Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, maƙagin rayuwata. Wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da aron numfashin da ya bani na rubuta wannan littafin na MATAN AREWA. Bayan kammala littafina na SALON ƘADDARATA. Ina roƙon Allah da ya tsare mini hannayena, wajen rubuta abinda zai zamu cutar ga al'ummar musulmai tare da tarbiyar su.


Oh my fans, i'm back no more waiting, ku shirya zama don ban zo da wasa ba, wannan karon salon na daban ne kamar yanda zubin labarin yake na daban kuma na mussamman, wanda suka karanta SALON ƘADDARATA da UWATACE SANADI shaidu ne akan hakan.


Page 0⃣1⃣

Hayaniyar daya karaɗe yalwataccen filin tsakar gidan mu, da carar da zakara ya tsala, su suka zamto ababen farkon da suka fara sallama a ƙofofin kunnuwana a wannan asubahin. Mirginawa nayi ina toshe kunnuwana da hayaniyar matan gidan mu, da ya zamto tamkar ibada idan har suka kuskurewa yin sa. To sai in ba lafiya, suka cika mini ƙofofin kunnuwana, Kafin na miƙe ina sakin wata miƙa na fito daga ɗakin.

"Tun daren jiya Salma, ta sanar dani ta ga shigowar Kubra cikin gidan nan, ina da tabbacin cewar a nan ta kwana. To menene abin ɓoyewa in ma sakin ta Habibun nan yayi ai banga abi......".

Furcin Umman su Salma kenan da suka yiwa kunnuwana dirar mikiya. Yayin da nake ƙarisowa inda suke tsaye cirko cirko, duk sanyin asubahin da ake busawa hakan bai dakatar dasu daga fitowa daga ɗakunan su ba. Bata ƙarisa zancen ba Umman su Anty Kubra tayi hanzari faɗin"Bakinki ya sari gumtun kashi, karyarki wallahi Hadiza dukkan mungun nufin ki akan ki zai juye ba akan ƴaƴana ba. In sha Allahu sai Mariya ta dawo cikin gidan nan tayi zawarci kafin Kubra tayi".

"Wannan kuma ƙarya ne, hatta bokan nakin yayi ƙadan wallahi, Mariya zama a gidan mijinta daram daram, yanzu ma aka fara".

Sai da suka gama ciwa junan su zarafi, sai a sa'ilin Ummata da take tsaye daga gefe ta soma baki"Haba Umman su Salma menene amfanin hakan a gaban ƴaƴanku, ku tsaya kuna ciwa junan ku zarafi. A kan maganar yaran da ba lalle bane ya zamto gaskiya".
Harara Umman su Kubra ta watso mata haɗi da faɗin"Malama waye ya saka dake balle ki ɗauki babban kashi?, ai bamu aike ki ba balle muga daɗewar ki, ko don saboda baki san ciwon ƴaƴa ba tunda ga zarkaɗeɗiyar budurwa kin garke ta a ɗaka har yanzu babu miji dole ki faɗi haka. Duk gidan nan an sawa ƴaƴana ido".

Dai dai lokacin da lasifikan masallacin dake kusa da gidan mu suka sallame sallan asubahi, Abban mu da su Baba ƙarami suka shigo cikin gidan a jere har suna karo da juna. Ganin su ya sanya kowa shiga taitayinsa.

A zafafe Baba yake faɗin"To Allah yayi safiya gari ya waye, an fara sana'ar karnukancin ko?, ana sallan asubahi amma ku kuna nan kuna tada wa mutane hayaniya. Wai shi ku kam yaushe za kuyi hankali ne?, ga ƴaƴa guɗai guɗai a gaban ku amma har yanzu baku san annabi ya faƙu ba, nasan duk wannan fitinar daga kece Zainabu".
Ya ƙarishe zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai, yana nuna Umman su Anty Kubra da ƴar manuniyar yatsarsa.

"A'a kar ka soma ɗaura mini laifi, daga shigowar ka baka ji ba'asin abinda yake faruwa ba kace laifina na".

Gyaran murya Abba yayi yana ɗaurawa da cewar"Menene yake faruwa?".
Cikin zafin rai Umman su Anty Kubra take faɗin"Kama Hadiza da ɗiyarta Salma nayi suna gulmar Kubra wai ta kwana a gida".
Na lura sai a sannan duk idanunsu suka sauƙa akan Anty Kubra, da take rakuɓe cikin ƙofar ɗakin su, Baba ƙarami yayi mata wani kallo yana cewar"Ke Kubra meye kawo ki gidan nan?".

"Baba ƙarami mun sama saɓani ne dashi Habibun, shine yace na taho gida".
Tsawa ya daka mata"ki tafi kai tsaye ki sanar dani abinda take faruwa kai tsaye, kafin nan kowa ya wuce yaje yayi salla".

Dukkan mu barin wajen muka yi, bayan an gama wurgawa juna harara da kallon uku kwata kowa taja zugar ƴaƴanta suka nufi ɗaka. Ummata da Anty Zakiyya muka shige ɗaki bayan mun ɗauro alwala muka yi sallan asubahi. Aikin daya kallafa a kaina na fito nayi na kowa ɗaki nayi kwanciyata. Na iske su Umma duk sun haɗo a falon Abba.

Gidan mu gidan gandu ne, daya haɗa dukkan ahalin mu waje guda tun daga kan kakanin mu har izuwa iyayen mu. Da kuma mu ƴaƴansu hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin matan gidan da kuma gasa a tsakanin mu ƴaƴan ahalin. Su biyar Abba suke a wajen iyayensu shine babba sai Baba sai kuma Baba ƙarami, ragowar biyun mata ne Goggo Suwaiba da Goggo Jummai da auran ta ya mutu ta dawo gidan da zama. Dukkanin su babu mai mata ƙasa da biyu Abba ne kawai mai mata biyu, Allah ya azurta ahalin da yalwan da ƴaƴa mata babban namiji Yaya Majid ne kawai sai kuma Nurain ɗan ɗakin su Anty Kubra, da bai wuce shekaru biyar da haihuwa ba. Mu uku ne a wajen Umman mu yaya Majid, Anty Zakiyya sai kuma ni, Daada kishiyar Umma ƴaƴanta uku Anty Maimuna, Anty Hasina da kuma Abasiya. Yayin da duk sauran ƴaƴan su Baba ƙarami da Baba ne.


Kawai gasa sosai a gidan mu da son ganin cewar kafi kowa. Al'ada ce a gidan mu duk wata ɗiya mace bata rufa shekaru goma sha biyar ake aurar da ita. Anty Zakiyya ce kawai ta kai shekaru goma sha tara ba a cikin ɗakin mijinta ba. Hakan ya zamto abin tsegumi da yafice a tsakanin mutan gidan mu. Abin nema ne ya samu wai matar ɗan doka ta haifi ɓarawo gori da shaguɓe babu irin wanda ba'a yiwa Umma da Anty Zakiyya ba.

Ina zaune a uwar ɗaka, ina biya karatuna Umma ta dawo daga zaman da suka yi tare da su Abba, da kallo na bita har ta zauna kusa dani tare da cewar"Na'ima ki tashi ki tafi islamiyya ga can su Abasiya sun shirya".
Zumburo baki nayi gaba kafin na kai ga furzo zancen cikina, ta ɗaga mini hannu alamar bata son jin komai daga gare ni, na miƙe na fice daga ɗakin a tsakar gidan nake jiyewa kunnuwana dalilin zuwar Anty Kubra gida. Wai sunyi faɗa da mijinta ne ta turo shi ta saman bene ya karairaine.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciyar da ta tokare mini ƙirjina na sauƙe, ina ƙara jinjina lamari a raina duk irin romon soyayyar da Anty Kubra suka kwankwaɗa da yaya Habibu, a lokacin bikin su har wani ji da kai Ummansu ta ƙaro tana ganin Allah yayi wa ɗiyarta ilhama zata auri mai hannu da shuni, mai gida da mota. Yanda suke soyayya abin zai ba wa kowa sha'awa amma yau ita ce da zuwan gida da sunan matsala.

Kwanon abincin da Umman su Salma ta dangwafa mini a gabana, na ɗauka na koma ɗaki kasancewar su Salman da muke ci tare yau kowa a ɗakinsu zata ci, nan na iske Anty Kubra zaune da Ummata gefe kuwa Anty Zakiyya ce tana naɗe kayan wankin da tayi. Gefe na samu nayi wa kaina mazauni ina kafe Anty Kubra da idanu da take maganar cikin zubda ƙwalla.

"Umma nasan kai kaɗai ce za ki gaya mini gaskiya a cikin gidan nan, wasu ma murnar dawowa gidan suke yi. Dan Allah abinda nayi shine dai dai ko kuwa na aikata kuskure?.Umman su Na'ima da nasan haka aure yake da banyi shi ba, akan gadona Habibu yake waya da wata yana faɗa mata wasu kalamai marasa daɗin ji da nauyi akan harshe wajen maimaitawa. Masu cike da batsa me na rage Habibu dashi da zai yi mini haka?".

Ta ƙare zancen tana kuma sakin wani kukan dake bayyanar da raunin dake cikin ƙalbinta, ina iya jiyo ɓoyayyiyar ajiyar zuciyar da Umma ta sauƙe kafin ta riƙo hannuwan Anty Kubra cikin nata ta riƙe sosai, kana ta soma cewar"Kubra shi aure ɗan haƙuri ne ko wacce kika ganta cikin ɗakinta, har ta kai wani matakin da take burge ki, take baki sha'awa to haƙiƙa haƙuri shine tsanin daya kawo ta wannan tudun. Kaso arba'in daga cikin MATAN AREWA su suke ɗaukewa kansu dukkan ɗawainiyar su dana ƴaƴan su, a gidan miji kama daga ci, sha da kuma sutura. Kaso ashirin na MATAN AREWA basa tarar da soyayya da kulawa a gidaden auren su, basa samun kulawa daga mazajen nasun saɓanin hakan ma sai dai a tarar da kishiyar hakan. Kiga aure shekara ɗaya wani baya ma rufa shekarar an rabu. Kaso talatin na MATAN AREWA basa samun biyan buƙata na auratayya daga wajen mazajen nasun wannan dalilin ya sa matan aure da yawa zama karuwai a cikin gidajen su, saboda rashin sauƙe haƙƙi daga mazajen nasun. Kubra kar kiyi mamakin cewar cikin kaso ɗari, kaso ashirin ne kaɗai suke samun kaso ashirin da biyar bisa ɗari na ababaɗen da na zayyananu miki su".

Sai da ta sauƙe ƙatuwar ajiyar numfashi kana ta ɗaura da faɗin"Cikin wannan lamarin akwai rashin kyautawa daga ɓangaren Habibun, amma kema akwai laifin ki Kubra komai ya faru bai kamata ki ɗauki wannan matakin ba".

Langwashe ƙafafuna waje guda nayi, sam na kasa kai koda loma ɗaya na abincin cikin bakina. Bana jin ko nayi yunƙurin hakan zai sama damar wucewa ta maƙoshina da nake jin yawun bakina ya ɗauke ƙaf. Tabbas MATAN AREWA na cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa cikin kalmomin da fatar bakin kan iya furtawa, idan har a auren soyayya a na samun irin wannan matsalar to ina ga auren dole?. Tambayar dana jefawa kaina kenan da na gaza cimma amsarsa, har izuwa lokacin da Anty Kubra ta katse mini hanzari ta hanyar faɗin.
"To yanzu Umman Na'ima ta yaya zan kaucewa wannan matsalolin, da yake ciwa ko wacce mace daga cikin MATAN AREWA tuwo a ƙwarya?".

Murmushin su irin na manya Umma tayi kana tace"Kubra wannan dalilin ya sanya aka ce shi aure bauta ne na ubangiji, kuma hanyar da mace kan iya samun aljannarta matuƙar tasan abunda take yi. Duk wani abu mai muhimmanci ba'a samun sa cikin sauƙi, Allah ya ɗaga darajarki ta hanyar baki mijin aure yau ga Zakiyya nan babu wanda ya taɓa tsayawa a ƙofar gidan nan, da zummar zuwa wajenta, ki nitsu kiyi tinani har ki gano matsalar ki, ki gyara domin ta hakan ne kawai za ki ƙara ɓarnan da kika yi".
Izuwa yanzu sosai hawaye suke gudu a fuskar Anty Kubra, ta buɗe baki da zummar faɗin zancen da ta maƙale a maƙoshinta. Ummansu ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo tamkar an cillo ta. Sai da ta ƙare mana tanadin kallo tsaf kafin ta wurgawa Anty Kubra dake durƙushe kusa da Ummata harara tana ɗaura da cewar"Ke kuma meye kike yi a nan?, zan yi miki kashedin ƙarshe kar ki kuskura dai dai da rana ɗaya. Kiyi gangancin tunkaran ɗaya daga cikin matan gidan nan da matsalar ki domin dangin yanzu basa rufe kattara don haka tashi ki wuce mu tafi".

"Haba Zainabu ai ni da su Kubra da Na'ima ɗaya na ɗauke su, babu wani bambamci a tsakanin su".

Tsaki mai dogon zango ta saka, tare da finciko hannun Anty Kubra da bata da niyyar tashi. Suka fice daga cikin ɗakin da hakan yayi dai dai da bugawan da ƙirjina yayi da matuƙar sautin ɗas ɗas ɗas.
Na kallo Umma nace"Umma wannan haƙurin tun kafin auren Anty Kubra ake faɗa cewar shi zata yi a gidan aurenta, in an kai ta. Shi rayuwar mace duk akan hakan yake kenan?".
Anty Zakiyya ce ta tanka mini a wannan karon, da tun ɗazu bata ce uffan ba"Na'ima bana son wannan yawan zancen nakin, ki tashi ku wuce islamiyyarki". Ta faɗa tana yin kicikici da fuska. Umma ta ɗan dara kafin tace"Barta Zakiyya ai tambayar abinda zai amfane tayi, ita ma kwana nawa ne idan Allah ya fito mata da miji za ayi nata, kinga kuwa don ta tambaya ba zamto laifi ba".

Tunin naji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniya, na tsani wannan furcin. Idan aka yi mini ita gusar mini da dukkan annurina take yi, ban sani ba ko don na taso ina ganin yanda sauran ƴaƴan gidan mu suke zuwa da matsalolin gidajen auren su babu ƙauƙautawa, hakan ya sanya aure ficewa daga raina oho.
Ƙananun maganar da Daada Umman su Abasiya ta fara wai na shirge a ɗaki nayi zamana, har suna neman yin latti ya sanya ni tashi na ture kwanon tuwon dake gabana na zara hijabina tare da ɗaukar al-ƙur'anina nayi wa Umma da Anty Zakiyya sallama na fito. Abasiya, Salma da Bilkisu da duk suke sa'anni na tarar duk sun gama shirin su.
Na iske Goggo Jummai suna ta mayarwa juna martani, da Umman su Salma wai akan ta zuba mata abincin karin bai ishe ta ba, tayi magana kuma ta gaya mata baƙar magana wai tunda ba gidan mijinta bane bata da wannan ikon duk abinda aka dafa aka bata kawai ta karɓa taci.

Sai da muka biya sashin Hajiya Babba kakarmu muka gaishe ta sannan muka fice izuwa islamiyyar safe da muke zuwa, idan nace na gane abu guda ɗaya takamanme cikin abubuwan da aka koyar damu haƙiƙa nayi ƙarya, na kuma faɗi son raina ne kawai. Domin tunda muka je har aka tashe mu ban fahimce komai ba, hankalina duk yana ga tinanin dana dasawa raina na matsalar Anty Kubra.

Taɓo kafaɗata da Salma tayi, ya sanya ni dawowa daga tunanin dana fara nisan kiwo a cikinsa. Na wurga mata wata uwar harara nace"Menene?".
Cikin gatse da son maido mini da magana tace"Uwar meye kuwa, kawai munga muna ta zancen bikin mu ne ke kinyi shuru kinsa fa su Abba sunce tare za'a haɗa mu, ke har yanzu ko tsayayye baki dashi, ga Malaman Yusuf na ajin ku duk ya nuna miki alamar so amma kin tsaya masa wani jan aji".
Tsaki Bilkisu tayi cikin taɓe baki take cewar"Ƙyale ta bari ajin ya tsinke muga yanda zata yi". Hararar nima na maida musu dashi kafin nace"Kwaji dashi don ni nan tinanin yanda zan tunkari su Abba, da batun bokon da nake son......".

Tun kafin na ƙarisa naga duk sun tintsire da dariya har da riƙe ciki da tafawa, ƙololuwar gejin ɓacin rai suka kai ni a zafafe nace"meye hakan ku kuma, kuna tafe kuna wannan dariyar kamar sabbin shiga hauka?".

Sai da suka tsaigata Abasiya tace"Ince kanki ɗaya ko Na'ima?, yanzu ke don baki da hankali da rashin kunya sai ki tunkari su Abba da zancen kina son kiyi boko, tab lalle kam".

"Kyale ta banda tsaurin ido irin nata, shi kuma auren jingine shi zata yi a gefe kenan ko meye oho mata".

Ɗauke kai nayi daga dukkan abunda suke faɗa, don yardan su Abba kawai nake buƙata. Duk cikin maganganun nasun babu wanda ya sosa mini rai kamar na Salma da take faɗin.

"To banda abin ki Bilkisu meye don tace boko zata yi, ba za tayi aure ba tunda ga nan Anty Zakiyya ma har yau babu aure ai don ita Na'ima tace baza tayi ba. Ba abin mamaki bane tunda abin daga na sama yake farawa yana bin ƙasa, har wanda suka biyo bayansa su ƙwaiƙwaya".

Sosai idanuna suka rufe bana da haƙuri ko kaɗan, domin bana barin ta kwana da an taɓo ni nake mayar da martani babu ɓata lokaci. Cikumo wuyar hijabin Salma nayi ina bin ta da ƴatsa domin bakina ya gaza furta mata koda kalma ɗaya ce. Da ƙyar Bilkisu da Abasiya suka ɓanɓare hannuwana daga cikumar da nayi mata, ina sakin ta ta fara tari babu ƙauƙautawa, kallo ɗaɗɗaya nayi musu na ɗauki hanyar gida ba tare dana kuma waiwayar su ba, balle jiran su mu koma tare kamar yanda muka saba.

Matar Baba ƙarami ta biyu, Umma su Anty Hajara da mu ke yiwa laƙabi da Hajiya kasancewar ance kafin aurensu, da Baba ƙarami tayi zaman saudiyya. Na iske a tsakar gidan tana wanki gefe guda kuwa Anty Jummai ce zaune ta miƙe ƙafafu ƙofar ɗakinta tana curin kalwarta, tana rero waƙar a kama sana'a mata, a kama sana'a mata cikin ɗaga murya.
Ciki ciki nayi sallamar da ba lalle kunnuwansu su iya jiye musu ba, tare da yi musu sannu da gida na yi wucewa ta cikin ɗakin Ummata.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________

Page 0⃣2⃣

Ban iske Umma a ɗakin ba, illa Anty Zakiyya tana tilawar karatunta, ko da kanta banbi ba na faɗa kan katifarmu nayi kwanciya. Duk tambayar da take jera mini akan lafiya ban amsa mata ko ɗaya ba, hakan nan hakan bai sanya ta ta daina ba.
Shigowar Yaya Majid yana tambayar ta meye ya faru, tace bata sani ba ya sanya shi daka mini wani gigitacciyar tsawan da ta haifar mini da kaɗawan ƴaƴan hanjin cikina. Babu shiri na tashi zauna.

"Menene yake faruwa ana miki magana kinyi wa mutane banza?".
Cuno baki gaba nayi kafin nace"Su Bilkisu ne suka ɓata mini can ma na baro su a hanya?".

"Meye haɗa ku dasu?".

Ya kuma tambaya cikin tsare gida, na amsa da cewar"cewa suka yi wai babu wanda ya taɓa cewa yana son Anty Zakiyya gashi yanzu har ana shirin bikin su".
Ajiye alƙur'anin hannunta da yake neman suɓɓulewa gefe guda Anty Zakiyya tayi tana tallafo kuncinta da hannayenta kafin ta kai ga sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi da ya tokare mata maƙoshi. Kallo ɗaya nayi mata na kawar da idanuna gefe guda, tunin kifiyar tausayin yanda ƙaddararta tazo ta harbi raina, dare jiya duk rabin daren sallan dare take yi,a bayyana take addu'ar in akwai rabon yin aure a rayuwarta kafin ta koma ga mahaliccinta, Allah ya fito mata da miji na gari.
Tsabar haushin daya zarge raina ko tashi banyi ba balle na taushi zuciyarta, don gani nake yi da nata laifin da ta ɗaurawa kanta zamarin kokuwa da ƙaddara, Allah ya sanya jumma'arta da nisa amma duk tabi ta ɗaurawa kanta damuwa akan zantukan da mutane suke yi, a shekarunta goma sha taran da take cikinsa.

Muryar yaya Majid da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya suka dawo dani daga nisan kiwon da na fara yi, a zancen da nake yi da zuciyata.

"Zakiyya kukan meye kike yi?, sai kace yau kika fara jin waɗannan maganganun, kamar yanda ni da Umma muka sha faɗa miki shi aur nufi ne na Allah kuma abinda ya hana ki mutuwa ki ya hana ki aure wato LOKACI, matuƙar kina cikin bayin da Allah ya tsara akwai aure a cikin rayuwarsu na duniya babu shakka sai kinyi Zakiyya".
Bata ce dashi komai illa sausauta kukan natan da tayi, shuru ya baƙunci na tsawon daƙiƙun da basu gaza huɗu ba, kafin Anty Zakiyya ta kawar da shurun ta hanyar cewar"Yaya Majid ko ba yau kunnuwana suka basa jiyo min irin wannan zantukan ba, amma wallahi ban taɓa jin ciwo a raina irin na yau ba. Wai ace Bilkisu sa'ar ƙanwar bayata ce zata faɗi hakan a kaina?. Yaya Majid ni kuma ƙaddara kenan haka Allah ya tsara min, yanzu ko tsakar gidan nan ban isa na fita ba sai a goranta min yaya suke zo nayi da raina?".

Ta ƙare zancen tana saka hannuwa tana tare ƙwallar da suka ciko mata kurmin idaniya a ƙoƙarin hana su kwaranya. Sosai yaya Majid yake fuskanto sai da ya tausasa muryarsa kafin ya shiga faɗin"Zakiyya ki sawa ranki dangana da haƙuri akan komai kinji?".
Kanta ta ɗaga masa, da hakan ya bashi damar miƙewa idanunsa a kanta yace"ni zan fita ki sanar da Umma in ta shigo".

"To a dawo Allah".

"Allah yasa".

"Amin".

Sai dana ga ya kai ƙofar ficewa nima na raka shi da addu'ar a dawo lafiya, ya amsa mini kamar yanda ya amsawa Anty Zakiyya. Ina jiyo sababin da Daada take surfawa a tsakar gida da bansan da wanda take yi ba, sai dana ƙare kwanciyana kana na fito nayi aikin da yake kallafe a kanmu na wanke wanke da shara.
Salma na iske har taja nata ta fara wankewa, don haka nima na ɗibo na fara nawa babu wanda ya tanka wani har muka gama. Na ware na sashin Hajiya Babba na kai mata, babu kowa a filin sashin natan sai takalman su Abba da Baba dana hango yashe a ƙofar ɗakin natan, kaina tsaye nayi wuce ta izuwa ga ɗakin girkin na ajiye kwanukan, kana na ɗauki tsintsiya na fara share filin.


"Tunda yarinyar nan tayi nadama ni ina ganin, kawai mu jira izuwa lokacin da Allah zai ba wa Habibun lafiya zai ayi wa tufkan nan hanci".

Zantukan Baba ƙarami da suka sauƙa a kunnuwa tamkar don naji yayi su, kafin Baba ya karɓe zance a zafafe yake faɗin"Muhammadu babu alamar nadama a tattare da yarinyar nan, don haka da zaran ya sama lafiya da kaina zan sanya shi ya sauwaƙe mata tazo gida ta zauna tunda hakan ta zaɓarwa kanta, ai shi aure ɗan haƙuri ne da kuma kai zuciya nisa ba komai bane ake hawa dokim zuciya".

Kagagin kukan da Anty Kubra ta saka, cikin dushashewar murya tare da fizgo numfashinta take cewar"Baba dan Allah kuyi haƙuri wallahi ina son Habibu ina son aurena, don Allah kar ku raba ni dashi mutuwa zany.....".

Bansan meya hana ta ƙarishe ragowar zantukan da ta ɗauko baa naji tayi shuru, sautin kukan da take yi ya yawaita. Tagwayen ajiyan ajiyan zuciya na sauƙe tausayinta duk ya maƙale a raina, ina ƙara tabbatar da sahihancin wannan

Please Login or Register in order to submit comment