Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san nika gona,gaba ɗaya yaran gidan nan basu da mutunci,kuma wllh saina koya musu hankali"ta fada kamar wata shugaba.

Aslam kuwa ji yayi dakin yayi masa ƙunci,yana buƙatar shan iska mai sanyi,dan haka tashi yayi kai tsaye bayan ya sauya kaya,daga manyan zuwa ƙanana,garden ya nufa,zuciyar sa sam ba daɗi.yana zuwa ya sami guri abakin swimming pool Yayi zamansa bayan ya zura kafafunsa cikin ruwan.ba abinda ke yawo cikin zuciyar sa,face kalaman Daddy,ya Nemo mata nan da sati biyu,to a ina zai nemo?wa yake da ita?amma yasan yadda zaiyi,zaiyi ta bawa Daddy haƙuri,idan lokacin yayi,akan zai nemo yana kan bincika wa ne,da haka zaiyi ta jan ran Daddy har ya hakura da zancen.

Kamar daga sama Islam ta hango Aslam,zaune bakin ruwa,murmushi tayi tare da radawa janbu magana a kunne"maza janbu jeka ciro min ayaba guda biyu,ka dawo yanzun nan.
Aikuwa cikin gudu da tsalle janbu ya nufi kan bishiyar ayaba,ba jimawa sai gashi ya dawo dauke da ayabar guda biyu ahannunsa.
Karba tayi tana murmushi,kafin ta bare ta cinye guda ɗaya,ta rike ɓawon,janbu ma bashi dayar tayi ya cinye.bawon ta karba sannan ta sauƙo daga kan bishiyar ahankali,dan basu da wata tazara da gurin wankan.

Ahankali ta lallaɓa, ta bayan Aslam,cikin sanɗa.
Tana zuwa bata jira komai ba kawai ta ingiza shi cikin ruwan nan,ji kake tinjimm!!
Aslam ya faɗa cikin swimming pool ɗin nan,aikuwa kansa ya bugu da jikin mariƙar shiga ruwan.
Runtse ido Aslam Yayi da mugun ƙarfi,sakamakon raɗaɗin azaba daya ziyarci kwakwalwar sa.nan da nan gurin ya fashe ,jini ya fara tsatstsafowa.dariya Islam ta sanya da karfi tana nuna Aslam da hannun ta.
Cikin sauri ya buɗe idon sa afusace jin Muryar Islam na masa dariya.hakan na nuna ita ta turashi cikin ruwan kenan?
"Wai wayaga tinjimi, ka ganka kuwa?wllh kamar wani barawon kaza,irin an kamashi ɗin nan yaci duka,hahhhhh"ta ƙyalƙyale da dariya.
Cikin fushi da ɓacin rai Aslam ya kama karfen shiga ruwan ya fara fitowa da mugun sauri,yau kam idan ya kama yarinyar nan,sai dai shima akashe shi,amma sai ya shaƙeta ta mutu.

Ganin ya fito cikin fusata ya nufota gadan -gadan ,yasa Islam saurin watsa wannan bawon ayabar dake hannunta,ai kuwa ba tare da lura ba Aslam ya taka bawon nan,ya kwashe shi,suuuuu yayi baya ƙafarsa ta lankwashe,sannan ya faɗa kan ƙafar.
"Wayyo Allah ƙafa ta"Aslam ya faɗa yana runtse ido,jin yadda ƙafar ta dauka wani duuummmm.
Dafe kansa yayi wanda ya ci gaba da sarawa kamar zai rabe gida biyu.sai juya kansa yake cikin azaba.
Islam kuwa takowa tayi zuwa inda yake kwance, tana masa kallon uku saura kwata. Kafin ta sanya dariyar mugunta tace "kaɗan ma ka gani,In dai nice wllh sai zaman gidanku ya gagare ka,ba dai Ni kake rainawa ba,kayi kuskure taɓa Islam,kuma wllh waɗan na abubuwan da ka kalla,baka gani abanza ba,saina ɗau fansar hakan,Ni rainon dawa ce bana ɗaukar raini"tana faɗin haka ta juya ta bar gurin ta nufi cikin gidan.
Aslam kwance yayi agurin cikin azaba,yana juya kansa,tabbas zuwa yanzu ya gama yarda, wannan yarinyar aljana ce.
Cikin dabara ya yunƙura tare da mikewa zaune,ƙafarsa tayi wani ƙaran da saida ya kwalla dan ihu yana runtse idon sa....

Masu karatu karfa islam ta ballawa Aslam kafa🤣🤣
Hohoho muje zuwa masoya,
Lamarin na gaba.

Mrs babi ce 💘💘
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Paid page

21/22


Please kada wanda ya fitar min da littafi,dan Allah domin na kuɗine.duk mai so ta biya ta karanta.🙏🙏


_______________Azabure Aslam ya nufi Islam,cikin gushewar tunani da rashin madafa,kai tsaye ya cakumo Islam wacce ke yarfe hannu cikin azaba tana ɗan tsalle,gurin da ruwan shayin nan ya zubo ajikinta kuwa,har yayi jaa sosai kamar zai tashi.
Ba ɓata lokaci Aslam ya rungumeta ajikinsa yana fidda wani irin numfashi mai kama da yana neman shiɗewa.
Wani irin rawa jikinsa ya kama,sakamon yadda tsinin boobs dinta ke sukar ƙirjinsa, runtse ido yayi da ƙarfi yana mai tura fuskarsa dai-dai wuyanta tare da sakar mata hucin iska daga hancinsa.

Itama Islam,wani irin yanayi ne mai matukar wahala agare ta taji yana ziyartar ta,wannan shine karo na farko arayuwar ta, da wani ɗa namiji ya taba rungumar ta ,kuma ba tare da kaya ajikinta ba,
Da ƙarfi ta lumshe idon ta,tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, abubuwa biyu ne suka tarar mata alokaci ɗaya,na farko raɗaɗin da ƙirjin ta keyi,na biyu rungumar da Aslam Yayi mata ba karamin daga mata hankali tayi ba,jin ta take kamar zata faɗi, jikinta rawa yake sosai,tsoro da fargaba suka baibaye ta, gashi ba ƙaramin dadin yanayin nasu take ji ba,idonta alumshe tana ƙoƙarin kwatar kanta daga gareshi,amma gangar jikinta ta ƙi bata wannan damar.
Shikuwa Aslam,sai wani shafa soft fatar bayan ta yake,yana karajin shauƙi fiye da wanda yake ji, gaba ɗaya ya shagala,ji yake kamar bai taɓa jin jikin mace mai ɗumi irin na Islam ba.nan da nan jarabar sa ta motsa hankalinsa yayi ƙololuwar tashi ,sai nishi yake kamar mai zazzaɓi.

Cikin ƙanƙanin lokaci,Islam ta dawo hayyacinta,ta fahimci halin da suke ciki ,lallai yau akwai bala'i, wannan azzalumi ne ya watsa mata ruwan zafi?kuma yaga jikin ta?sannan ya rungume ta? Ai kuwa ya taɓowa kansa bala'i wllh.
Aslam yana cikin yanayin sa na gushewar tunani da saɓa lamba,kawai saiji yayi an tunkudeshi da mugun ƙarfi,har saida ya buga kansa da jikin bango,da sauri ya dafe kansa,yana mai runtse ido,lokaci guda kuma ya dawo hayyacin sa.
Sannan ya fahimci irin ƙwafsin da yayi.
Ahankali ya ɗago kansa yana kallon Islam,wacce ke huci kamar zakanya,tana riƙe da towel din bayan da ɗaure shi akirjin ta, ta rufe boobs ɗin ta.
"Shikenan na kara kwafsawa,yanzu da wane idon zan kalli yarinyar nan?amma nasan me zanyi"Aslam ya faɗa cikin zuciyar sa yana mai kallon Islam cikin ɓacin rai ya fara magana"ke ƙaramar yar iskace,kina tunanin zuwan ki,gaba na da towel zai sa naji wani abu ne game da ke?hmmmmm,yarinya kinyi karya,domin bakya cikin tsarin matan da Aslam,zai iya jin yana sha'awar su ko ya shiga wani hali dalilin su,kuma wllh ina mai gargaɗin ki ki kiyaye zuwa inda nake,domin bana ƙaunar ki,bana son ganin wannan mummunar fuskar taki mai kama da an dama kashi,banza wawiya marar kamun kai"Aslam ya faɗa cikin ɓacin rai mabayya ni, wanda azahiri ƙoƙarin fidda kansa kawai yake.
Yana gama faɗin haka yayi saurin nufar ƙofar barin falon,dan baya ma fatan jin abinda zata faɗa ,yasan ba abunda zai masa dadin ji zata faɗi ba.

Cike da mamaki da al'ajabi Islam ke binsa da kallo,lallai mutumin nan,rainin hankalinsa yayi yawa, kan uba! Wato nice ma nake son ɗaukar hankalinsa?hmmmmm baisan wa ce ce Islam ba,wllh sai yayi dana sanin wannan iskancin da yayi min."baka taba jikin Islam abanza ba wllh saina koya maka hankali,banza ɗan iska kawai"ta fada cikin muryar jin haushi,da takaicin yadda ya faɗa mata magana kumaya fice ba tare da ta maida masa martani ba.
Kayan data dauko ta zara cikin fushi ta koma dakin granny.

Shikuwa Aslam,ko ganin gabansa bayayi sosai,haka ya fice daga falon,kai tsaye cikin motar sa ya nufa. Yana zuwa ya bude motar da sauri ya shige yana mai rige da malamar sa ,wacce tayi tsaye ƙyam kamar sanda.
Kife kansa yayi akan sitiyarin motar,numfashi yake saukewa da sauri da sauri,idonsa alumshe,sosai yake jin wata irin matsananciyar sha'awa na taso masa,tunda yake bai taba shiga irin makamancin wannan yanayin ba,anya kuwa yarinyar nan mutum ce?ba abinda ke yawo cikin idon sa,banda cikakku kuma tsayayyun boobs ɗin Islam,tsaki yayi yana mai jin tsanar Islam na ratsa dukkan sassan jikinsa.
Kusan minti talatin yayi cikin wannan yanayin,sai juya kansa yake yana lumshe ido da budewa,da gyar ya samu ya buɗe aljihun motar sa, ya ballo wasu ƙwayoyi ya watsa cikin bakinsa.
Gumi ne ya fara tsatstsafo wa agoshin sa yana sauke ajiyar zuciya,kusan minti biyar kafin ya tada motar ya bar gidan,fuskarsa ba alamun walwala ko kaɗan ya nufi asibiti.

Kamar yadda su mommy ke zato kuwa,hakan ce ta kasance,tare suka dawo gida da Aman,anan gida za'a ci gaba da kula dashi, Daddy ma nan da jibi suke sa ran zai dawo gida,dan ya ce bazai iya zaman asibiti ba,kuma jikinsa da sauƙi alhmdllh.

Yau kwana biyu da faruwar wannan abun,sam Aslam yaki bari su hadu da Islam,dan baya fatan ganinta kusa dashi,haka kawai,zai zauna yayi ta tunanin manyan boobs ɗin ta,yana jin yadda suke sukar sa aƙirji.
Hakan yasa ya yarda cewar Islam mayya ce ko kuma aljana.
Itama bangaren Islam tana nan tana ƙulla irin yadda zata ɗau fansa akan abinda yayi mata.dan ta rantse baici bulus ba,saita rama abinda yayi mata.

Yau ta kasance ranar juma'a,dan haka suna zaune gaba ɗayansu afalo, dan tuni an sallamo daddy, jiki alhmdllh yaji sauƙi yana yin komai da kansa yanzu haka yana part ɗinsa tare da babban amininsa ,da kuma yan dubiya.
har su jannat da granny duk suna falon.Islam na zaune kusa da granny tana sanye cikin wata riga iyakar rigar gwuiwar ta,itama cikin kayan hanan taje ta zabo, ba ruwanta,idan tayi wanka dakin hanan kawai take nufa ta ɗauki kayan da ranta ke so ta sanya.
Aman na zaune atsakiyar su, yana cin naman kaza.yayin da mommy ke yanka masa kayan fruit.
Gaba ɗaya hankalinsa na Kan Islam,sosai take burgeshi,kuma yana jin kaunar ta cikin ransa,sosai.
Kallonsu Islam keyi cike da jin kewar ahalinta, ko yaushe zata ga nata iyayen?ko suna wane hali yanzu?shin da ransu ma ko sun mutu?
Tayi nisa cikin tunanin da take yi taji an dafa mata kafaɗa, juyowa tayi da sauri ta kalli granny.
Cikin yanayi na damuwa tana,sauƙe ajiyar zuciya.

"Yata me ne ne yake damun ki?ko wani yayi miki wani abu ne?fadamin yanzu inci mutuncin mutum wllh ko waye "granny ta kai ƙarshen maganar ta cikin masifa.
Jannat ce cikin salon rashin kunyar ta tace "kuji dai grannyn nan,waye zai kula wannan abar harya bata lokacinsa, can dai tasan abinda ke damunta"ta fada tana murguda baki.

Tsawa mommy ta dakawa jannat,tace "jannat bana son rashin kunya,grannyn kike fadawa wannan maganar?sa'arki ce?"ta fada cikin ɓacin rai.
Turo baki jannat tayi tana ƙunƙuni.
Yunkurawa Islam tayi dan ba,jannat amsa,sai dai
Kafin tayi magana aka bude kofar falon,ƙamshin da suka ji ya cika falon ne ya tabbatar musu da cewar Aslam ne,dawowar sa kenan daga masallaci,yana sanye cikin farar shadda mai matukar kyau da ɗaukar ido,sallaya ce rataye akafaɗar sa, ta dama,sai hula baka da bakin takalmin,yayi kyau matuka kamar wani ango.

Da sallama ya ƙara so cikin Falon,kusa da mommy yazo ya zauna.nan da nan su jannat suka shiga cikin taitayi su,
Kallonsa mommy tayi cikin murmushi,tace "Aslam ka dawo?
Lumshe ido yayi tare da jingina kansa akafadun mommy Yana wani yatsine fuska,kafin yace "Yes mommy am tired wllh,barci nake son nayi"ya faɗa yana wani narkewa jikin mommy kamar ɗan yaye.

Kansa mommy ta shafa tace "kaci abinci saika kwanta ka huta.
Ahankali ya ɗago da kansa yana shafa kan Aman,ya ce "boy ya jikinka?"
Murmushi Aman yayi kafin yace "da sauki sosai yaya,nan da kwana kaɗan zan mike "ya faɗa cikin murmushi yana kallon yayan nashi.
Jinjina kai Aslam yayi,kafin yace "in sha Allah.
Duk abinda ke faruwa akan idon Islam,mamaki ,haushi, da takaici sun mamaye zuciyar ta,ji take kamar ta shaƙe wannan Aslam ɗin wllh,ji yadda yake wani kwanciya jikin mommy gidodo dashi.
Tatsi tayi mai ƙarfi wanda saida ya ja hankalin kowa zuwa gare ta.cikin ɓacin rai ta fara magana"wllh wannan abun kunya da yawa yake,haka kawai mutum gundundun dashi yayi ta likewa mamar sa?yo wannan abun ban haushi har ina?dan Allah kai Aslam ko kunya bakaji?dubi ƴan ƙannan ka,suna zaune aguri daban,amma kai daga zuwa ka wani zo kana ɗora wannan rafkeken kan naka mai kama da kwallon kwakwa,akan baiwar Allah,wllh ka rinkayin abinda ƙuda zai bika"ta fada cikin salon rashin tsoronta tana kawar da kanta can gefe.
Gaba daya ido suka zuba mata,cike da tsoro su jannat ke kallonta baki buɗe,jin irin kalaman da take faɗa wa yayan su,lallai wannan yarinyar rashin kunyar ta ya kai inda ya kai.
Hanan kuwa tsabar tsoro sai kwabe fuska take tana ƙoƙarin yin kuka. Anan kuwa dariya ke son kama shi,wllh Islam ta ita yaba magana,wai rafkeken kai kamar kwakwa"ya faɗa cikin ransa yana danne dariyarsa.
Gogan naku kuwa,saida ta fara magana ma ya san da ita agurin,kallon ta kawai yake cike da tsana da jin kamar ya shaƙeta ta mutu.lallai yarinyar nan,wai Ni take faɗa wa waɗan nan maganganun?agaban ƙannai na?kuma acikin gidan mu? Salon ta ja min raini gurin yara?kallon mommy Yayi,wacce itama take kallon Islam,da mamaki akan fuskar ta,ita tausayi. Islam take ji sosai,dan tasan rashin zama da babba shine babban dalilin da yasa bata girmama kowa.
"Hummmm ƴar nan kema dai kya faɗa,wannan abin tsantsani har ina,ki dai gani,wannan uban wasu kakan wasun,shine ke kwanciya akan uwar sa, ko kunya baya ji, yayi aure amma yaƙi,wllh cikin sa'annin sa akwai masu yaya biyu,amma shi kullum ba abinda ya tsana sama da zancen aure,Allah yayi wadaran naka ya lalace"granny ta fada tana taɓe baki.
Murmushi takaici Islam tayi kamar wata irin uwar nan tashi,kafin tace "to kema granny ta yaya zaiyi aure?bayan yana fita can yayi iskancinsa awaje,wllh dan baki san me yayi min bane rannan,amma wannan Aslam ɗin ba mutumin kirki bane wllh ɗan iska ne,bai gani ya gyal......
Tasss! Tasss!! Kake ji Aslam ya wanke fuskar Islam da wasu lafiyayyun maruka,wanda ya dauke ji da ganin Islam na wucin gadi,
Zaro ido su hanan sukayi, cikin tsoro,da gudu hanan tayi bayan mommy ta buya idanunta na zubda hawaye,itama dai jannat bayan kujera ta koma ta tsaya,jikin ta na rawa.
Nuna ta Aslam Yayi da ɗan yatsa cikin ɓaci rai yake faɗin"kinyi ƙarya,kice zaki tozar tani gaban ahalina, wllh baki haifu ba,ki sani Ni Aslam naci uwarki a iya shege, dan haka muzuba Ni dake shege ka fasa,daga ke har waƴan da ke daure miki gindi, kike iskancin da kika ga dama ina dai dai daku"Aslam ya faɗa cikin huci da tsantsar ɓacin rai,wllh badan yasan kashe mutum ba kyau ba ,da yau saiya kashe yarinyar nan kowa ya huta.
Cikin masifa da ɓacin rai,granny tace "wato Ni kenan,da ubanka ko?to wllh nikam nafi ƙarfin rashin mutuncin ka, sai dai kayi wa ubanka,kuma wllh sai Allah ya sakawa yar mutane marin da kayi mata" cewar granny tana rike kafadar Islam kamar tayi kuka.
Wani banzan kallo Aslam ya watsawa granny kafin yace "na mareta kuma zan sake marinta idan ta sake yimin rashin kunya"
"Ni ka mara ?
Islam ta fada cikin jin raɗaɗi da zafin marin da Aslam Yayi mata.idanunta sun ciki da hawaye.
"Na mare ki kiyi duk abinda kike ganin zaki iya banza yar tasha wawiya jaka" Aslam ya faɗa cikin masifa.
"Wllh kaine wawa jaki,kuma zaka san ka mareni, dama ina da ɗaukar fansa akan ka,to wllh ka ƙarawa kanka bala'i da masifa,kuma kaine dan tasha dan iska"Islam ta fada hawaye na zirarowa da idanunta.
Daga hannu Aslam Yayi da nufin ƙara mata wasu marukan,mommy ta daka masa tsawa"Aslam meye hakan?dukan ta zaka ƙara yi?"
Mommy ta fada cikin fushi,dan ba taji dadin marin da yayiwa Islam ɗin ba,ga sawun hannun sa nan ruɗu -ruɗu akan kyakykyawar fuskar ta.
Afusace ya juyo yana kallon mommy"baki ji irin rashin kunyar da take min bane mommy?"ya faɗa kamar zaiyi ihu dan ɓacin rai.
"Ko ma me tayi maka saika jira kaga irin hukuncin da zan ɗauka,amma agaba na kake marin ƴar mutane,wacce take matsayin amana agurin mu,ka bani mamaki Aslam,rai na ya ɓaci"mommy ta fada cikin haɗe rai.
A duniya ba abinda Aslam ya tsana sama da ganin mahaifiyarsa cikin fushi,kuma ace shine silar fushin nata.dan haka sauke hannun sa yayi,yana mai aikawa Islam mugun kallo.kafin yayi ɗakin sa da sauri cikin fushi.
Hawaye ne ke saukowa daga idanun Islam,bata taɓa jin kewa da son rungumar mahaifiyar ta irin na yau ba,amma wllh tayi alƙawarin Aslam bai ci banza ba,saita rama dukkan cin kashin da yayi mata.

Cike da tausayi,granny ke shafa bayan islam"kiyi hakuri yataAllah zai saka miki,kinji"ta faɗa kamar zatayi kuka.

Mommy ce tazo kusa da Islam ta kamo hannunta tare da zaunar da ita akan kujera,hannu ta sanya tana sharewa Islam hawaye,kafin cikin son kwantar mata da hankali tace "kiyi hakuri Islam,zanyiwa Aslam magana akan karya ƙara dukan ki, kuma ina son ki fita daga harkar sa,ki daina masa rashin kunya, dan babu kyau yiwa babba rashin kunya kinji"mommy ta faɗa tana rungume Islam tare da shafa bayan ta.
Cikin muryar kuka Islam tace "mommy mari na yayi fa! Wllh ba zan yarda ba,saina rama abinda yayi min,rannan fa wani daki ya kaini,yayi ta dura min yawun bakinsa cikin bakina,ranar nan ma haka ya ganni ba riga,kuma ya rungumeni yana ƙoƙarin yi min iskanci, wllh ɗan iska ne shi,kuma bazan taɓa yarda ba"ta kai karshen maganar ta da sanya kuka,Islam zata iya rantse wa bata taba yin kuka na ɓaci rai ba, tun tasowarta sai yau.kuma akan wannan bijimin san,wllh zai gane kuren sa.
Sosai gaban mommy ya fadi,salati kawai take cikin ranta,sun shiga uku,karfa Aslam ya jawo musu abin kunya?lallai dole ta sanar da daddy su san abinyi akan wannan matsalar.
Salati granny ta dauka"laaaa ilaha'illallahu! mun shiga uku,Ni dama nasan akwai dalilin da ya hana wannan yaron aure,ashe ƴaƴan mutane yake lalubewa?shine zai fara akan yar amana wllh bazan yar da ba,dole asan abinyi. Shiyasa kullum zaka ganshi,da lumsassun idanuwa kamar mai jin barci,ashe Fitina ce acikinsu"
Jannat da hanan kuwa sam basu yarda da abinda Islam ta fada ba,dan gani suke bata kai matsayin da yayansu zaiyi wani abu da ita ba,kawai ta fada ne dan tana son bata masa suna.

Shikam Aman tausayin Islam ne ya gama mamaye zuciyar sa,sam yana ganin abinda yayan nashi yayi bai kyau ta ba,koma menene bai kamata ya mari Islam ba.
"Meke faruwa ne?tun daga part ɗi na make jiyo hayaniya"
gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallon inda maganar ke fitowa.
Ba kowa bane face daddy,Wanda ke tsaye riƙe da karfen hawa benen da zai kaika part ɗin sa....

Masu karatu, me zai faru idan ya kasance Daddy Yana jin abinda suke fadi?
Muje zuwa
Mrs babi ce 💘💘
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: _____________"Kai Aslam meye kake faɗi haka?akan lafiyar taka ma saika nuna taurin kai?ko anfaɗa maka ana wasa da lafiya ne?to kayi hanzarin tsayawa ta duba maka ƙafar tun kafin raina ya gama ɓaci gaba ɗaya"
Daddy ke faɗin wannan magana cikin ɓacin rai,dan yasan halin Aslam da kafiya,idan ba zabu-zabu yayi masa ba,to bazai tsaya ta duba masa kafar ba.
Cikin jujjuya kai irin na shiga halin ƙaƙa nikayi Aslam ya kalli Daddy ya fara magana cikin marairaita"Daddy please Dan Allah ka kira koma waye yazo ya duba min ƙafar,amma banda wannan yarinyar wllh Daddy idan ta duba min ƙafata zafin da zanji cikin zuciyata saiya fi na raɗaɗin da ciwon nan kemin,Please mommy kisa baki"Aslam ya faɗa yana kamo hannun mommy, jikinsa zafi ƙau.

"Kai Aslam,bana son Shashanci fa,Ina faɗin magana kana musani?ranka zai matukar ɓaci wllh, kasan ba na son shirme ,ke Islam maza zo ki taimaka masa"Daddy ya faɗa ba alamun wasa akan fuskar sa.
Kallon mommy Aslam Yayi kamar wani Maraya yana karya wuya.lumshe ido mommy tayi alamun yayi hakuri Islam ta duba masa ƙafar.
"Daddy naga kamar baya son na duba masa,kawai ka nemo wani mai gyaran ya duba masa,dama Ni tausayin sa ne yasa na ce zan duba masa kafar,amma tunda baya so kawai bari na tafi"Islam ta faɗa cikin muryar tausayi tana juyawa da nufin barin ɗakin.

"Kinga Islam karki tafi, zoki duba masa ƙafar kinyi niyyar aikin lada karki fasa"cewar Daddy kenan ganin Islam na ƙoƙarin barin ɗakin.
Saida Islam tayi murmushin mugunta kafin ta juyo ta dawo cikin dakin.
"Maza Islam duba masa kinji"cewar mommy tana janyo Islam zuwa bakin gadon.

Zama Islam tayi agefen gadon tace "Miƙo ƙafar taka muga"ta faɗa cikin dakiya kamar wata uwarsa.
Tsabar haushi da bakin ciki yasa Aslam ya manta da ciwon da ƙafar ke masa ya wani turo ta bakin gadon da karfi, da hanzari ya runtse idonsa tare da damƙe zanin gadon,sakamakon azabar daya ji ƙafar nayi masa.
Islam kuwa ahankali ta sanya tattausan hannunta tana ɗan shafa ƙafar tasa sannu kan hankali,kamar tana masa waiwayi,
Wani yuuummm!!! yaji tsikar jikin sa na tashi,ahankali ya lumshe idon sa tare da sakin wani ɗan nishi,da bai shiryawa fitowar shiba.ji yake kamar sosa masa gurin take,wanda hakan yaso sanya shi cikin wani yanayi,ga lallausar fatar hannunta mai dumi dake ratsa kashin ƙarar tasa.sai wani lumshe ido yake yana ɓudewa.
Duk abinda yake idon Islam na kansa,tana kallon sa,ɗan jijjiga kai tayi tare da dan ne lips ɗin ta na kasa.cikin zuciyar ta tana mai cewa"zakayi bayani ne kwarton banza,wato kana jin daɗi ina shafa maka ƙafa cikin salon iskanci ko?yanzu zaka dawo hayyacin ka" ta kai ƙarshen zancen zucinta, tana mai cafke ƙafar tashi da ƙarfi.

Aslam Yana can ya fara lulawa duniyar jin daɗin sa,dan tuni zuciya da gangar jikinsa sun fara amsar tayin Islam,kawai ba sani ba sabo yaji wani ramtsatstse zafi ya ratsa kwakwalwar sa,sannan ya watsu cikin sassan jikin sa.
Da sauri ya buɗe jajayen idanun sa,ya sauƙe su kan fuskar islam.wacce ke kallonsa cikin wani salo na ɗaukar hankali,da murmushin ƙeta. Saurin kawar da kansa yayi tare da haɗe rai.
Ƙara matsa kafar Islam tayi da karfin Daya fi na farko.
"Washhhhh mommy "ya furta ahankali yana mai kamo hannun mommy idonsa arufe.

Sannu aslma,ai laifin ka ne,kabar ƙafar tayi maka tsami da yawa,dole kaji zafi sosai."cewar Daddy kenan cikin tausayawa.
Mommy kuwa kansa kawai take shafawa cike da tausayi.
Haka Islam ta dage tana ta matsa kafar Aslam cikin mugunta,saida ta tabbatar ya azabtu dan gaba ɗaya gumi ya gama wanke masa jiki,tuni zazzaɓi yayi nashi gurin.
Kafin tace "dadddy ya sami gocewar ƙashi ne,kuma ya bari har saida gurin ya kumbura,yanzu ma da gyar na gano hakan,dan haka yanzu zan gyara masa ƙashin, amma saiya ɗaure dan naga kamar rago ne"Islam ta fada tana nuna alamun tausayi akan fuskarta.
"Wani matsiyacin kallo Aslam ya bi ta dashi,wato shine ma rago?yanzu duk wannan iskancin data gama yi masa da ƙafa bata gama gyarawa ba kenan? Wllh yasan da nufi tayi masa hakan,amma ba komai akwai ranar ƙin dillanci,duk ranar daya shigo hannunsa wllh saita raina kanta.
"Karki damu Islam ki gyara masa,ai dole ya daure inba haka ba sai kafar ta sami matsala"cewar Daddy kenan.
Haka Aslam yana ji yana gani Islam ta kama ƙafarsa taci gaba da gana masa azaba,aganinsa, amma wannan karon kam gyara tayi masa na tsakani da Allah,dama kuma tana kallon ƙafar ta gane gociyar kashin ne ,kawai taso bashi wahala ne.
Idan kuka ga Aslam awannan lokacin saikun tausaya masa,dan ba ƙaramin wahala ya sha ba,sai cizon lips kawai yake yana juya kai.gumi kuwa kamar yayi wanka.
Su mommy sai sannu suke masa.

"Daddy na kammala,yanzu sai ya kula sosai banda garajen tashi idan zaiyi wani abu akwai buƙatar ya sanar dani,dan In nuna masa yadda zai motsa kafar"
"Sannu Islam Allah yayi miki albarka "Daddy ya faɗa cikin jin daɗin yadda take taimakon ahalinsa.

Murmushi tayi kawai tana kallon Aslam Wanda yayi lamo akwance,kansa akan cinyar mommy Yana maida numfashi. cikin zuciyarsa kuwa tunanin hanyar ɗaukar fansa yake.
"Mommy yanzu aɗan kawo masa farfesu mai yaji sosai ya samu yaci" Islam ta fada tana kallon mommy.
"To Islam Bari na haɗo masa yanzu mun gode ƴata"cewar mommy tana shafa kan Islam.

Murmushi tayi tana mai cewa,ba komai mommy zan ma jira ki kawo dan naji yanayin yajin da ake buƙata idan yayi kuma in dan kula dashi karya motsa kafar,tunda yanzu zai ji tana masa zugi "Islam ta faɗa tana kallon mommy fuskarta ɗauke da murmushi.

Murmushi mommy tayi kafin ta fice daga ɗakin ta nufi kitchen Dan haɗawa Aslam farfesun.
Tana ganin mommy ta fice ta kalli Daddy tace "daddy Ina buƙatar man zafi dan yin addu'a aciki, sai a rinƙa shafa masa"to Daddy ya ce sannan ya nufi ƙofar barin ɗakin,bashi da wata damuwa tunda yasan Aslam baida lafiya,bare yayi yunkurin yiwa Aslam wani abu,kuma yaji gargaɗin da yayi masa,dan haka hankali kwance ya fita dan kawo man zafin.
Daddy na fita Islam ta sanya dariya har da riƙe ciki.kallonta kawai Aslam ya tsaya yi ba tare da yace komai ba,to me zaice ya fuskanci abun na iso sai godiyar Allah kawai,amma tabbas tana da matsalar ƙwaƙwalwa.
Zagayawa tayi kusa da inda kansa yake, rungume hannu tayi tana kallon sa da fuskar tausayi kafin ta fara girgiza kai tana faɗin"Allah sarki malam tinjimi, kaɗan bani tausayi kaɗan,dubeka akwance shirim kamar kayan wanki,amma duk kai ka jawa kanka,taurin kai da rashin kunya sune matsalar ka,Ni kuma bana ɗaukar raini haka Allah yayi ni,shiyasa duk wanda ya shiga gona ta yake shan wahala,kai kuma abubuwan sunyi maka yawa,gaka ɗan iska mai shegen son mata,kai

Please Login or Register in order to submit comment