Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aɗakin sa.
Haka ya wuce yaran suna ta masa sannu da fitowa.
Yana shiga ɗaki kuma saiga Islam sun fito ita da granny.
Da sallama ya karasa dakin Daddyn nashi,zama yayi bayan an amsa masa sallar.
"Daddy barka da gida "ya faɗa cikin ladabi.
"Yawwa Aslam,ya ƙafar taka ?fatan dai ba wata matsala yanzu"cewar Daddy Yana kallon Aslam.
"Babu daddy ai tuni ƙafar ta warke sosai ma,bana jin ciwo ko kaɗan"cewar Aslam,Yana son jin abinda ya sanya daddy neman sa,dan shi sam ya ma manta da umarnin da daddy ya bashi na neman mata.
Jinjina kai daddy Yayi kafin yace "Alhmdllh,yanzu saika faɗa min inda ka samo yarinyar da zaka aura ko?dan yau adadin kwanakin dana ɗibar maka suka cika,dan haka ina sauraron ka"daddy ya faɗa fuska ba wasa.
Darammmm !!! Gaban Aslam ya faɗi,Dan shi wllh yama manta da wannan batun,kuma yana ganin tunda yayi rashin lafiyar nan,ai Daddy zai dan jinkirta akan batun,ashe Daddyn yana sane kuma bai manta ba.
Shiru yayi kansa a ƙasa,dan baisan me zai faɗa wa Daddyn ba.
"Ina sauraron ka Aslam,bana son shirme fa,kayi shiru kana wani sunkuyar da kanka ƙasa,kai nake jira"cewar daddy cikin dan ɗaga murya,dan yaga aslma na son kawo masa wargi.
Ɗago da kai Aslam Yayi yana kallon mommy,fuskar sa tayi kalar tausayi,mommy kuwa kawar da nata kan tayi dan kuwa bata goyon bayan Aslam awannan karon,itama tana so da ƙaunar ganin yayi aure.
Cikin sanyin murya Aslam ke faɗin"daddy kayi haƙuri Dan Allah aƙara min lokaci,wllh ban samu damar tsayawa na kalli yan matan Bama ,bare na zaɓi matar da zan aura,saboda wannan ciwon ƙafar da nayi,amma in sha Allahu zan kawo matar da zan aura very soon daddy"Aslam ya faɗa yana fatan amincewar daddy akan abinda ya faɗa.
"Zancen banza kenan,Aslam saboda ka raina Ni kuma baka da burin yin auren,shine zaka kawo min wannan maganar anan?to wllh na kara maka kwana uku,idan baka kawo min matar da zaka aura ba,zan ɗauki mataki mai zafi akan ka,dan haka zaɓi ya rage naka"cewar daddy kenan yana maida hankalinsa kan labaran da ake haskawa.
Kallon mommy Aslam Yayi tare da ɗan turo baki yana mai kamo hannunta,cikin ƙasa da murya yace "mommy please kisa baki ya ɗan ƙaramin lokaci mana"
"A'a Aslam,wannna karon ba ruwana wllh,duk hukuncin da Daddyn ku ya yanke shikenan,dan na fahimci ba son yin auren kake ba,haka kawai ka zauna sai jawa mutane rai kake,wllh ka samo matar kamar yadda ya faɗa"cewar mommy tana zare hannun ta daga cikin na Aslam.
Haka nan Aslam ya tashi jiki ba kwari ya bar ɗakin na daddy,tunani yake yanzu shi wa zai kawo matsayin matar da zai aura nan da kwana uku?shi fa sam har yanzu baiga dai-dai dashi agarin nan ba,duk wayewar su tayi yawa,shikuma mace yake so ya aura mai tarbiyya yar mutunci.yana wannan tunanin har ya kawo tsakiyar falon bai sani ba.saida yaji granny na faɗin"yoo ikon Allah,yau naga sabuwar tijara gangariya,yanzu kai Asalamu, kamar wani Giwa ka taho sanƙan-sanƙan kana neman take Ni?kalli yadda kake wani tafiya kamar bijimin sa ,wllh idan ka mangareni da wannan ƙafar taka kamar shebur saina rama,Dan zagewa zanyi mu doku da kai,ba tsoronka nake ji ba"cewar granny cikin masifa,tana matsawa gefe dan aƙasa take zaune,shikuma Aslam ya biyo ta jikinta sosai kamar zai bi ta kanta,wanda shi baima luraba ko kaɗan.
Tsayawa yayi tare da kallon granny yadda ta haƙikance tana bala'i girgiza kai yayi kafin yace "to sarkin faɗa amma dai banbi ta kan naki ba ko?saiki sarara da wannan surutun naki kamar aku"
"Wllh uwarka ce Aku bani ba ,yaron banza kawai,ai Gara kayi kayi auren ka bar gidan nan kowa ya huta mai baƙin hali"
Harara ya bankawa granny kafin yace "ba saiki yimin auren ba,cikin garin nan banga macen da zan iya aura ba,gaba ɗayan su basu da tarbiyya,yan iskane lalatattu. ba wacce zan aura "
Ya kai zancen sa yana yatsine fuska.kuma har lokacin idonsa bai sauƙa kan Islam ba.

Ita kuwa Islam jin abinda yake fadi,saitayi tunanin da ita yake,dan haka ranta yayi mugun ɓaci sosai,ita da ta fita harkar sa shine yake yaɓa mata maganganu haka?
Cikin zafin zuciya ta kalli granny tace "granny kinsan duk wanda yake watse wa atiti baya son yayi aure,sannan yana kallon kowa ne kamar halin su ɗaya,kuma da yawa masu cewar yaran mutane watsatstsu ne ,to sune manyan watsatstsu dake bata tarbiyyar yaran,daga baya kuma suce bazasu aure su ba da sunan basu da tarbiyya" tayi shiru tana huci da hararar Aslam,kana jin yanayin yadda take maganar ta kasan ranta abace yake,kuma kai tsaye take aika saƙo zuwa ga wani.

Sai lokacin Aslam ya San da ita agurin,kallon ta yayi fuskar sa ahade sosai,rabon da ya ganta kusan sati kenan,ashe mayyar tana gidan har yanzu?
"Kwarai kuwa Islama zancen ki haka yake,sune masu sanya yaran mutane suna latsewa a lungu,wllh tun wuri Gara kayi aure kafin mu nemo maka da kanmu"
"Allah ya kiyaye Ni Aslam ,anemo min matar da zan aura,ai wannan sai ya'yan da basu da galihu, masu bin gidajen mutane suna laɓewa,waɗan da suka gama yawon barikin su sukaga ba ci, sune akewa irin wannan, amma Ni cikakken ɗa ne wanda ke gaban iyayen sa,dan haka ina da cikakkiyar damar da zan zabi matar da nake son aure ba kowacce kara biti ba "Aslam na kawo wa nan azancen sa yayi wucewar sa zuwa ɗakinsa.
Nan ya bar Islam da tarin damuwa cikin ranta,wato itace marar galihu agidan?sannan wacce ta gama yawon iskancin ta?hmmmmm Aslam kenan zan nuna maka kalar nawa karuwan ci,zaka sha mamaki na Ni Islam.ta faɗa cikin ranta tana murmushi tuno da irin makircin da zata kullawa Aslam.

Washe gari da yamma,jannat tayi baƙo, dan haka ansha ƙwalliya cikin riga da siket na atamfa,wanda suka matse jikinta,shima sai da mommy tayi da gaske kafin ta sanya kayan,dan ita ƙananan kaya take son sanyawa.suna ɗakin baki suna hirar su ita da saurayinta, wanda hira ce wacce bata dace ba sam,dan jannat tana jikin saurayin sai shafa ta yake da taɓe-taɓe ajikinta,su aganinsu wannan itace soyayya.
Sunyi nisa sosai da shafe shafe su,wanda har basu sani ba,suke ta sauke nishi na jin dadi,dai dai lokacin kuma Islam ta taho dan zuwa garden,kawai take jiyo nishi sosai aɗakin,tunani tayi ko menene cikin dakin haka?dan bata san jannat na cikin dakin ita da saurayin ta ba,kawai ta sanya kanta cikin dakin,
Abinda idanunta suka gane mata ne yayi silar kwalla karanta,cikin tsoro.
Jannat ce kwance kan kujera yayi da saurayin ke kanta yana lashe duk wani sannan na jikinta,dan tuni anyi wurgi da rigar jikin jannat.
Ihun Islam kuma yayi dai dai da karasowar Aslam gurin,dan haka da sauri ya kunna kansa cikin dakin da yajiyo ihun,yana shiga idon sa yayi arba da jannat kwance maɗe -maɗe wani gardin yana sarrafata.
Tsabar tsoron abinda Islam ta gani jikinta rawa kawai yake da sauri ta nufi Aslam Wanda shima yayi mutuwar tsaye cike da mamakin jannat ɗin....

Muje zuwa anty mammy ce.
Mrs babi
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: ___________"Wllh sai kayi dana sanin faɗa min wannan baƙaƙen maganganun,zaka gani sainayi maganin ka,zaka gane Islam bata ɗaukar raini"tana gama faɗin haka cikin kuka da ɗaga murya ta nufi cikin gida cike da ɓacin rai.
Kai tsaye ta nufi part ɗin Daddy.
Nocking tayi tare da sallama,daga mommyn har granny suna ɗakin,dan suna tattaunawa ne akan maganar auren tare da daddy.
"Shigo mana Islam,fatan dai ba wata damuwa?"cewar daddy bayan yaji muryar Islam.
Ahankali ta tako zuwa cikin ɗakin,guri ta samu tare da zama tace "ba wata matsala daddy,har na yanke shawara ne,naga ba bukatar daukar dogon lokaci shine nazo sanar daku"tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Dukkan su fata suka rinkayi, Allah yasa ta amince da batun auren,karta ce bata yar da ba.
"Yi magana ƴar, nan muna sauraron ki,wllh har na fara jin cikina yana ƙara ƙulululu karki ƙi amincewa"cewar granny tana dafe cikin ta da zubawa Islam ido.
"A'a granny nazo ne in sanar daku cewar na aminci,zan auri Aslam,domin kuwa dama ya sanar dani cewar yana son aure na,nice dai ban bashi haɗin kai ba,saboda alokacin naga kamar shekaruna sunyi ƙanƙanta da yin aure,amma ahalin yanzu na amince dan nima ina sonshi mun dai dai ta kan mu,shine ma ya aiko Ni yanzu in sanar daku,wai shi yana jin nauyi"Islam ta faɗa har da sunkuyar da kai ƙasa"
"Alhamdullah wannna abu yayi min daɗi sosai,Hajiya ! Kiji fa dan Allah,dama yaron nan yasan yana son Islam ɗin maimakon ya nasar damu tun wuri shine ya tsaya kunbiya-kunbiya.ko meye na jin nauyin?
Na gode Islam Allah yayi miki albarka da wannan alfarmar da kikayi mana Nagode sosai"cewar daddy cikin farin ciki.
Mommy ma abin yayi mata daɗi sai murmushi take tana godiya ga Allah cikin ranta.
Granny kuwa guda ta sanya tare da faɗin"kai wannna al'amari yayi daɗi,to ko shiyasa dazun Asalamu ya tsaya ya kasa fita? so yake ya sanar damu suna son juna shida Islama! Ja'irin yaro ashe yana jin kunya, sannu Islam Allah ya yi miki albarka mun gode sosai wllh "

Murmushi yaƙe Islam tayi kafin ta mike tare da barin dakin.tana fita kai tsaye ta wuce garden,Kan bishiya ta haye tare da sanya kuka.Allah ya gani wllh bata son Aslam,tayi haka ne kawai,dan ta ƙunsa masa baƙin ciki,ta nuna masa bai isa yace batakai matsayin da zai aureta ba,kuma zatayi amfani da wannan damar ta gasa masa aya ahannun sa.zatayi duk mai yiwuwa Dan ganin anyi auren. Nan
Tana nan zaune kan bishiyar tana zubda hawaye,taji andafa kafaɗun ta ,da sauri ta ɗaga kai sukayi arba da malamin ta,cike da kewa da ɗokin ganin sa ta riƙe hannunsa tana ƙara ƙarfin kukan ta.
Murmushi yayi tare da shafa kan Islam,yana girgiza mata kai."ki daina kuka Islam,wannan itace ƙaddarar ki,zaki zama tauraruwa cikin gidan nan,zaki taimaka musu ta hanyoyi da ban -daban kuma kinyi dai-dai da kika amince da batun auren,karki ɗauki ƙiyayyar dake tsakanin ku abakin komai,wata rana zata gushe,farin ciki zai mamaye zuciyar ku,daga yau karki ƙara kuka,kizama jaruma kamar yadda na sanki, kina da aiki gagrumi nan gaba "yana kaiwa nan azancen sa,ya share mata hawaye tare da yin addu'a cikin tafin hannun sa ya shafa mata agoshinta.
Sannan yayi mata murmushi ya bace bat!.ajiyar zuciya Islam ta sauke,lokaci guda ta nemi damuwar ta ta rasa,dan haka sauƙowa tayi daga kan bishiyar ta nufi bakin swimming pool ta zauna tare da zura ƙafafun ta ciki.

Aslam kuwa yana can cikin dakin sa,baƙin ciki kamar ya kashe shi,duk da yasan cewar baza ta amince da batun auren ba,amma shi haɗata ma da akayi da shi,abin ba ƙaramin ƙona masa rai yayi ba,shi Gara ma kawai yayi auren kowa ya huta,dan haka zai nemi yarinya yar mutunci kawai ya aura.
Kwanciya yayi akan gadon sa yana mai tunanin ta ina zai fara neman auren?wa ya kamata ya aura,wayar sa ce tayi ƙara alamun ana kiran sa,dan haka dauka yayi tare da kangawa akunnen sa.
"Hello daddy,ok gani nan zuwa"ya faɗa yana mikewa tsaye,murmushi yayi tare da faɗin,harta sanar dasu kenan,hmmmm yarinya da kin yabawa aya zaƙin ta wllh"da sallamar sa ya shiga falon na daddy ya zauna.
"Daddy gani"ya fada kansa asunkuye.
"Yawwa Aslam,munji saƙon ka daga bakin Islam,amma meye na ƙin sanar damu gaskiyar abinda ke cikin ranka sai kace muba iyayen ka bane?ai babu hijabi tsakanin mu da kai"
"Ayi hakuri daddy,Ina gudun ɓacin ran kune shiyasa ban faɗa ba,amma tunda Ita ta faɗa shikenan Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkairi"Aslam ya fada cikin sanyin murya kansa a ƙasa ,farin ciki fal zuciyar sa.

"Ba komai Allah yayi maka albarka ya shirya ku,yanzu Abinda nake so dakai shine,ka ɗauki Islam kuje store dan ta zabi kayan da take buƙatar yin amfani dasu,tun dadewa nake son yin hakan,amma azuri yayi min yawa,to kaga yanzu aiki ya koma kan ka,sannan akwai buƙatar asanya ta amakaran ta ,duk da dai cewar tayi karatu,amma ya kamata ta koma,idan da hali sai ahaɗasu da hanan su kammala tare"daddy ya kai ƙarshen maganar sa yana kallon Aslam.
"To daddy za'ayi kamar yadda kace Allah ya ƙara girma"Aslam ya fada cikin farin ciki da tunanin komai yazo ƙarshe cikin sauƙi.
"Ohh!! Kinibabben yaro ana so ana kaiwa kasuwa ai wllh ka gode Allah ma dan samun wannna damar sai ɗan baiwa"cewar granny tana hararar Aslam.
Banza yayi da ita yana mai ficewa,shidai koma me za'ace bashi da matsala tunda an yakice masa auren wannan kucakar .

Washe gari da safe gaba ɗaya sun hadu wajen cin abinci,daddy ne kawai baya gurin dan yayi asubancin barin ƙasar ,kowa da abinda yake ci,Aslam yana zaune cikin shiga ta ƙananan kaya,sunyi matukar karbar jikinsa,fuskar sa kamar kullum aɗaure baya dariya.
Yayin da mutuniyar ke kusa da Aman, Wanda damuwa da alhinin rabuwa da Islam suka hana masa cin abincin sai juya cokali yake,
Granny kuwa an zage ana ba naman kaza hakkin sa,
Mommy dai tea kawai take kurba.
Jannat na gefe sanye da hijabinta tana cin jallof ɗin taliya data sha kayan lambu da naman ƙaramar dabba,sai hanan dake shan romo.
Ahankali Islam ta ɗago kanta tare da kallon Aslam,Wanda ya zage Yana cin kwai da dankalin turawa.
Harara ta banka masa kafin ta ɗan yi murmushi tace "kai Aslam,ka wani zage sai cin dankali kake,Please ka ɗanci taliyar nan mana,kasan bana son yunwa ta kama ka,Gara kana ɗan ci abu mai nauyi,duk da ma taliyar ba nauyi gareta ba"ta faɗa cikin maƙale murya tana murmushi.
Cikin mamaki Aslam ke kallon ta,wato wani sabon barikin ne wanna ta tsiro dashi,salon yayi mata wani abu ace shine marar gaskiya,hmmm yarinya Indai bariki ne kin tarar dashi,nidai tunda ba batun auren nan ai nafi kowa farin ciki,dan haka cikin ɗan murmushin da bai kai zuciya ba yace "A'a Islam banaso na cika cikina sosai,wannan ɗin ma ya ishe Ni,ke dai kiyi hanzari ki kammala,dan zamuje ki zabo kayan da kike ɓukata,sannan ranar monday zaki fara zuwa school"ya kai zancen sa yana murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo.
Ba haka Islam taso ba,so tayi ta bata masa rai yayi kurarin sa ta yadda idan anyi auren ma zatayi ta ɗora masa sharrin da zaiyi ta shiga matsala,amma duk da hakan ma zai zo hannu.kuma tana mamakin ta yadda akayi bai nuna damuwar sa ba ahalin yanzu kamar yadda yayi da farko.
Cikin ɗoki tace "kai amma ka burgeni,yau zan ga gari akaro na farko,Please idan mun fita ka biya dani guraren masu kyau, musha lemo tare irin yadda masoya keyi,bari naje na shirya"Islam ta fada tare da kashe masa ido ɗaya kafin ta nufi dakin hanan.

Binta yayi da kallo,yama kasa gane kan bayanin nata,wai susha lemo tare,irin na masoya,banza wawiya,can dai ƙyaje ki samo masoyin ki ba Aslam ba.

"Kai wllh Asalamu kayi sa'a,domin samun wannan yarinyar alkhairi ne agare ka,ji yadda take nuna maka soyayya gaban kowa,inaga anyi auren?wllh harna matsu ayi bikin nan,wai ranar nan za'aga yadda ake ado da taka rawar sabada"cewar granny tana wani juya kafada.

Dariya su jannat suka sanya,hanan tace "granny kiyi dai ahankali kar garin rawa kije ki karya kafaɗa"ta ƙara sa da dariya ƙasa-ƙasa.
"To muguwa mai baƙin hali,fatan ki ya sari ɗanyen kashi,ai lokacin ina budurwa,kaf garinmu ba wacce ta kaini iya rawar kalangu ta gani -kani gwalelen ka"granny ta faɗa tana ɗan karya baya.dariya sosai suka sanya sakamakon yadda granny tayi rawar,hatta mommy saida ta dara ,
Aman yace "woo matar gaskiya kinyi zamani kice haka kuke karya ƙugu alokacin yan matanci?"ya fada cikin dariya da ƙoƙarin kawar da damuwar dake cikin ransa.
"Sosai ma ai ina ,zuwa gurin mai kalangu zakaji an ɗauki ihu da sowa,ana gwanar rawa tazo hatta kidan kalangun sauya wa yake"ta faɗa cike da alfahari tana dariya.

Shidai Aslam kallon su yake yana kuma son fahimtar inda zancen su ya dosa,kamar fa granny na son cewa har yanzu shine wanda zai auri Islam,kuma yadda yaga Islam na masa wasu abubuwa kamar har yanzu zancen yana nan.
Kallon mommy Yayi cike da son ƙarin bayani yace "mommy wai me granny ke son faɗa min ne?nifa ban gane ba?"ya fada cikin yanayi na damuwa.
Kallonsa mommy tayi tare da ɗaure fuska tace "kamar ya baka gane ba?bayan kaine ka aiko Islam ta sanar damu alaƙar dake tsakanin ku da ita,kuma ta bayyana mana amincewar ta da taka akan auren,kuma dama Daddyn ku ya sanar dakai tare za'a hada bikin ka dana jannat,shine dalilin fitar dazakuyi yanzu,dan ta zabo kayan da take buƙatar amfani dashi kafin ahaɗa mata lefe.

"What !!!mommy me kike son faɗa min?yaushe mukayi wannan maganar da yarinyar nan?mommy ta yaya zan so wannan yarinyar?dama ba magana kuke min akan fasa haɗin auren ba?kenan ba zuwa tayi ta sanar daku bata sona ba?"Aslam ya fada cikin tashin hankali da tarin damuwa.

"Kai aslam karka maidamu wasu shashashai mana ! Wllh tun wuri karma ka kawo wani zancen banza,domin ranka zai mugun ɓaci agurin Daddyn ku kaji na faɗa maka"mommy ta faɗa cikin faɗa tana nuna Aslam.

Runtse ido Aslam Yayi da mugun ƙarfi,kenan wannan shine dalilin da yasa Islam ke masa wannan karuwanci?lallai yarinyar nan ta jawa kanta bala'i wllh sai tayi dana sanin yarda da wannan auren da tayi,haba wllh angama cutar sa, Indai aka aura masa Islam.

Dai-dai lokacin kuma Islam ta fito sanye da doguwar rigar hanan,ta atamfa,tayi matukar yi mata kyau sosai ,rigar a shape ce mai dogon hannu,sai stones da akabi rigar dashi gaba ɗaya,bata sanya mayafi ba ,kawai ɗan kwalin kayan ta ɗora akanta ba tare da ta ɗaura ba.

"Na shirya,ya kaga kayan fatan dai sunyi mini kyau?"Islam ta fada tana ɗan juyawa kamar mai tallar kaya.
Wani malolon baƙin ciki ne ya turnuƙe Aslam ,cikin masifa da ɓaci rai yayi kan Islam,
"Uban waye yace kije ki sanar dasu mommy nace ina sonki?yaushe mukayi haka dake Ni Aslam nace ina sonki?me zanyi dake ke wacece da zan yarda in haɗa soyayya dake ?meyasa kikayi min haka ?meyasa?"Aslam ya fada cikin ƙara ji da masifa.
Murmushi Islam tayi cikin barikan ci tace "saboda ina sonka ina ƙaunar ka,kaine rayuwata bazan taɓa iya rayuwa ba kai ba,dan Allah mommy ki bashi hakuri wllh nidai na amince ina sonshi,yana fushi ne dan abaya na nuna rashin amincewa ta"Islaman ta fada cikin marairaitar murya tana kamo hannun mommy.

Muje zuwa masu karatu .

Mrs babi ce
Anty mammy.
[29/12, 6:42 pm] Mamy Kabir: ___________"Dan Allah mommy ki bawa Aslam haƙuri,karya ce baya sona,dan bazan iya rayuwa bashi ba,shi nake so na aura mommy"Islam ta faɗa cikin marairaice murya tana rike hannun mommy.

Galala Aslam Yayi Yana kallon karuwanci irin an Islam,lallai yarinyar nan,saboda yace bazai aureta ba ,shine taje ta haɗa masa ƙaryar cewa shine ya aikota ta sanar dasu mommy amincewar su akan auren?wai ma to menene nufin ta na amince wa da wannan haɗin?me take nufi da yin hakan?kodai turo ta akayi ta shiga cikin rayuwar sa ne ?yana cikin wannan tunanin ya tsinkayo Muryar mommy tana faɗin"ki kwantar da hankalin ki Islam,badai kin amince da auren ba?kuma ki na son Aslam?
Gyada kai Islam tayi kamar ƙadangaruwa.
Cigaba mommy tayi da cewa-ki kwantar da hankali ki baki da wani mijin daya wuce Aslam,inhar mune muka haifeshi, kamar anyi auren nan angama"
Mommy ta faɗa tana mai shafa kan Islam.
"Nagode mommy idan har kuka aura min Aslam kungama min komai arayuwa"Islam ta faɗa tana ɗora kanta akafaɗar mommy,ɗago idonta tayi tare da kallon Islam,aikuwa carab suka haɗa ido,kashe masa ido ɗaya tayi tare da dage gira ɗaya tana murmushin kazo hannu.
Kamar Aslam zai ƙwalla ihu yace "mommy Kinga abinda take min ko?wllh wannan amincewar ba har zuciya tayi ba,akwai manufar ta tayin hakan,mommy please ki saurare ni wllh bana son yarinyar nan har cikin zuciya ta,kuma itama ba sona take ba kawai tana son baƙanta min ne"ya ƙarasa kamar zaiyi kuka yana riƙe hannun mommy.
Kuka mai ƙarfi Islam ta sanya tana faɗin "wllh ina sonka mommy wllh ina sonshi,shine rayuwata mommy kitaimaka min granny kiyi wani abu karna rasa rayuwata"Islam ta fada tana komawa jikin granny.
Kuka granny ma ta sanya harda rinji tana mai riƙe Islam ajikinta sosai"Allah sarki ƴata kiyi haƙuri Indai ina raye saikin auri Aslam,Indai ni ce na haifi ubansa,wllh saiya aureki,shashashan banza,to idan har ka samu ma ka auri wannan yarinyar ai wllh kayi sa'a arayuwar ka,dubeta fa son kowa ƙin wanda ya rasa,kaima borin banza kake yi, dan kasamu za'a haɗaka da ita banza mai kama da ƴan dambe"granny ta fada cikin masifa kamar zatayi dambe da Aslam,
Runtse ido Aslam Yayi,ganin gaba ɗaya sun kasa fahimtar sa,dan kuwa cikin fushi mommy tayi ɗakinta.
Da sauri Aslam ya rufa mata baya yana kiran sunan ta.

Islam na ganin haka ta yi wani kayataccen murmushi,shikenan burin ta ya cika,koba komai yanzu Aslam ya shiga cikin matsala sosai.
Hannu ta sanya ta sharewa granny hawayen idonta kafin ta ce"granny ki daina kuka,ba dai kin yarda da soyayyar da nakewa jikan ki ba?to insha Allah saina aureshi ya zama mijina,karki wani damu kanki"cewar Islam ta na sharewa granny hawaye.

"Wllh na yarda ƴata,kuma idan ya ce zai kawo wani shirme wllh sai in zage mu daku da shi in kakkarya masa ƙasusuwa in watsar da banza,inyaso daga baya a gyara shi"granny ta faɗa tana gwada yadda zata karya masa ƙashi.

"Wayyo granny idan kika karya shi kuma wazan aura "ta faɗa cikin shagwaba.

"Kuma haka ne,wllh zan ɗaga masa ƙafa ne kawai saboda ke yaron banza kawai"granny ta faɗa tana hararar hanyar dakin mommy.

"Lallai ma granny ya Aslam ɗin zaki kakkarya har ki watsar?
Idan ke baki karya shina shiya karya miki tsofaffin ƙasusuwa ki ya watsar" cewar hanan tana turo baki.

"Saidai ya karya na uwarki,kinji ko?ja'ira mai maka da takanɗa wllh ki bar ganin ina tausaya miki,duk randa na juyo kanki Allah ne kawai zai ƙwaceki"cewar granny tana hararar hanan.

"Yanzu dai granny ki gyale wannan shashahar ,kije ki kwanta ki huta,idan mun fita zan siyo miki tsaraba"cewar Islam cikin murmushi.
"Yawwa ɗiyata ki siyomin iyisikirim mai sanyin tsiya "granny ta faɗa tana nufar ɗakinta bayan ta ballawa jannat da hanan harara.
Murmushi Islam tayi tana zama akan kujera tare da ɗora kafa ɗaya kan ɗaya,kallon hanan tayi kafin tace
"Ki shiga taitayi ki hanan,manyan kima sunyi sun barni bare ke ƙaramar alhaki"

Shiru hanan tayi bata ce komai ba sai turo baki da tayi. Aman ne ya matso kusan da ita ya zauna shima jiki ba kwari,yace "islam me yasa kikayi wa yaya haka? Me yasa kikayi haka? Bakya tunanin akwai masoyan ki da dama dake jiran ki?Please ki janye wannan maganar Islam"Aman ya fada kamar zaiyi kuka "

Murmushi kawai Islam keyi tana kallon sa, saida ya kammala maganar sa kafin tace "nayi haka ne dan In nuna masa Islam tafi ƙarfin wulaƙancin sa,cewa yayi fa bazai aureni ba,harshi waye dazai ce baya sona ko yayi tunanin nima ina son shi ne? Zan aure shine kawai dan na koya masa hankali yasan Islam rainon dawa ce bata ɗaukar raini"ta faɗa tana wani girgiza ƙafa kamar boss.
Dafe kai Aman Yayi cikin damuwa yabar falon,hanan ma da jannat jiki sabule suka bar falon.ya rage saura Islam kadai .

Aslam kuwa bin mommy Yayi cikin ɗakin ta Yana kiran sunanta "Please mommy ki saurareni wllh yarinyar nan ba da gaske take ba,tana da wani ƙudiri ne akaina shiyasa,amma ba wani sona da take,mommy Dan Allah ki saurare ni"ya fada dai-dai lokacin sun iso dakin na mommy.
Cikin fada da daga murya mommy ta daka masa tsawa,
"Kai Aslam wllh ka kiyayeni!dan bana son shirmen banza,me kake son mai damu ne?ƙananan mutane ko me?to wllh tun wuri kama bar wannan maganar,tun kafin Daddyn ku yaji"ta kai karshen maganar cikin faɗa.
Shiru Aslam Yayi ganin yadda ran mommy ya ɓaci sosai,dan haka ya tausasa muryar sa yace "kiyi hakuri mommy,ba nufina in bata muku rai ba,kawai bana son ayi abinda zai zo ya zame mana matsala ne nan gaba,ko kuma ranku yazo yana ɓaci shiyasa,amma dan Allah kiyi hakuri"Aslam ya fada cikin ladabi.
"Ai yanzu ne kake son ran namu ya ɓaci Aslam,Dan me zaka rinka mai damu kamar wasu sa'anninka,ayi magana kuma daga baya kace ba haka ba"
"Mommy kiyi haƙuri please,kada ranki ya baci,yanzu ki faɗa min abinda kike son nayi"ya fada cikin ladabi da son kwantar mata da hankali.

"Kaje ka ɗauki Islam,ka kaita store ta zabo duk abinda ranta ke so,kuma bana son wannan halin da kake nuna mata,bana son takura Dan wllh inhar kace zaka ci gaba da ɓata ran yarinyar nan to zamu saba da kai"
"Kiyi hakuri mommy In Sha Allah zan kiyaye"Aslam ya fada cikin sanyin murya, tare da barin ɗakin, zuciyar sa kamar ana kunna

Please Login or Register in order to submit comment