Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da ƙyar na lallaɓa maman Hanan ta sama ta tura abincin da na girka mana cikinta ta kwanta saboda ciwon kan da ta labarta mini cewar ya adaddabe. Wunin ranar haka na ƙarar dashi tamkar wacce aka zarewa laka komai cikin sanyin jiki nake yinsa. Sai bayan sallan asr yaya Yusuf ya shigo gidan a kallo ɗayan da nayi masa na hango tsantsan tashin hankali da ya kara ɓoyiwa sai da ya bayyana ƙarara a bisa fuskarsa.
Tabarma na shimfiɗa mana domin maman Hanan na kwance a ɗakina, na kawo masa ruwa a nutse na ce"Yaya lafiya kuwa?".
Kafe ni yayi da idanu ya cije leɓɓansa na ƙasa kafin ya furto mini abinda suk hautsina ƴaƴan hanjin cikina har suka kusa sanya ni tuntsirewa duk da a zaune nake.
"Na'ima meyasa kika ɓoye min zuwan Anty Binta gidan nan?".

Ƙululu cikina ya bada sauti, sai da na numfasa na ce"Ban ɓoye maka da wani nufi ba, sai dai iyaka bana son ƙara tashar maka da hankali a wannan lokacin musamman irn furcin da ta furta masu firgitarwa".
Shuru ya biyo bayan zancen nawan na ƙarshe, sai da ya ɗau lokaci kafin ya ce"Yau mun je wajenta a kan matsalar yaya Auwal da matarsa ta kuma ƙara jaddada min komai".
Cafko hannuna yayi tare da sausauta amon muryarsa yana faɗin"Na'ima, Anty Binta tayi fushi dani tare da furta min cewar duk abinda kika jangwalo sanadin wannan bokon kar na fara tunkarar ta na kuma mance ina da wata ƴar uwa kamar ta. Ba zan hana ki wannan damar ba ko dan tabbatarwa mutane masu rangwamen tinani irin na Anty Binta cewar ba kowacce mace bace watsatstsiya don tayi boko, roƙona gare ki shine ki kula mini da amanata a duk inda kika shiga dan Allah".
Runtse idanuna nayi ina jin kalaman nasan suma yi mini amsa kowa cikin kunnuwana, sai da na jawo numfashina da yake garkewa a ƙirji kafin na sama zarafin cewar"In sha Allah ba zan baka kunya ba mijina".

Kamo hannuna yayi cikin nasa yana murzawa a hankali, tare da labarta mini musabbabin faruwar matsalar yaya Auwal da maman Hanan akan dai abinda ko wannan mu ya sa ni rashin biyar buƙata daga yaya Auwal ta tunkare shi domin kamo bakin zaren ya ƙira Anty Binta ya zazzage mata lamarin da ya ƙara turniƙe zuciyar maman Hanan. A cewar ta ya kamata a tsakaninmu su sama sirri ta yanda wasu abubuwan indai ba matuƙar tirkewa ya yi ba babu wanda zai ji su rufe su birne a tsakanin su, amma shi duk abinda ya faru har wanda Annabi ya haramta faɗen shi ga kowa watau abinda ya wakana bayan sun rufe ƙofa sai ya fayyacewa Anty Binta.
Take naji wani maiƙon zuffa sun tsatstsafo mini saman goshina, ɓoyayyayan ajiyan zuciya na sauƙe ina ƙara jinjina girman lamarin a zuciyata. Kamar yanda ya saba dawowa yau ma hakan yaya Auwal ya dawo bayan sallan isha'i tare suka yi abincin da yaya Yusuf ina daga ɗaka ina jiyo yanda yake tausar zuciya da ba shi haƙuri.
Washe garin ranar bayan Hanan da yaya Yusuf sun wuce makaranta, ƴan-uwan maman Hanan biyu da naji a tashin farko ta ƙira su da Anti Sadiya da Zuwaira suka ziyarce mu, cike da girmamawa na gaishe su bayan na baje musu tabarma a filin tsakar gidan na gabatar musu da ruwa suka jiƙa maƙoshansu.
Furzo balbalin masifar da Anti Zuwaira ta fara yi ga maman Hanan, shi ya hana ni miƙewa na basu waje da nake da niyya saboda tsawar ta tan da suka ratsa ni.

"Habiba ban sam yaushe kika lalace har haka?, wai ke sai yaushe ne za ki yi hankali ki san cewar annabi ya faƙu?. Auren nakin kike so ki ɗuntule ki dawo gida zawarci ko meye?. To wallahi tun wuri ki dawo cikin hayyacinki in ma wasu ne suke ziga ki to ki dawo gwadaben gaskiya, domin idan ba ki godewa rahamar Allah za ki godewa azabarsa, shin ke kaɗai ce macce da ta fara haɗuwa da matsala a gidan aure?, ko kuma a kanki za'a ƙare balle ki tada hankali kina ƙoƙarin zaran dala babu damo. Ki samarwa kan ki mafita da ke da mijinki".
Ɓarkewa da maman Hanan da tayi da wani kuka mai matuƙar sauti ya sanya jikina ƙara sanyaya, da ƙyar ta iya saisaita numfashinta da yake fita da wani sautin gu gu gu kafin ta zama zarafin furta"Dan Allah Anti ku fahimci ne wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, ni kaɗai nasan irin ƙunci da nake ciki a zamana da Auwal ina cutuwa. Ko sau ɗaya ne ku saurara daga gare ni ba wai duk abinda yake ya kimtsa muku ki hau ku zauna ba".
Ta garke zance tana ƙara ƙarfafa sautin kukan natan, jikina a sanyaye na miƙe ina tare hawayen da suka ciko mini koramar idaniyata na basu wajen na wuce ɗakina.
Jagwaf na faɗa kan gado cike da tausayin matan al'ummata, runtse idanuna nayi ina jin tashin sautin kukan maman Hanan yana ratsawa har cikin ƙoƙuwar kaina.
Sai bayan sallan zuhr suka tafi, yaya Yusuf ya ƙira ni a waya yana shaida mini cewar wata tafiyar gaggawa ta tazo masa ya ƙira wayar yaya Auwal baya ɗauka kuma bashi da ishashshen caji wayarsa zata iya mutuwa a ko yaushe don haka na sanar da maman Hanan ta ƙira yaje ya ɗauko Hanan daga makaranta.
Ban yi sanya ba na sanar da ita, da mamakina ta ja dogon tsaki tana komar da kanta ga matashin da take kwance.
A cewar ta tunda ya fice da safiyar yau ba tare ya san da zamanta cikin gidan ba, ba ta ga dalilin da zai sanya ta ɗaukar waya ta ƙira shi ba da ƙyar na lallaɓa ta amma ta turje sai ma miƙo mini wayar da tayi na ƙira shi bai ɗaga ba nayi na tura masa saƙo. Ban san makarantar ba maman Hanan kuwa ina da yaƙinin ba zata je ba domin ta hau dokin zuciya.
Shuru shuru babu Hanan, wayar yaya Yusuf kuwa a kashe take, haka na yaya Auwal ma daga bisa da na sake gwadawa a kashe. Tun ban mayar da hankali kan lamarin ba har hankalina ya soma tashi ganin yamma na ƙoƙarin kawo kai.

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 2⃣1⃣


Kasa zaune nayi balle tsaye sam na nema nutsuwata na rasa domin ya yi nisan kiwo da gangar jikina, mussamman da yaya Auwal ya daina ɗaga ƙiran da nake jeranta kafin daga bisani na ƙira naji ta a kashe kit, masa a kai a kai wayar yaya Yusuf kuwa a kashe.

Ganin maman Hanan ta nuna halin ko in kula game da lamarin sai ma furta mini tayi"Ki fa kwantar da hankali wataƙil ma yanzu tana tare da ita, ya ɗauko ta kawai haɗa ido ne dani baya ƙauna shiyasa ya kai ta kasuwar".
Yanda ta tsaro maganar tamkar akan idonta hakan ya wakana, lafawa nayi da ƙiran wayarsa ta san da bana gajiya da sauraron labarta mini cewar a kashe take.
Ƙarfe biyar saura yaya Yusuf ya dawo, ƙirƙiro fara'a nayi na dasa ta a kan fuskana ina yi masa sannu da zuwa kafin maman Hanan da ke zaune kusa na ita ma tayi masa amsawa yayi yana zama kan kujerar da na ɗauko masa.
"Ya gidan shuru ina Hanan?".

"Wallahi har yanzu basu dawo ba, wataƙil sai ya taso daga kasuwa tukunna".
Ɗan ware idonsa ya yi kafin yace"Su na tare kenan da yaya Auwaln?".

"Haka muke tinani".
Zumbur ya miƙe ya na faɗin"bari naje makarantar na duba, don bana tinanin ya ɗauko ta gashi wayata babu caji balle na ƙira malaminsu na tambaye su".
Bai jira na cewar mu ba ya fice a hanzarce, da kallo muka raka shi maman Hanan tana taɓe baki kafin ta miƙe ta shige ɗakinta. Har nayi sallan magrib babu yaya Yusuf babu alamar sa haka nan ma yaya Auwal izuwa yanzu har maman Hanan hankalinta ya soma tashi haka nan ma maman Anwar da ta shigo a lokacin.
Wasa wasa abin ya fara ƙoƙarin zarce tinaninmu domin har aka yi sallan isha'i babu su balle masu kama dasu, zugum zugum muka zabga tagumi kamar gidan makoki.
Ina jin wayata tana ruri nayi azaman jawo ta, a tinanina ko yaya Yusuf ne ganin sunan Salma ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sa ni ajiye ta gefe guda domin bani da sukunin da zan iya ɗaga ƙiranta a halin da nake ciki.
Kukan da maman Hanan ta tuntsire dashi ya sanya dakan lugudan dukan tara taran da zuciyar dake kwance ƙasan ƙirjina take yi, ina jin sautin kukan natan yana dukan kwakwalwata kwatankwacin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe. Tsaye nake tamkar gunki na gaza isa gare ta balle furta mata kalmar lallashi. Maman Anwar ne ce ƙoƙarin taushar zuciyarta.
Kukan take yi da iya ƙarfin bil haƙƙi da dukkan gaskiyarta, basu dawo ba sai ƙarfe goma sha ɗaya saura yanayin da suka shigo kaɗai ya isa ƙara tarwatsar mana da ragowar kuzari da ƙwarin gwiwarmu.
Cikin harɗewar harshe da mazarin da jikina yake tamkar ana jona mini lantarki nake furta"Yaya ina Hanan ɗin?, dan Allah ku sanar da mu kar ku barmu cikin ruɗa ni".

Dafe da kansa yaya Auwal ya shige ɗaki, ba tare da ya ce uffan ba. Dafe bangon yaya Yusuf ya yi saboda karkarwar da jikinsa yake kamar mace, saurin isa gabansa nayi kafin na sama zarafin cewa dashi wani abun, maman Hanan ta durƙushe a gabansa kan gwiwoyinta ta zube tare da haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo cikin hawayen da suke sintiri a dandamalin fuskarta ta furta"Dan Allah Yusuf ka sanar dani inda ƴata take, ka sanar dani zuciyata gab take da bugawa wallahi. Auwal ba zai dubi halin da nake ciki balle har na sama lallashi ya sanar da ni ba".
Sosai duk tausayinta ya garke a rayukan mu, ɗago ta nayi ta kwantar da kanta bisa kafaɗata tana rero kukan natan da nake jin sautin sa har cikin kunyata.
"Ki kwantar da hankalinki, in sha Allah babu wani abun da zai faru yanzu dai addu'arku ta fi buƙata".

Cike da kallon mamaki duk muke bin sa da na jiyamu, cike da rashin fahimtar inda zancen nasan suka dosa balle gano ba ki zaren. Zabura maman Hanan tayi kamar mai shafar iskokai ta ce"Yusuf ka sanar dani inda ƴata take wallahi tun kafin na haɗiye raina dan Allah na roƙe, ina Auwal ya kai min ɗiya?".
Sai da ya furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa kana ya ce"kiyi haƙuri Anti in sha Allah Hanan duk inda take tana cikin aminici kuma Allah zai bayyana ta a gare mu cikin gaggawa".

"Innalillahi wa inna ailaihir raji'un! me kake son faɗa Yusuf?, garkuwa aka yi da Hanan ɗin innalillahi".
Furcin maman Anwar kenan da suka ƙara hargitsa gidan, da ƙyar muka riƙe maman Hanan da take fizga da shirin ficewa daga gidan da zummar fita nemo Hanan da take faɗi. Sai da yaya Yusuf ya yi mata tofin wasu addu'o'in kafin ta lafa, cikin hawayen da suke ziraro mata take cewar"Gidanmu zan tafi, ba zan iya cigaba da zama da Auwal ba bazan ƙara awa ɗaya cikin gidan nan ba".

"Kiyi haƙuri Habiba in sha Allah, Allah zai bayyana ta. Ina za ki je cikin wannan baƙin daren?, sai dai ki kwana gidana muga abinda gobe zata haifar".
Karo na farko da na fara taka gidan maman Anwar, raka maman Hanan domin ta dage akan baza ta kwana a gidan ba. Jikina babu ƙwari na dawp gidan ina tsayar da idona akan ƙofar ɗakin maman Hanan da yaya Auwal ya shiga ya rufe kansa ba tare da ya kuma leƙowa waje ba, balle tsuma baki cikin zantukan da ake yi.
Ɗaki na nufa na iske yay Yusuf zaune ya haɗa kai da gwiwa kusa dashi na zauna ina tattaro nutsuwa da jarumtata waje guda kafin na ce"yaaya garin yaya lamarin nan ya faru?, bayan har saƙo na tura masa akan yaje ɗauko ta"
Numfasawa yayi tare da lumshe idanunsa, jijiyoyin kansa suka fito ruɗu ruɗu a goshinsa. Tashi nayi da sauri naje na ɗebo masa ruwa na kawo masa ya sha, riƙo hannunsa nayi na sanya cikin nawa ina murzawa a hankali a ƙoƙarin samar masa da nutsuwarsa.
A nutse na furta"Yaya dan Allah ka sama nutsuwa, ka sanar dani yanda lamarin nan ya faru".

"Yaya Auwal bai je ɗauko Hanan daga makaranta ba, duk da kuwa ya tabbatar min da yaga saƙon amma tunanin cewar maman Hanan ɗin ce ya sanya shi sharewa. Bata tare dashi kamar yanda kuka yi tinani domin shima bai san bata dawo gida ba, sai yanzun da naje makarantar suka tabbatar min da cewar wani saurayi yazo ɗaukarta kuma har mahaifinta ya ƙira a waya domin samun mai gadin ya bashi damar ɗaukarta, yaya Auwal ya tabbatar min cewar bai aka kowa ɗaukar ta ba, mun shigar da case ɗin hukuma sunce mu dawo gida in sha Allah zasu yi iya ƙoƙarinsu kan lamarin".

Sosai jikina yayi sanyi laƙwas, ina jin dukkan gaɓoɓin jikina tamkar ana bi sassara mini su. Ƙwalla suka ciko koramar idanuna zuciyata tana bugawa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata ɓalle allon ƙirjin ta fito waje ko zan ji sallama daga ambaliyar ruwar tashin hankalin dake gudana cikin ƙalbina.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Shi kaɗai na sama damar furtawa kafin haƙwarana suka datse harshena. Wai sai yaushe ne wannan masifar dake addabar mutanen AREWA na garkuwa da mutane zai zo ƙarshe?, wai sai yaushe ne talakan AREWA zai yi rayuwar ƴanci kamar kowa?, wai sai yaushe ne tsaro zai wadaci AREWA?. Sai yaushe zamu fara kwana rufe da idaniya biyu domin matsanar tsaron dake addabar mu ta hana damar hakan. Sai yaushe ne walwala zai wanzo a rayuwar talakan AREWACIN ƙasata?, sai yaushe ne hawayen talaka zai daina kwaranya tamkar burɗaɗɗan famfo?.

Ina kwanciya hankali ga yankin da ƙaddarar irin wacce ta dirarwa maman Hanan, ina nutsuwa ga yankin da uwa zata kwana ba tare da ta san inda ɗiyarta take ba, tana raye ko tana mace, shin taci abinci ko a'a to ma waye zai bata?.
Figitit na dawo duniyar zahari daga tinanin da nayi zurfi a cikinsa, sakamakon muryar yaya Yusuf da suka yiwa masarrafan jina diran mikiya.
"Rashin ɗaga ƙira da share saƙon maman Hanan da yaya Auwal yayi shine mafarin komai, duk da ita ƙaddarar bawa baya taɓa guje mata. Fatan mu dai yanzu Allah ya bayyana mana ita cikin aminci amma dole ne a zaunar da yaya Auwal a nusar dashi kuskurensa don bai kyauta ba kwatakwata a cikin wannan abun".

Cikin matuƙar ɓacin rai ya ƙare maganar, wanda har fuskarsa sai da ta bayyanar da hakan, ban iya cewa dashi komai don bana jin ko nayi ƙoƙarin aikata hakan zan sama haɗin kai daga bakina. Ranar yanda muka ga dare haka muka ga rana salloli kuwa munyi babu adadi muna miƙa kokenmu ga sarkin sammai da ƙassai mai juya yanayin zafi izuwa sanyi.
Har garin Allah ya waye na kasa yakice takaicin yaya Auwal da ya bari matsalar su da maman Hanan har ta shafi ƴar su ɗaya tilo da sanadin hakan ya yi silar jefa rayuwarta cikin hatsari da tsaka mai wuya.

Tabbas na ƙara jinjina haƙuri da juriyar da yawan matan arewa da suke yi cikin gidajen aurensu, tun asubar fari ba muka bayyana waje yayin da yay Yusuf da yaya Auwal suka koma ofishin ƴan sanda ni kuwa na faɗa gidan maman Anwar ƙiran da Salma ta uzura mini dashi ya sanya ni kashe wayar gabaɗaya na ajiye ta. Magashiyyan na iske maman Hanan tamkar wacce ta shekara tana jinyar sai sumbatu take yi tana kamo sunan Hanan zugum zugum muka zauna har sanda Anti Sadiya da Anti Zuwaira suka iso duk suna ƙara jajanta lamarin dukkan su danne maman Hanan suke da maganar komawa gidan da take tsaye a kai. Har dare babu labarin Hanan bayan isha'i kuwa aka wuce da maman Hanan asibiti sakamakon yankar jiki da tayi ta faɗi babu numfashi, ni da Anti Sadiya muka kwana a wajenta. Washe garin ranar sai ga matan gidan mu har da Ummata da Hajiya Babba suka duba jikin maman Hanan tare da jajanta lamarin.
Da mamakina har lokacin Anti Binta bata tako ƙafarta tazo gida ko asibitin ba, yaya Yusuf ke shaida mini mai gadin makarantar mana yana hannun ƴan sanda sun shaida musu inda masu garkuwa ne suka ɗauke ta to zasu ƙira su buƙaci kuɗin fansa amma har wannan lokacin basu ƙira ba.
Cikin wannan tashin hankalin da ban taɓa cin karo da makamancinsa ba, muka share kwanaki huɗu ana safiyar na biyar ɗin bayan sauƙowa daga sallan asubahi mutane suka farga da ramin gudanar ruwan da aka tona ba'a gama aikin shi ba an rufe ne kawai an barshi, bisa warin da yake tashi a wajen aka buɗe shi tozali da wani buhu aka yi da aka buɗe shi akan sinci gawar Hanan ciki.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un mun ga tashin hankali fiye da yanda kwakwalwa kan iya jimirin ɗauka.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 2⃣2⃣

A ruɗe aka wuce da ita asibiti, sakamakon ganuwa da aka yi da sauran numfashi tare da sanƙararren gangar jikinta, yaɗuwar labarin da suka iske kunnuwan mahaifiyarta duk da kuwa yanda aka so rufa maganar duba da yanayin halin jinyar da take cikin sa sai ta tsinci zancen, lamarin da ya ƙara ta'azzawa tare da ƙara girma da munin halin da take ciki don dole ma'aikatan asibitin suka yi mata alluran bacci. Ko da aka kawo ta asibiti ma'aikatan asibitin nunawa suka yi akan ba zasu iya taɓa ta balle har su yi wani yunƙuri sai an zo da jami'an tsaro duk makiya da nusar dasu halin da take ciki na matakai biyu ko tayi lafiya ko ta sauƙa a lahar hakan bai daɗa su da ƙasa ba balle yayi nasarar tsirgar da tausayi a zuƙatan dake cikinsu da basu da maraba da duwatsu.
Yaya Yusuf ne ya tafi domin zuwa da ma'aikacin tsoro, yaya Auwal kam zaune yake rungume da Hanan da take fitar da numfashi a wahalce hawaye ne suke sintiri bisa dandamalin fuskarsa tamkar mace domin sam ya gaza jurar ganin ɗiyarsa tilo cikin wannan halin.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!, wannan wani irin masifa ce haka?, wani irin ƙazamar al'umma ce muke rayuwa a ciki da tausayin da jinƙan bayin Allah suka yi ƙaranci. Zaluci ya yawaita a bayan ƙasa Allah wadaran wannan al'umma, ceto rayukan mutanen ma yanzu ya zama aiki dubi halin da yarinyar nan take ciki amma a barta yashe wai sai an taho da jami'in tsaro".

Furcin Anti Sadiya kenan cikin ƙaragi da koken kukan da ta runtsire dashi mai matuƙar sautin da ya karaɗe yalwataccen filin farfajiyar asibitin da baya rabo da shige da fice jama'a. Daskarewa nayi a wajen sam na gaza taɓukawa kaina komai babu shiri juwa suka shammacin ƙafafuna da suke rawa tare da nuna butulcewar su ga ɗaukar nauyin gangar jikina.j Idona ƙar akan Hanan da duk kamamninta suka sauya har izuwa lokacin da yaya Yusuf ya dawo da polices ɗin da case ɗin ɓacewar Hanan yake hannun, suna tafe su na shaidawa yaya Yusuf kuskuren da suka tafka ba rashin sanar dasu tun farkon ganin ta.

Sai a sannan aka fara ba wa Hanan taimakon gaggawa, tunin likitoti suka rufu a kanta tare da iya ƙoƙarin ganin sun dai dai fitar numfashinta. Suka bada tabbacin cewar fyaɗe aka yi mata cikin rashin adalci.

"Hanan Hanan Hanan, dan Allah ku kai ni na ga ƴata".

Furcin da ya fara fitowa daga bakin maman Hanan kenan a sa'ilin da ta buɗe ido bayan tabbatacin da likitoti suka bamu zuciyarta ta kumbura ta kuma kai matakin gajiya da aiki da tana cikin hatsarin bugawa a ko yaushe.

Anti Sadiya da Anti Zuwaira ne suka isa gare ta tare da kwantar mata da hankali ta hanyar sanar da ita Hanan na nan a raye. Da ido kawai nake bin ta ina jin nauyin da ƙirjina yayi mini tamkar anyi mini dutsi mai nauyin gaske, raina cike da tausayin MATAN AREWA da fyaɗe ya zamto tamkar wutar daji ruwan daren da bai tsaye ke matashin saurayi dake kan ganiyar ƙuruciya ba balle tsohon da ya ba wa shekaru hamsin baya.
Babu budurwa balle yarinyar da bata san kanta ba, an yiwa tsohuwa fyaɗe an tare ƴan mata a hanyar dawowa daga makaranto anyi musu fyaɗe, waɗanda suke killace cikin gida ma basu tsira daga wannan masifar ba balle waɗanda suka ke yawon titi da sunan talla. wai shin sai yaushe wannan abun zai zo ƙarshe?.

Tambayar da na jefawa kaina kenan, da na gaza cimma amsarta har izuwa lokacin da ihun da maman Hanan ta rangaɗa suka suyi wa ƙofofin kunnuwana sallama.
Yanka jiki tayi ta faɗi baya a sume bayan ta gama faɗin"Wallahi idan Hanan ta rasu, na gama aure da Auwal har abadan abada".

Ihun ƙwalawa likitan ƙiran da Anti Sadiya tayi, shi ya sanya su shigowa a hanzarce. Da sauri na fice daga ɗakin ina tare ƙwallar da suka ciko koramar idaniyata, na samu wani wajen can na zauna naci kukana son rayina. Sai a sa'ilin naji sanyi a raina ko yaya na rufe idon Hanan nake hangowa wanke cikin ciwo wani rashin imani ne yake tasiri a zuƙatan al'umma da babu tausayi balle tsoron sanin ubangiji yana kallon bawa ko ina ya ɓoye kansa za'a hakkewa ƙanƙanuwar yarinyar kamar Hanan.
Sai da aka ƙwala ƙiran sallan zuhr na tashi daga wajen, domin gabatar da salla kiciɓus nayi da yaya Yusuf da yake shirin fitowa shima ja da baya nayi don sosai yanayin da nayi tozali dashi suka ƙara jefa ni cikin tsoro da firgici.

Idanunsa sun ƙara ƙanƙancewa tare da rikiɗewa izuwa launin ja sosai, yanda ya datse leɓɓena sai da nayi tinanin ya ɓuya su don da matuƙar ƙarfi yayi hakan. Babu shiri naji ya fizgo hannuna tare da ja na cikin sauri muka bar wajen bai tsaya ko inna ba sai bayan ɗakunan da ake kwantar da majintan masu lalurar hawan jini kamar yanda idanuna suka hango mini rubutu a wajen.
Kujerun da suke shirye a wajen na ginin siminti, ya saki hannuna ya zauna yana dafe goshinsa danne tsoron dake taso mini nayi na zauna kusa dashi tare da aza hannuna bisa nashi dake dafe da goshinsa.

"Yaya Yusuf menene?, dan Allah ka samarwa kanka nutsuwa ta hanyar ƙarfafa kanka akan wannan lamarin shima yaya Auwaln ɗin duk a ɗimauce yake. Wanda wannan wani hali ne da duk wani uban zai faɗa yayin da wannan ƙaddarar ta faɗawa ƴars..".
Yanda ya ɗago yana kafe da idanunsa, suka tilasta mini haɗiye raguwar zancen ba tare da na furzo su wajen ba. Damƙar da yayi wa hannayena suka ƙara girman tsoron dake raina cikin wata iriyar hargitsatstsiyar murya yake faɗin"Na'ima uba fa kika ce?, yaya Auwal bai cancanci amsa wannan sunan ba domin matsayin ne mai girmar da ba kowa yake amsa sunan ba. Har sai yaushe irin wannan matsalolin zasu kau a tsakanin ma'aurata?, Allah kaɗai ya san illolin da irin hakan yake haifarwa a tsakanin al'umma gabaɗaya. Allah ya ɗauki rayuwar Hanan shikenan kowannan su zai ya huta sunyi sanadiyar rayuwarta".
Ya ƙare zancen yana sakin hannayena. Ɗif abinda ke taimaka mini wajen yiwo sautikan zantukan mutane mabambamta ya daina nashin aikin, domin daga wannan kunnuwana basu kuma jiyo mini ko kalma ɗaya daga raguwar furcin da yaya Yusuf ya ɗaura dashi ba sai dai ganin bakinsa yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da cewar zancen ya ɗaura dashi.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".

A faɗi cikim raina da yake mini soyar da ta sanya ni dafe saitin ƙahon zuciyata da yake harbawa da sauti da sauti. Sunkuyar da kaina nayi da hakan ya ba wa ƙwallar da suka wadaci idaniyata damar tsiyaya. Daga ni har shi babu mai lallashin wani domin kowa mabambamtan tunani ne cushe cikin ransa bayan raɗaɗin rasuwar Hanan da yake ratsa mu, a nawa ɓangaren takaicin al'ummar da nake rayuwa a cikin su ne da basu da maraba da dabbobi saboda rangwamen hankali da rashin tasirin imanin a ƙirjinansu, na shi ɓangaren kuwa bana raba ɗayan biyu takaicin yaya Auwal ne ke nuƙurƙusan sa bisa yanda ya nuna halin ko'in kula har wannan lamarin ya faru duk da kuwa ƙaddara ta rigayi fata kuma bawa

Please Login or Register in order to submit comment