Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawowa lafiya nayi masa bayan na gabatar masa da abinci ya nuna mini sai ya dawo zai ci, ya fice ni kuwa na koma ɗaki wajen Salma. Kumburarrun idanunta na zubawa ido da suke rufe kirif kafin na kai hannuna saman goshinta zafi gau jikinta ya ɗauka da hakan ya ke tabbatar da nisan da zazzaɓin yayi a jikinta. A gaugauce na ƙira yaya Yusuf na sanar dashi akan ya taho mata da maganin zazzaɓi in zai taho.
Sai da aka yi magrib na tada Salma tayi salla, tana kan sallayan yaya Yusuf ya dawo na amsho mata maganin tasha, sannan ta fito suka gaisa sosai ya bata wasu shawarwarin domin samuwar mafita game da wannan lamarin.
Nan ta kwana a cewar yaya Yusuf sai gobe muje gida gabaɗaya, Yau ma yaya Auwal tare da Mahmud suka dawo yaya Yusuf kuwa a falo ya kwan.
Ko da gari ya waye zazzaɓin natan ya ɗan sauƙa ba kamar daren jiya da ta kasa runtsawa ba, sai da na shawarce ta akan ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallan nafila ta miƙawa Allah kokenta. Tun kafin ƙarfe tara na gaba komai na kimtsa gidan tunin yaya Yusuf ya fice islamiyya daga can kuma zai tsaya boko, tare da Salma muka nufin nikam da niyyar wuni domin yaya Yusuf ya ce sai da yammaci in an taso daga islamiyya zai zo ya ɗauke ni muje gidan Anti Binta.

Har ƙofar gida mai adaidaitan ya sauƙe mu, hannuwan mu sarƙafe cikin na juna muka shiga gidan, tare da sakin sallamar da Goggo Jummai da Umman su Anty Kubra suka haɗe baki wajen amsa ta.

"Salma sauƙe yaushe inji maƙi baƙo".

Goggo Jummai ta furta, da hakan ya jawo hankulan sauran yaran dake wasa filin gidan suka rugo a guje suka rumgume mu. Hakan ya sanya Umman Salma bankaɗo labule ta fito turus ta ja ta tsaye ganin mu tare.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________________


Page 2⃣5⃣

Tabbas na hange tsananin firgici kwance cikin idanun Umman Salma, da na gaza rabe takamanman na menene. Na tozali da ƴarta cikin wannan halin na rashin nutsuwa ne ko kuma na ganin mu tare.
"Ke Salma lafiya?, a ina kuka haɗu da Na'iman?, yaushe kika zo garin?, ko jiya na ƙira wayarki bana samu".

Ta kai ƙarshen zancen tana nufo mu, kuka Salma ta ɓarke dashi tana duƙar da kanta bisa kafaɗun Ummanta. Ɗago ta tayi tare da jan hannunta da ƙarfi suka shige ɗaki tare da bankaɗo ƙofar ɗakin ta rufe da ƙarfin da sai da ya bada wani sautin gam.
Sai da na sauƙe numfashi kafin nima naja ƙafafuna da suka sanƙare na nufin ɗakin Ummata, kusan karo muka yi da Anty Zakiyya tana fitowa daga ɗakin ganina ya sanya ta washe baki haɗi da faɗin"Ke ce tafe Na'ima?".
Kaina kawai na ɗaga mata na shige ɗakin, Umma na zaune bisa sallaya da alama sallan walaha ta iddar rusunawa nayi gabanta na gaishe ta, ta amsa mini cikin kulawa sannan na gaida Anty Zakiyya ma.

"Kamar sunan Salma naji an ambata ko?".

Anty Zakiyya ta watso mini tambayar sai da na langwashe ƙafafuna waje guda kafin na ce"e ita ce tare da ita muka zo". Zaburowa tayi tamkar wacce aka tsikara da allura ta ce"Ina kuka haɗu da ita ke ɗin?".
Dukkanin abinda ya wakana na baje musu, ina iya jiyo sautin ajiyar numfashin da Umma da Anty Zakiyya suka saka kusan a tare kafin Umma ta fuskanto ni da faɗin"Innalillahi lalle rayuwar nan ta ƙara zama abin ban tsoro, ƙarya ya yawaita gaskiya yayi ƙaranci yayin da farashin tarbiyya yayi tsada riƙon amana kuwa ba'a ta nasa. Dole Salma ta shiga cikin ruɗu tabbas".

"Wallahi kuwa Umma, ba ki ga yanda duk ta fita hayyacinta ba duk a birkice take".

Haka muka cigaba da tattauna a tsakanin mu, ciki na shigowa Umma da zancen da muka yi da Hajiya game da Anty Binta tabbas na hango tausayi da zallar soyayyar da babu algus a cikinsa a cikin idanunta, ta kwanta mini da hankali sosai da har sai da na koka ga duk wanda yayi rashin samun abokiyar koka matsalarsa uwa ta gari.
Sai da nayi sallan zuhr yaya Majid ya shigo muka gaisa dashi, mun ɗau lokaci muna hira dukkan mu kafin na miƙe na shiga sashin Hajiya Babba muka gaisa sosai taji daɗin gani na sai tambaya take yi yaushe zan fara zuwa makaranta. Murmushi nake sakar mata kafin na ce"Hajiya ai tukunna da ɗan sauran lokaci, sai zangon karatun nan ya ƙare sannan za'a ɗauki sabbin ɗalibai".
"Ah to masha Allah, Allah ya nuna mana lokacin muna cikin rayayyu kuma lafiyayyu".

"Amin amin Hajiya".

Nan na zauna har Baba ƙarami ya shigo ya iske ni, na gaishe shi yana tambaya ta dalilin zuwana. Duƙar da kai nayi don haka nan naji na rasa ta cewa wani ɓangaren ina mamakin ta yanda basu san zuwan Salma gidan ba. Domin na tabbatar ko Hajiya ma bata sani ba domin da ta sani tabbas zata yi mini zancen. Ganin bani da wani zaɓin sama na sanar dasu ya sanya ni faɗa musu komai sosai ran Baba ƙarami ya ɓaci ya fusata aihun fu ya fice kamar wanda iska yake jan sa ya fice daga ɗakin.
Da kallo daga ni har Hajiya muka raka shi, kafin ta shiga cewar"Allah dai ya sauwaƙa hali irin na Zinaru, ace har wannan abun ya faru amma ba zata sanar da uban yarinyar ba?. Waye zai tsaya mata in ba shi ɗin ba, duk lalacewar uba ai dashi ake ado ba da uwa ba".
Zugum nayi kawai ina jin sauran zancen natan suna sauƙa a kunnuwana tamkar busar sarewa. Miƙewa nayi na fice na koma sashin mu ina sanyo ƙafata idona suka sauƙa cikin na Umma Salma idonta ƙulu ƙulu alamar ta sha kuka bisa masifar da Baba ƙarami ya balbale ta dashi. Harara ta zabgo mini haɗi da faɗin"Kin gama bin sashi sashi ina yaɗawa?, Allah wadaran rayuwar da ɗan uwanka shine zai yayata sirrinka ga wasu baren".
Caraf na jiyo muryar Baba ƙarami daga bayana, ya fito daga sashin su ya amshe zancen da faɗin"Zinaru menene laifin Na'ima cikin wannan lamarin?, don ta samar mata da wajen bakewa a gidanta ko meye?. Kuma da kika maganar bare duk cikin mu nan waye bare?. Tun wuri ki dawo hayyacinki kafin ruwan da kike niyo a cikinsa ya cinye ki".
Yana gamawa ya kallo ni haɗi da cewar"Allah yayi miki albarka Na'ima". A sanyaye na amsa da"Amin Baba na gode".

Daga haka ya fice ni kuwa na koma ɗakin mu, ban tarar da Umma ba illa Anty Zakiyya tana gyaran gado zama nayi kan ledan tsakar ɗakin dirsham tallafe da kuncina.
"Ke lafiyarki kuwa?".

Sai da na janye hannuna kafin na ce"Babu komai kawai tinani nake yi, wai sai yaushe lamarin gidan nan zai daidai ne?".
Murmushi ta sakar mini"Na'ima kenan ke dai lamarin gidan nan ai kawai sai dai addu'a. Gashi dai su Abba suna iya ƙoƙarin su amma kamar ana zubawa kafaffen ƙarfe ruwa kullum ba cigaba".

"Allah dai ya kyauta, ni kuwa ya labarin wannan mutumin da muka fara dake ran nan?".
Bata tanka mini ba sai da ta gama sanya rigar matashin dake hannunta, kana ta ce"Na'ima ai lamarin duniyar nan ya ƙara taɓarɓarewa, ni yanzu har tsoron auren ma nake yi domin sam babu Allah a zuƙatan samarin. Wai kinsa yanda nake tsammatawa mutumin nan kuwa nutsuwa da hangen nisa, a yanda yazo mini tamkar ba zai iya bin wata hanyar da mace tabi ba, zuwansa gidan nan har sau biyu ban sani ba ko don ban taɓa sanya wani saurayi bane a raina na ji na aminta da Adamu oho, ban farga ba sai da ya ɓullo min da inda zan yi zato ba. Ya nemi kafin na zama halaliyarsa ko da na nuna masa rashin amincewa ta game da lamarin har da guzurin wa'azi da tunatarwa nayi masa game da irin azaban da Allah maɗaukakin sarkin ya tanada da duk mai kusantar zina. Amma yayi kunnan uwan shegu dani ya janye jikinsa daga zuwa gidan nan, da na auri namiji mai irin wannan halayyan wallahi gwara na mutu banyi aure ba in yaso gorin jama'a ya taru yayi wa zuciyata illa har ta buga kowa ya huta".

Ji nayi wani abun ya tokare mini ƙirjina, wannan zantukan na Anty Zakiyya wallahi ba kaɗan ba suka taɓa mini zuciya tare da dukan ƙwaƙwalwata. Wai yanzu samun miji na gari ma ya zamto wahala yayi kuma tsada cikin gari, wani irin rayuwa ce wannan da kafin aure namiji zai nema budurwa ta sallama masa kanta, idan ba'a yi rashin dace da macen ƙwarai da ta kwankwaɗi tarbiya ta ƙoshi ba, sai a aikata aika aikan wanda daga ƙarshe azo ana cizon ƴatsa. Bayan ya gama cin moriyar ganga ya gudu ya yasar da koronta. Har yamma raina cunkushe na kasa samun nutsuwar ruhi. Bayan sallan asr aka tada wata hatsaniya a filin gidan tsakanin Umman Salma da Daada wai ta kama ta tana gulmar zuwan Salma gida har da ƙarin manda wai Abdallahn ma ba'a ana zargin ɗan damfara ne domin fuska biyu gare shi yanda ya bayyana yayin auren Salma ba hakan aka tarar dashi ba bayan aure. Rikici aka yi tamkar ba zai ƙare ba, har da jiwa juna rauni sai dasu Abba suka shigo tsabar ɓacin ran da suka rufewa Baba ƙarami idaniya ya zabgawa Umman su Salma kyawanan mari har guda uku tare da gindaya mata zazzafan kashedin matuƙar ta ƙara tada wani tashin hankalin a bakin aurenta kuma ƴaran dake tsakaninsu ba zai hana shi kora ta gidan iyayenta taje ta ɗanɗana zawarci ba tunda hakan ta zaɓarwa rayuwarta.

Tsit gidan ya nutsu kamar ba namu ba, domin ko wacce mace ta shiga taitayinta haka nan ba ƴaƴansu ƙarfe biyar da rabi ƙiran yaya Yusuf ya shigo wayata na ɗaga ya sanar dani yana ƙofar gidan, da dariya na isa gare shi ina faɗi cikin zolaya"Yaya nikaɓ Allah ya nuna mini ranar da zaka shigo cikin gidan nan kai tsaye, kai kullum sai nan maka jagora".
Rausayar da kai yayi yana kaɗa makullin mashin ɗinsa dake saƙale a ɗan yatsar hannunsa na hagu ya ce"Kin fi kowa sani kunyar mijin nakin ai, ni dai kam ba zan iya shiga kai tsaye ba".
Sai da na dara sosai na furta"Lalle kam na fi kowa sani amma kunyar nan ko ta mutan da sai haka". Na faɗa ina wucewa gaba yana biye dani a baya domin ya saya ɗauko wani leda a mashin ɗinsa sashin Hajiya babba muka nufa suka gaisa ya ajiye mata ledar hannunsa wanda bansan ko meye a ciki ba sai dai nafi kyautata zaton kayan itatuwa ne.
Sun ɗan taɓa hira kafin yaya Majid ya shigo suka nufi sashin su Abba, zan miƙe domin magrib da ya gabato Hajiya ta zaunar dani da faɗin"Na'imatu tabbas kin ciri tuta cikin mata kinyi dace da nagartaccen miji salihin bawa kamar Yusuf, na kore ki da kiyi masa biyayya gwargwadon iyawar ki matuƙar bai saɓawa Allah da manzonsa ba. A yanzu shine gaba da komai a rayuwarki hatta iyayenki basu da ikon da yake dashi da ke don haka ki riƙe aurenki ki kyautatawa mijinki ki ba wa mara ɗa kunya ko don wannan bita da ƙullin da sauran matan gidan nan suke yi miki da nufin su ganki kin dawo cikin gidan nan, ita ma Zakiyya Allah ya fito mata da miji ta samu tayi aurenta".

"Amin amin ya Allah, in sha Allah Hajiya zan yi dukkan abinda kika ce nima kaina nasan yaya ya fita daban ko a cikin jinsin su na maza. Bari na sa miki ruwa a bura magbir yana gabatowa".
Washe baki tayi tana ɓantaran goronta haɗi da cewar"Ai yanzu tunda aka yi bikinku, Hanifa ce ke yi min wannan ɗawainiyya sam bata gajiya ce da uwarku ɗaya sai ince a nono suka sha". Sosai na saki dariya domin yanayin da ta sakin zancen cikin sigar zolaya. Na tashi na zuba mata ruwa a buta sannan na ɗauki ledar da yaya Yusuf ya kawo mata kankana ce da lemo sai kuma abaya guda shida na zubo mata su a babban tire bayan na ɓare lemon na ajiye mata a gabanta. Na fice izuwa namu sashin alwala nayi na shige ɗaki nayi salla sannan na fara haramar tafiya dai dai ina saɓa hijabina Salma ta shigo ɗakin kallo ɗaya nayi mata na ɗauke idona daga gare ta har ta ƙariso ta zauna kusa da Anty Zakiyya da take duba wasu littattafa.
Sallama na fara yi Anty Zakiyya da hakan ya sanya Salma faɗin"Na'ima dan Allah ki zauna zamu yi magana".
Kamar banji ta ba nayi idanuwa suna hasko mini irin cin mutumcin da Ummanta tayi mini a faƙaice sanda nake alwala a tsakar gida har da faɗin na fice daga lamarin auren ɗiyarta naji da matsalar tawan auren da ta suffanta da jalli joga na wuce gadi.
Sai da Anty Zakiyya ta sanya baki sannan na ɗosana mazaunaina na zauna na ce"ina jinki".

"Dan Allah Anty Zakiyya, Na'ima ku bani shawara kan lamarin nan wallahi ina cikin tashin hankali tun ɗazu su Babba suke nemar wayar Abdallah a kashe daman tun ɓacewarsa nima na daina samunsa a waya haka nan iyayensa ma basa ɗaga ƙira na rasa abin yo gabaɗaya kaina ya ƙulle".
Ta kai aya wasu hawaye suna biyo gefe da gefen kuncinta, taɓe baki nayi ina kawar da kaina gefe na ce"Salma kiyi haƙuri in sha Allah komai zai zo ƙarshe dukkan tsanani yana tare da sauƙi matuƙar aka sanya haƙuri da juriya".

Anty Zakiyya ta ɗaura da"Haka ne Salma kiyi haƙuri sannan ki cigaba da miƙa lamuranki ga Allah. In sha Allah sai kinga haske ya bayyana a rayuwarki".
Tashi nayi na isa gare ta tare da dafo kafaɗunta kamar mai raɗa nake cewar"ni zan tafi amma dan Allah roƙon da zanyi gare ki shine kiyi ƙoƙari ki cire komai daga ranki, sannan ki dunga kai kokenki ga inda ya dace watau wajen mahaliccinki". Tashi tayi ta rumgume ni sannan muka fito hannuwanmu riƙe cikin na juna, kamar yanda na saba haka nan ma yau sai da nabi dukkan ɗakunan sauran matan gidan nayi musu sallama a ɗakin Goggo Jummai na iske Ummata muka yi sallama sannan na wuce sashin Hajiya ita ma nayi mata sannan su Abba da suka ƙara yi mana nasiha har da yaya Yusuf.
Daga nan gidan Anti Binta muka nufa, haka nan kawai na sinci kaina cikin faɗuwar gaban da bansan dalilin hakan ba, har muka isa babu wasu jama'a a gidan daga ita sai ƴaƴanta biyu Amir da Husna sai wasu mata biyun da ban gane fuskokinsu ba. Muna zama yaya Auwal da Mahmud suka shigo a ladabce na gaida Anti Binta kamar yanda nayi tsammani bata amsa mini ba illa bina da tayi da wani irin kallon ta ce"Daga ku kuma kuke?".

"Taje gida wuni ne, yanzu na ɗauko ta shine muka biyo ta nan". Cewar yaya Yusuf yana ɗan satan kallona sai da ta taɓe baki tamkar wacce taga kashi kamin ta furta"Husna tashi ku shiga ɗaki da ita zan yi magana da jinina".
Ciki-ciki nayi murmushi kafin na yunƙura na bi bayan Husna muka shige ɗaki, ban bari wani tinanin ya sama matsuguni cikin kunyata ba a ƙoƙarin kaucewa hakan na ɗauki wayata ina dannawa. Sai da muka yi sallan isha'i muka tafi.

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________________


Page 2⃣6⃣


Haka kwanaki biyu suka shuɗa sam zaman gidan ya kasa yi mini ɗaɗi, saboda kaɗaicin da ya daddabe ni ya hana ni tsakat. Kasancewar har yanzh maman Hanan bata dawo ba yaya Auwal da Mahmud kuwa sai dare suka dawowa asubar fari sun yi ficewar su abincin kari ma sai dai Mahmud ɗin ya dawo ya amsa musu su ci a kasuwa. Jarabawar ƙarin girma da tantance malaman makarantun gwammati da mai girma gwamma jaharmu ya sanya aka yi, wanda yaya Yusuf yana cikin wanɗanda aka tantance su cikin yardan Allahn da muka jingina dukkan lamuran mu gare sa sai gashi sunan yaya Yusuf ya bayyana cikin waɗanda suka sama ƙarin matsayi daga malamin primary ya zamto headmaster na makarantar ranar mun muna wa Allah godiyarmu sosai don raya duk tsawon darenmu muka yi muna nafila da jaddada godiyarmu gare sa domin ba wayonmu ko isarmu bace.
Haka rayuwa ta cigaba da gudana, kullum da tinanin Salma da nake kwana nake tashi maƙala cikin raina, gashi hannunta babu waya balle na ƙira ta naji halin da take ciki. Zafafan furcin da Ummanta ta yaɓa mini zuwana na ƙarshe gida da muka keɓe da Salma muna tattauna lamarin ya suka fara dawo mini cikin kwanyata tiriyan tiriyan.

"Na'ima wai sau nawa zan sanar dake cewar ki fita harkan Salma ne a cikin gidan nan?, matsalar gidan aure ai ba a kanta aka fara ba kuma ba kanta ne ƙarshe ba, sannan damuwar namiji ba zata taɓa jin silar rayuwarta ba tunda nima har yau ban daina zuƙa da fesar da numfashi ba duk da kuwa baƙin cikin Abban su dake raina. Ki fuskanci naki matsalar da kuma rayuwarki sai gobenki ta fi inganta akan wannan sanya idon da kike yi mawa ƴaƴana cikin lamuran su, kuma yau ko Abdallah takardar saki ya aikowa Salma na tabbatar gwara ita sau miliyan tunda ko bayan ranta ace ta taɓa auruwa kuma ko ta dalilin hakan darajarta da kimarta ta ƙaru a idanun mutane da yawa. A kan wacce bata taɓa aure ba".

Sosai maganganunta sunka daki kwakwalwata kwatankwancin yanda ake bugun gero yayin casa cikin turmi, suka baƙanta mini zuciyata da yake harbawa a hanzari fiye da kima ƙirjina ya shiga dakan lugudan tara tara. Sarai na gano inda maganganunta suka dosa domin zuciyata ta hashasho mini zancen da sauran gangar jikin suka amince dashi, dukkan zantukanta gugan zana take yi mini da kuma goran mini akan ƙaddarar da ta faɗarwa rayuwar Anty Zakiyya na jinkirin aure. Duk yanda naso daidaita numfashina da yake fizga lamarin ya gagare ni da ƙarfe na fizge hannuna daga cikin da Salma da ta riƙe gam, duk cin mutumcin da tayi a kaina bai dame ba kamar wanda tayi wa Anty Zakiyya. Ƙara kusanto Umman nasun nayi bakina yana rawa tamkar zai rawar ɗari har zanyi magana sai kawai na tina wataƙil furcin da zan furzar yanzu idan Ummata tayi ya baƙanta mata rai domin ta hana ne da wannan halayyar ta tunkarar wanda yake sama damu yayin ɓacin rai musamman sauran matan gidan mu da suke jin tamkar su ɓalɓale mu da fetir sun cinna masa ashana. Kaina kawai na gyaɗa ina barin wajen da sauri. Ina jiyo maganar da ta raka ni tashi kafin taja tsuka.
"Ai da kin tsaya kin tabbatar min da kin riƙa, kin kuma tabbatar min da an sama cigaban rashin kunyar da tun can nasan ki dashi shashawa kawai".

Ko sallama ban iya yi ba, na faɗa ɗakin Ummata kallo ɗaya nayi wa Anty Zakiyya da na tarar zaune dirsham a ƙasa ta zagba uban tagumi ga hawayen da suke fareti a dandamalin tudun fuskarta na ɗauke kaina gefe, ni kaɗai ina huci ji nake tamkar na koma na amayarwa Ummansu Salma duk zancen dake cikina ko zanji sanyi daga tafaffasan da raina yake yi mini.

"Ya Allah ya dubi lamarina, nasan ba mantawa kayi dani ba. Ka kawo min sauƙi daga ƙuncin da nake cikinsa idan da rabon aure a cikin ƙaddarar da ma'ikunta suka rubuta cikin littafina tun ina cin mahaifiya ka kawo min miji na gari nayi aure ko zan rayu cikin sa'ada da sallamar ruhi. Menene laifina? shin ko wani bawa shi yake riƙe da alƙalamin rubutun ƙaddarar rayuwarsa da kuwa yake jingina min laifin da ban da ikon canjaza ƙaddarata?, da hakan ne nima kaina da ban zauna har yanzu babu aure ba da na gaggauta rubuta aure cikin littafina da manyar harrufa, menene laifina don jinkirin aure ya faɗo a tsagin ƙaddarar da tun kafin samuwa ta bayan ƙasa aka rubuta dukkan abinda zai faru dani tun daga haihuwata har ranar da zan koma ga mahaliccina".

Furcin Anty Zakiyya kenan, da suka ƙara tarwatsa mini raguwar gwarin gwiwa da kuzarin jikina, tilasta na runtse idanuna saboda sarawar da kaina yake mini tamkar maƙeri ya sama ƙarfe yana sauƙe masa bugun guduma. Ranar Umma bata gidan domin tun zuwana Anty Zakiyya ta gaida mini yaya Majid ya kai ta ƙaramar hukumar geidam ta jahata ziyara wajen ƴan uwanta. Kasancewar mu a cikin potiskum muke, ni kaɗai na ta lallashin Anty Zakiyya har na samu ta kwantar da hankalinta ranar ban tsaya jiran yaya Yusuf yazo ɗauka ta kamar yanda muka saba in dai nazo gidan shi yake zuwa ɗauka ta da yamma in an taso daga islamiyya, abin hawa na nema na hau nayi tafiya ko sallama banyi wa matan gidan ba kamar yanda na saba domin tsabar taƙaicin bahagon tinani da ragwamen hankalin mutanen yankin da matan gidan mu suna sahon farko a ciki, na jingina laifin rashin yin aure ga duk wacce ƙaddarar hakan ya faɗa mata ba tare da la'akarin cewar dukkan bawa baya jugewa ƙaddararsa balle su yi masu uzuri da tinanin cewar komai lokaci ne matuƙar yayi babu mai dakatar dashi. Sashin Hajiya Babba ɓa da na leƙa na tarar da ita tana sallan ban tsaya jiran ta iddar ba nayi wuce ta.

Tun daga ranar ban sake marmarin zuwa gidan ba, sai dai na ƙira yaya Majid mu gaisa dasu Umma, a haka lokaci ya cigaba da shuɗawa kwanakin mu na duniya suna ƙarewa ba tare da mun farga ba sai ma ƙarin burirrukan da suka cika rayukan mu, kwanci tashi zangon karatu ya ƙara aka fara ɗaukar sabbin ɗalibai a makarantu sanin ba'a sanyi da borin jiki tunin yaya Yusuf ya karɓi takarduna da suke wajen su Abba ya nema mini gurbi a makarantar da yake headmaster kasancewar akwai sakandiri a haɗe, sai da ya kai ni na zana jarabawa tunda ba makaranta nayi JSSCE ba, na duƙufa da addu'a babu dare babu rana akan cikar burina haka nan ma Ummata da ƴan uwana, cikin ikon Allah da sakamako ya fita na sama science class wanda shine zai bani damar karanta mass communication a gaba har na cimma burin zama ƴar jarida kuma marubuciyar da nake fata da muraɗi, sosai su Abba da hajiya Babba ma suka yi mini murna haɗi da ƙara yi mini wasu nasihohin.
Dukkan abin buƙata yaya Yusuf tunin ya samar mini kama daga kan kayan makaranta da littattafai, kuɗi makaranta kuwa Baba ne yaso biya mini domin shima yana ƙaunar karatu a lokacin baya sanda muke yara har zaunar da mu yake yi inda muka ce ba zamu makaranta ba, yana bamu labarin yanda a lokacin su ilmi yake da arha sai dai ba kowa bane yasan muhimmanci kuma kyauta ne ga kowa har abincin da zai ci. Gida gida ake bi aka ɗaukar yara zuwa makaranta a lokacin hajiya Babba da marigayi mahaifinsu har a cikin tukunya suke ɓoye su domin har a gansu ace za'a kai su boko, saboda bahagon tinani irin nasu akan karatun bokon a wancan zamani.

Yaya Yusuf sam ya nuna mishi cewar zai ɗauki nauyin karatuna har na kammala in sha Allahu, su dai kawai su taya ni da addu'a Allah ya kaɗe sharri. Ana gobe zan fara zuwa makaranta da yamma yaya Yusuf ya dawo bayan ya gama cin abinci ya fice sallan magrib bai dawo ba sai da aka yi isha'i ya ce in shirya zamu gidan Anty Binta domin gobe Mahmud ma zai koma nashi makarantar.

Bansan dalili ba haka kawai na tsinci kaina cikin matsanancin faɗuwar gaba, a haka na shirya na ɗaura zungumemen hijabina kalar ruwan toka da ya rufe atamfar dake jikina.

Zaune a tsakar gidan muka iske ta, sai ƴaƴanta biyu da suke zaune gefe Amir da Husna, ganin mu ya sanya ta rage sautin rediyon da take saurara da aka saka waƙar marigayi Mammman Shata waƙar ta na tsaya ga annabi Muhammadu. Sai da muka zauna muka haɗe baki wajen gaishe da ita ta amsa mana babu yabo babu fallasa, sannan ƴaƴanta ma suka gaishe da yaya Yusuf, bai amsa ba illa zaro ido da ya yi fuskarsa babu alamar wasa ya ce"Itan baku ganta

Please Login or Register in order to submit comment