Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani,shiɗin fa yana kallon ki ko kin manta?tashi ki shiga ciki kafin nan ki bani wayar ki "Aslam ya faɗa cikin haɗe rai.
Hannu na karkarwa jannat ta mika masa wayar tana kuka,kafin ta tashi jiki ba kwari ta nufi cikin gida,tana fatan Allah yasa ba kowa cikin Falon.

Tana fita ɗakin ya rage daga Aslam sai Islam,sosai taji tausayin kukan da jannat keyi,tasan dole taji tsoron iyayensu su san wannan maganar,kallon aslam tayi wanda ya dafe kansa yayi shiru tare da lumshe idonsa,istigfari kawai yake cikin ransa yana tuba ga Allah,yanzu haka watarana za'ayiwa yarsa kenan idan bai daina ba?tun yanzu ga abin ya fara biyar ƙanwar sa,
Ƙarasowa kusa dashi Islam tayi tare da zama,ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon sa ta fara magana"kaga ka kwantar da hankalin ka,abinda ya faru ya riga ya faru,saidai Allah ya kiyaye gaba,sannan ya kamata kasanya ido akan ƙannan ka sosai,kasan yadda suke rayuwa,Ni dama na jima ina zargin jannat,dan kuwa ina jin yanayin yadda take waya,wani lokacin ma shike haɗamu faɗa da ita,kuma kayi shiru da maganar nan iya tsakanin mu,amma karka sanar da su mommy Dan gudun tashin hankalin su,tunda jannat ɗin tayi nadama,Ni dai nayi alƙawarin riƙe mata sirri ,kaima Please karka sanar da kowa"Islam ta faɗa tana kallon idonsa.
Shima kallon ta yake cike da mamaki,dama tana da hankali haka?ta iya magana mai daɗi da bada shawara.
"Shikenan na gode sosai da rufawa ƙanwa ta asiri da zakiyi,sannna in sha Allahu bazan sanar da su mommy ba,kawai abin ne yake damun zuciya ta,da baki zo kin gansu ba me zai faru?sannan tsawon wane lokaci suka ɗauka suna aikata wannan lalata?"
"Allah shiga barwa kansa sani,kayi ƙoƙarin manta wa da komai shine yafi,Ni bari na tafi dama lambu zanje neman janbu"Islam ta fada tana mikewa tsaye tare da fara tafiyar ta cikin salo .
"Na gode "Aslam ya faɗa ahankali yana bin bayan ta da kallo.
Juyowa tayi tare da balla masa harara tace "kaga malam ba dan ka gode min nayi ba,ra'ayi na ne kawai ,ka riƙe godiyar ka kagane"ta fada tana murguda masa baki tare da ficewa.
Kawai Aslam ya tsinci kansa da sakin murmushi,wato dai mai hali baya sauya wa,amma koba komai dai yau daya tayi abin ayaba mata,kuma yaji daɗi sosai.yana nan zaune ya fara duba wayar jannat,abubuwan da ya gani sosai suka tsorata shi,videos ne kala kala na sex da saurayin ke turo mata,sannan ga hotunan su Nan marasa kyan gani,chat ɗin su kuwa kasa karantawa yayi.
Haka ya tashi jiki asanyaye ya nufi ɗakinsa da wayar,ya ajiye bayan ya goge komai dake ciki.

Gaba ɗaya kwana biyu jannat ta sauya ta zama shiru-shiru yanzu ba rashin kunya ba surutu,kullum da hijabi da casbi ahannun ta,kuma Indai Mommy zata shiga kitchen tare suke shiga ,sosai takeyi yiwa kowa ladabi da biyayya agidan, mommy ba karamin daɗin hakan taji ba.tana kuma mamakin abinda ya kawowa ƴar Tata sauti lokaci ɗaya haka.
Aslam aranar ya Sami daddy da batun jannat,cewar saurayin ta yayi masa magana akan iyayensa zasu turo,kuma ya tambayi jannat ɗin tace da amincewar ta,dan haka Gara kawai su aurar da ita,inyaso ta kammala karatun ta agidan mijinta.tunda level 2 zata shiga yanzu.
Ba musu kuwa daddy ya amince,ba tare da yace wa Aslam komai ba game da nashi auran.

Yau kwana ki ukun da daddy ya ɗibarwa Aslam suka cika,kuma yau iyayen saurayin jannat suka zo,an tsaida magana akan nan da wata biyu za'ayi bikin,bayan kowa ya watse har baƙin da suka taya daddy karbar iyayen saurayin jannat,daga Daddyn sai mommy da Aslam,Aman kam tun da ya fara taka ƙafar sa ,kullum suna tafe zuwa garden shida Islam,tana koya masa tafiya a cewar ta,amma ko yaya yayi kuskure yanzu za'a matse kafar ace za'a maidata gidan jiya.haka zaiyi ta bata haƙuri yana taka tsantsan,wani lokacin harda su jannat ake taya shi tafiyar.

"To Aslam, Alhmdllh an gama batun neman auren jannat,nan da wata biyu za'ayi bikin,wanda kaine da kanka ka yanke haka,to dama na bari ka zabi lokacin ne da kanka,dan ahaɗa da naka.dan haka,saika yi mana bayani in yaso nan da gobe kaima sai muje neman naka auren ko"
Daddy ya faɗa yana kafe aslam da ido.
Shiru Aslam Yayi kansa a ƙasa,yana kasa magana dan baida abin cewa.
"Kai nake sauraro kayi shiru"cewar daddy.
"Am daddy adan ƙara hakuri dai a kammala bikin jannat ɗin in Sha Allahu kafin lokacin zan kawo matar da zan aura nima,ina nan ina bincike ne"aslma ya faɗa cikin sunkuyar da kai.
"Yanzun ma baka samo ba kenan ko?to shikenan na baka damar daya kamata in baka,kayi wasa da ita,dan haka sai ka saurari nawa hukuncin da zan zartar nan da lokacin"daddy ya faɗa ba tare da nuna ɓacin ransa ba.
"Na gode daddy"Aslam ya faɗa cikin murnar samun nasara,Dan atunaninsa daddy ya amince da batun sa ne.nan kuwa baisan me daddy ke shiryawa ba.

Washe gari daddy yace yana neman kowa aɗakin sa, bayan sun gama zama shida granny, da mommy,kome suka tattauna oho.
har da Islam, yace tazo dan zaman nata ne.aikuwa gaba ɗaya suka hallara afalon daddy,
Kowa yayi shiru yana sauraron abinda daddy zai faɗa,

Ahankali daddy ya bude taron da addu'a kafin ya fara magana.....

Bari mu jira me daddy zai ce .

Mrs babi ce
Anty mammy.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: ____________Gaba ɗaya sunyi shiru,suna jiran abinda daddy zai faɗa.
Ahankali daddy ya buɗe baki tare da yin addu'a,bayan sun shafa ne kuma ya fara magana kamar haka.
"Alhamdullah nasan zakuyi mamakin abinda yasa na tara ku anan,to ba komai bane sai dan yau ina buƙatar sanin tarihin Islam,domin aiwatar da wani ƙudiri nawa akanta,dan haka Islam,muna bukatar jin abinda kika sani game da rayuwar ki"daddy ya faɗa yana kallon Islam.

Ɗago kai Islam tayi tare da kallon daddy na wasu ƴan sakwanni, kafin ta sauƙe ajiyar zuciya tare da gyara zama ta fara magana.
"Ni dai sunana khadeeja amma Islam ake kira na dashi,kamar yadda malami na ya sanar dani.na taso cikin gata da kulawa gurin iyayena,mahaifina babban ɗan kwangila ne sosai,ba abinda na nema na rasa arayuwata.
Bazan iya cewa ga asalin garin mu ba,sai dai zan iya tuna abu guda game da rabuwata da iyayena.
Lokacin inada shekara takwas a duniya. Wata rana da daddare muna kwance ,kawai sai muka far jin harbi ta ko ina,lokacin Ni kadai ce agurin iyayena sai kanina wanda ahalin yanzu na manta sunan sa.
Tashi nayi ina kuka dan na tsorata sosai,ina zaune cikin dakina,saiga mama na,da babana sun shigo agigice,nan naji babana yana cewa mamana yan fashine suka shigo cikin gidan namu,kuma suna gab da ƙarasowa cikin bangaren da muke,dan haka maza-maza muzo mu gudu.haka babana ya sanya wata doguwar igiya ya fitar dani ta window mai nisa sosai,dan asama muke,ina ta kuka ina cewa suma su sauƙo mu tafi tare sai dai ,yana saukeni naji ihun mamana lokacin barayin sun ƙara so cikin dakin.kuka na ƙara sanya wa ina kiran sunan mama na da baba.
Duk abinda suke faɗi ina iya jiyowa, dan da ƙarfi suke maganar,naji suna tambayar babana,ina takardun kwangilar da aka bashi,dana sauran kadarorinsa.
Bansan ya akayi ba,kawai naji ihun mama na da baba na,kuma naji baba na Yana fadin"Islam ki gudu karki tsaya.
Ina nan tsaye cikin tsoro da firgici,kawai naga wani daga cikin yan fashi ya leƙo ta windown yana faɗin akamoni ahaɗa Dani akona mu gaba ɗaya.
Jin abinda ya faɗa yasa nayi saurin bin ƙofar baya na fice daga gidan ,ina gudu ina kuka.sosai na shiga cikin daji,wanda tsabar gudu kafata gaba ɗaya ta fashe sai jini ke zuba cikinta.
Ban daina gudu ba saida ƙarfi na ya ƙare na faɗi atsakiyar jeji.
Koda na farfaɗo na ganni kwance cikin wata bukka ansaka min magani cikin ƙafata. Tashi nayi na fara kuka ina kiran suna iyayena,awannan lokacin ne na fara haɗuwa da malamina, ina cikin kuka naji an daga kafaɗunta cikin rarrashi yake bani hakuri tare da faɗin zai kaini gurin iyayena idan na warke.

Haka nayi ta zama cikin jejin nan,daga Ni sai malamina,wani lokacin ingan shi wani lokacin kuma ina rasashi. Ahaka muka shaƙu dashi sosai.sai dai tunda nake zaune dashi ban taba ganin wani mahaluƙi yazo gurin ba ,kullum mu biyu ne muke rayuwa.
Ranar dana cika sati biyu agurinsa nace ya kaini gurin iyayena.
Ba musu kuwa yace In rufe idona.cike da ƙuruciya na rufe idona ina murnar zanga ahalina,koda yace inbude idona,aikuwa gaban gidan mu na gannu tsaye.sai dai ga dukkan alamu gidan gobara yayi dan gaba ɗaya ya kone yayi baki.nan take na fara kuka ina tambayar ina iyayena suke.wani makocin mu ne yake sanar da malamina cewar ai barayi ne suka shiga gidan suka kunna wuta da iyalan gidan gaba ɗaya,sai dai ansmi tabbacin dama bana cikin gidan,kuma suma iyayena an duba ko ina ba alamar sun kone acikin gidan,anfi zargin wutar bata rutsa dasu ba suka gudu.
Nidai iya sanina bansan wani dangi na mamata ba,sai dai lokaci lokaci muna zuwa wani gari inda yan uwan babana suke kuma Ni bansan ya sunan garin ba.dan haka koda aka bukaci kaini gurin yan uwan iyayena ,ba wanda yasan idan za'a nufa dani,dan haka wannan makocin namu yace zai rikeni.
Da farko ina zaune lafiya agidan,sai daga baya na fara fuskantar baranaza kala-kala.duka,zagi aikace -aikacen gidan duk Ni keyi,gashi niba wata babba ba,amma haka ake tulamin aiki,cikin ƙanƙanin lokaci na rame nayi baki sosai,ga yunwa makaranta kuwa tuni na daina zuwa.
Wata rana matar gidan ta kamani ta zaneni da daddare kuma ta kora ni waje.
Ina kuka cikin tsoro na duƙunkune jikina,sai naji Muryar malami yana cewa"Islam kiyi haƙuri haka taki ƙaddarar take,daga yau kin bar zama agidan nan,tashi mutafi.
Cikin farin ciki na mike nabi malamina ,muka koma can gidansa na daji,daga nan ya fara koya min karatu da yaruka iri-iri,bayan yan shekara guda ba irin Yaren da bana ji,nan yake kaini wata makaranta cikin ya'yan turawa,anan nayi firamare da sacondary .ya koya min duk wani abu na yan gayu,hakan yasa koda nazo gidan na ba abinda ban iya amfani dashi ba.shine ya koya min yadda zan kare kaina idan an zo cutar dani,abu guda ne bai sanar da Ni daba,inda iyayena suke,yace wannan ƙaddara ce zata haɗani dasu,bashi ne zai sanar dani ba.
Lokacin da matasa suka farga dani cikin dajin ,sun sha kawo min hari da burin cutar da rayuwa ta,amma Allah bai basu nasara akaina na,duk lokacin da wani yayi nufin cutar dani,malamina yana zuwa ya kawo min ɗauki.sannan shine ya ƙarfafamin gwuiwar zama cikin gidan nan,yace anan cikon ƙaddarata yake.
Wannan shine iya abin da zan iya fada muku game da rayuwa ta cikin dawa na girma ,nan ne gida na birrai datsuntssye sune suka zamo dangina bani da kowa sai malamina.bansan inda iyayena suke ba,kullum ina addu'ar Allah ya haɗani dasu"ta kai karshen zancen ta tana mai share hawayen dake zuba cikin idonta.

Shiru falon yayi kowa yana tausayin Islam da iri. Gwagwarmayar da tasha,lallai dole ayiwa Islam uzuri game da rayuwar ta.
Granny ne ce ta fashe da kuka tana mai kamo Islam zuwa jikinta. "Allah sarki Islam, kinga rayuwa Allah ya bayyana iyayenki,ya saka muku abinda waɗan nan mugayen sukayi muku,amma da alama malamin nan naki ba mutum bane,wani bawan Allah ne cikin aljanu yake taimaka miki Allah yasa ma Ni dai ina ƙaunar ki,dan kar watarana ya maidani kunkuru" cewar grannay tana dafe ƙirji da yarfe hannu.saida ta sanya kowa yayi murmushi agurin,wai karya maidata kunkuru.
"Haƙiƙi Islam rayuwar ki abar tausayi ce,amma in sha Allahu komai yazo ƙarshe,zamu kula dake cikin aminci,sannan zamu ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana iyayenki,sannan zamuyi ta cigiyarsu har Allah ya bayyana mana su.ki ɗauke mu ahalin yanzu mune ahalinki,kuma yan uwanki, domin kin zamo daya daga cikin mu.
Bayan haka kuma,nasan zaki so sanin namu tarihin dan haka zan sanar dake asalinmu,sannan zan nemi alfarma guda daya agareki,ina fatan zan samu?cewar Daddy Yana kallon Islam.
"Ina sha Allah daddy nayi maka alƙawarin zan yi maka duk abinda ka nema agurina in har ina dashi,zan baka"inji Islam cikin sanyin murya.

Ajiyar zuciya daddy Yayi kafin yace "alhmdllh Nagode ƴata.da farko dai kamar yadda kika gani yara na hudu Aslam,Aman ,jannat sai auta hanan,Ni dan asalin garin gumel ne dake cikin jahar Jigawa,zama da kasuwanci ya kawo Ni Abuja,matata daya Hajiya sadiya,ga mahaifiyata Hajiya Khadijah,mu biyu ta haifa ,amma ahalin yanzu saura Ni kadai,mahaifina ya rasu tun kafin ahaifi Aslam,sannan Hajiya sadiya yar Kano ce ,ta kasance ya ga aminin mahaifina,yan uwanta gaba ɗaya suna can kano.wannan shine taƙaitaccen tarihin ahalina.
Sai kuma taimakon da nake son kiyi min-yay shiru yana kallon yanayin Islam,wacce ta maida hankalin ta gaba ɗaya kan daddy.
Kafin yaci gaba.
Ina son ki taimaka ki auri ɗana Aslam,nan da watan biyu masu kamawa"
Ɗif!!kake ji duk wani motsi dake cikin dakin ya dauke,sakamakon daina bugawar numfashin su na wasu yan dakikai.
Gurum Aslam yayi yana kallon daddy,so yake ya kara tabbatar da abin da kunnensa yaji masa,kai sharrin iska ne ma ,ta dauko masa wata shirmen magana zuwa kunnen sa,hakan ba mai taba yiwuwa bane har abada.dan haka sai yayi ɗan murmushi tare da dafe ƙirjinsa dake wata irin bugawa kamar zai fashe.cikin zuciyarsa yace "kai zuciya ma bata da ƙashi,ko menene ya kawo min wannan shirmen mai kama da wasan yara?"
Aman kuwa baki buɗe cikin bugawar ƙirji yake kallon daddy da mommy tare da granny,ko kaɗan ba wata alamar damuwa ko mamaki akan fuskar su,alamu dai sun nuna cewar sun san da maganar, shike nan,ya rasa Islam,yayi dakon soyayyar ta abazan, innalillahi yanzu yaya Aslam ne zai auri Islam ba Ni ba?ya Allah ka cire min soyayyar ta daga zuciyata"Aman ya faɗa cikin zuciyar sa ,yana jin idon sa na kawo kwalla,da sauri ya sanya bayan hannunsa cikin dubara ya goge ba tare da kowa ya gani ba.
Jannat kuwa da hanann,kallon juna sukayi cike da mamakin daddy,ta yaya zai hada aure tsakanin ya Aslam da Islam,bayan kowa yasan rashin jituwar dake tsakanin su,impact ma sam Islam ba ajin sa bace,ya Aslam da yan mata ke rububi akan sa,shine za'a haɗashi da wacce tayi rayuwa cikin jeji tare da dabbobi?tan,lallai akwai drama.

Islam kuwa shiru tayi tana kallon daddy,zuciyar ta cike da wani tunani,ita dai bata shiryawa aure yanzu ba,kuma tana jin nauyin ƙin amsar maganar da daddy yazo mata da ita,amma dole zata bashi hakuri,badan komai ba,sai dan bazata iya zama da Aslam matsayin miji ba,tab me ma zatayi da wannan baƙin mai kama da buhun hatsi,dama dai ace Aman ne to koba komai zata amince saboda shi yana da kyakykyawar zuciya,amma wannna !ƙila ma yabi dare ya danne mata hanci da filo ta mutu.

"Karki damu Islam,bazan takura miki cewar saikin bani amsa yanzu ba,zan baki cikakkiyar dama kiyi nazari akan magana ta ,sannan ina so kiyi min kyakykyawar fahimta,banyi hakan da nufin cutar dake ko wani abu ba,nayi hakan ne bayan dogon nazari da tunani,sannan saida na shawarci mommyn ku da Hajiya ta,dan haka ki kwantar da hankalin ki,duk amsar da kika bani bazata ɓata min rai ba.
Kai kuma aslam,wannan umarni ne, agareka,muddin Islam ta amince da batun auren nan,to baka da wata mata sama da ita,wannan shine hukuncin dana yanke,zaku iya tafiya dukan ku"daddy ya faɗa yana jingina da jikin kujera.
Kallonsa kawai Aslam keyi,wai shin da gaske ne abinda kunnen sa suka jiye masa?aure daddy ke son hada shi da wannan yarinyar yar jeji?waya sani ma ko karya take labarin data faɗa musu, yawon duniyar ta kawai ta fito,lallai kuwa akwai tashin hankali mai girma cikin gidan nan,kuma wllh shidai bazai amince da wannan haɗin gambizar ba,haba yana za'a ce kamar shi Aslam Mahmud kabir,ya rasa wacce zai aura sai wannan kidahumar? impossible "
"Ko kana da magana ne Asalamu naga ka kasa tashi,bayan kowa ya watse?ko ja'ircin zaka mana,ai wllh ka godewa Allah ma,daya baka wannan zankadediyar yarinya son kowa ƙin wanda bai samu ba,yo iya binciken ka ai baka isa ka samo ya ita ba,ai wllh naso ace Amanu ne ya samu yar nan,yaro mai nutsuwa da hankali"cewar granny tana ballawa Aslam harara tare da turo dan kwali.

Shidai Aslam kallon ta kawai yake ,ba tare da ya fahimci me take faɗi na,dan zuwa wannan lokacin hankali da tunanin sa sam basa jikinsa.
Kallon sa ya maida kan mommyn sa,kallo yake mata na neman karin bayani,amma saita yi saurin kawar da kanta gefe guda.
Dan haka ya kara tabbatar da abin da kunnen sa yajiye masa gaskiya ne,lallai dole ya samo mafita tun wuri kafin lokaci ya kure masa.tashi yayi cikin zafin nama kamar zai tashi sama ,haka yake tafiya ya bar ɗakin na daddy.kallo daddy yabi sa dashi kafin ya girgiza kai,yana faɗin yaro gata nayi maka,bazaka gane hakan ba sai nan gaba.

Ba kowa afalon lokacin da ya fito,tsayawa yayi yana tunanin inda zai gano Islam,sai huci yake kamar zaki,dai-dai lokacin ita kuma ta fito daga kitchen dauke da robar ruwa mai sanyi.
Batayi aune ba kawai taji an fizgota tare da yin waje da ita.
Janta kawai Aslam keyi da mugun sauri,ita kuwa binsa take har da ɗan gudu,dan yafita saurin sosai.
Bai zame da ita ko ina ba sai garden.yana zuwa ya hankaɗota zuwa gabansa,saura kaɗan ta fadi kasa tayi saurin dafe bishiyar dake bayan ta.
Ɗago kai tayi tana kallon sa cikin haɗe rai da jin haushin abinda yayi mata.
Aslam kuwa saida ya ƙare mata kallo cikin ƙasƙanci kafin ya jinjina kai tare da nuna ta da hannu kamar kashi.
"Ba doguwar magana zanyi dake ba,kawai zan gargadeki ne,sannna in baki umarni,akan kada ki sake ki amince da wannan auren tatsuniyar,domin Ni Aslam ba sa'an auren ki bane,how comes ma?za'a haɗani aure da ke,ke wacece?me kike dashi?me zan aura ajikin ki?jaka kidahuma wawiya marar aji irin ki,Ni Aslam ace zan aura?wllh ko mata sun ƙare nafi ƙarfin ki,so kema nasan kinsan da hakan,dan haka ki hanzarta dakatar dasu,da wannan shirmen da suke son haɗawa Aslam is not your type"Yana gama faɗin. Haka ya tofa mata yawu tare da barin gurin.

Wani irin hucin bakin ciki Islam keyi,zuciyar ta kamar zata fashe,tsabar takaici da haushi kawai ta kama dukan bishiyar dake gefen ta tana kuka,
"zakaga irin hukuncin da zan ɗauka akan ka,nima bana sonka me zanyi da kai mugu kawai ƙaton banza,wllh saikayi dana sanin fadamin wannan baƙaƙen maganganun,zaka gani"ta faɗa da ƙarfi tare da nufar cikin gidan kamar zata tashi sama,kai tsaye part ɗin daddy ta nufa...


Mezatayi a part din daddy,karfa tace bata son Aslam?
Hmmmm muje zuwa masoya.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: _______________Zaro ido sosai Aslam Yayi cikin mamaki da tsoro,mamakin nashi ba komai bane face,ganin Islam kwance maɗe-maɗe akan gadon sa.
sannan abinda ya bashi tsoro kuma,ganin biri shima kwance akan gadon nashi,da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji.lallai yarinyar nan ta cika hatsabibiya tama rasa inda zata kwanta,sai kan gadon sa?kuma bayan haka harda biri?

Cikin ɓacin rai ya nufi inda Islam ke kwance,yana zuwa baiyi wata wata ba ya sanya hannunsa ya finciko ta tare da jefar da ita aƙasan dakin. Cikin huci yake kallon Islam,wacce tayi firgigit ta tashi aɗan tsorace,dan barci ya fara kamata kawai ta jita aƙasa.
"Har ke wace ce?da zaki hau min kan gado,da wannan ƙazamin jikin naki?how dare you?ya faɗa cikin tsawa, dan zuwa wannnan lokacin Aslam ya gama ƙufula sosai da Islam,baya kuma tsoron duk abinda zai faru,dole ya koya mata hankali.

Kallon sa Islam keyi cike da tsantsar haushin yadda ya wani cillar da ita a ƙasa kamar kayan wanki, "akan me zaka cillar dani haka kamar wata dabba? Dan kawai na hau wannan banzan gadon naka?"Islam ta fada cikin jin haushinsa .
"Saboda baki da mara ba da dabbar agareni,ke shaiɗaniya ce marar hankali,jaka kuma mahaukaciya,kisani duk abubuwan da kike min bawai ina tsoron ki bane,ina gudun ɓacin ran mahaifa na ne,wllh da tuni na gama da ke, dan ke ba komai bace face ƙaramar alhaki,na tsane ki! Bana ƙaunar ganin ki,ahalin yanzu kaf duniya bani da wanda na tsana sama dake ahate you ƴar bariki wacce bata sami tarbiyya ba"Aslam ya kai ƙarshen maganar sa da tsawa, kamar zai fasa mata kunne.

Kallon sa kawai Islam keyi,idanun ta sunyi jaaa sosai,haƙiƙa maganganun Aslam sun shiga zuciyar ta,sun matukar dukan ta,zafin da take ji cikin ranta kuwa,Allah ne kadai ya san iyakar sa.
Kallon kallon suke tsakanin su,ko wannen su,zuciyar sa cike da tsanar dan uwansa.
Ahankali Islam ta daga kafar ta ta fara tahowa zuwa gareshi ,sai da tazo gab dashi kafin ta tsaya.idanunta har lokacin yana kan kyakykyawar fuskar Aslam,ajiyar zuciya ta sauƙe mai zafi tare da huro iska daga bakinta,kafin ta fara magana.
"Kayi munanan kalamai akaina,ba tare da sanin ko niɗin wace ce ba,ka zage ni, ka kirani da karuwa marar kamun kai,sannan ka zagi iyayen na,kace basu bani tarbiyya mai kyau ba,ina so kasani,kamar yadda kake kallon iyayen ka matsayin waɗan da suka raine ka da tarbiyya haka nima nake kallon nawa iyayen,domin tarbiyyar da suka bani itace ta sanya na kawo har wannan lokacin cikin mutunci,abu guda dana sani shine,ba wani mahaluƙin da zai cutar dani in gyale shi,sannan wannan gidan naku bani na nuna ina da ra'ayin zuwa ba,baban ka shine wanda ya takura Ni akan saina biyo shi,bana son shiga cikin mutane ,saboda marasa adalci irinka,baku da wani buri daya wuce tozarta mutum,da son cutar da rayuwar sa.ka sani Aslam na tsane ka,kamar yadda ka tsane ni, bana ƙaunar ganin ka, i hate everything about you,Kaine mutum na farko daya fara sanya Ni kuka,kuma zakayi dana sanin aikata hakan,kuma kasani nasan duk halin da kake ciki,da sannu zan tona maka asiri gurin iyayenka da kake yaudara,janbu zo mu tafi"Islam ta kai ƙarshen zancen ta tana share guntun hawayen daya zubo mata tare da nufar ƙofar dakin.
Harara Aslam ya bita dashi yana faɗin"wllh duk ranar da kika ƙara zuwa dakina saina illata ki,banza useless kawai marar hankali"
Juyowa Islam tayi ta kafa masa idanu,kafin tace "wannan na saka shi cikin raina,duk lokacin dana bukaci zama cikin ɗakin nan naka,to tabbas zan zo kuma zan huta cikin sa, ba ɗan iskan daya isa ya hana ni"tana kaiwa nan azancen ta tayi waje da sauri.

Duka Aslam ya kaiwa bango cikin ɓacin rai yake faɗin."I hate you na tsane ki bana son ganin ki"ya faɗa da ƙarfi yana ƙara kaiwa bango duka .

Islam tana fida daga ɗakin ta nufi dakin granny,bayi ta shige da sauri,tana zuwa ta kunna shaya tare da zamewa gefe guda ta zauna tana mai sakin kuka.kuka take sosai tana mai tuna iyayen ta sosai yau ɗin nan take jin mugun kewar su,ƙaddara ta raba ta da su ta kawo ta inda ake zagin su da faɗa mata munanan kalamai.
"Wllh bazan Barka ba Aslam,saina ƙuntata rayuwar ka,saina hanaka farin ciki,kamar yadda ka sanya Ni kuka"Islam ta faɗa da ƙarfi cikin kuka. Ta jima tana kuka atoilet,kukan da zata iya rantse wa bata taɓa yin irin sa ba,tun da take arayuwar ta.amma yau silar Aslam ta zubda hawayen ta,ta yaya zata gyale shi?

Aslam kuwa gaba ɗaya tsantsanin gadon da ɗakin ma gaba ɗaya yaji yanayi,dan haka cikin takun dingishi ya bar ɗakinsa zuwa dakin mommy.
Tun daga wannan rana kuma ya fita harkar Islam,ko da wasa baya barin wata damar da zata haɗa su da Islam,baya ma zaman gidan,tun yana dingisa ƙafar sa har ya zo ya take ta,idan yana gida ma,to zaka sameshi part ɗin daddy, Dan baya son abinda zai haɗashi da Islam,sosai yake jin tsanar ta cikin ransa,baya ƙaunar ganin ta.

Bangaren Islam ma sam bata son ganin Aslam ahalin yanzu,bata zama cikin gidan ma,rai da rai tana garden,ita da janbu,suna kan bishiya.damuwa tayi mata yawa,tana matuƙar son ganin malamin ta,amma shiru tun daga ranar nan,bai ƙara zuwa gare ta ba.

Yau sati biyun da daddy ya ɗibarwa Aslam suka cika,dan haka suna zaune shida mommy apart ɗin sa yace"Madam,yau ne adadin kwanakin dana ɗibarwa ɗan ki ya cika,dan haka akira min shi ɗan jin inda zancen mu ya kwana"ya kai zancen sa yana canja tashar labarai.
Shiru mommy tayi bata ce komai ba,sai wayar ta kawai data ɗauko tare da kiran wayar Aslam,tana tunanin da wuya idan Aslam ya samo matar da zai aura kam,dan tasan halin Aslam Sarai .
Lokacin da mommy ta kira Aslam Yana ɗakinsa, wanda shigar sa kenan,yayi wanka.yana sanye da jallabiya kasancewar magrib ne lokacin,turare kawai ya feshe jikinsa da shi,ya fito.
Yaran gidan duka suna falo,banda Islam,shi wllh yanzu har mantawa yake da wata Islam,dan tun ranar da wannan abun ya faru bai kara sanya ta cikin idanun sa ba.dan ko abinci baya fitowa falo yaci,Gara ya ci abin sa

Please Login or Register in order to submit comment