Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels




🎄RAINON DAWA🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free page

1/2


Bismillahir rahmanir Rahim.
Ina farawa da sunan Allah,mai kowa mai komai,wanda ya bani ikon kammala littafin MACIJE NE lafiya,sannan yanzu na fara sabon book dina,RAINO DAWA.ina fatan Allah yasa yadda na fara lafiya ingama lafiya.

Wannan littafin mallakina ne,banyarda wani ko wata ya juyamin shi ta ko wacce sigaba,saida izinina.dan haka akiyaye.

Sannan ga masu bukatar biyan kudin wannan littafin zaku biya kamar haka.

Normal group 300₦
Update biyar a sati.

Special group 500₦ update bakwai asati, kuma zaku iya samun update biyu arana.

Sannan akwai manyan mata,wadanda ke bukatar atura musu private,Ina sane daku hajiyoyina.
Zaku biya 1000₦

Duka zaku turo kudinku ta wannan acc. Din.
Saratu Kabir.
U.b.a
2215749011.

Saina jiku masoyana na Amana Ina sane daku.




_____________Dajine mai cike da tarin bishiyu,dogaye masu yawan gaske,hakan yasa ta wani bangaren na dajin yake da duhu da sarkakiya,wani gurin kuma zaka ganshi akwai wadatar haske.

Dajin yana da matukar girma,wanda ke dauke da halittu kala-kala.baka jin komai sai sautin kukan tsuntseye kala daban -daban.

Kasancewar yanayine na damuna,hakan yasa dajin yayi lub-lub dashi,gaba É—aya bishiyu dake cikin dajin sunyi ganye koraye shar dasu kwanin sha'awa.
Wasu daga cikin ganyayyakin har ruwa zakaga yana diga daga jikinsu,alamun raba.

Kai tsaye zamu iya cewa dajin yana da yanayi na ban tsoro,wanda bazaka taba tsammanin akwai wata halittar dan Adam dazata iya rayuwa cikinsa ba.saidai hakan bai hana dajin kyau da kawatuwa a idon duk wanda ya kalleshi ba.

Akwai birrai da yawa cikin dajin,sannan ana tunanin akwai mugayen namun dawa dake rayuwa cikin dajin.

Can gefe guda na hango wasu bishiyu kusan guda goma,acure guri É—aya,kamar wanda aka hada kansu,suna da tsayi amma ba kamar sauran ba,da alama dai kamar yankesu akayi.

Daga kaina nayi É—an kallon iyakar tsayin bishiyun,saidai ga mamakina wata bukka na hango asaman bishiyun nan É—onono,da alama kuma akwai mutum dake rayuwa cikin wanann bukkar. Dan kuwa kana iya hango abubuwa irinsu kwanuka,abin zuba ruwa,daga gefe kuma ga wani guri mai tudu wanda ke nuna alamun gurin kwanciyane.

Daga can gefen bishiyun nan na hango wata yarinya tsugunne gaban wata yar korama dake dauke da ruwa mai kyau da haske,gefenta kuma zagaye da yan kananan shuke shuke,yarinyar ta juya bayanta,kuma ba kaya ajikinta,dan daga ita sai wani dan karamin towel data ɗaura shi asaman ƙirjinta,da alama dai wanka take,dan kuwa ruwa take diba tana watsawa ajikinta.

Ahankali yarinyar ta mike tsaye tare da tattare uban gashin daya zubo gadon bayanta ta nannadeshi kamar gammo. sannan ta janyo wani dan zani ta daure kan nata dashi.juyowa tayi ta fara tafiya cike da kuzari atare da ita. Ta nufi jikin bishiyar nan.
Masha Allah !!!shine abinda bakina ya iya faÉ—a,sakamakon arba da kyakykyawar fuskar yarinyar da akalla shekarunta zasu kai sha takwas,doguwace mai matsakaici jiki,bazamu iya kiranta da Siriya ba,sannan bazamu ce mata mai jiki ba kai tsaye.tana da kira mai kyau da É—aukar hankali, daga kasanta abaje take sosai,tana da hips,sannan tana da albarkatun kirji,jikinta shar shar yake,ita ba bakaba kuma ba fara ba,irin choculate colour É—in nance.
Tana da rawn face,dauke da madaidaicin hanci mai kyau,idanunta dara dara ne farare tass dasu,bakinta dan karami,mai dauke da pink lips,ataƙaice dai zamu iya cewa kyakykyawar yarinyace ta gani afada.

Hankali kwance take takawa cikin É—an sauri ta nufi saman bishiyar nan, abin mamaki tana zuwa naga ta kama bishiyar cikin wani irin salo da kwarewa ta fara hayewa kamar wata biranya.kawai kama jikin bishiyar take tana É—an tsalle sai kaga tayi sama.
Cikin abinda bai wuce dakika biyar ba naga ta haye saman bishiyar nan.

Zama tayi tare da janyo wani abu mai kama da akwati,saidai kuma da itace akayishi.

Budewa tayi tare da ɗauko wani irin kaya masu kama da fatar damisa ta sanya ajikinta.riga ce doguwa,wacce duka duka bata wuce iyakar gwaurinta ba.sai wani wando irin skin tite dinnan shima iya gwuiwa,gashinta ta ware tare da ɗauko wani mataji mai ƙarfi dan da alama da katako akayi shi.

Taje kan tayi sannan ta rabashi gida biyu ta daure.bayan ta kammala daure kan nata,saita dauko wani ƙaton zani ta lulluɓa ajikinta,ga mamakina saina ga ta tada sallah,saidai kuma haka tayi sallar nan gwauri a waje,kuma akwai kurakurai sosai cikin sallar.tana idarwa ta cire zanin sannan ta dauko wata ƙatuwar kwari da baka ta rataya awuyanta, sannan ta dauki wata yar karamar wuka,ta soke jikin rigarta,inda ta janyo wata jela jikin rigar ta daure ta abaya.kanta ba ko dan kwali haka ta kama bishiyar nan ta sauko kamar yadda ta hau.

Tsayawa tayi tare da kallon gefen ta,kafin ta sanya hannu abakinta,harshen ta ta lankwasa sannna ta huri iska,nan take wani sauti mai kara ya fara fitowa daga bakin nata,kusan second biyar tana fidda wannan sautin, kafin ta dakata.saman wata bishiya naga tana kallo,fuskarta É—auke da murmushi.cikin tsalle da gudu naga wani biri dan madaidaici yana sakkowa daga bishiyar.kai tsaye akafadunta yayi masauki bayan ya gama sakkowar.
Dariya tayi tare da shafo jikinsa tace "janbu, zamu fita yau da wuri nake son muje mudawa,dan haka ka dage sosai yau kaji"ta fada cikin harshen Hausa tana shafa birin,

Shikuwa birin wani dan ƙara yake yi,alamun yaji abinda ta fada kenan,kafin ya sauko daga kafaɗunta.

Wani bakin abu mai kama da fata naga ta janyo daga jikin bishiyar da ta sauko,daurawa tayi akanta yayi kamar bandana,kafin ta fara tafiya,cikin azama birin yana Binta,suka nausa cikin dajin.

Masu karatu ina zata da wannan kayan haka?

Wacece wannan yarinyar.

Muje zuwa .

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share as much as you can.fisabilillah.[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄




🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free page

3/4

Ga masu son karanta wannan littafi,zaku biya kamar haka.


Normal group 300₦
Update biyar asati.

Special group500₦
Update bakwai asati.

Gareku manyan mata,masu so ta pc.
1000₦

Zaku turo kudin ku ta nan.
Saratu kabir
U.b.a
2215749011


Evidence of payment
08148360851.







______________Tafiya take cike da izza,sam ba wata alama dazata nuna maka cewar tana cikin yanayi na tsoro.domin kutsa kai kawai take cikin dajin,yayinda baka jin komai sai sautin kukan tsuntsaye da kwarina.
Wannan birin da ta kira da jambu yana biye da ita,cikin dan gudunsa mai haÉ—e da tsalle.

Suna cikin tafiyar ne,ta hango wasu zomaye guda biyu.da sauri ta dakata,tare da daga wa birin nan hannu, alamun shima ya dakata,aikuwa dakatawar yayi tare da kamewa guri É—aya.

Kwarinta ta dauko da baka,ta sanya kibiyar cikin bakar,sanan ta É—ameshi sosai ta saita daya daga cikin zomayen nan ta sakar masa kibiyar.aikuwa cikin sa'a kibiyar ta caku acikin wannan zomon, nan da nan zomon ya fadi yana burbuwa, yayin da guda É—ayan ya zura da mugun gudu,yayi cikin wani rami.

Da gudu birin nan ya karasa gurin da zomon ke kwance yana burbuwa,daukowa yayi tare da dawowa gurin yarinyar.ita kuma yana zuwa ta karɓe zomon tare da yin Bismillah ta yanka wuyansa.
Zomon katone sosai,dan haka suna kamashi tace da jambu cikin muryarta mai daÉ—in sauti"jambu mu koma gida kawai,wannan ma ya ishemu "tana faÉ—in haka ta juya cikin takunta mai cike da burgewa,kamar tarwaÉ—a haka jikinta ke rausayawa.

Suna cikin tafiya ba zato ba tsammani wani ƙaton biri mai girma ya dira agabansu,birin baki ƙirin dashi,hakoransa jajaje, mai matukar muni.
Da sauri jambu ya dare kan kafadarta yana ihu,da neman inda zai boye ajikinta.

Ita kuwa cike da rashin tsoro ta ja ta tsaya,tare da kafe birin nan da ido,tana gyara tsayuwa.
Wani ƙara birin yayi tare da girgiza,kafin ya nufota da gudu.

Ja tayi da baya tare da zaro wukar data soke ajikinta itama ta nufi birin nan da gudu.
Abin mamaki suna haduwa tayi tsalle tare da darewa bayan birin ta soka ma wukar nan akafaÉ—arsa.
Wani ƙara birin ya sanya tare da yin wani juyi ya wurgar da ita can gefe.
Faduwa tayi tare da buga kanta jikin wata bishiya,ƙara ta sanya tare da dafe goshinta wanda ya fashe, da gudu birin nan yayi kanta baki buɗe yana ihu shima.
Saidai yana kusantowa gareta,wata irin bakar guguwa ta tashi,nan da nan gurin yayi duhu matuka,baka iya ganin komai sai karan birin nan dake tashi cikin guguwar nan,janbu ne ya garzayo gareta tare da tabata,yana É—an kara,ganin har lokacin tana kwance dafe da kanta.

Tashi tayi da sauri tana mai rungume janbu ajikinta,tare da zuba wa wannan guguwar ido,wacce ke kadawa aguri É—aya tana ta juyi,yayinda karan birin nan ke kara tsananta cikin guguwar.

Kusan minti biyu kafin guguwar ta lafa, sai kuma gurin yayi haske,can gefe suka hangi birin nan,cikin wani irin mugun yanayi,kwance yake gaba É—aya jikinsa jini ke zuba.

Tashi tayi tare da maida wukarta, tana bin wani farin haske da ido, sannan tayiwa janbu alamun su bar gurin.
Cikin hanzari suka bargurin tare da komawa inda bukkarta take.
Cikin salonta na kuzari ta haye saman bishiyar nan,tare da zama tana mai dafe kanta,dan kuwa ta bugu sosai.
Janbu ne yazo jikinta yana kallonta tare da dan karansa.
Kallonsa tayi kafin ta É—anyi murmushi tace "karka damu janbu,ba wani zafi fa,zai warke,ka kwantar da hankalinka"ta fada tana shafa bayansa.
Shikuma yana kara maƙalewa ajikinta.

Kamar wacce akace ta duba gefenta, kawai tana juyawa taga wannan zomon da suka kamo dazu, ajiye kusa da ita.
Sam batayi mamaki ba dan dama irin hakan tana faruwa,duk lokacin da wani abu yayi nufin cutar da ita,to wannan guguwa zatazo ta taimaketa, kuma bata taba barin Abunta awani gurin ba,kuma ta dawo makwancinta bataga abin nan ba.dan haka ta riga ta saba da irin hakan tun tasowarta cikin dajin nan.
Murmushi ta sake yi akaro na biyu kafin tace "janbu kamar dai kullum yauma kaga zomon da muka bari agurin can, ankawo mana shi"ta fada tana janyo zomon gareta.
Cikin kankanin lokaci ta fara gyara zomon nan da wukar da taje farauta, Ni dai bansan inda ta samo wuta ba,kawai naga wuta tana ci daga gefenta.murmushi naga tayi kafin taci gaba da aikinta, cike da rashin tsoro ko fargaba.haka ta gama hada naman nan taci wanda zata ci,ita da janbunta, sannan ta kwanta.kwanciyarta kenan barci yayi gaba da ita,yayinda janbu ma kwanta kusa da ita.
Iskace mai sanyi ta fara kadawa cikin dakin na tsawon minti biyu,kafin wani haske ya bayyana gefen da yarinyar ke kwance.ahankali hasken ya rikiÉ—e ya koma wani kyakykyawan saurayi,fari mai matukar kyan idanu,kallon yarinyar fuskarsa É—auke da murmushi,kafin ya buÉ—e rafin hannunsa,saiga wani dan karamin abu mai haske ya bayyana cikin hannun nasa,budewa yayi tare da lakuto wani jan abu adam yatsanshi,agishin yarinyar ya fara shafawa ahankali yana kallonta.

Gama shafawarsa keda wuya,gurin ya koma yadda yake ba ciwon,kamar ma bata taɓa jin wani ciwoba.

Haka wannan saurayin ya mike bayan ya gama shafa mata maganin,sannan ya zama farin haske yayi waje.
Wannan kenan.

Abuja birnin tarayya.
Da misalin ƙarfe uku na rana,cikin anguwar maitama, wani rantsatstsen gida na hango,mai matukar kyau da ɗaukar hankali, kaida ganin gidan kasan cewa,ko cikin masu kudin ma,to ba kowaba.dan tsayawa fadar kyan da gidan kedashi ma bata lokacine.

Kai tsaye na kutsa kaina cikin gidan domin dauko maku rahoto.

Wata hamshaƙiyar Hajiya na hango,zaune kan daya daga cikin rantsatstsun kujerun da sukayiwa falon ƙawanya,tana zaune da waya akunnenta,cikin wata hadaɗɗiyar kwalliya mai cike da kyau da tsari,irin ta manyan mata masu ji da gayu dakuma Naira.

Fara ce, amma ba irin can ɗin nan ba, kyakykyawar mace mai cikar haiba da zati,waya take, cike da nishadi,tana faɗin"yanzu Aslam ka kammala karatun ka,tun last week,Amma kaki dawowa gida,me yasa kake son zama cikin masu jan kunnen nan ne?ga kakarka nan kullum zancen ta daƴa Aslam. Gaskiya ya kamata ka dawo gida, muma muna bukatar ka kusa damu"ta kai ƙarshen zancen ta cike da nuna zallar son ganin wanda take wayar dashi.

Daga can daya bangaren,naji wata murya mai cike da izza,wanda kana jin muryar nan kasan ma'abocinta zaiyi son girma da rashin don raini.
"Ki kwantar da hankalinki,mommy zan dawo very soon,akwai Abinda Ya tsayar dani anan din amma dana kammala I will be back home soon kinji mommyna"ya ƙarasa cikin sigar rarrashi.

Ajiyar zuciya matar tayi kafin tace "shikenan Aslam,Allah ya dawo da kai gida lafiya,kannanka ma suna kewarka sosai"ta fada tana canza tasha da remot din dake hannunta.

Murmushi yayi kafin yace "ki sanar dasu,nakusa dawowa,saidai ina nan kamar yadda suka Sanni,dan haka saisu kula su nutsu,dan ba sassauci ga wanda yayi ba daidai ba"ya faÉ—a cike da salonsa na son girma.

"Ai sun sani,Bama saina ƙara faɗa musuba, yaran da idan kana guri ko ƙwaƙwƙwaran motsi basa iyayi,basu ba ma, hatta Aman baya wargi idan kana guri"ta faɗa cike da son tunasar dashi,ƙannan nashi fa basu manta halinsa ba.
Murmushi yayi yana kada kafa, haka yake so,ace duk iskancin mutum to yaji tsoron Aslam,Dan Aslam yana son raini ko kaÉ—an.sun jima suna hira ta waya da mahaifiyarsa,cike da nuna kulawa da kauna, har saida taji tsayuwar motar mijinta kafin sukayi sallama ta kashe wayar.

"Alhaji yanzu goben zaka tafi can Niger É—in, Kenan?"mommy ta fada,bayan mijin nata ya fito daga wanka,tana zaune abakin gado.

"Ina sha Allahu Madam,gobe zan tafi,akwai bukatar zuwana Niger gobe,saboda in duba abubuwa yadda suke tafiya acan,kinga shi Aman makaranta yake zuwa,dama da ace Aslam ya dawo ne to shi zan tura,amma tunda baya nan dole in je da kaina"ya faÉ—a yana goge kansa da towel.

"Shikenan, Allah ya kaimu,Amma dai ya kamata Ku tafi tare da Aman tunda kace amota zaka tafi,dan nikam ina tsoron wannan dajin dake tsaninmu da nijer,dan ance akwai abubuwan cutarwa cikin dajin"ta fada cike da nuna fargaba.

Murmushi Alhaji yayi,kafin yace "banda abinki ai komai nufin Allah ne,duk abinda ya faru da mutum dama can Allah ya nufa,dan haka karki damu,zamu tafi tare da Aman É—in,tunda gobe week end ne"ya faÉ—a lokacin da yake sanya kayansa.

Murmushi Mommy tayi kafin tace "Allah ya tsare hanya Alhaji"
"Ameen yace kafin ta zuba masa abinci yafara ci.


Misalin ƙarfe biyar yaran sukan dawo gida.cike da tabara suka shigo falon,
Cikin sakalci jannat ke kiran "Mommy mun dawo,wllh na gaji "ta fada tana jefar da jakarta aƙasan falon.

Hanan ma cike da sakalci ta jefar da jakarta tana zama ragwab akan kujera"wash Mommy ruwa zansha"ta fada tana turo baki tare da jingina kanta jikin kujera.
Mommy kuwa saukowarta kenan daga É—akin ta,tajiyo hayaniyar yan shagwabar ta ta,girgiza kai tayi tana zama akan kujera kafin tace"nikam zanga randa zaku girma wllh,sakalcinku yayi yawa,yanzu duba kigani jannat anan kika jefar da school bag din ki,kuma bazaki daukeba, sai dai adauke miki.
Ke kuma wai ruwa zaki sha,gaki ga fridge Amma jira kike adebo miki Kisha,Gaskiya lamarinku sai du'ai wllh"Mommy ta fada cike da jin takaicin sakalcin yaran nata.

Turo baki jannat wacce ataƙaice zata kau shekara kusan ashirin aduniya tayi,kafin yace "haba Mommy ɗaga dawowarmy,zaki fara mana faɗa,shiyasa wllh nake son Daddy ba ruwansa da faɗa"ta fada tana barin gurin ba tare da ta dauki jakarba.

Hanan ma tashi tayi tana kwalawa mai aikinsu kira"ramatu, maza ki kawomin ruwa dakina, bana son mai zafi "ta fada tana wajewa sama ita.

Girgiza kai Mommy tayi kafin tace "Allah ya shirya minku"
Aman ne ya shigo dakin da sallamarsa,yana kada keys É—in mota,zama yayi kusa da Mommy yana faÉ—in"ji Mom ya gida"
Murmushi tayi tare da shafa kan Aman tace "Aman ka dawo ?sannu"ta fada cikin murmushi.

"Na dawo mom inna granny ?ko bata dawo ba"ya faÉ—a yana duba wayarsa.

"Kasan ai bazata dawo ba,har sai kaje ka daukota,wai batason tuƙin driver bashi da sauri"ta fada tana dariya.

Dariya shima Anan yayi kafin yace "granny case,Bari naje na daukota,Dan gidan baya dadi idan bata nan wllh"ya faÉ—a yana mikewa cike da nishadi yayi waje ...

Wannan kenan.

Masu karatu muje zuwa ,sannu kan hankali,zaku nishadantu,kuma ku wa'azantu cikin wanna littafi. Bamu fara komai ba.

Mene babi💘💘

Share as much as you can.fisabilillah.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free page
7/8



GA MASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN,ZAKU BIYA KAMAR HAKA.

NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR SATI.

SPECIAL GROUP 500 ₦
UPDATE BAKWAI ASATI.

TA WANNAN ACC. ÆŠIN
SARATU KABIR
U.B.A
2215749011

EVIDENCE OF PAYMENT
08148360851.




_______________Wani irin baƙin hayaƙine mai tsananin duhu ya turnuƙe dajin,baka iya ganin koda tafin hannun ka.
Ba abinda ke tashi cikin dajin,sai wani irin ƙara mai fidda amon sauti mai firgitarwa.

Sai kuma ihun da matasan suka fara kwalawa ya biyo baya,tare da wani irin sauti mai kama da ƙaran bulala.
Ji kake fau-fau-fau.ihu suke,cikin azaba suna neman taimako,amma ko ganin su bakayi bare kasan ta ina zaka kaimusu É—auki,tun suna ihun da iya karfinsu suna neman taimakon,har karfinsu ya kare suka daina ihun.
Kusan minti biyu da daina jiyo ƙaran ihun nasu,gurin ya fara haske,wannan baƙin hayaƙin ya fara yayewa yanayin sama.
Taruwa yayi guri É—aya asararin samaniya yana juyawa,kafin yayi cikin dajin da gudu.

Matasan nan ne kwance cikin mawuyacin hali,gaba É—aya jikinsu yayi burÉ—i -burÉ—i da sawun bulala,sunyi kwance sharkaf sai nishi suke.
Sai kuma wani abun mamaki,sam ba yarinyar agurin,cikin tashin hankali suka ƙara bude idanunsu suna neman inda zasu ga yarinyar,amma bata ba alamarta.hakan ya tabbatar musu cewar aljana ce, dan haka da mugun gudu suka tashi da gyar sukayi hanyar kauyensu aguje suna ihu da kiran "aljana!aljana!!.
Nan suka bar duk wani kayan barautar da suka shigo jejin dashi.

Ita kuwa wannan yarinyar koda iskar nan ta turnuke gurun, can gefe ta mayar da yarinyar,sannan ta fara cin uban matasan nan,saida ta gama zana su kafin tayi gurin yarinyar dake kwance kamar me barci ta É—auke ta sukayi sama.bata ajiye ta ko ina ba sai cikin bukkarta.
Ahankali kuma iskar ta rikide ta koma wannan matashin daya shafa mata magani agurin da taji ciwon nan.
Kallonta yake fuskarsa amugun hade,yayin da take wani sauyawa kala -kala,baƙi,jaa,kore.
Idanunsa yayi jajur kamar wuta.
Kusan minti uku yana tsaye akanta,kafin ya murza hannunsa,saiga wani farin hayaƙi ya fito daga hannun ya nufi jikin yarinyar ya shige ta kafar hancinta.dan motsi tayi kadan kafin taci gaba da barcinta.


Washe gari kamar yadda Daddy ya tsara cewar zasu tafi Niger shida Aman, hakan ce ta kasance,bayan sun kammala shirinsu suka fito falo,inda gaba É—aya ahalin gidan ke zaune.
Sallama Daddy yayi dasu kafin suka rakosu har farfajiyar gidan,inda granny ke fadin"to gadai Aman nan,ka kula dashi,kasan yarone,gashi daga shi sai kai zakuyi tafiya,sannan akwai shi da tuƙi irin na yan tasha,wllh kayi masa gargaɗi sosai ya kula,Allah ya tsare hanya ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya"granny ta fada cikin yanayi na sanyin jiki.
Dariya Hanan tayi kafin tace "kai granny,wato tukin motar ma harda na yan tasha"ta fada cikin dariya.
"To yar nan duk wanda yake irin tuƙin da wannan ja'irin yaron keyi,ai wllh bashi da maraba da na yan tasha,jiya saura kadan na mayar da ya'yan hanjina"ta fada cikin darura.

Dariya sukayi gaba dayansu harda jannat da basa shiri da granny,Dan yanayin da granny rayi maganar abun dariya .
Murmushi Daddy yayi kafin yace "In Sha Allahu zamu kula uwata,bazan bari yayi mana tuƙin ganganci ba"ya kai zancen sa yana kallon granny,fuskarsa ɗauke da murmushi.

"Allah yasa dan nan,dan wllh Amanu ja'irin yarone mai wasa da rai,shikuwa rannan riritashi ake,idan ya tafi shikenan"granny ta fada tana watsa hannu da taɓe baki"
Dariya kawai suke cike da nishaÉ—in abin dariyar granny.

Mommy kuwa cewa tayi"yanzu Alhaji sai nan da kwana ukun kenan?

"Eh In Sha Allah,saboda aikin da yawa,zamu zagaya sosai,sannan akwai muhimman abubuwan da zanyi acan, amma bazamu wuce kwana uku ba in Sha Allah"ya faÉ—a yana kallon matar tashi cike da soyayya.
Sallama sukayi dai anan suka shige mota,mutanen gidan natajin kewarsu.
Har sun shiga motar Aman ya fito yazo kusa da granny yana mata rada"granny kinsan wannan irin tuƙin danayi dake jiya? To yau shizanyi da ɗan ki koma fiye dashi,tunda har wani cewa kika wai yayi min gargadi,wato dashi kadai kika damu ko hmmmmm"Aman ya faɗa yana gwafa,sannan yayi saurin shigewa motar ya tada jin granny na faɗin"wllh Amanu ta Allah ba takaba,dan bakin ciki,kuma kasani idan wani abu ya sami dana,wllh hukuma ce zata rabani dakai,hatsabibin yaro kawai"ta fada cikin salon ta na masifa.

Aman kuwa kwalo yayi mata kafin ya fice daga gidan. Gaba daya jikin granny yayi sanyi Allah sarki harta fara jin kewar Aman É—in, dan mutum ne shi mai barkwanci sosai.
Kallonsu tayi kafin tace "to ai sai a koma cikin gida ko,dan kuwa wllh ba mai fita daga gidan nan,da sunan yawo,har uwar taku"ta fada tana hararsu jannat,tsaki jannat tayi cike da rashin kunya kafin ta shige cikin gida abinda.

"Kinyiwa uwarki tsaki,kinganta nan,to ita kikayiwa tsaki,marar kunya mai kafar alwala"granny ta fada tana bin bayan jannat kamar zata kamota.
Girgiza kai kawai Mommy tayi kafin suna suka shige cikin gidan.
Tunda suka dauki hanya tafiya kawai suke, cikin tuki na tsinaki Aman ke jan motar,suna dan taba Shira da Daddy,sunyi nisa sosai kawai Aman ya fahimci kamar ana binsu abaya,nutsuwa yayi yana son fahimtar shin da gaske bin nasu ake ko yaya?dan haka saiya dan rage gudun da yake,aikuwa motar dake bayansu ma saita rage gudun,gabansa ne ya fadi lokacin daya karawa motar su gudu,yaga wannan motar ma ta Gara gudu,nan fa aka fara tsere akan titin,Daddy ne yaga irin gudun da Aman keyi,dan haka yace "Aman, wanann gudun kamar zamu bar duniya haka ?"
Cikin tsoro Aman yace "Daddy binmu ake abaya,tunda muka taho"ya faɗa yana ƙara take motar,ganin waccan motar har ta kusa cinmusu
Gaban Daddy ne ya fadi cikin firgici yace "subhanallah meke faruwa haka?su waye ke binmu da wannan gudun haka?me suke nema agaremu?ya fada cikin firgici yana kallon bayansa.

Ba zato ba tsammani suka farajin harbi yana sauka akan motar,Allah ma yasa motar harsashi baya hudata, nan suka ƙara gigicewa,lokacin sun kawo daidai dajin da yarinyar nan ke ciki.tsabar tsoro sitiyarin motar ya kwacewa Aman,suka nausa cikin dajin. Salati Daddy yake cike da tashin hankalin ganin yadda motar ke katantanwa cikin dajin,saida suka yi nisa kafin motar taje ta daki wata bishiya kafin ta tsaya. Gaba daya su Daddy sun shiga yanayi mai matukar wahala,dan kuwa tuni jini ya wanke musu jiki,dan Aman kam ya suma,can gefe guda motar ta cillashi cikin sarkakiya.
Da gyar Daddy ya iya zaro kansa cikin motar nan,yafito ya na kiran "Aman!Aman!!Amma baiga inda

Please Login or Register in order to submit comment