Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin ƙofar dakin na Hanan,mommy ta sanya hannu ahankali, tare da murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe.

"Ikon Allah"mommy ta faɗa cike da mamaki tana kallon cikin dakin.
Cikin rawar murya Hanan ta ce"kin gani ko mommy?wllh dama na faɗa miki,da idona naga kayan daƙin suna rawa,har gadon da take zaune ma rawa yake"Hanan ta fada cike da tsoro tana ƙara buya abayan mommy.

Turo ƙofar ɗakin mommy tayi, gaba ɗaya kofar ta wangale,ta yadda kowa zai hango abinda ke cikin ɗakin.
Da sauri jannat da granny,suka leƙa ɗakin, dan ganewa idanunsu abinda Hanan ɗin ta fada.

Sai dai cikin mamaki granny tace "a'a yau naga ikon Allah,hannatu me kike son nuna mana ne wai? Nidai banga komai cikin ɗakin nan ba,banda Islama dake ƙwance akan gadonki?"
Granny ta faɗa tana nuna cikin ɗakin da hannunta.

Da sauri Hanan ta bar bayan mommy tana mai leƙa dakin nata.ikon Allah dakin yana nan a yadda yake,hatta madubin daya fashe dazu,gashinan ƙalau ama'ajiyinsa,to me hakan ke nufi?ko dai idonta ne yayi mata gizo ɗazun?

"Hanan kullum ina yawan faɗa miki,ki daina saurin adar da magana idan baki tabbatar da ita ba,bana son karya,ta yaya kayan daki zasu kama rawa? kamar wasu ƴan gidan gala?"mommy ta fada tana kallon Hanan.

"Wllh mommy na gani,da idona na gani, lokaci. Da yaya yazo harya mareta shine ta dawo daki, nikuma na biyota dan In rarrasheta,kawai naga komai na dakin yana rawa"Hanan ta fada da iyakar gaskiyarta, tana marairaice fuska.

Tsaki mommy tayi tace"saboda bashi da hankali,daga zuwa saiya kama marin ƴar mutane baisan ko wa ce ce ba?mtsss tayi tsaki tare da barin bakin ƙofar ta shige dakinta.
Granny kuwa harara ta bankawa Hanan tace "banza wawiya marar hankali,inaga dai kin fara shaye-shaye ne, da ki ka sha shine take gaya miki ba dai-dai ba,yo Allah na tuba ko lokacin da muke yan mata da akayi yayin aljana yar caras,ai bantaba jin wai kayan daki suna rawa ba,bare yanzu. yara sai rashin hankali kawai da sangarta kuka iya"granny ta faɗa tana barin gurin itama.

Kallon jannat tayi wacce ke tsaye ba tace komai ba tunda suka zo gurin.
"Wllh anty jannat ba ƙarya nake ba,da idona naga tana kallon kayan dakin nan suna girgiza"Hanan ta fada tana kamo hannun jannat.
Ajiyar zuciya jannat tayi,kafin tace "ki barta kawai,idan ma wani tsafin takeyi,wllh saina tona mata asiri,dan nikam wllh na tsaneta bana ƙaunarta ko kaɗan,dama wannan kyan nata ai ba irin na mutane bane"jannat ta fada tana hararar Islam dake kwance akan gado, kuma da alama barci ma take.

"Kinsan me za'ayi?
Jannat ta fada tana kallon ƙanwarta.
Girgiza kai Hanan tayi,tana kallon jannat ɗin.
"Kizo mu shiga ɗakin nan muyiwa shegiya dukan tsiya, ta yadda tana tashi zatace barin gidan zatayi,kinga mun kawo ƙarshen tsafin nata"jannat ta fada tana wani girgiza jiki.
"Nifa anty jannat wllh tsoro nake ji,ba ruwana sai dai ke ki dake ta,amma Ni ba ruwana"jannat ta fada cike da tsoro tana gwabe fuska.

Hararar ta jannat tayi, kafin tace "banza ƴar kut........uba, matsoraciya kawai,Ni bari ki ga abinda zanyiwa shegiya"tana faɗin haka ta kunna kanta cikin dakin,har bakin gadon taje ta tsaya akan Islam dake kwance.
Ahankali Hanan ta shigo cikin daki,ta tsaya daga can jikin ƙofar bayan ta kulle.

Wayar caji jannat ta ciro tare da dagawa da nufin zabgawa Islam,sai dai duk yadda tayi ƙoƙarin sauƙe hannun fir yaƙi sauka,cikin razana da tsoro ta daga kai tana kallon hannun nata dake tsaye kamar sanda,kawai ba zato ba tsammani,taga hannun nata ya fara zabga mata wayar cajin nan ajikinta.

Ihu ta fara cikin razana da azaba,tana faɗin dukan kanta"wayyo Allah, na shiga ukuna,wayyo mommy kizo ki taimakeni, Hanan zoki taimakeni,wayyo bayana"abinda jannat ke faɗi kenan tana ihu,dan sosai dukan ke ratsa mata jiki.

Hanan kuwa tana tsaye bakin ƙofa,amma ita a idonta ba abinda take gani,face yayarta tsaye bakin gado tana kallon Islam,sam bata jin wannan ihun da Neman taimakon da jannat keyi.


Duka sosai jannat ta sha, kafin aka warɓar mata da hannun ya bugi, gefen gado.
Ihu ta sake kwallawa cikin azaba ta nufi bakin ƙofa tana kuka.ai da gudu ta buɗe kofar dakin ta fice.
Kallo Hanan ta bita dashi kafin itama tayi saurin ficewa daga ɗakin.
Suna fita Islam ta buɗe idonta,tare da sakin murmushi.
Tashi tayi ta zauna akan gadon tace "gobe ma ki ƙara tunanin zaki doke ni ki gani,da sannu duk saima gyara muku zama,har wancan basamuden yayan naku, marasa tarbiyyar kawai.
Tana gama faɗin haka ta tashi ta nufi toilet.

Jannat kuwa dakinta ta shiga da gudu ta buya alungun gado,kuka take sosai tana sosa jikin ta,wanda yayi burɗi -burɗi tsabar duka.
Hanan ce ta ƙaraso kusa da ita tana faɗin"anty jannat lafiya kike kuka?me kuma ya faru?naga lafiya kika fito daga ɗakina ?
Ta fada tana kallon jikin Hanan da yayi ruɗu-ruɗu da sawun bulala.
"Ubanki ne ya faru,shegiya muguwa,lokacin da nake cewa ki kawomin ɗauki inace tsayawa kikayi kina min dariya?wllh gaba ɗaya saina ci kan ubanku keda matsafiyar can,ficemin daga ɗaki"jannat ta fada cikin tsawa tana zarewa Hanan ido.
Da sauri Hanan ta bar ɗakin tana mamakin me yasa mu yayar ta ta haka?gaba ɗaya jikinta yayi burɗi-burɗin duka.

Aslam kuwa yana shiga ɗakinsa,wanda yake gyare tsaf,dan kullum sai an gyara masa dakin,ko yana nan ko baya nan,kuma masu aiki basa shiga dakinsa,dan shi mutum ne mai tsantsani, sai dai mommy ko jannat.
Kayan jikinsa ya cire daga shi sai single da boxer ya shiga toilet ɗin.
Cire boxer da single yayi kafin ya tsaya jikin shaya,tare da sakawarwa kansa ruwa.
Ba abinda idonsa ke hasko masa,sai fuskar Islam,da irin rashin kunyar data shuka masa,wani baƙin cikin ne ya turnuke masa zuciya sai huci yake yana dukan bango,wai wa ce ce wannan yarinyar? Me take taƙama dashi?
Runtse ido yayi da ƙarfi yana sauƙe ajiyar zuciya, kawai yaji hannu ta bayansa ana goga masa soso,da sauri ya buɗe idonsa,yana kallon toilet din,Amma ba kowa,hakan yasa shi,ƙara rufe idonsa, saidai kuma da sauri ya sake buɗe idonsa,jin kamar ruwan wanka ya sauya yanayin da ya fara wanka dashi,aikuwa yana bude idan sa,yaga cewar,jini ne ke sauka daga jikin shayar,wato da jinin yake wanka,
Cikin hanzari da zafin nama ya ja baya yana kallon shayar cike da mamaki, jini ya gani yana ta zuba daga jikin shayar,da sauri ya maida kallonsa jikinsa,nan ma jinin ya gani duk ya bata masa jiki.
Runtse ido yayi gabansa na mugun faɗuwa,kusan minti biyu kafin ya buɗe idon nasa,kallon shayar yayi,sai kuma yaga ruwa ne normal yake sauƙa,da sauri ya kai kallonsa jikinsa,nan ma ba jinin sai ruwa dake ɗiga ajikinsa.ajiyar zuciya ya sauƙe,yana kallon ko ina na toilet ɗin, kafin ya koma jikin shayar, wankan kan sa ya karasa kafin ya janyo towel ya daura tare da yin alwala,sannan ya fito.
Sai dai yana ta mamakin abinda idanunsa suka gane masa yanzu a toilet ɗin,to ko dai idonsa ke masa gizo?amma tabbas jini ya gani mai makon ruwa, yana zaune bakin gadonsa yanashafa mai, kamar wanda akace ya ɗago kansa, kawai kalli madubi,hoton mace ya gani zaune abayansa,ta jingina da jikin gadon, da sauri ya mike tsaye yana mai duba bayansa,amma baiga kowa ba,shiru yayi yana tunani cikin zuciyarsa,wai meke faruwa da shine? Kodai yayi gamo ne?amma koma dai mene ne Allah yafi karfinsa.
Wayar mommy ce ta katse masa tunaninsa,dauka yayi tare da karawa akunnensa,
Mommy ce ka sanar dashi ya fito suci abinci,to kawai yace kafin ya kashe wayar yayi waje.

Duk suna zaune akan danning table,gaba dayansu,shi kadai suke jira,jannat na zaune ta kafe Islam da ido cike da tsana da tunanin ɗaukar fansa, ita kuwa Islam,wacce ke zaune itama kusa da granny fuskarta Sam ba alamun wasa,ta haɗe rai sosai kamar bata taɓa dariya ba,Hanan ma tana zaune kusa da jannat tayi tsumu,gaba ɗaya atsorace take.
Ƙamshin turaren Aslam be ya saida musu zuwansa, dan shi idan yazo guri,to turaren sa ke fara muku sallama kafin shi.
Yana zuwa yace "hi Mom barka da dare"ya fada yana mata side hug kafin ya zaune akan kujera.
"Barka Aslam ka fito? dama kai muke jira tun dazu"

"Ohhh Ni jikar dubure,idon da ranka kasha kallo,wai wannan gardin ke wani ƙwaƙumar uwarsa yana faɗin haye mam,gaba daya ka dauko al'adar yahudawa.wannan bakar tijara har ina"granny ta fada tana kama kumatu.
Banza Aslam yayi da ita, sai harara daya watsa mata,ya fara cin abincinsa da aka zuba masa,sam hankalinsa bai kai kan Islam ba,baisan da ita agurin ba.

Sai tsinkayo maganar ta da yayi tana faɗin"ke malama wai meye kika ƙura min ido kamar wata mayya?ko naci bashin kine? Nifa bana son kallo arayuwata,wllh idan baki daina kallona ba saina ƙwaƙule miki ido"Islam ta fada tana zazzarewa jannat ido.da sauri Aslam ya ɗago kai ,
Baki buɗe ya ke kallon Islam,wai wannan wa ce ce ne?me ye alaƙarta da gidansu?meyasa takewa kowa hawan ƙawara ne?me ta taka?
Cikin ɓacin rai da jin haushi jannat tace "an kalleki dan uwarki,kiyi abinda zakiyi, shegiya gaki nan babbar mayya, ido kamar kwaruru, wllh saina rama abinda kikayi min, duk iya tsafin ki ,sai dai kiyi ki barni,banza ƴar tsintuwa yar bola,wayasani ma ko ke ɗin shegiya ce kizo mana gida zaki.....
Tasss! Tasss!!kake jin saukar maruka akan kumatun jannat,ihu jannat ta kwala tare da dafe kumatunta
"Wayyo mommy na shiga uku,ta ciremin haƙora"jannat ta fada cikin kuka tana rike da kumatun ta ga gefen bakinta yana zubda jini.
"Wllh idan kika sake zagina ,saina miki wanda yafi wannan,dan Ni bana tsoron kowa, ki tambayi babanku kiji,da gyar suka lallabani na biyosu,dan haka baku isa ku wulaƙanta Ni ba,dan niba baiwarku bace, kuma Ni ba wulaƙantacciya bace, kuma ba ruwana da girman jikin mutum wllh saina rama abinda akayi min,dan Ni rainon dawa ce bana ɗaukar raini"Islam ta fada cikin huci tana hura hanci.

Mamaki,al'ajabi gaba ɗaya sun rufe Aslam,yama kasa cewa komai,kawai kallon Islam yake cike da madarar mamaki,
Granny kuwa dariya ta sanya harda tafi tace "ahayye wallahi isilama kinyi min dai dai,wannan ja'irar yarinyar dama ba abinda ta iya sai rashin kunya, bata ganin kowa da gashi,na baki dama duk wanda ya taka ki,ki takashi,wllh karki rage masa ehe"ta kai zancen ta tana sanya lomar tuwon shinkafa abakinta.
Shiru mommy tayi kawai tana kallon Islam,abinda ta lura dashi,Islam yar rigima ce, bata yarda ayi mata ba dai-dai,kuma yanzu dai kam,jannat ce bata da gaskiya,dan haka cikin murya mai taushi,mommy tace "kinga Islam yi haƙuri zauna kici abincin ki,ke kuma jannat bana son irin wanann halin naki, mutum ba abin wulaƙantawa bane"mommy ta fada cikin muryar gargaɗi. Kallon mommy Jannat tayi cike da mamaki,tace "mommy kina gani fa marina tayi, kuma agidan ubana,Ni sa'arta ce"
"Na gani masu uba,ai uban naki shine ya kawo ta,dan haka bana son fitina"mommy ta fada cikin haɗe rai.duk da har cikin zuciyarta,taji zafin marin da Islam tayiwa Jannat ɗin,amma bata son ta zamo marar adalci.
Da gudu jannat ta bar gurin tana kuka tayi dakinta.
Kallon mommy Aslam yayi cike da mamaki yace "mommy wannan shine hukuncin da zakiyi kawai?kina kallo wannan jakar yar ƙauyen ta zabgawa jannat mari,Wanda ahaife nasan jannat ta fita,amma rarrashinta ma ki ke yi mom ?
Meke faruwa ne mom,wa ce ce wannan yarinyar agareku,?meye matsayinta agidan nan?WHO the hell is she"?ya fada cikin matsanancin ɓacin rai, yana ture flate ɗin abincin dake gabansa,tare da mikewa tsaye .
"Ni zan faɗa maka ko Ni wa ce ce da kaina" Islam ta fada tana matsowa kusa da Aslam cikin yanayi na nuna rashin tsoro ta tsaya agabansa tana kallon cikin idonsa.....

To fa
Muje zuwa masu karatu,mun kusa gama free page, mai bukata yayi payment kafin mu Dora da paid page.

Mrs babi ce 💘💘

Share as much as you can.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



🎄🎄 RAINON DAWA🎄🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚


Free page

19/20



GAMASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN ZAKU BIYA KAMAR HAKA.


NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR ASATI.


SPECIAL GROUP 500#
UPDATE BAKWAI ASATI.

SAI KUMA MANYAN MATA MASU BUƘATAR ATURA MUSU TA PRIVATE
ZA KU BIYA 1000₦

DUK ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN.

SARATU KABIR
U.B.A
2215749011

SAI KUN ZO.




______________Cikin zafin nama da ɓacin rai,Aslam ya tunkaro Islam,yana zuwa kusa da ita ya fizgota zuwa jikinsa,baiyi wata- wata ba,ya fara ƙoƙarin cire mata riga.

Mamaki,tsoro da al'ajabine suka kama Islam,me kuma yake ƙoƙarin aikata mata haka?me zaiyi da rigarta da yake ƙoƙarin cire mata?cikin nata salon zafin naman ta damke hannunsa,tana mai kallon idonsa,wanda shima ya kafe nashi idon cikin nata,
"Me kake ƙoƙarin aikatawa ne?meye nufin ka na cire min riga?ko dai bansani ba cewar da kuɗin ka aka haɗa aka siyi rigar?"ta faɗa cikin zazzaro manyan idanunta.
Babban ɗan yatsan sa, ya sanya tare da dalle mata lips cikin salon mugunta,harda cije lips ɗin sa.
Runtse ido Islam tayi sakamakon raɗadin azaba daya ziyarci kwakwalwarta.
Buɗe ido tayi ta kafesa da su,cikin tsantsar haushi da tsanarsa tace "Allah ya isa na,bazan taɓa yafe maka ba,mugu azzalumi, baƙi mai baƙar aniya,wllh zaka san Ni kayiwa wannan abun"Islam ta fada cikin zafin zuciya da jin raɗaɗin da lips ɗin ta keyi.
Shikuwa cikin salon mugunta ya kara sanya hannun sa ya matse mata baki sosai yana huci.
Ubanwa kike wa Allah ya isa?Ni sa'anki ne?wllh idan kika ƙara min rashin kunya zakiga abinda zanyi miki,shegiya mai idon mujiya"Aslam ya faɗa yana mai kara matse bakin Islam kafin ya murde lips ɗin ta da ƙarfi,sannan ya saki.
Da sauri Islam ta rike bakinta tana sauke ajiyar zuciya,dan shafo lips ɗin ta tayi,cike da mamaki take kallon jinin data gogo daga lips ɗin ta.
Kallon sa tayi,kallo irin na tsana da kiyayya,tace "ka sani wllh wannan jinin daya fita daga jikina bai fita abanza ba,kuma wllh sai kaga Abinda zanyi maka akan hakan,banza ɗan iska kawai,Ni ka sakar min riga in fice wawa"ta fada cikin mugun ɓacin rai tana ƙoƙarin cire hannunsa daga kan rigarta,wanda ya damke rigar gan dasu.

Kallonta yake,yana jinjina zallar rashin kunya da tsoro irin na wannan aljanar, anya kuwa wannan kanta ɗaya?kodai aljanu gare ta,ko iya kawo ta dakin nan da yayi,ya ci ace ta tsorata ,amma sai kara kaimin rashin kunya take,dole ya koya mata hankali.dan haka karfinsa ya saki tare da matse bakin nata ya buɗe shi,sannan ya tofa mata yawu acikin bakinta. Kuma yayi saurin matse hancin ta,bayan ya haɗata da jikin bango Ya matseta, ji kake ƙut!ta haɗiye yawun daya tofa mata abakin ta.zaro ido tayi cikin mugun tashin hankali tana kallonsa,shikuwa saida ya tabbatar ta haɗiye yawun sannan ya saki hancin nata.
Wani irin kuka Islam ta sanya cike da ɓacin rai,ta cakumo shi da iya ƙarfi ta,ta fara kai masa duka ta ko ina,tana faɗin"Allah ya isana mugu azzalumi,ƙazami wllh yadda kasa na sha yawun wannan ƙazamin bakin naka,wllh saikayi nadama,banza bunsuro kawai ɗan iska mai....
Bata sami damar karasawa ba, sakamakon jin bakin Aslam da tayi cikin nata.ƙamewa tayi agurin cikin ruɗu da mafificin tashin hankali.

Shikuwa cike da mugunta yake tsotsar lips ɗin ta yana cizon ta,tare da dura mata yawun bakinsa,
Ƙut-ƙut, haka take haɗiye yawun cikin rashin sanin abinyi.

Shikuwa Aslam da yayi nufin yi mata mugunta,sai yake neman rasa nutsuwarsa ,gaba ɗaya yaji yana ƙoƙarin shiga wani yanayi,hankalin sa gaba ɗaya ya tashi,sosai yake jin daɗin kissing ƙaramin bakin Islam,wanda har ya shagala.ba tare da yayi aune ba kawai yaji an damƙi wuyansa ta baya,da mugun ƙarfi,kamar za'a karya masa wuyan, nan take hankalin sa ya dawo jikin sa, sannan ya fahimci abinda yake aika tawa, da hanzari ya zare bakinsa daga cikin na Islam,wacce zuwa wannan lokacin gaba ɗaya jikinta banda rawa ba abinda yake,idanunta sunyi jajur dasu abin tsoro.
Da sauri Aslam ya ture ta daga kusa dashi,yana jin wata irin juwa na ɗiban sa,ahankali,idanunsa ke rufewa da budewa, wani tsalle Islam tayi tare da cafko maƙogaran Aslam,Wanda ya fara fita daga hayyacinsa.saida taga yana neman sheƙawa sanan tayi cilli dashi can gefe guda ya fadi tare da buga kansa jikin bango,nan take idanunsa suka rufe ruff! alamun ya suma.can gefe itama ta fadi tare da runtse idanunta,banda azaba ba abinda lips ɗin ta keyi,gashi ya fashe daga gefe, ya kumbura sosai.
Yunkurawa tayi cike da kasala ta nufi bakin ƙofar,tana budewa mai makon ta koma cikin gidan kai tsaye ta nufi garden,kallo ɗaya zaka mata kasan bata cikin hayyacinta.

Tana zuwa cikin lambun, ta kama wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ta haye samanta tare da kwantawa jikin wani reshe.
Runtse ido tayi cikin zafin zuciya da takaici,tunda take ba wani mahalukin daya taɓa mata irin abinda Aslam Yayi mata,wllh ta tsane shi,bata ƙaunar ganinsa,kuma saita rama abinda yayi mata.hawayene ke zuba cikin idonta ba tare da ƙaƙƙautawa ba,shine mutum na farko,daya sata zubda hawaye tun tashin ta ,kuma zaiyi dana sanin yin hakan.
Iskace ta fara kaɗawa mai sanyi,tare da wani haske daya mamaye kan bishiyar,hakan shiya tabbatar mata zuwan Malami ta.
Cikin ƴan daƙiƙu kuwa saiga malamin nata ya bayyana, murmushi ɗauke akan kamilalliyar fuskarsa.
Kallonsa take cikin kuka tana jiran taji me zaice.
Ahankali ya sanya wani farin gyalle ya share mata hawayen,kafin ya fara magana"ki daina kuka Islam, kiyi haƙuri da duk wani halin da zaki tsinci kanki agidan nan,domin ƙaddarar ki tana ɗanfare ne da wannan gidan, anan zaki sami farin ciki,bayan haka game da Aslam kece wacce zata sanya shi ya daidaita rayuwarsa,kece zaki bawa rayuwar sa tallafi,komai zai dai-dai, kici gaba da ƙoƙarin faɗin gaskiya komai ɗacin ta,ki shiga rayuwar Aslam sosai,ta hakan ne zaki sami damar gyara masa duniyar sa,ki kwanta kiyi barci babu damuwa cikin ranki,ina tare dake"yana gama faɗin haka ya sanya hannunsa tare da shafar idanun Islam ,cikin abinda ba zai gaza daƙiƙa biyar ba ,Islam ta lumshe ido, nan da nan barci yayi gaba da ita.


Washe gari da asubar fari,Aslam ya farka daga suman da yayi,ahankali ya buɗe idanunsa da sukayi masa nauyi,kanshi ya dafe tare da lumshe ido,sakamakon ji da yayi kan nashi na rasa masa.
Ɗakin yabi da kallo,na dan lokaci,nan take duk abinda ya faru jiya ya fara dawo masa cikin kwakwalwar sa tirya-tiryan.
Ohh shet!!me na aikata haka ne?me ya ruɗeni harna nayi kissing waccan ƙazamar? yanzu wane kallo zata rinƙa min,shikenan sabon raini zai shiga tsakani na da ita,amma bazan taɓa bari ta raina Ni ba,ko yanzu tayi min abinda bai min dai-dai ba,saina hukunta ta wllh.tashi yayi cikin jin ciwon jiki,sannna wuyansa na ɗan masa ciwo,barin dakin yayi ya nufi ɗakin sa. Wanka ya farayi kafin yayi Sallah,da kanshi ya tattare abubuwan daya fasa jiya,sannan ya sanya kayan motsa jiki ya nufi can garden.

Islam kuwa koda tayi sallah,kan bishiyar ta sake hayewa tayi zamanta,bayan ta ciri mangoro tana sha.ba abinda take kitsawa,sai irin tijarar da zatayiwa Aslam,tana nan zaune ta hango shi ya nufi gurin da gudunsa yana motsa jiki.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta,har da sauke ajiyar zuciya.kallon janbu tayi wanda ke kwance kan ruwan cikinta,tace "janbu so nake mu koyawa wancan wawan hankali, lallai karmu barshi har sai munga jini ya fita ajikin sa"ta fada tana kafe Aslam da ido,tana tuno yadda ya dure mata yawun bakinsa a cikinta ta shanye tass.

Shikuwa Aslam zuciyar sa daya,yake motsa jikinsa,bayan ya ajiye gorar ruwa da towel ɗinsa ,kusan minti goma sha biyar,sannan yayo jikin bishiyar da Islam ke kai,zama yayi kan wani dutse da akayi masa siffar kujera,da alama,an ajiye shine dan hutawa.towel ɗin ya ɗauka yana goge zufar data jiƙa masa jiki.
Ƙwal! Yaji saukar kwallon mangoro akansa.da sauri ya saki towel ɗin yana dafe kansa,dan sosai kwallon mangoron nan ya daki ƙeyarsa.dama gurin yana masa ciwo.
Daga kansa yayi yana kallon bishiyar,amma baiga komai ba,dan tana da duhu.gashi kuma da alama ba'a jima da shan mangoron ba.komawa yayi ya zauna,tare da ɗaukar gorar ruwan ya buɗe yana sha.saitin gorar Islam ta saito wani ƙaton mangoro ta jefo masa.ai nan take ruwan cikin gorar ya fito da yawan gaske,sai hancin Aslam,gorar kuma ta faɗi,nan da nan ya ƙware, tari ya fara kamar zai mutu,idonsa ya firfito yayi jajur dashi,durƙushewa yayi agurin yana tari sosai.haba aikuwa nan Islam tayi ta jifansa da mangoro,timm!!timmmm!!!,gaba ɗaya Aslam ya gigice ga tari ga jifa,ya rasa inda zai sanya kansa,ya tashi ma ya bar gurin ya kasa.
Cike da murmushin mugunta, Islam tace janbu hau kansa kayi ta yakushin dan banza,sai ka ga jini ajikinsa sannan zaka gyale shi.
Aikuwa da gudu janbu ya sauko,bai dire ko inaba sai kan kafadar Aslam,nan yayi ta yakushin sa ajikinsa da fuskar sa.
Iyakar ruɗewa Aslam ya ruɗe,sai ƙoƙarin korar birin yake daga jikinsa ya kasa hashi dama yana tsoron biri.janbu kuwa saida ya kai Aslam ƙasa,kuma yaga jini ajikinsa sosai kafin ya sauƙa daga jikin nashi,ya koma kan bishiyar da gudu.
Dariya sosai Islam keyi,abun yayi mata daɗi sosai,farin ciki fall zuciyarta,take kallon Aslam,wanda ke sauƙe numfashi,da gyar,yana kwance.
Kusan minti biyar ya kwashe kafin ya yunƙura da gyar ya tashi ya nufi gida,gaba ɗaya jikinsa ya kushin birin nan ne.
Saukowa Islam tayi daga kan bishiyar tana dariya"kayi aiki mai kyau janbu haka nake so,kuma wllh ban gama ramawa ba, zai gane kurensa"ta faɗa tana murmushi,kafin tace "janbu maza je kaci ayaba son ranka,dan kuwa tunda suka kawo mu gidan nan,bazamu zauna da yunwa ba, duk abinda ranmu ke so shi zamu ci"da gudu janbu yayi kan bishiyar ayaba,ita kuwa ta nufi cikin gidan.

Kai tsaye Aslam,ɗakinsa ya nufa,gaba ɗaya jikinsa ciwo yake,wani zazzaɓi ne ma ke ƙoƙarin rufeshi,tunani yake,wannan birin daga ina yake?waye ya kawo shi cikin gidan?ai kuwa Dole afitar dashi yau -yau ɗin nan.kwanciya yayi akan gado tare da lulluɓe jikin sa da bargo,dan kuwa tuni zazzaɓi yayi masa dirar mikiya.

Islam kuwa tana shigowa cikin gidan ta wuce ɗakin granny,lokacin granny tana lazimi,taga shigowar ta ko ina ta shiga tun dazu oho? granny ta faɗa cikin zuciyar ta,kafin taci gaba da lazimin ta . Islam kuwa kwanciya tayi akan gadon granny,ba jimawa barci yayi gaba da ita.

Misalin ƙarfe tara na safe, gaba ɗaya ahalin gidan suka hallara akan daining dan karyawa, kowa ya shirya,da sun kammala karin zasu wuce asibiti,dan akwai yiwuwar su taho da Aman gida,tunda ba ɗorin asibiti akayi masa ba.
Mommy ce tace jannat taje ta kira yayan su,koda taje akwance ta sameshi ya lulluɓe jikin sa.
Dan haka ta dawo ta sanar da mommy.
Da kanta mommy taje ɗakin nashi,ta ganshi kwance jikinsa zafi sosai.
Tambayar sa tayi me ya sameshi yace zazzabi ne ke samunsa,ganin baida lafiya ya sanya ta barshi,amma tace ya sha magani kuma yaci abinci, sannan ta fice,dan tasan jinya bata hana Aslam cin abinci.

Koda ta nemi akira Islam,granny ce tace ,a'a barci take abarta ta huta idan ta tashi taci.

Haka suka gama cin abincin su suka bar gidan,ya rage daga Aslam sai Islam cikin gidan.

Jikin Daddy da sauki sosai dan sosai suka sha hira da ahalin sa,nan yake tambayar ina Islam da Aslam? aka ce masa barci take,Aslam kuma baya jin daɗi.nan suka ci gaba da jajanta abinda ya faru,abokai da yan uwa sai zuwa suke duba su Daddy,asibitin acike da mutane yan dubiya,abinka da mutum mai mutane.

Sai kusan sha ɗaya zazzabin ya saki Aslam,Dan haka tashi yayi tare da yin wanka,ya shafa maganin radadi ajikinsa,gefen idon sa har ya kumbura.shiryawa yayi tsaf, cikin riga da wando na farin yaɗi mai kyau da tsada,yayi kyau abin sa.
Kai tsaye danning ya nufa ya haɗa tea yana sha.
Islam kuwa tana tashi itama wanka tayi,abin mamaki komai ta iya amfani dashi,bata tambayar komai,haka zaka ga tayi abinta kai tsaye,ko ina ta koyi amfani da irin waɗan nan abubuwan oho?

Bayan tayi wanka kuma saita rasa wane kayan zata sanya,dan haka fitowa tayi ta nufi ɗakin Hanan dake sama,daga ita sai wani Dan towel Wanda bai karasa gwuiwar ta ba,tafiya take cikin takunta mai jan hankali,da sanya jaruman maza risinawa.
Aslam ya kurbi shayi kenan,idonsa ya sauƙa akan ƙugun Islam,wani irin tarine ya taso masa,ba shiri ya watsar da tea ɗin bakinsa,yana ɗan bubbuga ƙirjinsa.
Binta yayi da kallo kamar wani sakarai,masha Allah lallai Allah yayi kira agurin nan,kalli yadda take juya hips ɗin ta cikin salo na jan hankali,abinka da dan hannu, nan da nan Aslam yaji yanayi sa ya sauya,sosai jikinsa ya fara nuna alamun bukatar mace,yana nan zaune galau,harta shige dakin Hanan.
Sam ya kasa cin abincin,surarta kawai idonsa ke haskowa,tsaki yayi yana mai jin haushin kansa,ya rasa wacce zai wani zauna yana tunanin surar ta sai wannan Shegiyar yarinyar mai kama da aljana,shifa yana zargin ma anya ba da gan-gan take wannan abun ba?dan kawai ta ja ra'ayinsa?aikuwa wllh tayi kaɗan,batakai matsayin da zata ja hankalinsa ba.

Kusan minti biyar saiga Islam ta fito riƙe da wasu riga da wando ahannunta.har ta sauko ta nufi ɗakin granny, idonta bai nuna mata Aslam ba ,Wanda ya ƙara Binta da kallo kalauuu!!

Saida ta

Please Login or Register in order to submit comment