Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaro ido nayi"Haba dai ɓacewa". Murmushi kawai yayi ya tada mashin ɗin muka fice daga makarantar. Duk yanda naso ya tsaya yaci abinci ƙiya wa yayi sai dai yayi mini alƙawarin dawowa kafin magrib sai yaci abincin fatan dawowa lafiya nayi masa ya wuce ni kuma na fara bubbuga ƙofar gidan. Tun ina yi a hankali har na zage ƙarfina na fara bugun ƙofar tamkar Allah ya aiko ni don na gama harsala zuciyata ta taho har wuya. Dukan ƙofar nake yi kamar hannuna zai tsinke amma babu alamar Husna ta taso balle na saka rai da buɗewa ƙofar. Sai wasu samari ne biyu da suke zaune tsallaken kwata suka taso, sallama suka yi mini tare da gaishe ni sannan suka tambayi abinda ke faruwa don a ƙalla nafi mintuna ashirin tsaye ina bugun ƙofar babu alamun Husna kamar gidan kurame nake bugu.
Zayyana musu nayi, ɗaya daga ciki ya haura katanga ya shiga gidan sannan ya buɗe ƙofar na shiga bayan na jera musu godiya sosai. Har wani tiriri zuciyata take yi tsabar ruwan ɓacin ran dake kwaranya a dukkan sassan magudanan jinin jikina, kamar wacce aka jefo haka na faɗa falon ina sakin jakan dake rataye bisa kafaɗuna.


Tana kwance a falon dafe da goshinta tana kallon rufin falon, tana ɗan jijjiga ƙafafunta da suke harɗe. Ji nayi hannuna ya zarta da hukunci ba tare da yin shawara da zuciyata ba, don ƙaran marin da na sauƙewa kuncin Husna ne suka sauƙa a ƙunnuwana tare da ƙarar da ta ƙwala kamar na yagi namar jikinta. Cikin ƙanƙancewa ido nake nuna ta da ƴar manuniyar yatsata ina faɗin"Kina zaune a nan kina jin yanda nake dukan ƙofar nan kamar zan ɓalle ta, shine ko yunƙurin tashi baki yi balle ki buɗe mini?, me kike nufi da nine Husna me nayi miki?, ko ƙanwata ta girme ki balle ni kuma ba zan laminci rashin mutumcinki ba don haka tun wuri kinsan abin yi".

Bilhaƙƙi nake maganar ina jin raina yana kuma tafasa tamkar balkwanon dake aman wuta, ina gamawa naja jakana fu na shige ɗaki raina a jagule nayi wanka nayi salla. Sannan na fito na ɗaura girki har dare na haɗa nayi don na huta gajiyar da na kwaso. Ko kallon inda take banyi ba don ko abincin da na zuba mata bata ci sai kuka take har da rawar jiki, ban damu ba na cika cikina sannan na ajiye na mijina nayi kwanciyata sai dai ba bacci nake yi ba don takaici ba zai barni ba wayata na jawo na ƙira Abbana muka gaisa munyi hira sosai kafin ƙiran sallan asr ya tilasta mini katse ƙiran.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Page 2⃣9⃣

Sai bayan magrib yaya Yusuf ya dawo, ina zaune kan sallayan da nayi salla ita kuwa tana kwance cikin kujera ta dugunƙune. Da sauri na isa gare shi tare da amsar ledar dake hannunsa ina yi masa sannu da zuwa ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar audu. Na fice kawo masa ruwa sanda na dawo naji shi yana tambayar Husna meya same ta, kukan da ta tuntsire dashi ya sani yi mata kallo ɗaya. Na ajiye masa ruwan tare da tsiyaya masa, karɓa yayi kawai ya riƙe a hannunsa yana sauraran maganar da Husna take tamkar zata shiɗe.

"Kawu bani da lafiya ne duk jikina ciwo yake yi min".
"Meya same ki?".

"Anti Na'ima ce tayi min dukan tsiya wai don na kishingiɗa bacci ya ɗauke, ta dawo tana buga ƙofa ban buɗe mata ba".
Da ƙyar ta ƙare zancen kafin ta fashe da wani ƙarƙarfan kukan da ko sanda na sauƙe mata marin bata yi irin sa ba, saurin ajiye kofin hannunsa yayi cikin zaro ido ya ce"Duka kuma Na'iman?". Ya faɗa yana kafe ni da ido take naji wani takaici ya ƙara rufe ni na kasa cewa dashi komai, hakan ya bashi damar cigaba da faɗin"To ma Husna in kin lura lokacin dawowarmu yayi sai ki dinga kasa kunne, ke kuma Na'ima ki dinga kai zuciya nisa nasan matata da haƙuri tabbas yau ɗin ma nasan kuskure da saƙar zuciyar da bata da ƙashi ne".
Nauyayyen ajiya zuciya na sauƙe a gajarce na ce"in sha Allah". Ina ɗago ido muka haɗa da Husna ta jefo mini wani kallon da ya sanya ni runtse nawa idanun ƙanƙanta da ƙarancin shekarunta suke sanya ni ɗaga mata ƙafa don dududu baza ta wuce shekara sha biyu ba a haife amma tana girman jikin da in mutum ya ganta kai tsaye zai tsammata mata shekaru goma sha biyar. Miƙewa nayi na kawo masa abincinsa na zuba masa dai dai ya ɗaga cokalin zai kai baki, Husna ta dakatar dashi da faɗin"Kawu yunwa nake ji, ɗazu zazzaɓin da nake ji bai barni na iya cin komai ba".
Tagumi na zagba hannu bibiyu, tare da kafe su da ido sai da ya kalle ni kafin ya ce"Bangane ba ki ci abinci ba?".

"E kawu banci ba".
Ta faɗa tana rau rau da mitsimitsin idanunta, tsaki ya ja mai dogon zango kafin ya ce"Zo ki ɗauki wannan ki ci". Ya tura mata plate ɗin gabansa cikin rawar jiki ya taso ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya kai ka rantse har girman Allah ta shekara bata yi gamo da shinkafa ba.
Wani ƙululun baƙin cikin suka hana ni taɓuka komai, balle fahimtar dashi abinda ya faru. Muryarsa da naji suka fizgo ni daga tinanin da na fara nisan ciwo ciki dake haɗe da mamakin kaidin da munafurcin Husna wanda zuciyata ke bani duk shirin mahaifiyarta ce. Har ya miƙe yana saka hular ya ce"Zan fita masallaci ki haɗa min shayi kawai in na dawo nasha". Daga haka ya fice ba tare da ya tsaya jin daga gare ni ba, nima miƙe nayi na shige ɗaki na daɗe zaune kafin nayi sallan isha'i na fito zan haɗa masa tea ɗin. Tana zaune inda na barta nayi wuce ta waje na tafasa ruwan zafi na zuba a flask na haɗo komai na tea ɗin na ɗaura akan babban tray na shigo ɗakin na wuce masa dashi, sannan na faɗa wanka ina ƙoƙarin ɗaura zanin wankana naji kamar alamar ficewar mutum daga ɗakin yayi kato da ƙofa, a hanzarce nayi gyaran murya don a tunanina ko yaya Yusuf ne. Jin bai amsa ba ya sani fitowa babu kowa a ɗakin sama sama na murza mai a fatan kana nayi shirin bacci cikin riga da wando masu santsi, zama nayi ina duba littattafaina har yaya Yusuf ya shigo na rufe ina masa sannu da zuwa tare da miƙewa na haɗa masa ruwan wanka. Kafin ya fito tunin na ciro masa nasa kayan baccin na taimaka masa ya wajen saka su, sannan ya ce na kawo masa tea ɗin. Turus na tsaya ganin ba yanda na ajiye flask ɗin na iske shi ba ga ruwan shayin cikin tray ɗin da na ɗaura shi ya ɗan zube, banyi wani yunƙuri ba har naji sa a bayana ya zaunar da ni kan cinyarsa ya jawo tray ɗin ba kasa hana shi har ya zuba ya karɓa kurɓa a hankali, kamar yanda na kasa ɗauke idanuna daga kansa, na kuma gaza hana zuciyarta wasiwasi.
"Menene ya faru?, da gaske ne Husna bata ci abinci fa?".

Maganarsa ta katse mini hanzari, sai da na numfasa na ce"Haka ne bata ci abinci ba, amma na zuba mata ita ce dai bata ci ba wai don na shigo na iske ta kwance a falo kuma na tabbatar tana jin duk bugun da nake amma tayi buris da ni har ya kai ni ga gaura mata mari". Murmushi naga ya saka mai sauti yana ajiye cup ɗin dake hannuna kafin ya furta"Na'ima kenan, wallahi duk abinda Husna ta irga min babu wanda ya shiga kaina balle zuciyata tayi aiki dashi, abinda kika ga nayi kawai don mu kuɓuta ne daga zargin Anty Binta na cewar na fifita ki sama da dangi da ƴan uwana".

Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe, ina kwantar da kaina a ƙirjina cikin raina ina faɗin yau da gobe ya wuce wasa ina tsoron ranar da makircin su zai yi tasiri a ƙirjina. Washe gari kamar kullum kafin bakwai na kammala dukkan aiyukana, har na tafasa doya na ajiye da zummar idan na dawo nayi mana miya. Yau ma na mayar da hankali sosai ga darrusan da aka yi mana, ba kamar english don malamar ta iya koyarwa ba ƙarya ga sakin fuska ga ɗalibai. Koda muka dawo gida tararwa muka yi garƙame da makulli duk muka tsaya cike da mamaki, wani yaro ya fito daga gidan maman Anwar da gudunsa ya leƙo mu sannan ya koma suka dawo tare da maman Anwar sai da muka gaisa ta ce damu"Ga ɗan makullin ɗazu ƙanwarki da kuke bari a gidan, ta shigo ta kawo min wai ta kuka wai ita zata gida na ce ko lafiya".
Tunda ta fara maganar na fahimci waye take nufi da ƙanwarta, Husna kenan karɓa nayi tare da yi mata godiya na buɗe gidan muka shiga. Gidan kaca kaca kamar wanda ya shekara babu wani halittan dake rayuwa cikinsa kaina na gyaɗa na wuce falo shima haka komai a barbaze zare hijabina nayi na fara tattarewa shi kuma ya juya mini baya yana waya, ƙarshen maganar kawai naji yana furta"Anty Binta gaskiya yanzu ba zan sama zuwa ba, sai dai zuwa bayan magrib mu zo".

Ko ƙala bance dashi na gama gyare falon, nayi wanka nayi salla ya ce dani zai dawo da wuri yaci abincin Anty Binta ce ta ƙira shi wai Husna tan gida, cikin ƙarfin hali na ɗaga masa kaina ya fice ko rakiyar dana saba masa banyi ba.

Bayan sallan asr nayi karatun alƙur'ani sosai, don kwana biyu bana yi da rana sai dai da kafin asubahi muyi da yaya Yusuf, har ƙarfe biyar sannan na tashi na ɗaura mana girki na fiddo da litattafaina ina yin aikin gidan da malamin lissafinmu ya bamu ina bugawa da calculatorn wayana, kafin magrib na kammala komai har gyaran gida nayi wanka, sai bayan salla yaya Yusuf suka shigo tare da yaya Auwal na fito muka gaisa sannan na zuba musu abinci tare suka fice masallacin sallan isha'i yaya Yusf ya dawo shi kaɗai, muka wuce gidan Anty Binta. Yau a ɗakinta muka iske ta duk muka gaishe ta amsa nashi nawa kam ɗauke kai tayi tamkar bata zan da wanzuwata a wajen ta ta hau faɗi cikin sababi kamar zata yi aron baki.

"Yanzu Yusuf ashe ko faɗuwa nayi na mutu baza ka iya riƙe min ƴaƴana ba?".

"Meya faru Anty?".

"Meye ne bai faru ba, dubi jikin Husna shatin lubga lugban bulala kwance ai ko jakar da kuka saka kuɗi. Suka sayo sai haka". Sai da ya sauƙe numfashi kafin ya shiga faɗin"Anty zan so ki fahimci wallahi zaman yarinyar nan na kwana biyu ina ankare da ita, babu wani aikin da take yi cikin gidan. Komai Na'ima ke abin ta bata taimaka mata da komai hatta girki ranan da aka saka kafin mu dawo ba yi tayi, haka na wuce islamiyya ba tare da naci komai ba".
A tsawace take cewar"To ai daman ba cewa nayi a sake mata aiki sai kace jaka ba, cewa nayi zata na taya ta da wasu aiyukan. Kuma da kake faɗin ka wuce islamiyya baka ci komai ai kaɗan ma ka gani ba dai boko ta fifita fiye da aurenta ba?. Wataran sai ka kwana baka ci komai bama". Daga ni har shi shuru muka tamkar waɗanda ruwa ya cinye kafin ta juyo gare ni"Ke kuma na dawo gare ki, bazan laminta maishe min da ɗa kamar jaka ko baiwa ba, ko da yake ai ba ki san wahalar ɗaukar ciki ba balle zafin naƙuda, tun da kika ƙwallafa rai ga bokon nan nasan ko cikin ba za ki bari ki ɗauka har ya kawo miki tsaiko ga karatunki. Wallahi daga ke har shi ku fita idona ga Husnan kuma zaka koma".

"In sha Allah makamancin hakan ba zai ƙara faruwa ba, Allah ya huci zuciyarki".

Na furta ina ƙoƙarin danne ƙwallar da suka ciko mini koramar idanu. Ta taɓe baki da faɗin"Ya fi dai".
"Ina Husnan?, sai tazo mu tafi".

"Ta shiga makwabta, bari Amir ya ƙira ta kafin nan ga furar da Abbansu jiya ya kawo na ajiye maka ita". Ta miƙe tana ɗauko masa ƙwayar furar da ɗan murmushi ya ce"ai kuwa na gode a sa min a leda mu tafi da ita".
A faƙaice ta galla masa haɗi da faɗin"saurin me kake yi a nan nake son ka shayen ta".

"To bari musha da Na'ima don tayi min yawa".

"Ita ma ai ba mantawa nayi da ita ba, akwai nata".
Jugum nayi kamar mai karɓan gaisuwar mutuwar iyayenta, har ya gama shanye furar tsat, saboda hirar da take jan shi dashi yayi hamdala kana ta ɗauki ƙwarya ta fita dashi, a kofi ta kawo mini na ce na ƙoshi ɗage kafaɗa cikin halin ta kula ta ƙira Amir ta ceya ɗauka ya fita dashi. Sai da muka jira Husna ta dawo kana muka tafi.

Muka iske yaya Auwal har ya dawo, ban sani ba ko yaya Yusuf ne ya sanar dashi abinda yake faruwa ya ƙira Husna yana mata faɗa tare da yi mata kashedin kar ta ƙara zuwa gida ta ce anyi mata wani abu ta same shi ta faɗa masa.
Har mun kwanta muka jiyo bugun ƙofa, ya saki tsaki sannan ya zara rigarsa yaje ya buɗe Husna ce tsaye riƙe da bargonta ina jin tana faɗin wai tsoro ne ya hana ta bacci.

Nayo zaton zai je yayi mata addu'a ne ta kwanta ya dawo, sai naga saɓanin tinanina da maganar da ya faɗa da suka sanya ni zargin na'uran dake jiyo mini zantukan da mutane suke furtawa ne bata naɗo mini muryarsa dai dai ba.

"Na'ima ku kwana tare da ita kawai, ni bari naje falon na kwanta".

Yana ƙarishewa ya fice tare rufo mana ƙofar, ko kallo ban ishe ta tazo ta haye gadon tare da rufuwa da bargonta tsabar takaici tamkar na sanya hannu aka na kurma ihu, ko da asuba bata tashi salla har na wanke banɗaki na fita na gyare tsakar gidan tare da ɗaura mana girki kafin ya ƙarisa na shige wanka. Ƙam na tsaya ganin gadona da yake jiƙe kamar an yi ɓari, na shiga ƙwalawa Husna ƙira sai da nayi baki biyar kafin tazo.

"Me ya faru da gadon nan? inda kika kwanta".

"Fitsari nayi".

Wani hawarwasa zuciya tayi, kafin tayi tsalle ta garke mini a ƙirji sai da na ƙare mata kallon tsaf na ce"Fitsari da girmanki da bakinki, za ki wanka kiyi min fitsarin kwance?".
"In ce dai fitsarin nan kowa yayi shi lokacin ƙuruciya har ke mai maganar".

Taku biyu ya kai ni gabanta na ɗaga hannu da nufin zagba mata marin da nake da yaƙinin da taga gilmawan taurari bisa idaniyata. Kafin na sauƙe mata ta zube ƙasa tana ƙwala ihun na kashe mata ido. A figice na ɗago kaina jin muryar yaya Yusuf a tsakiyar kaina.

"Subhanallahi Na'ima me nake gani haka?, me kuma tayi miki dan Allah ki dunga tausayina mana meyasa ko yaushe kike son haɗa ni da ƴan uwana ne suna ganin kamar na fifita ki a kan su".
Sororo nayi ina kallonsa, kafin Husna ta miƙe ta ƙamƙame da saurinta haƙuri ya shiga bata cikin kwantar da murya. Har da fita ya sayo mata cakuleti, ban furta masa komai kamar yanda shima bai nemi ji daga gare ni ba, har muka isa makaranta cikin babu wanda ya ce ko ƙalla, ko da aka tashi na nufi ofishinsa mai gadi ya dakatar dani tare da bani ɗari biyu wai shi ya ce inna zo a bani na hau adaidaita shi yana da wurin zuwa.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 3⃣0⃣

Har na iso gida ina cike da mamakin uzurin da ya tasowa yaya Yusuf, domin a sanin da nayi masa baya ƙaunar na hau adaidaita ko sa'ilin da nake gida na taho ban jira shi yazo ya ɗauke ni ba, tabbas naga ɓacin ransa. Amma yau da kansa ya ce na hau abin hawa. Tana bacci a falo na iske ta na wuce ɗaki ruwa na watsa nayi sallah na fito barkono na ƙwanƙwasa na soya mana manja kasancewar babu albasan da zamu yi miyar nawa na ɗeba ita ma na zuba mata nata na bar mata a kicin ɗin.
Tisa abincin nayi a gabana, sam na gaza ci tinanin uzurin da ya tasowa yaya Yusuf ya maƙale a raina, yanka huɗu naci naje na ajiye na dawo na kwanta ban tashi ba sai gab magrib.

Koda nayi sallan ban tashi ba, sai da nayi isha'i aka kawo wuta a hanzarce na jona wayata a caji domin na samu damar ƙiran yaya Yusuf, girki na ɗaura mana nayi dambu. Jugum na zauna riƙe da wayata da na tisa a gaba ƙwall suna zirara ta gefen kuncina, na ƙira layin yaya Yusuf yafi sau shurin masaƙi amma baya ɗauka ƙiran ƙarshe da nayi masa naji wayar a karshe ɗif. Babu shiri naji hawayen sun ziraro mini zuciyata tana bugawa daidai da tashin waƙar Ado gwanja da Husna take rerewa mai taken cas.
Tare suka shigo da yaya Auwal, na zabura na tashi tsaye har ya shigo kallo ɗaya yayi mini naga ya ɗauke kansa, nayi masa sannu da zuwa kansa ya ɗaga mini kawai yan jiya kansa mazauni akan kujerar mutum biyu dake falon. Kusa dashi na zauna muryata cike da damuwa na ce"yaya lafiya ina kaje yau?, na ƙira wayarka baka ɗagawa duk ka sanya ni cikin damuwa".

Lumshe idanunsa yayi haɗi da faɗin"Wani uzuri ne ya taso min, ƙiran da kika yi min kuma na gani kawai lokacin ina wani aikin mai muhimmanci ne".

"Amma yaya ko sau ɗaya da ka ɗaga kayi mini bayani ai, kasan tashin hankalin da na shiga kuwa?".

"To wai dole in zan fita kenan sai na sanar dake ko meye kike nufi?". A sanyaye na jijjiga masa kaina ya saki siririyar tsaki kafin ya furta"To wani uzuri ne ya taso min, idan kuma tuhuma ta za ki yi bismillah tunda naga maƙaryaci yau na zamto a idanunki. Duk abinda nake faɗa ba yarda kika yi dasu ba".

Duk wata gaɓar jikina tayi sanyi sosai, na sunkuyar da kaina da hakan ya ba wa ƙwallar da wadaci kurmin idanuna damar zirarowa, cikin muryarta da ta fara rawa nake cewa"A'a wallahi ko kaɗan ba tuhumar ka nake yi ba, tunda ka dawo mini lafiya alhamdulilla Allah ya baka haƙuri".

"Amin".

Ya amsa dashi kamar anyi masa dole, ya miƙe zai shige ɗaki nayi saurin faɗin"Abinci fa?".
"A ƙoshe nake".

Daga haka ya shige ɗaki tare da bugo ƙofar da ya tilasta mini runtse idanuna, dariyar da Husna ta sheƙa har da riƙe ciki ya sani cire leɓɓana da ƙarfin tsiya kamar zan huda su. Tashi nayi da nufin binsa domin na tabbatar da cewar akwai abinda yake damunsa jin ƙofar rufe ya sani jijjiga ta hakan ya tabbatar mini da ya kulle ta ciki, tilas na dawo na zauna cike da ƙunar rai.

Raina yana amayar mini da wani balbalin tashin hankalin, tunin naji ƙirjina yayi mini wani irin nauyi tamkar anyi mini ajiyar wani dutse, bai buɗe ƙofar sai daidai lokacin da muke kwantawa ya fito riƙe da bargo da matashi bai ko kalle ni ba ya cewa Husna ta tashi ta shiga ta kwanta, ta amsa tare da miƙewa ta shige ɗakin. Kamar bai san da wanzuwana a wajen ba ya fara tattare ƙanana pillows ɗin kujerar ya ajiye su gefe guda yana ƙoƙarin kwanciya nayi saurin miƙewa na riƙe bargon hannunsa cikin zubda ƙwalla na jefa idanuna cikin nasa da ya yi saurin kawar da nashi, duk yanda naso mu haɗa ido ya haucewa hakan. Wasu zazzafan hawayen suka shiga ambaliya a tudun fuskana, cikin ƙarfin hali na ce"Yaya menene yake faru?, dan Allah ka sanar dani ko wani laifin nayi maka?".

"Ba kiyi min komai ba, Na'ima dan Allah hutawa nake son nayi ki barni haka".
Ƙara riƙe bargon nayi na ce"Bazan barka ba yaya bazan barka, har sai ka sanar dani". Tsuka yayi tare da fizge bargon yayi kwanciyarsa haɗi da furto mini zancen da suka warware mini notinan kaina.

"In ba za ki kwanta ba, ki cigaba da tsayiwa a nan".

"Innalillahi wa inna ilahir raji'un". Shi kaɗai na iya furtawa kafin naja sagaggun ƙafafuna da jiri ke shirin jefar dasu ƙasa na wuce ɗaki, ko da na shiga na tarar da Husna tsaye bakin ƙofar da alama taji duk yanda muka yi dashi. Wani kallo na watsa mata zuciyata tana kwasa ta akan nayi kukan kura na shaƙe ta, kalmar A'uzibillahi na shiga nanatawa har naji sanya ya tsirgar mini a sashin ruhina. Tsawon daren banyi iya runtsawa ba domin banɗaki na shiga naci kuka kamar ba gobe kafin nayo alwala na fito na fara salla na daɗe kan sallayar ina miƙa kokena ga sarkin dake da ikon juya rayuwata.
Washe gari na tashi da ciwon kai, amma hakan bai hana ni yin dukkan aikace aikace na ba. Girkin safe da nayi mana ma bai ci ba, ya ba wa Husna ta ƙara akan wanda na bata. Ban ce dashi komai muka tafi makaranta haka muka rabu ba tare da fatan alkhairin da ya saba yi mini ba, wanda nayi masa kuwa a banza wai ƙwalawa bebe ƙira domin ko gizau bai yi ba balle nayi tinanin samun amsarsa, yau gabaɗaya rabi da rabi hankalina ya kaso har aka tashi yau ma mai gadi ne ya bani ɗari biyu kamar jiya na tari abin hawa na koma, daren ranar bai dawo ba sai ƙarfe sha ɗaya saura abinda da bai taɓa yi ba kenan tun bayan aurenmu, ana yin sallan isha'i yake shigowa gida don ko zaman majalisa baya yi.
Har lokacin banyi bacci ba ko kallon arziki bai yi mini ba ya wuce ɗaki, sai kuma ya fito don Husna har ta kwanta a lokacin, banɗaki waje yayi wanka ya dawo ya fara shirin kwanciya.

Durƙushewa nayi gabansa cikin zubda ƙwalla, da nake jin zafin su har cikin raina na haɗe hannayena biyu alamar roƙo kafin na ce dashi"Dan Allah yaya ka tausaya mini ka sanar dani abinda yake damunka, wallahi kayi mungun canjawa har ina ganin kamar ba mijina bai tausayi da sanyi bane nake magana dashi dan Allah ka sanar ni in wani laifin nayi maka mu fahimci juna".
Zazzafan iska ya fesar daga bakinsa"Babu abindaa kika yi min".
"To meyasa ka canja mini?".

Na jefa masa tambayar a gaggauce, ina son haɗa ido dashi domin na lura yanzu gabaɗaya baya ƙaunar hakan.
"Ba komai tunda nace miki ba komai to kawai ki yarda". Cikin sauƙe numfashi na furta"Shikenan na yarda da kai". Da hannunsa yayi mini nuni akan na zauna kan kujerar nabi umarninsa ya jawo ni jikinsa kamar wanda ya tina wani abun sai kuma ya zame nashi. Daidai sa'ilin da wayarsa ta hau ruri ya ɗaga banji abinda ake faɗi ta ɗayan ɓangaren sai cewa yayi"Gani nan zuwa".

Ya katse wayar yana rarumar rigarsa ya saka tare da ɗaukar makullin mashin ɗinsa, har ya kai ƙofar fita nayi saurin faɗin"ina zaka je cikin wannan daren?".

"Anty Binta ce ke son ganina".

"Kayi haƙuri zuwa safe, yanzu fa sha biyu ake nema".

Cike da ƙosawa ya dafe goshinsa"yanzu zan dawo kiyi kwanciyarki kawai". Ya fice a hanzarce kuka mai ƙarfi na saka cike da tausayin kaina ta yanda rayuwa tayi mini juyin juya hali. Kafin na miƙe da ƙyar na tura ƙofar falon na shiga ɗaki, ban san sanda ya dawo ba sai da safe nayi tozali dashi.
Tea kawai ya nema na haɗa masa yasha kaɗan, ya bani kuɗin abin hawa ya ce na hau na tafi makaranta zai tsaya a kasuwa wajen yaya Auwal.

Haka satikai biyu suka shuɗa muna wannan zaman da yaya Yusuf, da ko kalaman bakina zasu ƙare wajen tambayarsa abinda nayi masa cewa dani yake yi babu komai. Hakan nan ko ruwan hawayena zasu kafe kamar tafki da ƙasa ya tsotse ruwan cikinsa ba zan hangi tausayina a cikin idanunsa kamar da ba, sau uku ina tambayarsa zuwa gida yana hanani wai in ya sama lokaci zamu je tare. Babu abinda yake ƙara ɗaure mini rai da igiyoyin baƙin ciki da ƙunci kamar ko tsakiyar dare Anty Binta ta ƙira shi babu

Please Login or Register in order to submit comment