Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zancen na masu hikima"Nadama a ƙeya take".
Fitowar su Abba ya sani daidaita nutsuwana, duk na rusuna ina gaishe su suka amsa mini a taƙaice suna ficewa, kafin iyayen mu mata suma suka fito daga ɗakin suma suka fice Anty Kubra ce ƙarshe fitowa, daga duba ɗaya da nayi wa fuskarta na hango kumburi da canzuwar halittun fuskar. Ta gefena ta raɓa ta wuce hakan ya ba wa ajiyan numfashin da nake dakonsa damar sauƙa.

Kafin na cigaba da sharan da nake yi sai dana share ko'ina, Hajiya Babba bata fito ba, har na wanke banɗaki na shigo ɗakin natan bakina ɗauke da gajerar sallama. Amsa mini tayi tana daga kishingiɗe na zauna kusa da ita tare da yi mata sannu da hutawa ta amsa mini fuskarta tamkar gonar auduga.

"Hajiya ni kuwa ina son yi miki wata tambayar".

"Faɗi ina jinki Na'ima".

Musgutawa nayi ina lankwashe ƙafafuna waje guda, kana na ɗaura da cewar"Hajiya naga Anty Kubra ta fice tana kuka, gasu Abba ma duk sun fice rai a ɓaci. Dan Allah ki shiga maganar kar a raba wannan auren, a barta a ɗakinta kar ta fuskanci irin tsangwamar da Anty Zakiyya take fuskanta daga mutan gidan nan".
Sai da ta saki ƙatotuwar ajiyar zuciya kana tace"Na'ima kenan Na'ima baiwar Allah, duk abinda suke muku amma ke nufar ko wannen su kike yi da alkhairi. Lamarin Kubra babba ne ki taya ta da addu'a kawai kinji ko?".

A sanyaye na kaɗa mata kaina, tamkar maraniyar ƙadangariya kafin na kai ga cewa wani abun, ta tari numfashina da faɗin"Saura kwana nawa ne sauƙarku?".
Sai da nan dara don ƙa'ida ce, tunda aka tsayar da ranar yaye mu daga islamiyya. Dukkan safiyar duniya na shigo sashin Hajiya Babba sai ta tambaye ni adadin ragowar kwanakin da suke rage.

"Saura sati uku Hajiya kullum fa sai kin tambaya".

"To ai gwara inna tambaya ni da zan aurar da jikoki har huɗu sa'i guda ai dole na tambaya, domin mun tattauna da iyayenku cewar da zaran kunyi sauƙar nan ba zaku wuce watanni biyu a cikin gidan nan ba, za'a yi bikin ku su Bilki duk iyayensu mata sunce suna da samarin da suke zuwa wajen su. Ke ce dai daman za a jira".
Sosai naji raina yayi mini wani irin zafi, kalaman Hajiya Babba ba kaɗan ba suka daki raina, tare da samun nasarar turbuɗe mini hasken annurin fuskata na wunin wannan ranar gabaɗaya.

"Lafiya dai takwara kin barni sai magama nake ni ɗaya kimyi shuru, tunanin meye kike yi?".

Furzar da iska nayi daga bakina haɗi da cewar"Hajiya nida ko tsayayyen saurayi bana dashi, ayi nasu bikim kawai su da suke da samarin a hannu ni kuma idan Allah ya fito mini da miji koda na su Asma'u sai a haɗa ayi tare".
Sai da ta ƙare mini tanadin kallon tsaf, tamkar mai son gano wani gaskiyar dana ɓoye kana tace"Na'ima aure shine cikar darajan ko wacce mace, kimarki ba zai cika ba inba a same ki a wurare ukun nan ba, ko dai a tarar dake cikin gidan iyayenki, ko ɗakin mijinki ko kuma a iske ki a kabarinki, in sha Allahu kema Allah zai fito miki da miji kafin a kai ga lokacin sauƙar nakun".

"Uhmm".

Shine kawai abinda na iya furtawa a a gare ta, daga hakan ba kuma fahimtar ragowar zantukan da ta ɗaura dasu ba. Har izuwa sa'ilin da Nurain tazo wai Umma na ƙira ta, tare dashi kuma baro sashin Hajiyan Babban sai da muka zo ƙofar ɗakinsu sannan na saki hannunsa ya shige nima na nufi namu.
Wasu atamfofi Umma ta fiddo mini dasu, tace na kaiwa wata aminiyarta da ke nan bayan layi, nace wai saƙonta ne na wajen Hajiya Sa'adatu. Hijabina na saka na sundumi ledar zannuwan na fito dai-dai sanda Asma'u da Habiba suke fitowa cikin shirin zuwa makaranta kasancenwar su tasu ƙarfe sha biyu ake zuwa bayan ƴan firamari sun taso.
Kallon Asma'u nake yi nace"iyee har da hodarki a fuska, cau abinki".
Murmushi ta sakar mini tana juya mini idanunta, Habiba tayi caraf ta amshe zance"Ai Anty Na'ima wai ita a hakan malam Garba take so, banda wahalar da kai mutumin da aka ce yana da mata har ɗa ɗaya".
Haɓata na riƙo ina ƙara shan ruwan mamakin da zantukan Habiba suka shayar dani, kafin wata dariya ta suɓɓuce mini sai da nayi son rayina kafin nace"To kika sani ko zata je a ta biyu".
Harara ta watso mini ta finciko hannun Habiba suka fice fu, taɓe baki nayi cike da mamaki wai su ma sun san soyayya yaran nan da suke aji biyu a ƙaramar sakandiri.


A zaure na iske Daada da Anty Hasina da bansa sanda tazo gidan ba tsaye cirko cirko, tana tsegumta mata abinda ya faru da Anty Kubra, a cikin zancen nasun nake jin wai Habibun ya ɓoyewa iyayensa gaskiyar lamarin tare da ƙin sanar dasu ita ce ta turo sa daga beni, Baba ƙarami kuwa yace da zaran ya warke sakinta zai sanya Habibun yayi.

Tsumi tsumi na wuce ta gefensu, bayan nayi musu sannun da bata sama amsuwa ba. Gidan Aminiyar Ummata Baaba Asabe na nufa na kai mata saƙon da zan taho har da bani kuɗi wai na hau adaidaita, bayan ɗiyarta ta gama jeranta mini saƙon na gaishe mata da Anty Zakiyya.
Kamar wacce bata so haka nake tafiya a cikin layin nasu mai ƙarancin mutane, kamar daga sama naji an dafo ƙafaɗuna ta baya na juya a gaugauce cike da son ganin wanda yayi mini hakan. Wangale baki da hanci nayi ina bin Khadija Salisu ƴar ajinmu da muka gama ƙaramar makarantar sakandiri tare da ita, sanye cikin sabbin uniform dal, kalan ruwan samaniya ga safanta da tasha wanki tayi tas da ita.

"Khadija Salisu ke ce?".

Na faɗa har yanzu idanuna suna kanta, ta ɗan juya idonta kana ta amsa mini"Nice Na'ima ya kike ya su Bilki?"

"Duk lafiya ƙalau".

Tare muka fara jerawa muna tafe tana labarta mini, sunan sabuwar makarantar babbar sakandirin da ta jona kuma iyayenta sunce da zaran ta kammala makarantar koyan aikin asibiti za a kai ta.
Sosai nayi mata fatan alkhairi muka rabo akan zata kawo mini ziyara, duk saurin da nake yi har ƙafafuna suna harɗewa cikin zanina gani nake yi tamkar ba tafiya nake yi ba. Banda burin da ya ɗara na isa gida na amayarwa Ummata zantukan dake cikina.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Page0⃣3⃣

Kiciɓus nayi da Anty Hasina, tana fitowa daga sashin su Abba, Kasancewar nasu sashin ne a farko sai zaure tsakanin nasun da na Hajiya Babba, inda ɗakin yaya Majid yake. Namu sashin muda iyayen mu mata shine a ƙarshe.
Abasiya tana biye da ita goye da Abdul a gabanta. Hanya na basu suka wuce nayi wa Anty Hasina Allah ya maida ta gida lafiya, ban sa rai da samun amsa daga gare ta ba. Haka nan ban mayar da hankalina gare ta ba domin abinda dake kaina a wannan lokacin ya ɗara nata.

Umman su Salma da yake ranar girkin ta, ita na iske zaune a tsakar gidan, sai faman cika da batsewa take yi. Ban bi ta kanta ba nayi wucewa na izuwa ɗakin Ummata. Tsawan da Anty Zakiyya ta doka min ya sanya ni dai-daita nutsuwata lokaci guda, ina kai duba na gare ta.

"Ince dai lafiyar ki Na'ima?, za ki shigo ɗaki kamar an jefo ki ko sallama babu".
Sai a sa'ilin na tuna banyi sallama ba, na dafe goshina nace"Afuwan mantawa nayi".
Banta tanka mini ba don bata cika yawan zancen ba, illa ɗauke kanta da tayi daga gare ni. Hakan ya sani faɗin"Ina Umma?".

Ba tare da ta kallo ni ba tace"Tana sashin Hajiya Babba".
Bam tsaya sauraran ragowar zancen natan ba, na figi jiki zan fice ta cafko hannuna"Ina za ki?, ki jira ta ta dawo suna tattaunawa ne".
Ba don rayina yaso ba haka nan, na koma na zauna lokaci bayan lokaci Anty Zakiyya take kallo ni, ko kaɗan naƙi bata damar da zata jefa mini wata tambayar. Tufka da warwara kawai nake yi cikin raina waye zan fara tunkara da wannan zancen?, duk tunanin da yake kai kawo a ƙalbina Umma ita ce mutum ta farko da raina yafi samun nutsuwa akan na fayyace mata ƙudurina, nason komawa makaranta. Bayan ita kuwa wata zuciyar ta kitsa mini na sanarwa yaya Majid tun shi har karatun NCE ya kammala.

Shine mutum na farko da ya ciri tuta a gidan mu, yayi zurfi a boko saɓanin mu da dukkan mu madakatan mu ƙaramar sakandiri. Su Anty Halima da Anty Maimuna kam ma basu yi ba gabaɗaya, sai dai dukkan ƴan gidan mu mahaddatan al-ƙur'ani mai girma ne da kin sauƙe bakya wuce watanni biyu a gida za'a aurar dake.
A cewar su Abba ilmin boko da ƴaƴa maza ya dace, kuma domin su aka ƙirƙire shi ba ga ƴa mace ba. Don ita dukkan rayuwarta ƙanƙani ce ba kamar su ƴaƴa maza da suke cin gajiyar kansu kuma suke riƙe da gida ba. Wannan dalilin ya sanya bama wuce ƙaramar sakandiri a karatun zamani.

Sosai na sauƙe ajiyar zuciyar da ta jawo hankalin Anty Zakiyya izuwa gare ni, tace dani"Ke lafiyarki kuwa Na'ima?".
Har ga Allah banji daɗin katse mini, zancen da nake yi ni da zuciyata da tayi ba. Cuno baki nayi na miƙe na bar mata ɗakin nayi komawa ta ɗakin kwanan mu tare dasu Abasiya. Ina shiga na zube akan katifar mu ina karatan wasiƙar jaki a raina, ban sanda bacci yayi nasarar ɗebe ni sai ji nayi kamar a mafarki ana taɓo kafaɗata tare da ƙiran sunana.

A hankali na soma buɗe idona kafin na wangale su tar akan fuskar Bilkisu, ganin ta ya sanya ni sirkar da tsaki don har yanzu haushin ta nake ji akan furcin da tayi akan Anty Zakiyya. Kamar tasan zancen da nake yi a raina tace"Allah ya ba ki haƙuri, Ummanku ne tace a tada ki har lokacin salla zai ƙure".
Ban ce da ita ko kanzil ba, illa miƙewa da nayi na fice nayo alwala Umman su Salma ta baje kwanuka sai rabawa ƙananun yaran abincin take yi, tare da basu zazzafar kashedi akan duk wanda ya sanye miyarsa ba zata ƙara masa wani ba sai dai yaci haka.

Alwalan na kammala na dawo ɗaki, ba shimfiɗa salla na fuskanci alƙibla na tada sallah har na iddar Bilkisu tana zaune bakin katifar ta jawo bahon kayanta tana ta dube duben dana gaza gano abinda take son ganowa. Addu'ata na shafe da yake cike da roƙon Allah yasa ƙudurina ya samu ƙarɓuwa.

"Na'ima dan Allah, kiyi haƙuri akan abinda ya faru ɗazu kinji?".

Yatsina fuska nayi don daman nasan dole zata bani haƙuri, ko kaɗan bama iya ƙarar da wuni ɗaya ba tare da munyi faɗa da ita ba, amma kafin mu kwanta mun shirya.

"Ba komai amma kar ki ƙara yi mini irin hakan, bana so".

"In sha Allahu ba zai sake faruwa ba".

Ta faɗa tana ɗan murmusawa, na bita da kallo kafin nace"wai ke ɗin meye kika nema ne?".
Ta juya mini idanunta kamin tace"Kayan da zan saka da yamma nake dubawa, Zaidu ne zai zo na ma rasa wanin kayan zan sanya wallahi. Ki ara min wannan jar atamfar nakin mana ƴar-uwa".
Kallon uku saura kwata na watsa mata"Lalle ma kuwa, indai da kayana za ki zance, to tun wuri ki ƙira shi ki sanar dashi kar yazo don bazan bada ba ehe".

Marairaice murya tayi tare da ƙara lanƙwasata, ta shiga cewar"Haba Na'ima yanzu ba za ki taimaka min ba?, kinsan fa su Baba sunce kowacce daga cikin mu ta sanar da wanda yake zuwa wajenta, in da gaske yake yi ya turo iyayensa ana gama bikin sauƙar mu ayi komai a gama".
Bana ƙaunar cigaba da sauraran ragowar zantukanta, don haka na miƙe na ɗauko kayan na jefa mata nayi ficewa ta izuwa ɗakin Umma. Tana zaune kan sallaya tana lazimi na iske ta ganin hakan ya sa ni yiwa kaina mazauni kusa da ita, kuma shafa addu',ar tare sannan nayi mata bayyanin yanda muka yi da Baaba Asabe, na nuna mata kuɗin adaidaitar da ta bani.

Kafin na shiga inda in dan yanda zan fara bayyana zancen cikina, na lura duk idanunta a kaina suke don haka nayi sauri cewa"Umma ina wannan ƴar ajin namun, Khadija Salisu wacce take zuwa wajen su Bilkisu?".
Ɗaga kanta sama tayi alamar tana son tinano ta kafin tace"na gane ta aure tayi?".

Taɓe baki nayi nace"A'a Umma ita kam ai in gaya miki makaranta ta cigaba dashi, ɗazu da ina dawowa na haɗu da ita a hanya zata makaranta. Umma yasin kika ganta sai kin ƙara raka ta da wani kallon sha'awar".

"Masha Allah hakan ma yana da kyau".

Iya abinda Umma ta furta kenan a gajarce, da ya rage mini ƙwarin gwiwa na ɗan tsagaita. Kafin na aro jarumta da ƙarfin hali na yafawa kaina na ɗaura da cewar"Umma shine nima nace in munka yi sauƙan nan, kafin Allah ya fito mini da miji ko za ki yiwa su Abba magana, na ɗaura da karatun na na na na nawaan".

A rarrabe na ƙarishe zancen ƙarshe tamkar yaro mai koyar magana, sakamakon kallon ƙurillan da Umma take bina dashi tunda na fara maganar har na kai aya. Hakan ya sanya ni yin ƙasa da nawa ƙwayoyin idanun banyi gigin ɗagowa ba har izuwa lokacin da muryarta suka sauƙa a ƙofofin kunnuwana.

"Na'ima".

Ta ƙira sunana a kausashe, can ƙasan maƙoshina na amsa hakan ya bata damar ɗaurawa da"Kinfi kowa sanin al'adar gidan nan, da kuma yanda ake ɗabbakata babu yarinyar da take wuce matakin ƙaramar sakandiri a karatun boko, kuma ba za'a fara a kan ki ba. Ko ɗazu zancen da muka yi da Abban ku shine idan akwai wanda yake son ki, ki bashi damar fitowa ya gabatar da kansa kafin a kayi magana ta gemu da gemu, domin sauran ƴan uwanki duk nasu samarin zasu turo iyayen su cikin sati mai kamawa. Don haka kema ki nutsu kisan wanda za ki fitar a haɗa ku tare kamar yanda kuka taso a tare".

Ko garwashin dake ƙasan tukuban gashin tsire, bai kai zuciyata ɗaukan zafi ba a wannan lokacin. Idanuna suka ƙare sam na kasa sakin hawayen da suka cika mini kurmin idaniyata, har izuwa lokacin da naji hannayen Ummata a bisa nawa cikin taushin murya take cewa dani"Na'ima kinsan komai dake faruwa a cikin gidan nan, bakya buƙatar ƙarin bayani kina gani irin ƙalubale da gorin da nake fuskarta akan jinkirin auren da Zakiyya tayi, gashi yanzu har ana maganar auran ƙannanta amma ita har yanzu shuru. Yanzu kema idan kika ce makaranta za ki cigaba dashi sai duk ku taru ku zauna a gida, abin nema ya samu ace duk na hana ku aure ko meye?, burin kowacce uwa taga ƴarta a ɗakin mijinta nima akwai wannan burin a ƙirjina, Na'ima karki bijirewa umarnin mahaifanki, kar ki hana su sauƙe haƙƙinki dake kansu, na aurar dake. Sannan kar ki zamto ƴa ta farko da zata yi fatali da wannan al'adar".

Sosai maganganun Ummata suka kashe mini jiki, dukkan gaɓoɓina suka yi sanyi ƙalau. Tabbas nasan irin ruwar gorin da Anty Zakiyya take sha daga matan gidan mu da hakan har Umma yake shafa wasu lokutan, ba zan so dukkan mu mu zamto hakan ba, sai da na yarshe hawayen da ya fara gudu a fuskana ba tare da sani na ba, nace"Shikenan Umma in sha Allah bazan ƙara tayar da wannan maganar ba".

"Allah yayi miki albarka".

"Amin".

Na faɗa ina miƙewa na bar ɗakin, idanun mutanen dana iske a filin gidan daya dawo kaina, ya sanya ni saurin duƙar da kaina ina goge ragowar hawayen idona. Sanda na shiga ɗakin mu na iske su Bilkisu suna jira na muzo muci abinci nace bazan ci ba, na zube akan gado.

Har aka yi ƙiran sallan magrib na kasa tsinana komai, zuwa bayan isha'i masu samarin da zasu zo musu zance suka fara shiri Bilkisu, Salma da Abasiya duk suka fice suka barni ni ɗaya kwal a ɗakin. Da hakan ya bani damar cin kukana babu bai dakatar dani. Sai da nayi don kaina sannan na tsagaita, Salma ce ta fara dawowa fuskarta tamkar gonar auduga, sannan Bilkisu Abasiya ce ƙarshe.

Nan Salma ke faɗin, saurayinta Abdallah yace shi kam ma jibi iyayensa zasu zo, Abasiya da Bilkisu kuwa sati mai kamawa. Ban tanka musu ba har suka ƙarishe zancen su, don basu sanyo ni a ciki ba. Ban baau hankali na ba sai tashin da Abasiya tayi ta ɗauko wani leda daga cikin kayanta tana sincewa.

"Abasiya meye wannan hakan?".

Salma ta tambaya suna aikawa junansu kallon kallo ita da Bilkisu.

"Maganin mata ne, ɗazu Anty Hasina ta kawo min zan fara amfani dashi kafin lokacin biki na zama zamzam".



MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Page 0⃣4⃣


Sake da leɓɓe nake bin Abasiya da take ɓaro zancen ko a kwalar rigarta, balle taji kunya fayyace wasu abubuwan. Ban ɗauke idona daga gare ta ba sai sanda Salma tayi wani maganar da yaso sanya notunan kaina suncewa.

"Ƴar uwa za ki san min idan naga amfaninsa na sayi, da zarar Abdallah ya turo iyayensa zan amshi kuɗin gyaran jiki".

Sosai zantukan natan ya kuma shayar dani wani ruwan mamakin, yanda Salma take amsar kuɗin wajen Abdallah kai kace an riga da an ɗaura auren, haka nan ma Abasiya da Sagiru.

"Lafiyarki kuma ana magana kinyi shuru?".

Sai dana sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya kana nace"Mamaki kuke bani wallahi, yanda kuke zumuɗi da rawar jiki akan auren nan kamar zaku kai kanku gidan mazajen tun kafin kai ga ɗaura auran wannan rashin ajin har ina".

Tsirkar mini da tsaki Abasiya tayi, tana miƙewa ta ajiye ledar cikin kayanta inda ta ɗauko, sai da ta dawo ta zauna kana tace"kyaji dashi ai tunda ke a hakan kina ganin wani aji ne da ke, yarinya in za ki nutsu ki ba wa Malam Yusuf bori ya hau kiyi a wuce wajen".

In ma da nufin son harzuƙa ni tayi mini wannan zancen, tabbas haƙarta ta cimma ruwa don tunin naji zuciyana tazo mini har wuya, idanuna suka ƙanƙance na shiga nuna ta ƴar manuniyar ƴatsata kafin nayi nasarar raba tsakanin haƙwara nace da ita"Sai yau nasan har yanzu baku san inda yake muku ciwo ba, in ce dai mutumin bai taɓa buɗar baki ya furta mini kalmar so ba, amma shi har kuke zancen na bada kai bori ya hau. Ke kuma Abasiya tun kafin lokaci ya ƙure miki ki san abinda kike yi, tun kafin a kai ga ɗaura auren har za ki fara shaye shayen magungunan mata. Kinsan illarsu kuwa?, kinsan da meye aka haɗa su za ki hau bankawa cikinki su?".


"To don bai fito ya furta miki da bakinsa ba sai meye, ai dai naga duk makarantar babu wanda bai fahimci cewar malam Yusuf sonki yake yi ba, sai ki gaya min laifi don ke kin tunkare shi. Kuma da kike maganar maganin mata har da kawo illarsa ban sani ba ɗin, ince dai ina ke kin sani yar iya".
Raba dare nayi ina saƙa da warwaran tunanai bartakai da suka ƙi barin ruhina cikin sallama.
Ban sama runtsawa ba sai bayan sallan asubahi, na komar da haƙarƙarina na wanka. Kamar a mafarki nake jiyo tashin muryar Salma tana ƙiran sunana, na ware idona tar akan fuskarta.
"In ba za ki islamiyyar bane, sai ki tashi ki sanar damu malama ba sai kin sanya mu latti ba".
Ban kula ta ba don sam na shafa'a da lokacin zuwa islamiyyar, na ƙyar na miƙe ina karanto addu'ar tashi daga bacci kamar yanda addinina na islama ya koyar dani.
Fitowa nayi na tarar Anty Zakiyya har tayi mini aikina na safe, don haka na wuce kai tsaye izuwa ɗakin Ummata na gaishe ta sannan na dawo nayi shiri.
Ko abinci ban tsaya ci ba, don tunin Daada ta hau sababi na tsayar dasu don tsabar mulki, da jin kaina. Ban tanka mata na fito muka wuce sashin Hajiya Babba muka gaishe ta sannan muka kama hanyar islamiyyar.

Yau nayi ƙudurin fahimtar abunda kowa ya gano saɓanin ni, akan Malam Yusuf na ajin mu. Shi yake mana dukkan darrusan ajin mu, don haka na mayar da hankali yau fiye da kullum kullum.
Na lura ko yayi zai ɗago ya fuskanci ƴan ajin, sai ya sauƙe ƙwayoyin idonsa a kaina duk da kaina yana duƙe kan littafin tauhidin dake buɗe a gabana, hakan bai hana jikina bani cewar idanunsa suna kaina ba.
Har ya gama darasin ya fara tambaya, aka amsa masa kafin aka ɓarke da zancen batun sauƙan mu, kowa sai kawo nata shawaran da yanda taron zai kasance take yi, ni kuwa tunin na antaya cikin kogin tunanin da nayi nisan zango a cikinsa.

Jin muryar malam Yusuf ta dokin ƙofofin kunnuwana, ya sani saurin ɗagowa.

"Na'ima tunanin meye kike yi?, ana magana ke kinyi shuru?".

"Ba komai".
Na amsa dashi a gajarce ina basu hankali da basu sausauta ba daga zancen nasun. Har aka gama aka tsayar da matsaya akan zamu yi ankon atamfa da kuma hijabi, sai kuma kuɗin da zamu fara tarawa wajen malam Yusuf da zamu yi amfani dasu wajen yin abincin walimar.

Ban tsuma bakina ba, har lokacin tashin mu yayi, ƙarfe takwas na safe ko ya fara haramar tafiya.
Nazo fita daga ajin Malam Yusuf ya dakatar ta hanyar ƙiran sunana, dakatawa nayi tare da isowa gabansa.

Yayin da ragowar ɗaliban duk suke ficewa, kashe mini ido Balkisu tayi yayin da tazo ficewa ta raɓa ta gefena ta fita.

"Malam Na'ima".

A sanyaya na amsa masa"Na'am Malam".

Sai daya naɗe hannayensa dukka a ƙirjinsa kana yace"Naji ƴan uwanki duk suna cewar da sunyi sauƙa za'a haɗa da bikinsu, amma ke ban ji kina faɗin naki burin ba bayan haɗa karatunku".
Sai da na ƙara duƙar da kaina ƙasa ina ƙare ƙarfin riƙon da nayi wa jakata nace"E Malam haka ne dukkaninsu bikim tare da walimar sauƙar mu za'a haɗa".
Bai bani damar ƙarisawa y katse ni da cewar"ke kuma fa?".

"Malam ni bani da wani tsayayyan saurayin da nake kulawa a halin yanzu".

Jinjina kansa yayi kawai ya harhaɗa littattafansa, da hannunsa yayi mini alama akan muje na fice ya sanyawa ajin makullin sannan muk fara tafiya. Waige waige na fara yi ko zan hango su Balkisu amma ko mai kama dasu babu, hakan ya ƙara tunzura raina nayi ƙwafa da hakan ya sanya Malam Yusuf yi mini kallo ɗaya kafin yace dani"Lafiya kuwa?".

"Babu komai".

Sai da yayi taƙaitaccen murmushi kafin yace"Sun tafi ƴan tafiyar nakin ko?".
Ban iya cewa dashi komai ba, sai ji nayi ya kuma cewar"bari na raka ki har gidan".

"A'a malam nagode zan tafi kawai, wataƙil wani uzurin ne ya kama su shiyasa suka tafi ba tare da sun yi haƙurin jira na ba".

"Rakiyar tawan ce bakya so?".
Kaina na girgiza masa, "To jira ni na ajiye littattafan nan a ofishina na fito".
Bai jira ta cewa ta ba ya nufi ofishin malaman da suke jere da juna, ya murawa nashi makulli sannan ya shiga, cuno baki nayi don har ga Allah ya shiga rayuwata a wannan sa'ilin, har ya dawo ban gusa ba daga inda ya barni tsaye.

"Muje ko".
Tafiya muka fara yi a jere har muka fice daga cikin islamiyyar, jifa jifa nake amsa zantukan nasan da na lura baya gajiyawa da yinsu, haka nan rashin tankawa ta bai hana sa dakatawa ba.

Har cikin layin mu ya kai ni, ya tsay nisa kaɗan da gidan mu.
"To na kawo ki har gida, na sauƙe alƙwarin ko?".
Ya ƙare zance yana murmushi, kaina na gyaɗa masa da hakan ya bashi damar ɗaurawa da"To sai gobe a gaishe da mutan gidan".

"Zasu ji nagode".

Na faɗa ina ɗaukar miƙaƙƙiyar hanyar da zata kai ni har ƙofar gidan mu, ba tare da na karya kwana ba. Ina tafe ina ƙunci ni ɗaya har na isa gida. Ɗakin mu na nufa ina yaye hijabin dake kaina.

Salma da Balkisu, suka shiga kallom juna suna ƙunshe dariyar dake cikinsu, tsaki na tsirkar mai dogon zango ina naɗe hijabina kafin na ajiye shi cikin bagon kayana nace"kwaji dashi ai munafurcin banza".

Daga haka na fice daga ɗakin na nufi na Ummata, tun kafin na kai ga shiga nake jiyo tashin sheshsheƙar kuka, har na ƙarisa shiga cikin kwaridon ɗakin da Umma ta sanya labule ta masa tsakani da ainihin uwar ɗakin.

"Malama bazan iya cigaba da zama da Abban Walida ba, zan koma ƙauyen mu duk da kuwa bani da

Please Login or Register in order to submit comment