Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bane?, ko kuma bata kai ku gaishe ta bane?".
Zumɓoru baki duk suka yi gaba, suna satar kallon Anty Binta kafin suka gaida ni a daƙile na amsa ina sunkuyar da kaina ƙasa.
"Anty daman munzo sanar dake ne, in sha Allah gobe inda Allah ya kaimu zata fara fita makaranta".

Ina jiyo tsakin da ta tsirga tamkar wacce tayi tozali da mummunan gamo, mintuna biyu tsakani kafin naji ta furta"To ni kuwa Yusuf meye ya shafe ni da fara zuwanta makaranta?, in ce dai ka mance yanda muka yi da kai ko?".
Shuru yayi ba tare da ya amsa ta kuma cewar"ko da yake Allah ya sanya alkhair". Da sauri ya ɗago kansa da yayi ƙasa dashi haɗi da faɗin"amin amin yauwa Anty abinda ya kamata kice kenan".

"Ba shakka! Yusuf wallahi tausayi kake bani amma tunda haka ka zaɓarwa kanka shikenan akwai ranar ƙin dillanci tana nan tafe. Tunda ita Habiba har yanzu bata dawo ba, ba zai yiyu dukkan ku ku fice ku bar gida babu kowa ba Mahmud ma komawa makaranta zai yi shi kuwa Auwal yana kasuwa don haka ga Husna nan sai ku tafi da ita in ka fice ita ma ɗiyar gwal ɗin taka ta fice neman ilmin nasara Husnan ta dinga zama muku a gidan".

Raras! gabana yayi mummunan faɗuwa babu shiri na ɗago idanuna kaɗan ina satan kallon yaya Yusuf caraf idanun ya sarƙafe cikin na juna. Na yi sauri rusunar da nawa ƙasa ina jin soyar zuciya da tuno irin kallon banzan da Husna ke yi mini a duk sa'ilin da muka zo gidan, banda samu gindi yarinyar da ko su Asma'u sun girme ta take yi mini wannan abun, maganar da ya fara da naji su raɗau a masarrafun ji na suka dawo dani daga tinanin zucin da na afka.

"Anty, Husna kuma?, kinsa fa yanayin gidan nan yanda yake ɗaki ne ɗaya sai ƙaramin falo a ina zata dinga kwana tunda ko ɗakin baƙi bamu dashi?". Sai da ta kalle shi tsaf kafin ta ce"Idan ƙanwarta ce ai da kun sa inda zaku ajiye ta, wai Yusuf meye kake ƙoƙarin zama ne?, duk mace ta susuta ka, to wallahi ta fita idona tun muna shiri da juna kuma tafiya da Husna tilas sai dai in ban isa ba to sai naji".



MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Page 2⃣7⃣


"A'a Anty kin isa shikenan sai ta haɗa kayanta mu wuce".
Taɓe baki tayi gami da faɗin"wai dai naji ko ban isa ba, wallahi Yusuf kayi hankali domin na lura rumar soyayya ce ke kwasar ka. Tunda Husna ta kammala makarantar primary sai taje ku zauna tare kafin Allah ya fito mata da miji na kawar da ita". Ni dai shuru nayi musu tunda suka fara zancen bance ko kanzil ba har suka ƙarƙare ta umarci Husna da take ƙunƙuni ƙasa ƙasa da ta tashi taje ta shiryo kayanta ta fito mu tafi. Miƙewa tayi tana bubbuga ƙafa haɗi da turo zungureren bakinta gaba ta faɗa ɗakin Anty Binta ta rufa mata baya.

"Dan Allah Na'im..".
Saurin ɗaga masa hannu nayi ina fizgo numfashina da yayi mini wahalar fesarwa ban ce dashi komai har sanda Mahmud ya shigo da sallamarsa ganin mu ya sanya annurin dake kwance luf saman kamalalliyar fuskarsa kamar kara aka tsaga da yaya Yusuf domin su biyun kamar ɗaya, yaya Auwal da Anty Binta kuwa kammanin su guda sai dai su dukkan farare ne ƙal musamman yaya Yusuf ga wushiryar dake tsakankanin haƙwaransu.

"Sannunku yaya yaushe kuka zo?".

Muryar Mahmud kenan da suka fizgo ni izuwa duniyar zahiri, ganin yaya Yusuf bashi da niyyar cewa dashi wani abun hakan ya sanya ni ƙarfin halin kallon shi na ce"Bamu daɗe da zuwa ba, daman nazo muyi sallama ne naji gobe kai ma zaka koma makaranta".

"E wallahi fitar sassafe nake son nayi asubancin don na sama isa da wuri, ko baku zo ba daman ina da niyyar zuwa har gida nayi miki sallama Antina".
Taƙaitaccen murmushi nayi kafin na kuma faɗin"To Allah ya tsare haya ya kaika lafiya, ya kuma bada abinda aka je nema". Cike da maɗaukakiyar farin cikin yake amsa addu'ar tawan da kalmar amin amin amin, sai da ya jera kalma a jere sau uku ya ce"Kema yaya yake shaida min za ki koma makaranta, wataƙil kafin na dawo har kin kusa kammalawa"

"Yaushe zaka dawo?".

Sai da ya ɗaga kansa sama"Zan iya kaiwa shekara da wasu watanni kafin na dawo, don inna tafi sai na kammala zan dawo". Jinjina kai nayi ina masa fatan alkhairi shima yana dawo mini dasu game da karatuna da fatan cikar burina.

Mun ɗauki a kalla mintoti goma zaune kafin Anty Binta da Husna suka fito da mamaki nake bin Husna da kallon domin yanayin ɓacin rai da ƙuncin da ta shiga ɗakin dashi ba cikinsa ta fito ba, hasalima walwala da annuri ne suka wanzu bisa fuskarta mai ɗan duhu.
Ban dawo daga duniyar mamakin canzuwar yanayin fuskarta ba, ta ƙara shayar da ni wani zallar ruwar mamakin da babu tsirki. Kusa dani ta zauna tana sausauta amon muryata ta ce dani"Anti Na'ima dan Allah kiyi haƙuri akan abinda ya faru ɗazun".
Kaina kawai na jinjina mata alamar babu komai, naga ta sakarwa junansu wani irin kallo ita da Anty Binta kafin ta ce"To sai ku tashi ku tafi ko, kafin dare yayi".
Jikina sanyaye na miƙe nayi mata sallama na zura takalmana muka fice daga gidan Mahmud yayi mana rakiyar har ƙofar gida don ya a gidan Anty Binta zai kwana tunda daman a nan ya fara sauƙa duk kayan a nan suke.

Jakar kayanta yaya Yusuf ya karɓa ya saka gaban mashin ɗin sannan ya hau mu kuma muka hau baya muka tafi, sanda muka isa gida har tara sauta mintoti kaɗan don haka shirin kwanciya muka fara yi. Da kansa yaya Yusuf ya ɗauki bargo da matashin kai ya kaiwa Husna dake zaune a falo ina daga ɗakin ina jinsu yana jaddada mata cewar tayi shinfiɗi ta kwanta nan.

Sanda ya shigo ɗakin har na haye bisa gadon ina ƙoƙari kwantar da kaina kan matashi ya zauna kusa dani hannunsa nayi sun sauƙa saman goshina yana shafawa a hankali da gashina ya kwanta luf saman goshin a raunane ya shiga faɗin"Na'ima bazan gaji da ba ki haƙuri ba, domin nasan zuwan Husna cikin gidan nan da wani manufa Anty Binta tayi sa wataƙil don ta ƙuntata miki ta huce takaicinta game da batun karatunki da na dage a kai, kin san me ta ce min ranan?". Saurin gyaɗa masa kai nayi ya ɗaura da"Wai asiri kika yi min, amma ni nasan ba hakan bane don Anty Bin...". Saurin dakatar dashi nayi da faɗin"Ya isa yaya, Anty Binta kamar uwa take yanzu a gare ku na tabbatar ba zata yi abinda zai cutar daku ba, domin kowa ya shaida tana yi muku so da ƙauna mao tarin yawa. Akwai sirri a tsakaninku ta yanda wani abun ba lalle sai naji shi ba, kamar yanda nima tsakaninmu akwai sirri da babu buƙatar sai taji. Allah ne shaida har cikin raina ban fassara zuwan Husna gidan nan da wata manufa ba hasalima na mafice nufinta na son sauƙaƙa mini aiyuka".
Bai ce komai ba, illa tagwayen ajiyan zuciyan da ya dunga sauƙewa kamar wanda ya yi gudun ceto rai, hakan ya sa ni murzar hannunsa kaɗan da har yanzu ke saman goshina.

Lallausan murmushi muka sakarwa junan mu ya kawo kansa dai dai kunnena yana yi mini raɗa"Ni kam nayi dace da za'a tambaye ni matar aljanna tabbas dake zan nuna gimbiyata".
Lumshe idanuna nayi ya kashe mini ido ɗaya yana nufar banɗaki domin watsa ruwa, har ya fito ban runtsa ba tunani barkatai suka hana ni samu sukuni.

Tun asubahi na tashi na iske shi kamar kullum yana wurudi, na kwaɓe fuska kamar mai shirin yin kuka na kallo shi haɗi da cewar"meyasa baka tashe ni munyi tare ba?".

"Saboda ki tashi da wuri kinsa yau ce ranar ki ta farko a makarantar nan, bana son kije a makare don ba zan hana a hukuta ki ba".

Ciki-ciki nayi murmushi na diro daga kan gadon, sai da nayo alwala sannan na tada Husna shi kuma ya fice masallaci tare da yaya Auwal. Har na iddar da nawa sallan na zare hijabin kaina ban ji alamar motsin Husna ba hakan yasa nazo duba ta, turus nayi ganin ta koma baccinta tayi ɗaɗɗaya na tada ta, wata miƙa tayi tare da gallo mini harara haske tocilar wayar hannuna da ya haske ɗan madaidaicin falon ya bani damar ganin hakan, sai dai ban mayar da hankalina ba na ce"ki tashi kiyi salla Husna, har an kusa tasowa daga masallaci fa".

"Dan Allah malama ki ƙyale ni, in ce dai a kaina zanyi sallan nan ko to ki barni".

Sanƙarewa nayi a wajen har zan ce wani abu sai ga yaya Yusuf ya shigo ban yi tsammanin ganinsa a irin wannan lokacin ba domin nayi tinanin islamiyyar safe zai wuce. Fahimtar abinda yake faruwa. Ya sanya shi daka mata tsawar da ta kiɗima ta ta tashi a daburce tana rarumar ɗan kwalinta. Ta fice waje komawa ɗaki nayi na gyare shi tsaf sannan na wanke banɗakin dake cikin ɗakin. Na fito falo na tarar Husna na tattarewa wajen na fito na iske yaya Yusuf ya haɗa gawayi har ya ruru ya ɗaura ruwan zafi zai dafa mana taliyar yara, sannu nayi masa sannan na taya shi muka gama na tsaftacce filin gidan na zuba musu nashi tare da yaya Auwal domin yana gida sannan na juye mana sauran na juye mana muka ci tare da Husna. A gaggauce na gama shiri don bakwai har ta gota ina ɗaura ɗankwalina yaya Yusuf ya shigo ta cikin madubi na kalle shi yana tsaye bakin ƙofar ɗakin ya harɗe hannayensa a ƙirjina yana saki murmushi. Har na gama idanunsa suna kaina na taraya jakata a kafaɗata na iso gabansa sai na ganni ƴar guntuwa a gabansa na ɗaga kai na kalli fuskarsa ya kuma sakar mini wani murmushin kafin ya rungumo ni jikinsa. Idanunsa ya lumshe yana faɗin"Dan Allah matata ki kula min da kanki, wallahi ina kishinki Allah ya tsare min ke da kuma mutuncinki ya ba ki sa'a".
Lamau nayi a jikinsa kafin na ce"in sha Allah zaka same ni fiye da yanda kake zato, zan tsare kaina da kuma mutuncina".

"Na yarda dake".

Ya faɗa yana lakato mini gefen kunci, ya riƙo hannuna muka fito falo muka tarar da Husna zaune sallama muka yi mata na bata wayata don yana ɗebe mata kewa. Muka tafi bayan yaya Yusuf ya gama jadadda mata kafin mu dawo ta share gidan kuma ta tafasa mana taliya. Sosai na yaba da kyawun makarantar duk da kuwa kasancewarta ta gwamnati, amma ta bambamta da sauran ta fannin tsaruwa da wadatattun malamai kuma ƙwararru, sai da yaya Yusuf ya kai ni ofishinsa tukunna muka wuce sashin sakandiri.
Sai da muka je ofishin principal na rantaɓa hannu akan takardar dokoki da tsarin makarantar dake nuni da na yarda dasu kuma nayi alƙawarin ba zan ƙetare su ba. Sannan aka kai ni ajina mun samu da malami a ciki aka nemi izini sannan na shiga a benci na uku yaya Yusuf da malamin da suka kawo ni ajin suka juya.

Sosai na mayar da hankalina ga darasin da ake koya mana wanda ya kasance computer, darasi huɗu muka yi kafin aka kaɗa ƙararrawar tashi tada, ƴan mata biyu da na iske a bencin da suka gabatar mini da sunayensu da Maryam da Hafsat muka fito tare dasu.

"Kamar yau ce ranarki ta farko zuwa makarantar nan ko?".
Da murmushi a kan fuskana na ce"E". Ta gyaɗa kai ta ce"shiyasa amma kinga mu duk a nan muka yi jss mun saba". Gyaɗa kawai na saya da ɗari biyun da yaya Yusuf ya bani muka ci tare, sanda aka koma aji ma darasi huɗu muka yi aka tashi. Ƙarfe ɗaya muka tashi muka fito tare dasu Maryam a bakin gate muka yi sallama don a yanda suka shaida mini tare suke tafiya, sashin primary na nufa ofishin yaya Yusuf na tsaya daga waje ina yin sallama sai da ya amsa kana na shiga gani na ya sanya shi sauri ajiye takardan dake hannunsa yana karantawa ya miƙe.

"Ƴan makaranta an tashi ko?". Na gyaɗa masa cike da gajiya ya kuma faɗin"To bari na rufe office ɗin mu tafi, daman ke nake jira".

Tattare wasu takardu yayi, ya sanya cikin wata drawer sannan ya rufe ofishin da key muka nufi gidan muna tafe muna taɗawa har muka isa. Tun daga zaure muke rangaɗa sallama yafi baki goma amma ba'a amsa ba, hakan ya muka shigo kawai tsit filin gidan babu kowa muka wuce falo turus nikam naja na tsaya saboda ganin falon tamkar ba nawa ba duk anyi kaca kaca dashi. A hankali idanuna suka sauƙa a kanta gabanta da cup ga ledodin madara da milo ajiye a gabanta da kuma kofin jug, ta juya mana baya tana latsawa wayata da na bar mata ita.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Page 2⃣8⃣

Tsawar da yaya Yusuf ya kwaɗa mata ya sanya ta juyowa a firgice dake da ƙirjinta, alamar sosai tsawar ta shige ta.
"Meye haka kike yi?, har muna sallama ba ki ji ba ina hankalinki ya tafi?, sannan meya wargaza falon nan?".

"Daman daman daman yanzu nake son na tashi, na tattare wajen ban zata yanzu zaku dawo ba".
Kansa kawai ya jinjina ya shige ɗaki, na tako har inda take na ɗan duƙusa kafin na ce"Husna yaya falon kacakaca haka?, idan anyi amfani da abu ɗaukewa ake yi a mayar dashi inda ya dace ba ajiye ake ba a ko'ina, kinga ran kawunki ya ɓaci idan ya fito yanzu ki bashi haƙuri sannan gaba ki gyara". Wani kallo ta watso mini cike da tsiwa ta ce"laifin uwar meye nayi masa da zan basa haƙuri? ni ko a gidan ba'ayi min haka". Tana ƙara faɗin hakan ta miƙe ta fice bayan ta dakwafa mini wayarta da take kukan rashi caji a ƙasa, da kallo na bita kafin na cira kaina na shige ɗaki na tarar da yaya Yusuf yana banɗaki jakata kawai na ajiye na fito waje nayi alwala na dawo ko kallon inda Husna take zaune banyi ba, a falo nayi salla na zare hijabina na haɗa gawayi a gaggauce na ɗaurawa yaya Yusuf dafa dukkan taliya domin lokacin tafiyarsa islamiyya ya gabato, sai da na haɗa komai na zuba na shigo ciki na tattare falon tare da sharewa.
Yana zaune gaban madubi yana shafa mai, na shiga banɗaki na watso ruwa a ɗan gaggauce na fito na iske shi nan inda na barshi mai na shafa na zara doguwar rigar material ɗin da ta sauƙar mini har ƙasa haka na isa gare shi, tare da karɓan maɓallin hannun rigarsa da yake ƙoƙarin sawa na sanya masa.
Cike da kula nake faɗin"Allah ya huci ran gwarzona, Husna yarinyar ce dole wasu abun sai ana sanya ta a hanya duba da ƙarancin shekarunta, ita ma ta ce na baka haƙuri bacci ne ya ɗauke ta bayan fitar mu".
Kansa kawai ya ɗaga mini ba tare da ya ce dani uffan ba, na kamo hannunsa"Na ɗaura girki da zaka tsahirta da fitan na minti bakwai zuwa goma in sha Allah zai kammala, na fi so na cika maka cikinka kafin ka fita". Da ido yayi mini alama akan lokaci ya yi yana mini nuni da agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, na kuma shagwaɓe fuska sosai tare da haɗe hannayensa da nawa waje guda"Dan Allah Zaujiii". Sanyayyan murmushi ya saka ya ce"na ƙara miki wasu mintona goman akan wanda kika faɗa". Na saka tsalle ina masa godiya muka fito falo na duɓe firiji na kawo masa zoɓon da bama rabu da yinsa domin kuwa yana matuƙar son sa, na ajiye masa tare da tsiyaya masa a kofi na fita wajen girkina. Inda na barta nan na iske Husna ko gusawa ba tayi ba ina kyautata zaton ko sallan zuhr bata yi ba, bance da ita komai na mai da hankali ga girkina yana kammaluwa na zuba a flask na shigarwa yaya Yusuf nashi ciki da kaina na zuba masa kuma na dunga bashi har sai da na tabbatar da ya ƙoshi sosai sannan na miƙa masa ruwa ya sha yana hamdala ya fito na raka shi har zaure bayan ya amsa gaisuwar da Husna tayi masa a daƙile.


Na juye mana ragowar abincin nayi zaton ba zata taso taci ba, sai naga babu kunya ta miƙe ta share waje ta hau zuba taliyar da tasha kayan miya da korri a cikinta har na tashi ba barta, ina ankare da ita ko sallan asr ma ban ga alamar tana da niyyar yinsa ba, duk yanda naso tausar zuciyata da bata shawarar kau da kai ga lamarin yarinyar gani nayi ba zan iya yin shuru ina gani tana wasa da salla ba alhalin ta kai musalin da in bata yi ba ya dace an sanya tsumagiya a zane ta. Koda nayi mata magana kada baki tayi ta ce dani"Dan Allah malama ki barni na huta, ni ba an kawo ni gidanki don ki takura min bane kiyi harkarki nima nayi nawa in ce dai sallan nan ba ake zanyi wa ba?, don haka ki barni da ubangiji yayi min hukunci da kansa". Sosai nayi mamakin zantukan yarinyar, tamkar ana mata wahayin su, duk yanda zuciyata take tunzura ni akan na kai mata wani mungun bugu a bakin rashin kunyar, danne zuciyata nayi na shige ɗaki ina bibiyar darasin da aka yi mana yau ganin saƙon yaya Yusuf akan ba zai dawo ba sai bayan isha'i ya sanya ni ban ɗaura girki ba sai da nayi sallan magrib na fito na ɗaura ruwan tuwon garin masarar da zan tuƙa mana, miyar bushashshan kuɓewa nayi, na tattare komai hakimar na falo tana kwance, nayo alawa nayi sallan isha'i sannan na shiga banɗaki nayo wanka na shirya cikin doguwar rigan kamfala.
Tare muka ci abincin da yaya Yusuf ida kuwa na zuba mata nata daban, kamar ƙaramar yarinya ta fara jagwalgwala abinci ina ankare da ita sai dai ban ce komai ba, sai da yaya Yusuf ya ce"Lafiyarki ko yunwar ce bakya ji?, kike faman jagwalgwala abincin".
Radau radau tayi da ido"kawu bana cin miyar kuɓewa ni ko a gida".

"Shine kin fi ƙarfi ki buɗa baki ki faɗa ko?".
Kanta ta girgiza masa da sauri yayi ƙwafa kafin ya ce"Sai kije ki ajiye shi, ki haɗa shayi kisha ki kwanta". Na kallota cike da takaici na ce"Ai da kin faɗa mini sanda nake yi, da sai nayi miki wani abun da za ki ci".

"Barta kawai tasha shayin gimbiya".

Ban kuma cewa komai ba har muka gama cin abincin, na haɗa wanke wanke zan yi ya fito muka yi tare don na sama sauƙi da safe. Yau ma a falo tayi shimfiɗi tayi mana sai da safe don ganin idon yaya Yusuf muka shige ɗaki muka kwanta. Muna manne da juna muka jiyo bugun ƙofa kamar za'a ɓalle ƙofar ɗakin, duk muka zubawa ƙofar idanu kafin yaya Yusuf ya zame jikinsa daga nawa ya tashi ya buɗe ƙofar muryar Husna ce tana maganar kamar tana kuka.

A ɗan fusace naji yayi maganan"Za ki nutsu kiyi min magana ko kukan za ki cigaba dashi?".

"Kawu tsoro nake ji, na kasa kwana a falon tun ɗazu na kasa bacci da na rufe idona sai naji kamar wani abu yana nufo ni".

Ina jiyo tsakin da ya doka cike da takaici ya ce"muje nayi miki addu'a ki kwanta babu wani abun, kawai kin saka tsoron ne a ranki shiyasa" . Daga haka yaja hannunta suka koma falon, ƙarƙarfan ajiyan numfashi na fesar ina tallafe da kuncina har ya dawo ya rufe ƙofar ya zauna kusana. Na tari numfashinsa kafin yayi magana na jefa tambayar"Ta sama baccin?".
"Ta samu shiyasa na ɗan daɗe ai, sai da ta kwanta tukunna na dawo".

Kaina kawai na gyaɗa masa muka koma muka kwanta, kamar jiya yau ma tun tashin asubahi ban koma ba. Yau ya tsaya a islamiyyar safe don haka na gagauta kammala girkina na ɗumama mana raguwar tuwon jiya, sannan na share filin gidan tsaf ko tashi Husna bata yi ba har na shiga kammala na shigo falon, da nufin gyare shi tashin ta nayi tayi miƙa har ƙasusuwan jikinta suna bada wani sautin ƙaƙas. Na katse ta da cewar"kinyi salla ne?". Wulaƙantaccen kallon da ta watso mini suka turniƙe mini raina, har sai da na cire leɓɓana.

A harsale ta furto mini maganar da suka kai ni bango"Dan Allah malama ki rabu da ni, ki bar ni kiyi rayuwarki nayi tawa". Hannuna ya shiga rawa na ɗaga da zummar zabga mata kyawawan maruka kamar wacce ta tina da wani abun sai kawai na sinci kaina da sauƙar da hannuna haƙorina suna datse harshena, wata zuciyar tana raya mini cewar da wani manufar take yi duk waɗannan abubuwan musamman cewar da tayi dare jiya wai tsoro ya hana ta kwana falon, zuciyata ta darsar mini da zargi game da ita. Nayi alwashin ba zan ƙara shiga harkata ba a cikin gidan, aiki kuwa wanda aka yi ikirarin cewar shi ya kawo ta gidan domin ta taya ni banga ko alamun hakan ba domin tun zuwar ta bata gyara biyar ba amma ta ɓata goma. Kafin yaya Yusuf ya dawo na gyare ko'ina na saƙale turare tsinke a falo da ɗakin har na kammala shirina, abinci kawai yaci muka fito sai da ya ƙara jaddada mata kamar jiya akan ta ɗaura girki kafin mu dawo wanda zata iya yi. Sannan ta dunga saka sakata a ƙofar gidan sai mutum ya ƙwanƙwasa kana ta buɗe.

Rabuwa muka yi a hanyar da zata sada shi da sashin primary tare da yi mini fatan alkhairi nima nayi masa, ɗalibansa sai zubewa suke yi suna gaishe sa yana amsawa. Nima na ɗauki hanyar ajinmu, kamar jiya yau ma na ƙara mayar da hankali sosai ga darrusan da aka yi mana huɗu sannan aka fita tara, muna darasin ƙarshe principal da yaya Yusuf suka shigo ajin mu cikin basu cikakken girma malamin dake mana darasin ya basu hannun suka yi musabaha kafin principal ya fara yin da ya sanya ni jin kunya.
"Na'ima Muhammad Kabir, ɗalibar da aka kawo jiya matar aure ce don haka nake ji muku kashedi akan duk wanda aka kawo min ƙaran yayi mata wani maganar banza ya kuka da kansa, ga mijinta nan Malam Yusuf wanda duk kun san shi headmaster sashin primary".
Tsif ajin ya ɗauki shuru sai numfashin juna da suke saurara, har principal ya gama jawabinsa da faɗin"i hope you hear what i said?".

"Yes Sir".

"Good".

Ya furta suna ficewa tare da yaya Yusuf, darasin muka cigaba dashi sai dai na lura duk hankalin sauran ɗaliban yana kaina maza da mata, har aka ƙara ƙararrawar tashi na haɗa littattafaina cikin jakana muka fito tare da Maryam da Hafsat suka kallo ni fuskokinsu fal murmushi kafin Hafsat ta ce"Daman ashe kice matar da malam Yusuf ya aura?". Murmushi kawai nayi mata ta ɗaura da"A ƴan primary yake koyarwa amma kaf makarantar nan babu wanda bai san sa ba, yana da kirki sosai".
Murmushin na kuma sakar mata a karo na biyu, kafin Maryam ta amshe zancen da faɗin"Ai kuwa sai dai kiyi haƙuri ki yafe mana, domin musha gulmarsa akan rashin sakin fuskarsa musamman ga ɗaliban sakandiri mata, saɓanin ƴan primary da yake mayar da kansa kamar su idan yana koyar dasu. Duk rawan kan da ƴan aji shidan da suka gama suke yi akan sa ko kallo basu ishe shi ba, sanda aka kafe katin aurensa kowa mamaki yake da jinjina lamarin, don yanda muke masa kallon mai girman kai babu wanda yayi tinanin yana da budurwa har soyayya balle zancen aure, ashe ma ki ce". Ta ƙare zancen tana wurgo mini murmushin da sai da haƙwaranta suka bayyana.


Nima murmusawa nayi sosai har sai da ya bada sauti kafin na ce"kuma rashin fahimta ce yasa kuke masa kallon mai girman kai".

"Shiyasa muke neman afuwarki".
Dai dai nan muka isa bakin gate muka rabu dasu, ni kuwa na wuce sashin primary yana rufe ofishinsa na tarar dashi na dakata ya gama ya ɗan kallo ni kafin ya shiga faɗin"yanzu nake son zuwa nemo ki ai, na ce ko ɓacewa kika yi".
Ɗan

Please Login or Register in order to submit comment