Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aman ɗin yake ba.daga zaune yake jan jiki yana neman Aman, kawai sai ganin mutanen nan yayi tsaitsaye akansa,kusan su bakwai,ko wanne riƙe da bindiga ahannunsa.kuma fuskokinsu arufe ruf da baƙin kyalle.
Cikin tashin hankali da azabar ciwukan da Daddy yaji yake faɗin "dan Allah kuyi hakuri,kuyimin rai,me nayi muku?me kuke bukata wajensa?"

Dariya babban cikinsu yayi kafin yace "baka da bukatar sanin komu su waye,domin sanin bazai amfanar da kai komai ba,dan kuwa mutuwa zakayi,zamu kasheka ne,sannan mu ɗauki abinda muka biyo ka danshi,wannan shine aikinmu"yana faɗin haka ya saita cikin Daddy ya sakar masa bullet,Kara Daddy yayi kafin ya koma ya kwanta idanunsa suna rufewa da budewa,har suka rufe ruf.
Ganin haka wadandan mutanen suka nufi inda motar Daddy take kwatsa-kwatsa,suka fara dube -dube.saidai sunyi iyakar dubansu amma basu ga abinda suke nema ba. Cikin fushi babban ya dauko waya ya kira wata number"oga babu wannan takardun da kace mana acikin motar nan fa"ya faɗa cikin salon murya irin ta yan daba.
Bansan me akace masa daga ɗayan bangaren ba, naji yace "mun duba ko ina,babu sannan dan nasama bamu ganshi cikin motar ba, kuma gaskiya kasan wannan dajin yana da hadari,kawai ,zamu fito"yana faɗin haka ya kashe wayar tare da umartar yaransa su bar gurin.

Lokacin da suka sakarwa Daddy bindiga,dai-dai lokacin yarinyar ta farka daga barcin da take,zabura tayi cikin sauri ta sauƙo daga saman dakin nata.bayan ta rataya kwarinta da baka.cikin gudu take takowa zuwa inda tajiyo sautin bindigar nan.
Tafiya mai dan nisa kadan tayi kafin ta ƙaraso gurin da taji karan bindigar,mota tagani jikin bishiya tayi raga-raga,alamun hadari akayi agurin. Da sauri ta karasa tana duba-dube.aikuwa kwance ta ga Daddy cikin jini,dan haka cikin hanzari ta durƙusa tare da kara kunnenta sautin zuciyarsa,"da ransa "ta fada cikin hanzari tana dagowa. Gaba daya jini ya bata farraren kayan dake jikin Daddy,sannan gefen cikinsa ga alamar harbi nan,juyawa ta farayi tana kalle -kalle.dan kuwa ta tabbata bayan hadarin ma akwai mugayen da suka biyo bawan Allahn.

Cikin jarumta ta kama Daddy,da gyar ta miƙar dashi tsaye,hannunsa ta lankaya afadarta,ta fara tafiya dashi,duk da batafiyar yake iyayi ba,jansa kawai take, sunyi faduwa tafi nawa kafin ta kaishi bakin dakin nata,jikin bishiyar,ta kwantar da Daddy,kafin ta fara bashi taimakon gaggawa.abin mamaki,yarinyar nan yadda kukasanwata likita,haka tayi amfani da wukarta ta cirewa Daddy wannan harsashin daga jikinsa.ta daure gurin,sannan ta mike ta tattaro ganyayyaki,sukayi tudu,taja Daddy ta dorashi akai.sannan ta koma gefe tare da riƙe kugu tana kallon Daddy,sai uban nishi take gaba ɗaya ta haɗa zufa, tunani take wannan bawan Allah daga ina yake?kuma su waye suka harbeshi?me yayi musu?bata da amsar wannan tambayar,kuma gashi duk da ta ɗaurewa Daddy gurinn da aka harbeshi,amma jini zuba yake,akwai bukatar ta sanya masa magani,dan haka saitaje ta nemo ganyen dazai tsayar masa da jinin.
Juyawa tayi ta koma cikin dajin da sauri,dan harhado ganyayyakin dazata sanyawa Daddy agurin ciwon.
Cikin hanzari ta debi ganyayyakin da take buƙatar yin amfani dasu,sannan ta kamo hanya.tana cikin tafiya tazo saitin gurin nan,cikin sarkakiyar da Aman ya faɗa ta fara jiyo nishi kamar na mutum,dan dakatawa tayi tana kasa kunne,kafin ta zaro kwarinta da baka tayi ready,sannan ta fara takawa ahankali,har zuwa gurin,kwance ta iske Aman cikin jini,yana fidda numfashi da kyar,cikin hanzari ta maida kwarinta da baka sannan ta nufi inda yake kwance,dagoshi tayi da sauri tana jijjigashi.
ahankali Aman ya bude idonsa da suka mugun kumbura ya sauke akan fuskar yarinyar,cikin sarkewar murya yace "D..aaddy na...ki...Taim..akeshi"yana faɗin haka jikinsa ya saki yana ƙoƙarin sake sumewa,miƙar dashi ta fara kokarinyi ,saidai kuma sam ta kasa,saima fahimta da tayi kamar ya karye akafarsa.
Dan haka cike da dubara ta samo manyan ganyen bishiya ta dauresu akugun Aman,sannan ta sanya wata doguwar igiyar ta fara jansa har zuwa inda ta bar Daddy kwance.
Tana ajiyeshi itama ta zube agurin tana maida numfashi,dan tayi mugun gajiya gaba ɗaya jikinta yayi tsami.

Da gyar ta iya tashi zaune ta koma kusa da Daddy, da bakinta ta tauna ganyayyekin nan,sannan ta manna masa agurin da aka harbeshi,tsabar azaba saida Daddy yayi ƙara duk da yana cikin hali na suma.tashi tayi da ƙoƙarin hawa dakinta dan dauko abinda zata gyara musu ciwukan,amma saboda yadda ta gaji nan gurin ta zube itama tana nishi da gyar.
Ahankali sanyi ya fara ratsa kasusuwanta gurin yayi wani haske sosai har saida ta lumshe idonta,daga nan bata kara sanin inda kanta yake ba.

Hasken. Kuwa yana gama haduwa guri ɗaya, saiga wannan kyakykyawan matashin ya bayyana,cikin lokaci kankani yayi kansu Daddy, shafawa su Daddy magani yayi Aduk gurin da suka ji ciwon,sannan ya gyarawa Aman ƙafarsa inda ya karye.
Gurin yarinyar ya koma ya bude bakinta ya tsiyaya mata wani ruwa cikin kwalba mai kama da ta zinare,kafin ya dan bubbuga kumatunta yace"ISLAM"cikin wani sauti mai matukar amo da dadin sauraro,
Ahankali ta fara bude idonta tana kallon,saurayin daya kira sunan nata, saidai hasken dake gurin ya hanata ganin fuskar tasa,tunda take bata taɓa ganin,fuskarsa ba kullum cikin yanayin haske take iya ganinsa.
Murmushi yake mata kafin ya bace.da sauri ta tashi zaune,babu alamun gajiya ko ciwon jiki atattare da ita.
Kallonta takai inda su Daddy ke kwance,kamar yadda tayi tsammani ganinsu, a hakan ta gansu kuwa.

Murmushi tayi tana kallonsu,kafin ta nufi gurin koramar nan ta dauro alwala,tana mikewa janbu yazo ta gabanta yana tsalle tare da dan ƙara,murmushi tayi tare da shafa kansa tace"janbu yau na samo wasu bayin Allah cikin mawuyacin hali,yanzu haka suna nan kwance agida,kasan menene,malamina ne yayi musu magani,ahalin yanzu ba wata damuwa,saidai mujira su farfaɗo"ta fada tana murmushi tare da nufar gidan nata,kamar yadda take fadi.

Kai tsaye ta kama bishiyar ta hayetare da lulluɓa mayafinta ta fara sallarta ....


Muje zuwa sannu kan hankali masu karatu.

Mrs babi ce 💘💘

Share and comment as much as you can fisabilillah.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free page

5/6


Ga masu son biyan kudin wannan littafin,zaku biya kamar haka.

Normal group 300₦
Update biyar asati.

Special group 500₦
Update bakwai,asati.

Manyan mata masu son shi ta pc 1000₦

Zaku tura ta wannan acc.ɗin.
Saratu kabir
U.b.a
2215749011

Evidence of payment
08148360851.
Saina jiku.




______________"Bari naje na dauko ta yanzu,dan gidan baya daɗi,idan bata nan.Aman ya faɗa tare da miƙewa,cike da nishaɗi yayi waje.

Murmushi mommy tayi,dan tasan kiricin surukar Tata,idan tana guri,zaka sha dariya sosai.jannat ce ke saukowa daga matakalar benen, sanye take cikin wata riga mai yankakken hannu,wanda duka rigar Baza wuce gwuiwarta ba.kanta ko ɗan kwali babu,zama tayi kusa da mommy tana faɗin "mommy wai Ina granny?kodai bata nan ne?dan naji gidan shiru gwanin daɗi"ta faɗa tana lumshe ido.

Hararar ta mommy tayi kafin tace"yanzu jannat dan grannyn bata nan, shine kikaji gidan yayi miki daɗi Ko?to ki kwantar da hankalinki,yanzun nan zata dawo "ta faɗa tana ci gaba da hararar jannat.
Turo baki jannat tayi kafin tace"Ni wllh matar nan,takura Ni take agidan nan,yanzu zata fara kawo ma shirme kala-kala saikac...
"Jannat, bana son rashin kunya fa!granny kike fadawa wannan maganar?wllh ki kiyaye Ni"Mommy ta fa ɗa, cikin faɗa.

Shiru jannat tayi taci gaba da danna wayar ta. Tana turo baki,dan tasan halin Mommy yanzu saita ɓata mata rai,akan wannan tsohuwar.

Aman ne ya shigo cikin falon,yana dariya.guri ya samu ya zauna tare da kafe ƙofar shigowa falon da ido.

"Kai kuma lafiyar ka?ka shigo bako sallama kana dariya?ina grannyn take?kodai halin naka kayi mata?"Mommy ta fada tana kallon yadda Aman ke dariya.
Kafin yayi magana akan buɗe ƙofar falon,garamm!!!
Wata yar duma-dumar tsohuwa ce ta shigo cikin falon tana sababi"wllh Amanu akwai dan tijarar yaro, mutum sai ɓakar zuciya ta mugunta,yanzu daka rinƙa wujijjigani cikin wannan motar,so kayi ka kasheni, kai kuma ka zauna a duniyar kana ci gaba da jin daɗin ka ko?to wllh ta Allah ba takaba,dan bangama cin kaji da shan iyiskirin ba,kuma wllh zaka hadu dani"granny ke wannan maganar tana rike da kanta,dake juyawa.da sauri ta nemi guri ta zauna, dan Aman daya daukota amotar gudu yayi tayi da ita yana zagaye garin ,tsohuwace wacce zata kai kusan shekaru saba'in aduniya.saidai yanayin hutu da jin daɗi yasa tana nan garau da ita.taci adonta harda daurin dan kwali,ga wata uwar jaka saƙale ahannunta,da alama dai yar wankace.
Banda dariya ba abinda Aman keyi.cike da ƙoƙarin danne dariyarta Mommy tace "subhanallah granny me ya faru kuma?"

Cikin masifa granny tace "to ƴan sa ido,ina ruwanki?ko shishshigi?wllh bana son ana shiga tsakanina da Amanu,dan munfi kusa,bana son gulma"ta fada tana juyowa Mommy ƙeya.
Shiru Mommy tayi,dan tasan dama za'ayi hakan.duk irin tsiyar da Aman zaiyiwa granny,da kayi magana zata gwasale ka.

Jannat dai tana zaune bata ce komai ba,juyowa granny tayi ta kalleta cike da yatsina tace "to uwar mulki,bazakiyi min sannu da zuwa bama?saboda kin riƙa ko?"ta fada tana kallon jannat aɗage.

Harararta jannat tayi kafin ta miƙa tsaye tace "banda lokacin ki granny bazaki samin ciwon kai ba"tana faɗin haka tayi wucewarta zuwa ɗakinta.

"To tabbatacciya, ai idan bakiyi haka ba,ba za'ace miki marar mutunci ba,wllh idan kikayi wasa,zan zage mu dambatu dake agidan nan,dan ni da kikagani banyi ƙuruciyar tsoro ba,bare kice tsoronki nake ji, tass zan mutstsike miki wanna yan ƙirgan dangin da suke saki rashin mutunci" granny ta faɗa cike da masifa harda daure ƙugu da gyalen ta,alamun ta shiryawa danben.

Dariya sosai Aman keyi yana kallon dramar granny da jannat,sam dama basa shiri atsakaninsu.har Gara ma Hanan, da yake ita tana da ɗan tsoro.
Ganin granny ta zage sai masifa take,yasa Aman mikewa ta kamo hannunta yana cewa"haba matar,kiyi haƙuri mana,ki bar waccan blegger girl ɗin,karki biyeta ki ɓata wannan wankan naki,wllh baki ganki ba kamar wata minister"ya ƙarasa maganarsa cike da sigar kanbamawa.

Dariya granny tayi tana kai masa dundu"ja'irin yaro,ai In faɗa maka lokacin da nayi yan matanci na,karkaso kaga irin samarin dake sona,dan kuwa ɗan gidan marigayi Malam jafaru mai jaki, idan ya ganni,har faduwa yake dan kallona, saboda yadda nake cin ado.ba budurwar da takaini awancan lokacin, inada shekara sha daya,amma haka nake kamar sarauniyar kyau"ta kai ƙarshen zancen ta cike da nishadi tana kallon Aman.
Dariya Aman yayi yace "wai kice kinsha hawa kan jaki?lallai yan matan da kunfi na yanzu matsayi,harna haskoki akan jaki sarauniyar kyau"ya faɗa yana ƙara fashewa da dariya.

Ganin irin dariyar da Aman keyi harda ta rainin hankali ne,yasa granny tsuke fuska tare da ƙanƙance ido tace "kai Amanu bana son tashanci fa,meye na wannan dariyar kamar wani mahaukaci? Bayan kasan akwai yan sa ido agurin,wllh idan ka ƙular dani,yanzu zan zage kaima mu dambatu da kai,kasan ba tsoronka nakeba ehe"cewar granny tana buga hannu acinya.
Mommy dai na gefe tana ta ƙoƙarin danne dariyarta,dan gudun kartayi laifi,bakuma damar yin magana ,yanzu cibi yazama ƙari,dan haka tayi shiru abinta tana kallonsu,tare da yin dariya ƙasa ƙasa.
"Kinga granny taho mutafi dakinki,muyi hirarmu acan ai dani dake bata baci,kinga mun huta da masu son jin kwakwafɗin"Aman ya faɗa yana kamo hannunta,tare da kallon Mommy Yana dariya.

Girgiza kai kawai Mommy tayi,cikin dariya ganin yadda suka wani tafa da granny sannan suka wuce dakinta dake cikin falon.

Ba jimawa hanan ta fito,kwanciya tayi akan cinyar Mommy sukaci gaba da hira.


Ƙasar London,misalin ƙarfe hudu da rabi na yamma,
Wani kyakykyawan matashine kwance kan wani lafiyayyen gado,wanda yake da matukar girma,daga shi sai boxers ajikinsa, dogone sosai, yana da faffaɗan ƙirji, dan ga dukkan alama irin mutanen nan ne masu motsa jiki,duba da yadda jikin nashi yake amummurɗe.
Bakine amma ba irin can ɗin nan ba,fuskarsa mai cike da kwarjini da tarin haiba,yana da manyan idanu masu haske,da dogon hanci,bakinsa madaidaicine zagaye da gashin baki har zuwa gemunsa.lips dinsa jane mai duhu.atakaice zamu iya cewa kyakykyawa ne,mai kirar jaruman maza.
Gefensa kuma wata kyakykyawar baturiya ce kwance tana barci,ba komai ajikinta,sai bargon dake lulluɓe da rabin jikinta.tayi matashi da damtsen hannun saurayin.
Wayarsa ce tayi ƙara,hakan ya katse masa barcin daya fara daukarsa, bayan sun gama aikata alfasharsu,
Cike da yatsine fuska kamar wata mace ya daga wayar ya kara akunnensa ba tare da yayi magana ba.
"I will be there "kawai ya faɗa tare da kashe wayar.kallon yarinyar yayi dake barcinta hankali kwance, kafin ya zare hannunsa ya tashi zaune.wanka yaje yayi ya shirya cikin wasu riga da wando red and white, yayi kyau sosai cikin kayan.turare kawai ya fesa sannan yazo kan yarinyar yana kiran sunanta"Jennifer! Jennifer!!"ya kira sunanta da karfi fuskarsa ahade. Ahankali Jennifer tayi juyi tare da kallon Aslam dake tsaye yana muzurai.cikin barikanci tace "hi my man "tana ƙoƙarin tashi zaune.
"Maza ki tashi ki gyara min gida,kuma ki shirya yanzu kificemin daga gida ,zan fitane karna dawo na tarar dake" fa fi hakan cikin harshen turanci,yana faɗin haka ya jefa mata kudi masu yawa sannan yayi waje.

Binsa tayi da kallo cike da so da ƙauna,tana fatan Allah yasa watarana Aslam,yayi sex na gaskiya da ita,lallai data more,dan duk iya shegensa,baya yarda yayi sex da mace,saidai suyi romance ko wane irine,har su sami biyan bukata.duk yadda kikakai da nacinki kuwa,kuma bazai hada baki dake wajen yin kiss ba,saidai yayi miki akumatu ko goshi.wannan shine tsarinsa.rigarsa ta janyo ta rungume kafin tayi murmushi,ta koma ta kwanta.


Cikin dawa kuwa bayan yarinyar nan ta tashi daga barci,gurin ciwon ta, ta shafa taji gurin sumul ba alamun ciwo ko kaɗan,murmushi tayi tare da tashi ta kama bishiyar nan ta sauko.
Haka kawai taji tana son ta yawata cikin dajin,dan haka kai tsaye ta fara takawa cikin salon tafiyarta mai cike da jan hankali.
Tafiya take cike da rashin tsoro,tayi tafiya mai matukar nisa,kafin ta sami kan wani dutse ta zauna.
Zamanta keda wuya taji alamun tafiyar mutane,shiru tayi tare da kasa kunne,dan gurin da take zaunen yayi kusa da wani kauye,kuma bata cika zuwa ta wajen ba.
Sukuwa matasan nan yan farauta ne,su kusan hudu.suka shigo jejin dama sun saba zuwa,amma basu taba gigin shiga cikin dajin sosai ba.

Kafin tayi wani yunkuri kawai ta gansu tsaye agabanta.

Kallonsu tayi cike da rashin tsoro kafin itama ta mike tsaye.
Kallon juna matasan sukayi,tare da sakin murmushi,dayan yace "baba yaufa dawa tayi mai,kai ga wani kaya fa?lallai yau zamu huta"ya fada yana kallon sauran.

Daya daga cikinsu yace "ai wllh yau saina more sosai agurin nan,dan dagani itama fa kamar yar hannu,dan haka kawai bari kugani,Ni zan fara wllh"ya faɗa tare da tunkarar yarinyar.

Ja tayi da baya tare da zaro wuƙarta, ta tsaya cikin shirin ko ta kwana.ganin hakan datayi,suka tuntsire da dariya,dan gani suke ba'abinda zata iya musu.

Kai tsaye dayan nan ya tunkareta,tare da mika hannu da nufin kamota, saidai kawai yaji kett!an yankeshi abayan hannu.
Ihu ya kurma cike da jin azaba yana kallon hannun nashi.

Cikin mamaki suke kallon yarinyar,ransu aɓace suka nufeta dukansu, suna masu fidda wuƙake.

Ja tayi cike da jarumtata dame tana jiran ƙarasowarsu.
Aikuwa suna zuwa suka fara kai mata duka da wuƙake,ita kuma tana tarewacike da jarumta,ganin zata basu wahala ne yasa suka yi kanta gaba ɗaya.kasancewar Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi,suka samu nasarar rirriƙeta,ihu take tana ƙoƙarin kwacewa, amma ta kasa,cikin sauri dayan ke ƙoƙarin cire wando,kafin yayo kanta.

Wani irin kara ta kwalla,wanda saida dajin ya amsa kuwwa, nan da nan idanunta sukayi jaaa, suka fara fidda hawayen jini,kafin kace meye,tuni wani bakin hayaƙi ya lulluɓe dajin gaba daya.
Baka iya hango komai,sai wani irin ƙara mai amo da tada hankali.
Cikin lokaci ƙalilan ihun matasan nan ya fara tashi,cikin sauti mai ƙarfi,wanda kanajin sautin kasan maiyin ihun yana cikin azaba.


Masu karatu muje zuwa kubini sannu kan hankali.

Mrs babi ce 💘💘


Share and comment fisabilillah.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚



Free page

9/10





GAMASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN,ZAKU BIYA KAMAR HAKA.

NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR ASATI.

SPECIAL GROUP 500#
UPDATE BAKWAI ASATI.

ZAKU TURO KUDINKU TA WANNAN ACC. ƊIN.

SAATU KABIR
U.B.A
2215749011.

SAINA JIKU.



EVIDENCE OF PAYMENT
08148360851




_______________ Cikin dare Aman ya farfado, ahankali yake buɗe idon sa da su ka yi masa nauyi sosai.kasancewar dare ne hakan ya sa gurin yayi duhu, lumshe ido yayi cikin jin raɗaɗin da ƙafarsa keyi masa da ciwo.
Yunkurawa yayi da nufin ya tashi zaune, saidai sam ya kasa tashi zaunen, sakamakon tsami da jikinsa yayi gaba ɗaya.
Ahankali yake bin gurin da kallo, dan son gane inda yake, amma ya kasa gane War, ba abinda yake gani face alamun bishiyu dake tsaye agurin, sai kukan tsuntsaye,nan da nan tsoro ya kama shi,yayi saurin runtse idanunsa.tare da juyar da kansa,daga barin kallon dajin.

Tunani yake cikin ransa,to inane nan kuma?waye ya kawo su nan?ina Daddyn sa yake ?waɗan nan tarin tambayoyin ne cikin zuciyarsa,amma ba amsa.
Jin alamun kamar akwai mutum kusa dashi,yasa ahankali ya ɗan buɗe idonsa kadan,yana kallon Daddyn sa dake kwance,wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyarsa,tabbas wannan, Daddy ne akwance.dan haka maida idonsa yayi tare da rufewa yana tunanin ƙila mutanen da suka biyo su ne suka kamasu. ahaka barci yayi gaba dashi cike da alhini.

Washe gari da asuba Islam ta tashi tare da saukowa,saida ta dubasu kafin ta nufi ƙoramarta,alwala ta dauro sanann ta dawo, bayan tayi salla ƙasa ta sauko tare da wani kwano mai kama da akushi,an rufe shi da wani dan faifai.
Ajiye wa tayi kusa da inda suke kwance kafin itama ta zauna,tare da kafesu da idanu.
Sanyin asuba ne ya fara ratsasu,ahankali Aman ya buɗe idonsa, carab kuwa suka sauka akan Islam wacce ta zuba musu idanu,cike da tunani cikin ranta.
Tsoro ne ya matukar kama Aman,Dan haka cikin hanzari ya yunƙura da nufin tashi zaune yana faɗin"A' uzubillah, wacece ke ? Me muka yi muku?me kuke bukata atare damu?" Ya faɗa adam razane yana kallon kyakykyawar fuskar Islam.
Ita kuwa ganin yadda ya tsorota ne yasata matsowa da sauri tana faɗin"kayi ahankali,akwai karaya aƙafarka Ni ba komai zanyi muku ba,na taimake kune"ta fada tana mai kama kafadunsa ya tashi zaunen.

Kallonta yake cikin dan hasken da bai gama mamaye gurin ba,mamaki sosai cikin ransa, wannan fa macece,to me takeyi agurin nan?dan gashinan ya gani daji ne gaba da baya,

Kallon Aman tayi lokacin da ta koma ta zauna,sai kuma taga yana kallonta,harararsa tayi,tare da murguda baki sannan tace "kai ya haka ne kake ta kallona kamar zaka cinye Ni?
ta fada cikin salon muryarta mai dadi,da nuna ba tsoro.
Ajiyar zuciya Aman yayi kafin yace "mamaki nake, ta yadda yarinya mace kamar ke, ta kasance agurin nan? Sannan kuma ta yaya kika iya taimakon mu,?dan Allah ki fadamin kedin mutum ce ko aljan?sannan waye ya kawo mu nan gurin,nida Daddy na"ya kai karshen zancen sa yana dafe kansa dake masa ciwo.
Banza Islam tayi dashi, tare da mikewa ta nufi ƙoramar nan,Binta Aman yayi da kallo,tare da kallon kayan dake jikinta,zuciyarsa cike da tunanin anya mutum ce kuwa?ba jimawa ta dawo da ruwa cikin wata yar gwarya, ajiye masa tayi tare da cewa"idan ka gama kallon nasa saikayi alwala kayi sallah"tana faɗin haka ta mike tare da kama bishiyar nan ta haye,Aman yana kallon ta baki buɗe,cike da zallar madarar mamaki,kalli yadda take hawa bishiya, kamar wata biri gaskiya shikam yana mamaki da tsoron wannan yarinyar.

Aman yana cikin sallar Daddy ya farka,bakinsa dauke da salati.nan take abinda ya faru dasu,ya dawo cikin kwakwalwarsa tiryan tiyan.
Ahankali ya buɗe idonsa yana mai kiran sunan,Aman tare da juyawa gefe da gefensa yana neman Aman din,ba karamin daɗi Daddyn yaji ba lokacin da idanunsa suka sauka kan Aman yana Sallah.hamdala yayi cike da godiyar Ubangiji kafin ya yunƙura ahankali ya tashi zaune.jingina yayi da jikin bishiyar yana mai runtse ido,tare da jin yadda gurin da aka harbeshi ke masa zafi.

"Alhamdullah Daddy ka farka?sannu Daddy Ina ke maka ciwo yanzu?"Aman ya faɗa lokacin daya idar da sallar.
Juyowa Daddy yayi shima yana mai yiwa aman din sannu,tare da kallon kafar Anan dake daure,alamun karaya.
"Sannu Aman,kayi hakuri nina ja maka wannan kaddarar, dana Barka kayi zaman ka cikin yan uwanka, yanzu gashi an kama mu,an ajiye cikin wannan dajin"Daddy ya faɗa cike da damuwa.
"A'a Daddy kadaina fadar haka Please,dama can Allah ya ƙaddara mana faruwar hakan,kuma ba kamu akayi ba,mun kubuta daddy"
Jinjina kai Daddy yayi cike da jin jiki,yana mai lumshe idonsa.
Kafin yace "Alhmdllh Aman ina ne ?waye ya kawo mu ?
Kafin aman yayi magana sai ga Islam ta sauko,da sauri ta ƙaraso gurin Daddy ta durƙusa tana mai faɗin"sannu ya jikin naka"kallonta Daddy keyi cike da mamaki,wannan yarinyar fa?me takeyi anan?kodai iyayenta ne suka taimakesu?
Cikin muryar dattako Daddy yace "sannu yarinya, jiki da sauki,muna godiya sosai da taimakon ku garemu,ina iyayen naki suke,muna bukatar barin gurin nan,dan ganin likita"Daddy ya faɗa cikin muryarsa wacce kana ji kasan yana shan wuya.

Murmushi Islam tayi,kafin tace "bana da kowa,Ni kadai ke rayuwa anan,sannna saidai afita can bakin titi asami motar dazata kaiku asibiti"ta fada cikin nutsuwa tana kallon Daddy,
Cike da mamaki Dukansu ke kallonta,kafin daddy yace "yarinya,ke kaɗai ke rayuwa cikin wannan hatsabibin dajin?jinjina kai Islam tayi tana mai ballawa Aman harara,Wanda ya kafeta da idanunsa,yana yaba tsarin halitta da kyau da Allah yayiwa yarinyar.

Murmushi yayi ganin yadda take ta faman harararsa,kafin yace "Daddy ya kamata kayi sallah musan abinyi"

Ruwan Islam ta mikowa Daddy sannan ta koma can nesa dasu,dan basu guri Daddyn yayi alwalar.
Wannan akushin ta miko musu bayan Daddy yayi salla.
Budewa Aman yayi, cikin mamaki yake kallon akushin dake dauke da gasasshen nama sai turiri yake, sannan ya kalli Daddy.
Shima Daddy kallon Aman yayi jinjina kai,lallai akwai wani al'amari tattare da yarinyar nan,kuma ya ƙudiri niyyar bazai barta cikin wanan dajin ba yana bukatar sanin itaɗin ko wacece,zai tafi da ita gidansa,ya cigaba da riketa,domin tana bukatar taimako.

"Yarinya ina kika samu wannan naman?Daddy ya faɗa yana kallon Islam.
Murmushi tayi kafin tace" daga Allah "ta fada tana mai sunkuyar da kanta.

Kallonta kawai suke cike da mamaki da al'ajabin ta.
Sam Daddy baici Naman nan ba domin baya jin dadin jikinsa ko kaɗan,tunani yake cikin ransa,su waye waɗan nan mutane?me suke nema gurinsa?waye ya aikosu gareshi?yayi nisa cikin tunanin da yake yaji Muryar Aman yana faɗin"Daddy, zaman mu agurin nan fa akwai hatsari,ina tsoro kada mutanen nan su dawo, ko kuma wani abun ya samemu cikin wannan dajin"
Jinjina kai Daddy yayi kafin yace "akwai bukatar mu bar gurin nan kam aman, amma ta yaya ?ka gani dai ba wayoyi atare damu,bare mu kira azo atafi damu,yarinya muna bukatar taimakon ki,muna son barin gurin nan,sannan kuma ina son ki bimu zuwa gidanmu,domin zamanki ke kaɗai cikin dajin nan babban hadari ne,duba da kasancewar ki mace"
Daddy ya faɗa yana kallon Islam,wacce ke zaune daga can gefensu.

Kallon Daddyn tayi kafin ta mike ta nufi bayan wata bishiya ta tsaya,tunani take shin ya kamata tabi su Daddy zuwa gidansu?ko kuma tayi zamanta cikin dajin ya fi mata kwanciyar hankali,tunda ta kwatanta zama cikin mutane,amma hakan yaƙi yiwuwa,saboda kowa burinsa ya keta mata haddi,jikinta kawai suke da bukata,kafin su taimaka mata,saidai tana ganin Daddyn kamar baya daya daga cikin mutanen da ta hadu dasu abaya,shidin kamilin mutum ne,kuma dagani yana da sanin ya kamata.

harkene ya mamaye gurin da take tsaye,cikin murya mai cike da zaƙin sauti aka fara magana,
"Islam, kada ki tsananta tunani,jini bawan Allah nan,domin kaddararki tana tare dasu,bazan taɓa bari acutar dake ba ,ina tare dake ako ina kike"
Kallon hasken nan tayi,tare da lumshe ido,hakika tunda malaminta yayi magana,zata bishi,idan taga akwai matsala saitayi dawowarta nan ɗin.dan haka gurin su ta koma bayan hasken nan ya bace.
Zama tayi tare da yin shiru kanta na kallon gefen ta.
"Kinyi shiru yarinya baki ce komai ba,karki damu bazan taɓa barin wani abu ya cutar dake ba a zaman da zakiyi damu, sannan nima ina da yara dai -dai ke,ina son taimaka miki kamar yadda kika taimaka mana"ya faɗa cike da ƙarfafa mata gwuiwa.

Ahankali ta ɗago ta kalli Daddy kafin tace "shikenan na amince zan bika, saidai idan nayi karo da abinda bai gamsar dani ba,zaku iya nemana ku rasa ako wane lokaci"ta fada kai tsaye tana kallon Daddy.
Murmushi Daddy yayi yace "na gode da kika yarda zaki bini yata, dan kuwa jinki nake kamar yar cikina,
Yanzu ta yaya zamu bar gurin nan" ya faɗa yana kallon fuskarta.

Saidai muyi tafiya zuwa bakin titi, acan zamu samu mota zuwa cikin gari"ta fada tana mikewa tsaye tare da kallon Daddy, tace "Ina da abokin da bazan iya barinsa anan ba, wato janbu,idan ka amince zan tafi dashi "
"Bakomai yata amma ina shi janbun Dan banganshi tare da ke ba"cewar Daddy yana kallon gurin.

Hannunta ta sanya tare da danne harshen ta,tayi wani fito,nan da nan saiga janbu yana tsalle asaman bishi tare da nufota.
Kan kafaɗarta ya sauka yana kallon su Daddy.
"Ikon Allah ƴata wannan shine abokin naki kenan?to ba damuwa Allah yayi mana jagora.
Ameen Aman yace wanda yayi shiru tun dazu yana sauraron su,yaji daɗi sosai

Please Login or Register in order to submit comment