Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

____________________________________

H.W.A

Page 0⃣7⃣


Sosai ƙirjina yake mini lugudan dukan tara tara sau tara, sai da na runtse idanuna da tunin suka wadato da ruwar ƙwalla, kafin nayi nasarar raba tsakanin haƙwara da suke karafɗiya da juna suna bada sautin ƙas ƙas ƙas kamar sabuwar haihuwar jinjirar kazar da ruwan sama yayi mata ɗan banzan duka.

"Yaya Majid, ba wai zan bijirewa su Abba bane, ko kuma na haucewa nauyin mu da yake kansu da suke ƙoƙarin sauƙewa. Wallahi karatu nake son komawa, ina son na koma makaranta ina son nayi karatu mai zurfi, ina son na zamto ma'aikaciyar aikin jarida kuma marubuciya, da silata zan kawo sauyi ga rayuwar MATAN AREWA".

Har na ƙare zancen na kai aya, bai ɗauke idonsa daga gare ni ba, sai da ya numfasa kana yace"karatu in kina rabo a cikinsa, ko kina ɗakin mijinki za ki yi ta. Mata nawa ne suka yi karatu har suka cimma muradin ransa ahalin suna gidaden mazajensu wasun suma uwaye ne masu ƴaƴa, abin kawai sa rai da kuma jajircewa yake buƙata".
Sosai maganganunsa suka ratsa ni, nasan duk zantukan nasan suna da nasaba da irin tunanin Umma da Anty Zakiyya, har nayi sare da malam Yusuf na sake reshe na gama ganye. Na kore malam Yusuf kuma na rasa tsayayyen da zan tsayar a gaban su Abba.

Wayyo zuciyata zafi take yi mini, raina yana mini soya, ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zai ɓalle ya fito waje bayan ya ratsa nama da fatana.

"Shikenan Yaya Majid, in sha Allah in ya dawo ya furta hakan a gare ni zan bashi dama".

Na ƙare zancen cikin karyewar murya, matso ni yayi sosai kana yace dani"Na'ima in sha Allah, za kiyi wannan karatun da kike da burin yin sa, da kaina zan yiwa shi Malam Yusuf ɗin magana akan hakan kinji kar ki damu akan wannan".

Kaina na gyaɗa masa, ya sakar mini da murmushi, duk da halin da zuciyata take a ciki sai da nayi dauriyar mayar masa da murmushi.

Ɗakin mu na wuce bayan na ratsa matan gidan mu kaf, cirko cirko a tsakar gida an haɗa wata rigimar da ban tsaya sauraran maƙasudin ta ba. Abu ɗaya da kunnuwana suka jiyo mini, kafin su fara jin dishi dishi shine furcin Hajiya.

"Yo wani dare ne jamage bai gani ba, ai duk abinda yake cikin ɗan tsako shaho ya daɗe da sanin sa, meye bamu sani ba kinyi ƙulle ƙulle Kubra za ta koma gidan Habibu ƙarki ta cimma ruwa".

Cakumo Umman su Anty Kubra da bata raina ruwan shuka, haka nan bata barin ta kwana, ta kaiwa Hajiya. Lokuta da yawa zafin ranta da rashin ɗaukar raini, ya sanya mutane da yawa tunanin ko ita ce mahaifiyata domin akan wannan halayyar munyi tarayya.

Salma kawai na iske zaune bisa kafitar mu, ta zagba tagumi da hannuwa bibiyu, bamu kula juna ba nayi wa kaina mazauni can gefe.

A hankali na lumshe idanuna, da suke mini wani iriyar zogi. Ina kamo duk wata addu'ar da taso bakina. Ko rufe idona nayi sai na hango kaina a matsayin ma'aikaciyar nan ta jarida kuma marubuciyar abubuaan da suke faruwa yau da kullum a tsakanin al'umma, mussamman akan matsalar MATAN AREWA. Abinda ya daɗe yana nukurkusan rai da ruhina kenan, ina ji a jikina idan ban sama damar da zan amayar dashi ba, ba zan sama sallamar ruhi da kwanciyar hankali ba.

Ƙarƙarfan ajiyar zuciya mai bada zazzafan sauti, ba saka ina fesa da iska mai ɗumi daga bakina.
Hayaniyar da ta sarƙafe a tsakar gidan, har tana neman kai Umman su Anty Kubra da Hajiya fitta da raini a tsakanin su, ce ta cigaba da gudana ina daga ɗaki nake jiyo tashin muryan Ummanmu tana aikin basu haƙuri, amma kamar tana yi da itatuwa don babu alamar ban haƙurin natan yana tasiri a gare su.

Sai da Baba ƙarami ya shigo ya daka musu birki, tare da kafawa Umman su Anty Kubra zazzafan kashedin ta kama kanta, ta guji tasuwar wata fitinan dafa gare ta domin matuƙar hakan ya afku zata ga zahirin fushinsa da kuma abinda zai iya aikatawa.

Ko wacce mata ta lafa, don sosai ake ji shakka da tsoron Baba ƙarami fiye da su Baba da Abba.
Har aka yi sallan zuhr na kasa tsinana komai nazo a gani, komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar dashi, ina iddar da sallah na nufi ɗakin Umma na sanar da ita duk yanda suka yi da yaya Majid da matsayar da muka tsaya.

Banyi mamakin jin abinda tace ba, domin dukkan wata uwa da ta tara ƴaƴa mata a gabanta, bata da burin da ya wuce aurar dasu ga mazajen ƙwarai.

"To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin hakan, ita ma ƴar uwarki Allah ya kawo mata nata rabon kusa".

"Amin amin ya Allah Umma".
Sai da na ɗan nutsa nace"Umma ya maganar Maman Walida kuwa?".

Sauƙe ajiyar zuciya tayi kana tace"Har yanzu dai maganar tana gaban mai unguwa zuwa anjima ma in sha Allah, Abbanku zasu je. An kafa masa sharruɗan matuƙar ba zai ɗauki ɗawainiyyar da Allah ya wajabta masa ba na ciyar dasu, sufatar dasu, shayar dasu kula dasu in wata lalurar ta taso ba. To za'a raba auren kawai sai dai ita Maman Walidan ne naga kamar taba son hakan, tafi ƙaunar cigaba da zama dashi cikin ƙunci da uƙubar iyayensa a gare ta".

Sai dana sauƙe abinda naji ya tukare mini ƙirji, na haɗiye wani miyau muƙut kana na sama sararin faɗin"To Umma ita kuwa meyasa ta zaɓawa kanta, cigaba da zama dashi?".

"Na'ima kenan nima kaina wani lokacin ina ganin gaskiyarta, rayuwar yanzu ya lalace, tarbiya tayi tsada ta kuma yi wahala yaya aka ƙare ma da ƴaƴan suna gabanka kana lura da shege da fitar su, ma yaya balle kayi nisa dasu. Ai sai abinda hali yayi, babu tsayayyyen uba akan su balle danginsa su sanya idanu akan su. Yanzu da take nan ma ba sauƙe haƙƙin su yake yi ba balle a bayan idonta, ai sai abinda ya wakana kawai. Amma duka har da yi mata tsirara a gaban ƴaƴanta kam ya zarce iyakarsa ya kuma kamata an fuskantar dashi girman kuskuren da yayi".

Lankwashe ƙafafuna nayi waje guda, ina sauraron Umma da kunnuwan basira, tunin curin ƙwaƙwalwar dake cikin kunyar kaina take ba wa zantukan Umma matsugina tare da yi musu kyakykyawan haddan zama daram daram.

"To Allah ya kawo mata sauƙi, Allah yasa mu dace".

"Amin".
Umma ta amsa dashi, tana karkara akalan zancen natan izuwa faɗin, zata sanar dasu Abba game da zuwan malam Yusuf. Duk jikina mutuwa yayi na miƙe da kunya na fice sumi sumi kamar munafuka.

Sai yamma na leƙa sashin Hajiya Babba, na tarar da ita ta kishingiɗa. Ficewa nayi na koma namu sashin raina duk babu daɗi hakan nan na nema walwalta na tsawon wunin na rasa. Sai da nayi sallan magrib na fito na kamawa Umma wasu aiyukan da suka rage bata kammala, tare muka gama komai na girkin kasancewar Umman su Salma ta gama nata kwanakin ya juyo ga Umma.
Sai da aka yi sallan isha'i, aka raba abincin na fara ɗauka ina kaiwa ɗaki ɗaki, kasancewar ko wacce mata ware mata kwanonta daban ake yi don basa haɗuwa suci tare, kamar yanda mu ƴaƴan gidan muke ci tare da sa'annin mu. Wanke wanke kuwa kowa na ɗakin su yake yi, ba'a haɗawa.

Na Hajiya Babba na kai a ƙarshe, na tarar da ita tare da yaya Majid daga kallon ta ke bina dashi, hakan ya tabbatar mini da cewar Yaya Majid ya sanar da ita zancen Malam Yusuf, ban zauna ba ina ajiyewa na dawo ɗakin mu.

Muka ci namu abincin, tsaf muka yi shirin kwanciya, Salma tana zaune gefe guda ta takure kanta lokaci zuwa lokaci take miƙewa ta ɗauki madubi tana duban fuskanta zuwa wuyanta tana shafawa.

Balkisu da ta gaza haƙuri sai da tace da ita"Wai ke ɗin lafiyar ki dai ko?, tun ɗazu kin wani canja".

"Ko dai tunanin barin gida kika fara tun yanzu?".



Kanta kawai ta girgiza hakan ya bani damar cewar"To menene? don tun ɗazu da rana kike cikin wannan yanayin".
Sai da ta numfasa kana tace"Abdullah ne".

Haɗe baki muka yi wajen faɗin"Menene ya faru, basawa yayi ko meye?".

Shuru tayi da hakan, ya sanya zuciyana zuwa wuya don ta kiɗimar damu, na cafko hannunta nace"menene yake faruwa, meye Abdallahn yayi, ko wani abun ne ya same shi?".

Sai da ta ɗan yi nisa, tace" ɗazu ne da ya zo zance yazo min da wani magana, wai gaskiya rama ta tayi yawa shi ya fi son mace mai ƙiba, dole nayi ƙiba kafin a kai ga ɗaura auren mu".

Sakake nayi ina bin ta da na mujiya har ta kai aya, na sama damar faɗin"To ke kuma meye kika ce masa?".

"Na'ima meye kuwa zance dashi, shi ne fa wanda zan aura na amaa masa akan zanyi iya yi na naga abinda yake so ya samu, amma na rasa wata hanya zanbi ko maganin ƙiba zan fara sha irin zumar nan?".

Abinda na gaza ganewa, maganarta ta ƙarshen neman shawarin mu take yi, ko ko sanar damu matsayar ta take yi oho.

Kafin nayi wata maganar Balkisu ta tari numdashina da cewar"Tabɗijam yau ina ganin abinda yafi ƙarfina".
Sausauta amon muryata nayi kana nace"Salma ki kwanta da hankali, wannan ba abinda za ki ɗagawa kanki hankali bane, ki sanar dashi cewar wannan abinda yake so ɗin ba za ki iya yi ba. Cikin sigar da zai fahimce ki, to shi tun da can bai gano ramar takin ba sai yanzu. Da aski yazo gaban goshi, idan kika je za ki biye masa akan hakan to wataran ke kanki gabaɗaya ce zai ce ba ki yi masa ba, to a sannan kuma sai kiyi yaya kenan?".


Shuru ya ɗan ratsa tsakani ina mai saka ran cewar kalaman nawan zasu yi tasiri, dan da dukkan alamu suna aiki a jikin Salman yanda tayi shurun nan.

Doguwar tsakin da Abasiya tayi, shi ya sanya ni kawar da idona daga karantar yanayin fuskar Salma da nake yi.

"Aikin banza, ki biye mata ke kuma tunda ƙwaƙwalwarki an sanya dusa an toshe ta, har wani wai kice masa abinda yake so ɗin nan ba za ki iya ba, tana so dai ta guntule miki alaƙar nakun ne ki shekare a gida kamar yanda Anty Zakiyya ta share wajen zama a cikin gidan. Ni wallahi a yanzu da ake gab da sanya mana rana da Sagiru, babu abinda zai ce nayi wanda bazan yi shi ba, don jina nake yi kamar matarsa".

Sosai maganganun natan suka dokin raina, sai dai nayi ƙoƙarin danne zuciyata da take tafarfasa na kallota nace"To ai idan har soyayyar da yake ikirari yana mata, ba a iya leɓɓansa bane har zuciyarsa ya ratsa. Ba zai taɓa cewa da ita wai dole sai tayi ƙiba ko kuma dole tayi fari ba, shi soyayyar gaskiya ba ruwansa da wannan".

"Ahayye nanaye, to har ke me kika sani game da soyayya?, har yaushe kika samu wanda yace yana son nakin ma ko daga safiya zuwa yanzu ne duk malam Yusuf ɗin ya koyar dake wannan karatun?".

Naso mayar mata da martani, sai na tuna ko ba komai gaba take da ni domin Umma ta labbarta mini cewar kwanaki huɗu cur ta bani, ni kuwa ranar raɗin sunana aka haifi Salma, ranar da aka yi arba'in aka haifi Balkisu.

Murmushin da naji ciwo da raɗaɗinsa ya ratsa dukkan jikina, nayi mata kafin na maido da dubana izuwa Salma nace"To kinji dai nata shawaran, don haka ya rage naki ki ɗauki wanda kike ga zai zamto miki mafita".

Ina dasa aya a nan na miƙe izuwa ɓangarena, nayi kwanciyata hawaye suna mamala daga idaniyata, ranar dukkan darena amfani nayi dashi wajen tsayiwar dare ina yiwa Anty Zakiyya addu'ar Allah ita ma ya fito mata da miji, ko ta samu ta huta da wannan rayuwar.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________

H.W.A

Page 0⃣8⃣


Wayewar safiyar ranar na riga kowa tashi, tsaf na kammala dukkan abubuwan da suka kallafa a kaina kana nayi shirin islamiyya.
Sai da na biya ta ɗakin Ummata, na gaishe ta kana na leƙa ɗakin su Anty Zakiyya na tarar da ita tare da Anty Kubra, muka gaisa kana na fito wajen su Balkisu.

Har mu kai ga ƙofar fita, na jiyo murnar Umman su Anty Kubra sun sauƙa a kunnuwana.
"Ke Na'ima wuce ɗakin gwauruwar nan ki ƙira min Kubra".

Cak na tsaya, sai da na ɗauki daƙiƙu kana na waigo cike da rashin fahimta nake bin ta da kallo"wacece haka?".

Sai da ta tsirka mini da wata tsaki mai dogon zango, alamar a zuciye take kana tace"wace kuwa da ta wuce Zakiyya, akwai wata gwauruwar ce da ta ɗara. Ɗaki kowa ya watse ya barta ta mallake shi".

Taƙaitaccen murmushin gefen baki nayi, duj da naji zafin maganar natan ta ratsa ni, amma kaina kawai na jijjiga na wuce ɗakin Anty Zakiyya.

Har na sanya ƙafata ɗaya a cikin ɗakin, na jiyo dariya da shewar da su Abasiya suka saka suna tafa hannu, ban jiyo ba balle idanuna su ƙara gano mini wani abinda da zai ƙara harzuƙa ni.

Saƙon Ummanta, na sanarwar Anty Kubra nayi ficewa ta. Na tarar da har sun tafi sun barni don haka ni ɗaya na isa islamiyyar.

Har an fara darasi sanda na isa aji, na nema izni daga Malam Yusuf kana shiga na zauna a wajen zamana na ko yaushe ina fitto da littafina daga jakata.
Sosai na fahimta darasin na yau, don duk wata tambayar da aka yi ni na amsata.
Yau ma sai da aka ƙara tattaunawa akan walimar sauƙar mu, domin sai ƙara gabatowa yake yi, ga mai rai kam ma ya iso.
Harhaɗa littattafan mu muka yi, kasancewar lokacin tashi yayi har na kai ƙofar ficewa daga cikin islammiyar na jiyo dirin mashi mai ƙafa biyun malam Yusuf.

Ban waigo ba illa sausauta tafiyar tawan da nake yi, har ya iso sallama yayi mini na amsa a hankali kana na gaishe shi.

Murmushi yayi sai da wushiryar dake tsakankanin haƙwaransa suka bayyana, kana yace"Naga ai mun gaisa a aji ko?".

"To ai gwara yawan gaisuwa da yawan faɗa".

Jinjina kansa yayi"Bana son magana da mace a kan titi, kuma kema nasan hakan ba girmanki bane, yaushe kike gida nazo?".

Sai da na ɗanyi jim kafin nace"Ni ko yaushe ina gida, bama fita in ba islamiyya ba ko aike".

"To shikenan in sha Allah zuwa yamma zanzo".

"Allah ya kawo lafiya".

Da alama yaji daɗin gajerar addu'ar tawan da bata yawaita tsayi ba. Don har wani rausayar da kai yayi kamin ya amsa da amin. Muka yi sallama, da mamakina na isa ɗakin mu ban tarar da su Salma ba, ban kawo komai a raina ba don tinanina ko suna ɗakin uwayensu.

Don haka na wuce sashin Hajiya Babba, kamar kullum na iske ta kishingiɗe tana tasbihi da ƴan yatsun hannayenta.
"Takwara har kun dawo?".

"Haba Hajiya har ne ma?, ko don ba kya kike zuwa ba?".

"Har ne mana, dududu awanni nawa kuke yi?".

Kawar da zancen nayi ta hanyar yin murmushi ina yin ƙasa da kaina, kafin na fara yi mata tausa a ƙafafunta a hankali.

Cikin nutsuwa ta ƙira sunana, na amsa kaina yana duƙe.

"Jiya Majid yazo min da wani zancen da ya faranta min zuciTunin na sha jinin jikina, na kuma gano inda maganganun natan suka dosa. Don haka na ƙara nutsuwa da bata hankalina sosai.

"Takwara ina fatan kema ki mashe shi hannu biyu biyu, Allah ya sani da wannan damuwar nake kwana na tashi cikin raina, kullum du'a'ina bai wuce kema Allah ya fito miki da miji ayi tare da ƴan uwanki ba, sai gashi Allah ya amsa addu'ata".

Sai da na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya, kana nace"in sha Allah, Hajiya zan amshe shi kamar yanda kuke so anjima ma yace mini zai zo".

Na ƙare zancen ƙarshen ina matse ruwar ƙwallar da suka ciko kurmin idaniyata, duk wannan abun da ake tayi babu wanda ya tambaye ni ra'ayi na game da wannan haɗin, ko inna son shi, ko bana son shi, ko zan iya zama dashi ko akasin hakan oho. Kowa kawai burinsa na amshe shi kar na zaune a gida kamar Anty Zakiyya.yana, har ga Allah kunnuwana sun daɗe basu jiyo min daddaɗan labarin da ya sanya ni cikin farin ciki ba kamar zancen da Majid yazo min dashi jiya".

"To menene haka kuwa Hajiya?".

Sai da ta ɓantari guntun goronta, da ta since daga bakin zaninta kana ta ɗaura da cewar"Zance ne akan ki, da wannan malamin islamiyyar takun da nake jin sunansa a bakin su Balkisu. Yazo nan gidan ya bayyana manufarsa akan ki ga Majid, kuma in sha Allah yau iyayenku maza za'a sanar dasu domin a fara bincike a kansa".


"In sha Allah zamu tattauna da iyayen nakin".

Kaina kawai na ɗaga mata, ina mai cigaba da yi mata tausan a nutse ta yanda za ta ji daɗinsa.
Sallamar su Abba ya sanya ni watsa idanuna a ƙofar ɗakin har suka shigo dukkansu tare da Baba da Baba ƙarami suka zauna.

Sannu da shigowa nayi musu, suka amsa sannan dukkansu suka same daga kan kujeran da suka zauna suka gaida Hajiya, fuskarta kamar gonar auduga take amsa gaisuwar ƴaƴan natan cike da annurin da ya kasa gusawa daga kan kammalalliyar fuskarta.

"Daman yanzu nake son, a aika Majid ya ƙira min ku, sai kuma gaku daman wata magana mai muhimmanci nake son mu tattauna tare".

Gyara zama duk suka yi suna sauraron ta da kunnuwan basira, hakan ya bata damar ɗaurawa da cewar"Dama magana ne akan Na'ima".
Ina jin hakan na miƙe sumi sumi zan fice, Hajiya tace na dawo na zauna tunda magana ake yi a kaina.

"Akwai wani yaro malamin islammiyarsu ta safe da yazo gidan nan jiya, ya kuma bayyanawa Majid cewar tayi masa inda za'a bashi dama tabbas zai aure ta, ita ma kuma ta amsa akan yayi mata shine nake son ya gabatar da kansa a wajen ku ayi bincike. Idan an same sa d nagartattun halayya, kuma ya sama shaidar ƙwarai daga mutane sai kawai a bashi damar tuto iyayensa ayi a wuce wajen".


Sosai Baba yake sakin hamdala wata na bin wata kafin Abba da Baba ƙarami suma suk amshe.

"Alhamdulillah masha Allah, haka ake so ai idan ya ƙara zuwa sai kice dashi muna son ganin sa kinji ko?".

Kaina na ɗaga masa alamar naji, sai da na nema iznin tashi daga gare su, kana na fice bayan Hajiya tace dani na ƙira Ummata tazo.

Ɗakinta na nufa na iske ta da wata baƙuwa, na sanar da ita ƙiran da Hajiyan take yi mata. Kana na koma ɗakin mu, na zauna na daɗe a zaune ina saƙa da warwara a cikin raina, tare da tinanin makomar rayuwata da burin dake danƙare ƙasan raina.

Ganin zaman ba zai amfane ni da komai ba, ya sanya ni tashi naje ɗakin yaya Majid. Nayi sallama yafi sau huɗu sai a an biyar ɗin ya amsa.

Na shiga yana kwance ya na sauraron wayarsa, saman katifar nasan na zauna kana nace"Tun ɗazu nake sallam baka ji ba,na ma yi tunanin ko bacci kake yi".

"A'a ba bacci bane yi ba, wallahi wannan program ɗin nake saurara, shi ya ɗauke min hankalina".



Kaina na leƙa wayar tasan wasu mata ne biyu sun sha ado, fuskarsu sai ƙyalli take yi an zirara musu irin kwalliyar nan ta zamani.

Gefe kuwa wasu mutane ne, uku biyu maza ɗaya mace. Bansan sanda na buɗe baki ba ina binsu da kallon sha'awa Allah ya sani ba kaɗan ba suka burge ni.

"Yaya Majid su wanene waɗannan?".

Sai da ya murmusa yace"Wannan ta farkon BADARIYYA TIJJANI ALARAWI kenan, mai jan mayafin kuwa MADINA ƊAHIRU MAISHANU sunanta, ƴan jaridu ne ma'aikatan shashin hausa na Bbc hausa".

Kaina kawai na ɗaga masa kamar ƙadangariya har ya kammale zance nasan, na ƙara bin su da kallo lokaci guda ina ƙara jin soyayyarsu tana ƙara girmama da yaɗuwa a cikin raina, ban sani ba ko don ƴan jaridu ne abinda raina yafi soyiwa kenan a kaf aikin duniya. Kuma gasu mata jajirtattu akan aikinsu kamar yanda yaya Majid ya ɗaura da bani taƙaitaccen labarin su da irin aikin su.

Ƙwala mini ƙiran da Anty Zakiyya take yi, shiya katse mana zancen na fita. Tunda nayi sallan asr bugun da ƙirjina yake yi ya tsananta da bansan dalilin hakan ba, gabana sai faɗuwa yake yi.

Ina zaune a ɗakin mu, Nurain ya shigo da gudun yana faɗin"Anty Na'ima wai ana sallama dake a ƙofar gida".
Tunin ƙirjina ya fara gudun famfalaƙi, na sanya hijabina na fita, inda ya tsaya jiya na iske shi na isa da sallama ɗauke a baki na.
Fuskarsa yalwace da wannan kyakykwan murmushin, da duk saSosai na nutsu ina wasa da ƴan yatsun hannuna.
"Na'ima alal haƙiƙa tunda na fara koyarwa a islamiyyar nan, na kamo da soyayyarki kuma idan kika bani dama na sama karɓuwa a gare ki babu abinda zai hana ni mallakan ki na killace ki a cikin gidana, a matsayin matata".
Sai da ya sausata amon muryarsa, yana karantar yanayina can ƙasa yace"Ina sonki Na'ima, kuma ina fatan na sama karɓuwa a gare ki, ba zan cutar da zuciyarki ta hanyar tirsasata zama da ni ba komai za'a sai da amincewa da kuma yardanki".nda yayi ta take ƙara fito da asalin kyan fuskar tasan. Ya amsa sallamar tawan.

"Na same ki lafiya, ya kuma mutanen gidan?".

"Duk lafiya ƙalau".

"Masha Allah".
Shuru ya ɗan ratsa kana yayi gyaran murya, yana ɗaura da"Na'ima haƙiƙanin gaskiya na daɗe ina son sanar dake gaskiyar wani lamari, amma harshena ya ƙi bani haɗin kai wajen furta hakan a gare ki".


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________________


Page 0⃣9⃣


Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe, cikina yana bada ƙara ƙululu, sai dana fizgo numfashina kana nayi jarumtar faɗin"Na baka dama Malam, domin a zuwa ɗayan da kayi ƙofar gidan nan duk iyayena sunyi na'am da kai, sun kuma yaba da tsarin nutsuwa da hankalinka har ma da sanin ya kamata. Duk da kowa ba'a gano hakan a haɗuwar farko amma sun yarda da kai, bani da zaɓin da ya ɗara nasu don haka nima na aminta da kai".

"Zaɓin kanki da kanki, kunnuwana suke buƙatar ji daga gare ki, shin har cikin zuciyarki kin aminta da ni da kuma soyayyata, ko kuma kawai za ki yi biyayya don iyayenki sun amince dani?".

Sosai tambayar tasan tayi mini nauyi, gami da wahalar amsawa sai da na haɗiye wani miyau mai ɗaci da ɗacinsa naji ya gauraye duk wata kusurwa na cikin bakina. Kana na soma faɗin"Malam nima kaina na aminta da kai, sannan shaida ce akan kyawawan halayya da ɗabi'unka, ban taɓa soyayya ba sannan ban taɓa amincewa da wani saurayi ba sai kai don Allah kaji tsoron sarkin da ba'a ɓoye masa komai, masanin sirrukan da suke ɓoye dama na zahiri idan ba son gaskiya kake mini ba kar ka ɓata mini lokaci ka cutar dani".


A raunane na ƙare zancen ƙarshen, ina duƙar da kaina ƙasa don wasu zafafan hawaye ne suka taho mini.

"Na'ima ɗago idonki, ki kalli cikin idona domin a nan ne kaɗai za ki hange amsar tambayarki, ina sonki da dukkan gaskiyata sannan kuma so irin na aure".

A hankali na ɗago kaina nayi masa kallon ido cikin ido, sau ɗaya na janye nawa ina ƙoƙarin saisaita kaina da tare hawayen da bansan dalilin kwaranyan su ba a wannan sa'ilin, abu ɗaya da zuciyata take kimtsa mini shine burina nason yi karatu, zama marubuciya da kuma ma'aikaciyar jarida shikenan ya zamto mafarki kenan.

"kin yi shuru?".

Figigi na dawp daga tunani mai zurfin da na fara zurmawa, ina ƙaƙalo murmushin dole na dasawa fuskana, a ƙoƙarin tabbatar masa da kore masa kokanto da samar masa da nutsuwa akan babu komai.

"Su Abba sunce suna buƙatar ganinka idan kazo".

Fito da idanu waje yayi haɗi da cewar"Allah yasa ba kashedi za ayi min akan har na ƙara zuwa wajenki ba, ko kuma ace anyi miki miji zuciyata ba zata iya ɗauka ba".

Taƙaitaccen murmushin gefen baki na saka, ina ƙara mamakin Malam Yusuf duk tsarewarsa a cikin aji sanda ya fara koyarwa a makaranta babu yarinya ta ya taɓa buɗewa haƙwaransa da sunan dariya, hakan ya sanya har yanzu da yawa suke masa kallon mai girman kai.

"A'a ba haka bane sun dai ce suna buƙatar ganin ka".

Na faɗa ina masa nuni da hanyar shiga gidan, raina maƙil da mamakin yanda ya saki jiki da baki yana wannan zantukan, daman

Please Login or Register in order to submit comment