Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fa ka zata da farko ina taɓa maka ƙafa ne dan kaji daɗi,shine har da wani lumshe ido,kai ga jarababbe, daga mace ta rabeka saika fara layi kamar ɗan giya ko?ai da gangan nayi maka hakan,sannan na ƙara tada ciwon yadda zamani zafi sosai kafin na gyara maka.kaga nan gaba saika ƙara yimin abun da ba daidai ba next time ƙarya ƙafar zanyi"ta faɗa tana nuna yadda zata karya ƙafar tashi da hannunta.

Bakin ciki,ta kaici,tsana ,haushi sune suka taru suka cunkushe zuciyar Aslam,ji yake kamar ya kurma ihu ko zai samu sassauci cikin zuciyar sa, shi mutum ne da bai fiye son doguwar magana ba,amma yarinyar nan ƙarfi da yaji nema take ta sanya shi yazama mafadaci,amma bazai kula ta ba,sai dai taga sakamako aƙasa.dan haka yayi shiru bai ce mata komai ba,sai zuciyar sa dake masa zafi kamar wuta.

Islam kuwa jin baice mata komai ba yasa taji haushi cikin ranta.
Cikin masifa tace "wato ka maida ni mahaukaciya, ina ta magana kayi shiru ko?ta faɗa tana bugar ƙafar sa mai ciwon.
Runtse ido yayi da ƙarfi yace "washhh,kafin ya buɗe idon ya sauke akan Islam --to meye marabar ki da mahaukatan aike bayan hauka ma jahilci da rashin sanin girman na gaba dake,sannan da rashin tarbiyya sune babbar damuwarki, ga dukkan alamu iyayen ki basu baki tarbiyyar mai kyau ba,sam baki da kamun kai,sannna da ganin ki riƙaƙƙiyar karuwa ce, kin gama yawon iskancin ki shine kikazo nan kike cutar da rayuwar mu, I hate you with all my heart,sannna ki saurari sakamakon abinda kika yi min sai kinyi dana sani Kum....."

Da ƙarfi Islam ta toshe kunnen ta, tare da sanya wani irin ƙara mai firgitarwa,wanda sai da yayi sanadin da turarukan dake kan madubin Aslam suka faɗi ƙasa tare da tarwatsewa.
Banda rawa ba abinda jikin Islam keyi,tunda take arayuwa ba wanda ya taɓa gasa mata maganganu makaman tan irin wanda Aslam ya yaba mata yanzu,hakan yayi matuƙar ƙona mata zuciya,yadda ya ke jifan iyayen ta da munanan kalamai, lallai Aslam baida tarbiyya ko kaɗan, yana buƙatar gyara.
Cikin wani irin yanayi na rinewar kwayar idon ta,daga fari zuwa jaa sosai,ta buɗe idon tare da saukesu akan fuskar Aslam,Wanda yayi kasaƙe yana kallon ta cikin mamaki,anya yarinyar nan mutum ce?daga yin ihu kalli yadda kwalaben turare suka farfashe?gaskiya koda ta kasance mutum akwai shafin aljanu tare da ita.
Ƙurrr ta kafe Aslam da idanun ta,wanda suka koma masu ban tsoro, magana ta fara cikin wani irin sauti mai kama da tsawa"kayi kuskuren shiga gona ta Aslam,baka isa kaci mutuncin iyaye na ka zauna lafiya ba,zan gwada maka irin tarbiyyar banzar da suka bani ka kuka da kanka"Islam ta fada cikin zubda wani irin hawaye mai kama da jini.tana kaiwa nan ta juya cikin takun sauri ta bar ɗakin,inda sukaci karo da mommy ta taho daga kitchen da gudu,dan taji ihun da Islam ɗin kwalla.
"Lafiya kuwa islam? Me ya faru?ko dai yayi miki wani abun ne?"cewar mommy tana riƙe kafaɗun Islam ɗin.

Kallon mommy Islam tayi, kafin ta girgiza kanta ahankali tana sakin murmushin yaƙe,wanda kallo ɗaya zakayi mata kasan bai kai har zuciya ba."ikon Allah meye wannan kuma yake zuba daga idanun ki kamar jini?"cewar mommy tana kai hannu kan fuskar Islam.
Kafin hannun nata ya ƙara sa kan fuskar, Islam tayi saurin barin gurin.kai tsaye kitchen ta wuce inda mommy ke dafawa Aslam farfesu.robar dakakken yaji ta ɗauka ta zazzafar cikin tukunyar sosai,sannan ta juyyuya yadda baza'a gane ba ta rufe tare da ficewa daga kitchen ɗin

Binta kawai mommy tayi da kallo tana mamaki abinda idanunta suka gani,to kodai kukan jini yarinyar take yi ne?amma meye zai sa ta yi kukan jini ita da ba aljana ba?cikin dakin na Aslam ta shiga,dan tambayar sa abinda ya faru.
Yana nan kwance,ba alamun damuwa akan fuskar sa,saima murmushi data ga kamar yanayi,dan ba karamin daɗi Aslam yaji ba,yau ya ɓatawa Islam rai ,dan haka zai ci gaba da faɗa mata maganganu masu zafin da zasu iya fasa mata zuciya kowa ma ya huta.
"Aslam me kuma kayi wa Islam naga ta fita ranta abace?sannna kamar ma kuka take har da jini"cewar mommy bayan ta shigo cikin dakin.
Ahankali Aslam ya buɗe idonsa yana kallon mommy"mommy nikuma da nake kwance me zan mata?kinga barci ma ya fara ɗauka na,bansan bata cikin ɗakin bama"ya faɗa cikin halin ko inkula yana mai da idonsa ya kulle.

Shiru mommy tayi na ɗan wani lokaci kafin ta fice,farfesun ta zubo masa cikin kula,ta hado da flate da cokali ta dawo dakin.
Dai-dai lokacin Daddy ya kawo maganin zafin.sai dai mommy tace Islam ɗin ta fita,sai dai ya ajiye idan ta dawo tayi addu'ar ta shafa masa.
Koda mommy ta zubawa Aslam farfesun nan,ai yanayin cokali ɗaya ya fara zare ido,dan yaji sosai ne aciki.gashi shi kwata kwata baya ƙaunar yaji."mommy bazan iya cin wannan naman ba,yaji yayi yawa"Aslam ya faɗa yana gwabe fuska.
"Na san baka don yaji Aslam,Amma Dole ka daure kaci,ko dan samun lafiyar ka"mommy ta fada tana dibo naman cikin cokali.
Haka mommy ta tusashi gaba,yana cin naman,duk loma ɗaya saiya sha ruwa,da gyar yayi loma biyar yace ya koshi.ji yake harshen sa kamar zai zazzago dan zafin yajin.
Mommy kuwa ficewa tayi daga ɗakin ta kai flate ɗin kitchen.
Gaba ɗaya Aslam ya rasa inda zai tsoma rayuwar sa,idonsa yayi jajur banda azaba ba abinda bakinsa keyi,ahankali ya dauko daga kan gadon ya nufi toilet cikin ɗingisawa,yana ɗan runtse ido,kan sink kawai yake ya tsaya tare da bude bakin sa yana kwara ruwa aciki.amma kamar ƙara zafin yake.
Cikin gigita ya zame tare da zama agurin yana mai runtse ido.

Islam kuwa har ta bar falon tayi wani tunani dan haka kai tsaye ta juyo cikin gidan bayan ta kira janbu.dakin Aslam suka shiga yana hannunta.lokaci Aman yana barci afalo,dan shi yafi Zama sosai afalon saboda masu zuwa duba shi.
Suna shiga ɗakin tace "janbu daga yau anan zamu rinka hutawa, akan wannan gadon, dan haka maza hau mu kwanta"ta fada tana sakin janbu,shikuwa ya ɗare kan gadon aman.
Itama hawa tayi tare da yin miƙa kafin ta janyo filo ta kwanta.
Kusan minti biyar kuwa barci ya fara daukarta, dan sosai taji daɗin gadon.

Saida Aslam ya kwashe kusan minti goma cikin wannan mawuyacin hali kafin ya yunƙura ya mike,wanka yayi tare da sanya rigar wanka ajikinsa,sannan ya fito .zuciyarsa daya
Yaga shiryawa cikin wasu riga da wando,marasa nauyi,wandon iya gwuiwa ne,sai rigar mai yankakken hannu ce.turare ya feshe jikinsa dashi,kafin ya nufi gadon.
Kasancewar barci yake ji sosai kuma ɗakin nashi ba haske sosai ya kashe kwan mai haske ,hakan ya hanashi ganin Islam da janbun ta.
Kai tsaye ya haye kan gadon tare da kwanciya.miƙa hannunsa yayi dan ɗauki wayarsa kawai yaji ya kai hannun sa kan abu mai matukar laushi.
Azabure ya tashi zaune tare da danna Madannin hasken dakin.nan da nan ɗakin ya gauraye da haske.
Cikin firgici ya zaro ido sakamakon abinda idanunsa suka gane masa......

Ko me ya gani?
Muje zuwa.
Anty mammy.
[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: _______________Da ƙyar, Aslam ya yunƙura ya miƙe tsaye yana cije leɓe,dan sosai ƙafarsa ke masa wani irin zugi da raɗaɗi.
Ga jikinsa duk ajiƙe,yanzu idan ya shiga gida mai zai ce musu? sai kawai yace Islam ce ta jefeshi cikin ruwa?kuma ta kayar dashi?ina! Hakan bazai yiwu ba.dole dai ya nemo mafita.
Ahankali ya fara ɗingisawa, ya nufi jikin bishiyar da Islam ta sauko,zama yayi aƙasan bishiyar yana mai runtse idon sa,me ya kamata yayi wa yarinyar nan ne ya huce?ya fuskanci,sam bata da cikakken hankali,tsaf zata iya kashe mutum,ya zama dole yasan matakin dauka akanta.

Kusan minti biyar yana zaune,ya ga dai zaman baida wani amfani,dan haka ya yunƙura da gyar yana runtse ido,ya tashi tsaye,sai huci yake tsabar ciwon da ƙafar sa keyi,gani yake kamar ma gociyar ƙashi ya samu.

Cikin gidan ya nufa ahankali yana dafa bango,ga jiki duk ajiƙe.yana buɗe ƙofar falon yayi arba da Islam ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana cin apple,Aman Yana ta mata surutu,ita kuma sai murmushi take.

Ahankali yake takawa zuwa cikin falon,saida yazo tsakiyar falon,Islam ta tuntsire da dariya,tana faɗin "ɗaya! biyu !! Uku!!!"tana dariyar ta alamun takunsa take ƙirgawa.
Cak Aslam ya ja ya tsaya tare da runtse idanun sa,zuciyar sa na masa zafi,yana kara jin tsanar Islam cikin ransa.
Da sauri Aman ya kalli inda Islam ke kallo tana dariya,ɗan uwansa ya hango da jiƙaƙƙun kaya ajikinsa, ga shi ya ɗage ƙafa ɗaya,kuma da alama ciwo yaji.
"Yaya me ya same ka haka?me yasa naga jikin ka ajiƙe ?ƙafar ka ma yaya kamar ciwo kaji fa"Aman ya faɗa cikin yanayi na nuna tsantsar damuwa.

Ɗan satar kallon Islam Aslam Yayi,aikuwa shi take kallo ta dage gira ɗaya tana jiran jin abinda zai faɗa.
Kawar da kai yayi yana kallon Aman kafin yace "am ok bro,I just fall down,and I think I get injury in my leg"Aslam ya faɗa cikin harshen turanci,dan kar Islam taji me yace ta ƙarya ta shi.
Aikuwa saiji yayi ta sanya dariya tana faɗin"Lear !wllh he's telling you lear,is better ma ka sanar dashi gaskiya,dan ba Yaren da zakayi Islam bata ji me kace ba"ta faɗa tana kallon Aslam da murmushi.

Mamaki sosai ya kama Aman,yarinyar dake rayuwa cikin jeji ina ta koyi Turanci?dan shikam iya tunaninsa kamar tun ƙuruciya take cikin wanan hatsabibin jejin.
Shikuwa Aslam da bai san inda take rayuwa ba,kawai dai yayi mamakin ashe ta je school,dan baiyi expecting tana jin turanci ba.

Ci gaba yayi da nufar ɗakinsa,ba tare da ya kara furta komai ba,yana jinta tana faɗa wa Aman cewar"wllh ƙarya yake maka,nice nan na cillashi cikin ruwa,sannan na sanya masa ɓawon ayaba ya taka ya faɗi"ta ƙarasa maganar da dariya.

Marairaice fuska Aman yayi yana kallon Islam yace "haba ƙanwata, baki kyauta ba gaskiya,yaya fa is like second father to us,shine babban yayan mu,dan Allah ki daina masa rashin kunya bana jin daɗi,and.....

"Kai dalla malam ya isheka haka, saboda yayan ka ne shine kake son kareshi?Ni baka ga irin rashin mutumcin da yake min ba ko?to wllh yanzu na fara bashi wahala,dan saina ɗau fansar duk abinda yayi min, dan kuwa bana yafiya"Islam ta fada cikin salon masifar ta tana hararar Aman.

Shiru Aman Yayi yana kallonta, yasan halin ta da masifa,kuma shi baya son ranta ya baci, amma sam baya jin daɗin yadda take yiwa yayan nashi sam,cikin sanyi murya yace "kiyi hakuri Islam bawai dan ya na matsayin yaya na nake faɗin haka ba,kawai dai naga gaba yake da ke,kuma koba komai ance bin naga bin Allah"ya ƙarasa cikin sanyin murya kamar wanda ke tsoronta.
Harara ta watsa masa fuskarta ahaɗe, sannan tace "wato Ni kafura ce bana bin Allah ko?kai wllh fa kaima ka kiyaye ni, kar kaga ina kula ka nuna ɗan mutunci kace zaka ringa faɗa min baƙar magana,idan na dawo ta kanka,wllh ba za kaji daɗi,dan sai na hana wannan karyayyar ƙafar taka warke wa"ta fada tana nuna ƙafar tasa da ke ɗaure.

Murmushi yayi tare da girgiza kai,lamarin Islam kam,sai du'ai sam bata da gwani."to nikam kiyi hakuri karki ƙarasamin ƴar ƙafar tawa in zama gurgu,kinsan ƴan mata bazasu aureni ahaka ba"ya faɗa cikin murmushi.
"To dole ne sai kayi auren?ba sai kayi zaman ka agida ba,dama waya ke son wani aure ana zaune ƙalau ?kaga Ni bari na tashi barci ma nake ji ka ishe Ni da surutu"Islam ta fada tana mikewa tsaye,da yar rigarta iya kwauri.
Kallo aman ya bita dashi,yana jin wani irin abu na ɗarsuwa cikin zuciya da jikinsa,shi wllh da zata taimaka ta daina sanya kayan nan da ta taimakeshi,dan sosai take sanya shi cikin wani hali idan ya ganta da wannan shigar.
"To kallamu,ka fara ko?kai kam Aman bakaji daɗi ba wllh,kallo sai kace maye"Islam ta fada tana watsa masa harara.
Ajiyar zuciya yayi kafin yace "Please ƙanwata dan Allah ki daina sanya irin waɗan nan kayan,domin suna bayyana surar ki sosai awaje,kuma kinsan akwai matsala idan har ina kallon ki ahaka"Aman ya faɗa cikin marairaita kamar zaiyi kuka.

"Kuttt!!! Lallai ma Aman,yanzu kayan da nake sawa ma,sai an zaba min?to ina ruwan ka da shiga ta?wllh ba wanda ya isa ya hanani yin shigar dana ga dama,kuma ai bance ka kalle Ni ba,bare kaga akwai matsalar,banza kawai mai hanci zororo kamar karas"tana faɗin haka ta jefa masa guntun apple ɗin dake hannunta,tare da murguɗa baki ta juya zuwa dakin granny Jikin ta ko ina na girgiza.

Lumshe ido Aman yayi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,Allah ya gani shikam wllh duk lokacin daya ganta da irin wannan shigar,mafi yawan lokaci yana tsintar kansa cikin felling sosai,dan ba ƙarya ko makaho yasan akwai ƙira agurin.
"Allah ka mallaka min Islam matsayin mata ta"ya faɗa ahankali yana Binta da kallo har ta shige ɗakin granny.

Aslam Yana shiga ɗakinsa da gyar ya cire riga da wandon sa ya kwanta akan gado,kansa ciwo yake ga ƙafar sa,sai zogi take masa.tsabar bakin ciki da takaici,ko maganin rage radadi bai shafawa ƙafar ba.
Haka yayi kwance aɗakin har dare,
Dan ko abincin rana ƙin fitowa yayi yaci,mommy kuwa kasancewar tana fushi dashi,ko neman akirashi batayi ba.

Aikuwa kafin dare kafa ta kumbura suntum, nan da nan,har ta zuba masa zazzaɓi,amma saboda taurin rai irin na aman yaƙi fitowa aduba masa ƙafar haka ya kwana bai ko runtsa ba.
Koda suka kammala breakfast,school su jannat suka wuce ita da hanan.
Aman ne ya kalli mommy yace "mommy Yaya fa tun jiya banga fitowar sa ba,kuma da alama baida lafiya,dan yaji ciwo akafar sa jiya,ya kamata adubo sa" jinjina kai mommy tayi kafin tace,nima tunanin da nake yi kenan,gaskiya ba lafiya ba,bari naje na duba da kaina"ta fada tana mikewa ta nufi dakin Aslam ɗin,dan dama dauriya kawai take,amma tun daren jiya take son sanin wane hali yake ciki,ta sanshi sarai da ɗacin rai,sai yayiwa kansa horon yunwa,gashi ba shi da juriya akan yunwa.
Yana kwance cikin bargo sai rawar sanyi yake,haƙoran sa har haduwa suke da juna.da sauri mommy ta karasa cikin dakin,ta yaye bargon daya rufe jikinsa dashi,daga shi sai single da boxers.
"Subhanallah! Aslam, baka da lafiya?meke damunka?ta fada tana kai hannunta tare da taɓa jikinsa,zafi ƙau jikin nashi kamar wuta,
Ahankali ya buɗe idanunsa da sukayi jajur dasu,ya kalli mommy dake shafa kansa.
Cikin rawar murya yace "mommy ƙafa na ciwo take sosai, sanyi nake ji mommy"ya faɗa jikin sa na rawar sanyi.
Kallon ƙafar tasa mommy tayi,zaro ido tayi ganin yadda ƙafar ta kumbura sosai"Aslam Ina kaji wannan ciwon haka?garin yaya?me yasa ka bari har gurin yayi tsami haka? innalillahi bari na sanar da Daddyn ku,anemo mai gyara"tana faɗin haka ta fice da sauri.
Lokacin Islam na zaune kusa da Aman,tana shafa masa wani magani agefen ƙafar sa, shikuma sai kallonta yake,mommy ta fito da sauri ta nufi saman Daddy.kallon juna Islam da Aman sukayi,kafin Aman yace "da alama yaya bai da lafiya,dama tun jiya bai fito,kin gani ko Islam,kuma wllh yaya bai iya ciwo ba"taɓe baki Islam tayi kafin ta ce "ina ruwana karya iya ciwon mana,In yaso ma ya shekara yana ciwon bai dame Ni ba"ta fada tana ci gaba da shafa masa maganin.

"Amma fa kece silar ciwon nashi Islam,yanzu ko kaɗan bakiyi nadama ba?"
Aman ya faɗa yana kallon ta.
Aikuwa matse gurin da take shafawa maganin tayi da karfi,har saida Aman Yayi ƙara yana riƙe hannun ta"wayyo Allah Islam zaki karya min kafa,yi hakuri na tuba bazan ƙara magana ba"Aman ya faɗa cikin sigar rarrashi Yana kif-kif ta ido,dan yaji zafi sosai.
Sakin ƙafar tayi tana mai faɗin"wllh da saina ƙara karya maka nan gurin ma,dan naga surutun ka yayi yawa,shikenan kuma Allah bazai jarrabi bawan sa ba,sai ka ɗora min kace Ni ce?shi ragon ina ne da ɗan wannan abin da nayi masa zai sashi jinya?"
Kafin Aman yayi magana,saiga mommy da daddy suna saukowa,
"Daddy barka da fitowa"aman ya faɗa cikin girmamawa.
"Yawwa aman sannu ya kafar taka?fatan dai kana jin sauƙin?"cewar Daddy Yana shafa kan Aman .
"Alhamdullah Daddy Ina jin sauƙi sosai"
"Masha Allah haka akeso,Islam sannu ko,fatan dai ba wata matsala?"Daddy ya faɗa yana kallon Islam, fuskar sa dauke da murmushi.
Murmushi tayi itama kafin tace "ba komai Alhaji ya jikin naka?"
"Jiki kam Alhmdllh ai na warke,ina ƙara godiya sosai agareki yata Allah yayi miki albarka"Daddy ya fada yana kallon Islam,murmushi tayi bata ce komai ba.
"Alhaji da kayiwa mai gyaran waya kawai yazo,dan sosai ƙafar tashi ta kunbura,ina ga dai ko targaɗe ko kuma tsagewar ƙashi ya samu"mommy ta fada cikin yanayi na damuwa.
"Eh hakan za'ayi bari na kira malam haru in yaso saiya zo ya duba ƙafar tashi"Daddy ya faɗa yana ƙoƙarin cire wayar sa daga aljihu.

"Daddy Nima na iya gyaran targaɗe da gocewar ƙashi ko tsagewa " Islam ta fada da sauri tana kallon Daddy.
Fasa ɗauko wayar yayi yace"af !aini na manta ma wllh,muna da mai gyara agida,Hajiya ga Islam,dan kinsan ita ta ɗaurewa Aman karayar sa"
"Wllh nima na manta Alhaji,hankali na ne duk atashe,ganin yadda ƙafar tasa ta kunbura sosai,
Yanzu muje Islam ki ga yadda ƙafar tayi"cewar mommy tana kama hannun Islam.

Dakin suka nufa Daddy na binsu abaya.
Aman kuwa zaro ido yayi yana jin faduwar gaba ,Allah yasa Islam karta ƙara wa yaya Aslam wani targaɗe.

Kai tsaye suka shiga ɗakin na Aslam,ba kowa cikin Falon sai ƙamshi da sanyin ac.
Sosai ɗakin yayi wa Islam mugun kyau,har taji cewar dama dakin tane.
Shiga sukayi cikin uwar ɗakan, inda Aslam ke kwance kan luntsumemen gadonsa, ya rufe jikinsa da bargo.
Kallon dakin kawai Islam keyi cike da sha'awar dakin,dan sosai taji tana son dakin cikin ranta.komai neet an ajiye shi gurin daya dace,sai ƙamshi ke tashi ta ko ina.
"Lallai na samu gurin huta wa wllh"Islam ta fada cikin ranta.
"Islam duba masa kafar ki gani"cewar mommy tana yaye bargon daga jikin Aslam.
Waral!Aslam ya bude idon sa,jin sunan da aka ambata ,matsayin wacce zata duba masa ƙafar,tab Islam kuma?itace mai duba masa kafar?ina bazai yiwu ba,haka kawai ta zai miƙa kafa wannan ƴar dabar fara ta murde masa ƙafar,bayan itace silar shigar sa cikin wannan halin da yake ciki,
Yunkurawa yayi da gyar ya tashi zaune fuskarsa hade yace "mommy waye zai gyara min kafar ? Badai wannan yarinyar?wllh Indai itace Gara ƙafar ta lalace da na yarda ta taɓa min ƙafa" Aslam ya faɗa cikin mugun ɓacin rai yana huci......

Masu karatu ya kuke gani?
Anya Aslam zai yarda Islam ta duba masa ƙafar sa kuwa?
Kun ji dai Islam tace ta sami gurin hutawa,ya kuke ganin zata kaya tsakaninsu da Aslam?

Muje zuwa taku ce dai,
Anty mammy

Mrs babi💘💘
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: _____________Tsabar tsoron abinda idanun Islam suka gani,jikinta rawa yake ta nufi inda Aslam ke tsaye kamar gunki,cikin shocking.tana zuwa gareshi ta kama gefen rigar sa tace,"Aslam ka gani ko?kaga halin da ƙanwar ka ke ciki,kalli abinda jannat keyi acikin gidan ku,tare da wannan shegen mai kama da talo-talo"Islam ta fada cikin ɓacin rai da tsoro.

Kallon ta Aslam Yayi,zuciyar sa na wani irin bugawa kamar zata fito,haƙiƙa abinda idanunsa suka gani yau,yayi matuƙar girgiza shi,mamaki da al'ajabi sun hana shi yin koda ƙwaƙwƙwaran motsi.kallon jannat kawai yake wacce ta gama kiciniyar maida rigarta, jikin ta sai rawa yake tana kallon yayan nata.

Shima saurayin yana tsaye ya kasa motsi sai zare ido yake.
Girgiza Aslam da karfi islam tayi ,da ƙarfi tace "tsaya wa zakayi kana kallon wannan shegen fitinnan ne daya zo har gida yana ƙoƙarin bata maka ƙanwa?wallahi yau bazaka bar gidan nan salin alin ba,saika ci ubanka,nan gaba bazaka ƙara zuwa gidan mutane kayiwa ƴaƴansu iskanci ba"Islam na kaiwa nan maganar ta tayi kan saurayin jannat gadan gadan,tana zuwa ta wanke shi da maruka har uku masu zafi da shiga jiki.dafe kuncin sa saurayin yayi yana kallon Islam,dan sosai marin ya shige sa.

"Bar kallo na annamimi dan iska,wllh kaima kana zaune agabanka za'a lalata ƙanwar ka,maha'inci mugu azzalumi yau zaka yabawa aya zaƙin ta"Islam ta fada tana kaiwa saurayin nan duka ,tun yana kallon abun kamar wasa, ya 'na kare kasan har ya kasa kare kannasar,dan irin dukan da Islam ke masa,abin zai baka mamaki,naushinsa kawai take da bashi ƙafa.abinka da yayan masu kudi,dama jiki ba kwari nan da nan ya galabaita ahannun Islam sai jini ke zuba ahancin sa da bakin sa.
Kuka sosai jannat keyi hannun ta aka,ganin yadda jini ke fita ta baki da hancin saurayin nata.
Cikin mutuwar jiki da tarin damuwa Aslam ya tako zuwa inda saurayin nan ke kwance Islam na jibgarsa,hannu ya sanya cikin sanyin jiki ya kamo hannun Islam, cilak! ya miƙar da ita tsaye tare da riƙe kafadar ta yana kallon ta,idanunsa sunyi jaaa,sosai.girgiza mata kai yake alamun ta daina dukan saurayin.
Cikin huci da fushi ta fizge kafaɗar ta tana faɗin"ka barni na hukunta wannan shegen yaron,domin sune suke lalata yayan mutane.
"shegiya kema mai kama da muciya, ana. Kallo ki haka ashe shaiɗaniya ce ke,yanzu idan mommy taji wannan labarin me kike tsammanin zai faru da ita?wane halin damuwa kike tunanin zata shiga? Jannat kin cuci kanki,kin ɓata tunanin ki,wllh ban taba tunanin wayonki na banza bane sha sha sha kawai"
Cikin kuka jannat tace "wllh ba laifi na bane shine yace wai....
Tass Islam ta dauke ta da mari tana huci."rufemin baki,wawiya idan yace kiyi abu sai kiyi?uban ki ne shi?ko shi Aslam ne ?banza marar wayo kawai"
Durƙushewa jannat tayi agurin tana kuka sosai,tare da kamo ƙafar yayan ta,
"Dan Allah yaya kayi haƙuri,wllh sharrin shaidan ne,kayi min duk hukuncin da zakayi min,amma karsu mommy suji wanan maganar,nayi nadama yaya "jannat ta fada cikin kuka sosai harda shashsheƙa.

Kallonta kawai Aslam keyi,zuciyar sa na masa zafi sosai,ashe haka iyayen waɗan da ake lalatawa rayuwa suke jin zafi aransu?bai taba jin nadamar abinda ya ke aikatawa ba arayuwar sa sai yau,shi gani ma yake kamar shine ya jawa jannat faruwar wannan al'amarin.
Hannunsa ya sanya tare da kamo kafaɗun jannat ya miƙar da ita tsaye.kallonta yake ba tare da yace komai ba.
Fuskar sa ba walwala ko kaɗan.
Ita kuwa sai kuka take jikinta na rawa.
Saurayin nan haka ya ja jiki ya zauna a ƙasa tare da jingina bayansa jikin kujera sai maida numfashi yake.
Cikin rawar murya yace "dan Allah kuyi hakuri,wllh sharrin shaidan ne,In shaa Allahu hakan bazata ƙara faruwa ba,na tuba yaya Aslam ka ya femin" ya faɗa cikin zubda hawaye.
Kallonsa Aslam yayi bayan ya zaunar da jannat kan kujera shikuma ya jingina da jikin bango.
"Yanzu kai wannan abunda kukeyi aganin ka shine soyayya?meye ribar ka idan ka lalata rayuwar wacce kake so?shin da gaske kake ƙaunar jannat?"
Aslam ya faɗa da Muryar sa da tayi mugun sanyi.
"Wllh da gaske nake ƙaunar jannat,kuma auren ta nake son yi "saurayin ya faɗa da sauri yana kallon Aslam.
Ajiyar zuciya yayi kafin yace shikenan,ina son ka turo magabatan ka domin ayi magana adaura muku aure,amma ka kula kada ka sake yunƙurin aikata irin wanan abun da kuka yi yanzu tashi ka tafi gida"
Aslam ya faɗa yana ƙarasowa kusa da saurayin ya miƙar dashi tsaye tare da gyara masa kwalar rigar sa.
"Na gode yayanmu in sha Allah zan sanar da iyayyena kuma duk yadda ake ciki zan sanar da jannat ta faɗa maka"cewar saurayin yana sunkuyar da kansa ƙasa.
"A'a daga yau bazaku sake yin waya da jannat ba,sannan bazaka ƙara zuwa hira ba,har sai an gama maganar auren ku,dan wllh Ni har yanzu Ban wani yar da da tuban ka ba ja'iri fitinanne"cewar Islam kenan cikin tarar numfashin sa.
Jinjina kai Aslam Yayi yace "tabbas wannan maganar haka take,ba waya ba hira har sai mun gama magana da iyayenka, kaje kawai"
Sumi -sumi ya kama hanyar barin falon yana ɗan ɗingisa ƙafa,har ya kai bakin ƙofa,juyowa yake son yi dan ya kalli jannat Islam ta daka masa tsawa"kul!! Karka sake ka waigo wllh maza ka fice daga ɗakin nan "ta fada cikin tsawa.
Da sauri kuwa ya ƙarasa ficewa daga ɗakin,yana mamakin wannan wace yarinya ce mai shegen ƙarfi da iya subirbuɗar mutum haka?

"Ke kuma jannat yanzu irin tarbiyyar da mommy ta baki kenan?yanzu irin rayuwar da kike yi acikin gidan ku kenan?meye ribar ki akan aikata irin wannan?meyasa baki sanar damu cewa aure kike so ba?da tuni mun aurar dake ba sai kinzo kina zubar mana da mutunci ba"
Kuka sosai jannat keyi kamar ranta zai fita,bata taɓa jin kunya da nadama irin ta yau ba,"dan Allah yaya kayi hakuri wllh sharrin shaidan ne da son zuciya,amma wllh bazan sake ba,kayi min duk hukuncin daya dace,amma dan Allah karufa min asiri kar su mommy suji wannan maganar "jannat ta fada cikin sarƙewar murya tsabar kuka.
"Dole su mommy su san halin da kike ciki jannat,domin kinci amanarsu ,kuma keda kika saɓawa Allah meye naki na jin tsoron bayin sa su

Please Login or Register in order to submit comment