Join Our WhatsApp Group

YATSUNMU Complete Hausa Novel Document by YATSUNMU


YATSUNMU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51536



YATSUNMU

Reading Time: 4 Hours

Added On: 16, Jul 2023

Author: Sadnaf ,

Ebook Compiler : Princess Aysha Muhammad

Author Group : PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 280.62 kb

File Type: txt

Views: 1229+

Download: 624+

Last download: 2 days ago

Description/Story: Compiled by Princess Aysha Muhammad
Copied by Umar Dalha

*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_




*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesing story*




Page 1_5



*BASHIR*


*BASHIR MAGIDANCI NE YANA SANA'AR SIYAR DA KAYAN ROBOBI,IRINSU BOKITIN WANKA NA ROBA,PARKER,PO,KWANDO BUTA DA DUK WANI ABU DA YA DANGANCI ROBA,YANA DA MATA D'AYA FATEEMA DA YARA HUD'U ALIYU SHINE BABBA HAMIDA MABIYINSA,SUMAYYA,SAI AUTA NURA,BASHIR DAI DAI GWARGWADO YANA K'OK'ARIN YAGA YACI K'ARFIN BUKATUN GIDANSA GA WANDA YAKE DA GODIYAR ALLAH ZAI IYA CEWA SUNA CIKIN RUFIN ASIRI DAI DAI GWARGWADO DAN BASU RASA CI DA SHA BA,NA DAI DAI TALAKA BASHIR BASHI DA MATSALAR KOMAI DAN YANA GODEWA ALLAH A MATSAYIN DA YA AJIYE SHI DUBA DA Y🅰TSUN MU BA D'AYA BANE,IN WANI YAFI KA KAFI WANI,MATSALARSA K'WAYA D'AYA CE MATARSA FATEEMA TANA DA HANGEN WAYANDA SUKA FISHI,BATA TAB'A GODEWA ALLAH A MATSAYIN DA YA AJIYESU HASALI MA CIKIN GORANTA MISHI TAKE TAMKAR SHI YA D'ORAWA KANSA TALAUCI BASHIR NA MASIFAR HAK'URI DA ITA,BATA BASHI GIRMA A MATSAYIN MIJINTA,BATA JIN KUNYAR TA ZAGESHI AGABAN 'YAYANSA*



*ALHAJI AHMED*

*MAK'OCIN BASHIR NE GIDANSA NA JIKIN GIDAN BASHIR CUSTOM NE YANA KUMA WASU BUSSINESS D'IN,MAI KUD'I NE YANA DA MATA D'AYA KHADIJA DA YARA HUD'U SHIMA,WALEED SHINE BABBA SAI MABIYINSA NANA KHADIJA,SUNAN MAHAIFIYARTA AKA SA MATA ANA CE MATA NANA SAI MUHAMMAD,SAI AUTA AISHA ANA CE MATA MEEMEE, ALHAJI AHMED DA MATARSA KHADIJA MUTANEN KIRKI NE DAN BASU DA GIRMAN KAI KO KAD'ANHANNUNSU A BUD'E YAKE AKWAI SU DA KYAUTA DA ALHERI,SUN KUMA SAN DARAJAR MAK'OTANSU,SUNA ZAMAN MUTUNCI SOSAI DA BASHIR DA IYALINSA WANAN KENAN*





Fateema ce ta fito daga d'akinta a fusace tana "Bashir na gaji na gaji da irin wanan rayuwar da nake yi a gidanka na masifaffen talauci,kamar daga kanka aka fara talauci,babu chanji ko kad'an ballantana cigaba,shekara goma sha biyar da aure,kullum jiya e yau kaf unguwa nan babu Wanda ya kai ka talauci,yanzu dubi mak'otanmu kullum shanawarsu suke,kai bazaka zuciya kayi kud'i kamar Abban waleed ba,nida yaranka sai kace almajirai,yaushe rabon da ka min d'inki a gidanan,yayanka haka suke yawo kamar Almajirai,abinci babu na kirki,duk dare tuwo,safe dumame,tuwo na Neman ya mana tsiro,haba na gaji wlh na gaji,wlh gwara gidanmu sau dubu da gidanka,"



Tunda Fatima tafara magana bashir ya sunkuyar da kansa zuciyarsa na masa zafi,duk maganganun da take na k'ona mishi zuciya,ayanayin da yake ciki baya jin zai iya magana dan idan ya bud'i baki zai yi magana zai iya fashewa da kuka Dan mutum ne shi mai raunin gaske,bai ce mata komai ba ya ajiye d'ari ukun hannunsa akan kujera 'yar tsuguno dake tsakar gidan,dan dama sabida kud'in daya bata ta fito tana gaya mishi magana,hanyar waje yayi bayan ya ajiye kud'in Fateema kuwa ta bishi aguje ta rik'e bayan rigarshi tana,"wlh kazo ka kwashi kud'inka dan ban ga abinda d'ari uku zai min a gidanan ba nayi cefanan rana nayi na dare ko kunya baka ji ba,mak'otanka na bad'a dubu d'aya dubu biyar kai kana bada d'ari uku,Allah ka kwashe kud'inka bazan iya cafenan d'ari uku ba ehe"


Zuwa wanan lokacin Bashir hawaye ya taru a idonsa cire hanunta yayi daga ruk'on da ta masa yace,


"Fateema dan Allah mai yasa kike min haka ne? Naga dai talaucin nan bani na d'orawa kaina ba,abinda kika kasa ganewa har gobe Y🅰TSUN MU BA D'AYA BANE,KAFI WANI,WANI YAFIKA, ina godewa Allah a matsayin da ya barni,dan ni nasan nafi mutane dubu,Wlh ko iya lafiyar da Allah yabani arziki ne," katse shi Fateema tayi da sauri tana "wlh karyane babu Wanda kafi,kaf duniyar nan kafi kowa talauci,duk gidajen makotanmu danake shiga wlh babu Wanda ya kai ka talauci,sai kace dan kai aka yi talauci a duniya"?

Bashir da kalamanta ba k'aramin tafasa masa zuciya yake ba hawayen da yake hana su zubowo ne suka hau tsare a kumatunsa,cewa yayi "Fatima kenan banida abinda zan ce miki sai dai nace Allah ya shiryeki dai dai gwargwado ina k'ok'arin sauk'e nauyin da Allah ya d'ora min,ina Baku rasa ci da sha ba,Baku" '' katse shi Fateema ta k'ara yi da sauri tace "in kana cewa ci da sha wlh wani irin bak'in ciki ne yake rufeni,wane ci da sha kake bamu,tuwon massara da shinkafa 'yar Hausa da koko da kosai da muke ci shine har wani ci da sha da kake bamu,naji kana bamu chi da sha,sutura fa sai sallah sallah,nan makaranta kasa yaranka ana arziki duk ana gwamnati ka jefa su,da antashi kace yaranka na makaranta,kaf unguwarnan,yaranka kadai ke zuwa makarantar gwamnati,Bashir dan Allah dubeni ahaka ka auroni,arame a kanjame,waye zai gani yanzu yace ni fara ce,zaman gidanka ya maidani bak'a k'arfi da yaji,haba na gaji wlh Allah na gaji,bazan iya cigaba da zama dakai ahaka ba,tun da saurana gwara ka sakeni inje in auri mai kud'i in samu in ringa kula da 'yayana,kasan Allah Bashir na baka nan da wata d'aya idan dai ba asamu chanji ba wlh gidanmu zan tafi,kai bawa kana fatan ace in kayi aure ace jin dadin gidanki yafi na gidanku,Amma dan masifa nafi jin dadin gidan iyayena,Khadija matar Alhaji Ahmed da mai ta fini na fita Kyau nesa ba kusa ba Amma dubi Wanda take aure har motar kanta ne da ita,haba na gaji"


Fateema tace tana girgiza,Bashir kasa magana yayi dan jikinsa har wani rawa yake,sabida b'acin rai,fita yayi daga gidan yana share hawayen da ya zubo mishi,tafe yake yana surutai shi kadai yana "Allah kana kallon baiwarka kana kallon irin cin mutuncin da take min akan Jarrabta daka min na talauci,ba ni na d'orawa kaina ba kai ka d'oramin,na rungumi jarrabtar daka min da hannu bibiyu Allah ka dubeni da idon rahama kabani ikon cinye wanan jarrabtar da kamin,Ya Allah ka nisance ni da haram ka kusanceni da Halal,ya Allah kar ka bani ikon k'auce hanya dan halin Dana ke ciki,Alhamdulillahi Ala kulli halin,Allah ina gode maka kullum bazan kuma fasa gode ma ba", ahaka Bashir ya nufi shagonsa yana surutai shi kadai.,


Fateema kuwa tana ganin ya fice taja tsaki ta nufi d'akinta,tana shiga d'akin hijabinta dake bak'in k'ofa ta zaro tayi waje.



Gidansu Alhaji Ahmed ta shiga da sallamarta,a Palo ta Tarar da Khadija a zaune tana duba d'inkunan da aka kawo mata,Khadija murmushi ta saki hak'oran maccanta guda biyu suka bayyana a lokacin da take amsa sallamar da fateema tayi,sannu da zuwa Khadija tayi mata tana mik'ewa tsaye Fateema itama murmushin tayi tana amsawa ta samu d'aya daga luntsuma.luntsuman kujerun dake palon ta zauna,aranta tana Allahuma arzukuni,duk da ba wanan ne k'aro na farko da take shiga gidan ba dan shekara d'aya kenan tana shiga gidan amma Indai ta shiga sai tabi ko ina da kallo tace Allahuma arzukuni a zuciyarta,Kayan makulashe aka kawo mata kamar yanda dai aka saba kawo matan dan indai zata shiga gidan sau hud'u arana sai an kawo mata wani abun,gaisawa suka k'ara yi bayan Khadija ta ajiye farantin ta zauna akan kujerar da ta tashi ta cigaba da duba kayan, bismillah Fateema tayi tafara cin potatoe ball da nama da aka ajiye mata da kunun gyad'a,da yake wajen 9 ta shiga gidan abun da suka karya dashi ta kawo mata,Fateema cewa tayi "Khadija sababin d'inki kika yi ne"? Dan ada Hajiya take cewa Khadijar,khadijar ce ta hanata ce mata hajiya tace bata so taringa kiranta da sunanta dan sa'anin juna ne su.


Khadija murmushi tayi tace "eee wlh d'inkunan Dana bayar aka kawo min amma abun haushi wlh duk basu yi min irin style d'in Dana zaba ba,acikin dinkuna goma dana bayar guda hud'u ne kawai suka min irin Wanda na zab'a kingansu nan" Khadija tace tana d'aga dinkunan tana nuna mata,Fateema da yake ta San kan maula mik'ewa tayi da sauri ta nufi inda take tana " kai kai kai amma d'inkunan nan sunyi kyau tsalli,kinga yanda suka yi kyau kuwa," tab'e baki Khadija tayi tace "wlh ni basu min kyau ba ko kadan,guda hud'un nan ne kawai suka yi kyau"

Rik'e baki Fateema tayi tana d'aga sauran tana " yanzu tsakani da Allah wadanan basu yi kyau ba ina laifi ai in ni nasamu wanan bana jin zanyi barci,tab kina dasu ne shiyasa kika cewa basu miki kyau ba amma in ba haka ba ni banga aibun kayan nan ba," murmushi Khadija tayi tace "to ki kwashe kayan na bar miki tunda ke sun miki kyau" fateema zubewa tayi akasa dan dama tasan zata bar mata dan indai ta nuna tana San Abu sai Khadija ta bar mata,godiya tafara k'okarin ta zuba mata Khadija ta d'aura fuska tana bata San irin wanan zasu yi fad'a,ahaka Fateema ta shantake a gidan suna hira,Khadija ganin sha biyu tayi ne yasa tace mata bari ta shiga kitchen ta d'ora abincin rana,har kitchen Fateema ta bita ta ringa tayata tana had'iyar yawu,sai da ta daidaici ta kusa gamawa tace mata zata tafi,Khadija ce mata tayi dan Allah ta tsaya ta zuba mata taci, Fateema girgiza mata kai tayi da sauri tana ta koshi ta fice waje dan tasan Khadija zata biyota da abincin,kuma da yawa take zubo mata,yanda zai ishi ita da yaranta, har mamakin halin Khadijar take bata tab'a gajiya duk da kusan kullum sai ta shiga gidan,kayan da Khadija ta bata ta zuba akan gado ta fara d'ad'agawa tana tsallen murna dan had'add'un kaya ne wajen kala shidda atamfa uku less shadda da material,tana cikin gwagwad'a kayan 'yar aikin Khadija tayi sallama hanunta d'auke da k'aton kula da wani zungureren jug yana tsiyayyar sanyi,da sauri ta k'arbi kula da jug d'in tana an gode, tana ganin ta fice daga gidan tayi sauri ta bud'e kular,cinyar kaza ta d'auko ta yaga tana lumshe ido,sai data cinye har kashin ta k'urbi lemon ginger, ta rufe kular tana lasar hannu,idanta ne ya sauka akan kud'in da Bashir ya ajiye mata dazu ta buga uban tsaki tace " Mitsiyaci kawai",mik'ewa tayi ta fara jera kayan a sif.



Wajen k'arfe d'aya da rabi su Aliyu suka dawo daga makaranta,d'akinsu suka wuce suka cire Uniform d'insu suka fito tsakar gida suka zauna akan tabarmar da Fateema ta shimfid'a Nura wajen murhu ya kalla dan yaga ko anyi girkin rana,ganin babu alamar an hura itace a gidan bane yasa ya kyab'e fuska yana k'ok'arin magana,Fitowar Fateema daga d'aki da kula a hannu ne yasa suka saki murmushi gabad'aya dan sun San abincin gidansu waleed ne,zasu ci dadi,Fateema ganin suna murmushi ne yasa itama tayi murmushi ta ajiye kular tana " yara kenan ma sun San abinci mai dadi,ballantana manya, Allah dai ya rabamu da wanan talaucin,ni dai ina gaji tafiyata zanyi wlh,Aliyu maza d'auko mana faranti mu juye,Aliyu mik'ewa yayi da sauri ya d'auko farantin,ta juye fried rice da soyayyan kazar akai,bismillah suka yi da sauri suka fara ci suna loma baga uwar ba baga yayan ba,bayan abincin ya kare duk da sun koshi,sai da suka ringa sid'e farantin,bayan sun gama sid'ewa Fateema ta raba musu kazar,aikuwa har kashin suka taune suma, Nura yana gama cinye nasa, ya Kalli Fateema yace " Umma muma kiringa mana irin wanan girkin kina sa mana kaza" tsaki Fateema tayi tace " ina mitsayacin ubanka yaga arzikin da zai siyi shinkafar gwamnati ballantana akai ga ya siyi kaza,ai ubanka bashi da kud'in ko da siyan fara ne" Aliyu da Hamida da yake suna da wayyo take suka d'aura fuska Hamida tace "Umma zagin Abbanmu fa kike bai kamata ba yana mana k'ok'ari" mari Fateema ta d'auketa dashi tana "an zage shin ba mitsiyaci bane" Hamida hak'uri ta bata ta mik'e ahankali ta d'auki farantin tana share hawaye.


Fateema daddare sabida bak'in hali irin nata, tuwon massara tayi daddare da miyan kuka bako mai sai maggi,tuwon ma mai tauri tayi,ta loda a kular Bashir ta kai d'aki ta ajiye mishi,Hamida ta kalla tace mata taje gidansu Khadija tace mata dan Allah intayi girkin dare ta San mata,ta bawa Nura tuwo tayi kuma Nura baya cin tuwo, Hamida ba asan ranta ba ta nufi gidansu Khadija dan tana jin kunyar rok'on da Fateema take aikenta tayi kullum,da k'yar ta fad'awa Khadija sak'on ummanta,aikuwa cikin rawar jiki,Khadija ta nufi kitchen ta zubo abinci awani katon kula ta kawo mata,tace tace tana gaisheta har ta kai k'ofar Palon,Khadija ta kirata ta bata wani Leda cike da kayan tea da bread mai yanka yanka guda biyu,har kasa Hamida ta d'urkusa tana mata godiya,Khadija ta kai mata duka tana bata so.


A soron gidansu ta samu fateema atsaye,da sauri ta k'arbi kular hanunta,tana kar ta tsame naman ciki bata sani ba,akan tabarma ta zauna ta juye tuwon shinkafa da miyar agushin dayaji naman rago,tace musu su matso suci tun kafin mitsiyacin ubansu ya dawo,matsowa suka yi da sauri suka fara ci banda Aliyu da Hamida,wani mugun tsawa Fateema ta Daka musu tace zasu sa hannu ko sai ta ci ubansu,da sauri suka sa hannu suka fara ci,sai da suka gama ci Fateema taga ledar kayan tea d'in da Khadija ta bawa Hamida, da sauri ta jawo ledar tana ganin kayan ciki ta saki murmushi tana

"Allah kayi wa matar nan albarka gobe zamu sha shayi da madara"

Mik'ewa tayi da sauri ta d'auki ledar ta kai d'akinta ta b'oye ta fito ta zauna akan tabarmar tana gyatsa.ana kiraye kirayen sallar Ishai Bashir ya dawo ahankali yayi sallama kamar mai tsoro dan yana fargabar irin rashin mutuncin da Fateema zata kuma masa yau,duk da yau ya d'an yi bajinta ya siyo lemon bawa da ayaba,Dan ya burge fateema,su Aliyu ne suka amsa sallamar,Fateema kuwa ta kau dakanta tana sakin tsaki,jiki asanyaye ya k'arasa kan tabarmar yana satar kallon fateema ,dan kwalliya tayi sosai da material d'in da Khadija ta bata,Bashir kuwa ganin bai tab'a ganinta da kayan bane yasa yayi ta satar kallonta,ledar dake hanunsa ya ajiye,fateema ta juyo tana kallon ledar,jawo ledar tayi tana tab'e baki, tozalin da tayi da lemo da ayaba ne yasa taja dogon tsaki tana "kai fa nan ka gama k'ok'ari ko? Ko kunya baka ji ba,ana shigowa da kaza da tsire kai ka shigo da lemo da ayaba,mtsss" ta k'ara Jan wani dogon tsaki ta mik'e ta shige d'aki,bayanta yabi da kallo har ta shige d'akin wani kullutu yaji ya tsaya mishi wuya,ahankali ya dawo da kallonsa kan yayansa,Aliyu da Hamida yaga sun canza fuska da alama basu ji dadin abinda Fateema tayi wa mahaifinsu ba,murmushi ya k'irkiro yace musu su d'auki lemo da ayaban suje su wanke su zo su raba" mik'ewa yayi yabi bayan Fateema,yana shiga d'akin yaganta a kwance akan gado sai girgiza k'afa take,zama yayi agefenta yace "Fateema wai yaushe zaki daina wulak'antani agaban yarana"

Wani mugun harara...


Read / Download YATSUNMU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album