Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito ba,shi Daddy ma ba ruwansa da sanin asalin ta,kawai burin sa yayi aure,shine yake son hada zuri'a da ita.
ɗan juyowa yayi ya kalli Islam,wani bakin ciki ne ya ƙara turnuƙe masa zuciya,ganin yadda take wani hura hanci kamar wata tsiya, ji yake kamar ya shaƙeta ya huta.

"A'a wai ya haka ne?meye kuma zaka wani rinka satar kallo na?wllh kurwa ta kurr,inkai maye ne kaci kan ka,haka kawai da wanne zanji?ga wannan marin da motar keyi na gardawa, duk ya dameni, ji nake kamar nayi amai,kuma bazaka barni da wannan bala'in haka ba,saika kafamin wannan idanun naka,masu kama da kana jin barci?to bana son kallo ehe,ni.....

Bata sami damar ƙara sa wa ba,sakamakon buge mata baki da Aslam yayi cikin fushi.
"Wllh idan ki ka ce zakimin rashin kunya anan zane ki zanyi in cillar dake agurin nan,banza fitsararriyar yarinya kawai"Aslam ya fada cikin fushi yana jifan Islam da mugun kallo.

Islam kuwa kallon sa kawai take tare da riƙe bakin ta,ranta yayi mugun ɓaci.
"Wllh bazan yafe maka ba,mugu kawai,haka kawai kasanya wannan hannun naka mai kama da shebur ka kwaɗamin abakina? Allah saiya saka min wllh"ta faɗa cike da jin haushin sa.
Shima cikin jin haushin yadda take masa rashin kunya,ko tsoron sa bata ji yace "wllh idan baki rufemin baki ba zan yi maganin ki ne agurin nan,wawiya daƙiƙiya marar hankali kawai uban waye yace da kishigo motar?tunda qarin gardawa take?saidai inkece gardiyar da tasanya motar wari,dan kuwa ke kin ma fi bunsuru wari"ya fada cikin mugun fushi yana figar motar da mugun gudu.
Ji kake ƙummm!!
Kan Islam ya bugu da jikin kujerar,da sauri ta dafe kan nata tare da runtse ido.
"Wllh duk baƙin cikin ka sai dai kayi ka barni amma nidai nan gani nan bari,kuma bazan fasa faɗin kai mugu bane,dan ba tsoron ka nake ji ba wllh sai Allah ya saka min kuma wllh ni bana wari koda ban sanya turare ba,dan Ni bana amfani da banzan turare na ƙasar nan ma "Islam ta fada afusace idanun ta na kawo ruwa,Amma tsabar taurin rai irin na Islam tayi saurin maida hawayen .

Hannu Aslam ya sanya akaro na biyu ya ƙara buge mata baki har saida lips ɗin ta ya fashe.
Kuka Islam ta sanya tana mai kallon jinin data gogo daga lips dinta,cikin kuka da jin haushi ta kama dukan Aslam tana faɗin "Allah ya isana mugu,kalli yadda ka fasamin baki?wllh sai na rama,bashi ka ɗauka azzalumi kawai"Islam ta fada cikin kuka tana dukan gefen kafadar Aslam.
Tsayar da motar Aslam Yayi dai-dai sun kawo bakin store ɗin,wanda yake mallakina Aslam ɗin ne,dan haka haɗe hannayen ta yayi guri ɗaya tare da zaro manyan idanunsa da sukayi jaaa,saboda ɓacin rai yace "wllh idan baki nutsu ba zan miki dukan tsiya cikin motar nan,kuma in jefar dake anan gurin bani da asarar komai,banza maƙarya ciya,gidan uban wa kike shafa turaren kasar wajen ? Gara ki min shiru ,ki nutsu,dan nan ba gida bane,inkin ga dama ki fito "yana faɗin haka ya warɓar da hannayen nata tare da ɓude motar yayi ficewar sa.
Bakin ciki kamar ya kashe Islam,wllh bashi ya ɗauka,saita baƙanta masa kamar yadda ya baƙanta mata itama,kuma wllh duk baƙin cikin sa, saiya siya mata ƙayan nan,kuma wllh lodar kayan zatayi dan yayi asarar kudin sa.tana gama wannan tunanin tayi saurin fitowa tare da bin bayan sa, tana share hawayen da ya maƙale gefen idon ta,dama kukan nata ba wani hawayen kirki.

Lokacin data fito harya kusan shigewa cikin store ɗin,dan haka da sauri ta cimma sa, tana balla masa harara.

Juyowa yayi ya kalle ta cikin yatsina yace "ashe dai zaki fito ƙaramar tsagera"
"Ai badan kai na fito ba,ra'ayin kaina ne yasa na fito"ta faɗa cikin tsiwa tana murguda masa baki.
Banza yayi da ita suka shiga cikin store ɗin,aikuwa nan da nan ma'aikatan gurin suka fara gaida Aslam,cikin girmamawa da nuna farin cikin su,dan ya jima baizo gurin ba,komai ta online yake gudanar wa.
Taɓe baki Islam tayi ganin yadda suke ta wani girmama Aslam,
Cikin jin haushin su tace "aikin banza wahalallu marasa aikin yi,ku rasa wanda zaku girmama haka sai wannan saƙaƙon,mtssss"ta buga uban tsaki tana riƙe ƙugu.

Sukan basu fahimci inda zancen nata ya dosa ba,amma shikam oga Aslam, Sarai ya gane da shi take,banza yayi da ita gudun karta tsinkashi gaban ma'aikatansa,
Ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin mata ya umarta akan ta raka Islam ta zabi abinda take bukata.
Shi kuma ya shige wani ɗaki.

Aikuwa cikin girmamawa matar wacce zatayi sa'ar jannat tace "to ƙanwata muje ko"ta faɗa cikin sanabe tana kallon Islam da murmushi.

Wani banzan kallo Islam ta wurga mata kafin tace "ke dalla Malama bana son iyayi,wacece ƙanwar taki?kinga nayi kama da ƙanwar ki?kije can ki nemi ƙanwar ki ba Islam ba,bana son shishshigi,ki wuce kawai kiyi abinda aka saki"Islam ta fada cikin yarfi.
Aikuwa sosai budurwar nan taji kunya tare da haushin Islam, dan ma ba mutane agurin, ita tunanin ta Islam ƙanwar Aslam ce,ita kuma aduniya tana bala'in son Aslam, shine take son kama ƙafa da Islam ɗin,saidai taga wannan yarinyar bata da kunya.dan haka simi-simi ta ja babban kwando tare da yin gaba Islam tabi bayan ta.

Ba ƙaramin kaya Islam ta debo ba, dan kwandon ma saida yayi kaɗan ta riƙo wasu ahannun ta.
Budurwar nan sai hararar Islam take ,ba damar yin magana dan tana tsoron rasa aikin ta.
Haka suka zo gurin biyan kudi aka lissafa, kuɗi sun doshi dubu dari uku da hamsin,dan kaya masu tsada Islam ta zabo,wasu ma ba amfani zatayi da suba,kawai ɗiba take tana zubawa cikin keken,banda gayyar ƙananan kaya data lubgo,da kayan cinye -ciye.

Koda aka fadawa Aslam kuɗin kayan mamaki yayi sosai,amma bai nuna damuwa ba,ya basu atm yace su cira, duk da sun nuna ba sai an karbi kudin ba,amma yace a'a su cire kawai.
Haka aka loda kayan cikin Boot ɗin motar Aslam.
Ta jima zaune cikin motar tana ta cin chocolate ɗinta,data ɗauka cikin waɗanda ta lubgo,kafin Aslam ya shigo cikin motar.
Kallon ta yayi yadda ta ke cin chocolate ɗin ta hankali kwance.
Kafin ya jinjina kai ya tada motar.haushi fal cikin ransa.

Maimakon suyi hanyar gida sai kawai Aslam ya wuce gurin shagunan sa,da ake dinka zallar hulunan sawa, masu kyau da tsada,suna tafiya ta buga wani uban tsaki wanda yasan ya Aslam saurin juyowa ya kalle ta.
Cikin haɗe rai tace "kaga malam dan juya kamaidani wancan shagon,dan nayi mantuwa,naga wata alawa kuma ban ɗauko ba" ta faɗa kamar tana bashi umarni.

"Saboda ubanki ne ya bani kuɗin ko?baki san zafin neman su ba kika kashemin kudi wajen kwata million sannan yanzu kice in koma zaki ɗauko alawa,ai ko da kuɗin babanki na gina store ɗin baki isa ki sani na koma baya ba"ya fada cikin ɓacin rai.

Sai lokacin Islam ta san wai ashe gurin ma nashi ne.duk da zagin uban ta da yayi, ya matukar ƙona mata rai amma saita haɗiye ɓacin ran tace "kash!! Wai kana nufin gurin ma namu ne?amma me yasa baka faɗa min ba? Ai wllh da yau duk wanda taje siyayya gurin bazai biya ko sile ba,amma ba komai za'a tara gaba, abu namu maganin akwabemu,bari nayi saurin shanye waɗan nan uban alawowin dana ɗebo in yaso saina sake sabon shiri"ta fada cikin murmushi idon ta akan Aslam,Wanda yayi galala yana kallon ikon AllahWato ma ita abinda tayi bai dame ta ba,wata barnar take ƙoƙarin sake yi masa?hmmm,ya ga da uban da zata dawo store ɗin.
Ƙyale ta yayi baice mata komai ba,dan gani yake magana ma da ita ɓata lokaci ne,dan haka yayi mata banza,tana ta neman maganar ta,har ta gaji tayi shiru ganin bazai kula ta ba,haka tayi ta shan chocolate ɗin nan,data shanye zata ɗauki wata.

Har suka zo gaban manyan shagunan nashi,buɗe motar yayi tare da ficewa,kuma ya kulle motar,koda Islam tayi yunkurin fitowa ,akulle taji ƙofar,tsaki tayi tace "aikin banza ya kulle motar,ko nufin sa inyi zaman jiran sa anan?kamar wata baiwar sa?to uban me ma zaiyi agurin nan,maimakon ya kaini gida shine ya wuce yawon karuwancin sa dani,dan gurin nan da da gurin karuwai yayi min kama,gashi nasan janbu yana can yana nema na"ta fáda tana wani taɓa baki tare da gutsirar chocolate ɗin ta.

Shikuwa Aslam,Yana zuwa shagon suka gaisa da ma'aikatan sa ,cikin mutunta wa da girmamawa,kai tsaye ya wuce babban office ɗin da yake zama idan yazo.
Office ne haɗaɗɗe mai kyau,harda ƙatuwar katifa ta huta wa,dan haka,bayan sun kama lissafin kuɗi da managern sa na gurin,kan karifar ya haura tare da kwanta wa, tunani kala-kala cikin ransa,yanzu idan ya auri yarinyar nan,ya makomar auren nasu zata kasance?shin akwai ƙa'idajjen lokacine da zai sake ta ko kuma zama zasuyi tayi har abada?amma ta yaya zama zaiyi ahaka?bata sonshi,shima baya sonta?Allah yasa anayin auren suga iyayen ta, sukuma suce basu yarda da aurar musu da yarinya da akayi ba,dan haka dole ya sake ta,shikenan komai zai zo masa cikin sauƙi, ya zama dole gareshi ma ya fara neman iyayen nata cikin sirri,ta yadda zasu bayyana cikin sauri koma kafin ayi auren,amma ta yaya zai zauna da mace kuma ba tare da yana samun nutsuwa da ita ba?shidai bazai taba zubar da girmansa yazo gurin wannan abar da sunan neman hakkin sa ba,tabb!! ALLAH ma ya kiyaye wannna ranar.
gashi yayi alƙawarin bazai ƙara ƙetare gonar da bata saba,duk da shi iyakarsa romance ne,amma yaga illar yin hakan,kuma ya tuba, Wanda Yayi abayama Allah ya yafe masa.
Haka Aslam yayi ta saka da warwara cikin ransa,yana cikin haka barci ɓarawo yayi gaba dashi.

Islam kuwa tun tana cin chocolate ɗin nan cikin marmari, har tazo ta fara gundurar ta, gaba ɗaya ta zubar masa da bawon chocolate har Kan seat din da yake zama,kuma duk dan neman magana tayi,ta ɗora ƙafar ta akan gaban motar.
Tsaki ta farayi ganin har lokacin bai dawo ba,sai masifa take ita kaɗai cikin mota,Bama wanda yasan da mutum cikin motar,tunda irin baƙin glass ɗin nan ne ajikin motar.
"Aikin banza kawai,yazo ya shanya mutane cikin wannan akwalar motar tasa ya tafi yawon karuwan cin sa,wllh zai dawo ya sameni,saiya bani bayanin inda ya tafi ya barni cikin wannan gwangwani nasa,anfaɗa masa Ni mai gadi ce?mugu kawai "Islam ta faɗa cikin jin haushi kamar ta kwalla ihu,dan kusan awarta ɗaya cikin motar bai dawo ba.
Wasa-wasa Islam fa tayi awa kusan uku cikin motar,ga yunwa da ciwon ciki dake damun ta, dan ba shan wasa tayiwa wannan chocolate ɗin ba,gashi dama ƙarshen wata ne,riƙe take da cikin ta tana juya kai,dama irin wannan lokacin tana shan wahala idan zatayi period,bare kuma yanzu ta haɗa da zaƙi.
Sai murƙususu take rike da cikin ta,tun tana daure wa,har ta fara kuka tana ambaton sunan Allah"innalillahi wayyo Allah cikina,zan mutu! wayyo baya na la'ilaha'illallahu muhammadar rasulullu, Wayyo Allah na, cikina !ciki!!abinda Islam ke ta faɗa kenan tana rike da marar ta dake azabar ciwo kamar zata balle tana kuka.
Gashi wannan lokacin ba malamin ta,dama shike bata magani da ta fara wannan ciwon.
Yanzu kuma ba mataimaki sai Allah,inka ganta saita baka tausayi,nan da nan lokaci ɗaya tayi ramar dole kamar marar lafiya
Aslam kuwa bai farka daga wannan nannauyan barci ba,saida aka fara kiran sallah,ahankali yayi miƙa tare da karanta addu'ar tashi daga barci tare da buɗe idonsa.
"barci nayi kenan?"ya fada cikin cool voice,kafin ya mike ahankali,ya shiga toilet,alwala yayi bayan ya kama ruwa,ya fito,saida ya gabatar da salla yana zaune kafin ya tuno da Islam cikin mota.dafe kai yayi da sauri yana runtse ido,harga Allah ya manta da ita, da sauri ya duba agogon Rolex dake hannunsa,kusan awa huɗu yayi yana barci, subhanallah,idan wani abu ya same ta cikin mota fa?ko kuma tana buƙatar yin wani uzurin? Wayyo sam baiji daɗi ba,dan bashi da nufin cutar da ita irin haka.da sauri ya mike ya zari wayar sa da car key Yayi waje cikin hanzari.
Yana zuwa ya buɗe motar yana kallon inda take zaune,
Cikin tsoro da firgici ya shiga cikin motar tare da zaro ido ya kallon islam cikin tsoro.
Dan zuwa wannnan lokacin tuni Islam ta sume tsabar zafin ciwo,hannun ta rike da marar ta,ta ɗora kanta akan seat ƙafafun ta dire aƙasan motar.
Cikin tsoro da hanzari Aslam.ya dagota yana jijjiga ta, cikin tashin hankali ya fara kiran sunan ta karon farko arayuwarsa" ke ISLAM !buɗe idonki mana,menene ya sameki?Islam !Islam!!ya faɗa cikin ruɗu yana jijjigata, innalillahi karfa yarinyar nan ta mutu?me zai cewa su mommy? "ya salam" ya faɗa yana haɗata da jikin sa ya rungumeta tsam yana jin wani irin zafi cikin ransa.....

Muje zuwa masu karatu


Mrs babi ce
Anty mammy.[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: ______________Ta cikin motar Aslam ya kalli tayoyin motar tashi,cike da mamiki yake kallon tayoyin dake asace.
Da sauri ya ɗago kansa yana kallon Islam dake tsaye tana kaɗa masa car keys ɗin dake hannun ta,fuskarta ɗauke da murmushi.
Duk da aslam yasan cewa dama Dole Islam sai ta ɗauki fansar abinda ya faru,dan bazata taɓa barinsa ya tafi amatsayin tsautsayi ba,amma bai taɓa tsammanin zata rama ta wannan hanyar ba,wato ta kulleshi cikin mota,bayan kuma ta sace tayoyin motar gaba ɗaya.
Islam kuwa murmushi take ta yi tana tsaye gaban motar ta yadda Aslam zai hangota sosai.
kissing ɗin tafin hannun ta tayi tare da hura masa iskar alamun kiss.sannan ta kashe idon ɗaya tare da juyawa tabar gurin tana murmushi ga car keys ɗin ahannun ta.
Yana kallo ta bar gurin ba yadda ya iya.
Da ƙarfi ya daki sitiyarin motar tare da lumshe ido ya jingina kansa jikin kujerar motar.
Bai taba tsammanin Islam zata yi masa wannan ɗanyen aikin ba,kuma ai ya bata hakuri,sannna bada niyya yayi mata ba.yanzu ya zaiyi gida ba kowa?gashi baba mai gadi yana can bakin get kuma akwai tazarar da ko yayi wani yunƙuri,sam baba mai gadi bazai jishi ba.
Cikin sauri ya zaro wayarsa daya ɗauko adaki.
Zaro manyan idanun sa yayi tare da kafe wayar da ido,sakamakon yadda yaganta tayi kwatsa-kwatsa,gaba ɗaya an fasa creen ɗin wayar.
Waya mai matuƙar kyau da tsada,wacce ta kasance sabuwar shigowa dan dai-dai kun mutane ke da irin ta.sannan akwai abubuwan sa masu matuƙar muhimmanci aciki.amma yanzu kalli wayar yadda ta tashi daga aiki?dan ko kunnuwa taƙiyi, Lokacin daya ɗauko ta sam baiga wannan aikin da akayi mata ba,dan yana zarowa ya cusa cikin aljihunsa.
Waye yayi masa wannan aikin?shiru yayi yana tuno abubuwan da suka faru daga safe zuwa yanzu.
Tabbas Islam ce,dan yaganta dazu aɗakin sa,ashe ba mafarki yake ba da gaskene? Lokacin yana barci,ya ganta cikin dakin,sam bai kawo aransa Itan bace yayi tunanin mafarki yake,dan barcine sosai cikin idonsa.
to lallai awannan lokacin tayi masa wannan danyan aikin.

Shiru Aslam Yayi zuciyar sa na bugawa da ƙarfi cikin ɓacin rai,ahankali ya lumshe idonsa tare da sakin ajiyar zuciya akaro ka barkatai.kawai saiya kwantar da kujerar da yake kai yayi kwanciyar sa aciki motar. bayan ya ƙara gudun ac.
Duk yadda yayi ƙoƙarin kawar da ɓacin ransa, ya kasa.nan da nan idanun sa sukayi jaaa sosai,tunanin irin hukuncin daya kamata yayi wa Islam yake,amma duk hukuncin daya yanke,sai yaga yayi mata kaɗan.

Haka Aslam yayi ta zama cikin motar nan,zuciyar sa kamar ta kama da wuta,gashi har magrib ba wanda ya dawo gidan.

Islam kuwa tana can gurin granny Suna ta hira da dariya.amma bata shigo dakin granny da key ɗin motar ba, saitayi saurin shiga ɗakin Aslam ta ajiye makullin akan madubi tana dariya sosai.kafin ta tafi ɗakin grannyn.

Saida ana kiran sallar ishsha sannna su mommy suka dawo.can nesa da Aslam motar su tayi facking suka fito,da sauri Aslam ya tashi yana ɗaga musu hannu,amma kasancewa glass ɗin baƙi ne, sam basu kula dashiba suka wuce cikin gida suna labarin bikin.
Dukan sitiyarin motar Aslam yayi da ƙarfi tare da ɗanna horn, amma tuni sun shige har sun kulle ƙorar falon.
Ajiyar zuciya Aslam Yayi,ji yake kamar yayi kuka,amma yayi alƙawarin bazai nunawa Islam yaji haushin abinda tayi ba,zai barta ahalin yanzu har sai ranar da aka ɗaura musu aure,anan zata gane bata da wayo.
Cikin Sa'a saiga Aman ma ya dawo.dan haka cikin sauri Aslam ya fara yi masa horn.

Fitowa Aman Yayi yana kallon motar yace "to yaya kuma me yakeyi cikin mota har wannan lokacin?bari na gani ko lafiya?naga yana min horn"
Aman ya fada yana nufar motar.
Yana zuwa ya fara ƙoƙarin buɗe motar amma yaji ta akulle,ɗaga kai yayi ya kalli yayan nashi dake mai alamun ya buɗe motar.
Rubuta masa Aslam Yayi cewar,akulle motar take,kaje gurin Islam ka karɓo makullin kazo ka budeni.
Ya nuni masa ta gaban motar.
Cikin mamaki badai kulle shi Islam tayi ba ?Aman ya kalli yayan nashi,jinjina masa kai yayi alamun yaje ya karɓo.
Da sauri Aman ya nufi cikin gidan yana jinjina hali irin na Islam,ya rasa mai yasa take wa yayan sa haka,sam bata tsoron Aslam,duk abinda ta ga dama shi take ma,kuma ahaka ake ƙoƙarin haɗa su aure.
Ba kowa cikin Falon, kasancewar mu mommy ɗakunan su suka wuce dan gabatar da salla.
Dakin granny Aman ta wuce,dan yasan Islam na can.
Lokacin daya shiga granny na sallah, Islam kuma tana zaune tana kurbar tea.
"Islam Ina car keys ɗin yaya Aslam?"Aman ya fada daga tsaye yana kallon ta.
Ɗago kai tayi ta kalle shi, ita sam tama manta da batun Aslam wllh,ashe shegen yana nan cikin mota?murmushi Islam tayi kafin tace "ya bani ajiya ne zaka tambaye Ni?"ta faɗa tana kurbar tea ɗin ta.
"Please Islam ki sanar dani inda key ɗin yake koba komai ya fito yayi sallah?"aman ya fada cikin sigar rarrashi.
"To kaduba ɗakin sa mana koyana can,Ni meye zanyi tayi da key ɗin motar sa ahannuna har yanzu ?kaduba kan madubin sa"ta faɗa tana ajiye kofin tea ɗin.

girgiza kai Aman Yayi kawai,tare da ficewa cikin sauri.makullin ya dauko agurin data ce,hakan ya ƙara tabbatar masa ita ta kulle Aslam cikin motar.
Cikin sauri yaje ya buɗe Aslam daga cikin motar,
Ajiyar zuciya Aslam ya sauke mai ƙarfi,lokacin daya fito daga cikin motar,jingina bayan sa yayi da motar kafin ya lumshe idonsa,aƙoƙarin sa na kawar da ɓacin ran da ke cinsa.
"Yaya is ok, kayi hakuri karka bata ranka dan Allah"Aman ya fada cikin tausayawa ɗan uwan nasa,Allah kadai yasan tsawon lokacin daya ɗauka cikin motar nan.
Buɗe rinannun idanunsa Aslam Yayi tare da kallon Aman,baice masa komai ba ya nufi cikin gidan.
Alwala yayi tare da fitowa ya nufi masallaci,yayi alƙawarin bazai sake kula Islam ba,har sai ranar da aka ɗaura musu aure,lokacin zai nuna mata shi ba tsaran ta bane.dan haka koda suka zo cin abinci bai nuna komai ba haka yaci abincin sa ya tashi da wuri.

Washe gari da safe ya kai Islam makatan kamar yadda pricipal ya fada,duk irin yadda Islam ke neman sa da bala'i sam ƙin kulata yayi,ta taɓa nan ta taɓa can,ta kunna redio ta kashe haka tayi tayi,amma yaƙi kula ta.dan kanta ta gaji ta hakuri tare da jan tsuka.

Duk wani interview da ya kamata ayiwa Islam anyi mata,sosai malaman sukayi mamakin ƙoƙarin ta,hatta uban gayya saida ta burgeshi,dan wata tambayar ma kafin agama take bada amsa.dan haka ajin su hanan aka kaita.kujerar gaba aka ajiye ta kusa da moninta.
To ranar dai ƙalau akayi karatu aka tashi islam bata kula kowa ba,hatta hanan bata kula ba.
Lokacin da aka tashi,driver yazo ɗaukan su.harta buɗe motar zata shiga ta hango wata yarinya zaune tayi tagumi,da alama jira take azo ɗaukan ta,haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata arai.da yake akwai bangaren primary cikin makaranta,yarinyar ma da alama bata wuce aji biyar ba a frimary.
Rufe motar Islam tayi tare da nufar yarinyar.
Hanan na mata magana akan tazo sutafi ina kuma zata?amma ko sauraron hanan batayi ba.
Tana zuwa ta zauna kusa da yarinyar.kyakykyawa da ita mai saurin shiga rai.
Tana zama yarinyar ta juyo tana kallon Islam,murmushi Islam tayiwa yarinyar itama ta maida mata martani,tana mai cewa"anty kema ba'azo ɗaukan ki bane?"yarinyar ta faɗa cikin muryar ta mai daɗi tana kallon islam.
Kallon yarinyar Islam keyi cike da jin wata irin ƙaunar yarinyar cikin ranta tace"a'a an zo daukana kinga motar can,ta faɗa tana nuna motar tasu,kafin taci gaba--ke na gani shine nazo gurin ki,naga kamar kina cikin damuwa,ya sunan ki?kuma Meya sameki kika zauna anan ke kaɗai?bayan naga an tashi masu irin kayanki tun dazu"Islam ta faɗa tana kallon yarinyar.
Turo baki yarinyar tayi kamar zatayi kuka tace "anty tun ɗazu aka tashi,amma ba wanda yazo ɗaukana daga gidan mu,kuma Ni wllh na gaji,kinga yaya Hisham yace zai zo ɗauka na yau,amma baizo ba abbana kuma baya ƙasar"yarinyar ta faɗa tana wani yatsina fuska.
Murmushi Islam tayi tana jin son yarinyar sosai cikin ranta,akwai iyayi yarinyar ga wayo.
"To kiyi hakuri ya Hisham zai zo yanzu kinji?ya sunan ki?
Islam ta faɗa tana shafa kan yarinyar.

"Sunana Aisha Amma abbana Yana cemin mamana,anty kema ya Hisham yayan ki ne?"A'isha ta fata tana kallon Islam.
Dariya Islam ta ɗanyi mai sauti kafin tace "Ni bani da yaya sai Kani,amma daga yau kema ƙanwata ce kinji?"Islam ta faɗa tana kallon A'isha.

Murmushi A'isha tayi kafin tace "to anty mu kulla ƙawance"ta faɗa tana miƙowa Islam hannunta wanda ta sarke yan yatsun ta guda biyu.
Dariya Islam tayi kafin ta mika manuniyar ta tare da shigarwa cikin yatsun Aisha tana ware wa.
Kafin wani daga cikin su yayi magana sukajiyo horn din mota.
Da sauri A'isha ta mike tana tsalle "anty ya Hisham yazo na tafi sai gobe bye bye"ta faɗa tana nufar motar da gudun ta.

Murmushi Islam tayi tare da bin bayan yarinyar da kallo,sannan ta mike ta nufi motar su.
Hanan sai cika take tana batsewa,amma ba damar magana,dan tsoron Islam take.
Tun daga wannan ranar kullum Islam na tare da Aisha,hatta abinci ita ke ba A'isha abaki,kuma bata taɓa yarda wani yayiwa yarinyar koda kallon banza ne.musamma take tafiya bangaren yan frimary ta tambayi A'isha ko wani yayi mata wani abu,duk ranar da ta kama yaro kuwa yayiwa A'isha koda kallon banza ne,saita daddoke yaro kuma tasashi yaba A'isha hakuri.cikin ƙanƙanin lokaci Islam tayi suna cikin makarantar,dan duk wanda ya taɓa ta,saiya yabawa aya zaƙinta.kowa tsoron ta yake cikin makarantar.
Shaƙuwa ce sosai tsakanin A'isha da Islam,duk gidan su Aisha ba Wanda bai san da Islam ba,kamar yadda labarin A'isha ya isa gidan su Islam.
Iyayen A'isha suna jin daɗin yadda Islam ke kula musu da yarinya,kuma sunyi alƙawarin wataran sai sun ziyarci gidan su Islam,dan yin godiya.

Yau saura kwana uku bikin Islam da Aslam,duk wani gyara da akewa jannat shi akewa Islam,kasancewar yawancin abubuwan gyaran masu dadine,wanda maman Yusuf yar mutan saƙkwato ta haɗawa mommy shi,yasa sam Islam bata ƙin ci ko shan duk abinda aka bata.
Tayi wani freesh da ita har yar ƙiba ta kara,ba abinda ke damunta,uzurin gabanta kawai take,kuma yau kusan sati guda basu hadu da Aslam ba,tana ta mamakin ina ya shiga kuma oho.

Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya yaji kunya,yau ta kasance ranar juma'a,wacce dubban daruruwan mutane suka shaida daurin auren Muhammad Aslam da amaryarsa Islam,akan zunzurutun sadaki,dubu dari da hamsin,sai kuma jannat da nata angon Saleem akan sadaki dubu dari.sosai mutane suka halarci gurin daurin auren,Kasancewar aslam baida abokai hakan tasa koda aka gama daurin auren can part ɗin sa da aka gyara inda zasu zauna ya nufa.ko ina agyare fes sai ƙamshi ke tashi ta ko ina,an tsara part ɗin sosai,yayi kyau.yana zuwa ya cire babbar rigarsa ya kwanta akan gado yana tunanin wai yau shi Aslam aka daurawa aure,kuma da yarinyar da ya tsana,wacce take masa kallon sa'anta,bata bashi girmansa ko kaɗan,cije lips ɗin sa na ƙasa yayi tare da jinjina kai yana tunanin irin yadda zai gyara Islam,duk wannan iskancin nata wllh sai ya saita ta.
Yanzu zata gane asalin waye Aslam,yasan zuwa yanzu mommy ta gama aminta yana son Islam,Dan sosai yake nuna kulawar sa agareta idan suna gaban su mommy.

Waya ya dauka tare da kiran mommy.tana daga wa yace cikin shagwaba "mommy wllh yunwa nake ji,akawomin abinci please"ya ƙarasa adan marairaice.

" Ayya Me yasa ka zauna da yunwa Aslam?har abinci fa na aika maka dazu,amma akace baka nan,yanzu kana ina?"cewar mommy cikin kulawa.

"Ina wancan sabon part ɗin "ya faɗa ahankali.

"To bari akawo maka abincin yanzu"

"To mommyna"Aslam ya fada da ɗan murmushi.
Itama murmushin tayi tare da kashe wayar.

Gidan acike yake da yan uwan mommy Dana daddy,sosai yan uwan mommy keta jin haushin wannan haɗin na Aslam da Islam,dan gani suke ga ya'yan su amma aka wucesu aka haɗa Aslam da bare.dan basu san asalin wacece Islam ba,kawai mommy tace musu yar abokin daddy ce.

Bayan mommy ta gama haɗawa Aslam abincin cikin wani ɗan kwando ta fito dan neman yaron da zai kai masa.
kiciɓis sukayi

Please Login or Register in order to submit comment