Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita komai ba illa Maman Hanan tayi ƙarfin halin furta"Haba Anty a matsayinki na babba mai kamace ki ba furta irin wannan kalamin, ita ƙaddara babu abinda yake tare ta ko hana wanzuwanta cikinmu babu wanda yayi zaton hakan zata kasance, kiyi mata fatan alkhairi domin kamar yanda shi Yusuf ɗin yake jininki ita ma fa haka take abar so ce ga ƴan uwant..".
Katse ta Anty Binta tayi ba tare da dire zancen da ta ɗauko ba, sai ta kalle ta tsaf kana tace"Dalla rufa min baki ke har me kika sani game da zaman duniya, yaushe ma Lamin ta haife ki aka yi auran nakin?. Ko don kinyi haihuwar wuri kafin ki rufa shekara?, Anyi min fin ƙarfi akan lamarin nan amma ga fili ga mai doki ina nan ina zaune za'a je a dawo wata matsalar zata kunno kai a dalilin wannan boko yayin da zan zame kaina na sulale kamar kifi babu wanda zai sani".

Kamar kazar da aka kwararawa tafashashshen ruwan zafi haka na jawo jikina na matso gabanta, cikin rawar jiki da na murya nake cewar"Anty dan Allah kiyi haƙuri bani da wani mungun nufi ko wani mummunan ƙuduri game da wannan lamarin, Allah ne shaida ta sannan shi ya san abinda yake ɓoye cikin raina shi kaɗai zai iya yi mini adalci. Ban tirsasa Yusuf akan wannan batun ba hasalima shi ya ƙara bani ƙarfin gwiwa da ban sama goyan bayansa tabbas babu yanda na iya dole na haƙura, ina roƙonki da ki bini da fatan alkhairi da addu'ar samun nasara in sha Allah zan kare mutumcin kaina da igiyoyin auren da suke kaina".
Miƙewa tayi tsam! haɗi da cewar"Ai yi mu gani in tusa zata huta wuta". Tana gama furta hakan ta ja ƙafafunta ta fice daga gidan rai a matuƙar ɓace babu shiri nayi wani kuka ya turniƙe ni na kuwa sake shi da matuƙar ƙarfi Maman Hanan tana aikin lallshina tare da bani baki. Cikin sarƙafewar harshe nake cewar"Anty na fara karaya, na gaza gano inda maganganunta suka dosa tana tinanin ba zan iya riƙe kaina ba kenan?, Wallahi bana ɗaya daga cikin irin waɗannan matan Anty ki yarda da ni". Na ƙare cikin matsananciyar kuka lallashina ta cigaba dani har na tsagaita da kukan kamin ta ce"Na'ima dukkan nasara bata samu sai an fuskanci ƙalubale masu tarin yawa, duk wanda kika gani a tudun nasara tabbas ya wuce bigiren tudu da gangare masu wuyar tsallakewa don haka kar da ki sare. In sha Allah wataran za ki cika burinki".
Shuru kawai nayi ba don maganganunta sun sama gurbin zama a cikin kaina ba, tashi nayi naje na wanko fuskana na gama wasu aikace aikace na duk jikina babu kuzari har yaaya Yusuf ya dawo daga islamiyyar safe ban gama warewa ba sai dai ban bayyana masa komai ba duk yanda ya kai ga tambayar dalilin canzuwar yanayin nawan cewa dashi nayi kaina ne ke yi mini ciwo, haka nan na roƙo maman Hanan akan bana so Abban Hanan ko Yaaya Yusuf su san da zuwan Anty Bintan bana son ta dalilina su sama rabuwar kawuna. Da ƙyar na zaunar dashi yaci abinci don sam baya son cin abinci, sai da yaci yafi bayan yace dani na shirya da ya dawo zamu je gidanmu.

Ranar na wuni jikina gabaɗaya babu kuzari, lura da haka ya sanya Maman Hanan bata fito ko'ina ba ko gidan maɓan Anwar ɗin da bata fashin zuwa bata je ba, har Yaaya Yusuf ya dawo muka shiryo zamu tafi na leƙa ɗakinta nayi mata sallama ta rako ni har ƙofar ɗakin tana faɗin"Da na san da fitar ai da tun daren jiya, na tambayi Abban Hanan izni munje tare".
Murmushi na ƙaƙalo na ce da ita"Babu komai Anty wataran sai muje".
Sai da muka tsaya a hanya yaaya ya saiwa su Abba kankana da su abarba Hajiya Babba da su Ummata kowa nasu daban sai dariya nake yi masa haka nan muka wuce gidan, a ƙofar gidan ya faka. Kallo shi nayi ina ɗage masa ido ɗaya ganin ya tsaya a ƙofar gidan"Lafiya Yaaya?, ka tsaya a nan ba zaka shigo bane?".

"Ki dai shiga kiyi wa yaya Majid magana ya fito yayi min jagora wajen shiga wajen su Abba".
Dariyar dole zancen nasan suka sanya ni"Lalle Yaaya wannan kunyar nakan sai kace wata mace, ai yanzu an zama ɗaya nan fa gidanku ne to meye sai anyi maka wani jagoranci kuma?". Na ƙare zancen har da ƴar shagwaɓata, murmushi yayi kamin ya ce"Haka ne kam su Abba iyayena a gare ni, tunda suka haifo min macen ƙwarai kamar ki".
Murmushin jin daɗi naji ina rausayar da kai, na wuce gaba yana biye dani ɗakin yaya Majid rufe yake an danna masa makulli don haka sashin Hajiya Babba muka fara shiga ta tarbe mu cikin fara'a da matuƙar jin daɗi tsabar murnar ganin mu har rasa inda zata ajiye mu tayi kamar zata maida mu cikinta.
Mun daɗe a wajenta har sai da Baba ƙarami ya shigo muka gaisa, na miƙe izuwa sashinmu da mamakina na tarar da tsakar gidan kamar anyi shara domin babu kowa daga matan har ƴaƴansu.
Ɗakin Ummata na nufa kaina tsaye, na iske ta da wasu mata biyu ganina ya sanya ta sallaman su a gaggauce. Matsowa jikinta nayi na gaishe ta a ladabce ta amsa mini tana bina da kallo a ƙoƙarin son karantar yanayin fuskana. Katse kallon nayi ta hanyar faɗin"Umma ina Anty Zakiyya fa, tun shigowata ban ganta ba?".

"Na aike ta gidan Asabe karɓo min saƙo, amma na tabbatar duk inda take yanzu tana kusa da gida, yaushe kika zo ke ɗaya ce ko da mijin nakin?".

"Mun ɗan daɗe a sashin Hajiya Babba muka zauna, tare muke".
Kanta ta ɗaga ta ce"Lafiya ko?, don naji zuwan nakun yau a bakin Babanku sai dai bai sanar dani dalili ba".
Ƙululu naci cikina ya bada ƙara, sai da na musguta na sanarwa Ummata komai cikin kuka na ƙare zancen ina faɗa mata abunda ya faru safiyar yau furcin da Anty Binta ta jefa mini akan nazo na raba mata kan ƴan-uwa.
Jawo ni jikinta tayi cikin sigar lallashi take cewar"kiyi haƙuri Na'ima yanzu kuka ba shine mafita ba, tabbatar mata da saɓanin tinaninta a game dake za ki yi ta hanyar kame kanki bisa wannan damar da kika samu nayin wannan kararun. Na'ima na hore ki da ki riƙe mutuncin kanki da na aurenki har ki tsinka yarda da mijinki yake dashi a kanki, zan yi fushi dake a duk lokacin da wani ab....".

Saurin rufe mata baki nayi, ina jijjiga mata kaina"Umma kar ki ƙarisa don Allah, in sha Allah zan tsare mutumcina ba zaku same ni da aikata wani mummunan abun ba ku yarda da irin tarbiyan da kuka bani ko hakan ma ba zai barni na kauce hanya ba".

"Haka ne Na'ima, Allah ya ba ki sa'a yasa a fara cikin nasara".

A sanyaye na amsa da kalmar amin, kafin Yaya Majid ya ɗago labulen ɗakin yana shaida mana su Abba suna neman mu ni da Umma, miƙewa muka yi muka biyo bayansa iske matan gidan namun nayi suna zazzaune duk nabi na gaishe su suka amsa mini babu yabo babu fallasa.
Sashin su Abba muka nufa, Hajiya Babba da su Abba, yaya Majid, Goggo Jummai da kuma Yaaya Yusuf muka tarar zaune.
Zama muka yi kafin Abba yayi gyaran murya ta soma faɗin"Na'ima mijinki yazo mana da maganar komawarki makaranta, bamu da ikon hana ki domin a yanzu addini ya fififta ikonsa akan namu. Jan kunne zan miki tare da gargaɗi Na'ima ki riƙe mutuncin kanki ki sani wannan damar kin same ta ta silar yardar mijinki kar kiyi wani abunda zai rusa wannan yarda. Allah ya ba ki nasara".
Sosai jikina yayi sanyi na amsa da amin can ƙasan maƙoshina, haka Baba da Baba ƙarami ma suka ɗaura da nasu nasihan kafin Hajiya Babba da Goggo Jummai ma suka yi nasu. Sosai duk nasihohin nasun suka ratsa jijiyoyin jikina, sunyi mini fatan alkhairi sosai. Muka fito nayi mamakin yaɗuwar zancen tsakanin matan gidanmu.



MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 1⃣9⃣


Sai da muka yi sallan asr, a gidan Ummata ta bani abinci da ruwan sha na kai wa yaya Yusuf da suke tare da yaya Majid a sashin Hajiya babba. Na kai musu na dawo na tarar da Anty Zakiyya ta dawo Umma sai faɗan daɗewa da tayi take yi mata tana bata haƙuri da faɗin cewar taje ta iske baaba Asaben ne kwance babu lafiya shine tayi mata wasu ƴan aikace aikace.
Sai da na sanya baki Umma ta lafa, domin sanannen abu ne bata ƙaunar ta aike mutum yaje ya share waje yayi zamansa kamar an aiki bawa garinsu.
Zaman hira muka kafa da Anty Zakiyya na labarta mata komai. Iska ta furzar daga bakinta kana ta ce dani"Na'ima tabbas na taya ki murnar kasancewar wannan abun, amma kina ganin kamar wannan fushin Anty Bintan ba zai shafi zamanki da Yusuf ba?".
Cire leɓɓana nayi da ƙarfi sosai, na gaza samun amsar da zan bata domin kaf! tinanina ya ƙare. Ban kai ga cimma samun amsar ba ta katse ni ta hanyar ɗaurawa da faɗin"Shawaran da zan ba ki shine ki dade da addu'a babu dare babu rana, ki kai kukanki ga mahaliccinki ya ba ki sa'a cikin wannan lamarin".

"In sha Allah". Na furta cikin sanyin jiki da na murya hira ta fara jana dashi har na ɗan saki jikina cikin hirar take labarta mini cewar jiya Abasiya a gida ta kwana safiyar yau su Abba suka kaɗa ƙeyarta ta koma gidan Aminu. Riƙe haɓa nayi cike da zallan mamakin da ya bayyana ƙarara a bisa fuskana na ce"Me yayi zafi kuwa haka?".
"A to kinsa Daada bata fiye son lamarin ƴaƴanta yana fita ba, don da ta zo ma ko su Abba bata sanar ba Anty Hasina ta aika aka ƙira mata a son ransu su kaɗai su rufe maganar babu wanda yaji, sai kuma Goggo Jummai tayi tozali ta ita, ta kuwa hau yi musu bararara har dai zancen ya bazu. Wai taga saƙo a cikin wayar Sagirun an turo masa shine ta tada hankalinta tayi masa rashin ta ido shi kuwa ya mammake ta ya kuwa ɗebo ƙafarta ta zo gida".

"Tirgashi! ita kuwa Abasiya akan wannan har zata rashin hankali da zuwa gida, kamar bata san yanayin gidan ba daga aurenta ta fara zuwa gida da sunan matsala salon ayi ta yi da ita ana yanaɗiɗi".
"Ke dai bari ai kuwa dai sai dai kar a kuma, don wannan ya afku".
Shigowar Hanifa tana shaida mini wai Hajiya tana ƙirana ya sanya mu kallon kallo ga junanmu ni da Anty Zakiyya. Miƙewa nayi na biyo bayanta, muka yi kiciɓus da Umma ta tambaye ni inda zani na shaida mata tace naje na dawo don su yaya Majid suna waje suna jirana.
A uwar ɗanta na iske Hajiya zaune bisa bakin gadon ƙarfenta ƙiran zamanin da, na zauna akan ledar dake malale a tsakar ɗakin na ce"Gani Hajiya an ce kina nema na".
Musgutawa tayi tana naɗe hannayenta waje guda kafin ta furta"Na'ima daman na ƙira ki ne akan wani zancen da naji yana yawo cikin gidan nan, wai mijinki ya amince miki za ki koma makarantar boko iyayenku maza ma duk sun ba ki goyan baya".
Shuru ya biyo bayan maganarta ta ƙarshe, na rasa gano inda maganganun natan suka dosa. Sai da ta ɗan zame daga zaman da tayi ta kuma cewar"Na san Binta ƴar su Yusuf mai gidanki da daɗewa nayi mata farin sani ciki da waje, a da can ƙawata ce na ƙut da ƙut halayyanta ya sanya ni janye jikina daga gare ta. Amma ko aurena na fari ita tayi min babbar ƙawa dawowa na daga saudiyya muka raba gari da ita, Binta shu'umar mace ce ta ajin ƙarshe wacce idan ta ƙwallafa rai akan abu to babu abinda yake dakatar da ita sai ta cimma burinta ko da kuwa zata haucewa hanyar Allah, na sama labarin cewar bata amince da wannan karatun da za ki koma ba a bakin mijin nakin yana sanar da Majid har yanda ya shawo kanta, a yanda na san Binta ba za ta taɓa sakar miki mara kiyi fitsari ba sannan ki bar murna don karenki ya kama zomo bar ganin Na'ima an yi mata fin ƙarfi ta amince na tabbatar da walakin goro a miya taja da baya ne ba don ta gaza ba sai don ƙara yin wani sabon shirin".
Dam-dam ƙirjina ya bada sautin ɗas ɗas ɗas, kafin na zame na zauna dirsham a ƙasa tallafe da kuncina sam na gaza furta komai har sai da ta dafa kafaɗata ta furta mini abinda ya ɗan sanya ni jin sausaucin wutar raɗaɗin dake ruruwa cikin zuciyar dake kwance ƙasan ƙirjina.
"Ba na gaya miki hakan bane don ki tashi hankalinki, ko kuma don na tarwatsa ƙwarin gwiwan da kike dashi akan lamarin nan. Na sanar dake haka ne domin ki shiryawa komowar Binta gare ki daga ke har mijinki za ta iya aikata komai akan wannan ƴan uwan natan ba, babu abinda zai gagare ta aikatawa wajen ta karkato da hankulansu sunyi mata biyayya ko da ba'a son rayukan su ba, ki sanar da Ummanki ita ta taya ki da addu'ar Allah ya tserar dake daga kaidin Binta".
Sosai dukkan wasu gaɓoɓin dake jikina suka yi sanyi laƙwas, tamkar wacce aka bi dukkan sassan jikinta aka sassara da adda, cikin ƙarfin hali na cira kaina tare da jefa ƙwayoyin idanuna cikin na Hajiya na fizgo numfashina kafin na sama sararin faɗin"Na gode Hajiya tabbas kin sanar dani babban lamari a lokacin da ya dace, sai dai kaina ya kulle menene zai sanya ta aikata dukkan wannan abun?".
Sai da ta saki wani gajeren murmushi kana ta ce"Na'ima har yanzu ke yarinya ce ba ki gama sanin me rayuwar duniya ta ƙunsa ba balle kisan inda ta dosa, Binta ta wuce dukkan saninki sannan akan ƴan-uwanta babu abinda baza ta iya aikatawa a da babu wanda yayi tinanin cewar zata bar su har su kulla mace balle a kai ga yin aure har su tara iyali bata yarda da kowa ba akan wannan ƴan-uwan natan matuƙar kuwa mutum ya raɓe su to daga sannan zata sanya ido sosai akan sa".
Shuru nayi ina nazarin zantukanta da har yanzun suke yi mini amsa kuwa cikin masarrafun jina, tabbas zantukanta suna kan turba musamman da nayi la'akari da yanda take juya komai na cikin gidan ba ma kamar sha'anin Yaya Auwal da maman Hanan, autan su Mahmud kuwa ban taɓa ganinta sai sau ɗaya da yaya Yusuf ya nuna mini shi a hoto domin yana can sudan yana karatu ko bikinmu ma bai zo ba. Tabbas akwai ayar tambaya kan wannan batun, sallamar Nurain shi ya katse mini hanzari na dawo duniyar zahiri daga na tunanin da nayi nisan kiwo cikinsa.
"Anty Na'ima wai ki fito inji yaya Majid".
Iya abinda ya ce kenan, ya ruga a guje ya fice yana baran lemon dake hannunsa da yaya Yusuf ya kawo. Cikin ladabi da girmama ƙaunar Hajiya gare ni nayi mata kyakykyawan godiya da addu'o'in gama da duniya lami lafiya sumul, ƙwarai na hangi tsagauron tausayina cikin idanunta da hakan kaɗai ya ishe ni samun tabbaci akan duk zancen ta ta faɗi mini game da Anty Bintan. Har ƙofar ɗakinta ta biyo ni tana yi mini fatan alkhairi cikin karatun da zan fara ganin mu a haka shi ya jawo hankulan sauran matan gidanmu kamar mayen ƙarfe izuwa gare ni, suna taɓe baki sallama nayi musu azalzalan da yaya Majid yake ta fama yi mini akan na fito mu tafi shi ya hana ni samun damar zama da Ummata balle har mu tattauna wannan gaggarumar matsalar da ta gusar mini da dukkan nutsuwa kwanciyar hankalina.

Har muka isa gida bana fahimtar hirar da yaya Yusuf yake yi mini, wanda bana raba ɗayan biyu na murnar samun cikakken goyan bayan mahaifana ne don yanda bakinsa ya kasa rufuwa fara'a tamkar gonar auduga. Ban mu iske maman Hanan ba domin ƙofarta har an saƙala kwaɗo Hanan kuwa ta tafi islamiyya. Ranar gabaɗaya yaya Yusuf bai je islamiyya ba ruwan wanka na kai masa yayi wanka sannan nima na shiga, tare dashi muka ɗan kimtsa gida sannan na fara haramar ɗaura mana girkin dare, tana daka mini albasa da attaruhu.
"Za'a yi jarabawar tantance malamai in sha Allah wani sati, sannan wanda suka cancanta za'ayi musu ƙari girma a taya mu da addu'a".
Sai da na jinjina kaina na ce"Masha Allah, Allah ya taimaka Allah yayi jagora. Tabbas zaka tsallake dukkan wannan jarabawan domin nasan nawan gwani ne ko a cikin aji". Murmushin jin daɗin addu'ar tawan yayi ya amsa da"Amin amin ya Allah ƴar aljanna, in sha Allah da zaran zangon karatun ya ƙare za'a fara ɗaukar sabbin ɗalibai kema za ki sama gurbin karatu na yanke shawaran kawai zan nema miki a karatan da nake koyarwa tunda haɗe yake da sakandiri gabaɗaya".
Duk da nasan hakan bai wuce shiri na Anty Binta, amsawa nayi da"Allah ya nuna mana lokacin, hakan ma yayi dai-dai sai muna tafiyarmu tare. Na kula da abina sosai".
Murmushin nan nasa mai ɗaukar hankali yayi ya ce"Wai ina maman Hanan ne taje haka?".
"Wallahi ban sa ni ba, don ba ta ce mini zata je wani wajen ba".
Bai ƙara cewa komai ba, har muka kammala haɗa komai na miyar ɗanyen kuɓewa, ganin lokaci yayi ya sanya fita zuwa ɗauko Hanan daga islamiyya. Sai da aka ƙwala ƙiran sallan magrib maman Hanan ta dawo, lokaci har yaya Yusuf ya ɗauko Hanan na wanke ta taci abinci tana ɗakina tana wasa da wayata. Bata bani damar tambayarta inda take ba don tana amsa sannu da dawowan da nayi mata tayi wuf ta shige ɗakinta.
Daren ranar bacci ya gagari idanuna sai faman juyi nake maganganun Hajiya sun hana ni sakat, tinani da fargaba suka zamto abokai na. Gashi ban sama damar tattauna da kowa ba game da lamarin, ba zan tunkari yaya Yusuf da zancen ba domin hakan kamar rage mini daraja zai yi a idanunta wataƙil yayi tinanin kamar so nake na haɗa kaina da Anty Binta a fannin matsayi, duk da kuwa zuciyata tana bani kyakykyawan tabbaci akan zai fahimce ni sai dai ta ina ma zan fara sanar dashi wannan zancen mai nauyin furtawa akan harshe?.
Miriginawa nayi da nufin gyaran kwanciyana, riƙon yaya Yusuf yayi min gam gam ya hanani samun damar aiwatar da hakan. Duk duhun ɗakin bai hana ni hango fuskarsa ba take naji wasu hawayen sun wadaci idaniya zantukan Anty Binta na safiyar yau yana yi mini kururuwa a cikin kunnuwana, ƙirjina yayi bugun da ya tilasta mini runtse idaniyata da hakan ya ba wa hawayen da nake maƙale damar kwaranya. Cikin raina ina addu'ar Allah ya bani ikon kiyaye yaƙini da yardar yaya Yusuf a kaina kar na bashi kunya, sanadin wannan karatun na ƙara zamtowa abar alfahari gare shi da iyayena gabaɗaya.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

__________________________________________

Page 2⃣0⃣

Kwana biyu a tsakani Anty Binta ta ɗauke ƙafarta daga zuwa gidan. Addu'a na duƙufa dashi babu dare babu rana duk sanyi baya hana ni tsayiwar dare.
Rigimar da ban san mafarinta ba ta kunno kai tsakanin maman Hanan da yaya Auwal tun sanyin safiya suke mayarwa junansu zazzafan martanin da suka sanya mu fitowa tamkar waɗanda suka ji ihun gobara, kafin yaya Yusuf ya fara ƙwanƙwasa musu ƙofar ɗakin a hankali. Basu buɗe ba balle mu sanya rai ga tunanin zasu amsa ragowar zancen yake yi illa kukan Hanan da yake ƙara ratsowa ta cikin ɗakin.
Mun daɗe tsaye a wajen kafin yaya Auwal ya buɗe ƙofar rai a matuƙar ɓace ya ɗauki hanyar ficewa daga gidan na lura tsabar ɓacin ran da suka yiwa idanunsa lulluɓi shi ya hana shi samun zarafin kallon mu tsaye a wajen. Cikin sauri yaya Yusuf ya rufa masa yana ƙwala ƙiran sunansa, sanƙararrun ƙafafuna da naji su tamkar basa cikin jikina naja su izuwa ɗakin maman Hanan tana durƙushe can ƙuriyar ɗakin na hange ta Hanan kuwa na yashe tsakiyar ɗakin tana rusar kuka kamar matan mamaci.

Da sarsarfa na isa ga maman Hanan sai dai tun kafin na iso gare ta ta ɗaga mini hannu cikin ƙaragin kukan ta furta mini"Dan Allah Na'ima ki fita, ki fita bana son ganin kowa ki bar ni na roƙe kiiii".
Ta ƙarishe zancen ƙarshen natan tana kuma tuntsirewa da matsanancin kuka tare da jan kalman. Kamar gunkin india da aka sassaƙa na kasa gaba balle baya zuciyata tana bugawa da sauri da sauri Hanan na ɗauka na fice daga ɗakin wasu siraran hawayen suna gangaro mini ta gefen da gefen idanuna.
Da ƙyar na lallashe ta tayi shuru, ta kwanta bacci bayan nayi mata wanka tisa ta gaba nayi na zagba taguwi iwa wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta.

MATAN AREWA, matan yankina kuma al'ummata tabbas suna cikin halin walagigi. Matsalar aure babu wacce basa fuskanta sannan babu mai fahimtar matsalar domin ta zamto kukan zucin da mai shi ne kaɗai yake jin raɗaɗin. Haƙuri shine kalmar da ta sama gurbin zama a harshunan iyaye da yawa ba tare da la'akarin ƙuncin da ƴaƴansu suke fuskanta a gidajen mazajensu ba. Cikin matsalolin auren da yawa ba'a taɓa sauraron ɓangaren macen sai dai ayi ta furta mata kalmar haƙuri.
Figitit na dawo izuwa duniyar zahiri daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, sakamakon jin fitowar maman Hanan tana ƙoƙarin dannawa ƙofarta ɗab makulli, a zabure na fito ma damƙe hannunta tare da ƙwace makulli da jakar kayan dake hannunta.

"Anty dan girman Allah kiyi haƙuri kar kije ko'ina dan Allah".
Na furta ina yi mata magiya bata kula ni ba ganin hakan ya sa ni nayi wuf naje na rufe ƙofar gidan. Na dawo ina bata haƙuri bayan na ja hannunta izuwa ɗakina.

Kallon fuskarta da ta kumbura sumtum nayi duk halittun fuskar suna sauya na ce"Anti komai na duniya sai an sanya haƙuri ake kaiwa ga cimma gaci, ban san abinda ya haɗa ku ba amma dan Allah na roƙe da ki zauna a warware komai".
Idanannun idanunta ta watsa su akan fuskana"Na'ima a zauna a warware komai fa kika ce?, waye zai warware wannan ƙullin?, babu wacce zata zo domin hakan face Anty Binta wacce ita ce musabbabin faruwar komai babu abinda za'a warware sai dai ma a ƙara jagula komai. Wallahi Na'ima nayi dana sanin auran Auwal nayi dana sani haɗa zuri'a dashi nayi nadamar kasancewa matarsa, nayi nadama kasancewar uban ƴata. wai shin har sai yaushe ne MATAN AREWA zasu rabu da wannan tarin matsalolin?, wallahi Allah kaɗai yasan adadin matan dake fuskantar matsala irin nawa a gidajen aurensu. Babu inda zan kai matsalarta mahaifina ya rasu tun ina da ƙarancin shekaru ni ce ƙarama gidanmu ina da yayu mata biyu, mahaifiyarmu tsufa ya kama ta ta yanda komai sai anyi mata ba zan iya je mata da matsalolina ba domin in nayi hakan kamar na ƙara sauƙaƙa mata hanyar tafiya izuwa kushewa ne".
Iska mai zafi na furzar daga bakina ina zame hannuwana biyu da na tallafe kuncin dasu, ina jin kalaman maman Hanan suna dukan kwakwalwata kwatankwacin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe. Riƙo hannunta nayi dukka na sanya su cikin nawa kafin nayi ƙarfin halin danne ruwar ƙwallar da suka ciko koramar idaniyata na ce da ita"Anty tabbas nima na fahimci irin zaman haƙurin da kike yi da abban Hanan, amma rayuwar ƴarki za ki duba wane irim tarbiya zata taso dashi bayan kinyi fatali da ita yanzun kin tafi, tun ina ƙarama nake ganin Ummata tana sulhunta irin wannan matsalolin amma yanzu na roƙe ki da ki zauna muka dawowar shi tukunan".
"Na'ima bazan iya ba domin Auwal ya nuna bana buƙatar zama da ni, Allaj ne mafi sani Auwal baya biya mini dukkanin buƙatar aure abin nasan tamkar da gayya yake yi, wani abin takaicin komai zai faru tsakanin mu zai ya shaidawa Anty Binta".

Haƙuri na ɗaura bata har ta ɗan lafa ba, ɗakin na barta kwance na tattare tsakar gidan sannan na ɗaura mana girki cikin rashin kuzari na gama komai kafin na ɗauki wayata na danna ƙiran yaya Yusuf har ƙiran ya katse bai ɗaga ba na ƙara ƙira a karo na biyu shima babu amsa.

Please Login or Register in order to submit comment