta basu suci suna zaginta,mallam lawal bai da katabus saboda Ramatu ta zamarmai matar jaraba,har gwara ita Aziza in yayimata mgana tanaji Tunda tasan halinshi bayamata da wasa yanzu jikinta sai ya fadamata,Duk da tanajin Haushinsa acewarta yafi son Azeema akanta,dakuma hudubar mahaifiyarta,Aziza irin yaran nan ne masu shegen kwadayi,tunda ta lura da Abun arzikin da Suwaiba kema Azeema sai takoma shisshigema Suwaiba,ammh sai bata,bata Fuska ba saboda bata mu"amala da yaro mara kunya,uwa uba kuma basu shiri da Ramatu saboda rashin da"anta da kuma yadda take muguntama Azeemar.
   

Suwaiba saboda kar ace tayi sonkai,sai ta sanya Aziza A mkarantar da Azeema keyi,tare da islamiya ammh duk da haka baisa tafita daga bakin Ramatu ba,kullum bata da Abun zagi sai ita,tanabi gidan suna gidan biki tana fadin tana zaman kanta,don ko danta data haifa ba"a san asalin fa,bashi da uba,kilama dan gaba da Fatiha ne,itako Suwaiba kotakan Ramatu batabi saboda ta fahimci jahalici ke damun Ramatun shiyasa,Azeema kuwa tun bayan barin Aliyu gidan batakara sakashi a idonta ba,wani lokacin ko yazo tana gida tana fama da aiki,kuma baya kwana suke juyawa,Ranar dayazo yakwana itakuma tatafi gidan Baba Ade ta kwana tana dawowa goggo ta ce mata yanzu su gadanga suka koma kaduna,sai dai ta ciji yatsa ammh tana so taga yaya Aliyu taga Shin yakara girma ko yananan yadda yake,yanzu yana fara"a kokuwa haryanzu fuskarnan tasa ba Rahama.
  

Shiko Aliyu suna kammallah Command sch Haisam ya tafi BUK KANO yana karantar Accounting,ayayinda Aliyu ya fada ABU ZARIA yana karantar Scicology,yaso yatafi NDA ammh sai Kawu bala yace yafara hada Digerinsa First kafin yatafi,Akuma lokacin ne gwannatin datahau mulki ta bayyana Sunan Kawu bala amtsayin Kwamishinar yada lbari ta jahar kaduna,Babu laifi kawu bala yatara Abun Duniya domin yana gudanar da kasuwancinsa bayan aikin gwannatin,kuma haryanzu yana karantama gidan radio Nageria kaduna lbrin Turanci da fassaransu na hausa.

         #Comment,share and Vote..#
         #Janafy...#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH..HAUWA .S.ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


_*Assalamu Alaikum janafty Freeking Fans,gawani albishir din danake tafe muku dashi,Ko kuna da lbrin shahararriyar marubuciyar zamanin nan,wacce ta dade aharkan Rubutu,tana fayyace muku,yadda yanayin zamantakewar rayuwar da kullum take,wacce tadade tana haskaka zuciyarku da dadaddan littafanta masu dadi da Fasaha,masu dauke da darussa masu dimbin yawa,kada nacika ku da dogon lbri Ina Nufin NABILANCY LUV(Antyn S&S) wacce tazo muku da wani Salon lbri mai Tafiya da salon zuciyar mai karatu bakowani littafi bane illah...,MAKAUNIYA..(Labarin cin Amanar kauna)kunemi naku kusha karatu domin amfana da Abubuwan ban mamakin dake cikin littafin,Karki bari karka bari abaka lbrin MAKAUNIYA..(Labarin cin Amanar kauna)*_



*Chapter5*
   

    ""Cikin Nasara ya kammallah karatunshi yana gamawa ya tafi NDA wato Nagerian Defence Acadamy yayi wata ashirin da hudu ma"ana yayi Short Service kenan,yana gamawa yafito amtsayin SECOND LEUTANET,Tunda Aliyu ya Fito amtsayin Soja gwazonshi da kuma yadda yake Kaunar Abun Aransa yasa,nan da nan yayi Fice kowa ya sanshi,Saboda yana Bama Abu muhimmanci uwa uba kuma jarumi ne,mara tsoro shekaransa daya dawani Abu ya samu karin girma Zuwa LEUTANET,daganan yayi ta samun cigaba tare da karin mikamai Har zuwa yanzu dayake mtsayin CAPTAIN wanda yake karshinshin 1 DIVISION NIGERIAN ARMY KADUNA..

 
Shekarunsa na haihuwa kimanin 30 kenan,duk inda ake Neman cika da cikar zati da Haiba Aliyu Gadanga ya hadashi,Kyakyawane na gaske,sakamakon kamar dayake da mahaifinsa,in ka gansa akallo farko sai ka yankemai Hukunci dayana da girman kai,saboda mutum ne,mai iko da takama,yana da jinkai,in yana wani Abun sai kadauka yahada jini da Sarauta saboda yadda yake gudanar dawasu abubuwansa,Yana da karancin Fara"a Akan Fuskarsa wani lokacin ya hade Fuska sai yabaka,tsoro sai ka ga yana wani Abu kamar afilin daga,Aliyu gadanga miskili ne na karshe wanda Abokan aikinsa ke masa lakabi da *CAPTAIN A A TAMBARI BUZU..* gashi ya kasance mutum ne dabayason Raini da Sakarci,baya da wasa ko kadan,yana da mugun son Girma kamar gyambo,yana so ka bashi girma koda kai din ka girmesa atakaice dai,yana son Abashi respect na karshe,kana baya da wasa yasan salom mugunta kala,kala,A iya shekarunsa ya fuskacin kalubalen Rayuwa na yadda ake masa kallom mara Uba,wanda ba"a son Asalinsa ba,Shiko Mahaifiyarsa tarigaya datamai duk wani ,bayani,banda Sunan mahaifinshi da yanki daya fito basu san komai nashi ba,bai damu ba,saboda duk Abunda masu Uban zasu takama dashi,toshi ma zaiyi takama dashi harma ya darasu.

  Madina da mardiya dukkansu sunyi Auren nan kaduna,sai Haisam dake aiki yanzu da First banka A kano,Sunan GOGGO Yasamo asali ne,saboda su Haisam da suke kiranta da hakan,sakamakon ita din kanwar mahaifinsu ce,sai Shima Aliyun yake cemata haka,har sunan ya bita kowa Goggo,Aliyu mata basa gabansa domin da suna gabansa da tuni ya lalace,don yana matakin farko a jami"a yake samun tayin yan"mata yasani sarai ba saboda komai suke manne masa ba,sai saboda kyansa da ajinsa,Shiyasa baya damuwa,bayajin kunya kartama mace rashin mutum agaban kowaye,Gashi da zuciya ta bala"i,baya da tsoro balle shakka Goggo ce kadai sai kawu ke iya tankwarashi in yayi irin wannan bakar zuciya,baya da bakin da zai Furtama Gaggo Rashin Sanin takamammam dangin mahaifinsa na damunsa,saboda goggo ta kasance wata uwace mai mallakama Danta komai saboda ta inganta nashi rayuwar,yawan nunamata damuwarsa tamkar butulceni agareta,shiyasa koda wasa bai taba nuna mata Abun na damunsa ba.

   CAPTAIN JABIR Amini yake garesu ko nace dan"uwa,domin Tun Shigansa,NDA suka hadu,da farko In da Jabir yabiye ta halin Aliyu bazasu taba zama abokai,sakamakon Shi jabir Mutum ne,ma yawan Fara"a da sakin Fuska,uwa uba kuma ga barkwanci,sakamakon Aliyu da yake wani gim dashi Fuskarnan kullum babu alamu rahama,to sanin hali dakuma abota da Allah ya hada shikenan suka zama Aminai,tunda kowa yasan Halin kowa,Suna aiki awaje dayane Anan kaduna,Haka Shima Haisam babu ruwansa,mutum ne Shima mai fara"a Da son lbri sakamom Abokin nasu dayake wani murdadde mai iyamai sai Allah daya hallicesa.

Bayan kowani Sati uku yake zuwa gida,ganin Goggo to duk sanda yazo nan yake ganin Azeema tare da ita,duk da yana so ya tambayi wacece,ammh miskilanci da rashin son Raini yasa yake basarwa sai Goggon ne dakanta take shaidamai Diyar marigayiya Fatima ce tabe baki kawai yayi bai wani nuna wani tsausayi ba,ko yaba mganar goggon mahimmanci,itama sanin halinsa ya satakama kanta dashi,Tun ganin Farko da Azeema tayima Aliyu bayan dadewar datayi bata ganshi ba,Allah ya sakamata tsoronshi,saboda ita arayuwarta ta tsani soja,saboda yadda takejin lbrin Rashin tsausayinsu,to Ranar data ga Aliyun ma da kakinsa ne,yazo gidan Goggo fuskarnan babu Annuri kafarsa sanye cikin wannan katon takalmn nasu,wanda in suka taka ka dashi,ko baka mutu ba,sai kayi jnya mai tsawo,lokacin data ganshi ya shigo dakin goggo,itakuma tana sharemata dakin,goggo na ciki,yana dago labule suka hada ido,ai saboda tsoro batasan sadda tayada Abun sharan ba ta kwantsama ihu ba,Wata razananniyar tsawa ya dakamata yana hararanta,saboda ganin yadda take neman Raina mai,wayau shi da gidansu ya shigo ta faramai ihu,tsawan data kara firgitata ta tsorata sai ga fitsari,shar yana zubowa ta kafanta saboda tsoro,dama Azeema akwai dan banzan Tsoro kamar farar kura,Baki yarike yana kallon yadda take shatata fitsari tana kamkame jikinta,aiko karisa shigowa dakin yayi yana kwanto belt dinshi yana fadin"Bush girl yanzu zaki durkusa ki shanye kazantar dakikayi kuwa..."Yake fada yana Shirin kwanto belt Goggo ta fito tana zabgamai harara,kafin tamaida kallonta kan Azeema taga yadda take rawan sanyi saboda tsoro fada Goggo ta hau gadanga dashi kan yazo ya tsorata mata diya korashi tayi,dole ya fice yana tsaki yaso goggo tabari ya lallasa yarnyarnan,banda iskanci da samun waje kamartane zatayima mutane Fitsari a tsaye,shibaima fahimci shiya firgitata ba,to tundaga ranar Azeema take Tsoron Aliyu wanda take kira da YAYA CAPTAIN,bata yarda tadawo gidan ba,sai da yakoma,Baya zuwa gidansu,ammh yana zama wajen sana"ar baba lawal ta kayan gwari,saboda kamar kawu bala,yake kallonsa ko bakomai yaba da gudummuwa arayuwarsa duk da yanzu yadan manyanta.

AZEEZA tunda Allah yasa ta dora ido kan Aliyu,watarana sun dawo daga mkranta suka ganshi wajen babansu,Azeeza saboda kallo sai da takusa fadi,sai da Azeema ta riketa,kallonsa take bata ko kiftawa Azeema ta tambaya waye wanchan na tare da baba? Azeema ta bata amsa da cewa"La baki ganesa ba,Yaya captain ne fa,na gidan Goggo..."Aziza najin haka gabanta yafadi kardai ace dan Shegen nan ne,mara asali,ammh ko gayen yana da kyau,ya hadu,wasa wasa ranar Tunanin Aliyu bai bar Aziza tayi sukuni ba,Tun tana daukan Abun wasa hartazo ta tabbatar da cewa takamu da son Aliyu,gashi ko mgana basu tabayi ba,saboda yana ganin yarinyar yaji lbrinta bata da kunya ko kadan,shiko baya hulda da marasa kunya yanzunan yarinya tanemi rainashi sai yaci ubanta ko agefen kwalan riganshi,shiyasa koda wasa bai taba sakarmata fuska ba tasha ganinshi baknta na rawa tahau gaisheshi shiko sai yagadama ne ma zai amsa da lafiya lau,daga haka ya gimtse fuska,Wani lokacin yake kawai take tana biyema Ramatun intana zaginsa,saboda bataso ta fahimci halin datake ciki.
Ramatu kuwa ya tsaneta saboda rashin kirknta baitaba gaisheta ba ko zasu bangaji juna kuwa,shiyasa itama bata kaunarshi,duk inda ta zauna bata da mgana sai nashi dana mahafiyarshi,tasha kawo karansa wajen Goggo tama danta mgana baida tarbiya,sai dai Goggo tabata hakuri tace zatamai mgana,ranar data faramai mgana,cema goggo yayi"in batayi hankali ba duk randa ta shiga gonarshi sai ta zagaya anguwanan tana tsallen kwado.."dakuwa goggo tamai tana fadin"Tunda kasata nima zaka iya sakani kenan"Ko ajikinsa saima cema Goggo dayayi"Shi dai bai ce itaba,so karta sa kanta aciki..

Goggo macece mai fada,da shiga Abunda babu ruwanta,indai akan Da'ntane Aliyu,wanda takema kira da GADANGA,Tana da yawan barkwanci da son wasa,shiyasa ya maidata kakarsa,in kaga yadda ake daru tsakanin Gadanga da goggo sai cikinka ya kulle,in yadade baizo ba,tadinga kira tana fadin"Gadanga ko amun yaji ne? saboda kullum da tsiya suke rabuwa,Dakuma yazo ko kwana ba"ayi za"a tsiyace,goggo kenan da Aliyu gadanganta.

   Aliyu mutum ne,mai yawan karfin sha"awa shiyasa tunda ya fahimci haka,sai ya rika azumin litini da alhamis,Ammh duk da haka Abu yaci tura sai ya yanke hukuncin fara neman Aure,koda kuwa da yan"matan dake haukan Sonshi ne,yafara neman wata mufida yar kaduna ce,Soyayyarsu batayi nisa ba,suka rabu,sakamakon mahaifinta yace bazai bata shiba,saboda yayi bincike ba"asan asalin sa ba,abun bai dameshi ba ya rabu da ita,bayan ita ya nemi Ummi yar katsina ce Itama itace ke mutuwar sonshi,ita harmgana tayi karfi,su kawu na Shirin zuwa komai ya rushe,bayan ita sai da akayi biyu,duk karatun dayane,Abun ya soma damunshi,duk matsayinshi ace anamai Wulakanci wajen neman Aure ana tozartashi kan baida uba,tun daganan ya watsar da komai ya cigaba da azuminsa kwatsam suka hadu da Ni"imatullahi akaduna wajen Dinner wani abokinsu shima Soja itakuma kawartace ai Tunda ni"ima ta hanga ido,taga Aliyu ta mutu akanshi,sai da tasan yadda tayi kafin tabar kaduna ta kafa gwannatinta.

Ni"imatullahi Ahmed Sidi na iya,diyace ga kwamishar yansanda na jahar gombe,kuma ya'ce daya tilo da iyayanta suka haifa,yar gatace ta karahe,wayayyiyace domin duka digeree dinta harzuwa master dinta ba A Nigeria tayima ba,yar kimanin Shekara ashirin da biyu aduniya,Fara gajera ammh itama babu laifi tana da kyau,Lokaci daya son Aliyu yayimata reshe harda rassa,tun bayabi takanta haryafara saboda yadda take gigitashi da salon soyayyarta,lokaci daya suka afkama juna da soyayyah mai zafi,ba"a dauki wani lokaci ba ya gabatar da kanshi wajen kwamishina zuwan farko duka iyayyan nata sun yaba da zabin diyar tasu ammh sai dai kash,kwamishina na bincikawa sai aka cemasa don makusa Captain Aliyu baida makusa,sai dai makusan guda dayane,rashin takamammen waye mahaifinshi,da kwamishina yaji haka yaso ya butse,ammh sai diyarsu ta nuna,in ba Aliyu ba sai mutuwa,dole aka yarjemai ya turomai magabantashi,kawu bala da mallam lawal sukaje,tun farkon mganar Auren sune jagoran komai har zuwa aka saka ranar Aurensu wata uku,murna wajen Ni"ima ba"a mgana,ta bangaren Aliyu dai laba"asa,donshi babu mai gane yanayinsa.

Da Azeeza taji lbrin Auren da Aliyu zaiyi sai da ta kwanta asibiti saboda firgici da damuwa,Duk iyayanta suka damu,kamar Azeema taji lbri,duk irin diban albarkan da Azizar take mata bata damu,tanajin yar"uwan nata har ranta sabanin ita Azizar datake zaune da Azeemar don bata da yarda zatayi ne,ammah har aranta take jin ta tsaneta batasan dalili ba,kodon hudubar mahaifiyarta akanta ne,ohoabunda kawai tasani bata ma kaunar ganin Azeema cikin Farinciki tafiso ita da uwarta suyi farinciki,itakuma ta dauwama cikin kunci,ayanzu haka shekarun Azeema 20 ayayinda Azeeza take da 15 ammh dayake tana da girman jiki,in akace shekarunta kenan wasu ma basu yarda,dauka suke ita ke gaba da Azeemar.

Ganin gabatowar Biki yasa Aliyu yafara gyaran gidansu,kusan dai Aliyu bawani mai kudi bane,Baya da burin tara arziki,ko yau adinga lbrinsa,amtsayin shi wanine,shidai burinshi ya taimaki kasarsa da lafiyansa da kwazonsa,kodon watarana in ya mutu atuna dashi,yana da Rufin asiri daidai gwargwado,Saboda baidawani dawainiya akansa,goggo ce haryanzu kawu baidaina hidima dasu ba,hatta shi Aliyu,son duk kudadansa,suna kammalle abanki ne,gidan nasu dama dan madaidaicine mai yalwar dan tsakar gida gefe wajen zubda ruwa,sai Famfo,daganan yammah akwai wani daki,ciki daya,nan ne dakin Aliyun,sai daga gabas dakuna guda biyu,daya goggo naciki,daya kuma tana ijiye kayan Abinci da sauran karikice,yana tashi gyaran ya bude dakunan goggo ya hadesu waje daya yayi mata babban falo da Dakuna barci guda biyu da tailot yazubamata kayan more rayuwa sai daga waje yayi musu katon madafin girki,sai barayinsa,dayake buge dakin,yayi ya hade musu Falo da two bedroom da kichen da Bayi,saboda nan zasu fara zama kafin su wuce kaduna,Tsakar gidan ma yasa aka kankare,aka saka interlock,Daga wajen kuma aka fitar da garejin mota,saboda motarsa,baya ma zuwa da ita gomben,saboda ba wajen adanata,yafi hawa motar haya Abunshi,don shifa Babu ruwansa bai dauki Duniya da zafi ba,akayi fenti mai kyau da kayatarwa daga wajenma an gyarashi sosai,tundaga nesa kana hangoshi yana daukan ido..

Tunda biki ya matso yan bani na iya suka damu kwamishina da tsegumin Aliyu,har mgana takai ga kaninshi wanda zai bada Auren Ni"ima,tun kafin Daurin Aure yaso adakatar da mganar,ammh kwamishina yaki yarda saboda yadda mahaifiyar Ni"imar da rike wuta,saboda sanin yadda diyarsu ke mugun Son Aliyu,Ni"ima kuwa tayi rawan kafa,kamar mene,duk da danginta sukaje mata jere,suka dawo suna raina inda Aliyun zai ijeta,harda uwarsa,uwa uba harda anguwan suka raina,sunce ta yaku bayi ce,ma"ana ghetto area ce,Da fari Ni"ima tayima Aliyu mgana,ammh sai ya numata shidin bawani bane,in zata zauna dashi ahaka,Final,in kuma tanaganin tafi karfin nan,To door iz open babu lalle ba dole,shi bazai dau wannan Rainin ba,don baicemata shi wani ne,ba,Shi kawai Sojan Nigeria ne,mai bama kasarsa gudummmuwa.,Dole Ni"ima tai ta bama Aliyu hakuri,domin zaga zaga yayimata,dakyar tashawo kanshi,ya hakura,tasan halinshi sarai baida wasa,shiyasa take kafkafa dashi kada ta balloma kanta Ruwa.

Ranar Daurin aure kiran da Kanin kwamishina yayimai kenan kan su bazasu bada diyarsu,ga wanda baida cikakken Asali ba,Sai yaga Dangin Maihaifinsa,tukunnah inko basu,to sai dai yayi hakuri bazasu basu diyarsu ba,Kwamishina baida yadda zaiyi dashi,dole ya bashi goyon baya,wannan Shine musabbabin Abunda yafaru awajen Daurin Aure,da yadda Daurin Auren yakoma kan AZEEMA, da duk Abubuwan da suka biyo baya...

*Karshen Asalin Tushe*

*Yanzu muka Shiga gabar,ku biyoni don ji yazata kaya gadai gwarzo nan Captain Aliyu  Abdulnaseer Tambari buzu,dakuma zaratan matan Azeema,Azeeza,da Ni"imatullah..*

         #Comment,share and Vote..#
         #Janafty...#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘 Ladingo yar Mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*NOT EDITED*💥

*Chapter 6*
         

    Jabir ya dade dakin Goggo suna hira sai wajen 10:00pm na dare,Goggo taga Aliyu baida niyyar bude kofar shashensa,fitowa tayi da kanta ta isa har kofar shashen tahau bugawa tana fadin"Gadanga kazo,ka bude kofarnan.."kazo ka bude nace ko?goggo take fada cikin fada.

  Yana kwance akan Daya daga cikin kujerun Falo,inda Allah ya taimakeshi lokaci da"akazo za"a yima Ni"ima jeren kayanta,hanawa yayi,saboda bazama zasuyi anan dinba,cemusu yayi kada su damu,ko gidanshi na cikin barikin akwai komai,so no need su wahalar da kansu,dayake dama already ya rigaya daya gyara barayinsa nasa bayan ya kawatashi dakayan alatun more rayuwa.

  Yanajin Buga kofan Goggo,da maganart,ammh yayi mata banza,yana kwance dagashi sai boxers kadai,babu ko riga ajiknsa,gashin kirjinsa yayi kwance luf dashi,Idanunsa suna lumshe ne,ammah ba barci yake ba,Damuwa tareda bakinciki ke mukurkusan shi,shi yanzu bama ta Ni"ima yakeyi ba,ta makomar rayuwarshi yakeyi,"Waye Mahaifinsa?inda gaske Goggo takeyi shi ba shege bane,to ina mahaifinsa da Danginsa suke? Tambayar da haryau bai samu mai amsamai ba.

Goggo jin Shuru ya sata matsa jikin tagan kofan tana fadin"wlh ko kazo ka budemin,ko in kira gardawa suzo su

Please Login or Register in order to submit comment