Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bayyana itama jikinta sanye da kayan mkranta ga jakarta ahannu,daga Azeema har goggo da kallon mamaki suka bita,itako sunkuyar dakai tayi kafin tasaka gwiwowinta akasa Tana fadin"Don Allah Adda Azeema kiyi hakuri ki yafemin Duk Abunda nayi miki,wlh Sharrin shedan ne,Ke yar"uwatace danafi so fiye da komai Arayuwata duk inna ce,take zugani ina miki Rashin kunya,ammh bada son Raina bane,ammh yanzu na Tuba,wlh bazan kara jin zugan inna ba,don Allah kiyafemin...",Tafada tana fashewa da kuka,Kallon Goggo Azeema tayi itakuma ta gyada mata kai,da hanzari ta isa ga Azeeza ta dagota ta Rumgumeta tana fadin"Shiiii..Kidaina kuka Azeeza na yafemiki dama bantaba rikeki Araina ba,Na yadda shedan ne yakeso ya raba tsakaninmu..Bakomai Allah yayafemana gabadaya.."Lamo Azeeza tayi tana wani dan mirmishi kafin ta dago tana fadin"Duk inna..."Shiiii...Kiyu Shuru hakanan ma,karki manta inna fa mahaifiyarkice fata kawai zakimata Allah yasa ta gane itama.."

Azeeza wajen Goggo Ta nufa itama ta duka tana rokonta dagota goggo tayi tana fadin"Dukkanku ya"yana ne,babu wanda na ware acikinku,Allah ya hada kanku.."Suka amsa da Amin nan fa su Azeeza aka share kafa akayi kari mai lafiya kafin goggo ta rakasu zuwa bakin Titi su hau Daidaita Dari biyar Goggo taba Azeema tace suyi kudin Abun haawa zuwa da dawowa sauran kuma suyi kudin Tara dashi,murna sosai sukayi suna ta mata godiya har suka kulema ganinta tana Faman daga musu hannu,acikin keken napep din ma sai Hira Azeeza kema Azeema itako dayake bata da yawan mgana mirmishi kawai take mata sai ko eh ko A"a..Azeeza bata damu ba,dama komai sai Abun Ahankali juyawa tayi tana kallon gefen Hanya kafin tayi wani bazawarin mirmishi tace" Dis is juz d begining..Yanzu wasan ya fara Adda Azeema kinyi kuskure babba wajen yarda dani ganinan zuwa cikin Rayuwarki domin na wargazata...",Tafada tana cije baki har saida Taji zafi alebenta.





*Comment,share,and vote...*
*Janafty...,*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


*I dash d whole page for u my Rival..👭...HUWAILATU😂😜popular Name MISS ZERK..ga page dinki nan,karki wani damu Ana tare,dama aie Abun Uwargida na Amarsu ne.....*😂😂

            *Chapter 13*

   

    ---------------------Rayuwa Tana ta gudu kamar yadda muke cinye Lokaciinmu da kwanakinmu Aduniya,suke gangara suna Neman karewa,masu imani ne da masu tunawa da zasu mutu kadai suke Shiga Tashin hankali in suka Tuna hakan,ammh akasin haka ko ajikinsu To hakan ce Tafaru da Azeeza Domin koda da wayewar gari, bata taba Nadamar ko jin Abunda take Shirin Aikatawa baida kyau ba,ko taji zuciyarta ba dadi in Tayi Tuni da Cewa Azeema yar"uwanta ce.

  Duk wata hanya da Azeeza zatabi ta Shigema Azeema da goggo tayi,yanzu sun bata dukkan Amanna,gidan take Wuni,sai dare take komawa gida,tare suke komai da Azeema kamar wasu yan biyu,inna Ramatu kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu,Saboda sabbin halin Azeeza tafito dashi shiko Mallam lawal Abun yayi Mai dadi don Azeeza tazo ta rokeshi gafara kuma ya yafemata Yana ta sakamata albarka,Inna Ramatu Abun ya Daure mata kai sosai kuma tayi tambayan Duniyan nan Azeeza tayi mata banza bata mata wani bayani ba,kuma bata yarda ta fadamata Abun da ke Ranta ba ko alama daga ita sai Allah kadai suka san Abunda ta binne Aranta.

  Duk Zuwan da Azeeza take gidan goggo bata taba katarin,ganin Azeema Shashen na yaya captain ba,wanda Abunda take ta jira kenan,kullum sai dai su Tare dakin goggo susha hiransu,yau dai kam Tayi sa"a domin tana Rafka sallama atsakar gidan Azeema ta daga labulen Shashen gadanga tana fadin"Azeeza Shigo nan.."Tafada kai tsaye tana mata mirmishi Ran Azeeza yayi sanyi jikinta na Rawa ta nufi Dakin Tana washe baki,bude mata kofar Azeema tayi tana fadin"Yau goggo barci ke cinta,Har na dawo,bata sani ba shiyasa na Shigo nan don kar na dameta.."Dariyan yake Azeeza tayi tana fadin,"eh gaskiya ne..."Tafada tana bin makeken falon da kallo,wanda yaji lafiyayyun Royal chair,idonta wurgawa kawai yake tana karema Falon kallo,Azeema ce ta Kalleta tace"Zauna Azeeza bari na kawo miki Ruwa kinci Abinci? tatambayeta girgizamata kai Azeeza tayi ta kasa mgana saboda wani hoton gadanga data gani bisa wani tebur din glass,dake chan jikin bango,kyam tayi ma hoton tana kallo,itako Azeema bata lura ba kichen Ta nufa tana Fadin"Bari na dafa miki indomie..Nima ita nagama ci yanzu.."ko jinta Azeeza batayi ba hankalinta yatafi ga hoton Yaya captain,A hoton yana sanye da wasu fararen kayan hatta cambos dinsa fari ne, safa ma haka,acikin wani fili ne akayi hoton kamar dai asansanin horarwa ce,yayi tsalle yana dariya aka dauki hoton,Azeeza saboda shauki batasan sadda ta karisa kusa da hoton ba ta saka hannu ta dauki Frem din tana kallo,hannunta ta sanya tana shafa hoton sai ga Azeema ta fito tana fadin"Yanzu zata nuna na zuba miki,yunwa ba dadi..'Tafada tana karisawa kusa da ita.

Saurin waskewa Azeeza tayi tana fadin"kinga hoton danazo kallo Adda Azeema Allah yaya captain yayi kyau sosai ahoton nan.."Mirmishi Azeema tayi kafin ta amshi hoton tana fadin"Gaskiya yayi kyau kam.."Tafada itama tana kallon hoton kafin ta ijiyeshi inda yake,Talabijin din dake dakin ta kunna tana fadin"Muyi kallo Azeeza mu rage zaman Shuru.."Yake Azeeza tayi kafin tataho ta zauna tana satar kallon bedrooms din dake jere Shuru ya biyo baya Azeema ita hankalinta na wajen kallo yayinda Azeeza ke saka yadda zata fara dakan Ruwan Cikin Azeemar batare data sani ba.

  Zuwa chan wata dabara ya taso mata sai tayi Farat tace"Adda Azeema nace ba..",Dagowa Azeema tayi kafin tace"mekike son Fadane Azeeza..? Yar dariya Azeeza tayi kafin tace"Wai nace yaushe yaya captain zai dawo ne..? Kai tsaye Azeema tace"Wlh bansani ba Azeeza..",Wani sanyi ya Shiga zuciyar Azeeza murna ya cikata sai ta barsa,lokaci daya ta bata rai Tana fadin"Toh meyasa Adda? bakwa waya ne.."?Jin Abunda Azeeza tacene ya sata Dagota kanta tama Azeeza kuri da ido,sai taji kunyan cewa basa waya..Cikin in ina tace"Eh..Armm..Munayi mana..'Tafada kafin tayi zaraf ta mike tana fadin"Bari na dubo miki,kila yanzu Ta isa yi.."Tafada kafin ta fada kichen,Tana Shiga Azeeza ta buga kafa tana fadin"yes...Komai na tafiya kan Tsari.."Take fada tana dariya Sai ga Azeema ta fito dauke da filet wanda ta zubo indomie aciki sai Lemon cway data daukomata ta kawomata nan Azeeza Ta share kafa ta warba tana ma Azeema hira wanda Rabin hira duk na dakan Ruwan cikinta ne,itako Azeema bata ma iya maida mata amsa sai dai tayi mirmishi ko ta gyada kai,wai Azeeza harda tambayanta ya lbrin Ni"ima Saboda mamaki sai da Ta bude baki tana kallonta,harda cemata wai ta mike tsaye don tagane yaya captain haryanzu yana Son Ni"imar,Rike baki Azeema tayi tana auna kankantar shekarun Azeeza ammh tana mganar manya,sai kuma mganar data Fada ta tsaya mata arai...Sam bataji dadin Jin Abunda Azeezar ta fada akan Yaya captain yana Son Ni"ima haryanzu ba, Batasan dalili ba,sai taji duk zuciyarta babu dadi..Lura da haka da Azeeza tayi sai tayimata sallama takoma gida ammh Ranta Fes Domin tayi hakane ta tusama Azeema tsanar yaya captain koma tana Sonshi ta cire Tunda zuciyarsa na ga wata..Kuma taga alamun Nasara kodaga yadda Azeema tachanza Tun lokacin dataji mganar...

________________

  Ta Sauka daga keken napep kenan Tabashi kudinshi Ta nufo kofar gidan Kamar a Mafarki taga wani kamar gadanga zaune bisa bayan motarshi Jabir na tsaye agefe,dukkansu suna sanye da Riga da wando,wandon blue ne sai Rigar Farace kafafunsu sanye cikin booth,Kowannensu hannushi dauke da wani ubansu agogon Fata na kamfanin Rado,Fuskarsu cike da Annuri,Hannayensu dauke da gorunan Ruwa suna kurba,Da hanzari Goggo ta karisa Gadanga ne ya fara hangota da hanzari ya diro daga motar yana cema Jabir"Ga goggo chan ta dawo.."Yafada yana karisawa gareta,Maida kallonsa Jabir yayi inda goggo ke tahowa tana ta washe baki,dariya yayi yabi bayan Gadanga..

   Suna karisowa goggo Ta Rumgume gadanga tana fadin"Oyoyo gadanga..Kai ammh kai ja"irin yaro ne ka iya zuwan da Annabi ya hana..Au tare ma kuke da jabiru kai marabanku da bakin sassafe.."Ta fada tana Sakin Gadanga takamo hannu jabir wanda ya duka yana gaisheta Fuskarsa Gadanga ba walwala yace"Wai goggo daga ina kikene da wannan Farar safiyan..",? Bata Fuska tayi kafin tace"ya'yana na Raka mkranta sun makara suna Tsoron duka,shine naje mkranta na fadamusu basu da hankali ne,matar auren zasu daka,kuma ma matar Auren matar soja,Aliyu gadanga.."Tafada kai tsaye ko ajikinta galala Gadanga yake kallonta kafin yace"Wasu ya"yan naki..? asakarce goggo ta kalleshi don ta gane tambayan Rainin wayau yayi mata,kauda kai tayi kafin tace"Matarka Azeema da kanwarta Azeeza ko ba ya"yana bane..? tafada tana zubamai ido,Bata Fuska gadanga yayi kamar zaiyi kuka,Tsaki goggo taja kafin tace"Ohon maka kabar wani tabe Fuska kamar kaga kashi,ni wlh al"amarinka wani lokaci na ban mamaki,bansan wakake tabema Fuska ba,mganata ko ni din kaina..? dariya ta kwacema Jabir yace"kai goggo ya"za'ayi ya tabe miki Fuska,kila mganar ne bataimai dadi ba..'Yafada yana kallon gadanga Ta wutsiyar ido wanda yayi gaba yana fadin",Don Allah goggo kibar wannan mganar juz open d door.."Harara Ta zabgamai kafin tace"Alqur"an Sai ka fasasara mai kace daga karshe,kasan dai na hanaka juyamin yare ko"Ta fada a fusace,dariya ta kullema Jabir ciki yace"Goggo cewa fa yayi ki bude kofar.."Dariya goggo tayi kafin tace"oh yanzu nagane,nima fa da inajin Turancin nan miyar kuka ne suka danneshi wlh,ammh da in na Fara Turanceku harshi gadanga sai na kureshi.."Ta fada tana bude kofar gidan wanda ta samai kwado sanda zata Fita,Dariya takama Aliyu,sai dai ya share Shiko Jabir harda kaiwa kaasa saboda dariya,Aliyu ne ma ya kwashi jakukkunansu ya Shiga dasu Kafin yakoma ya Shigar da mota gareji,Shiko Jabir yana chan wajen goggo yana janta da hira suna dariya datace zata dora musu girki cewa sukayi akoshe suke..Komawa goggo tayi ta zauna Aranta tana fadin"Dama banyi niyyah ba,kwaci kaniyarku don Ni ina da Sauran dan wake na najiya wanda Azeema tayimana.."tafada Aranta tana mirmishin mugunta,tunda ta lura daga gadanga har abokin nasa yan Air ne,komai sai sun Tsara suke aiwatarwa.

Shiko Aliyu yana Shiga Sashensa Abunda ya bashi mamaki abude ya gani bai kawo komai Aransa ba,sai ya ce kila goggoce ta bude don tagyaramai ammh sai mai ko"ina tas sai tashin kamshi,ga remot kan kujera ga Talabijin akunne,bai gama mamaki ba sai da ya leka kichen yaga komai net..Ga kuloli nan da alamu ba"a dade da wankesu ba,baki ya rike yana Tunani ko goggo ta dawo shashenshi da kwana ne,don ya san zata aika,Da hanzari ya fice zuwa dakin goggo suna tsaka da hira da jabir ya Fado yana Fadin"goggo chan Shashen kika koma da zama kuma? akarkace goggo ta kalleshi kafin tace"me..?meka gani hala.."yace"alamun mutum na Rayuwa awajen..'tsaki goggo taja kan tace"ji wata tambayar banza,dama da mutum mana,ka manta ka ijiye mata...Toh Azeema ce ke zaune aciki..'Tafada kai tsaye tana Hararanaa,Tsaye yayi yana zare ido,don shifa ya manta da wata Azeema balle har ya Tuna da Abunda ya faru dafe kai yayi kafin yace"Toh goggo miye laifin barayinki,naga dai kema kina da dakuna.."goggo tace"Eh na saukan baki ba,ammh ba wajen ijiye matar gadanga ba,.."Tafada tana kallonsa,yanajin Abunda goggo tace yafice saboda yasan halin goggo ta kan wannan mganar sai ta maida Abun ya zama babba,yana Fita jabir ke tambayan goggo dama Azeema tatarene,nan fa goggo ta gyara zama ta kwashe From A to z bata rage komai ba.mamaki yakama jabir don ko kadan Aliyu bai Fadamai ba Fatan Alheri yayi musu da Fatan zama lafiya.

  Shiko Aliyu saboda bacin Rai waje yakoma ya zauna akofar gida yana latsa latsen waya saboda Haushi,yasan Halin goggo tsaf zatamai tas agaban Jabir shikuma ya samu Abun Tsokanarshi,shiyasa ya fice daga gidan ko Ransa zaiyi sanyi,yafi awa biyu har aka kira sallar azahar yatafi massllaci yayi achan suka hadu da jabir suka dawo Tare nan kofar gidan sukaci burki Aliyu Daure Fuska yayi saboda ya riga yaasan Goggo ta fadamai komai Saboda bakin goggo fa Sikat ne yariga ya santa Sarai Shiyaasa yasha kunu kallonsa jabir yayi kafin yace"Kai Dude ashe Azeema tatare,Toh yanzu ina zan Dinga sauka Tunda yanzu kayi iyali.."Kai Tsaye Aliyu yacemai"Nima Tunanin danakeyi kenan,gwara na saman maka wani waje don bazan iya hadaka shashe daya da iyalaina ba.."kallonsa Jabir yayi kafin yace"Kan ubanchan,yo meye Nufinka bunsuru ka maidani..Toh kona ina akuyanci bazan bi iyalinka ba.."Ko kallonsa Aliyu bai yi ba yace"Kaji dashi dai."Jabir yace"Muji dashi dai,Wai Dude ya mganar zuwa wajen yarinyar nan kafa san don ita nazo garin nan.."wani kallo Aliyu ya watsamai kafin yace"Dama ni kake jira na rakaka..? gyada mai kai yayi dan mirmishi Aliyu yayi kafin yace"U are not Serious,Tunkan dare yayi maka mallam kanemi mai rakaka,Ban da kana ajawo gaja harwata budurwace zaku hadu awaya kafara Dating dinta kuma wai harda zuwa zaka wajenta,toh bada niba Allah kiyaye hanya.."Yafada yana buga kafadanshi.

  hararansa Jabir yayi kafin yace"Toh ina Ruwan mutum..Karkaje kar Allah yasa ka rakani nima ba bako bane a gombe,mganar budurwata kuma ka iya bakinka don daga yanayin muryata nagane cewa babbyn Ta hadu wLh.."Dariya Aliyu ya fashe dashi kafin yace"Allah mazaje.Toh anjuma ka Shirya muje sai na ganta."Riko kafadansa yayi kafin yace"Da gaske Dude.."gyadamai kai yayi Alamar da gaske ne,Hannu jabir ya bashi suka kashe kafin yace"Tanque Dude...,"Bakomai yima kaine ai.."gadanga yafada Saurin mikewa Jabir yayi yana Fadin"bari na kirata nabata Suprise kasan bata san na Shigo gombe Ba.."Kallonsa kawai Aliyu yayi kafin yace"yakamata mr love.."ya fada yana bin Jabir din da kallo yadda ya wani rabe gefe yana rage murya girgiza kai kawai Aliyu yayi yana tsausayawama  Jabir don ya shiga tsaka mai wuya kafara soyayyah da wacce baka taba gani ba.

  Yana nan zaune yana latsa wayarsa yaji karan mashin agabansa,kamar zai Share sai kuma yaji ya kasa yana dagowa yayi mugun gani Azeema ce da Azeeza sukayi 2parking kuma Azeema ce a tsakiya ga Azeeza nada jiki duk ta cinye wajen Shiyasa aka matse Azeema ajikin mai mashin,kutumar ubanchan Galala Aliyu yayi yana kallon yadda kirjin Azeema ya manne da bayan mai mashin,Azeeza data Fara sauka ta gefen ido ta kallon Aliyu tana ganin yadda kacokan hankalinsa yana ga bin Azeema da wani kallo,Addu"a take aranta Allah yasa yazo ya mareta,domin Tun asaman layi Azeema taso su sauka Azeeza ta hana kamar ta sani suna shaho kwanar layin tahangi jabir,kafin ta hangi yaya captain da gayyah takara matse Azeema ta kara hadewa damai mashin kuma taki yarda asaukesu ko"ina sai kofar gidan goggo,itako Azeema bata lura da Abunda ke Faruwa ba ta dirko daga kan mashin tana laluban jakarta zata dauko kudi,daga bayanta taji ance"kai..."gabadayansu suka waiga har mai mashin din,yana tsaye ya harde hannuwansa bisa kirji da hannu ya nuna mai mashin din kafin yace"kai..Come here,karka bari nazo domin Abun bazai yi kyau ba.."

  galala mai mashin din ke kallon Aliyu kafn yace",Kai mallam dawo Natsuwarka domin ni bakaga nayi kama da lusarin Namiji ba,anki azo din zokayi Abunda zakayi don uwarka..."Jin Abunda yacene ya kusa saka Azeema Fitsari awando,saboda tsoro baya taja kafin tace"Armmm...Yayan mune fa mallam..,"Tafada bakinta na Rawa shiko Aliyu mamaki ya daskaran dashi,saboda jin kai tsaye wani banza ya zaganmai uwa Takowa ya farayi yana kallon mai mashin din yana wani cije baki,ganin haka yasa Azeeza Saurin Rumgume Azeema tana fadin"wayyo Adda Azeema kibama yaya captain hakuri,sai da nace mudaina hawa mashin ammh kullum sai kice sa mun hau ai ga irinta nan.."Wani banzan kallo Aliyu yabi Azeema dashi ashe bata da hankali bai sani ba,duk duniya babu Abunda ya tsana irin yaga mace ta hau mashin koda ita kadai,wato ita saboda taceewa su biyu suke hawa saboda wulakanci ko,yau zai koyamata hankali,shikuma mai mashin din daga yau bazai kara Dauka wata mace ba sai dai ko in matarshi ce.

Itako Azeema mamakin Azeeza ne ya cikata,ita yaushe take cewa su hau mashin sau biyu fa suka taba hawa,yau din ma babu abun hawa ne,wannan din ma dakyar suka samu Shiyasa suka hau su biyu,ammh ji Abunda take fada,bata samu zarafin mgana saboda yadda gadanga ke hararanta yana jifanta wani dirty look,itako Azeeza bayan Azeema takoma tana leke Farinciki Duk ya cikata burinta daya yanzu Shine Ya kifkifama Azeemar mari.




    *Comment share,vote...*
    *Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


*I Dedicated dis page to u guyzs KHADIJA CANDY NOVELS..(mama)❤,BENEFICIAL WRITERS💕,JANAF NOVELLA 💖1and2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3 and REAL LADINGO FANS😘 Tanque all For u Hot comments Sakallahu Filjannah HABIBATIES*😍



       *Chapter 14*

  Yana karisawa kusa da mai mashin din ya dunkule hannu ya tokare mai hanci da baki lokaci daya yasaka hannu ya matsemai baki,jinin daya Fito daga bakinsa da hancinsa sai da ya sashi ya hadiye kafin ya sakeshi,baya yayi kamar zai Fadi saboda yadda yaji kansa yayi Aliyu yasaka hannu ya taroshi yana fadin"mekace ne dazu? dan maimaitamin banji dakyau ba..."Yafada yana kallonsa,mai mashin daya sha wuya yakalli Fuskar gadanga zuwa hannunsa yaga yadda Naman jikinsa ke jida saboda Fushi ai bakinsa na Rawa yace"ban..bance komai ba yallabai.."Wani killer smile Aliyu yayi kafin yace,"Next time kakara dauko mace daya ma,ba biyu ba zaka ga yadda zanyi dakai.."mai mashin yace"Bama zan kara dauka ba yallabai wlh maza kawai zan koma dauka.."good.."inji Aliyu kafin yajuya yana Fadin"oya Sauka daga kan mashin dinka ka dauketa bisa kanka karka sauke har saika bar layin nan.."Sororo mai mashin yayi Tsawa ya dakamai ai da gudun hanzari ya daga mashin din da hannu bibbiyu ya wuce yana waige Jabir dake gefe yana waya Tikar dariya kawai yake,yana ba budurwan Nasa lbrin Abunda ke faruwa,su ko su Azeema Tuni suka Shige gidan goggo suna Rawan jiki,Da goggo ta tambayesu Azeema kasa mgana Tayi Azeeza ce ta maida bayani Yadda akayi Dariya goggo tayi tana fadin"Banda Abun gadanga miye na Sauke Fushin kan mai mashin,.."Abun yaba Azeeza mamaki yadda lbrin yaba goggo Nishadi,suna cikin maida mganar ne sai gadanga ya shigo yana Shigowa kai tsaye Azeema ya nufa sai da yazo gabanta kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi kafin tayi Saurin sadda kai,Nunata yayi dayatsa yana fadin"ke babban banza ce ashe bansani ba,..To dis one wil be d last time dazanganki bisa mashin din wani kato,daga yau ki dinga hawan Keken Napep tunda na lura sakarcin naki gaba yake ba baya ba.."Yafada kafin ya juya,Galala goggo tayi tana kallonsa itako Azeeza kamar ta kurma ihu saboda murna baki goggo ta rike kafin tace"toh wayace maka Azeema na hawa mashin,Toh na tabbata rashin Abun hawa ne,bata da zabi ammh Azeema bata hawa mashi yo Allah na tuba inamatake zuwa balle ta dinga hawa mashin..."Cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallon Azeema yadda take kuka hawayenta na diga Tsausayinta ya kamashi maida kallonsa yayi kan Azeeza nan da nan Tayi wiki wiki da ido tsuramata ido yayi yana nazarinta,itako Tuni jikinta yahau mazari Abunka ga mara gaskiya,takowa yayi zuwa gabanta yana karemata kallo kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi tana wani kifta ido matse goshi yayi kafin yace"Ni sa"an wasanki ne.. ? Shuru tayi tana Raba ido tsawa ya dakamata kafin yace"Nace  ni sa"an wasanki ne..? da sauri Azeeza ta girgiza kai tana ja da baya,Wani tsawan ya dakamata kafin yace"Oya get out..Wannan yarinya wlh idonta na kama dana mayu,"Yafada yana kallon goggo ai da hanzari Azeeza ta fice ko waigo dariya takama goggo sai da dara gimtse Fuska Aliyu yayi kafin yace"Wai don Allah goggo meyasa kika sakarma wannan yarinyar Fuska ne,nifa banyarda da ita ba sam,idonta namin kama da na munafukai ne wlh.."Rausayar dakai Goggo tayi kafin tace"Toh mai gani hanji kai kowa bai maka ba,toh ko dole ka sota Tunda kana Auren yayarta.."baiyi mgana ba kawai ya fice cike da takaichin yadda goggo takasa Fahimtarsa sai yana ji ajkinsa tamkar yarinyar Tafi Azeema iya Duniyanci da wayau bayaso wani Abu yafaru agaba...

  Goggo ita tayita lallashin Azeema har tayi Shuru ammh takasa daina jin Haushin kanta da mamakin Azeeza,itako Azeeza kwana tayi takaichi da bakinciki domin yaya captain yazo ya Rusata mata komai ammh ba komai yanzu tasaka kafa babu gudu babu ja da baya,bayan mangariba Jabir ya shirya Shida gadanga suka wuce Gra domin haduwa da budurwan ta jabir wacce suka hadu ta waya,ba laifi yarinyar tana da hankali da kunya babanta dan kasuwa ne,yarinyace bazata wuce sa"an Azeemar ba itama SS2 take a babban sakandiri Abun na jabir yaba Aliyu mamaki yadda yaga yana wani Rawan kafa agaban yarinya saboda Haushi mota yakoma yana game awaya Don yaga lalacewar na Jabir yayi yawa.
..

  Sai pas ten suka dawo,koda suka dawo Goggo da diyarta tuni sun dade da kulle shashensu Sun kwanta suma basu bi ta kansu ba Aliyu ya kargame kofar gida suka fada shashenshi domin kwanciya,Abunda yabama Aliyu mamaki Jabir suna shirin kwanciya ya dasa waya da yarinyarnan kamar wani namamajo Ko gajiya basuyi Haushi yakama Aliyu ya fice daga dakin ya Shiga dayan bedroom din ya kwanta,nan yaga kayan Azeema da kayan kwalliyarta wadanda goggo ta siyamata,tsayawa yayi yana kallon kayan yana wani Tunanin yama Rasa ta ina xai Fara Taimakama rayuwar yarinyar don ya lura tana bukatar wani akusa da ita,Bata da sakewa ko kadan,bata da sani kan komai,shibaima san meke damunta ba,kullum kai asunkuye ko kuma ka ganta tana kuka,ada yana tsausayama kansa na Rashin cikakken Asali ammh yanzu yafi tsausayama Azeema Domin ita tana da uban ammh maraici da rayuwar Rashin yanci ya dabaibaye Rayuwarta uwa uba bata taso tare da kowa ba,Shiyasa wautarta tayi yawa,kwana yayi yana Tunanin mafita da yadda zai bulloma al"amarin.


    ***************

Washegari da Safe da wuri Azeema ta Shirya domin wucewa mkranta Bayan ta karya ta zauna tai zuru tana jiran ko Azeeza zata biyo mata su Tafi ammh Shuru goggo na lura da ita bata dai mata mgana bane ta tsayane taga iya Gudun Ruwanta zata fasa zuwa mkrantan ne saboda Azeeza bata biyomata ba ko yaya ne? Tana nan zaune Aliyu yayi sallama ya Shigo dakin goggo jallabiya Mai Ruwan Tokace ajikinsa,Tanajin sallamasa tayu zumbur ta mike tana mazurai Sau daya ya kalleta yakauda kai kusa da goggo ya isa yazauna ya gaisheta amsawa yayi yana Riko hannunta Da hanzari Azeema ta duka tana gaisheshi a dakile ya amsa kafin ya kalleta yace"Goggo metake jira bata tafi mkranta ba 7:30 fa ya wuce.."Kallonta goggo tayi kafin tace"Yauwa gwanda da Allah ya kawo ka gatanan,tambayeta nima Tundazu naga ta Shirya ammh ta nemi waje ta zauna bansan metake jira ba.."Sunkuyar dakai Azeema tayi Aliyu zai yi mgana kenan Jabir ya Shigo dakin Shima yana Sanye da jallabiya baka yana ganin Azeema ya washe baki yana Fadin"Ah ZEEMA kin tashi lafiya.."Dan Rankwafawa tayi tana gaisheshi Ansawa yayi cikin sakin Fuska yana fadin"Lafiya lau Zeema ya mkranta hop dai ana maida hankali.."Gyada kai tayi cikin kunya Gadanga dake zaune yayi Wuf ya mike yana fadin"Ke muje.."fuska ba walwala kallonsa jabir yayi kafin yace,"Toh miye nawani cewa kuje naganeka bakin ciki kake don ta dan Rankwafa dazata gaidani ko? hararansa Aliyu yayi kafin yace"Eh.."Adakile Akarkace Jabir ke kallonsa kafin yace"Dalili..? ko kallonsa Aliyu bai yi ba yabi bayan Azeema data fice da Sauri har zai Fice ta waigo yana fadin"kaji dan Rainin wayau ni dana rakaka zence jiya Budurwanka tama gaisheni ne,kunata rawan kafa ko Tunawa dani ai bakayi ba.."Yafada yana dariyan keta kafin ya fice Baki Jabir yakama lokaci daya yana Sosa kai goggo dake zaune gefe tace"Au zence kukaje jiya ko? to ai Allah yakamaku ja"irai.."tafada Tana dariya Sosa kai kawai jabir yake kafin yayi Wuf yafice yana fadin"Goggo ma gaisa da Rana."Yar dariya goggo ta sakeyi kafin tace"kai Jabiru da gadanga bansan wanda yafi wani Shegantakaba.."Take fada kan tatashi ta fada kichen domin ta kwaso musu Abun karinsu.

shiko Aliyu Tiryan Tiryan yake bin Azeema abaya suka fita daga gidan har zuwa bakin Titi kanzil bai cemata ba,itako tsoro yahanata ko waigo Suna zuwa ya taran mata wani dan adaidaita suka gaisa cikin mutumci kafin yadan duka sukayi mgana,ya fadamai ne Nawa zai Dinga biyansa yana zuwa yana dauka Azeema kullum yakaita mkranta ya dawo da ita,nan mai Adaidaita yace ya yarda buh ammh sai dai yafison adinga biyanshi Duk sati saboda halin Rayuwa..Nan take gadanga ya amince yace yakaita ya dawo sai suyi mgana bayan ya nunamai gidan da in yakaita zaizo ya sameshi,baya yayi yana kallonta kafin yace"oya ki Shiga yakaiki.."tsam tayi kafin tafara waige waige lura da hakan dayayine yasa shima ya waiga yana fadin"wakike

Please Login or Register in order to submit comment