Join Our WhatsApp Group

DUK KARFIN IZZATA Complete Hausa Novel Document by DUK KARFIN IZZATA


DUK KARFIN IZZATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 140839



DUK KARFIN IZZATA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 24, Jan 2024

Author: Star Lady ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : The talent troupe writer's

Author Phone : 09162620621

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 750.27 kb

File Type: txt

Views: 1022+

Download: 1040+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: 
[7/3, 5:44 AM] Al~Quyraemey: *💫STAR LADY💫*

https://chat.whatsapp.com/Cx1u7E8LUUX1XY8pJeHfMO

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 1*


💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖

London United Kingdom

Wasu haɗaɗun samari ne zaune awani katafaren palo mai girman gaske,Mai ɗauke da manya manya sofa set 2,launin Brown da ratsin milk, gawasu triple staircase ɗaya ta bangaren hagu ɗaya bangaren dama ɗayan kuma a tsakiya daga gefe kuma wani haɗaɗen table ɗin chin abin chine, ga wata makekiyar Tv a gefe guda,palon yaji komai da ake buƙata dan in nache zan tsaya zayyana muku ha'ɗuwar palon nan tofa sae mukare littafin nan a palo kawae, kae dakaga wajen kasan baƙara min dukiya aka narka awajen ba,"zaune suke,shiru ba mai magana " kowa da abin dayake fuskar nan tasu kuwa tamkar an aiko musu da sakon mutuwa " gasu kyawawa sosai kamar larabawa

Farare ne sosai dukkan su kamannin su ɗaya kallo ɗaya zaka musu kagane yan uwan juna ne amma biyu dake zaune a saman sofa mai zaman mutun 2 nan,sunfi kama da juna sosai dan kuwa kamar an tsaga kara, haka suke suna da dogon hanchi sosai, ga manya manyan ido sai dai abun mamakin kowa dakalar idansa biyu daga chikinsu dake zaune saman sofa guda kwayar idansu ash colour ne biyun dake gefe kuma idan nasu light green ne shikuma ɗayan idan sa baki ne, ga idon nasu manya manya " ga ɗan karamin red lips, ga lallausan bakin saje kwanche a guskar su, sai dai uku daga chikin su gemun su bai da tsawo sosai san nan kuma suna da gashin kai mai tsawo har baya kamar mace.

"wani haɗaɗen saurayi ne ya sauko daga staircase ɗin tsakiya yana faɗin haba DON yabaku'shiryaba Aryan Aiman yusuf Ahmad me kuke jira

(nikoh nache daman wayannan turawan sunajin hausane)

ɗago ido DON yayi "wadda shi idansa ya kasanche light green ne,yana faɗin "shirin zuwa in kuma Khalid,Akule khalid yace "shirin zuwa Nageria mana ko kun manta gobe za'a ɗaura auren hisham,mike DON yayi yana faɗin "bazanje ba nikam san nan yanufi saman stair ɗin ban garen hagu,da sauri khalid yajuya daniyar yasha gabansa,Yusuf yamike yarike sa, a'fusache khalid Yajuyo yana faɗin "yusuf kasakeni " Yusuf ya ɗago ido shima dai idan nasa light green gasu manya manya masu kyan gaske yache "aa khalid bazan sakekaba kafasan kokabishi ba chanza magana zaiba saidaima kubata,yakamata ache idan dasabo kasaba ɗan kasan, yaya prince fa idan yayi magana to yayine baya chan zawa, shiyasa muka chanza masa suna daga prince Safras muka maidashi DON, dan in yayi maganafa it's done angama baya chanza wa "pls yusuf ka kyaleni wlh yau kam dole DON, ya chanza magana haba dan allah ai kobazaije bikin kowaba dole yaje na hisham, saboda tare muka taso gaba ɗayan mu, dukkan mu abu ɗaya'ne chewar khalid "ɗaya daga chikin matasan dake zaune saman sofan ne yamike yache "to ni ma dai ba zuwa zanyi ba, yana gama fadin haka yajuya yanufi stair ɗin ban garen hagu "a fusache yusuf yajuyo yana binsa da kallo yace what wae Aryan meyake damun kune "ɗaya daga chikin su'ma yasake mikewa yana faɗin to dai kunsan tsakanina da Aryan, babu ban ban chi, idan yayi abu, nima zanyi idankuma bai yi'ba nima bazan yiba, dan tare aka haife mu kuma tare muke komai, yana kaiwa nan ya juya shima yanufi stair ɗin bangaren dama " kwashe wa da dariya Ahmad yayi, yana fadin amma Aryan da Aiman yan iska'ne wlh anafaman kashe wutar da DON yake kokari kunna'wa su kuma zasu kunna nasu. "akule yusuf yache kaikuma Ahmad menene hakan to ae wan nan ba abun dariya bane,ae ko zakuyi'wa, kowa irin wan nan rashin mutunchin tofa banda hisham, kar'kamanta fa tare muka taso, tare mukeyi duk wani abun daza muyi komai namu iri'ɗaya duk da iyayen mu ba ɗaya ba, katashi muje mushawo kan DON tukunnan muje musamu yaya Aryan, dan shine matsalar idan yache zaije tofa Aiman mai sau'kine, dan shi duk abun da Aryan ya aika'ta shima ae'katawa zai yi " kama hanyar tafiya khalid yayi yana faɗin wlh yau DON ya batamin rai haba dan allah " da sauri Ahmad ya rufe'masa baki da hannun sa yache ya isa yanzu dai muje mushawo kansu dan sulhu muke nema dasu ba faɗa ba "faɗa masa dai chewar yusuf " haurawa saman stair sukayi wani katafaren hadadde palo suka shiga " palan ya tsaru iya tsaruwa komai na chikinsa farine tas harta labulayen suma farare ne tas ga manya manya sofa set ɗaya gawani makekiyar plasma TV dake gefe,babu kowa a palon sae karan AC dake tayi, kai tsaye suka nufi chikin betroom ɗin,"subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangiji jama'a ninaga aljannar duniya,manya manya sofa set ne,set 1 ga wani ɗan karamin table a tsakiya,gefe guda kuwa wani katafaren gado wadda ko mutun 10 zasu iya kwan chiya a kae, daga ɓan garen hagu kuwa kofar dressing room ne,sae kofar toilet kusa da dressing room ɗin, betroom ɗin ya tsaru'ne sosai idan nache zan tsaya zayya no muku tsaru war batroom ɗin nan to zamu kwana mu wuni bamu gama ba"kwanche DON yake akan katafaren gadon'sa dake shin fiɗe da white bet shit,kwan che yake ya miƙe kafar'sa har tawuche gadon tsawo,ya chire rigar sa faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe ga wani gashi dark black mai tsantsi kwan che a kan faffadar kirjin nasa, damtsen hannun nan nashi kuwa tamkar zasu fashe,saboda karfi, kamar wani sa'daukin yaƙi,"yana'jin shigon war su Khalid amma ko kallan inda suke baiyi ba
yusuf ya wuche wajen courting ɗin yasa hannu ya yaye,wata kofar glass ne ya bayyana awajen daga chikin daki kana kallan me a wajen,wajen shaƙa'tawane mai dauke da runfa da kugeru awajen da wata table a tsaki yar kugerun, agefen kuwa wani dan karamin pool ne mai kama da baf ɗin wanka, yana ɗauke ta sky blue ruwa

"DON pls katashi muna'san magana, da kai ne chewar Yusuf" shiru DON yayi kamar baiji su ba "hayewa gadon Khalid yayi,yana faɗin pls prince katashi mana, ko kallan inda suke DON bai yi'ba bare su sa ran zai amsa musu, "haba big bro dan allah to imma bazaka tashi ba,pls kaba mu amsa dan awan nan karan ba shiru muke san kayiba, kanaji koh chewar yusuf " DON dae bai tanka su ba "a fusace Ahmad yace look DON dan Allah kar ka che bazakaje bikin hisham ba wlh idan kayi haka baka kyauta ba,kasani hisham fa jinin mune " dogon tsaki DON yaja atakai che yace in kungama zanchen naku saiku fita kubar'min ɗaki, dan kuna damuna wlh " afusa'che Khalid yafara magana wlh bazamufita mu zakawa iskan'chi to barikaji dole kaje bikin hisham, in bahakaba sai dai kazaba ko,mu kokuma ka kasanche kai kadai "a'takaiche DON yace ae daman ni ka ɗae nafijin daɗin rayuwa "haka kache koh, baisake che musu ko uppan ba haka sukayita surutun su har suka gaji sukamike suka fita suna fita " DON ya daukoh wata remot ya saita'ta saitin kofar dakin ya danna remot din jikake lok lok kofar tana kulle kanta,ajiye remot ɗin yayi yajuya yana fiskantar wajen shaka tawan,

Su yusuf kuwa suna fita dakin, DON ɗakin, Aryan suka nufa wani ɗan corridor suka bi ɗan tafiya kaɗan sukayi suka shiga palo Aryan, komai na palan iri ɗaya ne dana DON sai dai na Aryan ash colour ne babu kowa a palo kai tsaye betroom ɗin sa suka nufa,da sallama a bakinsu suka shiga, Aryan yana zaune yana aiki a laptop shikuma Aiman na kwanche yana latsa waya " chikin ladabi da neman sulhu yusuf yafara magana wai me hakane bro,baikamata muyiwa hisham haka'ba,pls kar kuche baza kuje ba " daga Aryan har Aiman ɗin ba wan da ya tanka yusuf " akule yusuf yakuma chewa pls wai meyasa ku keyin hakane dan Allah " yusuf idan fa yaya Aryan ya yarda zaije nima wlh zan je, amma in bazai jeba takin takalmi babu inda zanje nima chewar Aiman " juyo Yusuf yayi yana kallan Aryan da ko kallan in da suke su bai'yiba bro dan allah kar kache bazakaje ba' dan wlh ko bazakaje bikin kowa ba ya'zama dole kaje na hisham dan kuwa hisham yazama tam kar jinin mu ya'zama tamkar ɗan uwan mu,a'fusache Aryan yajuyo' yana faɗin "kasan dai bani da yayan daya wuche DON koh to ko bikin shi ake bazan jeba " a'fusache khalid yache wai meyasa bakuda hali mai kyau ne dan allah, daurin aurefa kawai zakuje,"shiri Aryan yayi bai sake tan kasu ba yachi gaba da aikin sa " yusuf kuwa kallan Aiman yayi yace bro zo muje waje muyi magana

palon suka fita, yusuf yayita lallaɓa Aiman har ya yarda zai bisu "kowa ya nufi ɗakin sa dan shirin tafiyar,

shir'yawa sosai sukayi suka fito suka haɗu a babban palo,"to bari na tambayo mana Aryan sae muyi using jet nashi koh chewar yusuf ya karisa maganar yana hayewa stair ɗin yanufi dakin Aryan, a kwanche ya same sa yana latsa waya, harara Yusuf ya wunga masa kafin yache zamuyi anfani da jet naka "batare da ya kalle'sa ba yache adawo lfy " juyawa yusuf yayi yafito, yasa mu su Khalid a palo suka jera zuwa waje motochi 4 suka ɗauke su zuwa Airport, Khalid Yusuf, suka shiga mota ɗaya Aiman Ahmad suma motar su ɗaya, saura moto chi 2 kuma sojoji yaran Yusuf ne a chiki, a jere motochin suka chera da matsakai chin gudu suka miƙi hanyar fita daga gd, da sauri security dake bakin gate suka wan gale katafaren gate ɗin, a hankali suƙa danna han chin moto chin waje,suna fita su ka karawa motochin gudu, sosai suke sharara gudu chikin kan kanin lokachi suka isa Airport, suna isa suka tarar an gama shirya komai su ka ɗai ake jira su tashi, basu wani ɓata lokachi ba suka fito daga motochin,suka nufi jet ɗin Aryan suka shiga suka zauna ba wan da yache da ɗan uwan sa kala kamar an musu zuwa dole karfe 7 na safe jirgin nasu ya ɗaga suka lula a sararin, sama'niya sai babban birnin tarayya Abuja Nigeria

Jirgin su na sauka a Airport na Babban burnin ta'rayya, dan kara dan karan motochi masu numfashi ne sukazo ɗau kan su, wan ɗa a'kallah yawan motochin zasu kai 8 ga kuma motochin 5 na sojoji abaya " wasu jib ga jib gan sojoji guda 4 ne suka diro kasa daga samar motar su fiskar sun nan babu annuri ko kaɗan riƙe suke da manya manya Gun a hannun su, su na takawa irin takun jaruman maza,suka nufi su Yusuf, da sauri biyu suka tare bayan su biyu kuma suka tare gaba, Yusuf kuwa sae taku yake kamar wani sa dauki,har suka karisa wajen motochin,da sauri sojojin dasu gaban su suka fara buɗe musu kofar motochin, Khalid da Yusuf suka shiga mota ɗaya Aiman da Ahmad kuma suka shiga mota ɗaya,hannu sojojin suka ɗaga suka sara wa Yusuf san nan suka rufe kofar motochin,da gudu suka juya suka nufi nasu motar, sauri sauri suka motochin key, da matsakai chin gudu suka bar Airport ɗin,suka miki shin fi ɗadɗiyar titi gudu suke shararawa sosai har suka kusa chikin anguwar wuse 2 bakin wani katafaren gida na alfarman kae kaga ganin gidan kasan ya tsaru,suna karisawa bakin gate ɗin suka rage gudun motochin nasu, wani soja dake zaune kan plastic chair ne ya taso da sauri ya wan gale musu katafaren gate ɗin, kusa motochin chikin gida sukayi kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin sojojin suka fito da sauri suka buɗewa su Yusuf kofar motar, a nitse suka fito,jingina da jikin motar Yusuf yayi yana bin gidan da kallo,gidan part 4

wani saurayi ne yafito daga ɗaya daga chikin part na gidan ya nufo su Yusuf yana ɗan murnushi, da sauri ya karisa wajen yayi hugging na Yusuf yana faɗin Wellcome,my brother's bai jira amsar Yusuf ba yasake sa yabi su Khalid ma ɗaya bayan ɗaya yana hugging nasu, bayan yagama hugging nasu ne ya dawo da kallan sa kan Yusuf yana faɗin,"Yusuf DON da Aryan basu zo bakoh "sorry hisham Yusuf ya faɗa yana ɗan sosa kai, murmushi hisham ya ɗanyi yana faɗin bismillah muje chiki,gaba yayi suka bishi a baya,part nashi suka nufa,a haɗaɗ'ɗiyar palon sa suka zaune, shiru sukayi ba mai magana dan duk kansu ba masu yawan surutu bane almost 15 mnt Yusuf ya katse musu shirun da chewa, " Hisham ana gama daurin aure nanfa, zamu wuche kano,da sauri Hisham ya ɗago yana faɗin "haba yusuf sai kace ko rin ku ake dan Allah kun fa San ni bani da wani friends Sai ku taya kuke san naje wajen dinner ba friends, "aa Hisham tun dana che maka ana ɗaura aure zamu wuche tofa sai mun tafi,dan kuwa mu iya ɗau rin aure kawai mu kazo "nasani Yusuf amma pls ku bari sae gobe ku wuche,mikewa Aiman yayi yana faɗin "yau zamu tafi ba sae gobe ba kuma karfe 4 dai dai zamu bar garin man ko an daura auren ko ba a daura ba yana gama faɗin hakan yanufi waje, girgiza kae kawai Khalid yake, shiru Hisham yayi dan kuwa yasan ko me zai che musu bazasu tsaya ba tunda su kache yau zasu wuche tofa ba abun da zai hana su tafiya,dan duk chikin su ba mai magana ya sauya in sun yi magana sun yi ne ba chan'ji,shiri suka zauna palon ba wan da yasake chewa ko uppan

Aiman kuwa yana fitowa waje kai tsaye inda sukayi parkin na motochin su yanufa, da gudu ɗaya daga chikin sojojin dasuka zo dasu ya nufo shi buɗe masa mota yayi,Aiman yashiga ya zauna,ya zuro kafar sa waje ya chiro wayar sa yana latsawa, gefe sojan yakoma ya tsaya yana jiran permission su tafi almost 20 mnt yana zaune yana latsa wayar sa, ɗago kai yayi zai yiwa sojan magana sai wayar sa tafara ringing,bin screen ɗin wayar yayi da kallon ganin sunan Aunty Mardiya che ya sashi jan dogon tsaki,har wayar ta katse bai ɗaga ba kira na 2 yasake shigowa, tsaki yakuma ja kafin yayi picking call ɗin ya kara wayar a kunne yana faɗin hello, daga ɗayan ɓangaren "Aunty mardiya tace...


Read / Download DUK KARFIN IZZATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album