Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka ake yi zuwan saurayi na farko wajen budurwa?. Na jefawa kaina tambayar da na gaza cimma amsarta har muka isa cikin zaure.

Ya dakata daga nan, yayin da ni kuma na isa ɗakin yaya Majid na zayyana masa komai da sauri ya fito suka gaisa ta hanyar yin musabaha. Na wuce ciki saboda yayi masa iso wajen su Abba.

Tun kafin na kai ga shiga ɗakin mu, naka duk matan gidan suna bina da kallo da alama magana ta suke yi shigowa ta ya sanya tsahirtawa.

Su Salma na iske zaune a ɗakin, ina sanyo ƙafata suka tuntsire da wata ƙarƙarfan dariya mai sautin gasken, kallon ɗaɗɗaya nayi musu kafin nace"ince dai lafiyarku ko?".

Da ƙyar Balkisu ta tsayar da dariyar ta take yi, har da riƙe ciki tace"Sai yanzu?".

"Bangane sai yanzu ba?".

Na tari numfashinta, Abasiya ta ɗaura da"Masoya kenan sai yanzu soyayyar ta ƙare, gaskiya zan so gani idon Malam Yusuf sanda yake furta miki kalmar so".

Ƙara bushewa suka yi da wata dariya, ciki ciki nayi tsaki kamin na zauna bisa katifar mu nace"Kyaji dashi kenan, abinda ya dame ki kenan nikam dai bashi bane a gabana, don da na sama goyan baya ma wallahi makaranta zan koma don ni ba wani son shi nake yi ba".

"Kut, lalle Na'ima amma dai kinsa malam Yusuf ba tsararki bane ko?, wallahi ya fiki kyau da kuma aji ga haɗuwa da kuma sanin kimar kansa don ba kowacce yake kulawa ba, ai ke kece kika sinci dami a akala".

Furcin Balkisu kenan, Salma tayi caraf ta karɓe zancen"A to gaya mata dai tana wani jan ajin banza, banda sharrin soyayya ma ina ke ina malam Yusuf".

Wata dariyar suka ƙara saka, har na buɗe baki da zumma mayar musu da amsa yaya Majid ya ɗago labulen ɗakin haɗi da cewar"Kizo sun gama zai wuce".


Yana ƙare faɗin hakan ya juya, a tare su Salma duk suka zari hijabansu wai zasu je gaisuwa, takaici haka nan suka ɗura mini na bisu a baya, don dole don wallahi naso yin zamana na ƙi fitowa muyi sallaman sai naga rashin dacewar hakan.

Suturu suke ta zuba mishi, da mamakina naga yana biye musu abinda sam ko cikin wasa da raha baya yi a islamiyya kenan. Abasiya har da faɗin wai yanzu ta zama Antinsa tunda yana son ƙanwarta.

Ganin isowa ta ya sanya su yi masa sallama suka koma cikin gidan. Kaina a duƙe ya soma cewar"Naga su Abba kuma sunyi min tambayoyi na amsa, ki taya ni addu'a Allah ya sa na cinye wannan jarabawar".

"In sha Allah zaka kaye ta".

"Allah ya sanya".

"Amin".

Nace ina gyara tsayiwata kamin ya ce dani zai wuce sai kuma wani lokacin, fatan sauƙa lafiya nayi masa kana muka yi sallama yace ba fara shiga gida tukunna.

Hakan kuwa aka yi sai da na shiga kana ya ja mashin ɗinsa ya tafi, haka nan na since kaina cikin matsananciyar faɗuwar gaba da tararradi, ganin na gaza samun nutsuwar ruhin ya sanya ni nufa ɗakin yaya Majid yana tsaye yana ɓalle maɓalle rigarsa zai fita masallaci saboda magrib da ta gabato na iske shi.

"Har ya tafi kenan?".

Kaina na ɗaga masa alamar e, ya kuma cewar"To ya na ganki kamar ba lafiya?".
Sai da na sauƙe numfashi ba tare da na shirya ba wasu hawaye suka ɓalle mini suka fara gudu akan dandamalin fuskana, a tare da na yi wani yunƙurin hana hakan ba.

Kalmar subhanallahi, subhanallahi, subhanallahi kawai yake ta faman maimaitawa cikin bakinsa. Kafin ya ƙariso gab da nayi yana faɗin"Ke Na'ima lafiya kuwa?".

Kaina na ɗaga masa nace"yaya Majid yanzu shikenan inda su Abba su gama gudanar da bincike a kan malam Yusuf, har ya turo iyayensa shikenan duk burin da nake dashi akan karatu ya bi iska kenan?".

Ina iya jiyo ɓoyayyar ajiyar zuciya mai ƙarfi da ya sauƙe"Na'ima ai shi aure baya hana karatu, kamar yanda nasha faɗa miki matuƙar kina da buri akan karatu babu makawa sao kinyi shi don haka ki kwantar da hankalinki kinji ƙanwata, yanzu zan fita masallaci inna dawp sai mu gama maganan".

Tare muka fito dashi, yana ƙara kwantar mini da hankali da kuma ƙara mini ƙarfin gwiwa.

Masallacin ya wuce, ni kuwa na shiga ciki sai da nayi alwala na shiga ɗaki n mu nayi salla, na daɗe akan sallayan ina addu'ar Allah yayi mini zaɓi mafi zamowa alkhairi a gare ni dama rayuwata gabaɗaya.
Ko da na fito Anty Zakiyya na iske tana kaɗa miyar bushashshan kuɓewa, na zauna gefen ta ina yi mata sannu da aiki, ta amsa mini fuskar nan a sake.

Nan nake tambayar ina Umma don tun kafin zuwan Malam Yusuf, da naje ɗakinta sanar da ita Hajiya Babba nason ganinta, ban ƙara ganin idonta ba. Nan take sanar dani cewar Maman Walida tazo sun fita tare, kaina na jinjina lamarin Maman Walida ya riƙe mini rai.
Sai da ta gama kaɗa miyar, ta raba abincin ko wani ɗaki aka sanya na matar ɗakin, kana na fara kai wa.
Muka ci namu tare da su Salma, sai bayan sallan isha'i Umma ta dawo sai da na bari ta huta kana naje na sanar da ita duk yanda muka yi da Malam Yusuf, Anty Zakiyya da take zaune tana sauraron mu ta taso ta rungume ni ta baya, har da ƙwallar farin ciki take yi mini, tana mini addu'o'in sanya alkhairi. Sosai naji zuciyata ta ƙaraya naso sai anyi nata bikin, kafin za ayi nawa amma ga yanda Allah ya tsara komai cikin mu babu mai ikon canja ƙaddara.


Na lura Umma ma dauriya kawai take yi, take lallashin mu amma ita ma zuciyarta soya take yi mata, sai da safe nayi wa Umma na zarce ɗakin mu. Ban bi ta kan su Abasiya ba da suke kitsawa Salma zance akan maganar nan da muka fara jiya na Abdallah.

Kwanciyana nayi sai dai sam bacci ya ƙaure ce mini, har aka yi ƙiran assalatun farkon ƙar a kunnuwana.
Safiyar duk mutanen unguwar mu muka wayi gari cikin matsanacin tashin hankali, da ruɗewa. Wata amarya aka kawo jiya da wayewar garin yau aka tarar da gawarta ta ƙone kanta, bayan fitar mijin izuwa sallan asuhabi, a yanda jifa jifa ya fara bazuwa a cikin unguwa wai auren dole aka yi mata ba tare da son ranta ba.

Ranar Umma da wasu mata biyu da suke aiki irin nata, da kansa mai unguwar unguwarmu ya sanya aka tara musu iyaye maza suka wayar musu da kai akan illolin auren dole ga ɗiya mace, mace halitta ce rauni da zuciyarta bata iya ɗaukan zama inuwa ɗaya da wanda ya kasance ba zaɓin ranta ba.
Har sai da aka ƙwala ƙiran zuhr kana suka tashi daga taron, har yamma muna cikin jimami kowa jikinsa yayi laƙwas tamkar waɗanda aka yiwa dukan tsiya, da yammacin ranar Anty Kubra ta koma ɗakin mijinta bayan dogon nasiha da jan kunnen da su Abba suka yi mata haka nan ma Umma tayi mata da ta shigo yi mata sallama. Haka nan ta koma ta cigaba da jinyar mijinta. Bayan sallan magrib yaya Majid yake shaida mini xuwan Malam Yusuf..

Dogom hijabi na saka, na fita na iske su tare da yaya Majid ganin fitowa ya sanyi shi yi masa wani maganar da ban iya tantance abinda ya faɗa ba, ya bar wajen sallama nayi masa ya amsa. Kafin muka shiga jajantawa junan mu abinda ya faru, duk jikina ya ƙara yin laƙwas.

Lura da yanayin da na faɗa yace"Zuwana yanzu munyi da su Abba sunce zuwa jibi idan suka kammala bincike a kaina, zasu bani damar gabatar da iyayena".

Kaina na jinjina nace"ina fatan ba'a zaurara maka ba?".

"Ko kusa in sha Allah zanyi iya ƙoƙarina, ganin na samar da komai akwai ginin da muka yi tare da yayana. Wanda yanzu haka shi yana da mata lefe da sadaki ne kawai ya tare min wanda shima akwai adashin da nake yi da na ɗauka zanyi komai".

Sosai na jinjinawa ƙoƙarinsa haka muka cigaba da tattaunawa, muka kuma ƙara fahimtar junan mu, dawowar su Abba daga masallaci ya sanya ni dawowa cikin gida, na barsu tsaye da Malam Yusuf.
Kamar yanda su Abba suka gudanar da bincike akan Malam Yusuf, ba'a same shi da wani mummunan ɗabi'a ba haka nan ya sama kyakykyawan shaida daga jama'a, sana'ar koyarwa yake yi, a mabambamtar makarantu har uku, islamiyyar mu ta safe, da na yara na yamma sai kuma makarantar primary da yake koyar da yara.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

______________________________________

Page 1⃣0⃣


Tunin shirye shiryen sauƙar mu ya kamo hanya gadangadan, kowacce daga cikin mu saurayinta yayi bajinta wajen bata wasu kuɗaɗen domin hidimar sauƙar tamu. Don zamu yi ankon atamfa da kuma hijabi ga kuɗin da muke tarawa a wajen Malam Yusuf kullum ɗari biyu.

Duk dani ya ɗauke mini hakan, a matsayin nashin gudumawar na sauƙar kasancewar bai yi mini irin yanda samarin su Salma suka yi musu ba, ta hanyar basu kuɗi kasancewar shi ɗin abun yazo masa a gaggauce duk da kuwa yace mini daman a shirye yake, amma yana buƙatar wasu kuɗaɗen.

Gashi maraya ne, shine auta a wajen iyayensu hakan ya sanya sauran ƴaƴinsa uku yi masa kara suka haɗa masa lefe tsaf.
Ana saura kwana goma sauƙar mu, aka kawo lefen Balkisu ranar munsha kallo don har da maƙwabta. Firirita wajen Ummansu kuwa ba'a kwatancen sa, don tunda ake aurar da ƴaƴa a gidan mu ba'a taɓa kiwa wata koda kwatankwacin irin lefen Balkisu ba.

Ban sani ba ko hakan ne, ya turnuƙe ƙalbin Abasiya oho. Don wunin ranar gabaɗaya ƙarar dashi tayi cikin ƙunci. Bata kwana a ɗakin mu ba tace a ɗakin Ummansu zata kwan, cikin mu babu wanda ya damu da hakan.
Kwana biyu tsakani aka kawo na Salma, babu laifi Abdallah yayi ƙoƙari da bajinta sosai, kasancewar ba ma'aikacin gwamnati ba kamar Aminun saurayin Balkisu. Hasalima shi direban babban mota ne. Sagirun Abasiya kuwa ɗan kasuwa ne.

Yaya Majid ne yayi mini ankon atamfar, yayin da Malam Yusuf yayi ƙudurin yi mini ankon hijabin Ummata ta gargarɗe ni akan har na ɗaura masa nauyi, musamman da yanzu aski yazo gaban goshi.

Zaune muke a ɗakin mu, Abasiya tana aikin rubutawa Sagiru saƙon, akan kuɗin gyaran jiki da har yanzu bai kawo ba, a cewarsa wai sai wasu kayan da yake tsammata zuwan su, sun iso zai bata.

A nutse Salma ta kallo ta kafin ta shiga faɗin"Haba Abasiya ke kuwa kiyi haƙuri mana, tunda yace zai ba ki ai zai bayar, kiyi wa Ummanku magana ko aro ne sai a nema a fara abinda ya kamata in ba yabar sai a biya".
Kamar jira take yi Abasiya, ta kuwa shiga furzo da zantukan dake cikinta"Ai dole kice na ara saboda ke Abdallah bai yi miki wasa da hankali ba, ya cake miki kuɗin gyaran jikinki tsaf a hannunki ai dole kice dani haka".
Sai da tsirgar da wata tsaki, mai dogom zango kana ta ɗaura da faɗin"Ni wallahi da su Abba ma zasu saurara ni, da nace dasu na fasa auran Sagir sam ya fiye mammaƙo. Da Allah zai fito min da wani hamshaƙin wallahi da tunin na mance da wani mai kama da Sagir".

Duk kallo duka tsura mata, cike da mamaki har ta kammale zancen natan. Bamu gama dawowa hayyacin mu daga shayar da mu ruwan mamakin da ta yi ba, zantukan da ta ɗaura dasu suka bugin kunnuwan mu.

"Wallahi duk ya fita raina, sai yanzu ma nake hango zallar wautan da nayi. Da na zaɓi Sagir a matsayin wanda zai zama mijina mtscheew".

"Ke Abasiya ince notonan kanki basu sunce ba ko?, Sagiru ne fa kika faɗin wannan maganar akan sa, duk soyayyar da kuka yi kin manta kenan?".

Furcin Balkisu kenan da ya sanya Abasiya ƙara tunzura ta hayayyaƙo kamar zata cinye Balkisu ɗanya"Sagirun to ubana ns shi ɗin?, da bazan iya gudanar da rayuwa babu shi ba, ko shi ɗin numfashina ne da za ki ce ba zamu raba gari dashi ba?".

Tana ƙara zancen ta miƙe ta fice cikin matuƙar ɓacin rai, da kallo duk muka raka ta ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfi da ya sanya ni runtse idanuna. Ina mamakin meya shigarwa Abasiya kunyar kanta da take wannan furcin, ta manta yanda Sagiru yake ɗawainiya da ita, bata shakkar tunkarar sa da duk wani buƙatar kuɗi idan ta taso mata, kwanakin baya sai da Abba yayi mata zazzafan kashedin har ta ƙara shigo masa gida da duk wani abunda ya fito daga hannun Sagiru in dai bashi yayi niyya ya bata ba.

"Allah ya kyauta".

Iya abin dana furta kenan, kafin muka jiyo sowan ƙananan ƴaƴan gidan suna yiwa Goggo Suwaiba.
Zumbur muka miƙe har muna rige rigen fitowa, tana zaune akan tabarma duk matan gida suna daga gefe ƴaƴa kuwa sun mamaye ta, don nisa ba kusa ba tafi Goggo Jummai sakin fuska da jan mu a jikinta, uwa uba ga kyauta kamar bata san ciwon nema ba.


Kamar yanda kowa yake zaune kusan ta, muma hakan muka yi kafin muka fara gaishe ta. Tana amsa mana cikin sakin fuska.

"Kaga Amaran nan da kwana goma".

Duk sunkuyar da kai muka yi cike da kunyar zancen natan, da hakan ya sanya ta sakin taƙaitaccen murmushi kana tace"nazo muku da wani sirrin gyaran jiki da idan kuka riƙe shi in sha Allah kun mallake mazajen ku, babu bin boko balle malaman tsubbun da za suta cin kuɗaɗenku a banzan, ga kuma kaucewa daga gwadaben Allah".

Wayyo Allah ai ji muka yi, kamar ƙasa ya buɗe duk mu shige tsabar kunyar da tayi mana sarƙa.

"Goggon yara kenan, da kin haɗowa Zakiyya ma nata haɗi ko Allah zai yanke mata wannan zaman gidan haka".

Furcin Hajiya kenan da ya sanya ni, taune leɓɓana kamar da ni tayi zancen take naji raina yana mini soya ainun.

Ɗan murmusawa Goggo Suwaiba tayi"Me kike ci na baka na zuba?, ai ita ma lokacinta ne bai yi da zarar yayi babu abinda zai hana ta yi".
Zuwa yamma kamar kullum duk muna sashin Hajiya Babba, kamar yanda hakan ya zamto wata al'ada na ahalin mu, duk sanda aka tashi auren da ƴaƴa mata Hajiya Babba ita take ɗaukar nauyin yi musu gyaran jiki da wasu gyare gyaren. Kasancewar ta kanuri gaba da baya.
Zuwan Goggo Suwaiba sai abun ya ƙara armashi, don sosai ake mana duk wani gyaran da ya kamata, wanda bai wuce zarafi da cutar da lafiya ba.
Duk muna zaune, yaya Majid ya bogo sallama zai shigo Goggo Suwaiba ta dakatar dashi.
"Malam dakata mana, ai ba'a shigowa kai tsaye menene?".

Sai da ya dara kamin yace"To Malam Yusuf da Abdallah ne a waje suna son kallon amaran su".

"Yau naga ƴaƴan zamani kaje kace musu, ba zasu sama damar gannin su ba suyi haƙuri".

Furcin Hajiya Babba kenan, sai faman sababi take yi tsabar nacin tsiya ba zasu bari a gyara musu matam tsaf ba, zasu zo su tsaye mata a ka. Duk muna zaune, yaya Majid ya bogo sallama zai shigo Goggo Suwaiba ta dakatar dashi.
"Malam dakata mana, ai ba'a shigowa kai tsaye menene?".

Sai da ya dara kamin yace"To Malam Yusuf da Abdallah ne a waje suna son kallon amaran su".

"Yau naga ƴaƴan zamani kaje kace musu, ba zasu sama damar gannin su ba suyi haƙuri".
Furcin Hajiya Babba kenan, sai faman sababi take yi tsabar nacin tsiya ba zasu bari a gyara musu matam tsaf ba, zasu zo su tsaye mata a ka. Duk murmusawa tayi, muka yi muna jiyo Goggo Suwaiba da take ba wa Yaya Majid saƙon yaje ya sanar dasu bayan magrib su dawo.
Sosai muka tsummu, ƙiran sallan magrib da aka fara yi, ya samu miƙewa muka fice izuwa ɗakin mu, alwala nayi. Nayi salla sannan na fito ɗakin Ummata tunda bikin ya rage saura sati biyu take yi mini nasiha haka nan ma yau ita ce ta ƙara yi mini, da ya haifar mini da tsiyayar da ƙwallar idaniya.


Na faɗa jikinta ina rero kukana tare da faɗin"Umma wallahi tunda aka sanya rana na da Malam Yusuf, na gaza samun nutsuwa naso sai an fara auran Anty Zakiyya kafin nawa. Amma haka Allah ya tsara zuciyata tafasa take yi inda na tina cewar na kusa tafiya na barta, da zantukan mutan gidan nan da basu san ƙaddara ba balle suyi wa wanda ya faɗa kansa uzuri".

Bubbuga bayan ta soma yi cikin sigar lallashi, a haka har bacci ya ɗauke ni, Koda Malam Yusuf yazo sashin Hajiya Babba na kai shi suka gaisa har da su Goggo Suwaiba, ɗaya bayan ɗaya matan gidan mu suka fara zuwa suna gaisawa kafin aka koma ga kan ƴaƴansu.
Daga nan sashin su Abba muka garzaya, ya gaisar da su Abba. Umma kam fir tai yarda su haɗu, Anty Zakiyya kam sosai suka gaisa har faɗin wai ta damƙa masa amanata in yaci shi da mahaliccinsa.

Rakiya nayi masa, ya ɗauki dubu biyar ya bani wai nayi hidimar walimar sauƙar mu, na nuna masa ya barshi kawai shi da yake da hidimar biki a gabansa. Yanda naga yayi kicikici da fuska ya tilasta mini amsar kuɗin.
Koda na koma gida, na iske an kafa dandalin yi dani. Wai yafi ni kyau da aji nisa ba kusa ba, ban tanka musu ba nayi wucewa ɗaki ina jiyo zancen da su Daada suke yi, akan jinkirin rashin kawo lefena da ba'ayi ba, kuma yace a shirye yake amma har yanzu shuru.

Wasa wasa walimar mu, ta ƙarato. Duk munyi ankom atamfar da hijabi mun wanke kawunan mu, lalle ne dai kam Goggo Suwaiba tace kar muyi don ba zai fita ba nan da sati ɗaya, har muyi na biki.

Ranar sauƙar Abba, Baba, Baba ƙarami suka kawo shinkafa kwano biyar aka dafa, matan gidan mu da suke je suka taho dashi. Sosai walimar namun ta sama halaltar manyan baƙi, ciki kuwa har da mai martaba sarki da wasu jigajiga a gwammatin garin mu. Ni nayi ta ɗaya, Balkisu na biyu sannan Salma. Abasiya kuwa tana cikin jerin mutane biyar da aka ba wa kyautar alqur'ani izu talatin, bayan na sauƙa da aka basu.
Munsha kyaututtuka daga baƙi, su Salma ma duk samarin su sun zo, lattin zuwan da Sagir yayi kuwa Abasiya har da kukanta muka ta yi mata tsiyar ashe duk zancenta ƙarya ne na ciki na ciki.

Haka taro ya watse, muka rabo cike da kewar yan ajin mu da duk suka yi mana alƙawari zuwa bikin mu, da yake sati mai zuwa in sha Allah.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

______________________________________

Page 1⃣1⃣


Daren ranar duk wanda ya gan mu, sai yayi sha'awar mu domin an ture komai a gefe. Kowa sai yi mana fatan alkhairi yake yi babu babba babu yaro, sauran yayan mu mata da suke gidan mazajensu na nisa har sun fara isowa Anty Hajara da Anty Maimuna, sai kuma Anty Hassana su kam tun yau suka iso.

Ragowar ma duk sun halalci walimar tamun, amma sun koma gidan su, sai ana saura kwana huɗu ɗaurin aure zasu zo.

Daren ranar Malam Yusuf yazo, munyi hira sosai dashi har ya ƙira yayarsa a waya muka gaisa da ita. Don ya shaida mini cewar bashi da ƙanwa mace, su huɗu ne a wajen iyayensu da duk sun rasu yanzu.

Babbar su macece, sai wansa da zamu zauna gida ɗaya da matarsa yaya Auwal sai shi sannan autan su Mahmud.
Kayan kataho kama daga kan gado da kujeru, duk Abba da Baba ƙarami ne suka yayi mana dai dai ƙarfin su, wanda kuɗin su bai wuce munzali ba, ledar tsakar ɗaki dasu labulaye kuwa Goggo Suwaiba da Goggo Jummai ne suka yi mana, yayin da Baba ya sai wa ko waccen mu firit da keken ɗinki a cewar sa duk mu kama sana'a.

Hajiya Babba ta yi mana turaren wuta, kuɗin sayan kayan kitchen kuwa kowacce sadakinta akan damƙawa uwarta, ta saya mata abinda ya kamata dashi.
Nan hankali ya kuma tashi, don duk cikin mu sadakin Salma ya ɗara na kowa. Nikam ma har yanzu ba'a kawo leden ba . Hakan ya ƙara rura wutar tsegumi a tsakanin mutan gidan mu, yayin da uwar kowacce a cikin mu fafutukanta bai wuce ace ta haɗawa ɗiyarta kayan kicin ɗin da ya zarce na kowa.

Da kuka naje wa Ummanmu sakamakon wata maganar, da naji a masarrafar jina ta fito daga ɗakin Umman Balkisu. Wai wataƙil ma malam Yusuf, ba aurena zai yi da gaske ba kawai wasa yake mini da hankali, in ba haka ba meyasa har yanzu ba'a kawo lefe ba balle a kai ga maganar sadaki, tunda mu a gidan mu du tare ake kawowa. Kuma gashi ya nuna cewar a shirye yake.

"Umma na shiga ukuna, zuciyata zafi take yi mini wallahi wai shin da gaske Malam Yusuf ba da gaske yake yi ba?, yaudara ta kenan zai yi?, to ma meye dalilinsa na aikata hakan a gare ni?".
A jere na jefa mata tambayoyin, ba tare da na samar mata da wani damar da zata amsa mini na farkon ba balle n biyu du na haɗe mata su.

Sai da ta fesar da numfashi mai ɗumi daga bakinta, ta sausauta muryarta kana ta soma faɗin"Na'ima ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu komai zai daidaita, kiyi masa uzuri tunda ya furta cewar cikin satin nan za'a kawo to mu sanya ido mu gani".

Sai da na zuƙe majinar kukan da ta zo mini, kana nace"Umma duk maganar da ake yi kenan a cikin gidan nan, ɗazu har Asma'un sai da ta jefa mini magana akan hakan a faƙaice".
Ina iya jiyo yanda ta sauƙe ajiyar zuciya a ɓoye, kafin tace dani"Kar wannan ya dame ki dududu kwana nawa ne ma suka rage miki a cikin gidan nan".
Saurin taran numfashinta nayi, ba tare da ta dire zancen natan ba"To Umma ke da wasu kuɗin za ki sai mini kayan kicin?".

"Na'ima Allah zai yi kinji, ki daina damun kanki".

Shuru kawai nayi, ba tare da na kuma cewa da ita uffan ba. Domin ita ma kanta tasan da cewar a irin wannan lokacin banda ikon hana zuciyata shiga damuwa game da wannan lamarin.

Wunin ranar Abasiya bata zauna, a gida ba domin sai jele zuwa kasuwa suke yi, Anty Maimuna ta tsaye kai da fata wajen sun kammala dukkan shirin su. Haka nan ma Balkisu Anty Hassana da wasu ƴan uwan Ummansu da suka fara zuwa, suna tsaye akan lamarinta.

Kamar ko yaushe bayan sallan magrib, yaya Majid yace dani Malam Yusuf na waje yana jirana, sai da na ɗan kimtsa kana na fita yana tsaye inda ya saba tsayawa jikin mashin ɗinsa, na iske sa ya amsa sallamar da na isa dashi ɗauke a bakina, cikin sakin fuska.

Tun kafin na gaishe shi, ya marairaice fuska yana sauƙe ajiyar zuciyar da kunnuwana suka jiyo mini sautinta da ƙarfi.

"Maƙagin wannan zuciyar shi kaɗai, yasan irin azabtuwan da tayi na rashin sanya ki cikin idanuna kwana biyu".

Duƙar da kaina nayi cike da jin kunyar zancensa, na kaucewa maganar ta hanyar gaishe shi, sai da ya murmusa kana ya amsa.
Nan yake sanar dani cewar gobe in sha Allahu za'a kawo lefe, daman jiran zuwan wasu dangin mahaifiyarsa da suke nisa, shi ya hana a kawo tuntunin. Tagwayen ɓoyayyun ajiyan zuciya na sauƙe, ina faɗi cikin raina an gama da wannan matsaalar.
"Allah ya kaimu, kuma Allah kawo su lafiya".

Na fara a zahiri ya amsa mini da cewar"Amin".
Shuru ya ɗan ratsa, kamin yayi gyaran murya yace"Ina son sai miki waya, ko da ƙarama ce ta yanda zamu dunga yi magana da juna a kai a kai, kema ko kya huta da rubutun wasiƙa".

Babu shiri wata gajerar murmushi ta suɓɓuce mini, na kuwa yi ta don jin ya takalo abinda ba zai yiyu ba. Ban gama darawa ba ya katse ni ta hanyar cewa"Maganan tawa ce, ta sanya ki dariya haka?".

Tsagaitawa nayi don dole, nace"To ai wallahi in dai wannan zancen ya kai ga kunnuwan su Abba, sai an karairaya ni. Wai wai ai mu dukkan mu bama karɓa abin hannun saurayi ko da kuwa an sanya muku rana, a cewar su Abba ya tanada miki komai sai kinje cikin gidansa".
Jinjina kai yayi"Madalla da gidan tarbiya, tabbas hakan shi ya kamata, yanzu nima dole na ba wa tawa zuciyar haƙuri akan ta rage zumuɗi har a ɗaura sanda za ki shigo gidana a matsayin mallakina".
Na buɗe baki da zummar bashi amsa, fitowar Abasiya daga cikin gida tana gaishe da Malam Yusuf ya sanya ni sararawa. Bata ce dani uffan

Please Login or Register in order to submit comment