Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saurin katse katse kiran tana dafe kirji kunya duk ya kamata.

Shiko daganan cikin gidan ya Shigo su goggo suna Falo ya gaishesu Rasa inda Azeema take yasa ya kira hibban madina ya tambayeta akunne,Nuna masa sama tayi alamar Tana Upstairs,Sosa kai ya Shiga yi kafin ya mike rike da hibba ya fara Taka Steps,dukkansu nuna sukayi basu gansa ba,kowcce ta dauke kanta,su Zafira suna ankare da yayan nasu,suna danne dariya,Sai da yakawo kofar dakin kana yace ma hibba"Toh maza koma wajen goggo yanzu zan dawo.."Jin haka yasa takoma da gudu tana murna,murda kofar dakin yayi ya Shiga da sallama,tana zaune kan gado,kanta babu dankwali tayi tagumi don bata zata zai zo ba,ganin ya Shigo yasa tadawo natsuwarta harda wani juya baya,Ganin haka yasa yayi Saurin karisawa gareta ya rikota yana Fadin"Am Srry pretty... ba gani ba.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,Jin yafara chanzamata yanayi yasa ta saki jikinta itama ta rumgumeshi tana Shakan kamshinsa harda su lumshe,Matseta yayi yana Fadin! I miss u pretty.."Miss u more and more Yayana.."Kamkame juna sukayi kafin sufara sumbatar juna kamar wasu mayunwata,Azeema fa ba dama,domin Ture Captain tayi ya fada gefe tabishi ta danne tana wani kallonsa ta gefen ido,idonsa ta sa hannu ta rufe kafin ta hau zare kayan jikinta bata barshi ya bude ido ba,sai da yaji tana zaremai Rigar Shirt din dake jikinsa,Bai yi gaddama ba ya taimaka mata suka cire duka kayansu blanket ya jamusu suka Shige,Yau Azeema da zafinta take kai Farmaki Shiko yana Neman kare kansa,kafin kace kwabo an lulu barnin da bakowa ke zuwa ba Sai me rabo,.

Tsawon minti talatin kafin su samu Natsuwa Rumgumeta captain yayi yana saka mata albarka domin Duk sanda zai kusanci Azeema ji yake babu bambamci da daren Farko,abunka da mai Shigar ciki tare sukayi wanka kafin yayi wanka tsarki ya fito ya barta itama tayi,kayan jikinsa ya maida,sai lokacin kunya Abunda suka aikata ya Shigeshi yanzu taya zai iya Ratsa mutanen falon ya Fita haka dai ya kukan Kuran Fita,domin alokacin anata kira kiranyen sallar mangariba,Yana Fitowa yaci sa"a babu kowa afalo,sai su hibba suna wasa,Da hanzari ya sauko ya Fice,yana Fitowa yaci karo da su Haisam suma sun Fito zasu masallaci,suna ganinshi suka tsaya suna kallonsa yake yayi musu yana Fadin"Muje mana,ba sallah zaku ba.."Haisam ne yace ahankali"Kayi wanka kuwa..? zaro ido yayi kafin yace",Wankan me? Jabir ne ya duke yana kallon Umar kafin yace"Wankan Janaba mana.."wani dogon tsaki Aliyu yaja yana fadin"Janaban Ubanka,kudai yan iskane idonku na kan Sunnah kuna saka ido,kuka sani ni banda lokacinku kunga tafiyata. "Yafada yanayin gaba,suko suna mai dariya,Umar dake gefe yana dariyan yadda yaya Captain din ya hade rai,wai shi dole tsare gida har sukaje masallaci bai kulasu ba wai shi adole bayasaon Raini,cikinsu maimartaba dasu Kawu ya Shige dasuka mai mgana yace"Gaskiya ya lura zaman dayake acikinsu ma zubar dakaine,a mtsayinshi na magidanci mai mata harda ciki,sukuma amatsayinsu na yara kaskancine,kawai su kama kansu shima yanzu zai chanza taku ne,gwara yafara zama cikin manya Shine mutumcinsa"baki Haisam ya rike yana fadin"Kut..Kai wai ban girmeka ba..?"Wani banzan kallo Gadanga ya jefamai kafin yace"Koda ka girmeni ai baka halliceni ba.."Yafada yana wucewa ya barsu suna zaginsa shida jabir,Aransa yace",Na bar kara zama cikin yara daga yau.."yafada yana yar dariya😜😹

Tun Adaren Aliyu ya samu kiran Ni"ima Tana mai murna,bayan itama harda mahaifiyarta tabamawa mami,wacce ketayashi murna itama amsa musu yayi kafin yayi musu godiya suka yanke kiran,Shuru yayi yana Nazarin wani Abu kafin ya saki ajiyar zuciya yana ayyana Abubuwa dadama.


Washegari suka wuce birnin zaria,A Fadar maimartaba suka yada zango,Maimartaba sarkin zazzau yaji dadin wannan ziyarar ta Sarkin Agadez maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yace dama yaji lbrin zuwansa bai zaci zai zo har Yankinsa ba,An gaisa cikin mutimci sosai kafin wasu jawaban su biyo baya,Maimartaba sarkin zazzau yayi mamaki wai sarki guda ya zauna agarin zaria abaya,lalle Allah mai hikima da kari,su jabir kam sai zagaye masarauta suke,suna fadin"daliin kaza gadangare kansha Ruwan kasko,yau gashi dalilin gadanga sun shiga masarautu dadama,haka su madina ke Fadi,ummah ko baki yaki Rufuwa godema Allah kadai take,domin dalilin goggo sun taka in ba basuyi tsammani ba,daganan Fadar tare da rakiyar Adalin Sarkin zazzazu suka iso anguwan dasu Goggo suka zauna,Allahu akabar Asalin gidansu nan nan kawu ya gyarashi yasaka wasu mutane suna zauna don Allah,saboda su kula da gidan karya lalace,zuwansu gidan yasa Sarki da Suwaiba suka tuna wasu al"amura da suka gabata inda dakinshi yake awanchan karon yanzu wajen ne aka kafa famfo,Maimartaba ya kurama wajen ido,hawaye suna taruwa a idonsa hakama Goggo,mutane anguwa kuwa da lbri ya samesu sunyi matukar mamaki,akwai dattawa dake da rai haryanzu,sai kuma wadanda suka samu lbrin bayan abun ya Faru,basu jima ba suka koma masaurata Tunda Allah ya wanke suwaiba da Da'nta,daganan kaduna suka dawo saboda Shirye Shiryen Tafiya chan Masarautar Tambari buzu ammh bayan An maida Auren goggo.


Kawu da Maimartaba basuyi Shawara dakowa ba,washegari bayan sallaar Jumma"a aka maida Auren goggo da Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,akan sadaki dubu Dari biyar,wanda awajen Daurin harda Maigirma gwannan jahar kaduna,Wanda aka daura amsallacin Sultan bello,Yan mazan ne kadai suke da masaniya sai da suka dawo gida suke Fada,goggo jitayi Abun yayimata wani banbamrakwai daki ta Shige tarufe kanta ganin yaran sun Faramata shakiyanci da Amarsu😛,Gimbiya Fasilatu kam dataji lbri kamar ta mutu takeji ga Danta Shima gabadaya taga baya tsaginta yana manne da dan'uwansa kamar wani zai rabasu,ga gimbiya Razeenah itama ko ajikinta harda ita cikin masu cewa agyara musu goggo,don so suke maimartaba ya rude fa😿Ummah mai babban daki kuwa wani lokacin tafi zama cikin Su Jabir kodon yadda take sakasu dariya,suko su Zafira basu iya saakewa ciikinsu saboda yadda su Haisam da jabir ke damunsu da kallo,Umar ne ya lura har ya shafama Aliyu,dariya takamasa yana fadin"Daz great,karabu dasu lalle wasu yara zasu dawo cemin babban yaya"Yafada yana dariya har ga Allah Abun yayi mishi dadi ko banza zai samu hanyar sakamusu da Abunda sukayi mishi,kuma zumuncinsu zai kara karfi fiye da Da.


Washegari kawu ya umarci Ummah da Goggo da Azeema da Aliyu su tafi gombe su tattara kayan goggo,tayi sallama da mutane saboda jibi zasu tafi chan masarautar Agadez,Gimbiya Razeenah ma tace zata,nan su Zafira sukace suma wlh sui sunje suna makale da princess dinsu,Mota biyu sukayi daya Aliyu ke driving tare dashi Umar,sai baya kuma Ummah da gimbiya Razeenah sai Goggo,dayan motar kuma Haisam da Jabir sai Azeema da Su zafira,wadanda su Jabir suka dinga jansu da zence,itako Azeema sai dai tayi musu mirmishi,suko yan matan basu saba ba duk kunya sukeji,Aliyu ko bini bini ya kira Jabir awaya yana fadin"Subi mai mata da kanne a hankali in ba hakaba ya hana abasu auren"Shuru sukayi suna Tunanin kashinsu ya bushe Tunda yaji lbrin ai sufa sai Abunda suka gani.


Sun isa gombe lafiya,su ummah suka Shiga gidan suka fara hadama goggo kayanta masu amfani,itakuma goggo tafara Shiga makota sallama,suna sallama tana kuka,sune har gidan Baba Ade,wacce itama tayi damara tace wlh da ita za'a Raka goggo masarauta😜goggo ko taji dadi tace ta Shirya su koma kaduna tare,kai goggo mai jama"a ce haka layi yacika,duk gidan data Shiga sai sunyi kwallah rabuwa da goggo Shekaru wajen talati sai yau kwatsam ace za"a rabu,toh basu da yarda zasuyi Tunda yanzu goggo ta wuce da saninsu matar sarki guda,Anan sukejin lbrin dawowar Azeeza goggo taja hannun Azeema suka Shiga cikin gidansu,Wlh da goggo da Azeema da sukaga Azeeza basu iya ganeta ba,saboda yadda tazama wata kamar kwarangwal duk kiban nan bata yanzu ta rame ta lalace tayi baki sai wasu kuraje afuska,ta kode ta lalace tana kwance kan tabarma daga ita sai daure gaba tana wani numfashi ba dadin ji,dukawa Azeema tayi gaban Azeeza tana kallonta tana hawaye take Fadin"Azeeza..Kice kika koma haka meyafaru dake? Inna ramatu dake gefe ne tace tana hawaye"Haka Aka dawomin da ita Azeema,ashe tun kamata da"akayi take rashin lafiya,ciwo ba"asan daga ina yake ba,tunda dai tadawo take kuka da kirjinta sai kuma ciwon kai mai tsanani,tabari muje asibiti,taki bari bansan me take so amata ba.."Kuka share share Inna Ramatu take tana durkushe gabansu goggo tana fadin"Don Allah Azeema da goggo ku taimaka kumin aikin gafara,wlh harda hakkinku ke bibiyanmu,na kyamaceki na wahalar dake,ke kuma goggo nabata miki suna sosai agari na cewa Aliyu bashi da uba gashi yau Allah ya nunamin iyakata,Ga Azeeza itama wlh harda hakkinki Azeema don Allah ki yafemata.."Tafada tana kuka,kamar zata Shide Azeema kuka take tana rike hannun Azeeza wacce ke miko hannu tana so tayi mgana Rikota Azeema tayi tana fadin"Sannu Azeeza Allah yabaki lafiya na yafemiki Duniya da lahira.."Tafada tana hawaye hakama goggo ta riketa tana jadadda yafiyarta,suna nan durkushe sai ga Mallam lawal sun Shigo Shida su gadanga,Shikanshi Aliyu dayaga Halin da Azeeza ke ciki sai da ya kauda kai,jabir ne yafara Fadan meyasa ba"a kaita Asibiti ba,Mallam lawal ya amsa da fadin"Ba inda zan kaita indai da kudina ne,kubarta tana girban Abunda ta Shuka ne.."Goggo ce ta katseshi da Fadin"A"a mallam,kada kace haka itama ya'ce kamar kowa,kuma tayi nadama don Allah ka yafemata"Jin sun saka baki yasa yace ya yafemata,Azeeza na kwance tana kallon Captain Aliyu tana hawaye,domin duk inna tabata lbrin mahaifinsa da duk Abunda yafaru,hawaye take tare da nadamar Abunda ta aikata,gashi yanzu tana ji ajikinta mutuwa zata yi,ammh kuma zata mutu da soyayyar Aliyu aranta domin ba ita ta dorama kanta ba,Aliyu ya Furta yayafemata,ammh fa Susinshi baijin zai iya badawa,Azeema ce tabata Dubu hamsin,wanda cikin kudin da kawu yake bata in yazo take Tarawa,Haisam da tsausayi,shima 50k yaba Inna Ramatu yace akai Azeeza Asibiti Allah yakara lafiya,Shidai jabir da Aliyu sisi basu bada ba,don aransu ma dadi sukeji ko banza anrage mugun iri,sallama sukayi musu suka Fito,inna ramatu har kofar gida kamar zata kwanta musu saboda godiya,nan nema goggo tace su Mallam lawal su tashi su dawo gidanta da zama ta mallaka musu halak malak,in Kawu sun dawo zai sa azo abuge gidan nasu ahade musu da wannan,Hakika mallam lawal yaga karamci,domin nan take maimartaba dake chan yace asanar da mallam lawal An biya musu kujeran makka,shida matarsa ai inna Ramatu harda Faduwa saboda taji Abun abazata ne,oh Duniya yau ga wanda ta wulakanta,sune gatansu Ashe,godiya sukayi ta zubawa kamar ba gobe,goggo ko tayi rabon kudi sosai,haka mutane suka cika bakin motarsu suna Fatan Allah ya kaddara saduwa gimbiya domin dai sun san,cewa kila sai dai kuma a lahira,koda suka bar anguwan haka goggo ke kuka babu wanda ya nemi hanata domin sabo yawuce komai,shikanshi Aliyu da bai cika zama ba, yau yaji Jikinsa yayi sanyi da barin gombe koba komai cibiyarsa ta haihu tana Gomben,ammh kafin sutafi saida ya biya mkrantarsu Azeema sukayi mgana da principal din,cewa Azeema zatayi tafiya,koza"a samu wacce zata cigaba da rubuta mata jarabawan kan tadawo,da hanzari ya amsa mai da za"a samu,kudi mai yawa Aliyu ya bashi sukayi sallama,bayan ya damka mishi Exam card din Azeema wanda yakarba Ahannunta.


Koda suka dawo kwana daya kadai suka kara suna kamallah Sauran Shirye Shirye,Hatta mazajensu Madina sunce dole suma su nemi Yarda awajen aikinsu suma suzo Awuce dasu domin fa dama daya take zuwa arayuwa,goggo ko Ummah ta isheta da kayan gyara itako goggo kunya tana fadin"Umaima wannan Abun kunyar har ina,tsofai tsofai dani,shima fa Maimartaba din ya tsufa don Allah kubarni haka"Ummah tace"haba goggo Shikenan kuma shi Tsoho bayason jin dadi,shima fa yasan dadi,nidai don Allah koda munje chan kisaki jiki,keda maimartaba ku Famshe Riban soyayyarku wanda baku fanshe ba abaya don Allah.."kallonta kawai goggo keyi tana dariya,su madina ko suna taya Ummah Rokon goggo,,Hatta Azeema ba"a barta abaya ba,ta Shige sawun masu son maimartaba ya samu chanjin yanayi😜😂Dole goggo ta yarda tana amsa komai aka bata tana ci,to ya zatayi Allah ya hadata da yaran zamani.


Takowani bangare Shiri yakamkama,Washegari karfe 10:00am na Safe jirginsu yatashi Abirnin tarrayyah Abuja,tunda sai dasuka Koma Fadar gwannati,maimartaba Sarki Abdulnaaeer yayi godiya da Shugaban kasa,kafin su wuce zuwa kasar Niger cikin babban Jirgin da suka zo dashi daga masarauta,Tafiyar data hada mutane dadama,Maimartaba da iyalansa,wadanda suka zo sai su kawu,Ummah,da Su Anty mardiya kowacce da mijinta da yayansu,sai jabir da haisam da Aliyu da Umar,sai goggo da Azeema da Baba Ade,Sune jirgin ya diba zuwa babbar Masarautar Tambari buzu wanda Tuni Lbri ya iske Masarauta cewa maimartaba na bisa hanya Shida duka iyalansa tare da wani Abun mamaki wanda zai bayyanama Masarauta.


_Ina godiya da Addu'o'inku...Ngd Sosai Allah yabar zumunci da zaman Tare..._



*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


*O Allah, You are the only supreme being worthy of worship, We associate no partners with You and only from You alone we seek for Guidance, Protection and Forgiveness for our sins. Ya Allah save us from the Darkness and Loneliness of the Grave, from the Torments of Hell Fire and finally make Jannatul Firdaus our final abode, Amin. Juma'at Mubarak!*


*Chapter 35*


"Koda Su Aliyu suka isa barrak,sun tararda angama dukkan Training din da za"ayi har anfara Tura sojoji zuwa yanki da ake tashin hankali domin kwantar da tarzoma,suma din sai da suka nemi izini,kafin abarsu su Tafi suna dawowa babu wani tsaiko aka Turasu kowane da bacth dinshi Captain Aliyu An hadashi da wasu sojojin Cameron ne zuwa Maiduguri ayayinda Jabir aka Hadasu da sojojin Chadi,zuwa yobe,shikuma Umar da Sojojin Nageria aka hadasa zuwa Kaduna adajin nan na birnin gwari ma"ana dogon dawa,babu wanda aka hadashi da wanda yasani Tafiya ce ta taimakon kasa da kasa saboda haka babu gudu babu ja da baya,kwana daya sukayi kafin suyi sallama da junasu kowannesu yabi tawagarsu suKa dauki hanya,Dukkansu kowani yatafi da niyar Taimakon kasarsane,dakuma Matakinsa na soja da kuma alqawarin da suka dauka na kare kasa da al'ummah dake cikinta,barikin gabadaya tayi rakwa rakwa gabadaya Rabi da kwatanta duk basu sai wadanda ba"a rasa ba sudin kuma sun kasance suna kasa ne,sosai basu gama sanin wasu dabarun yakin ba.


Ko kafin kace me,Kafafen yada lbrai sun watsa wannan lbrin na Tafiyan wadanan sojojin tare da rokon yan Nageria da su mika godiyarsu ga Kasar Niger da cameron hade da chadi bisa kokarin kawo musu zaman lafiya da tsaro akasarmu ta nageria,haka Aka dinga nuna hotunansu tare da tawagar kowanne,ciki ne da kuma rokon barar addu"ansu garesu na Allah ya basu Nasara suje lafiya su dawo lafiya,Ni"ima taga gwarzonta harda kuka sai da tayi tana mai Addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya nan tayi alkawarin duk sallarta sai ta sanyashi ciki,dukkansu sojojin babu wanda yatafi da wata waya ahannunsa sai dai wayar tsaro,wanda zasu dinga mgana da junansu in wani abu yafaru,ko kuma su kira bariki in suna bukatar wani Taimako.


***************


Inna Ramatu da Mallam lawal sun tattara sun koma gidan goggo da zama Duniya sabuwa mai tattare da Farinciki,Inna Ramatu in ta tuna Abunda tayi ta aikatawa ga goggo da Aliyu sai taji kunyan gashi yau tana raban Arzikinsu,Azeeza kuwa bata kowa take ba,sai ta kanta domin Jikinta gabadaya ya rikice shiyasa iyayan nata suka kwasheta suka kaita general hopital inda nan take aka bata gado,tare da wasu gwagwaje,sai gashi gwajin farko angano Azeeza ta dauke da hawan jini,kuma jininta yayi mugun hawa sakamakon ta sakama kanta damuwa,toh tayama Azeeza bazata damu ba,tabiyema Sharrin Shedan da Duniya gabadaya,Sai daga baya take ta Nadama da Danasani,da"ace tayi yaki da zuciyarta bata biyema Rudin Duniya ba da yanzu bata cikin wannan Halin koda Allah bai yayemata soyayyar Yaya captain ba,toh zai yayemata kaso mafi yawa acikinta,kila ma harta samu miji gangariya tayi aurenta bayan tana zaune lafiya da yar"uwarta mai Sonta Adda Azeema,gashi yanzu komai ya lalace duk Burinta babu wanda ya tabbata,Tun Aduniya tafara ganin ishararta inga Randa muka tashi gaban ubangijinmu,ayanzu haka Azeeza tafi kaunar Mutuwa fiye dakomai domin Tasan kotarayu babu amfani ga Rayuwarta domin hatta mahaifinta ya tsaneta,kuma da wani ido zata cigaba da kallon mutane bayan Duniya tagama sanin Duk Abunda ta aikata.

Ammh duka wannan halin data Shiga batabama kowa laifi ba,sai Mahaifiyarta Inna Ramatu,don Tun tasowarta inna bata taba kwabanta ba akan tayi ba daidai ba,kullum goyon bayanta take,koda Abun nan kuwa bamai kyau bane,Inna zata mara mata baya,bata taba koda zaginta domin gyaran Tarbiyanta ba,duk halin data Shiga ayau inna ce Sila domin Baba yana iya bakin kokarinshi wajen basu tarbiya,ammh sakamakon Inna ramatu ya isa gabadaya bata ganin Baba da mutumci,duba Adda Azeema bata da uwa,ammh kalli irin kyawawan dabi"unta da kuma hakurinta da sanyin Halin ta,ammh ita datake uwa ammh bata mori kowanni hali ba sai na mugunta,lalle Rashin Tarbiyama ma wani babban ginshikine sosai ga rayuwa yayanmu na yau da kullum.

Ranar data kwana biyu Asibitin jikin yayi zafi sosai take jin jikinta,Mallam lawal dayazo yana haraman Tafiya Azeeza takirasa da muryan ciwo.."Baba...? tafada tana mika masa hannu,matsowa yayi yana Fadin"gani Azeeza me kike bukata? yafada yana rikemata hannu,runtse ido tayi hawaye suna zubomata tace"Bana bukatar komai sa Yafiyanka baba,hakika na kasance yarinya marajin mgana wacce batabin umarninka ko kadan,ka Furta ka yafemin domin bana ji zaka dawo ka sameni.."Tafada tana kuka sosai,daga inna har mallam lawal jikinsu yayi sanyi Rike hannunta yayi yana fadin"Kiyi Shuru Azeeza kibar Fadin haka mutuwa da rayuwa duk ta Allah ce,mganar yafiya kuma nadade da yafemiki Azeeza Allah yabaki lafiya.."Yafada yana sharemata hawaye,mirmishi take mai har yayi musu sallama ya Fita,inna dake gefe ta rafka tagumi tana Tunanin makomar rayuwarta,Taji Azeeza ta kirata da dan karfi tashi tayi ta isa gareta tana Fadin"Gani Azeeza mekike so? Hannun Inna ta riko tana Fadin"Babu komai Inna,kawai wata wasiyya zan bar miki,koda bayan Raina don Allah inna kada ko bayan kin kara haihuwa kiyimata ko kiyimishi irin tarbiyan dakika bani,ki kasance uwa tagari ga ya"yanki don samun Rabauta ranar gobe kiyama.."Tunda Azeeza Tafara mgana Inna Ramatu ke kuka,tana fadin"Tabbas nazama banzar uwa,na kasance shashasha da na kasance lamba daya wajen Shigarki wannan Halin,Don Allah Azeeza ki yafeni don Allah,wlh na tuba,kuma nayi miki alqawarin zama uwa tagari,tare da zama mace tagari ga Abbanki.."Dukkansu kuka suke bamai lallashin wani Azeeza ce tafara tari mai karfi,inna tana kokarin Tashi taje takira likita Azeeza ta rike hannunta gam tana Fadin"a"a inna karki Tafi,ki tsaya kiyimin kallon karshe don in kika tafi baza ki dawo ki ganni da rai ba.."Inna Ramatu da jikinta yayi sanyi Tafada jikin Azeeza tana kuka,wanda take ta tari tana Numfarfashi,Ganin idonta na kafewa yasa inna Saurin Maimaitamata kalmar Shahada cikin ikon Allah Azeeza ta karba batama karisa ba idonta ya kafe sama jikinta ya saki.


Innalillahi wa"inna Alaihirraju'un,Kullu Nafsin za"ikatul Maut,kowani mai Rai sai ya dandani Dacin Mutuwa,yau dai ga Azeeza ta amsa kiran mahallincinmu Tatafi da duka burinkanta da mafarkanta Allahu akbar Shiyasa akace ka Shuka alheri kodon Watarana bakasan Yaushe zaka mutu ba,Inna Ramatu Kuwa tayi Tawakalli tare da Azeeza ta kwana har sai da Asuba ne ta kira mallam ta sanar dashi,cikin tashin hankali yake kiran sunan Allah,Gabadaya jikinsa yayi sanyi yakara tsorata da rayuwa Fadi yake Aransa Na yafemiki Azeeza Allah ya karbi bakuncinki.


Sai da gari ya waye Mallam Lawal yazo akayi cike cike aka basu Gawan Azeeza suka zo da ita gida,Lokacin mutuwar ta Azeeza tagama zagaye gari kowa sai Fatan dacewa yake mata,Ba"a dauki wani lokaci ba Inna Ramatu da kanta tamata wanka ta Shiryata aka dauketa Akayi mata sallah,Aka tafi da ita zuwa gidanta na gaskiya,Allah sarki Rayuwa kenan komai yayi Farko yana da karshe gashi yau Azeeza an tafi an bar Duniya an kaita an Turbeneta daga ita sai Halinta,sai Fatan muma Allah sa mucika da imani AMEEN.


Mallam lawal ya kira Kawu Bala da kanshi ya sanar dashi Rasuwar Azeeza,salati ya dingayi Abun ya tabashi,haka daya sanar da Ummah itama ta shiga sallallami tana Fadin"Kaji Abun Allah ko,yanzu Duk Abunda tagamayi Ashema ba rayayya bace kai wanda bai bi Allah da manzonsa ba awannan Rayuwar wlh yaji takaichi Allah ya jikanta da Rahama"Kawu ya karba da Ameen da Ameen,Ummah ita takira su Madina ta sanar dasu Rasuwar Azeeza,su kansu Mutuwar ta dakesu,nan sukace in Su Ummahm zasu don Allahu su sanar dasu suma su bisu suma mallam lawal gaisuwa.


Kawu da kanshi ya kira Maimartaba Awaya ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,lokacin suna tare da goggo ya mikamata wayar Kawu bala ya sanar da ita Rasuwar Azeeza,mikewa goggo tayi tana Fadin"innalillahi wa'inna Alaihirraju'un Yaya Wata Azeezan? yace"Azeeza dai kanwar Azeema diyar mallam lawal"Dafe kai goggo tayi Tana Fadin"Allahu akbar kabirin ashe Ashe ganin karshe mukayi mata nida Azeema,kai Allah kabamu mutuwar Shahada,Allah ya karbi bakuncinki Azeeza"Kawu da Maimartaba dake zaune suna karbawa da Ameen,


Dauke kwallar data zuboma Goggo maimartaba yayi bayan Kawu ya yanke kiran,Kanta ta dora bisa kafadansa tana Shesshekan kuka,babu shakka mutuwar Azeeza ta daketa,mutuwar matashiyar budurwa ko bakomai Yadda ta dauki Azeema ya'haka tadauki Azeeza,Allah yajikanta da Gafara,hannu maimartaba yasa ya Rumgumo goggo yana buga bayanta alaman lallashi yake Fadin"Shiii..Kibar mata kuka hakan nan,mutuwa fa dole ce gimbiyata,addu"an mu kadai take bukata yanzu plz wipe ur tears"Yafada yana dago Fuskarta,Tirr na kame gefe ina kallon Salon soyayyah manya bansan sanda na saki ihu ba ina Fadin Allah dai ya biya Ranka Shidade😂

Goggo ta dago tana riko hannuwan maimartaba tace"Yallabai na😱😹Bakowa nake Tunani ba sai Azeema kaga fa ga Halin data keci yanzu ya zataji in taji mutuwar kanwarta wacce ita kadai gareta"Ajiyar zuciya maimartaba yayi kafin yace"Hakane karki damu da wannan ki kiramin ita ni dakaina zan sanar da ita.."Yafada yana kallon kwayan idon goggo,wacce tawuce luu,zuwa kirjinsa tana share kwallarta Shiko yayi Saurin tarbanta yana Bubbuga bayanta alamar lallashi domin yakijinin yaga goggo cikin damuwa,Gimbiya Fasilatu data Shigo Turakar maimartaba yanzu,tun da zata Shigo Fadawan bakin Shashen suka sanar da ita Gimbiyar Mata fa tana ciki,saboda haushi ko sauraransu batayi ba,ta Shigo ciki kai tsaye,aiko tayi mugun gani,har tagama Tsayuwarta basu san da kafuwarta ba,kishi ne ya Rufemata ido yasa ta Fice da hanzari tana share kwallah,ahanya taci karo da gimbiya Razeenah ita da bayinta zata shashen Ummah mai babban daki,tana ganinta tayi Saurin daidata fuskarta,wanda ta riga ta makaro tuni ta gnta,sai da sukazo gota juna kana gimbiya Razeenah tace mata"wlh kina wahalar da kanki Fasilatu,kinfi kowa sanin yanzu baki da wani Fada gun maimartaba,dama fa arashin uwa ne akanyi uwar daki,in ma zaki kama kanki ki kama,in kuma zaki cigabane toh bismillah,iskane zai cigaba da Wahalar da mai kayan kara.." Tafada ahankali yadda babu mai jinta sai ita gimbiya Fasilatun,tana gama Fadin haka ta wuce ta barta nan tana cizon yatsa


Goggo da kanta taje har Shashen Azeema ta taho da ita har Turakar maimartaba,in kuka ga Azeema alokacin sai kun mata kuka,saboda yadda ta rame ga cikinta ya fara Fitowa azahirin batu tana Fama da kewar mijinta,gashi ko awaya ba"a samunsu,hakama suma Zafira ma take cikin damuwa,don Safaratu kadai ke waya da Haisam suko su biyun Shuru ne kawai,Maimartaba cikin lallashi da nasiha ya sanar da Azeema rasuwar Azeeza,Tashin hankali wanda ba"a sakamasa Rana,haka Azeema ta mike jikinta na Rawa Tana Fadin"Azeezar ce ta rasu? take Fada kamar ta fita daga hayyacinta goggo ce tayi Saurin mikewa ta rikota ta rumgumeta tana lallashinta,kuka sosai Azeema take tana Tuna Fuskar Azeeza data gani na karshe,Tayi kuka kamar Ranta zai Fita,kome Azeeza tayimata wlh bata taba jin tadaina sonta ba,jininta bata da wata yar"uwa data Fita,haka wuni kuka tana rarrashin kanta ita kadai,maraici ya lullubeta babu uwa babu uba akusa ga rashin miji ga Rashin yar"uwa Duk lokaci daya Haka dai ta rarrashi zuciyarta harta kira Babanta tayimai gaisuwa tace ya bama Inna Ramatu wayar tamata gaisuwa,inna Ramatu najin sallamar Azeema Tafashe da kuka,ai sai itama Azeema tacigaba da nata,saboda yadda suke koke koke ne yasa mallam lawal ya karbe wayan ya kashe saboda ya lura cikinsu ba wacce zata iya mgana alokacin.




*BAYAN WATA UKU*


Lokaci yayi Ta tafiya ayayinda Abubuwa dadama suka Faru ciki harda samun Nasaran dawowar Tawagarsu Umar,tsakaninsu da Tawaagar su Jabir kwana goma ne,Kuma Alhamdulillah an samu nasorori dadama,ansamu Kashe kashen rayuwa wasu sun Raunata gaskiya ammh Tunda ansamu Abunda Ake nema Shikenan.

Iyaye da yan"uwa da abokan arzuka sunyi murna da dawowar ya"yansu lafiya,Jabir da Umar sunyi Farinciki sake haduwa da juna abunda basuyi tsammani ba ballatana Fata,yanzu Fatansu suga dawowar tawagarsu Aliyu wanda ta kasance kusan itace ta karshe bata dawo ba.

Daga chan

Please Login or Register in order to submit comment