Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yahani Aurenta dana samarma kaina mafita,yanzu Ni Azeema Saboda Ranin dakimam yakai haka harzaki bude baki kice ina Shanshanci ko? yafada idonsa yana wani juyawa Shuru tayi ta kasa mgana,dauke kafarsa yayi yana Sauke ajiyar zuciya kafin yace

  "Koda ina Saurayi ban lalace ba Azeema,kuma saboda Rashin sanin darajan kai narasa lokacin da zan yi Shashanci sai lokacin da kika zama jini da hanta na,kikagama mamaye dukkan Numfashi,bayan kin zamo uwar ya"yana?...Yafada yana nuna kanshi,Kuri yayi mata da ido,ganin yadda yake kallonta ne yasa ta sadda kai tana jin Nadamar Abunda Tafada.

Juyawa yayi zai Fita Yana Fadin"Babu komai Rayuwace..."Yafada yana kokarim Ficewa Saurin Shan gabansa Azeema tayi jikinta duk yayi sanyi,sadda kai tayi kafin tace"Ni ban fada haka har zuciyata ba kawai na fadane Saboda Haushin Ratayen nin dakayi shine kawai Fa.."Tafada idonta na kawo Ruwa,hannunta ya riko kafin yace"cikin ni dake waya Fara rataye wani ehe? nina Fara jan fadan daga baya ban kiraki ba kika kidaga kirana ba? ko ban Nemiki ba? yafada yana kallon kwayan idonta.

Raurau tayi da ido kafin tace'Nima alokacin Haushi naji ka doramin laifin da kasani ba laifina bane.."Matse mata hannu yayi yana Fadin"toh naji ammh kome nayi miki pretty ai ni mijinki ne,yakamata dakika dawo ki girmamani amtsayina na mijinki ammh kiduba yadda kika watsar da Rayuwata why pretty?yafada kamar zai mata kuka,itama kukan ne ya kawomata kawai Sai tafada jikinsa tana Fadin"Nayi kuskure mijina don Allah ka yafemin.."

Rumgumeta Yayi kamkam yana Fadin"Shii..Is ok komai ya Wuce nima kiyafemin kinji.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,kamkame juna sukayi kamar wani zai Rabasu Fadi yace"Do u know wht? i miss u So much pretty wlh ko barcin kirki banayi saboda Tunanin kina Fushi dani plz karki kara barina,Rayuwa babu ke tamkar rayuwace babu jinin jiki.."Hawaye suka zuboma Azeema tace"Me too i miss u more,kuma i promise u am not let u down insha Allahu.."Jin haka yasa yadago kanta yayi Saurin dora lebenshi bisa nata yana yimata wani salo,wanda Tuni da dage ta nadeneshi tana mikomai harshenta da hanzari ya kama,yana mata wani Sumbata mai gigita ya"ya mata,kafin kace me,sun Rikita junansu,dama Azeema daga ita sai Tawel,wanda Tuni Aliyu yayi Fatali dashi,cak ya dauketa sai bisa gadonta,anan aka warware komai,Aliyu Tunda ya Shiga birnin Azeema Shikenan ya Susuce Fadi yake"pretty don Allah ki zauna dani,wayyo..""'!Dadi wlh kina Rabuwa dani zan mutu ne..!Sai da Ta rufemai baki sanin basu kadai bane agidan,Itako daman Baba lami tana Falo,tun sadda taji hayaniyarsu ta kwashe yara su Shige daki,aranta tana addu"ar Allah ya daidaita ma"auranta.

Sai da komai ya kamkama bayan Sunyi wanka sun sauya kaya kana Suka Fito falo cin abinci,sunyi Shar dasu gadanga ko bakinsa har kunne,Ranar ma bisa Dining akaci abincin,Shiyasa Baba lami na ganin haka tace ita adaki zataci nata,saboda taga yau ma"auratan babu dama fa,aiko gadanga yaci tuwon nan sosai yana ta zuba santi,suna kammallahwa ta kwashe komai takai kichen,tana dawowa Tashiga dakin Baba lami ta basu Anwar nono,suka sha kafin tayi mata sai da Safe ta Fice,dakinsu ta koma inda uban gayyar ke jiranta tana Shiga ko ya kamata ya kamkame yana wani lumshe ido,datayi mgana sai yace shifa wlh an wahalar dashi dayawa gwara abarshi ya famshe da kyau.

Shikenan zaman ma"auratan ya Daidaita basu kara samun wata mtsala ba,sai ma wani karin so da kaunar juna sukeyi,Ranar da Azeeema tacika sati dadawowa Ranar Gimbiya Razeenah takoma Niger,ammh sai da Ummah ta matsamata ta rakata gidan Jabir taga zafira,murna ba"a mgana kuwa duk da basu dade ba,ammh sunji dadin zuwanta,ai Safaratu dake kano najin lbri takira Ta tana kuka akan wlh itama bata yarda ba sai tazo mata yata iya dole ta Shirya Ummah tarakata taje ta wunin mata,suka rasa ina zasu sanya iyayan nasu saboda farinciki kowacce tayi kiba bulbul Daga gani suna samun kulawa daga mazajensu,bata samu damar komawa wajen su Azeema ba,sai dai sukayi sallama ta waya dasu,suna bata sakon gaisuwa zuwa ga yan gida.

*BAYAN WATA BIYU*

Bayan wata Biyu Da Dawowar Azeema,Tuni su Afiya sunyi wayau sunkara girma kamar ba yan wata hudu ba ita kanta Azeemar tayi kiba takara haske da kyau,to takowani bangare suna samun kulawa,ga kulawar miji kamar ya cinyeta danya bata gasu ga,sunje kaduna sau daya bayan dawowarta,kuma su Haisam da jabir,sun zo Rana daya kowanne da matarsa sun musu kwana daya suka koma,mganar Auren Umar kuwa yazo Nageria sau daya Kawu maimartaba ya wakilta akan mganar babu wata bata lokaci har ansaka Rana Wata biyu yanzu haka biki baifi sati biyu ba ya rage,suna so suyi Shiri gabadaya ne daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai Tsarki ne su sauke farali.

Koda Azeema taji lbrin Auren Muneera da Umar bataji komai ba,illah tsausayama Ni'imar datayi domin ko qur'ani zata dafa,Mijinta bayi da Ra"ayin Aurenta yanzu,ammh bata sani ba ko zuwa gaba,domin tataba latsashi akan mganar Ni"ima yayimata Fada sosai yace babu Ruwanta bata fishi sanin Ni"imar ba,daganan takama kanta,bayan an saka Ranar su da Umar,har Abuja sukazo suka wunin mata ita da Ni"ima sai alokacin Azeema tafahimci wacece Ni"ima sam bata da mtsala ko muneera datakeda Rawan kai yanzu duk ta rageshi,Ni"ima Tunda tazo take wahala dasu Afiya da wannan yayi kuka ta sabeshi ta goya,ta dauki wannan Ta hau jijjigawa,ita dai Allah ya Doramata sonsu,Umar da kanshi ya maidasu har  gombe da Kayan kwalliyan da Azeema ta hada musu,da farkoma kin karba sukayi sai da tace ko Sun Raina ne?shiyasa suka karba,Shiko Aliyu Tun zuwansu bayan sun gaisa yayi Ficewarsa ko daxasu Tafi Azeema ta kirasa awaya sai cewa yayi Allah kiyaye hanya yanzu zasu Shiga meeting ne,Azeema bata jin Dadin Abunda yayi ba sam wlh duk kunya yakamata,daya dawo sai da tamai mgana banza da ita yayi bai Tankataba Aransa yana fadin"mata masu Duniya yanzu fa daya dawo sai tace yayi laifi kuma oh sudai bamai iya musu sai wanda Ya hallicesu.


Yan Nageria basu Tafi Agadez da wuri ba Sai da Aka Daura auren Umar da Muneera wanda Kawu ya karbomai Aure don maimartaba bai samu zuwa ba,su goggo suna chan suna Shirye Shiryen Zuwan Amarya suko su gadanga sai Awashegari suka dumgumo zuwa Masarauta dashi da jabir da zafira sai Haisam da Safaratu,sai Kawu bala da Ummah,sai Anty madina da Anty mardiya,kowanne da yayansa da mijinta,sai Kawu lawal da inna Ramatu,sai Azeema da ya'n ukunta sai Baba lami,wanda daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai tsarki Sai ko Amarya Muneera da angonta Umar,sai Aminiyarta Ni"ima,sai kanwar babanta daya da kuma Yar"uwan mamanta dasu kadai akazo saboda nisa,don itama Amarya da angon dasu za"a Tafi chan Saudiyan.

  Koda suka isa Masarautar Tambari buzu ko"ina ya cika da mutane anata Shagulgulan zuwan amarya,kai tsaye Shashen goggo aka kai amarya sai Awashegari ne,aka Kaita Fada jakadiya ta sanyanmata alkayyaban Sarauniyar Tambari buzu ta biyu,maimartaba ya sanyamusu albarka kafin awuce da ita Shashen mahaifiyarsa,bayan anfito da ita daga shashen Gimbiya Razeenah,daganan Ita Gimbiya Fasilatu tabasu kyautan kudi harda zinare,suka rankaya zuwa Babban Shashen na Yarima Umar,wanda lokacin kadan zasu zauna da sun dawo daga kasa mai tsarki zasu tarrara su koma Niamey inda yake aiki.,Duka duka kwana biyu su Ni"ima sukayi suka koma Nageria cike da Abun arziki tare da karramawa irinta masarautar Tambari buzu.

******************

  Duka duka Sati biyu ne da zuwansu garin Suka tattara duka Ahalin suka yada zango abirnin madina,harda su Maimartaba da duka matansa guda uku,gaskiiya wannan Tafiya tafiyane mai cike da Nasara,domin sai da suka kwana goma Amadina suna Ziyara kafin su wuce garin makka,inda kowa ya zage Yana ta ibada babu kama hannun yaro,Azeema data ganta gaban ka"aba sai da tayi kuka,haka tayita rokon ma Mahaifiyarta gafara da kuma Azeeza,sai ta rokon ma mijinta fatan nasaran rayuwa dakuma Allah ya rayamata ya"yanta cikin Tafarkin Adinin islama.

Kwanansu goma Sha daya agarin makka,lokacin angama aikin hajji,su maimartaba da matansa da kawu Da ummah da mallam lawal da Baba Ade,da Inna Ramatu,a birnin makka suka bar su Gadanga suka koma gida,domin dukkansu ba gida zasu koma ba,daganan birnin london suka yada zango,sai da sukayi sati kafin su Wuce Canada,nan din sati sukayi kafin daganan su wuce india A birnin New Delhi,sai gasu har gidan Drkhabir khan,wanda Fadan irin murnan da Sukayi Shida matarshi bata baki ne,har cikin asibiti suka shiga zo kuga yadda ake ihun zuwansu love birds,sai hotuna ake dasu ana Daukan Su Afiya wadanda suka kara wayau suka girma,nan ma sai da suka Shafe sati suna yawata gari kafin suyi haraman komawa gida,ta Abuja suka sauka daganan aka Rabu kowa ya nufi inda yafi wayau sudai su gadanga sunzo gida ne,Haisam daganan suka wuce kano Shida Safaratu,sai su jabir dasu Anty madina suka wuce kaduna,Umar da Muneera kuma Tun a India suka rabu su jirgin Niger zasu Shiga sukuma suka Shigo na Nageria.

Bayan dawowansu ba Dadewa Aliyu yaje ya karboma Azeema takardun ta na gama mkranta a gombe yazo yayi mata Rigisteration a BASE UNIVERSTY inda zata karanci PHAMARCY,murna wajen Azeema ba"a mgana Ranar da zatafara zuwa daukan lecture saboda zumudi ko barci batayi ba,gari na wayewa sai ga sabon Suprise,sabuwar motar ta kirar Toyota 306 Aliyu ya dankamata yace Ayi karatu lafiya,Ai Azeema kamar zatayi hauka haka ta makale Aliyu tana kuka tanamai godiya,dama already ta iya mota bayan dawowarsu Abuja,sai ta dinga barin ma Baba lami su Afiya tana tafiya mkranta,inkuma sunada interval a mkrantan takan dawo gida Ta basu nono takoma.

Azeema shiganta mkranta takara wayewa sosai,kuma bata yarda tayi kawa da kowa ba,saboda kashedin Gadanga akanta,tsakaninta dakowa hy hy ne gashi Kwakwalwarta naja kaf Depertment dinsu asan da zamanta mai kokari ce,gata da kamun kai da tsare gida babu Ruwanta da naza,matan ma kwarjini take musu tsoron tanka mata suke,Wani lokacin batajin Tuki da kanta Shiyake kawota yakuma zo ya dauketa Domin preetty tazama shi,shikuma yazama ita,Abunda ke kara sawa yake kara sonta ko mai takeyi bata iya hadashi da Laluransa,shi na musamman ne,domin duk Abunda takeyi dayazo da bukatarsa zata ijiye taji dashi,shiyasa yake kokarin tallafamata tasamu tayi karatun nan saboda shine babban burin Azeema ayanzu.

_Today is a special Day To me_💃💃💃💃

*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


    *KA'RSHE*.... _END_😥👏🙌✌

            *Chapter 40*

     
""Azeema bata Rufe Shekara da Shiga mkranta ba,Ciki ya bulla ajikinta,lokacin sunyi jarabawar Karshen semister,sun tafi hutu suna Shirin zuwa aji biyu,Inda Allah ya taimaketa Su Afiya shekaransu daya lokacin da wata daya,tuni sun yi girma suna Tafiyansu ko"ina,in ka gansu bazakace Azeema ta haifesu ba,sakamakon basa kama da ita ko kadan,Sai da da Aliyu suke kama,kana ganinsu daga gashin kansu zaka zargi kodai sun hada jini da larabawa ko Buzaye cikin biyu za"ayi daya,balle yadda Su Afiya suka dauko bakin gashin babansu,suna kanana dasu,ammh in Azeema tamusu tsifa ta daure musu da band Abun sai masha Allahu kawai.

Da farko Azeema tayi bori game da cikin jikinta,ta dinga kawoma Aliyu uzirinta,ga yara basu bar shan nono ba ga Kuma karatunta ita yanzu ya zatayi,zama da ita yayi yayita lallashinta dayaga taki yarda sai ya dauketa sukaje wani privet hopital suka samu wata likita,yasanar da ita mtsalansu nan da nan ta Shiga yima Azeema Fadan,ya Allah zai bata kyauta kuma tayimai butulci,tasan Adadin mutanen da suka zauna a inda take,suna mata kuka Allah bai basu haihuwa ba,koko tasan Adadin mutanen dake zaryan awannan hospital din duk dan Allah ya basu haihuwa? Azeema ta girgiza kai Hawaye suna zubomata tacigaba da Fadin"Kuma Shine ke Allah yabaki Kike neman kiyi butulci toh ahir dinki domin sai Allah yabarki da dubaranki,ai yafi ki sanin kina da ya"ya kuma ya zabeki acikin dubu ya baki wannan kyautan,toh tun Wuri ki daga hannu sama ki godemai kada Allah yayi Fushi dake"

jin haka yasa Azeema ta daga hannu hawaye na zuba tana godiya ga Allah,nan likitan ta sausauta takaramata da shawarwarin yadda zata kula da kanta da ya"yanta,Tunda ma taji su Afiyan sukai shekara daya tace ta ciresu anono babu damuwa,Sai acigaba da basu abinci wanda zai cigaba da gina musu jikinsu,magungunar karin lafiya dana karin jini ta Rubuta musu sukayi mata sallama,sai da suka biya phamarcy suka siya magungunar kafin su Wuce gida,Ranar dai Azeema kuka ta Wuni yi,Aliyu na aikin lallashin Tunda aiki ya riga ya sameshi.

  Haka Azeema ta cigaba da kula da cikinta sukuma su Afiya Ta ciresu anono ta damkama Baba lami tana cigaba da kula dasu,itama kuma tana Renon Cikinta tana kuma cigaba da karatunta babu wani mtsala domin Aliyu na tsaye kanta ita da ya"yanta,Cikin ikon Allah sai ga Azeema ta haihu kusan lokaci daya da Zafira,Azeema ta haihu yau Zafira ta haihu washegari Kuma duka mata Ranar suna Yar wajen Azeema taci sunan Gimbiya Razeenah,,suna kiranta Sajida,sai yar wajen zafira taci sunan Mahaifiyar Jabir wato khadija suna kiranta Meenal,tsakaninsu da Safaratu kwana goma sha biyar ne ita ta sauka ta haifi danta Namiji wanda yaci sunan kawu Bala,suna kiransa da Sajjad.

 
*AFTER 5 YEARS*

""Ashekaru biyar da suka gabata Abubuwa dadama sun Faru na Farinciki da akasinsa,na bakinciki Shine Rasuwar Ummah mai babban daki,tare da Rasuwar Baba Ade wadanda suka rigamu gidan gaskiya,Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansu Da Gafara Ameen.

Ababen Farinciki kuwa Shine Shekaru biyu dasuka gabata Maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yayi murabus daga kan karagan mulki ya nada da'nsa Aliyu Abdulnaseer Tambari,wanda yayi Retire,a aikin Soja,suka tararra shida da duka iyalansa suka dawo Niger da zama lokacin Azeema ta kammallah karatunta sai tazo nan tayi bautar kasarta,Nadin sarauta da sai da aka jadaga kafin Ayishi domin Aliyu Tuburewa yayi Shifa baya bukatar Sarauta yafi bukatar Aikinsa Fiye da komai,ga Umar nan Adorashi shi yabarmai har Abada,Sai da yaga maimartaba yanuna bacin Ransa sosai,kuma su Kawu bala da Mallam lawal suka tayimai Nasiha kafin ya yarda,itako Azeema daga sama taji Abun kamar almara wai Aliyunta zai zama sarki,bata nuna Rashin goyon bayanta ba,saima kara karfafamai gwiwa dataitayi,lokacin ma tana da wani cikin ajikinta,Shi duk damuwarshi daya yasan baza"a barshi yazauna da Azeema ita kadai ba,dayayimata wannan complain kallonsa tayi tana dariya tace"To sai me Ehe,ai wlh bana da wani haufi akan Sadaukina ko yanzu wata ta Shigo na tabbata ni Azeema nayi mata zarrah har Abada,saboda haka karka Damu kanka ga Ni"ima,babu wacce ta dace ka aura sai ita,domin itama masoyiyarkace ta gaskiya nekamar muneera taji lbrim wacce ke Fadin kyawawan Halayyan Azeema domin tana bata girmanta amtsayinta na Matar wan mijinta,ita ma Azeema tana tafiyarta da ita yadda Yakamata.

Sai Ranar Daura aure kana Sarki Aliyu Abdulnaseer Tambari buzu,dashi da tsohon sarki Abdulnaseer tambari buzu,sai ga kanin kwamishina daya hana auren Ni"ima Da farko kunyama tanahashi bada auren akaro na biyu,sai wani ne ya basu Auren,yau ga mahaifin Aliyun dayace sai yazo,toh gashi gabanshi wanda ko daga ido ma yakasayi ya kalleshi bayan Daura Auren kwana daya kawai sukayi Aliyu ya tarraro matarsa suka dawo masarauta,inda ya hadata da Azeema yajata mata kunne,kuma koma baijamata Ni"ima Ta riga data sani Azeema ta mata Zarra,ko goggo Fadan datayi mata kenan Ta girmama Azeema,kowama haka yake Fadi,aiko dole ta girmama Azeema ko taki ko taso,itako Muneera bata zo bikin ba,suna Niemiy, cikinta ya Tsufa yarima Umar ne kadai yazo,shima kwana biyu yayi yakoma Wajen aikinsa.

Ni"ima Ta yarda Azeema ce ke gaba da ita binta take sauda kafa,domin Aliyu ya sanar da ita da Amincewarta ya aurota,so dole ta godemata,ita kuma Azeema ta kama girmanta domin itace Shugaban matan Sarki kuma Sarauniya kwara daya tal mai mulkan zuciyan Aliyu,kowace Ranar datake da kwana zata bi miji Turaka,ammh ita Azeema Aliyu da kanshi yake binta,ita ta hanashi saboda tabashi hadin kai ya kwantanta Adalci.

   Ayanzu haka Ni"ima nada diya daya mace mai Suna Umaimah,suna kiranta Ummah,sai Azeema wacce takara bayan Sajida tayi Jabir,sai Bala na karshe wanda suke kira Kawu,Muneera ma ya"yanta biyu Aliyu da Abdulnaseer,sai Jabir dake da uku Haisam kuma biyu haryanzu Safaratu bata kara haihuwa ba,zaman lafiya tare da zumunci yana kara karfi atsakaninsu Inna Ramatu kuwa da Mallam lawal Tuni maimartaba yaci galaba akan Baban Azeema sun dawo masarauta da zama,yau sai ga Inna Ramatu na tsoma biyar tana wanke goma,harta da bayi tana dashi bayan katon Shashen dasuke zaune wanda yaji kayan alfarma.

Su Afiya kuwa sun girma don Suna da shekaru Shidda kenan Aduniya yara ne kanana ammh masu Tunanin manya mgana chakwai babu wanda basayi sun ruga sun saba da Baba lami da Maminsu Ni"ima Shiyasa Azeema in ba wani Abu sukeso ba,basa ma nemanta suna Sheshen Tsohon sarki Abdulnaseeer ko Shashen inna Ramatu ko wajen Ni"ima.,ayanzu haka Azeeema nda katon phamarcy acikin Masarautan wanda Aliyu yasa aka kirkireshi saboda ita da kuma karatunta aka Cikashi da mgunguna,duk Abunda ake bukata konawani mgani zuwa kawai za"ayi A nunamata da kanta zata je ta dauko mganin saboda tariga ta karantu akai.

Shekara Daya da da komawarsu Niger,Siyasa ta kusanto,kawu ya Fito takarar gwannan jahar kaduna cikin ikon Allah kuwa yasamu nasaran Hayewa kujeran gwannan jahar kaduna,ayanzu haka suna gidan gwannnati Abunsu,suna cikin Shekara na biyu kenan akan karagan mulkin.



  ********************

   Sarauniya Azeema ta zauna a kayatattacen Falonta wanda yaji kayan alfarma zaune take Akan wani Tuntu,jikinta sanye da wata alkayabba mai Ruwan zaiba,kallo daya zakamata ka Fahimci tsabar hutu da Mulki tare da jin dadi sun lullube Azeema,tare da wani girma kamar ba yar Shekara 28 aduniya ba,gefenta yar Amananta ne Baba lami,wacce haryanzu suna tare basu rabu Azeema na nan A uwar dakinta

Tuffa takeci Baba lami na gefenta suna mgana kan Wani lokacin achan baya Baba lami na bata lbrin ada ita batasan Tuffa ba,don ita ta aza wani Abu ne dabam,dan dariya Azeema keyi cike da Nishadi,sai ga Anwar ya Shigo da gudu bayanshi Afra ne basu dire ko"ina ba sai jikin Azeema Baba lami ke fadin "A'a megida meye yafaru kuma? wayar hannunsa ya mikama Azeema yana Fadin"Ummi wayarki wlh Tun dazu afra ta dauka tana miki game aciki,kuma Abbu sai kira yake"Karbe wayar Azeema tayi tana kallon Afra dake hararan Anwar,shiko yana mata gwalo,kunnenta ta kamo ta matse tana Fadin"Kin Rainani ko,bakijin mgana ta ko? har yaushe zance kada ki kara daukan min waya ammh bakiji ko,wlh koda wasa kika kara sai nasa sarkin dorina ya zanemin ke,wuce kibani waje.."Tafada tana sakinta,kuka ta fashe dashi ta Fada jikin Baba lami,itako tariketa tana lallashinta tana Fadin"Ke share hawayenki,so kike Maimartaba yace ya fasa auren,kefa matar sarki ce maza share hawayen"Tana Fadar haka ko ta Share hawayenta ta mike tinkis tinkis ta Fice sai Shashen su goggo tana zuwa Ta fada jikin Tsohon sarki Abdulnaseer,tana kuka rikota yayi yana fadin"waye mai tsautsayin daya tabamin ke? matse kwallah tayi tana Fadin ba"Ba Ummi bace ta min Fada ba..",Baki Maimartaba ya rike yana Fadin"a.hhhh babban mgana lalle dole Ummi zata Fuskanci Hukunci kinji share hawayenki kinji amaryata"goggo dake gefe ita da Gimbiya Fasilatu suka tabe baki suna Fadin"Wannan amaryan taka ta Cika shagwaba"cewar goggo,Mele baki Afra tayi kafin tace"Sarkina ka koresu su fita"Dariya maimartaba yayi kafin yace"Angama ranki shi dade..,kutashi ku fita tunda kunji Abunda Amarsu tace",Tashi sukayi dukkansu suna Fadin"Ko bakace ba gaka gata zaka nememu ne"Mirmishi yayi yana Fadin"injiwa Ga Amaryata ni ba wanda zan nema"Yafada yana dariya itako Afra ji'iran Yarinya harda musu gwalo.

achan bangaren Afra na Ficewa wayar Azeema ta sake daukan Tsuwa jin Riging tone din mai kiran kadai sai da ta murmusa,mikewa tayi tsam ta koma cikin bedroom dinta tabar Baba lami suna chasheta ita da Anwar dama dan Rigimar tane,sai ta fada bisa gado kana ta daga kiran Tana Fadin"Allah taimaki maimartaba mai mulkan mutanen agadez..."Mirmishi yasaki mai kayatarwa kafin yace"Kin Fadi jarawabawa pretty,cewa zakiyi maimartaba mai mulkan zuciyar Azeema Shikadai,da'ace kin Fadi haka Tun Farko da kinsamu wata kyauta.."Dariya tayi mai kayatarwa tana Fadin"ko ayanzu ban makara ba bari na gyara maimartabana wanda ke mulki tare da iko azuciyar Azeema ita kadai.."Dariyan Farinciki yayi kafin yace"Maki goma pretty..."Bata Fuska tayi kafin tace"kawai maki goma Yaya captain"saurin katseta yayi da cewa"ba kawai bane preety maki goman dana baki,sunfi maki darin da wani zaici awajen jarabawan Fita daga jami"a,yanzu dai duk ba wannan ba,nayi kewarki kwana biyu ne,wlh ko zaman Fada nakasa yi,shiyasa nace atafi hutun rabin lokaci,shine na samu daman kiranki.."Baki ta rike tana Fadin"a"a Mijina,kafasan sai gobe ne zaka dawo wajena,yau Ni"ima ce keda Turaka,don Allah ka zauna,karfa ka manta akwai hakkin jama"a dadama akanka,bani so ka zama mara adalci agaresu don Allah..."Shuru kawai yayi yana jinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan pretty zanyi Abunda kikace,Ammh wlh bazan boyemiki ba, nidai an cuceni an hadani da aiki ga Sarauta ga karin kwanaki kafin na kasance dake mtseww.."Kawai taji ya yanke kiran,ajiyar zuciya ta sauke tana Tunanin yaushene yaya captain zai rike Sarautar da Allah ya bashi,kullum cikin cewa yake shi an cuceshi anhadashi da aiki,daman ma tana iya bakin kokarinta da batason mai zai yi ba,tashi tayi tsam ta Wuce shashen Ni"ima don batajin dadi tun jiya tana ta fama da amai da zazzabi likita tazo ta gwada ta ta tabbatar da ciki ne da ita

Koda Azeema ta isa shashen Ni"ima chan ta sameta kwance su Jabir nata duduma kanta,shida Sajida,Ummah kuma na gefe tana wasa,Afiya babbar banza ta zaune kan kujera tana ta lissafin banza,domin itace sak mahaifinta kwata kwata bata da yawan Mgana,ko zasu kashe kansu bazata tataba tankasu ba,tsawa Azeema ta bugamata tana Fadin"zan makeki yanzunan,wawiya kawai kina ganin bata da lafiya bazaki iya hanasu damunta ba,ammh kina zaune kamar wata sokuwa.."Narke Fuska Afiya tayi kafin tace"To ni Ummi ya zanyi dasu.."Harara Azeema ta sakarma kafin tace"Maza kwashesu sukai su Shashen momy yanzu"Dakai ta amsa kafin ta mike taja hannun Ummah da Sajida jabir kuma ya bisu abaya,don sunsan hali Azeemar bata musu da wasa saboda taga kaf masarautan babu mai Kwabamusu yara,suna ta Abunda suka ga dama,karisawa tayi ga Ni"ima wacce ke kwance ta zauna agefenta tana Fadin"ya jikin naki Uwar biyu.."Yar dariya Ni"ima tayi kafin tace"Wata uwar biyu nima Ummi wlh bani son cikin duka duka Shekaran Ummah daya fa"Yar dariya Azeema tayi kafin tace"lalle nema Mami,toh Tun Wuri ki maida wannan mganar ki hadiyeta karki bari Maimartana yaji,don ranki sai ya baci,kin manta na sanar dake su Afiya nada Shekara daya na samu cikin Sajida,ki godema Allah bata da Wani rigima kina yayeta ki mikomin ita nan,in zasu tafi nageria hutun karshen Shekara su tafi ma da Ummah da takwaranta don tana nemanta.."Jinjina kai Ni"ima tayi kafin tace" To Shikenan Allah ya kaimu yakuma saukeni lafiya"Da Ameen Azeema ta karba kafin tafara kalle kalle tana Fadin"Mami nifa wlh ina jin kamshin maimartabana,anya baya na nan shashen kuwa.?

mikewa Ni"ima tayi tana Fadin"kema kinsani yanzu haka shashenki yaje bakinan,shine ya biyo sawu,dama ana Cika awa biyu baizo ya ganki ba,ai maimartaba sai yallabiyansa.."Tafada tana yar dariya ita ta ganshi Tun sanda ya Shigo falon,hannu yasaka mata abaki alaman tayi Shuru ya make bayan labule.

yar Dariya Azeema tayi kafin tamike tana Fadin"Au kema kin biyema su goggo ne,To shikenan ni kingama tafiya ta Tunda Abun hakane.."ko taku batayi ba yayi caraf ya dagata sama yana juyi da ita,ihu taso ta saka ya damke mata baki yana dariya kwabe Fuska tayi ta Maki rawaninsa sauko da ita yayi ya rike hannunta yana Fadin"Ke baki da kunya Sarki guda kike duka ko"Hannu ta daga takara makemai kewa tana Fadin"Bakajin mgana ko bance karka fito ba,sai angama zaman fada ba? Tafada tana murde kunnensa dake cikin Rawani,rike hannunta yayi yana Fadin"Wayyo Allah yi hakauri mama Azeema.."Yafada harda matso ido,gabadaya dariya Ni"ima da Azeema suka saka harda tafawa,hararansu yayi kafin ya hade rai yana kallon Ni"ima yace"Dukkanku kallon ku nake,kwana biyun bawacce ke kula dani,ke ya nuna Ni"ima Tunda kikayi ciki shikenan kifara lalaci baki da aiki sai barci da kwanciya,ke kuma ya nuna Azeema,baki da aiki sai yima yara Fada da dukkansu,da anyi mgana sai kice kada abarsu su sangarce,ammh ga aikin mijinki bakya yin ko daya,Allah Zaku sani ne,Aure zan kara dama Sarkin Garin dosso yamin Tayin Diyarsa gimbiya Aisha.."

Azeema ce tayimai wani kallo tana Fadin"au Allah to sai me,Toh Allah kawo ta lafiya ko tazo mungama kwashe romon da sauran wani mazantakan ka sai dai Ta auri saura wlh ko Mami?"Kai Ni"ima ta gyada tana Fadin"Mema zatayi da Tsoho wanda duk baki yacika da goro.."Dukkansu suna mgana ne yana musu wani kallo,sai da suka gama kana ya rike baki yana Fadin"Kutumelisi,ke yanzu nine zaki kallah kice kungama kwashe romon ko? lalle

Please Login or Register in order to submit comment