Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba nima banyi gigin cewa da ita wani abun ba, tayi wucewarta sai yanzun na lura da Sagiru da yake tunkaro wajen cikin motarsa da fitillunta suka dalle ƙofar gidan mu.

Sai da ya gama daidaita parking, nayi zaton shi zai fito sai nayi arangama da saɓanin tunanina. Naga Abasiya ta ɓalle marfin ƙofar ɓangaren mai zaman banza ta shige.
Maganar da Malam Yusuf ya ɗora dashi, da suka yiwa ƙofofin kunnuwann diran mikiya daga sama ya sanya ni figitit na dawo daga kallon da nake yiwa Abasiya har ta shige motar.

Sunkuyar da kai ƙas nayi ina sauraron ragowar zance daya ɗaura dashi, ƙiran sallan isha'i da lasifikan masallacin kusa da gidan ya ƙwala, ya tilasta mana yin sallama da juna, duk da kuwa har raina ni naso hakan domin na tabbatar ko shakka babu Abba ko Baba ko Baba ƙarami ɗaya daga cikinsu ya fito ya iske nida Abasiya duk muna tsaye da samari a ƙofar gida ranar ba mu ba hatta uwayen mu ma sai lamarin ya shafa.

Sam basa lamintar tara samari a ƙofar gida, indai bai wuce mutum ɗaya ba amma ya zamana duk mu ɗin muna tsaye da samarin mu shine abinda suka yi hani.
Haka muka yi sallama da Malam Yusuf akan gobe danginsa zasu kawo lefe gidan mu, ina komawa ciki na sanar da Umma tayi murna sosai wanda baya rasa nasaba da farin cikin da tayi tozali dashi malale a saman fuskana.

Haka nan ma Anty Zakiyya ta nuna zallar farin cikinta, ciki kuwa ba ya yaya Majid da yake ta faman faɗin kalmar"Alhamdulillahi kwana biyu an canja daga, maganar ki da ake yi lungu da saƙon gidan nan, kai Umma indai haka wasu dangin suke babu rufawa juna asiri sai ma fatan sirrin juna ya tono, Allah wadaran s....".

Saurin kwaɓan sa Umma tayi"Kul Majid kar na ƙara jin, ka furta wani abun makamancin haka".
Shuru kawai nayi, shima kenan da yake namiji wanda sai ya wuni baya cikin gidan. To mu kuma da muke zaune ko yaushe dasu fa?.

Wayewar safiyar ranar sosai gidan mu ya ƙara cika, kasancewar lokacin biki sai ƙara gabatowa yake yi yau saura kwana biyar. Ƴan uwan Umman ma da yawan su sun zo domin bata taɓa aurar da ɗiya ba sai a kaina hakan ya sanya su yi mata kara, kwan su da ƙwarƙwatan su duk sun zo.

Da yammaci sai ga ƴan uwan Malam Yusuf a gidan mu, sun kawo lefe kuɗar da aka rankaɗa shi ya tabbatar mini da isowar ina zaune daga cikin ɗakin, zumbur su Salma duk suka miƙe suka fice wai zasu kallo.
Sashin Hajiya Babba aka kai kayan kamar yanda aka yi yayin da aka kawo na sauran, an musu tarba na ban girma da mutunci da suka tashi tafiya aka basu tukwuicin naira dubu goma.
Ina zaune inda suka barni zuciyata tana dakan lugudan tara tara, Habiba ta faɗo ɗaki a guje harara na zabga mata"Meye hakan?".

Sai da ta mayar da numfashin gudun da ya taro mata, kana tace"Anty Na'ima kinga kaya kuwa?, akwatuna masu taya har guda biyar danƙare da kaya".

Sakake nayi ina kallonta, kafin na bata amsa Balkisu da Salma suka shigo.

"Kai gaskiya Malam Yusuf yayi namijin ƙoƙari, wannan lefen kaɗai ya isa fayyace gaskiyar zancensa cewar a shirye yake".

Furcin Balkisu kenan kan na furta wani abun Salma tayi caraf"Gaskiya kam son barka wallahi, akwati huɗu duk da kaya. Zannuwa fa asha takwas Goggo Suwaiba ta irƙa, hijabai kuwa takwas cif, takalmi biyar ga sarƙa da ɗan kunne da ƙanana kaya banda su kayan kwalliya kai tufarkalla".

Daɗi, farin ciki ko murna cikin ukun nan na gaza rabe wanne na zo mini a wannan lokaci, kuka mai ƙarfi da bansan dalilin zuwansa ba na ɓarke dashi wiwi na shiga rero shi.
"Dalla banza kuka meye kike yi?".

Salma ta furta tana fizgo ni jikinta, duk da yanayin da nake ciki hakan bai hana ni wurga mata harara ba, ita ma ta rama.
Ranar naga tsantsan baƙin ciki tuburan daga mutan gidan mu, don kuwa babu wacce ta buɗi baki tayi wa Umman mu Allah ya sanya alkhairi.
Duk hakan bai ɗaɗani ba, balle ya dame ni kamar abinda Abasiya tayi kuka tayi tsakanin ta da mahaliccinta wai a ƙira Sagir ace masa ko ya ƙara mata lefe ko ta fasa, domin daga lefen Salma da Abdallah yayi mata akwatuna takwas, da wasu a baho, har da na uwa da uba. Sai nawa domin Balkisu da Abasiya duk nasu uku uku ne, Daada da Anty Maimuna suka ƙwaɓe ta.

Washe gari aka je mana jere, kowacce da dangin uwarta ake je gudun tsegumi amma sai da aka yi, har rigima aka so haɗawa dangin Umman su Balkisu da dangin Daada.
Ana gobe ɗaurin aure su Abba suka haɗa mu gabɗaya, suka yi mana nasiha mai ratsa jijiya da ɓargo ta yi kanekane cikin jiki. Haka nan ma Hajiya Babba tayi mana nata kafin Goggo Suwaiba da Jummai suka ɗaura dashi sa'an nan uwayen mu munsha kuka har muka godewa Allah.

Da zazzaɓi na wayi gari, ɗinkin leshi ruwan toka, da zanen baƙi baƙi Baba ƙarami ya saya mana aka ɗinka mana, shi muka saka. Yayunmu matan suka haɗa kuɗi suka ɗauko mana mai kwalliya aka tsantsara mana, muka fito fes yaya Majid kuwa ya kawo mana mai hoto aka tayi haska mu, ƙarfe sha ɗaya dai dai aka ɗaura aure, a ranar su Abba suka ce kowacce za'a kai ta gidan mijinta.

Laffaya Hajiya Babba ta ɗaura mana, aka kai mu ga uwayen mu domin yi mana nasihar ƙarshe.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

______________________________________

Page 1⃣2⃣

Sosai nake kukan bilhaƙƙi da dukkan gaskiyata, ko kalma ɗaya na gaza furtawa illa kukan da na tsananta yinta. Da ƙyar na iya ƙarfin halin faɗin"Anty Zakiyy...".

Ragowar suka maƙale mini a maƙoshi, ba tare da na ƙarisa ba. Rungume juna muka muna sakin wani irin azababben kukan da ya ɗarsar da tausayin mu a zuƙata duk mutanen dake wajen. Bamu taɓa rabuwa ba sai wajen kwana, cikin babu wanda ya taɓa tafiya kwana biyu, dukkanin rayuwar mu tare muka taso zaman kusa da kusa wai zaman gira da ido, inji masu hikimar sarrafa zance. Amma yau zan tafi tafiyar da ake yi mini fatan zama dindindin sai dai mutuwa ta raba.

Tabbas aure yaƙin mata, in ba shi meye zai raba soyayyar nan dake tsakanin uwa da ƴa. Ya raba ƙarfin ƙaunar dake sarƙafe tsakanin ƴan uwa.

Da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikin Anty Zakiyya, aka fita da ni izuaa sauran ɗakunan matan gidan, ba yabo babu fallasa duk suka yi mini addu'ar zaman lafiya da samuwar zuri'a ɗayyaba.
Kiciɓus da muka yi da yaya Majid a ƙofar gida, ya sanya hawayena ƙara ƙarfi ƙamar burɗaɗɗan famfo sosai shima yayi mini nasiha, Dai dai sa'ilin nan aka fito dasu Balkisu ma za'a kai su, fizgewa nayi daga riƙon da yaya Majid yayi a hannunawa na isa gare su, muka rungume juna sosai dukkanin mu muke sakin ƙwallar rabuwa da juna, duk da kuwa duk a garin za mu zauna. Salma ce kawai zasu wuce jahar mijinta kasancewar ba ɗan nan bane aiki ya kawo shi.
Mun ɗai sakanni a haka, kafin aka wuce da kowa ga motar da mijinta ya kawo domim ɗaukar amarya.

Yaya Majid ya sanya ni cikin ɗaya daga cikin motoci biyu da Malam Yusuf ya turo domin ɗaukar amarya.

Goggo Jummai da dangin Ummata mutane uku, sai kuma su Habiba su kenan suka kai ni. Anty Zakiyya bata je ba, saboda matsanancin kukan da take yi Goggo Jummai tace ta zauna kawai. Bani da yawan ƙawaye domin duk ƙawayen su Salma ne. Tsiraru daga cikin su muke zumunci dasu.

Har motar ta taka burki ban tsagaita daga kukan da nake yi ba, wanda ya taimaka wajen ƙara sauƙar mini da wani zazzaɓi mai ƙarfi. Hannuna riƙe cikin na Goggo Jummai gefen haduna kuwa Adda Huriyya ƙanwar Ummata muka shiga cikin gidan, shigowar mu ta sanya matan da suka yi dandazo a gida sakin guɗa sosai, sai da aka fara kai ni wajen danginsa na uwa da uba da suka haɗo na gaishe su, sannan wajen Babbar yayarsu Anty Binta kana ɗakin matar yaya Auwal ita ma muka gaisa sannan aka kai ni ɗakina.

Nasiha sosai suka ƙara yi mini, tare da nusar dani cewar shi zaman aure ibada ne kuma ɗan haƙuri ne da kau da kai ga wasu abubuwan samuwar hakan zai ya haifar da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata.
Duk tafiya suka yi, domin su Abba sunce kar wacce ta kwana a gidan amaran. Sun tafi sun barni da kewar su maƙil a raina, ga zazzaɓin da yake ƙara ƙarfi a jikina. Matan da muka iske a gidan ma, a sannu suka fara watsewa na tabbatar da hakan sakamakon jin hayaniyar da ta ragu. Sannan Anty Binta ta shigo tayi mini sallama akan zata koma gidanta tare da wasu dangin nasun, sai Allah ya kai mu ta dawo.

Ina zaune kaina ya ta'azzare ni da balaƙeƙƙen ciwon, naji zaman mutum a kusa na figigi na ɗago kaina domin sam banji shigowar sa ba sai zaman da yayi.

Komar da kaina nayi na sunkuyar, ban san dalilin zuwan wani kuka mai ƙarfi da ya kufce mini ba. Sosai yake lallashina da dukkan kalman da yake da yaƙinin za ta yayyafawa wutar dake ci a cikin ƙirjina ruwan sanyi. Tabbas Malam Yusuf ya cika cikakken masoyi domin da taimakonsa zazzaɓin da ya lulluɓe ni ya sauƙa mun gabatar da dukkan abubuwan da ake yi a ranar da aka kai amarya ɗakinta kama daga gabatar da sallar nafila domin nuna godiyar mu ga mahaliccin mu.

Wayewar garin ranar ba laifi naji sauƙi a jikina sosai. Ina yin sallan asubahi na gyara ɗakin tun kafin Malam Yusuf ya shigo don a falo ya kwana fahimtar da yayi tsoro ya dabaibaye ni, kasancewar ban taɓa keɓewa da wani namijin ba balle kwana ɗaki ɗaya.
Tsaf na gyare abinda na taɓa, na shiga banɗakin dake cikin ɗaki nayi wanka sannan na shirya cikin riga da zanin atamfata. Na zaun nayi zuru da idanu kewar ƴan uwana ta hana ni sakat.
"Na'ima wannan kukan ya isa haka, kinji ki daina in sha Allah za ki saba".

Muryarsa da suka dirarwa ƙofofin kunnuwana, ya sanya ni ɗago kaina nayi masa kallo ɗaya, kawar da zancen nayi ta hanyar rusunawa nace dashi"ina kwana an tashi lafiya".
Sai da ya faɗaɗa murmushinsa kafin ya amsa da"Lafiya ƙalau Amarya ya kwanan baƙunta?".
"Alhamdulillah".

Na amsa dashi ƙasa ƙasa, wanka ya shiga hakan ya bani damar fita falo na kimtsa ina gamawa sallamar da matar yaya Auwal ta shigo dashi suka ratsa ni. Murmushi muka sakarwa juna sai da ta zauna na gaishe ta, ta amsa sai zolaya na take yi wai ya kuka, murmushi kawai nake yi mata kafin ta fita ta shigo mana da abin karin mu.

Sai da ya shirya tsaf, ya fito muka ci abincin tare yana ɗan jana da hira. Jin hayaniyar dake tashin tsakar gidan ya ƙaru ya tabbatar mana da ƙarin mutanen da suka cika gidan, su Anty Binta ne suka zo muka gaisa tare da yin sallama da danginsu da zasu koma yau. Zuwa ƙarfe goma ƴan gidan mu suka zo har da Anty Zakiyya, sun taho mini da ragowar kayana da ba'a taho dashi ba.

Munsha hira sosai har da matar yaya Auwal Anty Habiba da ƴarsu ɗaya Hanan. Fitar Maman Hanan ya sanya wasu ƴan uwana Abbana da suka zo ganin ɗakina kafa hirar cewar zaman da facala yafi zama da kishiyiyo gudu gom, a cewar su sanya ido, hassada da baƙin ciki ne yake wanzuwa a tsakaninsu wasu ma idan ba'a yi dace da matan ƙwarai ba har raba kawunan mazajen nasun suke yi.

Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe, ni kaɗai ina nazartar yanayin Maman Hanan da yanda ta tarbe ni da safiyar yau sai dai bahaushe yace yau da gobe shi ke sanya mutum sanin haƙiƙanin kowa da kowa.
Sai yamma lilis suka tafi, haka akk jera kwna biyu kullum sai ƴan gidanmu da baƙi sun zo ban sani ba ko hakan ne ya rage mini kewar su da nake yi oho.

Satina ɗaya a gidan miji ban taɓa girki ba, kullum Maman Hanan ita take yi. Cikin ƙanƙanin lokacin da na zauna da ita na fahimci macece mai sauƙin hali sam bata da wani aibu ga ta iya zama da mutane, wani lokacin sai dai naji kunya domin kafin na tashi ta gama komai na karin kumallo sai dai na taimaka mata da shirya Hanan izuwa makaranta. Domin tare suke fita da Malam Yusuf kasancewar a makarantar da yake koyarwa take.
Tare muke cin abinci, mazajen mu ma nasu tare. A falonta muke ci domin yafi nawa girma da fili, dukkan biyayyar aure da ladabi babu wanda bana yiwa Malam Yusuf, zaman lafiya da ake wa ikirarin cewar yafi zama ɗan sarki muke yi tsakanin mu.

Wata yammacin da na cika kwanaki goma cif, sai ga Salma a gidan bisa jagorancin Habiba. Zumbur nayi ina sakin kwanon samiran da nake wankewa na rungumo ta cikin tsantsan farin cikin ganinta.

Hannunta naja muka shige ɗaki, bayan sun gaisa da Maman Hanan na kuma gabatar mata da ita, sam na gaza zaune balle tsaye tsabar murna na kawo mata ruwa da ragowa cincin ɗin biki da bai ƙare ba.

Furcinta da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya, suka datse duk annurin fuskana.

"Ke kuwa Na'ima meye haka kike yi?, wai meye kika ɗauki aure ne, bautar ubangijinki ko kuma bautar wata ƙatuwar daban?. Ashe duk zantukan da nake ji gaske ne wai tare da facala malam Yusuf ya ajiye ki. Ta yaya zaku more amarcinku ga ɗakinki ga nata haba Na'ima har wanke-wanke kike mata?".
Da idanu nake bin ta har ta dasa aya, tana yatsina fuska kafin nace da ita wani abun. Habiba ta ɗaura da faɗin"Ai wallahi Anty Salma damma ba ki ji irin zancen da ake yi a gida ba, kowa tausayinta yake yi wallahi in kinji yanda su Goggo Jummai suke fassara wuyar zaman da facala ba za ki fara amincewa ba wallahi".

Sosai naji na tsinci zuciyata a wuya, wani miyau mai ɗaci yana game mini dukkan cikin bakina. Idanuna a ƙanƙance nake cewar"Ke Habiba dakata mini, bana son rainin banzan har wani tausayina ake ji to akan meye?, akan na girmama zaɓin su na son ganin na fitda miji, sama burina nayin karatu?, ko kuma akan na yarda zanyi zaman aure na zama aljannata?. Duk wanda ya saba jin tausayina bai burge ni ba ke kuma Salma kin bani mamaki".

Na ƙare zancen ina wurga musu harara, kowacce da nata.

"To abin kuma haka ya zama?, to Allah ya ba ki haƙuri ni daman sallama nazo yi miki jibi in sha Allah warhaka mun ɗaga daga garin nan, sai katsina".

"Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya".

A furta a gajarce don sun gama baƙanta mini rai, duk yanda suka so ja na da hira rasa samun kaina suka yi, har suka tafi nayi musu rakiya na dawo. Sai da na cika sati uku, Ummata, Hajiya Babba da ragowar matan gidanmu suka zo ganin ɗakin, maƙalƙalewa Ummata nayi cike da kewar ta. Da wayar Maman Hanan na ƙira malam Yusuf na shaida masa zuwansu nan take yazo suka gaisa da suka tashi tafiya ya ɗauki dubu biyar ya ba wa Hajiya su hau abin hawa.
Tun kafin su fice daga gida, suka fara zancen da suka je gidan Balkisu ba haka Aminu yayi musu sha tara na arziki yayi musu kuma ya bai da su gida a motarsa. Duk da naji amma ban nuna musu ba nayi musu rakiya zaure inda Umma ta ƙara yi mini wani nasihar bayan ta haɗe mu tare da malam Yusuf, godiya muka yi mata kana suka tafi.

Raba girki muka yi, bisa shawarar Anty Binta da ba'a tsallake dukkan zancenta matuƙar ta furta. Tare mazajenmu suke cefenan girki kowa kowacce tayi wannan bibiyu kafin ƴar uwarta ta amsa.

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

____________________________________

Page 1⃣3⃣

Abu ɗaya da na lura dashi, shine daga yaya Auwal har malam Yusuf izuwa autar su Mahmud. Basa tsallake maganar da duk Anty Binta tayi, wataƙil saboda kasancewar su marayu ita ce kamar uwa a gare su. Soyayyata ga karatun wanda babu algus a cikinsa, haka bai hana ni yin biyayyar aure ba

Zaune muke a tsakar gida tare da Maman Hanan, dafe goshinta tayi tana faɗin"wash".
Na kallota cike da kulawa, ina gyara zaman Hanan saman cinyata da nake yi mata tsifa nace"lafiya kuwa?".

"Wallahi ciwon kan nan, ya matsa min in ga gobe dole naje asibiti ganin likita".

Sai da na murmusa kana na kuma faɗin"To Anty ko dai ƙanwa ko ƙani Hanan za ta zamu?".
Ita ma sai da ta dara sosai, kafin ta tsagaita ta ce dani"Na'ima kena ke dai kawai ayi sha'ani, wataƙil har sai kinyi ƴaƴa biyu Hanan ba'a yi mata ƙani ba".
Saurin taran numfashinta nayi ba tare da ta dire zancen da ta ɗauko ba"Hans Anty ke kuwa meyasa kika ce haka?".
Sai da ta sauƙe wata ajiyar zuciya mai ƙarfi da sautinsa ya sauƙa a masarrafon jina kana ta shiga cewar"Na'ima kin gani nan shekarata uku da aure, watana goma cif a gidan a gidan Auwal na haifo Hanan. Yanzu shekaranta ɗaya da wata nni ta goshi biyu, tun bayan na yayeta bamu ƙara haɗa shimfiɗa da Auwal ba, tun ina haƙuri da jarumtar jurewa ta hanyar in bai neme ni ba nima bazan kai kaina gare shi ba, har na gaza kama kaina ni da kaina zan kai kokena gare shi amma yayi biris da ni tamkar ayi wa dutse dundu. Na kai ƙori gida aka haɗa mu domin jin ko bashi da lafiya ne amma ya tabbatar mana da lafiyarsa gas wai kawai yana son bada tazara ne tsakanin Hanan da wanda zamu haifa nan gaba".

Sai da ta numfasa, tann tare ƙwallar da suka wadaci idaniyarta kana ta ɗaura da"Tun ina ƙarama mahaifina ya rasu, na taso ne da mahaifiya kawai duk kunyar dake tsakanin matan hausawa da sirikansu duk Innata ta jingine wannan gefe gudu, domin da kanta take karɓo wa Auwal taimako domin har yanzu taƙi yarda cewar lafiya ƙalau yake. Burinta a ko yaushe bai wuce ta ganni ɗakin miji ba, abinda take guje min bai wuce zawarci ba".

Jin nayi duk wani gaɓar jikina yayi sanyi laƙwas, zuffan suna keto mini daga dukkan mafitar gashin dake cikin jikina. Tabɗijam tashin hankali wai mai takaba ta taka gawa har yanzu akwai ashe akwai irin Maman Hanan a bayan ƙasa?, matan da zasu jure wannan abun duk don farantawa iyayensu?.

Zancen da ta ɗaura dashi ya sani figigi na dawo duniyar zahiri daga na tunani da na fara zurmawa cikinsa.
"Mamaki kike yi ko Na'ima?".

Kaina na ɗaga mata don sam na gaza samun abinda zan ce da ita, murmushin nan da akewa laƙabi da kafi kuka ciwo, raɗaɗi gami da ƙuna ta sakar mini kafin tace"ai ke dai kawai ayi sha'ani, amma wallahi kinji rantsuwa kenan ko akwai MATAN AREWA da yawa cikin wannan halin, wanda idan ba macen da imani ya kafo a zuciyarta ba sai ta kaucewa hanyar Allah ta faɗa bin maza alhalin da igiyoyin aure ɗauke a kanta".
"Amma Anty tabbas akwai cutarwa a cikin wannan lamarin, kuma ya kamata a duba halin da za ki shiga shekara gudu ba kwana ɗaya ko sati ɗaya bane, ya dace ayiwa tufkan hancin tun kafin kwaɓar tayi ruwa".

Taƙaitaccen murmushi kawai ta sakar mini, ba tare da tace dani uffan ba, sai ma ƙoƙarin kaucewa zancen nawan ta da soma yi ta ƙarfi da yaji. Ganin kamar bata so ya sani yiwa bakina linzami sai dai bani da iko akan zuciyata da zan iya hana ta tinane tinane game da lamarin, ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe ina kallon Maman Hanan ta gefen ido, tabbas sai yau na ƙara gaskaka wannan zancen mai cike da hikima akan zuciyar mace ta kan iya ɗauka da jure damuwar da namiji ba zai iya ɗaukarta ba. Ta kan jure komai ta cigaba da gudanar da rayuwarta tamkar dai-dai take, ahalin ita kaɗai ta san sukar da zuciyarta take yi mata.

Har daren ranar bani da wani cikakken walwala ballle kuzarina ya sauƙa a jikina, dawowar malam Yusuf daga masallaci isha'i ya sanya ni sakin murmushin dole ina yi masa sannu da zuwa murmushin shima ya maido mini dashi kana ya zauna na zauna kusa ƙafafunsa ina cire masa safar ƙafarsa.

"Amarya kuma uwargida kin tare gaba kin tare baya, daga ke babu wata".

Ire-iren kalaman Malam Yusuf kenan, da duk sanda ya ambata mini su suke sanya ni nishaɗi da ƙololuwar farin ciki. Sai dai ban taɓa yaudaran kaina akan cewar ni ce ɗaya babu ƙarin ba balle har na zari dala babu gammo na ɗaurawa kaina damuwa haka siddan. Nasan romon soyayya ce a yanzu take kwasarsa kuma take yin tasiri a cikin jikinsa, duk da kuma na tanadin dukkan sirrin biyayyan da zai ja da ran kwanakin aurena.
"Tashi ki zauna".
Yace da ni dai-dai sanda na kammala cire masa safan dake ƙafansa, kusa dashi nayi wa kaina mazauni yace na rufe idona banyi musu ba na rufe idona kirif naji ya kamo hannuna ya ɗaura mino wata leda.

Cikin zaƙuwa da son ganewa idanuna menene, na buɗe idona na fara buɗe ledar kwalin waya xe sabuwa gal nayi tozali da ita sai sheƙi take yi, duk da bata cika girma ba domin ƴar ɗanne ce tecno. Amma sosai naji daɗin kyautar karo na farko kenan da na mallaki waya ta kaina a rayuwata.

"Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi ya azurta ka da halal ya ƙara nisanta ka da haramun komai ƙanƙantansa, nagode yayana".

Sai da ya ɗan tsuke fuskarsa yace"nikam in ce dai na hana faɗin wannan yayan ko?".

Murmushi na saka ina duƙar da kaina ƙasa,tun bayan auren mu na tsiri ce masa yaya, tun baya amsa mini inna faɗa har ya fara amsa sunan.

"To ka fara amsa addu'ar mana".

"Ai na amsa a raina ji ne kawai kaji yi ba".

Ɗan shagwaɓe fuska nayi hakan ya sanya shi saurin amsa yana murmushi, tare da jawo ni kusa dashi sallamar yaya Auwal da kunnuwana suka jiyo mini ya sanya ni faɗuwar gaba, hirar mu ta ɗazu da Maman Hanan ya dawo mini cikin kunyata. Taɓo kafaɗana da Yaya yayi ya sanya ni dawowa hayyacina, ya ɗage mini ido ɗaya"lafiya kuwa?".
"Lafiya ƙalau".

Na fara ina daidai nutsuwa a ƙoƙarin tabbatar masa da zancen nawan na babu komai, sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya ɗauke kansa muka cigaba da hira, nan nake shigar masa da kokena akan son zuwa gida ganin Ummata da Anty Zakiyya, ya bani tabbacin sai na cika shekara cif a ɗakin miji kana naje gida a al'adar hausa haka nan abin yake.
Zumɓuro baki gaba nayi, har muka fita muka ci abinci muka dawo. Da damuwar akan halin da auren yaya Auwal da Maman Hanan yake ciki na kwana maƙale a raina sam na gaza samun nutsuwa mussamman da muka raya darenmu tare da yaya sai wani tausayinta ya kuma yi wa ƙalbina lulluɓi.

Safiyar ranar daga masallacin sallan asubahi Yaya ya zarce islamiyyar safe, bai dawo ba sai ƙarfe tara tarbansa nayi cikin kulawa kamar yanda na saba na kai masa ruwa banɗaki ya shiga yayi wanka kafin ya fito na fiddo masa da kayan da zai sa na ajiye masa akan gado da duk wani abunda zai iya buƙata na komo falo na zauna, ina latsa wayata da har da sim a cikinta lambar Ummata, Abba da yaya Majid da na haddace su na saka a wayar da burin ina saka kati su zan ƙira mu gaisa.
Fitowar Yaya ya sanya ni ajiye ta gefe guda ina masa sannu da fitowa abincin karin kumallo na gabatar masa domin na kari basa ci tare da yaya Auwal kasancewar shi ɗan kasuwa ne da wuri yake fita.
Tare da Hanan suka fita izuwa makaranta, bayan nayi masa rakiya zaure ina binsa da addu'ar kariya. Shigowar Anty Binta ya sanya shi dakatawa daga fitar sai da suka gaisa kana ya fita, muka dawo ciki tare da ita na shimfiɗa mana tabarma a tsakar gidan duk muka gaishe ta tare da Maman Hanan.
Ta amsa idanunta suna kaina tar, tayi riƙo da haɓarta sai da ta kalle ni tsaf kana tace"Na'ima rakiyar mijin ne za ki

Please Login or Register in order to submit comment