Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

JIDDA Complete Hausa Novel Document by JIDDA


JIDDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 79645



JIDDA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 04, Jul 2024

Author: Maman Mama ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08067081020

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 398.26 kb

File Type: txt

Views: 1950+

Download: 2511+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: 
*Happy New Year 2021*
Allah yasa mun shiga a sa'a ameen

*💔 JIDDA 💔*

*By*

*Maman Maama*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu alaikum masoyana da masoyan littattafai na. Kamar yadda nayi alkawari tun kafin in fara *Tagwaye* cewa zanyi su su biyu da *Jidda* to alhamdulillah an kammala Tagwaye ga kuma Jidda nan yazo muku, ina kuma fatan zaku karbe shi kamar yadda kuka karbi Tagwaye koma fiye da haka.

Dan dai idan nace *Jidda* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *Jidda* ba zan iya cewa an barki a baya. It is going to be a hit, that I promise you.

Tafiyar *Jidda* da banbanci da sauran littattafai na, banbancin kuwa shine about 70% na labarin Jidda is based on true life events, musamman daga farkon sa zuwa tsakiyar sa, karshen sa ne kawai zai zama fiction yadda zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shine from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share hawaye, so get ready to do both.

Littafin Jidda na siyarwa ne kamar yadda na riga na fada tun kafin fara Tagwaye. Da farko nayi niyyar sai na gama gabaki daya zan fara posting, but I found out cewa ba zan iya ba, without your motivation I lost my courage, wannan ya tabbatar min idan babu readers babu *Maman Maama* dan haka zamu fara a haka.

Sai dai ba za'a ke samun posting kullum ba saboda alhamdulillah kullum responsibilities suna kara yi min yawa ne, I guess wannan shine girman ko? Lol. Za'a ke fashin kwana dai dai, misali in akayi Saturday ba za'a yi Sunday ba sai Monday. Yes, nasan wadansu ba zasu iya jira ba and I advise them to wait sai anyi nisa ko kuma ma su bari a gama sai su karbi document. Please in kinsan ba zaki iya jira ba kar ki biya, don't pay and be pressuring me please. Fashin kwana dai dai so that you will have well arranged and well edited episodes insha Allah. I assure you that ba zakuyi dana sanin siyan Jidda ba, it is going to be one of your best dan for me *Jidda* already ya kere wa saura a zuciya ta.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067801020

Please banda kira, WhatsApp only

Again dai ina tunawa nasu siyan online novels cewa copyright (hakkin mallaka) na marubuciya ce, ita kadai take da right din copying da kuma sharing littafin ta, duk wanda yayi hakan bayan ita to ya shiga hakkin ta kuma duk munsan cewa Allah baya yafe hakkin wani har sai shi ya yafe da kansa.

Allah yasa mu gane ameen.

Akwai 18 free pages insha Allah

Asha karatu lfy

*Episode One........The Beginning and the End of Me*

Free page

A duk lokacin dana duba rayuwata, kamar in inaso in bada labarina, na rasa dalilin da yasa bana iya farawa ta farko na, bana iya farawa ta lokacin da aka haife ni ko kuma ince lokacin da na bude idona na ganni a duniya. A kowanne lokaci in na duba bayana ina farawa ne da ranar dana fara ganinsa, a gurina wannan ranar, wannan hour din, wannan minute din da kuma wannan second din da idanuwan sa suka shiga cikin nawa a lokacin ne rayuwata ta fara. A lokacin ne kuma rayuwata ta kare.

Ranar visiting day ce a makarantar yammata ta garin Taura dake jahar Jigawa. Kasancewar yan ss3 ne kadai a makarantar suna zaman extension wanda ake yi lokacin zana jarabawar karshe ta secondary ya saka makarantar take shiru ba kamar sauran ranakun visiting ba.

Ni da babbar kawata a lokacin, Mufida, munyi duk abinda yake al'ada ta dalibai dan wannan ranar, munyi wanki da guga da kitso, sannan muka tashi da wuri mukayi wanka muka yi kwalliya dai dai irin wacce ake barin dalibai suyi sannan muka fita class area tare da sauran ɗalibai dan jiran tsammani, duk da dai muna saka ran tabbas za'a zo mana visiting daga gidajen mu dan ba'a taba fashin zuwa mana ba sai dai in da kwakwkwaran dalili.

Can nesa muka samu benchi muka zauna, dan ba'a bari dalibi yaje gurin sai an kira shi sai su headgirl da kuma prefect on duty. Kasancewa ta health prefect kuma kasancewar ba duty na bane ranar yasa nayi zamana muna hira excitedly da Mufida. "Yaya Mukhtar yace min zaizo, yace tare da matarsa Aunty Halima ma zasu zo" Mufida tace "hmm. Ni bansan ma dawa dawa za'a zo min ba. Nasan dai Mama confirmed zata zo"

Kiran sunana da mukaji anayi ya saka mukayi saurin juyawa cike da mamaki. Na kalli agogon fatar da yake hannuna, few minutes after ten, nooo there must be a mistake dan nasan yan gidan mu ko wanka basu gama yi ba balle girki balle har su dauko hanya daga kano balle su zo. "Hauwa'u Habib" aka sake kirana. Na mike ina kallon Baba mai kiran alkhairi da yake tsaye da takarda a hannunsa "Baba? Hauwa'u Habib da gaske?"

Ya nuna min takardar, "karanta da kanki in kina ganin ban iya karatu ba" na girgiza kai na "akwai Hauwa Muhammad Habib, ko dai ita ce akayi mistake, ni ba yanzu zasu zo ba sai yamma suke zuwa" yayi gaba yana cewa "sai kije can ki gani ai, in bake din bace ba sai ki dawo ki kira waccan din" na gyada kai tare da binsa da sauri ina yiwa Mufida signal cewa ina zuwa, yana ta zabga sauri, ni kuma in akwai abinda ban iya ba to sauri ne, generally ma ni komai nawa a sanyaye nake yinsa tun daga magana har tafiya har komai. Da wahala kaji ni na daga murya.

A gaban staffroom, inda few iyayen yara suka fara zuwa kuma mostly maza ne suka fara zuwa na hango motar Abban mu, nan take jikina yayi sanyi, shikenan ta faru ta kare anyiwa mai dami daya sata, shikenan Abba shi kadai yazo. A lokacin na ganshi ya fito daga staffroom yana duba agogon sa sannan ya dago kai briefly ya kalle ni yace "kiyi sauri mana! Kina tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, sauri nake yi daurin aure ne dani a gumel shi yasa banzo da iyayenki ba"

Na durkusa a gabansa "Abba sannu da zuwa, ina kwana?" Bai amsa ba ya cigaba da magana "kiyi sauri ki dauki sakon ki in wuce, already ma na makara har goma ta wuce. Umman ki ce ta tsayar dani wai sai ta soya miki miya" ya karasa yana zagaya wa baya tare da bude booth, na bishi can na sake gaishe shi "Abba ina kwana?" Ya fito da kwalin indomie da bagko ya ajiye sannan yace "lafiya lau, ya karatun? Komai dai lafiya ko? Babu wata matsala ko?"

Na gyada kai na automatically hawaye yana zubowa. Ya tsaya yana kallona, "kuka kuma? Wato kin fi son uwarki akai na ko? Shine kike kuka dan ni nazo uwarki bata zo ba ko?" Nayi saurin girgiza kai ina share hawayena. Wasu kuma sababbi suna replacing dinsu. Yace "kinga, sauri nake yi yanzu shi yasa ban taho dasu ba, kuma suna can suna rigimar tasu da suka saba. Ki bari in na koma gida, in mun sami albashi, sai in hado su da wani a cikin yayyenki ya kawo su ki gansu"

Na sake share hawayen ina gyada kai, sannan nace "Abba ina Farhan?" Ya danyi murmushi yace "tana can tana kuka wai sai ta biyo ni, rigimammiyar yarinya kawai, duk halinku ai iri daya ne" sai kuma ya fara shafa aljihun sa "kinga na manta ma ta bani takarda in baki. Yar banza, ko me ta rubuta a ciki?"

Ya dauko wata farar takarda daga aljihunsa ya miko min na karba ina dan murmushi kadan sai kuma hawaye suka biyo murmushin, ina ta burin ganin ummana da yanuwana, shi Abba ma yana daga can karshe a list din wadanda nake son gani.

Ya sake mayar da hannun sa aljihu ya dauko 1000 ya miko min. "Kun kusa kammala wa ai, in kika lallaba kayan nan da kuma kudin nan zasu ishe ki. Sai ki dage da karatu dan naga kamar kinfi yanuwanki son karatun, gashi nan kaf yan uwanki mata babu wacce take morar karatun ta duk sun biye wa mazajensu sunyi zamansu suna zuba yaya. In kika dage kika ci ssce sai ki wuce kiyi nursing, ko Allah zai saka in mori kudina a kanki"

Na gyada kai "insha Allah
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download JIDDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album