Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mufara da kwalliyah, girki wannan sai anjuma zamu Shiga kichen Shi pratical zamuyu kingane.."gyada kai Azeema tayi kafin Anty madina ta Furta..

  

*KWALLIYAH..* ita kalmar kwalliya ko ahausance sai da aka kawatata kafin Afurta,Ita mace kuma dama asanta yar kawa da kwalliyace,kwalliya kala kalace,akwai wacce akeyin wanka kawai asaka kaya Shikenan,anyi kwalliya toh ni ba ita nake Nufi ba Azeema Firstly Ki lakanci kayan da in kika saka Suna amsanki,riga da Sikat ne,ko kuwa Riga da zani ne? Doguwar rigane? ko kuwa kayan Rumgumar darling ne,ma"ana kananan kaya na zaman Falo,da inda kika karanci Kayan da sukafi fitar miki da Sirrin kyau sai ki lazimci dinka ira irensu,bayan nan kada ki dauka ance kwalliya ki zata wannan kwalliyan ta zamani ne data Fito ta hauka,ki saka Foundation ki zamo aljannah garin gyaran ido ki Rasa gira,No ba ita ba Simple make up,wacce da an kalli mace asan ta san Abunda take,kuma kallon Fuskarta zai sa agane kedin classic ce,ki shafa hodarki sai jambakinki wanda yayi daidai da kalan kayanki Shima kada ki cika,ki laziminci sanya kwalli domin Farin idon mace bai da kyan gani,ki koyi kashe dauri kala kala domin burge mijinki koyi salon Tafiya mai daukan hankali duk zan koya miki wannan,Ki sanya dan kunne da sarka ki sanya awarwaro,da Sauran kawan mata kada kibari mijinki yadinga shakan wari ajinki basai kin zama kwado wajen wanka ba,kiyi koda sau biyu Arana da wankan gaisuwan Safe da waankan barka da dawowa megida,wankan safe ta Kayanmu na hausawane Atamfa ko leshi,ko wht ever dai,da yammah kuwa english wear ne,mai wando ne mai sikat ne,sai dai wanda kika zaba duk dayane ya kasance dai koya kika gilma kamshi ke binki shiyasa duk Rinti duk wuya kada ki Rasa humra ko kiyima Turare yaji sam kada ki Fara Azeema domin kamshin na jan Hankalin Namiji zuwa gareki tare da Kara dankon kauna,sai Abu na gaba
 

*IYA SALON MAGANA.* Kefasan akwai dayawa matan da basu iya mgana da miji ba,wata in tana mgana da mijinta kamar tana mgana da wani kaninta ko tsaranta ba karya harshe ba Tautausawa ba girmamawa bawani karkwasa balle wani Shagwaba a"a sai dai kawai damkam dinkin kamar wata Sauna ko sakarya yakamata mata su gane harshenki yazamanto kala kala ne,ma"ana harshen da zakiyi mgana da mijinki dabam,wanda zaki amfani dashi wajen mgana da kawarki dabam,wanda zakiyi da makotanki dabam,kai kowa kinsan yadda zaki karya harshe ki iya salon mgana dashi Sai kiga kin zama mace mai aji da kima a idon Jama"a,mganar yadda zaki karya harshe wajen Miji Shine First look at me Azeema kamar ace kene Abban Hidaya muna zaune haka kamar zanyi mai wata mgana mai muhimmanci abu na Farko sai na Fara jan Hankalinsa zuwa gareni,bayan na kuramai ido na langwabe wuya gefe daya na marairaice To indai yaga kinsamai ido haka zai bar dukkan Abunda yake ya tambayeki"Noor meya faru ne?Zaki Fara rigimarki ko? ke kuma dagajin haka sai ki shagwabe Fuskarki da muryanki kice"Abban hidaya ya mganarmu Ta Ranar naji haryanzu bakace komai ba.."Ki karishe kinamai Fari da ido,toh lokaci daya zaki ga ya Rude yana tambayanki wata mgana,ke kuma sai ki kalailayeshi bisa jikinsa,domin yin nesa da Jikin miji na rage Shakuwa Shawarata gareki Jikin yaya captain yazama wajen zamanki matukar yana gida ta hakane body contact dinku zai Shaku da juna,kuma shi Namiji yanason adinga mannemai ana lafemai bisa jiki,kin Fahimta..? ajiyar Zuciya Azeema ta Sauke kafin tace"Na gane Anty madina.."ta gyda kai tana fadin"Naji dadin jin hakan yanzu bari muje gaba lokaci na Tafiya,Abu na karshe kuma wanda yafi muhimmanci Shine
 

  *SALON KWANCIYA..* Zaro ido Azeema tayi Da Sauri tana Rufe baki da hannu hararan wasa Madina ta mata Tana Fadin"Stop joking Azeema Abu ne mai muhimmaci infact ma Shine ginshikin Aure,so u better listening very carefully don zai miki amfani ki cire kunya domin dama rayuwar aure sai ka cire dukkan wata kunya kake iya mace mai aji da Kima a idon mijinta.."Saurin gyada kai Azeema tayi,kafin Anty madina ta dora da cewa

  "In Akace Salon kwanciya ba Ana nufin komai bane illah yadda zaki iya Salo salo tare da hikimar Sarrafa mai gida A Shimfida,Na farko bawai ki zama wata dussa ba,kina kwnce duk inda miji ya juyaki ki juya kamar wata bichan No ki zama kece kike jan Ragamar Abu kezaki dinga sarrafashi Ta salo kala,kala wanda zai gane yes yana tare da cikakkiyar mace wacce ta san Kanta,ki sance wacce zaki jiyar da mijinki dadi takowani Fanni,ki sanyashi yayi miki kuka harda koke koke,ki sakarmai jiki,shima ya sakar miki kada kiji kunya ki saki jikinki ki Tsotse mijinki daga sama har kasa,shima haka kuskuren da mata yakeyi Shine sai ga mace wai sunyi Fada da miji sai kiga ya nemeta Shimfida,wai Saboda yabata miki rai sai kiga mace tayima namiji sharaf yayi yadda yagama dama dake,bawani Taimako,toh hakan kuskure ne,wlh yana kawo tsana koda bata miki rai yayi,in kika tsage kika farantamai wlh tallahi da kanshi zai gane yayi Kuskure har yabaki hakuri,Azeema sai kin dage sai kuma kin zage damtse,domin Duk cikarki mace matukar baki gyara chan headquater ba duk abanza,kinga magungunar dana baki kina amfan dashi,duk dakaina na hada kayan Ni"imar mata ne,Kayan Gona ne,sai su aya dasu dabino,sai su kanunfari da Sauran itatacenmu,kada ki bari Fruit yadinga Wuceki duk Rana,ki lazimci Shansu akoda yaushe,domin Babu Abunda yakaisu kawoma mace Ni"ima kamar Shi,ga madara ga zuma koda baki dashi siya madararki ta sajet kullum na Hamsin ki dinga kalata da zuma duk safiya ki dinga sha kigani wlh sai kin bani labari,ammh yanzu mata sun Haukace da mganin mata kamar ibada,Abun haushi ma sai wani lalacewa Daya Fito yanzu sai kaji ance wai kashin tantabarama mganin mata ne kasiddan,ke kuma don kina wawiya Tantabara ta Fitar da cuta ke kuma ki siya,ki dinga Turawa kamar wata zararriya wlh mata mu Farka da wannan Siya siya dakikeyi da sana"a kikama da kudin daya fiye miki wlh domin yanzu kishinki Abun hannunki dakuma yadda kika dauki Aurenki,matukar Baki da sauran Abubuwan nan,koda mganin dubu dari zaki sha wlh kullum Asauna zai dinga kallonki,babu wani cigaba sai ci baya daga Karshe sai kifara Tunanin kila an samiki hannu ne,toh in zaku Farka tuni ku Farka kikama Allah da manzansa ko kya rabauta Ranar gobe kiyama..."Jinjina kai Azeema tayi tana Fadin"Tabbas mganarki haka take Anty madina kuma nayi miki alqawarin insha Allahu bazan baki kunya ba.."Damke hannunta madina tayi tana fadin"Yauwa matar yaya Naji dadin jin haka,yanzu mike muje Falo na koyamiki salon tafiya masu jan Hankalin maigida So nake ki rikitamin yayan Nawa fa.."Tafada tana Dariya da Hanzari suka mike atare suka rankaya zuwa babban Falon Gidan,wanda Tuni mai aikin ta tsaftaceshi,takoma kichen tana wanke wanke kwanuka.

Anty madina ta dage sai koyama Azeema salon Tafiya take,da yadda zata dinga mgana cikin jan aji da shagwaba,bata barta ba sai da ta tabbatar da ta iya kuma ta kwatanta kana ta kyaleta,daganan taje ta kwanta itama tace taje ta kwanta sai zuwa anjuma su Dora daga inda suka tsaya.

    ********************

""Kokafin Sati daya tacika Tuni Azeema Tazama yar gari,in ka ganta bazaka iya ganeta farat daya ba,tayi haske tayi kiba fatarta ta goge sosai,ga iya daukan dressing ga Tafiyar Daukan Hankali salo salo Natafiya da Da Namiji ba wanda Azeema bata sani ba,salon kwanciya kuwa ta haddace kaloli sunfi kala ashirin wanda Anty madina ta zage Ta nuna mata su pratical Tagani kuma ta kwatanta mata,Hakika Azeema ta karu da Anty madina ta bangarori dama,ta bangaren iya girkin zamani,snaks,ne da Abincimu na gargajiya ba wanda Azeema bata iya ba,ga Shi ta koyi iya zama da kowa yanzu ga iya karya harshe kamar wata uwar mata,domin yanzu Tuni mganarta yakoma shagawaba shagwaba saboda yadda ta haddatu,bangaren gyaran jiki kuwa har dilka Anty madina tayi, mata,magungunarta kuwa tun kafin satin su cika Azeema tasan ta zama mace domin kowani gaba na jiknta yanzu yana bukatar motsawar da Namiji ne,ga Ni"ima da Allah ya zuba mata wuni take chanza pants😂saboda yoyo,ita kanta Madina tayi mamakin Saurin daukewar da Azeema tayi komai cikin lokaci kadan,Shiyasa Aranar data cika sati Anty madina takaita wani shagon kwalliyan mata aka yi mata gyaran kai da kunshi mai kyau da daukan Hankali,zanen Fulawa hannu da kafa,ja da baki,nan da nan Azeema ta dawo taraurauwa, Satin na cika Ummah ta kira Madina tace  tadawo da ita yau goggo tace su mikata dakin Mijinta,madina bata Haufi kan Azeema ba domin tasan bazata ta bata kunya ba,tuni ta hadamata kayanta cikin manyan akwatuna guda uku wanda Ta siyamata,Tuni bose ta kawo Dinkunan data dinkamata,tare da kananun kayan data siyamata hade da kayan kwalliyanta da duk Abunda zata bukata,Ita kuma Azeemar Ta Shirya cikin wata Atamfa milk da zanen ja ajikinta dinkin Riga da Sikat,wadanda suka kamata sukayi mata cas dasu hip dinta da boobs dinta duka sun bayyana ta cikin kayan,ta Daure gashinta da band dinta bayan ta kafe kanta da Daurin zara buhari,fuskarta da make ammh simple one ne,kafarta sanye da takalmi half cover ja,haka jakarta sai mayafinta ma ja ne,tayafoshi bisa kanta wanda kallo daya zakamata kasancewa eh lalle wannan Azeemar ba itace Azeemar nan ta gombe ba,wannan Azeemar Kaduna ce,domin wayewa tare da wani kissa da kisisina na mata Tuni Azeema tayi haddanshi,ko yadda take takunta kadai ya isa masu karatu ku gane cewa Azeema fa tayi Shiri sosai kan zama da yaya captain,Karfe Hudu direba ya kwashe su,ita da Anty madina da yara Harda mai aikinta gidan gabadaya suka tafi,kusan tare suka Isa gidan su da Anty mardiya wacce tazo itama amika Azeemar gidan yaya captain da ita.

  Ita kanta Anty mardiyan bata iya gane Azeema ba ,sai da Anty madina Ta sanar da ita,rike baki tayi tana mamakin wannan al"amari lokaci daya ta Tahau jinjinama Madinar saboda Namijin Kokarin datayi akan Azeemar,atare suka shiga babban Falon gidan inda suka tarar da Ummah da Baba ade sai goggo suna zaune suna hira,Suka Shigo madina da mardiya sune kan gaba,sai Azeema dake bayansu tana rike dasu hidaya dakuma ya"yan Anty mardiya,Ummah tatashi tana faman Tarban ya"yanta cikin Farinciki,har Azeema Tashigo ta gaishesu ba wanda ya Shaidata Itako ganin haka sai ta koma gefe tana Wasa dasu hidaya Ummah ce ta kalli Azeema tana fadin"Madina hala wannan Kanwar megidanki ne.."kallon juna sukayi su duga ukun kafin Madina da mardiya su kwashe da dariya goggo ce ta katsesu da fadin"Wai ni ina diyatace banganta ba..? Dariya madina ta saka tabama Mardiya hannu suka kashe,kafin mardiya tace"gaskiya na jinjinama madina,yanzu ko dukkanku ba wanda ya gane Azeema? galala suke kallonta kafin Goggo tace"ina Azeemar..? Azeema dake gefe ta daga hannu tace"Gani fa anan goggo Tundazu nake kallonki ammh sai naga kamar baki gane ni ba.."Tafada tana yar dariya.

  Ai gabadaya goggo da Baba Ade da Ummah Suka saki baki Suna bin Azeema da kallo,madina ta mike tana fadin"Azeema tashi ki juya musu su kara ganinki da kyau.."cikin kunya Azeema ta mike tana juyawa,ai bata gama ba Ummah ta mike ta Rumgumeta Tana fadin"Job weldon makka da madina wlh kin yi aiki mai kyau Allah ya biyaki.."goggo ko fadi take"Azeema tace tadawo haka? lalle yanzu bani da shakka akanki diyata,Madina Allah yayi miki albarka kin cece aure Allah yayima Rayuwa albarka."Haka Baba ade keta kwararama Madina da Ummah addu"a Ummah ce ta mike tace"ya kamata muyi harama kafin dare yayi ko? Madina tace"Ummah Ni da nace nida mardiya mufarayin gaba saboda gyare gyare da goge Tunda dai mace bata taba zama agidan ba,dole gidan yana bukatar gyara,in mun kammallah sai mu kiraku awaya sai ku taho da Azeemar.."Jinjina kai Ummah tayi kafin tace"Eh kuma fa kinyi mgana,to ku hanzarta sai mu mu taho daga baya.."Jin Haka yasa Madina da mardiya suka mike kowacce Ta dauki jakarta,tare da yar aikin Madina suka tafi yara kuma suka makalema Azeema sai ummah tace abarsu,direba ya kwashesu tare da akwatunan Azeema da Sauran kayanta,Koda suka isa barikin Sojojin dake babban get basu barsu sun Shiga ba,sai da madina ta kira yaya captain tace gasu abakin barrak dinsu,an hanasu Shiga,cikin lokaci Captain ya yi musu waya sai gasu madina abakin apartment din Aliyu nan suka tarar da Aliyun da jabir suna tsaye,dukkansu sanye da Fararen kaya riga da wando masu tambarin Army daga gani suna wani Training ne,da hanzari Aliyu ya isa garesu sukuma suka firfito suna gaisheshi ya amsa yana tambayansu ya yaransu,bai tsaya wani mgana ba,ya mika musu makullin gidan yana fadin"Ga key din nan,already koda kuka kirani muna kan wani aiki ne.."karba Madina Tayi cikin girmamawa,wucewa yayi Shiko Jabir ya tsaya yana gaisawa dasu yana mamakin mai ya kawosu,nan take Shaidamishi Azeema ce zata tare anan barikin,baki Jabir ya saki yana mamakin Aliyu don ko alama bai taba Fadamai ba,koda ya tambayeshi mai su Madina zasu zo suyi cewa yayi bai sani ba,Shi yakarasu har kofar gidan kafin ya juyo yabi bayan Aliyu da gudu har ya cimmai yana fadin"Sannu uban yan Sirri ko nace bakin munafiki boyen mai ake mana,toh naji Ashe zaka samu wajen hutu ne ba lbri.? ko kallonsa Aliyu bai ba harma ya cire rai da zai yi mgana sai chan yaji yace!eh taya zan gayamaka Tunda kai yaro ne,haryanzu baka girma ba,ka bari in ka kara kwari mayi wannan mganar.."baki jabir yakama yana fadin"kutumar ubanchan Ammh fa ka raina min wayau,kalli Mazantakana dakyau yasin tafi taka kwari da juriyan wahala.."Kallonsa Aliyu yayi kafin yace"Allah ko,kenan ka jaraba ka gani,"Eh na jaraba mana,.."yar dariya Aliyu yayi kafin yace"eh lalle ka lalace kenan kana Shigo da wata ciki kenan da daddare...? kallonsa Jabir yayi yana fadin"ina kenan..? ciki gidan ka mana,kana jarabawa...? baya Jabir yaja yana Fadin"Allah ya isa da sharrin daka kullamin,ni ko Rumgume mace bantabayi ba."kai tsaye Aliyu yace!"Toh kagani haryanzu da Sauranka yaro,Kabari ka girma ma tattauna mganar.."daga haka ya wuce yabarshi nan yana Duramai zagi harda Allah ya isanshi Abun yamai zafi,duk kwanan karfin halin dayakeyi ammh gayen chan yacemai yaro Tabdijam dole ya mike tsaye.

  Su madina Sunyi Abun da himmah,basu dauki wani lokaci ba suka tsaftace gidan gabadaya,duka bedroom din guda biyu sun lailayesu da zannuwan gado masu kyau da ban Sha"awaa,Falon kuma sun gyare komai duk da gidan bai yi kura ba Sosai,sai kichen shima suka gyarashi Suka tsaftace ko"ina suka kunna Turaren wuta nan da nan gida ya kaure da kamshi,suna gamawa suka kira Ummah sukace su taho,daman Suma Ashirye suke hijabi kadai suka bama Azeema ta sanya suka Fito suka tafi Direba ya kwashesu sai cikin barraks,Suma din sai da aka tsaidasu aka kira Aliyun da kanshi kafin su samu Shiga cikin barikin,Sai gasu har kofar apartment din Aliyu Wani soja ya kawosu,Su madina suka Fito suka taresu zuwa cikin gidan,Da kafar dama Goggo ta umarci Azeema data Shiga gidan,basu direta ko"ina ba sai bisa makeken gadon gadanga Domin ga alamu nan ya nuna dakin yake kwana,saboda wardrope din dakin cike da kayan sawanshi,yawata gidan Su goggo suka fara suna saka albarka,Itako Azeema Tuni Madina ta sakata ta hince ta fada wanka,kafin ta fito sun Fito mata da kayan da zata sanya Wani Fefa less Orange ammh light dinshi,dinkin Riga da zani,rigar half jamfa ce,ammh fa yayi kyau sosai bata Daura Dankwali ba,Sai gashinta data Daureshi da band,sai wani babban Orange din vail mai duwatsu ammh yana da Sansti sosai bisa gadon daya sha Zanin gadon alfarma,suka zaunar da ita bayan Sun Fesheta da Turaruka masu kamshi,tuni ko"ina na gidan na tashin kamshi,Madina da mardiya suna ciki suko su goggo suna Falo,Ummah takira Aliyu tace sun gama zasu tafi,ba a dau wani lokaci ba Sai gashi sun Shigo shida Jabir,wanda duk wulakancin da gadanga kemai bai hakura ba sai da ya biyoshi.


Am Srry For d Typing errors bansamu lokacin Editing ba.

        
        #Comment,share,and vote...#
       #Janafty,Aka Shakira...#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*Wannan Shafin nakune, AISHA SULAIMAN😘,Dake da AMEENA ISAH..Abokan Aiki😂😹Allah kara hazaka malaman mkranta,😝Endless of Love Habibaties*

       *Chapter 19*

    """Dukawa har kasa sukayi dukkansu suna gaishedasu goggo da Ummah da baba Ade,sukuma Suna amsawa cikin sakin Fuska da Annushuwa Jabir ne yace"Ashe goggo kuma Azeema zata tare,? toh Allah yabasu zaman lafiya.."Goggo ta karba da "Amin Amin Jabiru saura kai,yakamata kaima ka fito da matar aure hakanan zaman gaurancin ya kare ko.."Dariya yayi yahau Sosa kai Aliyu ne yayi caraf yace"Goggo wannan yaron kikema mganar Aure,tab ai bai isa ba tukunnah.."kafa Jabir ya sa ya tokari Aliyu yana Hararansa kafin yace kasa kasa"Sannu wanda ya isa.."dariyan mugunta Aliyu yayimai kafin yace ahankali yadda da Bawanda zaiji"Gashi kaga alamar isar tawa.."ya fada yana nunamai Dakin da yaji Surutun su madina ciki da ido,tsungulinsa Jabir yayi har sai da yasa kara yana sosa wajen,Suko Su goggo basu gabe zun zata wata mganar arziki sukeyi.

  Ummah ce tace"Toh gadanga mufa zamu yi harama.."sadda kai yayi yana fadin"Tun yanzu Ummah baku bari sai anjuma.."baki Ummah ta rike tana fadin"wane mu Rufamin Asiri yanzu ma bakajin Fadan da kawunka yake tayi ba wai meya zaunar damu haryanzu bamu dawo ba."goggo ta karbe da cewa"Atoh da gaskiyansa muma jibi jibin nan zamu koma inda mukafi wayau.."kai tsaye Aliyu yace "Goggo ai ke kinzo kenan bazaki koma ba.."Kada kai tayi kafin tace"Toh ubana Shehu.."gabadaya dariya suka kwashe jin kalaman goggo,shiko gadanga murmusawa yayi kawai,Ummah da kanta ta Shiga ciki ta tararro Su madina tare da Azeemar suka Fito falon gabadayansu goggo ta hada tayi musu nasiha mai kashe jiki daga karshe tayima Aliyu jan hankali mai hade da gargardi akan ga Azeema nan Amanace agaresa in yaci Amanarta toh ya sani Amanar Allah zata cisa,bata da kowa sai shi sai Allah sai kuma su Ummah,wanda goggo ta dankamata amanar Azeema,ita kuma ta saka hannun bibbiyu ta amsa,Aliyu yayi alqawarin rike Azeema bisa Amana da gaskiya,koda akabama Baba Ade damar mgana kasawa tayi saboda kuka godiya taitayima goggo da gadanga kafin takoma tana sanyama Ummah albarka,Azeema ko tafadamata in ta kuskura ta sabama mijinta da gangan Allah bazai kyaleta ba,Azeema tana ta kuka,kukan Farinciki da kewan rabuwa da goggo,bata kara tsinkewa da al"amarinsu sai da suka mike zasu Tafi,nan fa Azeema tace batasan wannan zencen ba tamakale goggo tana kuka,wanda duk dauriyar goggo sai ta koka da gudu ta fito daga gidan Tana Share kwallah,Ummah ce ta umarci Aliyu daya rike Azeemar wacce ta ki sakin hannun Baba Ade,ta bayanta yaje ya Rumgumota dakyar ya bambare Hannunta ana Baba Ade,Jabir ne yatafi rakasu zuwa bakin motocinsu Sukansu su hidaya kuka suke wai sai sun zauna wajen Anty Azeema,madina na dariya ta iza keyarsu tana fadin"Kajimun yara da ballo Ruwa oya ku wuce muje gida gobe sai na saka direba yadawo daku.."kowanne amotar dayazo yakoma Mardiya daganan bata koma gida ba direban madina ya Sauketa gida ita kuma ya karisa da ita gida su kuwa su goggo suka koma gidan kawu cike da Murna tare da kewar Azeema dashi kanshi gadangan.

Jabir daganan bai koma gidan Aliyu ba ya Shige gida yana Fatan zaman lafiya atsakanin ma"auratan biyu,Shiko Gadanga daga lokacin daya Rumgume Azeema yaji wani Fitinannen kamshi ya ziyarceshi wanda sai da yasakashi ya lumshe ido,saboda yadda kamshin yake bin kofofun Hancinsa,Akasalance Aliyu ya isa ga Azeema ya zaunar da ita kan kujera yana bin ta da kallon yadda gabadaya ta cikwukwiya kanta jikin mayafin dake jikinta,Bai mata mgana ba, kawai sai ya samu kanshi da dukawa agabanta ya saka hannu yana jayemata mayafin yana fadin"Cire sai kiyi kukan da kyau,wannan sai ya tare miki kofar Numfashi.."Yafada kai tsaye Jin Abunda yace da kuma kokarin zare mata mayafin dayakeyine yasa ta tsaya da kukanta cak tana Sauransa jin Abunda yace ne,yasa ta sakarmai mayafin ya ida zameshi sai ga kanta ya bayyana tare da gashinta,wanda wajen zame mayafin Ribon dinta ya biyo,tuni gashinta ya bazu bisa gadon bayanta,yanayin gyaran gashin ne,yasa harta gaba ya zuraro ya rufemata ido,Galala Aliyu ke binta da kallo yana tamtamar kamar ba Azeema bace an samu saba nomba,saboda Mamaki,hannunta ya riko sai yaji wani santsi da laushi tare da wani dumi ya ratsashi Sakinta yayi da Sauri yana binta da kallon harda leka Fuskarta ganin haka ne yasa tayi mirmishi ta sanya hannu ta maida gashinta baya idonta karaf acikin na Aliyu wanda yake durkushe gabanta,baya yaja yana kallonta,itako kai ta lamgwabe Tana wani narkewa kamar wata mara lafiya,Da hannu Aliyu ya Nunata yana Fadin"Wai..Wai Az..Azeema ce? yafada bakinsa na rawa.

Mirmishi Azeema ta saki kafin tayi wani Far da ido tace"Eh Sunana Azeema buh found of correction yaya captain wannan ba Azeemar gombe bace dis one na be Azeemar kaduna,kadunan ma wacce tatare adakin mijinta yau.."Zaro ido Aliyu yayi yana bin bakin Azeema da kallo kalamanta sun basa dariya wanda baisan sadda yayi zaman yan bori agabanta ba,harda dora duka hannuwansa kan ciyarta yana dariya har saida duka hakoransa talatin da biyu suka bayyana,Azeema saboda mamaki itama shagala tayi ta kallon Aliyu saboda yadda Dariya tayi matukar yimishi kyau,nunata yakeyi yana dariya kafin ya hau tafi yana Fadin"woww..Very good Wato Ba Azeemar gombe bace ko? wannan ta kaduna ce..? gyada kai Azeema tayi tana lamgwaba kai hannu Aliyu ya mikamata yana Fadin"Congratulation Azeema.."mikamai tayi ayangance kafin tace"Thanks you.."Tafada tana matse hannunsa har sai dayaji alamun haka ajikinsa,Saurin zare hannunta tayi kafin ta dauki mayafinta ta maida tana fadin"Au na manta bakayi siyan baki ba.."kallonta kawai yake yana mamaki,shifa haryanzu bai gama tantancewa Azeema ce tadawo haka ba,mikewa yayi daga kan kujera ya zauna kusa da ita yana fadin"Au hakane fa Zeema kaduna,toh nawane bakin na siyeshi yanzu.."yafada yana lekan Fuskarta Shikanshi yana mamakin yadda ganin Azeemar ahaka take bashi wani Nishadi da Farinciki

 

   "Ta cikin mayafin Azeema ta karya murya tana fadin"Ba da kudi nakeso ka siya baki na ba,da Abu mafi daraja nake ka siyeshi yanzu nan."Tafada tana lankwashe murya Mirmishi Aliyu yayi kafin yace"Meye shi indai na mallakeshi ni zan baki shi yanzu.."kai tsaye tace" *ZUCIYARKA...*"..."Dam gaban Aliyu ya buga yayi kasake yana kallonta,itako tana kallon yanayinshi ta cikin mayafinta ganin yadda yayi yasa tayi Saurin cewa"karka damu in bazai Samu ba yau,zan bika bashi ko zuwa gaba zaka bani kayana,Kayi alqawari..? kallonta yake kai tsaye yana mamaki wai yaushe Azeema ta iya mgana cike da Tausasawa haka,kai gyada ya mata kafin yayi mgana ta mikamai hannunta dayasha jan lalle da baki tana fadin"mu kullah..."Hannun yabi da kallo kafin ya mikamata nashi ta sarke,lokaci daya tare da zare mayafinta ta barshi iya kafadanta,idonta ta saka anashi ayayin da Shima ita yake kallo,gabadaya wani yanayi ke fuzgarsu kuma sun kasa dauke idonsu akan juna wani Shauki na dibamsu,Azeema tayi kokari zare hannunta ammh Aliyu yaki Saima kara damke hannunta da yayi,Rausayar dakai tayi tana binsa da kallo tare da kayan jikinsa baki ta tabe kafin tace"Lalle ni Aure na ya bambamta da kowacce mace,hakama tarewata ta farko,ata biyu ma da bambamci sosai.."Tafada tana kallonshi gira yahade yana kallonta kafin yace"meyasa kikace haka?kai Tsaye tace"Saboda daren Farkon kowata amarya acikin bedroom ango ke tarar da ita,Ammh sabanin ni afalo angon nawa ya tarar dani,kuma kowacce amarya Ana siyan bakinta da kudi hannu,ammh nawa bakin abashi aka Siyeshi,abu na karshe kowanni ango yana Shigowa dakin Amaryarsa sanye da Manyan kaya harda babban Riga hannunsa kuma dauke da kayan ciye ciye,ammh sabanin nawa ango sanye da kakin Sojoji n...."Dariyan Da gadanga keyi ne ta dakatar da Azeema da mganarta,ta kuramata ido tana kallonsa Shiko gira ya dage mata kafin yace"Matar Soja kenan,komai Nasu na dabam ne,buh dont worry indai manyan kayane bari naje na sauya, mganar kayan ciye ciye kuma mai z
azaki ci,yanzu zanyi waya akawomiki,Tunda na lura wannan Azeemar ta kaduna da gaske takeyi.."Yar dariya Azeema tayi cike da Aji tace tana mikewa"Lala,Ai kuma indai yayi kwantai to sai da kowa ya hakura ni ban cika cin mike ba.."Tafada tana Fadawa bedroom da kallo Aliyu ya bita yana mamkin Azeemar gabadayanta.

  Tana Shiga bedroom din tayi Saurin Fadawa wanka Umarnin Anty madina ne,ta dade a tiolet din tana wanke lungu da sako na jikinta kafin ta fito,har ta fito Aliyu bai Shigo ba,ammh taji motsinshi afalo,a gurguje ta Shafa manta mai hade da Turaranka kamshi ta bulbule kowani lungu da

Please Login or Register in order to submit comment