Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa wuta haka yake ji.

Afalo ya tarar da oganninyar ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.kallon tsana yake mata,yana jin kamar yaje ya shaƙeta ta mutu kowa ya huta.
Islam kuwa tana ganin sa ta tashi cikin takun ta mai ɗaukar hankali ta nufi inda yake tsaye yana watsa mata wani mummunan kallo.
"Masoyi! Ka fito kenan ?zamu iya tafiya?"ta faɗa cikin wani salo tana kashe masa ido.
Ji Aslam Yayi kamar ta soka masa nashi cikin zuciyar sa,afusace yace"kije can dai ki nemi masoyin ki,dan Ni har abada bazan taɓa sonki ba, wllh dana soki Gara In dawwama bani da zuciya aƙirjina ,bare harta darsa min sonki,dan wlllh na Tsaneki bana ƙaunar ganin ki"ya faɗa cikin huci kamar wani zaki.

Wani shu'umin murmushi Islam tayi tana kaɗa jikinta
, kafin ta kalli Aslam sama da ƙasa tace "wayaga bijimi, wllh Ni yanzu dariya ma kake bani,saboda idan kayi wani abun kamar taɓaɓɓe haka kake,kuma da kake iƙirarin baka sona,Ni waya faɗa maka ina sonka?ƙila ma yadda nake jin tsanar ka cikin raina, kai baka jin koda rabin ta akaina.kuma ka sani zanyi amfani da wannan damar ne dan In ƙuntata maka in zame maka ƙarfen ƙafa,sannan ka gane cewar Islam ba kanwar kasa bace, na wuce ajin tsageranci irin naka"Islam ta fada cikin nutsatstsiyar murya tana murmushi,ta yadda bawanda zai gane maganganu masu zafi take fadawa Aslam.

Shiru Aslam Yayi,yana sauraron ta.dan sai yanzu ya gane cewar, tana zurmashi yayi ta nuna ɓaci rai gaban kowa, yayin da ita kuma take ƙuntata masa cikin ruwan sanyi,daga yau shima zai sauya kalar nashi salon zai nuna mata shima ɗan barikine.
Dan haka matsowa yayi sosai daf da ita tare da rangwafowa saitin fuskarta,har suna iya jiyo saukar numfashin juna akan fuskokin su.
"Na gode da nuna min hanya da kikayi,daga yau zan nuna miki nima cikakken ɗan tasha ne kuma taɓaɓɓe,sannan good player,zamu fara wasan ne daga yau,zamu gani nidake waye zaiyi nasara,matar Aslam Mahmud kabeer"ya kai ƙarshen maganar sa yana mai shafa gefen fuskar ta cikin salon sa da yake narkar da zuciyar yan mata.

Wani yarrrrr Islam taji tun daga tafin ƙafarta har zuwa babban ɗan yatsan ta, da sauri ta ja baya tana Banka masa harara gabanta na bugawa da sauri-da sauri.
Murmushi Aslam yayi tare da kamo hannunta cikin nashi ya ce"muje amaryar Aslam ko?"ya fada yana wani matsa mata hannu cikin salon mai tada hankali tare da kashe mata ido....


Manage please wayata ba caji ne.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: _____________Islam kuwa riƙe take da gefen rigarsa tana kuka mai shiga zuciya.kusan minti goma suka ɗauka cikin wannan halin,kafin ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa,jingina bayanta tayi jikin kujera tana share hawayen dake zubowa daga idanunta.
Kallonta Aslam yayi fuskar sa ba yabo ba fallasa,kafin ya tada motar suka nufi gida.
Kafin su ƙara sa gida ya tsaya ya sai magungun da likita ya rubuta masa, tana zaune cikin motar bata uhmm,bare uhm -uhm. Sai zuciyar ta dake ƙara cika da tsanar Aslam.da tunanin ɗaukar fansa.
Haka ya dawo da ledar magungunan ahannun sa,ya ja motar suka tafi.
Saida Yayi facking ɗin motar sannan ya ga wayarsa dake ta kawo haske,dan a silent ya saka ta.kira rututu yawanci na mommy ne, dan haka kiranta yayi tare da karawa akunnen sa bayan ya gama facking.yana tsayawa Islam ta fito daga motar tare da nufar cikin gidan.
"Hello mommy "Aslam ya faɗa bayan ta ɗaga wayar.
"Ina ka kai yarinyar nan ne tun safe?maza ka dawo min da ita,kuma bana buƙatar ganin wani abu da ban yarda dashi ba atare da ita"tana gama faɗin haka ta kashe wayar.
Shiru Aslam Yayi Yana bin wayar da kallo,me mommy ke nufi kenan?kodai tana zargin ya tafi da yarinyar ne wani wajen dan yayi mata wani abu?yanzu kuma idan ta shiga ta sanar da mommy wata maganar ta daban fa?anya kuwa mommy zata yarda cewar daga asibiti suke? Ya Salam"ya faɗa yana dafe kansa ,sai kuma yayi saurin fita daga motar tare da nufar cikin gidan.

Gaba ɗaya suna falo,dan lokacin anyi sallar magrib,kowa da abinda yake,Mommy na zaune tana kallon ƙofa,zuciyar ta cike da tsoro,dan bata san abinda ke faruwa ba,fatan ta ɗaya shine Allah yasa abinda zuciyar ta ke raya mata ba shi bane.tana nan zaune gurum,taji ƙaran buɗe ƙofar,Islam ce ta shigo cikin Falon da sallama abakinta.
Da sauri mommy ta miƙe tana nufar inda Islam take"Islam ina ya kaiku?me ya faru?me yasa kuka daɗe?"mommy ta faɗa tana riƙe hannun Islam tare da kallon jikinta.
Murmushi Islam tayi da ƙoƙarin kawar da damuwar ta tace"kai mommy da Aslam muka fita fa, me kike tsammanin zai faru,yawo kawai mukayi tayi da kai ziyara gurare, mommy kar ranki ya ɓaci"Islam ta faɗa dai-dai lokacin Aslam Yana shigo.sosai yayi mamakin yadda Islam ta rufa masa asiri,ko da wasa bai tsammaci hakan ba,ahankali ya sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah da Islam bata yi masa wani sharrin Ba,amma yana mamakin dalilin ta na ƙin sanar da mommy abinda ya faru.

"Har naji daɗi hanaklina ya kwanta Islam,bakiji yadda tsoro ya kamani ba,ganin tun safe kuka fita amma baku dawo ba,yanzu kije kiyi wanka da sallah kici abinci ko,granny na can tana cigiyar ki"mommy ta faɗa cikin murmushi tana dafa kafadar Islam,
Murmushi itama Islam tayi,kafin tace "aikuwa nima nayi kewar granny sosai,mommy kice ya kawo min kayana kalli yadda ya shigo ba kayan"Islam ta faɗa cikin shagwaba.tana shigewa dakin granny.

Shikuwa Aslam Binta yayi da kallo cikin mamakin ta,shifa atunanin sa zata sanar da mommy abinda yayi mata,amma madadin haka ma kareshi tayi,lallai yasan ba banza tayi hakan ba tana da dalili.
"Me kuma ka tsaya tunani Aslam?ka kawo mata kayan mana may be tana da buƙatar su yanzu"cewar mommy kenan tana kallon Aslam.
Kallon mommy Yayi tare da jinjina kai ya fice,kayan ya dauko ya shigo dashi falon.

Hanan da jannat waɗanda suke zaune afalon tun dazu ,ya umarta dasu kaimata kayan dakin granny.
Haka suka ɗauka kuwa suka kai mata.lokacin har ta shiga wanka,sai granny dake zaune bakin gado tana magana ita kaɗai"to Ni gani nayi idonki kamar wanda kikayi kuka,wllh ƴar nan ki fadamin gaskiya idan wani abu Asalamu yayi miki na rantse da Allah zage zanyi daga Ni sai ɗan tofi da shima,mu daku iya dakuwa dashi,dan wllh bana tsoron sa"
"Wai ke granny baki da wani aiki saina dakuwa, sai kace gidan ƴan dambe?ai wllh ko dani aka barki baki isa darawa ba,bare yaya Aslam,kindai ga yadda Allah yayi masa halittar ƙarfafa"hanan ta faɗa tana ajiye ledojin hannun ta.
"Hananu ungo taki,granny ta faɗa tana mata dakuwa,kafin taci gaba,yo girman jikin sa na banza,ai gaɓa gaɓa bashi bane,abin azuciya yake,lokacin ina budurwa samari ma tsorona suke wanda sukafi Asalamu girman jiki ma bare shi.wllh. Duka zan masa,bare wata ke da kike tsaye kamar muciya zororo"granny ta faɗa tana nuna Islam,ita dai jannat bata ce komai ba,tana ajiye wa tayi waje.
Turo baki hanan tayi tana mai faɗin "gaskiya granny ki daina ɓata min suna wani hananu?kuma ki daina cemin kamar muciya,kina nufin fa atsaye na tafi bani da shape ko hips?ta faɗa tana turo baki.
"To ina kika ganshi?ai wannan sai Islama,yarinya son kowa,ga diri abuɗe ƙasan ta yake kamar turmi, ba irin naku ke da jannat ba,kamar na tsuntsuwa "granny ta faɗa tana cuno baki.
Haushi ne sosai ya kama hanan,na yadda kullum granny ke kushe su tana yabon Islam,tsaki tayi tare da barin dakin itama.
Nan granny ta fara ɓude kayan cikin ledar .
"Kai amma Islama kin iya zabe kalli kiga kayan nan?irin na turawa,kinga da anyi auren saiki yi ta sa abinki,dan zasu miki kyau wllh"granny ta faɗa tana bare wata chocolate mai daɗin gaske.
Lokacin Islam ta fito daga wanka,zuwa Wannan lokacin tuni jinin yazo mata,kuma marar ta daina ciwon,dan haka shiryawa tayi tsaf sannan ta zauna bakin gado suna ɗan hira da granny,tana Shan tea ɗin da aka kawowa granny,Dan kullum saita sha tea da dare.

Bayan sati guda da faruwar wannan abun,sam Islam ta fita daga harkar Aslam,bawai Dan ta hakura ba,sai dan ta samu ya saki jiki ta yadda zata rama abinda yayi mata cikin ruwan sanyi.
Shikuwa Aslam sai yake jin haushin yadda take share shi,idan yana guri saita nuna kamar bata ganshi ba,ko in tana zaune yazo gurin saita tashi.hakan yana sosa masa rai,gani yake kamar raini ne hakan.
Yau ma suna zaune afalo ita da Aman,Aslam ya shigo riƙe da uniform,Yana zuwa falon ta fara ƙoƙarin barin falon,bata son zama inda yake,dan tasan muddin suka zauna saita takale shi,kuma bata son hakan yanzu,so take saita hukun tashi tunkunna.

"Ke tsaya ki karbi wannan,gobe zaki fara zuwa school,zasu miki interview inkin cancanci shiga ajin su hanan zasu sakaki, in kuma kan ba komai dole kije js 3"ya fada da son takalota.
Juyowa tayi ba tare da ta lalle shi,ta miƙa hannu ta karbi kayan da yake miƙo mata tare da ƙoƙarin tafiya.

"Ke wai Ni sa'an kine?ya zaki rinƙa min abu kamar wani dan aiken ki ne?bazaki ce min kin gode ba,ahaka zaki karbi kayan kiyi gaba,kinsa da yadda na samo wannan school ɗin"Aslam ya fada azafafe yana huci.

Kallonsa Islam tayi sama da ƙasa,kafin ta taɓe baki tace "Ni na saka nemo min makaranta?nace maka bani da ilimi ne?kona bukaci neman ilimi ta hannunka?kai kasa kanka,dan haka bani da lokacin yi maka godiya Malam "ta faɗa cikin tsiwa tana barin gurin.
Binta Aslam Yayi da kallo cikin jin haushi,duk fafutukar da yayi wajen nemo mata makarantar amma da irin wannan iskancin zata saka masa kenan?

"Yaya kayi hakuri kasan halin Islam,bai kamata kana damun kanka akan lamarin ta ba"Aman ya faɗa yana kallon yayan nasa dake huci kamar kububuwa.

Lumshe ido yayi tare da fadin" aman bansan me yarinyar can ke nufi dani ba,yanzu ahaka za'ayi mana auren tana rainani?wane irin zama kake tunanin zamuyi?gashi sam su mommy sun kasa fahimta ta"da ya fada cikin damuwa yana kallon Aman.
"Kayi haƙiri yaya ahankali zata gyara,idan kunyi auren kai da kanka zaka koya mata yadda zata girmama ka"ya fada yana kallon Aslam.

"Hmmm wannan mai taurin kan ce kake tsammanin zata girmama Ni?yarinyar da bata tsorona ko kaɗan,inaga ma ba wanda ta raina arayuwar ta sama dani,kuma wallh zata sha wahala ne koda anyi auren" ya faɗi hakan tare da barin falon,baisan me yasa ba,ahalin yanzu baya son yadda take share shi,take nuna shi ba komai bane,yafi so koda faɗa ne ta kulashi suyi.inyaso yayi mata masifa itama ta rama .

Shiru Aman yayi yana tunanin dama shine ya samu damar da yayan sa ya samu mana,da ba abinda zai hanashi koyawa Islam sonshi,kuma zai kula da ita fiye da tunani,amma kash!! Daddy Yayi sauri. Yanke hukunci wanda dolen sa ya hakura da soyayyar Islam cikin ransa.

Washe gari kuwa kamar yadda Aslam ya fada,haka Islam ta shirya cikin uniform din, doguwar riga ce iya ƙwauri sai dan hijabi iya kafaɗa,rigar fara ce sai kasanta blue, haka hijabin ma ya kasance fari ne,sai kanbas fari da safa.ba ƙaramin kyau kayan sukayi wa Islam ba,ta sanya turare ajikinta mai kamshin daɗi.cikin takun ta na izza ta fito daga dakin granny,Dan mutanen gidan duk suna kan danning, ta fito tana tafe tana rangwada wanda zakayi tunanin da gangan takeyi,amma haka tafiyar ta take ,gaba ɗaya saida suka juyo suna kallon ta.banda Aslam,Wanda yayi ƙoƙarin sosai wajen hana kansa kallon ta.
"Masha Allah ƴata,kayan nan sun karɓeki sosai "mommy ta faɗa cikin murmushi.
Murmushi tayi itama tana zama kusa da granny tace "na gode mommy"
Kallonta granny tayi tana mai sakin dariya harda gudakafin tace
"Wllh kamar wata yar kasar waje,wannan kayan sunfi miki kyau akan kowa Islama,Allah ya bada Sa'a,kuma ban yarda ki ragawa kowa ba,duk wanda ya taɓaki ki maida masa martani cikin makarantar nan, bana son ki tsaya su raina ki"cewar granny tana buga cinya da cuno baki.

Dariya Aman Yayi yace "to ke granny da ake wa mutum faɗa yayi karatu,amma ke kina mata huɗubar tayi faɗa anya karatun kike so tayi?ya fada yana dariya .

"To saita tsaya araina ta? Kai kaji banzan,wllh kar naji karna gani, kiyi karatu kuma ki kwatar wa kanki ƴanci"
"Mu Bama a faɗa amakarantar mu "hanan ta faɗa tana shan tea.
Jannat dai bata ce komai ba dan yanzu haka ta koma bata cika surutu ba sam.
"Karki damu granny,kinsan ni ai bazan dauki tsageranci ba, wllh duk wanda yayi min kan kara saina yi masa na itace"cewar islam kenan tana cin soyayyen dankali.tare da hararar saitin da Aslam yake zaune.

Ahankali Aslam,Wanda tun fitowar ta bai ɗago kai ya kalle ta ba,duk da yadda yaji suna fadin kayan sunyi mata kyau,sai yanzu ahankali ya sauke idonsa akan fuskar Islam,wacce take nan fayau ba ko kwalli,amma tayi matukar yin kyau,fatar ta har wani sheƙi take.
Yasan kuma dashi take wannan maganar Tata,dan yana ɗagowa suka haɗa ido tana hararar sa. ajiye kofin hannun sa yayi tare da mikewa yace "mommy ya kamata mu tafi yanzu,dan lokaci yana ja,idan ta shirya ta sameni cikin mota"yana faɗin haka koyayi waje abinsa.

"Islam maza ki kammala ku tafi karki makara"
"To mommy "Islam ta faɗa tana mikewa.sallama tayi musu kafin ta fice.

Maimakon ta nufi motar ta Aslam, Wanda yake ciki yana jiran ta,kawai saita nufi garden,cikin mamaki yake kallon ta ,mekuma zatayi agarden da sassafen nan? yana nan zaune cikin mota yana tunani yaji tana buɗe bayan mota, baisan me ta saka ciki ba,kawai taji ta rufe ta zagayo ta shiga gaba.
Kunna motar yayi tare da nufar makarantar.

Ba wanda yayiwa wani magana cikin su, sai kira'ar sudies dake tashi cikin motar,har suka iso makarantar.
Ƙoƙarin buɗe motar aslam keyi idonsa ya sauƙa kan janbu dake kokarin dawowa gaban motar kusa da Islam,zaro ido Aslam Yayi tare da saurin matsawa jikin window yana rarraba idanu,ganin yadda birin ke ƙoƙarin ƙetarowa gurinsa...

Muje zuwa
Mrs babi ce.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: ____________"Ya Salam,ke !Islam tashi mana,menene ya sameki?am sorry I don't mean to do that,barci ne ya ɗauke ni, Islam Please wake up"Aslam ya faɗa cikin damuwa yana kallon fuskar ta,wacce hawaye ya gama bushewa.
Ko motsi Islam batayi,sai yadda ya juya ta kawai take binsa,cikin hanzari ya maidata kan kujera tare da ɗaura mata seat belt ya kunna motar tare da janta aguje yayi asibiti da ita.
Yana zuwa asibitin ya kira family doctorn su cewar yana tafe da petient.
Doctorn yace masa ya shigo da ita office ɗin sa kawai.
Aikuwa yana facking ɗin motar, ya buɗe ya fito,sannan ya zagayo inda Islam take ya ɗauke ta cak! Kamar yar tsana ,dan sam Islam bata da nauyi.
Kai tsaye ya nufi office ɗin doctorn da ita.
Kwantar da ita likitan yace yayi akan wani gado dake office ɗin,kwantar da ita yayi tare da tsayawa yana kallon ta,bai taɓa jin tausayin ta irin na yau ba,kuma sam bai ji daɗin abinda ya same ta ba.

Tambayar sa likitan yayi mai ya sameta har ta suma,
"Doctor I have no idea kawai na ganta asume bansan menene yayi silar suman ta ba,kawai ka duba ta"cewar Aslam Yana kallon likitan.
Ruwa likita ya fara ɗaura mata,kafin ya fara ƙoƙarin ganin numfashin ta ya dai dai ta.
Cikin nasara kuwa ta farfaɗo,saidai tana farkawa ta tashi da ciwon marar.dafe marar ta tayi tana kuka."wayyo Allah marata zan mutu,Aslam kazo ka kaini gida,wayyo Allah na"abinda ta tashi dashi kenan tana murƙususu,jikin ta har rawa yake.
Da sauri Aslam ya riƙe hannun ta yana faɗin"sorry Islam yanzu zamu tafi gida,kuma maran naki zai daina ciwo kinji"ya fada cikin tausayawa ganin yadda take ta haɗa zufa jikinta na rawa.
Allura likitan yayi mata,dan ya gane meke damun ta,kuma yana tunanin ko tasha kayan zaƙi ne.yana mata allurar kuwa cikin ƙanƙanin lokaci marar ta lafa mata sosai,ta daina murƙususun.tayi lamo kan gadon idonta arufe,ba abinda take rayawa cikin ranta,sai irin matakin da zata ɗauka kan Aslam.
Can suka koma kan kujera shida likitan yana faɗa masa,ai period ne zai zo mata,kuma da alama ta sha zaƙi, sannan irin hakan tana kasancewa ga ƴan matan da basu san maza ba,wasu magani yana musu aiki,wasu kuma dole sai idan anyi musu aure sun tara da namiji,kafin suke daina wannan ciwon marar.

Shiru Aslam Yayi Yana sauraron likitan har ya kammala bayanin sa,ahankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da yiwa likitan godiya,sannan ya buƙaci arubuta musu magani su tafi gida,tunda jikin nata da sauki,gashi tun safe suka fito yanzu kuma yamma tayi.

Haka likita ya rubuta musu magunguna,dai -dai lokacin kuwa,tuni ruwan da aka sa mata ya ƙare,likitan ya cire mata.
Cikin sanyin murya da tausayi Aslam yace "zaki iya tashi ne,ko ina taimaka miki?
Banza tayi dashi kamar bataji me yace ba,dan mugun haushinsa take ji matuka,wato tasan da gangan ya barta cikin mota,kuma ya kulle,dan kawai ya tsane ta, yana kuma son ta mutu,badan Allah yasa da kwanan ta agaba ba aida tuni ta sheƙa,zaiyi bayani ne wllh"ta faɗa cikin zuciyar ta tana mai ci gaba da kwanciyar ta.
Ba irin maganar da Aslam baiyi mata ba,amma tayi biris kamar batajin sa,ƙoƙarin ɗaga ta yayi ganin bazata tashi su tafi ba,
Amma sam taƙi yarda ya taba ta,ɗaya kawo hannu zata buge hannun .yasan haushin sa take ji,amma ai shima bada son ransa yayi mata hakan ba,shine take wani neman raina masa hankali dan taga yana lallaɓata,nan take shima ransa ya ɓaci,cikin tsawa yace "ke dalla malama ki tashi mutafi,In kuma anan zaki kwana sai nayi tafiya,dan ina da abubuwa masu muhimmanci agabana" Aslam ya fada cikin fushi yana hararar ta.
Ko ci kanka Islam batace masa ba,kuma batayi yunƙurin tashi ba.hakan ya karasa hasala Aslam,sai huci yake ransa ya gama ɓaci.
"Kayi mata ahankali Aslam,kasan yarinya ce kuma bata da lafiya , bari nayi mata magana "cewar likitan yana dafa kafadar Aslam tare da kallon Islam ,wacce ke kwance ko motsi batayi.
Murmushi likitan yayi yana mai cigaba da kallon Islam dan lokaci guda yaji ta kwanta masa cikin ransa, kyakykyawa da ita mai saurin shiga rai.
Ahankali ya matsa kusa da gadon da take kwance, ɗan leƙa fuskarta yayi,dan ta basu baya.cikin taushin murya da sigar rarrashi ya fara mata magana"
" Sannu ko, Ƙanwa ta,yi hakuri ki daure ki tashi,In kuma kina jin ciwo ne saiki faɗa min, In baki magani kinji?yi haƙuri daure ƙanwa ta"likitan ya fada cikin taushin murya sosai.
Hararar likitan Aslam Yayi,aransa yana cewa "ji banza yadda yake wani maƙale murya kamar wani mace,wawa kawai"Ya fada cikin zuciyar sa yana harara likitan da yaji haushinsa ya kamashi lokaci guda,ganin yadda yake yiwa Islam magana kamar wani saurayin ta.
Aikuwa ahankali Islam ta yunƙura tare da zama akan gadon kafin ta sauƙo daga kan gadon ahankali,fuskar nan Tata amatuƙar ɗaure.ta nufi ƙofar fita daga office ɗin ta fice.
Binta sukayi da kallo dukan su,Aslam wani bakin ciki ne yake nuƙurƙusar zuciyar sa,wato shida yayi mata magana tayi banza dashi, saboda ta maidashi ɗan iska,amma wannan garan yana mata magana ɗaya, tabi umarnin sa, lallai ta raina shi,ko gidan uban wa ma tasan wannna banzan da har zataji maganar sa sama da tashi.rai bace shima ya nufi ƙofar office ɗin da takardar maganin ahannunsa.
"To Aslam Allah ya sawake agaida gida,Please akula da petient sosai saina zo dubiya"likitan ya fada cikin murmushi yana kallon Aslam dake barin office din.
Ko ci kanka Aslam baice masa ba yayi waje da sauri,tare da buga ƙofar da ƙarfi,ji kake buumm ! Ƙofar tayi ƙara.
Saƙare likitan yayi yana bin ƙofar da kallo,meye kuma ya ɓatawa Aslam Rai haka?ko dai ɓacin ran yarinyar ne yasashi wannan fushin?any way,koma dai menene shiya shafa,shikam yaga mata,kuma zaibi sawu,dan yarinyar ta tafi da imanin sa, masha Allah ga diri.
Aslam kuwa cikin ransa yake faɗin"shege, gidan ubanka zaka zo?wllh duk randa naga wannan shegen agidan mu da sunan yazo gurin Islam,saina ci uwarsa,daga zuwa ya duba ta shine yake wani shishshige mata.
koda ya ƙarasa Islam bata cikin motar,mamaki ne ya kamashi,to ina kuma ta tafi?ko wane gurin tayi kuma?kamar wanda akace ya duba hanyar fita daga asibitin,aikuwa ya hango Islam har ta kusan ficewa daga asibitin.
Dafe kai yayi tare da lumshe idonsa,to gidan uwar wa zata?wa tasani anan?wannan yarinyar nema take ta zame masa matsala arayuwa,salon tayi wani gurin ta ɓata,ace da gangan ya batar da ita,ta ja masa damuwa.
Shiga yayi cikin motar tare da bin bayanta,lokacin har ta fice daga asibitin,ƙafar ta ko takalmi babu,ta miƙe kwaltar tana tafiya abinta.
Gabanta yasha da motar tare da tsaya ya buɗe mata ƙofar motar, alamun wai ta shigo.

Ko inda motar take Islam bata kalla ba,ta zagaye motar taci gaba da tafiyar ta.ƙara tarar gabanta yayi tare da buɗe motar yace "bazaki shigo bane ko yaya"ya fada cikin faɗa da ɗan tsawa.
Sake kaucewa tayi tare da ci gaba da tafiyar ta duk da yadda takejin jikin ta ba kwari,gashi marar ta na mata ciwo kaɗan -kadan, amma ta gwammace tafi aƙasa,akanta shiga motar sa
.cikin haushi da ɓacin rai Aslam ya fito yayi kanta,yana zuwa bai jira wata-wata ba ya sure ta ya juya gurin motar da ita.
Dukan sa Islam keyi cikin haushi da kunar rai tana zille wa,tare da faɗin.
"Dalla malam ka sake ni, bana son iskanci,Wanda kaje kayi bai isheka ba shine zaka rinƙa tabamin jiki,dalla saukeni bazan shiga motar taka ba,banza mugu kawai" abinda take fadi kenan cikin ɓaci rai tana dukan sa da son kwacewa.amma riƙon da yayi mata bazata iya kwacewa ba,har ya sanyata cikin motar ya kulle tare da zagayawa mazaunin driver ya shiga shima. kuka mai tsanani Islam ta sanya tana tureshi tare da dukan ƙirjinsa.
"Ka budemin na fita bana so !bana so" abinda take fadi kenan Muryar har sarƙewa take.kana jin yadda sautin kukan ke fita kasan taji zafin abinda Aslam Yayi mata matuka.duk yadda yaso riƙe hannayen dan ta daina ƙoƙarin dukansa, kin yarda tayi,bori kawai take masa cikin mota tana kuka da kai masa duka,ganin haka yasashi kawai ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam-tsam.ta yadda dole ta haƙura da dukan nasa tayi lamo kan faffaɗan ƙirjinsa tana kuka mai sosa zuciya.

Lumshe ido Aslam Yayi Yana sauraron kukan tana,yana jin ba daɗi cikin zuciyar sa.duk da irin yadda yake jin ya tsane ta,amma dole yaji ba daɗi cikin ransa,tunda shine silar wannan kukan Nata.
Islam kuwa ta riƙe gefen rigar sa ƙam _ƙam tana kuka sosai harda shashsheƙa.....


Hmmmmm masu karu anya kuwa waɗan nan mutane ?
Muje zuwa dai.

Mrs babi ce
Anty mammy.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: _____________Murmushi Aslam yayi,tare da kamo hannunta cikin nashi yace "muje ko amarya Aslam"ya fada yana wani matsa mata hannu cikin salon sa mai tada hankali tare da kashe mata ido.
Sosai Islam ta runtse idanunta,sakamakon yadda yake matsa hannun nata,cikin salo mai wuyar fassara wa,wani irin yanayi take ji ajikinta,dan haka da sauri ta fizge hannun ta,tare da balla masa harara tace "malam karka ƙara taɓani bana son iskanci"ta fada cikin ɗaure fuska tana nufar ƙofar fita daga falon.

Murmushin mugunta yayi tare da bin bayanta yana mai faɗin"da gaske bakya son iskanci?lallai aiki ya ganki dan kuwa niɗin cikakken dan iskane,kuma zakiga salo-salo na iskanci iri-iri,dama ai saboda kina son iskancin kika ce saikin aureni,kuma Indai iskanci ne kinsamu yarinya"ya fada dai-dai lokacin sun kawo wajen motar sa,mai shegen kyau da tsada.
Tsaki Islam tayi tare da tsayawa jikin motar ta na masa kallon sama da ƙasa"ai dama ba sai ka faɗa ba,nasan kai ɗin riƙaƙƙen dan iska ne,sai dai wallahi ka sani,zan aure ka ne badan wannann tunanin ba,dan kuwa koda wasa kace zaka taɓani,wllh zakaga yadda ake bala'i"ta faɗa cikin tsiwa tana murguda baki.

Murmushin gefen baki Aslam Yayi,tare da cije lips ɗin sa na ƙasa,cikin ransa yace "yarinya aiko mutuwa zanyi baki isa in nemi wani abu ajikin ki ba,bare kiyi tunanin zanyi sex dake,Allah ya tsareni"amma azahiri buɗe motar yayi ya shiga tare da faɗin"Allah ya kaimu lokacin zanga abinda zakiyi innazo hawa kanki "ya fada kai tsaye ko ajikinsa.
Kallon sa Islam tayi baki buɗe,dan ita kam kalmar tashi tayi mata nauyi,wai inyazo hawa kanta?sai kace wata doki.
Banza tayi dashi tare da buɗe gaban motar ta shiga.wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗi suka ratsa hancin ta,har saida ta lumshe idon ta,kafin ta buɗe tare da jingina bayan ta da jikin kujerar.

Kunna motar Aslam yayi,tare da barin harabar gidan,fuskar sa aɗaure sosai,wllh shi har kunya ma yake ji agansa da wannan yarinyar, Ai ajinsa sai ya zube,adaina ganin girman sa,haka kawai yana zaman sa lafiya za'a ƙaƙaba masa wannan alaƙaƙai ɗin,wacce basu san daga ina ta

Please Login or Register in order to submit comment