Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusan shiga ɗakin sannan taji ajikinta ana kallonta,juyowa tayi karaf idonsu ya haɗe dana juna.
Da hanzari Aslam ya kawar da kansa yana jin faduwar gaba.
Islam kuwa murmushi tayi tare da juyowa ta nufi inda yake.tsaye tayi akansa tana taɓe baki da kare masa kallo.
Shikuwa duk da yadda gabansa ke faduwa, hakan bai hana shi ɗaure fuska ba kamar hadari,yi yayi kamar bai ganta ba ,yaci gaba da ƙoƙarin shan tea ɗinsa.

Dariya sosai Islam ta sanya tana nuna shi,runtse ido yayi cikin jin zafi aransa, ya tsani dariya haka kawai ma bare kuma ace shi ake yiwa.
"Kai Allah sarki sannnu amma kasha jiki,ai wllh so nayi birin nan ya ƙwaƙwale maka idanu,sannan ya gwagwuye wannan leben naka masu cin haram--ta ɗan dakata tana murmushin wulaƙanci,kafin taci gaba--nasan kana ta tunanin waye wannan wanda yayi maka irin wannan tijara?to albishirin,ka,ba kowa bace face Ni Islam rainon dawa,kuma wllh ban gama da kai ba, ina nan zan ci gaba da ƙuntata maka ,sai kayi dana sanin abinda kayi min"ta kai karshen maganar ta tana hararar sa.
Afusace Aslam ya mike tsaye yana kallon Islam,tsabar bakin ciki da takaici,kawai ya dauki kofin tea ɗin nan ya watsa mata ajikinta.
Wani irin zabura Islam tayi arazane sakamakon zafin daya ratsa jikinta,dan kuwa tea ɗin akwai zafi sosai,wanda saida yayi sanadiyyar zamewar towel ɗin dake jikinta,nan da nan,albarkatun ƙirjinta suka bayyana muraran,suna kallon Aslam,
Dammmm! Dammmmm!! Dammmmm!!!ƙirjin Aslam Yayi wata muguwar bugawa,nan da nan jikinsa ya dauki rawa,yawun bakin da ya ƙame,sakamakon arba da manyan breast ɗin Islam da yayi,suna kallonsa,
Azabure yayi kanta cikin gushewar tunani,da rashin madafa.....


Wai shin wa ce ce Islam?

Waye Kuma Aslma?

Shin su waye iyayen Islam?

Sannan me alaƙar Islam da malaminta?

Hmmmmmmm.
Masu karatu, laifin daɗi karewa,anan muka kawo ƙarshen,free page na wannan littafin,
Dan haka ga mai buƙatar ci gaba da karantawa,sai yayi hanzarin biyan kudinsa kafin mu ɗora daga inda muka tsaya.

Karku manta ,yanzu labarin zai fara.

Akwai cakwakiya sosai cikinsa.



Mrs babi ce💘💘
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers🎄🎄



Free page

17/18




GA MASU BUƘATAR BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN ZAKU BIYA KAMAR HAKA.

NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR A SATI.

SPECIAL GROUP 500₦
UPDATE BAKWAI ASATI.


SAI KUMA MANYAN MATA MASU BUƘATAR ATURA MUSU PRIVATE,ZA KU BIYA 1000₦


DUK ZAKU BIYANE TA WANNAN ACCOUNT ƊIN.

SARATU KABIR
U.B.A.
22 15749011


SAI KUN ZO.




______________Tsaye ta yi a gaban Aslam,tare da kafe shi da idanuwan ta,masu matuƙar ɗaukar hankali,ko kaɗan ba alamun tsoro ko shayinsa atare da ita.wani shegen kallo take watsa masa,tana ɗan jijjiga jikinta,kusan minti ɗaya tana kallonsa kafin ta buɗe baki ta fara magana.
"Ni nan Islam,rainon dawa ce,bani da kowa sai malami na,sannan Ni ba kowa bace cikin gidan nan,sai dai fa,ba wanda yake da ikon hana ni yin abinda raina ke so,ko kuma ya hanani gyara abinda na ga ba dai-dai bane, zan gyara wa kowa kuskuren sa,koda kuwa gemunsa na jan ƙasa--tayi shiru tana sauƙi ajiyar zuciya kafin taci gaba ---wannan shine alaƙa ta da gidan nan,fatan ka gamsu Mrs arrogant"?
Ta fada tana dage gira guda ɗaya.

Shiru kawai Aslam Yayi, mamaki al'ajabi da kuma kallon iyakar ƙarfin hali,sun hanashi koda yin ƙwkwƙwaran motsi,she can't believe,ace wanann ƙaramar yar tsakuwar ke tsaye gabansa tana fada masa waɗan nan kalaman,a gaban mommy,kuma mommy tayi shiru.
Kallon Islam yake cike da mamaki,kamar yadda itama ta kafeshi da ido.
Jinjina kai yayi kafin yace cikin zazzafar murya"lallai ke ƙaramar karuwa ce yarinya,amma ki sani Ni Aslam bana ɗaukar raini,zan gyara miki zama,da sannu zaki sauke wannan rawar kan naki,kuma ki gane ,nan ba gidan ubanki bane,baki da ikon gyara kowa cikinsa,sai dai ke agyara miki zama,wllh badan ina tsoron abinda zai biyo baya ba,da saina tattaka ki agurin nan,sai dai nasan duka ɗaya idan na miki mutuwa zaki,amma da sannu zaki san waye Aslam"yana gama faɗin haka yayi hanyar ɗakinsa,ba tare da yaci abincin ba.
Kiran sunan sa mommy tayi"Aslam! Aslam!!ka dawo kaci abincin mana"mommy ta faɗa cikin daga murya,dan har yayi nisa tsabar yadda yake sauri jikinsa na rawa.
Cikin muryar fushi yace "No thank mom,tunda kin samu wannan abar,inaga idan ita taci baki buƙatar mu muci"ya faɗa cikin zafin rai yana juyawa yaci gaba da tafiya.
"Kar yaci mana mommy,ki barshi,ai cikinsa ne,banza mai baƙin hali irin na kafuran da"cewar Islam kenan tana komawa inda ta tashi,tare da zama.haushin Aslam takeji sosai,ya cika girman kai da faɗin rai,kamar wani uban mutane.
Karaf maganar Islam akan kunnen Aslam,runtse ido yayi cikin mugun jin zafi azuciyar sa,da hanzari ya kara sauri dan barin gurin,dan wllh idan yaci gaba da sauraron muryarta,tabbas zai shaƙe wuyanta,kuma bazai barta ba sai yaga bata numfashi.
Yana shiga ɗakin sa,ya fara watsi da duk abinda yaci karo dashi,zuciyarsa kamar zata kama da wuta,ba abinda yake bukatar ahalin yanzu kamar ya kasance da wacce zata kore masa damuwa,gashi agida yake ya zaiyi kenan,haka yayi ta haukarsa yana fashe fashe,yayi alƙawarin saiya koyawa yarinyar nan hankali,ta yadda ko hanya baza ƙara bari ta haɗa su ba,gaba ɗaya ya yanke hannun sa,amma ko ajikinsa,ganin idan yaci gaba da zama zai je ya mutu da baƙin ciki ne adaki,hakan yasa yayi saurin zarar,mukullin mota yayi waje.
Lokacin daya fito afusace,Islam na cin naman rago da akayi farfesun shi,hankalinta kwance.
Granny na faɗin"ai Ni wllh jarumtar ki tana burgeni ƴar nan,kin iya koyawa mutum hankali,wllh halin mu ɗaya dake,Ni nan da kika gani,lokacin inada shekaru kamar naki,tsabar masifar faɗa yar dambe ake cemin,dan Ni in zage mu dambatu da mutum ba ƙaramin aikina bane,sam bana ɗaukar raini.amma dai kiyi ahankali ɗan kuwa Aslam yana da baƙar zuciya,duk sanda ya kamaki ahannun sa,wllh zaki daku"granny ta fada tana kai ƙatuwar tsoka bakin ta.
"Tab ai wllh sai-dai mu doki juna,dan bai isa ya dakeni in gyale shi ba wllh,shida ba ubana ba,kuma bashi ya kawo Ni gidan ba"ta fada cike da rashin tsoro tana murguda baki.
"Ai kuwa dai sai dai kiyi iyakar ƙoƙarin ki,dan Aslam mugune"cewar granny tana taɓe baki,tare da hararar mommy.

Mommy dai tana zaune bata ce komai ba,tayi shiru tana tunanin ta yadda zata bullowa,al'amarin,dan bazata zuba ido Islam tana yiwa manya rashin kunya haka ba,koba komai,akwai buƙatar anuna mata matsayin wanda ya girmeta,tunda Ita dai bata fahimci ba'ayiwa babba rashin kunya ba,amma dole ta jata jikinta,ta nuna mata abinda ya dace.

Hanan kuwa tsabar tsoro da fargaba sun hanata cin komai,ji take kamar tayi fitsari a wando,dan tasan Islam ta janyo musu cin uba.

Kai tsaye Aslam ya nufi ƙofar fita daga gidan,banda rawa ba abinda jikinsa keyi,duk irin kiran da Mommy keyi masa,baiko juyo ba,bare ta sa ran zai kulata.
Dafe kai kawai mommy tayi tana fatan Allah ya tsare mata shi.

"Barshi,ya tafi ɗan tijara Ni dai bazan bari a cutar da ƴar nan ba wllh" cewar granny tana bin bayan Aslam da harara.

Suna kammala cin abincin,granny ta kama hannun Islam tace "kinga taso mutafi can dakina,anan zaki zauna,dan In koya miki dabaru na zaman duniya ,da yadda mutum zai ƙwaci kansa ako ina ne"ta fada tana kama hannun Islam suka nufi ɗakinta dake ƙasa ,kusa dana Aslam.dan dakunan mazan a ƙasa yake.
Da sauri mommy tace "Amma granny da an barta tare da Hanan,zata fi sakewa"
"An ƙi abar tan,ke bana son shishshigi fa,ina ce ɗana ne ya kawo ta gidan?to ki barta ba ruwanki aguri na zata zauna"tana gama faɗin haka suka wuce ɗakin nata.

Girgiza kai kawai mommy tayi, tana jin ba daɗi cikin ranta.
Hanan ma tashi tayi tace "mommy Bari naje ɗaki, zanyi assignment ,ta fada ranta fess, Dan dama tsoron kwana take tare da Islam ɗin"jinjina kai mommy tayi ba tare da tace komai ba,hanan ta wuce ɗakinta.
Ita kuwa zama tayi agurin tana jiran dawowar Aslam.

Shikuwa Aslam yana fita daga gidan,yayi tafiya mai nisa cikin fushi,kafin ya sami gefen titi yayi fakking yana zaune shiru,kusan minti uku,kafin yayi saurin zaro wayarsa,wata number ya kira tare da karawa akunnen sa.

"Ki na ina?ya faɗa cikin angry voice ɗinsa.
Ita kuwa wacce ya kira ɗin,cikin rawar jiki take amsa masa"ina gida Aslam,saukar yaushe?"ta faɗa cike da ɗoki.
"Ki sameni nan kusa da anguwar ku, bakin plaza yanzu "yana gama faɗin haka ya kashe wayar tare da runtse idonsa,tunani fal cikin ransa,na irin uƙubar da zai yiwa waccan yar tashar.
Cikin zumuɗi yarinyar ta mike dama tana sanye cikin wata doguwar riga wacce bata wuce ƙwaurinta ba, gashi ta kamata damm, ajikinta,dan haka turare ta fesa ajikinta,sannan ta kara gyara fuskarta,ta janyo wani dan siririn mayafi ta fice daga gidan,bata ko sanar da mahaifiyar ta ba.

Kai tsaye inda yace mata nan ta nufa da motar ta,yana hango ta ya kunna hasken motar,dan ta gane shine. Aikuwa da zumuɗi ta ƙaraso gareshi,fitowa tayi daga cikin motar ta,ta nufi tashi,cikin kwarkwasa,da tafiyar jan hankali.
Shikuwa ya kafeta da ido kamar tsohon maye,tana shigowa cikin motar ƙamshin ta ya kara tunzurashi,ga ɓacin rai.
Ba bata lokaci ya janyota jikinsa ya fara aika mata saƙonsa mai wuyar gogewa.
Ita kuwa daɗi kamar ya kasheta,tana matukar kaunar Aslam,Amma shi sam baya ta Tata,lallai yau dama ce agareta.dan haka ta zage itama tana sauke masa hadda.
Kusan awa guda suna romancing juna cikin motar,gaba ɗaya sun fice daga hayyacin su,burinta kawai Aslam Yayi sex da ita,sai dai duk yadda taso da hakan ya faru,sam Aslam yaki bata haɗin kai,daga ƙarshe ma ture ta yayi daga jikin sa tare da jingina kansa jikin kujera, yana sauƙe ajiyar zuciya da sauri da sauri.

Cikin mutuwar jiki da buƙatuwa ta matso jikinsa tana shafa ƙirjinsa tare da ƙoƙarin zare belt ɗin wando jikinsa.
Hannunta ya rike tare da cirewa daga jikinsa .sake maida hannun tayi tana mai faɗin"haba Aslam ya haka?kasan dai idan muka bar juna ahaka zamu cutu,Please ka bari miji daɗin mu mana"ta faɗa tana ƙara maida hankali wajen son cire belt din,sannan tana ƙoƙarin haɗe bakinsu guri ɗaya,
"Stop !!!" Ya faɗa cikin daka mata tsawa, yana huci cikin zafin rai,dan shi maimakon yaji zuciyarsa tayi sanyi, sai wani ɓacin ran ne ma ya kara mamaye zuciyarsa.
Da sauri ta zare hannun ta tana kallonsa cike da sha'awa.tana maida numfashi,gaskiya guy ɗin nan ya kwafsa mata,saida ya tada mata hankali,sannan zai wani gyaleta,gashi sam yaƙi bari ko ɗan tsotsar lips ɗin sa tayi, amma ba komai in Sha Allah saita Sami Abunda take so agareshi.

"Fice min daga mota"ya faɗa cikin haɗe fuska ba tare da ya bude ido ba.
Kallonsa tayi cike da ƙauna,kafin tace "Please Aslam,idan kana so ma Ni sai in bika can gidan mu kwana "ta fada cikin marairaicewar murya,
Wani shegen kallo da ya watsa mata ne yasata sunkuyar da kai ba shiri.
"Saboda ke daƙiƙiya ce ko?saina ɗauki karuwa na kai gidan mu,gaban iyayena ko?"ya faɗa yana mai kafeta da jajayen idanunsa,wanda jaraba da masifa ta sa suka rinar masa da su.
Cikin rausayar da kai tace "Ayya Aslam ba haka nake nufi ba, dan Allah kayi hakuri,naga kamar ranka aɓace yake,shiyasa nake ƙoƙarin sanyaka farin ciki, amma kayi hakuri"ta fada cikin sanyin murya tana mai sunkuyar da kai.

Tsaki yayi tare da cewa"ki tafi gida,zan nemeki, kuma wllh idan har naji labarin kina kula wani dan iskan,wllh saina ci uwarki kinsan halina"ya faɗa yana dage gira ɗaya.
Jinjina kai kawai tayi,tana gyara rigarta, sannan ta fice daga cikin motar.

Ya jima agurin bayan tafiyar ta,har lokacin ransa aɓace yake,zuciyarsa sai tafasa take,kallon wayarsa yayi yaga har ƙarfe sha ɗayan dare, ga miss calls ɗin mommy birjik,yasan zuwa yanzu mommy har ta gaji da zaman jiransa,ahankali ya kunna motar tare da juyawa gida.koda yaje gidan,mommy ɓata falon,ta gaji da zaman jiransa ta shiga ɗaki.
Kai tsaye shima ya nufi ɗakinsa, dai-dai lokacin kuma ,Islam ta fito daga ɗakin kaka,wai zata je neman janbu ko yana lambun gidan.
Tana fitowa shi kuma Aslam yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa.
Tsaki tayi lokacin data ganshi yana ƙoƙarin shiga ɗakin.
"Dole ma asanya doka cikin gidan nan,dan bazamu laminci yawon dare ba, sai mutum yaje ya gama yawon karuwancinsa,sai lokacin da yaga dama sannan ya dawo gida,wllh bazan laminci ganin wannan ɓarnar ba ehe"Islam ta fada cikin daga murya tana buga cinya.
Tsaye Aslam Yayi gyam!! abakin ƙofar dakin nashi, shi bai shiga ba kuma bai juyo ba,maganganun Islam ke masa yawo cikin kansa,lallai ya kamata ya nuna wa yarinyar nan asalin karuwan cin nashi,ko zata gane shi ba sa'anta bane.
Afusace ya juyo tare da tunkarota kamar wani zaki.
Ita kuwa tana tsaye ko motsi batayi ba, jira ma take ya ƙara so taga abinda zai iya mata.
Shikuwa yana ƙarasowa ya saɓeta akafaɗarsa,tare da juyawa ya nufi ƙofar fita daga falon.
Dukansa ta fara cike da masifa tana faɗin"kai malam meye hakan?wannan wane irin iskanci ne?zaka wani saɓeni akafada kamar yarka,?dalla ka saukeni,bana son iskanci banza bujimin sa kawai"ta fada tana dukansa da iya ƙarfinta.amma ko nuna alamun yana jinta ma baiyi ba.kai tsaye ya nufi boysquaters da ita.
Bai direta ko ina ba sai cikin wani ɗaki,mai dauke da babban falo da ɗakunan kwana guda biyu.yana sauke ta ya kulle ƙofar da makulli,kallonsa take cikin rashin sanin me yake nufi da hakan,tace "kai wllh tun kafin raina ya gama ɓaci, ka buɗe min ƙofar nan, bana son iskanci "ta faɗa cikin masifa tana wani kashe ido.

Murmushin mugunta yayi kafin ya fara takowa cikin ɗakin,yana tunkarota."me kike ci na baka na zuba,ai zan nuna miki irin nawa salon karuwancin ne,dan ki tabbatar da Ni nafi ƙarfin iya shegenki,dan uwarki "ya fada dai-dai lokacin daya ƙaraso kusa da ita.
Ɗan ja baya tayi,dan kusancinsu yayi yawa,har saida taji gabanta na faduwa.
"Dalla malam bani guri kaje can ka nemi yar iska irin ka amma Ni nafi ƙarfin ka "ta fada cikin rashin kunya tana ja baya.
Runtse ido yayi cikin ɓacin rai,aduniya yana matukar jin ciwon yadda wannan yar yarinyar ke zagin sa,da fada masa baƙaƙen maganganu.

Buɗe idonsa yayi da suka ƙara kaɗawa sukayi jaa, yayi kanta kamar zaki yana faɗin"wllh yau saina ci uwar ubanki,zan nuna miki Ni Aslam naci uwarki a iskanci.ya faɗa yana mai fizgota zuwa jikinsa.
Baiyi wata wata ba ya fara ƙoƙarin .......

Masu karatu muje zuwa ,da alama Islam fa ta tsokano maza.koya zata kaya ?

Ku biyoni sannu kan hankali.

Maza kuyi payment ga duk mai bukatar ci gaba da karanta wannan littafin.

Sannna ga masu buƙatar wannan littafin,iya maza kawai.
Su tuntuɓi wannan number
08067072477.
Iya maza kawai.

Anty mammy
Mrs babi 💘💘

Share as much as you can.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: ______________tsaye Daddy yake yana kallon su,kuma yaji duk abinda Islam ke faɗi, shi dama yana mamakin dalilin da ya sanya Aslam baya son ayi masa zancen aure,wato ashe akwai Abinda yake aikatawa,shine kuma yake son lalata ƴar daya dauko matsayin amana?lallai dole ya dau mataki akan wanna al'amarin.

"Ba komai Alhaji, dama yanzu zan zo part ɗin naka,jira nake bakin su tafi,idan wani abun kake buƙata ka faɗa sai akawo maka yanzu"cewar mommy kenan tana kallon mijin nata,dan tafi son suyi maganar anutse.

"Kuji min munafuncin banza? ya zaki ce ba komai?bayan kuma akwai komai ɗin,ai wllh ba batun rufa-rufa,haka kawai acuci yarinya kuma kice ba komai,saboda ɗan ki ne ko?"granny ta fada cikin masifar ta tana zarewa mommy ido.

"Ba haka bane granny,Kinga wannan maganar bai kamata ayi ta anan gaban yara ba,kuma wllh niba ɓoye masa komai nake don yi ba,nafi son in sanar dashi a nutse Dan samun mafita"mommy ta fada kamar zatayi kuka.

"Ƙyaji dashi wllh sai an faɗa masa maganar nan ehe"
Cewar granny tana wani fari da ido kamar yarinya.
Ahankali Daddy ke taka benen,har ya sauko ƙasan falon,zama yayi akan kujera yana mai kallon granny,kafin yace "Hajiya ki yi hakuri ki kwantar da hankalin ki,domin ba wanda ya isa ya cutar da yarinyar Nan agidan nan,kuma in gyale shi,duk abinda take faɗa ,naji akunne na,kuma zan ɗauki mataki kwakwkwar akan Aslam"
Daddy ya faɗa cikin ɓacin rai,yana kallon mommy.
Kafin yace "lallai -lallai Aslam ya sameni yanzu a part ɗina"
Sannan ya juyo yana kallon Islam wacce ke zaune ta turo baki,cikin ɓacin rai ,zuwa lokacin kuma ta daina kuka.
"Kiyi hakuri Islam,ban dauko ki zuwa gidan nan dan acutar dake ba,In Sha Allahu zanyiwa tubkar hanci"Daddy ya faɗa cikin yanayi na kwantar da hankali.
Kallon Daddy Islam tayi kafin tace"ai wllh Alhaji,badan ina jin nauyin ka ba,da irin abinda zanyiwa wancan ɗan iskan ko,hmmmmm,amma duk da haka wllh saina rama ƙona Ni da yayi aƙirjina,sannan ya kalle min abinda ba wanda ya taba gani, Allah ya isa na wllh mugu kawai"Islam ta fada tana bin hanyar ɗakin Aslam da harara.

"Kiyi hakuri Islam,kuma na gode da ya zamo kina ganin ƙimata har kike saurara masa "Daddy ya faɗa cikin ɗan murmushi,shikam karfin halin Islam na burgeshi,sannan yarinyar ta shiga ransa sosai,jinta yake kamar yar cikin sa.
"Ato Gara dai ayiwa tubkar hanci, dan wannan yaron mai kama da na mamajo bamu san me zaiyi nan gaba ba.
Mommy dai shiru tayi kanta a ƙasa,tana sauraron abinda granny ke faɗi,can cikin zuciyarta kuwa ,tsoro ne sosai maƙare,yaushe Aslam yazama haka?idan aure yake so ai Gara ya faɗa ayi masa,meye nashi na rungumar yar mutane,ita fa ta gane kissing ɗin Islam yayi baki da baki,shine ita kuma take tunanin yawun sa ya bata .

" Madam ina son akira min Aslam yanzu,ya sameni a part ɗina"Daddy ya faɗa yana mikewa yace da granny"hajiyata Bari na koma na ɗan huta"

"To ɗan nan Allah dai ya kara maka lafiya,ya kuma bayyana waɗan nan mugayen da suka so cutar da kai"ameen Daddy ya ce tare da wucewa part ɗin sa.

Tashi mommy tayi ta nufi ɗakin Aslam,tana ta tunane -tunane.


Ɗago kai Islam tayi,kawai suka haɗa ido da Aman ya na kallon ta.tsaki tayi tana hararar sa kafin tace"Ni wllh na tsani kallo arayuwa ta,kai kuwa Aman idan ka kama kallon mutum kamar tsohon maye haka kake,ina dalili kayi ta kallo na kamar zaka cinye Ni"Islam ta fada cikin fada tana hararar Aman.
Shikuwa Aman murmushi yayi yana kara jin kaunar Islam cikin ransa,wllh komai tayi burgeshi take, haka yake son matar da zai aura ta kasance mai tsiwa.
"Kai ƙanwata, yaushe na kalle ki?Ni da nake kallon jikin kujera"Aman ya fada cikin murmushin sa mai kyau.

Kallon sa Islam tayi tare da taɓe baki tace "lallai kuwa ƙanwar ka,ta ina muka haɗa dangi?inba shishshigi irin naka ba?can dai ka nemi ƙannan ka,bani ba,Ni ba ƙanwar kowa bace"Islam ta faɗa tana turo baki.
Dariya Aman Yayi kafin yace "koba komai,dai nasan yanzu baki da yan uwan da suka fimu, kuma idan ke baki ɗauke Ni matsayin yaya ba,Ni na ɗauke ki matsayin ƙanwa ehe"ya faɗa shima yana turo baki yadda takeyi.
Kallon sa tayi,ganin yadda ya wani turo baki yaso baya dariya,dan haka ta ɗan kurmusa.ta buɗe baki zatayi magana,saidai
Kafin tayi magana, jannat ta ja wani uban tsaki tana tace"aikin banza wai mutum ba kowan kowa ba,kuma ba dan kowa ba,amma shegen tsirfa da iyayi,ko me za'a kalla anan? Muma kuma bamu buƙatar ki matsayin dangin mu,dan kunci ƙarfin haɗa iri da kucakakamar ke"ta fada cikin yatsina tana nuna Islam kamar wata kashi.

"Keee!! Jannat wllh ki kiyaye Ni, dan yanzun nan zan ɓaɓɓallaki in watsar agurin nan,banda asara.ina ruwanki da Ni?gidan naki ne ?ko ke kika kawoni gidan?banza mai zubin karuwai,wllh ki kula da kanki,duk ranar dana damƙeki sai jikinki ya fada miki,shi ai yayan naki yaga abin kallon,shiyasa yake kallo wawiya kawai"Islam ke faɗin wannan maganar azabure kamar zata doki jannat ɗin sai harara take banka mata.

"Wllh kinyi ƙarya yar karoro,baki isa ki faɗa min magana agidan mu ba,gaki nan karuwa mai bin maza,zakiyiwa ɗan uwana sharri,wllh yaya Aslam ya wuce da ajikin ki,mai kama da mayya,gara tun wuri ki hada kayan ki ki bar mana gida.

"Kee jannat meye hakan ?baki da hankali ne ?zaki rinka mata gori?ko baki san wanda ya kawo ta gidan ba?wllh idan na sake jin bakin ki sai na tattaka ki"Aman ya faɗa cikin zafin zuciya yana hararar jannat.

"Barta tayi,ai idan batayi haka ba bazata nuna ita marar tarbiyya bace ,wllh nikuwa akan yarinyar nan ,zan iya dokuwa da uban kowa ehe"
Cewar granny cikin masifa tana mikewa tsaye itama.dan duk abinda suke yi tana zaune .
Mommy ce ta fito daga ɗakin Aslam bayan ta sameshi kwance akan gado ya ƙurawa silin ido,kallo ɗaya zakayi masa kasan ransa abace yake."maza kazo inji Daddyn ku"ta fada tare da barin dakin,ba tare da ta jira amsar saba ya fito.

"Meye kuma ?me akeyi naga kun wani mimmƙe tsaye?ko faɗan ne? Mommy ta fada tana karasowa.
"Mommy wannan yar karoron ce ke son raina min hankali,kuma wllh kan uwar uban shegiya zanci la'ada waje dan niba sa'arta bace...

Tasss!! Jannat taji saukar mari akumatun ta, da sauri ta dafe kumatun tana kallon Islam,wacce ta wanke mata fuska da mari,
"Kai -kai -kai!! Ni kika mara "jannat ta fada cikin mamaki.
"An mareki, kuma idan kika sake rashin tarbiyya agaba na,wllh saina ƙara miki wani,banza yar tasha agaban mahaifiyar ki kike zagi dan baki da ɗa'a,wllh da sannu zan saita miki kwakwalwarki"Islam na gama faɗin haka ta juya tare da barin falon ta fice waje.

"Yawwa ƴar albarka kinyi dai-dai Allah ya baki ikon gyara wannan fitsararriyar yarinyar "cewar granny tana barin gurin,ranta fess.dan dama haushin jannat take ji ta raina ta sosai.

"Kuka jannat ta fashe da shi tana faɗin"mommy kina gani?agabanki wannan yarinyar ta mare ni?wllh bazan yar daba,saina rama"
Jannat ta fada cikin kuka tana buga ƙafa aƙasa, irin na tabararrun yara.

"Na gani, kuma tayi dai -dai jannat yau she zakiyi hankali ne?kullum kina girma kina da ɗa cin kashi?Indai rashin tarbiyya ne kije kiyi tayi,Ni kuma bazan hana yarinya ƙarama koya miki darasi akan rashin dacewar zagi ba"mommy na faɗin haka tayi wucewar ta ɓangaren Daddy.

Zaman yan bori Jannat tayi tana kuka harda shura ƙafa,wllh saita ci kaza-kazan Islam,hanan ce tazo kusa da ita tana rarrashinta,kamar zatayi kuka.
Shikuwa Aman tsabar haushi wayarsa kawai ya dauko yana latsawa.

"Keeee!!!! Uban me aka miki kike wa mutane wannan haukan kamar karamar yarinya?"
Aka dakawa Jannat tsawar da tayi silar haɗiye kukanta.
Aslam ne ya fito daga ɗakinsa, fuskar nan kamar hadari .

Cikin rawar jiki Hanan ta ce"yaya wannan Islam ɗin ce ta mare ta"
Wani malolon baƙin ciki ne ya tokare maƙogaron Aslam,wai wannan yarinyar wace irin annoba ce haka agaresu?ta takurawa kowa agidan,tsabar baƙin ciki bai san sanda ya kaiwa jannat duka da ƙafar sa ba,da sauri jannat ta kauce dukan ya bi iska.
"Shegiya a sararriya,yanzu ki rasa wacce zaki zauna kinawa kuka sai waccan yarinyar?sa'ar ƙanwar ki?wllh kin ji kunya,ba abinda kika iya sai tara samari da iya shege acikin gida ko?ki zauna tayi ta saki kuka,wata rana ma kakkarya miki ƙasusuwa zatayi ta watsar banza sha sha sha"ya na kaiwa nan azance sa yayi wucewar sa ɓangaren Daddy.cike da jin haushin jannat

"Wllh saina illa ta yarinyar can "cewar jannat ta na ci gaba da kukan ta.
Hararar ta Aman Yayi kafin yace "ko ita ta illa taki ba,banza ba karfin kirki sai rashin kunya,Ni wllh tayi min dai-dai ma"ya faɗa yana mai da kansa kan waya.
"To baƙin mugu dama haka zaka ce mana,kasa ido zaka ga abinda zanyi mata"Jannat ta fada tana tashi afusa ce,fuuuu!!! Tayi ɗakin ta.Hanan kuwa kan kujera ta koma ta zauna cike da tsoro,sai rarraba ido take.

Faɗa sosai Daddy ya rufe Aslam dashi,lokacin daya shiga ɗakin,ko amsa gaisuwar da Aslam keyi masa ma bai yi ba.ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,sai da Aslam ya Raina kansa,yaji kamar zuciyarsa zata kama da wuta,hakuri yake ta bawa Daddy Amma ko sauraronsa baya yi.sannan ya ɗora da cewa"kuma wllh Aslam,na baka nan da sati biyu ka kawo min matar da zaka aura,idan ba haka ba,Ni da kaina zan zaɓa maka,tashi ka bani guri mutumin banza kawai"Daddy ya faɗa cikin fushi.

Sosai fargaba ta kama Aslam,aure kuma ?to shi wama zai kawo matsayin matar da zai aura?bayan ba shi da budurwa,sai dai abokan harka? impact ma shi bai shiryawa aure yanzu ba.haka kawai ya ɗorawa kansa damuwa.haka ya koma ɗakinsa jiki ba kwari,yana ta tunane tunane,shi gashi ba aboki gare shi ba,bare ya nemi shawara.itama mommyn da yake ɗan shawarar da ita,tayi fushi,dan ko kallon sa bata ma yi.

Hakuri sosai mommy ke bawa Daddy tana kwantar masa da hankali akan lamarin Aslam,har ta samu ya sauko daga fushin da yake.

Kai tsaye garden Islam ta wuce ,kan bishiyar goba ta hau tayi zamanta,bayan ta kira janbun ta,lumshe ido tayi kamar mai barci,sai dai sam ba barcin take ba ,tana tunanin rayuwarta,da kuma iyayen ta, ko suna wane halin yanzu?ko sun mutu ma waya sani.ahankali ta kai hannun ta tare da shafo ƙirjin ta,inda Aslam ya watsa mata ruwan zafi,ƙwafa tayi tare da furta"wllh saina rama,zaka

Please Login or Register in order to submit comment