Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayaji cewar zasu tafi da Islam, dan shima bai goyi bayan zamanta agurin ba.

Ba abinda Islam ta dauka aɗakin nata face kwarinta da baka,dan ta bar komai agurin ne saboda shirin ko ta kwana,dataga akwai matsala saita dawo gidanta.

Haka Daddy ya yunƙura ya Mike yana dafa bishiya.wata sanda Islam ta mikawa Aman Dan ya dafa sandar su tafi.

Ba ƙaramar wahala suka sha ba kafin suzo bakin titin, da gyar Daddy ya kai bakin titin duk da Saida Islam ta rikeshi.

Suna fitowa suka ci Sa'a wani mai mota zai wuce Abuja da sassafe,ganinsu cikin wani hali na bukatar taimako yasa shi,tsayawa ya daukesu, yana ta kallon Islam tare da sakar mata murmushi.

Kai tsaye asibiti ya nufa dasu,cike da mamaki Aman ke kallon drivern dan kuwa asibitin da suke zuwa, nan ya kawo su.
Kasancewar Daddyn sananne nan da nan aka shiga dasu emergency,yayi da Islam ta zauna abakin ƙorar dakin da aka kwantar dasu,

Mutumin nan day kawosu ne yazo gurin Islam yana mai kallonta,fuskarsa ɗauke da murmushi yace"Islam kada ki damu,kin shiga hannu na gari,kuma kamar yadda na faɗa miki, ina tare dake ako ina kike"ya faɗa yana mai kallon fuskarta .

Sai lokacin Islam ta gane malaminta ne,dan haka murmushi tayi itama tana mai kallonsa,amma ba tace komai ba.....

Can gidan Daddy kuwa hankalinsu ya tashi sosai,dan sunyi ta kiran wayoyin su Daddy amma, ba wacce ta shiga.hankalinsu yayi mugun tashi sosai.
Suna zaune afalo mai gadi yazo yace ana sallama dasu, da sauri suka fito gaba dayansu,nan ake sanar dasu su Daddy na asibiti.

Hankali tashe suka nufi asibitin gana dayansu cikin ruɗewa da tashin hankali,su jannat kam kuka suke.....



Muje zuwa masu karatu.

Yanzu zamu fara.

Mrs babi ce💘💘

Kuyi hakurin jina shiru banjin daɗi ne.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚


Free page

11/12


GAMASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN,ZAKU BIYA KAMAR HAKA.

NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR ASATI.

SPECIAL GROUP 500₦
UPDATE BAKWAI ASATI

ZAKU TURO TA NAN.
SARATU KABIR.
U.B.A
2215749011

EVIDENCE OF PAYMENT
08148360851.

SAINA JIKU

*_Masu son Littafin MIJIN MALAMA suyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾_*
https://arewabooks.com/u/nimcyluv





____________Su Mommy ne zaune gaba dayansu, afalo.
Hankalinsu gaba ɗaya atashe yake,dan sam Daddy bai saba irin wannan tafiyar ba,duk inda yaje daya sauka zai kira ya sanar dasu.
Amma yau gashi tun jiya suke neman layinsa dana Aman,ba Wanda suka samu, hakan ba karamin abu bane gaskiya.

Mai gadi ne ya shigo ya sanar da Mommy wani mutum yana sallama awaje, cikin sauri suka fito gaba dayansu,nan mutum wanda daga asibitin aka turo shi ,yake sanar dasu daga asibiti ne ake nemansu,ankai Daddy yayi accident.

Cikin tashin hankali suka nufi asibitin,gaba daya,arude suke,dan su jannat ma tuni sun fara kuka.

Lokacin da suka isa asibitin,tuni an gama ba su Daddy taimakon gaggawa suna dakin hutu,Aman ba'a sake masa wani daurin ba ,dan kuwa sunce wannan daurin da akayi masa yayi sosai,dan sunyi scanning kuna sunga komai yayi dai-dai.

Daddy ma jini aka sanya masa,dan ya zubar da jini sosai. Dan haka su mommy na zuwa aka basu damar ganin su Daddy,Dan daki daya aka ajiye su.

Tun aharabar asibitin granny ke kuka tana faɗin"wayyo Allah baban Asalam, jiya -jiya katafi, muka rabu da kai lafiya,ashe hadari zakayi?dana dan albarka, ku kaini na ganshi Ni fadimatu naga ta kaina"da gyar mommy ke rarrashin granny tana faɗin"granny kiyi shiru,inba haka ba bazasu bari ki gansu ba,zasu hanaki shiga"

Cikin masifa granny ta ballawa mommy harara, kafin tace"to aniyarki ta biki har gadon barcinki,wllh banga dan tijarar da ya isa ya hanani ganin dana da jikana ba,dan ba wanda ya haifa min shi,yar shishshigi kawai"ta fada tana hararar mommy tare da kunna kanta cikin dakin.
Girgiza kai kawai mommy tayi kafin tabi bayan grannyn,su jannat na take mata ba.

Kuka sosai su jannat keyi,mommy kan sai hawaye,granny ma kuka take harda majina,lokacin da Aman ya gama basu labarin abinda ya faru,da yadda suka kuɓuta.
Daddy haƙuri yake basu akan suyi shiru,ai an suna arziki,tunda suna raye.
Fyace majina granny tayi da habar ,zaninta,kafin tace "Allah sarki ina yarinyar take yanzu?Allah yayi mata albarka har naji kaunarta cikin raina wllh"
Daddy ne yace jannat ta duba waje zataga yarinyar ta shigo da ita.

Lokacin kuwa Islam na zaune tare da malaminta, amma ba wanda yake ganinsa sai ita kadai,kallonta yayi da murmushi kafin yace "yanzu sabin ahalinki zasu zo su shiga dake,ki kwantar da hankalinki,duk lokacin da kikaso ganina,zan bayyana gareki,sannan ki riƙe aranki wadan nan mutanen alkairine agareki,kizama mai juriya Islam"ya karasa zancen sa yana mikewa tare da shafa kan Islam,wacce ke kallon sa cike da tarin tambayoyi abakinta,amma sam idan suna tare bata iya furta komai saidai kallo.haka tana kallo yazama haske ya bace bat.

"Kece wacce kuka zo da daddyna yanzu"Islam ta tsinkayo Muryar jannat tana mata magana.
Kallon jannat tayi kafin tace "Ni ce"
Kallonta jannat keyi tunda ga sama har ƙasa kafin ta taɓe baki tace "zo muje"tana faɗin haka tayi gaba .
Binta Islam tayi da kallo kafin tayi ƙwafa tace "wannan da gani bata ji,zan gyara miki zama wllh,Ni rainon dawa ce,bana ɗaukar raini"ta fada cikin haɗe rai kafin ta mike tabi bayan jannat.

Suna shiga dakin,mommy ta kamo hannun Islam tana mai cewa"sannu yata, Allah yayi miki albarka,mun gode sosai kin taimakemu"murmushi Islam tayi tana kallon mommy,lokaci guda taji matar ta kwanta mata aranta.
"To ai saiki barta tazo gurina nima inyi mata godiyar,mutum komai saiya nuna iyayi akai"granny ta fada tana janyo hannun Islam tare da hararar mommy.
Murmushi mommy tayi tana mai kallon Daddy dake kusa da ita.lumshe mata ido yayi alamun tayi hakuri,itama idon ta lumshe masa alamun ba komai.

"Sannu yar nan,kinyi abin kwarai,abin ayaba maki,kin ceci dana da jikana,dan haka zaki zauna tare da Ni, zan kula dake ba wanda zan bari yayi maki ba daidai ba agidan nan, kinji"granny ta fada tana shafa kan Islam,
Jinjina kai Islam tayi kafin ta kalli jannat wacce ke ta faman yatsina.
Aman kuwa sai bin Islam yake da kallo cike da ƙauna,shi komai nata burgeshi yake, kai tsaye take komai ba boye boye.
Kallon granny Islam tayi kafin tace "kijawa wannan matar kunne, dan naga tana min wani kallon raini,Ni bana ɗaukar raini duk wanda ya takani, zan takashi, Ni rainon dawa ce bana ɗaukar raini"ta fada cike da haɗe rai tana kafe jannat da ido.
Cike da mamaki jannat ke kallon Islam,sannan ta yunkuro cikin gadara zatayi magana mommy ta Banka mata wata uwar harara,hakan yasa ta maida fushinta ganin asibiti suke.amma zata nunawa wannan yar dajin ita ba kalarta bace.

"Indai wannan marar kunyar ce muma hakuri mike da ita,kuma wllh na baki dama,idan tayi miki ba daidai ba ki rama dan nima ta isheni da rashin kunya"cewar granny tana hararar jannat.
Ran jannat gaba ɗaya ya gama ɓaci.sai huci take tana hararar granny ta kasa -ƙasa.

Daddy ne yayi gyaran murya kafin yace "ku tafi da Islam gida,tayi wanka abata abinci taci sannan ta huta,duk abinda take bukata atabbatar anyi mata shi"ya faɗa cikin muryar dattako yana kallon mommy.
Haka mommy da yaran suka koma gida,akan ita zata dawo anjima,tunda granny tace Dole ita bazata koma gida ba,saidai mommy taje gidan yanzu.

Ko acikin mota Mommy da Islam ne agaba, sai jannat da hannan abaya.hakan ba karamin ƙara kular da jannat yayi ba,tunda kowa yasan ita ke zama agaban mota idan zasu fita,amma an zo ansa wannan kucakar amazaunin ta.

Koda sukaje gidan,ganin cewar Islam zatayi sa'ar hanan,dan haka sai mommy tace suje dakin hanan ɗin tayi wanka acan,hanan ta bata kaya ta sanya.
To hanan tace sannan tace wa Islam"zo muje daki "tayi gaba abinta.
Tsaye Islam tayi tana kallon inda hanan ɗin ta nufa,ita fa sam arayuwarta, bata son wulaƙanci,kuma yadda ta fahimci yaran gidan basu da mutunci ko kaɗan,kuma wllh bazata dauki sakarcinsu ba .

Ganin bata bi hannan ɗin ba yasa mommy tace "ƴata kije dakin hannan kiyi wanka kinji?zan kawo miki abinci kici,saiki huta,ki saki jikinki,nan tamkar gidanku ne"mommy ta fada cikin muryar kwantar da hankali.murmushi Islam tayi kafin tace "to Hajiya"
Hannunta mommy ta kamo tace "ba Hajiya ba,mommy kinji"
Jinjina kai Islam tayi kafin tace "to mommy"
Tana mai bin bayan hannan.

Tsaki jannat ta ja mai ƙarfi kafin tayi sama itama,bakin ciki kamar ya kasheta.
Aikuwa karaf akan kunnen Islam,dan haka da sauri itama tabi jannat din,taku biyu uku,ta cimma jannat,tana gab da shiga ɗakinta dake jikin na hanan,taji an fizgota tayo baya.
Arazane ta yi dan ƙara tana rike wuyanta.cike da mamaki take kallon Islam dake tsaye cikin haɗe fuska,aikuwa cikin masifa tayi kan Islam"ke dan uwarki saboda baki da mutunci,Ni kike jawa riga ta baya?dan kut....
Dassss !!!jannat taji an bale mata lips,da mugun ƙarfi,hakan ya hanata karasa maganar da tayi niyya.
"Idan kika sake zagina,wllh saina miki dukan tsiya agurin nan,banza marar hankali,karkiga nazo gidanku kiyi tunanin zan dauki raini ,wllh kikayi min ba dai-dai ba duka zaki sha,Ni rainon dawa ce bana daukar raini,ki kiyaye"Islam na gama faɗin haka tayi ɗakin hanan,abinta.
Tsabar haushi da bakin ciki da ɓacin rai,jannat kuka ta sanya ta shige dakinta tare da banko kofar.
"Wllh saina ci kan uwar yarinyar nan,har Ni zata bugewa baki?agidan ubana?wllh saina ci uwar yarinyar nan"ta fada cikin kuka tana jifa da fillows din kan gadonta.


Mommy kuwa tana shiga ɗakinta ta dauko wayarta tare da kiran Aslam,
Yana kwance kan kujera yayi dai-dai, da gashi sai gajeren wando da singlet,yana shafa kan wata baturiya dake kwance kan ƙirjinsa,wayarsa ta dauki ruri.
Jin ringtone din mommynsa ne yasashi saurin dauka,saida ya dai-dai-ta nutsuwarsa kafin ya daga.
"Mommy na, barka da gida"ya faɗa cikin muryarsa mai daɗin sauraro.
"Aslam, daddynka yana asibiti,shida Aman, jiya aka taresu akan hanyarsu ta zuwa Niger,kuma an harbi daddynku acikinsa, Aman kuma ya karye,tare da manyan raunuka,Allah ne kawai ya kiyaye da tuni sun mutu.
Dan haka duk abinda kake ka ajiye ka dawo gida"mommy na gama faɗin haka ta kashe wayarta, haka ne kawai zai sa Aslam ya dawo gida, ajiyar zuciya tayi tare da mikewa,sannan ta shiga kitchen da kanta.

Aslam kuwa jin abinda mommynsa ke faɗi,tuni ya ture yarinyar dake kwance akan ƙirjinsa ya mike tsaye,"hello !hello!!mommy kina jina ?hello"yake ta fada cikin tashin hankali,amma ina mommy tuni ta kashe wayar ta.
Hankali tashe ya fara hada kayansa,cikin gaggawa yake komai,yarinyar sai tambayar sa take lafiya amma ko takanta baibi ba.
Waya ya dauka ya kira wata number yace yana son jirgin da zai tashi zuwa Nigeria yanzu.

Cikin Sa'a ya samu wanda zai tashi nan da minti ashirin.
Haka yayi ta kiran numbers din su Daddy da Aman, Amma basa shiga.
Yana gama shirinsa ya fito riƙe da jakarsa da abubuwan da zai bukata.lokacin yarinyar na zaune kan kujera.mika mata keys din gidan yayi yace "ta kulle masa gida ta kaiwa mark mukullin, Yayi ficewarsa.

Cikin ƙanƙanin lokaci da bazai gaza awannin uku zuwa hudu ba,Aslam ya sauƙa afilin saukar jirage da ke birnin tarayya Abuja. Kai tsaye ya dauki mai taxi,ya nufi gida.

Lokacin daya isa gida mommy tuni ta koma asibiti ita da jannat suka koma, dan haka daga Islam sai hannan,agidan. Dan haka kulle ƙofar hanan tayi lokacin dazata shiga wanka,ta bar Islam afalo tana cin abinci,tana sanye da kayan da hanan ta bata ta sanya,riga da wando ne ajikinta,rigar ta sauko har gwuiwarta,sai wando wanda ya kasance three quarter ne, kanta ba dan kwali sai gashinta data daure, ko mai abata shafa ba,amma tayi kyau shar da ita,abinka da mai kyau.

Norking din kofar ake tayi,tana zaune tana ji,amma batayi yunkurin tashi ta buɗe ba.saida ta kammala cin abincinta, sannan ta tashi cikin takunta mai cike da ɗaukar hankali ta nufi ƙofar,jin an Dada danna door bell din da ƙarfi kusan sau uku.
Tsaki tayi tana faɗin"wai waye wannan haka?nifa gaskiya wannan tsirfar bazan iya da itaba,haka kawai ake kulle kofa sai mutum yana ta tashi budewa,"ta fada cike da ƙosawa tana jan tsaki,kafin ta buɗe kofar.
Kallon- kallo ake tsakanin Aslam da kuma Islam,inda shi yake kallonta cike da ɓacin ran ba'a buɗe masa kofa da wuri ba, sannan yana mata kallon rashin sani,gashi sai wani yatsina fuska take tana kallonsa.
Cikin rashin damuwa Islam ta gyara tsayuwar ta ,ba tare da ta kauce masa daga hanya ba, sannan ta wani karkata kai tana kallonsa tun daka sama har ƙasa kafin tace "malam daga ina?wa kake nema?masu gidan basa nan suna asibiti,saika bisu can"ta fada cikin wani salo irin mai kama da na yan daba tana juyawa da nufin komawa cikin falon.

Kan uban nan,wannan ɗin wacece?wacce marar kunyar ce take min irin wannan tambayar agidan mu?lallai ,zan koya miki hankali,ya faɗa yana fizgo rigarta ta baya.....

Masu karatu yanzu wasan zai fara,
Muje zuwa
Mrs babi ce 💘💘

Share and comment fisabilillah.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


🎄🎄 RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)




Elegant online writers📚📚


Free page

13/14



GAMASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN, ZAKU BIYA KAMAR HAKA.


NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR ASATI.


SPECIAL GROUP 500₦ UPDATE BAKWAI ASATI.


GAREKU MANYAN MATA MASU BUƘATAR ATURA MUSU TA PC.
ZAKU BIYA 1000₦.

ZAKU TURA KUDIN TA WANNAN ACC. ƊIN.

SARATU KABIR
U.B.A.
2215749011

SAI KUNZO.





_______________"Kan ubancan,wannan ɗin wacece?wace marar kunyar ce take min wannan tambayar agidan mu?lallai zan koya mata hankali,zaki san waye Aslam yau"yana gama faɗin haka cikin zuciyarsa,ya wani fizgo Islam ta baya.
Da mugun ƙarfi ya fizgota cikin salon sa na mugunta.
Ba zato ba tsammani, kawai Islam taji an fizgota ta dawo baya,bugawa tayi da jikin bango,sosai ta buge kanta ta baya,dan lokacin da Aslam ya fizgota kaucewa yayi,maimakon ta fado jikinsa,sai ta bugu da bango.dan ƙara ta sanya tare da runtse idonta cike da azaba,dan ta bugu sosai.gashi ya damke mata gashi da ƙarfi cikin hannunsa.
"WHO the hell are you?wacece ke?da har
Kike iya kallon kwayar idona kina min wannan tambayar ta raini?kinsan waye Aslam kuwa?bana son raini ko nuna ban isaba, kishiga hankalinki,wannan gargadi na ne gareki,bansan koke wacece ba,amma yau kawai naji na Tsaneki,kada ki bari wani abu ya sake haɗani dake "
Duk da irin azabar da Islam Ke sha,dan kuwa kallo ɗaya zakayi wa idanunta wanda ta buɗe su lokacin da Aslam ya fara magana,kasan cewa tana shan azaba ,tana karbar kida ahannun Aslam,Amma cikin nata kalar zafin ran,da mugun ɓacin rai,tayi wani yunkuri tare da juyar da hannun Aslam din,sai gata ta kwace kanta daga hannunsa.
Gabansa ta matso sosai kamar zata rungumeshi,banda huci ba abinda takeyi, idonta yayi jajur,ta fara magana"lallai kayi gangancin yi min wannan kalar muguntar, wllh!wllh!!wllh!!!ka ajiye aranka,saina rama duk wani kalar cin kashi dazakayimin agidan nan,kamar yadda bansan ko kai waye ba ,Nima bakasan koni wacece ba,bazan taɓa daukar rainin hankali da wulaƙanci ba,dan Ni ba wulaƙantacciya bace,Ni rainon dawa ce bana ɗaukar raini"Islam ta fada cikin zazzare masa ido,kuma ba tare da nuna tsoro ko shayinsa ba,duk da yadda yake tsaye agabanta kamar Giwa,ita kuwa tana nan yar ɗull,akasansa.

Cike da zallar mamaki Aslam ke kallon Islam,wai wannan wace yarinyar ce?me ta taka haka agidan nan?shidai yasan adangin mommy Ko na Daddy ba irin wannan yarinyar yar tijara,to a ina suka samota? Tambayar da Aslam keyiwa kansa kenan cikin mugunyar bacin rai,ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu.
Cilli yayi da jakar dake hannunsa,jikinsa har rawa yake tsabar ɓacin rai,kasancewarsa mutum mai matukar son girma,da son anuna shiɗin babbane gana ƙasa dashi,sai abinda Islam tayi masa yazo masa abazata,kannansa har wanda daga shi sai shi,ahaihuwa ma,tsoron sa yake ji,amma wannan abar da baifi yayi loma daya da ita ba ,itace take tsaye gabansa tana fada masa maganganu masu zafi haka?inaaaa!!!wllh bazai yiyuwa.
Kallon ta yake cikin ɓacin rai,yana tunanin irin hukuncin da zai mata,itama kuma bata fasa kallon nashi ba,idonta ƙurr, akan kyakykyawar fuskarsa,wanda ɓacin rai ya mamayeta.

"Zakiyi dana sanin haduwar nan tamu dake ta farko,zan nuna miki ke karamar yar iska ce,iyakar ki Nigeria,wllh saina san ya ki cikin tashin hankalin da saikin zabi mutuwar ki akan rayuwa"Aslam ya faɗa cikin wata irin zazzafar murya,har sarkewa muryarsa keyi,tsabar ɓacin rai.

Wani shegen murmushi Islam tayi,kafin tace "nima ga nawa albishir din,ka sani,bazan taɓa gajiyawa da rama duk wani abu da bai gamsar dani ba,wanda zakayi min,zan zamo maka alaƙaƙai,zan zame maka ladangaren bakin tulu, Ni Islam rainon dawa ce bana ɗaukar raini"Islam ta fada cikin gadara tana karkada jiki.
"Keeeeehhhh!!! Aslam ya daka mata tsawa tare da daga hannunsa ya sharara mata mari mai matukar zafi,ji kake tauuuu!!!har saida falon ya amsa.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Hanan daga wanka,zaro ido tayi sakamakon ganin ya Aslam ,kuma ya wanka wa Islam mari, da gudu ta ke saukowa daga matakalar Benin,harta ƙaraso garesu.jikinta banda rawa ba abinda yake.cikin rawar murya tace "yaya da...n ... Allah ...kayi hakuri bakuwar Daddy ce ...tare suka zo ,kuma itace ta ceci rayuwarsu"ta fada cikin tsantsar tsoro tana mai kamo Islam,wacce ta daskare atsaye riƙe da kumatunta,wanda Aslam ya kashe mata su da mari,tunda take arayuwarta,ba wani mahalukin daya taɓa daga hannu ya sharara mata mari haka,sai wannan mutum,lallai ya tsokano tsuliyar dodo,wllh tashin hankali yanzu suka fara.
Kallon Hanan yayi tare da watsa mata wani shegen kallo na ki kiyaye,ko na dawo kanki.
Da sauri ta koma bayan Islam ta buya,jikinta na rawa.

"Wannan shine last warning da zan miki ki kiyayeni,bani da kyau,ba'a shiga gona ta afita lafiya"yana kaiwa nan yayi waje cikin fushi da ɓacin rai.
Driver ya kira suka tafi asibitin,zuciyarsa kamar zata kama da wuta.
Islam na tsaye bakin ƙofar nan riƙe da kumatunta dake mata zugi,idanunta sunyi jaaa sosai,ahankali Hanan ta zagayo gabanta ,cike da tausayawa tace "sannu,amma meye ya hadaku da yaya daga zuwansa?dan Allah kiyi nesa dashi,har zuwa lokacin da zai bar kasar nan,wllh yaya ya wuce duk yadda kike tunani,sam baya son rashin kunya,ke kuma naga alama kamar halinki ne rashin kunya,koda zakiyiwa wasu karki ce zakiyiwa yaya Aslam domin ya wuce tunaninki"Hanan ta kai aya tana kokarin kamo hannun Islam.

Cikin masifa da jin haushi Islam ta fizge hannunta,tare da watsawa Hanan kallon daya sata ta ja da baya.
"Wllh ya dauki bashi,bazan taɓa yafe wannan cin mutuncin da yayi min ba,ba wanda ya taba marina sai shi,kuma yayi kuskure,sannan Ni bana tsoron uban kowa,bare wannan basamuden ya tsoratani,baki mai bakar aniya, zaisan ya taba Islam,ni rainon dawa ce bana ɗaukar raini"tana kaiwa nan tayi sama cikin sauri ta shige dakin Hanan.

Zama tayi akan gado ta lankwashe kafafunta tare da kafe jikin bango da ido,zuciyarsa sai tafasa take.jikin tane ya kama rawa kamar mai farfadiya,nan da nan kwan dake haska dakin ya fara farfari,gaba ɗaya kayan dake cikin dakin
hatta gadon da take kai girgiza yake,ji kake fasss!!! madubin dakin ya fado ya tarwatse.
Da gudu hanan ta hawo saman,saidai abinda ta gani,yasata komawa falo da gudu tana ihu,jikinta sai rawa yake,anya kuwa wannan mutum ce?daga shiga daki gaba ɗaya kayan dake cikin dakin sun kama jijjiga? "na shiga ukuna "ta fada cikin tsoro tana kokarin kiran wayar mommy.


Aslam kuwa kai tsaye asibitin suka nufa,har suka ƙara sa cikin asibitin zuciyarsa na masa zafi da suya. akan me wannan karamar yarinyar zata iya tsayawa agabansa tana masa rashin kunya?me ta taka ?wacece ita?daga ina take ?wllh saiya nuna mata shi ba sa'an yara ƙanana bane irinta.haka ya fito daga cikin motar zuciyarsa ba dadi,fuskar nan kamar hadari,ya wani hade ta sosai.
Cikin izza da tsarin tafiya irin na sadaukan maza yake tafiya,duk inda ya keta ƙamshine kawai ke tashi.kai tsaye ya nufi dakin dayasan ana kwantar da ahalinsa idan sunzo asibitin, ahankali ya tura ƙofar bakinsa dauke da sallama.

Gaba ɗaya suka juyo cikin hanzari,jin Muryar Aslam,granny ce ta mike da sauri tayo gurinsa,ɗauke da madaukakin farin ciki"Asalamu, kaine nake gani ko ido nane? Allah mun gode maka, shegun masu jan kunnen can sun gyale mini jika"Ta fada tana kamo hannunsa.
Baice komai ba kawai kallonta yayi tare da danyin murmushin yake.
"Wllh kuwa shine,sai dai har yanzu bakin halin yana nan,yaro saikace kafuran farko,kullum cikin ƙunci?ai wllh maganin wannan halin naka aure,shine kawai zai daidaitaka tunda ka koyi halin yahudawa"ta fada tana mai taɓe baki.

Wani shegen kallo Aslam ya watsa mata kafin ahankali ya furta"ba saikiyi min auren ba,tunda akanki nake zaune"yana faɗin haka ya zare hannunsa ya nufi gadon da daddy ke kwance.

"To dan tijara Ni kake fadawa haka?wllh zaka gane kai karamin tijararrene,banza basamuden wofi kawai,daga zuwanka ana murna zaka fara yiwa mutanen nonsi ,(wai tana nufin nonsense)lol.
Ta fada tana komawa gurin data tashi tare da turo baki,wai adole tayi fushi.

"Daddy sannu, hankalina yayi matuƙar tashi,lokacin da Mommy ke sanar dani abinda ya faru,amma Daddy an sanar da hukuma kuwa"?Aslam ya faɗa fuskarsa ɗauke da damuwa.
Shafa kansa Daddy Yayi kafin yace"karka damu Aslam jikina da sauki,kuma yan sanda nata bincike akan al'amari,sannu kasha hanya "Daddy ya faɗa yana murmushi,dan yaji dadin ganin dan nasa.

Gadon da Aman ke kwance Aslam ya koma,tare da shafa kan Aman ɗin yana mai faɗin"boy sannnu ya jikinka"
Murmushi Aman yayi yace "da sauki yaya kasan am strong like you"murmushi Aslam yayi tare da kallon mommy,wacce ta kawar da kanta daga kallon Aslam,duk da irin dadin da taji lokacin daya shigo dakin,amma tana son nuna masa kuskurensa na kin dawowa gida.

Lumshe ido yayi, da kokarin kawar da damuwarsa,kafin ya nufeta.yana zuwa ya rungumeta tare da ɗora kansa akafadunta.
Cikin salon sa na barikanci yake faɗin"am sorry my love,nayi kuskure bazan ƙara ba kiyi hakuri,kinji?Please ki rungumeni, kona samu sassauci cikin zuciyata. I miss You alot"ya faɗa yana kara kwantar da kansa sosai tare da lumshe idonsa.

Abinka da uwa da ɗa,tuni mommy taji zuciyarta tayi sanyi,ta rungume danta ajikinta sosai tana mai sauke ajiyar zuciya,sannan ta shafa kansa tace "i miss You too sweetie,fatan bazaka kara komawa London ba"ta fada tana ɗan kamo kunnensa.

"Wayyo my love kunne na zai cire"Aslam ya faɗa cikin shagwaba,kamar ba shine ya gama horancewa yanzun ba.

Dariya sukayi harda Daddy,Dan yasaba ganin wannan tabarar ta Aslam idan yana gaban mommynsa.
Hararar Aman Aslam yayi yana mai faɗin"kai Ni kakewa dariya ?"ya faɗa cikin ɗaure fuska.
Da sauri Aman ya tsaida dariyarsa ya fara dan tari yana faɗin "mommy ruwa!ruwa mommy na kware"yana faɗa yana kallon idon Aslam.Dariya Daddy Yayi yana mai fadin"ai fa horo ya dawo,yanzu kowa zai nutsu"

"Ohh ni yar nan,naga abinda yafi karfina, na shiga uku na lalace,wannan wane irin zamani muke ciki,yanzu ke kuwa yar nan agabana,kike kama danki na fari kina runguma?kai wannan tijara tayi yawa,wllh kiji tsoron Allah,wannan ba halin kwarai bane ,dan fari kunyarsa akeji bawai kayi ta jansa ajikin kaba "granny ta fada tana hararar mommy.

Jannat da tunda Aslam ya shigo dakin batace komai ba,sai sake nutsuwa da tayi dan gudun karta saba layi, yanzun nan taci na jaki,sai lokacin ta kalli granny tace "kuji granny,Ina ce nan kike ta ihun kuka kina anuna miki danki,kin shiga ukunki shi kadai gareki karya mutu,lokacin da aka kawo Daddy asibitin nan,amma yanzu zaki wani hana mommy nuna wa danta soyayya"jannat ta fada tana hararar granny.

"Jannatu kaniyarki,kunji yarinya da salon munafurci da iya kulla sharri? wallahi idan baki fita harkata ba,zan zage mu muci uwar sabada dake aɗakin nan,kinsan ba tsoron ki nake jiba"granny ta fada cikin masifa tana gyara mayafinta.

Daddy ne yayi ta ba granny haƙuri Dan ta day zafi sai masifa take,sannan yasa jannat ma ta bata hakuri,kafin granny tayi shiru da maganar,dan sai babatu take tana faɗin wllh sai su doku da yarinya.

Sai da aka kira magrib sannan suka fara shirin tafiya gida,dan kuwa bakwai ake fitar da yan jinya,saboda tsarin asibitin mai zaman jinya baya kwana ,saidai kazo da safe ka tafi da yamma.

Haka suka taho gida gaba dayansu,mommy da Aslam agaban mota,sai jannat da granny abaya,ana ta gwabzawa.

Suna zuwa suka tarar da Hanan zaune afalo tayi gurum,cike da tsoro,tana ganinsu ta tashi da sauri ta rungume mommy sai kuka.

"Mommy wllh waccan Islam ɗin ba mutum bace ,kuje kuga abinda tayiwa dakina dazun nan,da idona naga kayan dakin suna jijjiga da kansu.

Cike da mamaki suke kallon ta,"jijjiga kuma kamar yaya"mommy ta fada tana dagota.

"Muje ku gani kawai mommy"ta fada tana kamo hannun mommyn suka nufi sama.

Dama tuni
Aslam yayi shigewarsa ɗakinsa,dan ya gaji sosai,so yake yayi wanka sannan yaci abinci ya kwanta.

Suna zuwa ƙofar dakin Hanan,mommy ta kama ƙofar ahankali ta turata
"Ikon Allah "mommy ta fada cike da mamaki tana kallon dakin.....


Masu karatu muje zuwa,

Sannan mun kusan kammala free page,Dan haka mai buƙatar littafin nan yayi saurin biyan kudin sa,kar sai munyi kisa sannan mutum yace yana so,mun riga mun wucesa.


Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free page

15/16





GAMASU SON BIYAN KUDIN WANNAN LITTAFIN ZAKU BIYA KAMAR HAKA.



NORMAL GROUP 300₦
UPDATE BIYAR A SATI.


SPECIAL GROUP 500₦
UPDATE BAKWAI ASATI.

SAI KUMA MANYAN HAJIYOYI MASU SON ATURA MUSU PRIVATE ZAKU BIYA. 1000₦


DUK ZAKU BIYANE TA WANNAN ACCOUNT ƊIN.


SARATU KABIR
U.B.A
2215749011

Sai kun zo.





_______________Da zuwan su

Please Login or Register in order to submit comment