You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
nayi shi na kwnata lamau zazzaɓi mai zafi yana rufe ni ko yunwa bana ji balle sha'awar wani abu burina kawai yaya Yusuf ya dawo na amaryar masa da zantukan cikina sai goman daren ranar ya dawo.
Da masifa ya shigo kaina akan girkin da banyi ba, ban kula ba tsabar taƙaicin da ya turniƙe ni idona a runtse na ce dashi"wacece wanda na tarar daku tare?".
Sai da ya saki tsaki mai dogon zango kafin ya furta"wannan kuma ba abinda ya shafe ki ba ki fara bani amsar tambayar da nayi miki tukunna".
"Ya shafe ni tunda da mijina na ganta dole naji wacece ita".
Tsaki ya kuma ja a karo na biyu ya yi ficewarsa ya barni da sakin wani kukan mai ƙarfi, kullum ina tinanin ina tarin ilmin yaya Yusuf ya tafi ne?, wani irin nisa suka yi dashi da baya aiki dasu cikin lamuransa?. Wani balbalin kishin mijina yana mamaye ni ashe haka kaifin kishi yake? ko kuma nawa ne yazo daban da na sauran?.
Dole wata zuciyar ma ta jinshayi mata da yawa su aikata abinda zasu zo suna dana sani da cizon yatsa daga ƙarshe. A haka nayi jinyata na gama ba tare da wani kulawa ya shiga tsakaninmu ba. Har muka yi hutun zangon karatu wannan karon nayi na ɗaya. Bana bashin yin addu'ar da Umma ta bani amma babu abunda ya canja zani wani lokacin gabaɗaya sai naji auren ya fita a raina fit.
Har mun koma makaranta rannan ya ce Husna ta haɗa kayanta zata koma gidan. Bayan tafiyar su ina zaune tsakar gida ina sana'ata watau kuka da tinani, naga maman Hanan da Anti Sadiya sun shigo tunin naji wani sabon karsashi ya sauƙa mini na ruga na ƙamƙameta a jikin ina murnar dawowarta. Na taya su share ɗakinta fes kafin Anti Sadiya ta haɗe mu tayi mana nasiha mai ratsa jiki.
Farin cikin ganin maman Hanan ya mantar dani kwatan damuwata, har dare ina ɗakinta. Ina ta zolayan Yaya Auwal daga cewar za shi kano sai gashi ya dawo da matarsa ba tare da sanin kowa ba na rike haba ina jinjina maganar nan ta masu hikima tsakanin mata da miji tabbas sai Allah. Ita ma tayi mamakin ganin tara ya wuce yaya Yusuf bai dawo ba. Washe gari tun kafin na tashi maman Hanan ta gama komai naji daɗi sosai ko da na dawo daga makaranta na samu ta gama abinci gyara gidan kawai na taya ta dashi. Ta kallo ni tare da tambayar abinda ke damuna.
Na nuna mata ba komai, ina sakin ƙwallar da na gaza samun ikon tsayar dasu. Ta faɗa ni da faɗi"Na'ima sanar dani damuwarki in dai ba wanda bani da hurumin jinta bane".
Tirjan tirjan na kwashe komai na faɗa mata, tunda abokin kuka ba'a ɓoye masa mutuwa. Ta tausaya mini matuƙa kafin ta ce dani"Na'ima daman aure ya gaji haka, kowacce da salon nata ƙaddaran. Daman babu soyayyar da take dawwama sai dai ƙauna amma ki cigaba da addu'a komai yayi farko zai yi ƙarshe kiyi haƙuri".
Allah kaɗai yasan adadin MATAN AREWA da kalmar haƙurin nan tayi sanadiyar bugawa zuciyarsu, in dai wannan haƙurin da nake yi na zama da yaya Yusuf shine irin haƙuri da ake yiwa kowacce yarinya yayin bikinta nuni dashi, tabbas akwai wahalar ɗauka da barazanar bugawan zuciyoyi.
Dawowar maman Hanan ya sauƙaƙa min abubuwa da yawa, domin in zamu yi jarabawa bata bari na na ɗauki ko tsinke cewa take nayj karatu kawai. A sss two zan rubuta fefe, kamar yanda tsarin yake jamb muka fara yi na sama 230 nayi murna sosai haka nan ma iyayena, yaya Yusuf kam da takardan sakamakon da na ciro na nuna masa bata da maraba da takardan tsire a wajensa. Daren ranar ya turmushe ni ya kwaci haƙƙinsa kamar yanda yake mini kullum, na rasa ina tarin ilminsa na addini yayi ƙaura ya tafi. Duk da yaya Auwal ya zaunar damu domin jin matsalar mu Kalmar nan dai ta hakuri ya yi ta nanata a cewar sa wai tsananin son da Anty Bintan take yi musu yake saka wannan abun. A raina na ayyana har turo Husna da tayi ta kasa ta tsare shima duk a cikin son ne ko kuma da son kai zan fassara haka?.
A haka har muka kammala waec and neco. Tunda muka fara nake fama da zazzaɓi ga kasala wanda na danganta haka da gajiyar da nake kwasowa a makaranta. Ranar da muka gam jarabawa na tambayi yaya zuwa asibiti da ƙyar ya barni aka auna ni aka tabbatar da samuwar cikin sati shida a jikina, wani kukan tausayin kaina ya ɓalle mini da tausayin abinda ke cikina, ko da nazo na sanar da maman Hanan Murna tayi ta yi har da roƙona wai ina na haiho mace mu dinga kiran ta da Hanan.
Muna zaune yaya ya shigo fuskarsa kamar hadirin gabas, ya gajarce ya ce"Na'ima ina son magana dake". Ya shige ɗaki.
"Tashi ki bishi, ki nuna masa wannan sakamakon na tabbatar yau sai ya taka tsalle don murna, kuma ina ji a jikina shi zai kawo ƙarshen komai".
Ba don na gamsu da maganganunta na ɗauki takardan na bishi, yana tsaye a falo ya bani baya hannayensa naɗe a bayansa, a raunane na ce"Gani".
Ya wullo mini takardan hannunsa a fuskana, da maɗaukakiyar mamaki na furta"na menene?".
"Takardan saki ne, na sake ki saki uku Na'ima na sake ki bana ƙaunar cigaba da ganin fuskarki".
Babu shiri juwa suka shammaci ƙafafuna da suke rawa, na zube a ƙasa hawaye suna wanke mini fuska. Furcinsa suna mini amsa kuwa a kunnawa, runtse idanuna nayi ina addu'ar idan mafarki nake yi Allah yasa na farka domin wannan shine mummunan mafarki da na taɓa yi a rayuwata.
******** Alhamdulillahi book one has come to an end, ga masu buƙatar book two zaku iya yin payment akan n500 kacal i ensure you cewar ba zaku yi nadamar sayan littafin nan ba. Mutane goman da suka fara payment zasu biya n300 ne, dalilin dawowar maman Hanan gidan yaya Auwal, bayyanar makircin Anty Binta a fili, yanda rayuwa zata kasancewa Na'ima bayan mutuwar aurenta, halin da malam Yusuf zai shiga idan ya dawo hayyacinsa, menene makomar cikin dake jikinta, menene sirrin da Maman Hanan da Maman Anwar suke boyewa a tsakanin su?, and babban abunda zan taɓo shine yanda malaman makarantun gaba da sakandiri suke amfani da ɗalibansu domin wani cikar buri nasu, matan leccarori sai dai kuyi haƙuri don ba zan ɗaga ƙafa ba duk suna cikin book two. Ga masu buƙata you can contact me via this number 07038908713 sai na ji ku**********
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels